in ma ya
kama yayi wa Munceban fada ne a gabanta yana
yi in ya so idan suka shiga daki sai ya lallashi
matarsa tunda ya san yawanci ita akc kwara, idan
abin ya ci tura sai ya dangana da kiran Adda
Fadima a waya don ta zo ta taya shi lallashi.
Yauma haka ta kasance bayan sunci
abinci sun gama, yacc, "Tashi ki shirya mu je
anguwa". Ya yi shirin fitar ta su ne don yasa mai
walwala. Tace, "Iana kuma zamu da daren naan,
baka bari sai gobe ido na ganin ido mujc “, yace
"ke dai shirya yanzu nake sin muje". Ta tashi ta
shiga dakin baccinsu ta sako jibi bisa atamfar
dake daure a jikinta ta fito tace, "na. shirya
muje". Suka fito suka rufe sasansu suka shiga
WATA KUSAN nde Rahmatu Hassan Zaria
suka yi wa Goggo sallama cewa za su anguwa ta
dube sutace, "Da đareni na ku kuwa ina zaku je?"
nyace,bg lneg n eua!
AT"Za mu je can gidansu Baffane za ta yi musu
sallama gobe/idaizanowucc za mu tafi tare"
Goggo tace/"Au zaka tafi da ita gobe shine baka
gaya min ba sairyanzu da na tambayi inda za ku
jeplallaiMujeebu dabi'unka sun canza". Yaсe,
i "Kiyi hakuri Goggi da bań shirya tafiya da ita
ba Hajiya ce ta damu ba su ganta ba kwana biyu
tunda zanzo taceinzo misu da ita, ni na ma
imanta shine dazu talyi mini waya take tuna mini,
kin galai babu abinda za ta ce tana so in kasa yi
mata, ko ke za ki ce ban kyauta ba", tace "Ai fa
ga ka dariya kare kanka, wannan hujjar ta shiga,
shike nan sai kun dawo"
ima ed Gidansu ya fara kaita dama ya dade bata
jo ba tana ta yi masa nacin za ta je don tana
kewarkistInnarta da Kannenta amma ya dinga
share zancen sa yau da ya yi niyya don kansa;
bata san døn ta samu walwala ya yi mata haka ba
danoya san zatassamu müddin ta ga innarsu da
'yaniuwantan da baban ta da take mararin son
ganinsa.ni ndansg 8
Yana biye a bayanta suka yi salama suka
shiga gidansua tskar gida suka iske matan gidan
tawbinsu ta gaishe isuuran ta bar Mujeeb suna
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gaisawa ta wuce dakinsu. A gado ta ga Innan a
kwance sallama kawai ta yi ta isa kanta tana
taımbayar "Lafiya Innarmu na ganki a gado? Ba
dai har zaki yi bacci bane haka da wuri". Та
yunkura ta tashi zaunc tana cewa, "lafiya ta
kalau gajiya ce kawai nayi, yau na yi ayyuka da
yawa. Daga ina kike da daren nan?" tacc, "daga
gida muke ni da Yaya Mujeeb ne, gaya nan
shigowa", tana cikin gida Innan ne suka ji
sallamarsa daga falo suka fito, ya risina ya gaida
Innan ta amasa cike da sakin suka ta cc, "ashe
baka koma ba?" Yace, "Eh, ban koma ba sai
gobe, tare da Munceba ma zamu tafi shi yasa
nace a bari mu zo tayi muku sallama". Tace,
"Goggon taku ta yarda ka je da ita nc?, yace
"E, ta yarda, ni ma can su Hajiya suka damu in
zo musu da ita, wai ta kwana biyi bata je ba sati
na sama tarc zamu dawo". Tace, "To Allah ya
kiyayc hanya don Allah a gaishe mana da su idan
an je". Yace, "Za su ji Insha Allar
Sun dan yi hira sanan yace Mustafa ya
koma ne?" Inan tace, "Shima paji yace gobe zai
koma yanzun nan ya fita, ina jin yana dakinsa".
Mujeeb ya mike yacc "Bari in ganshi in bai fice
ba".
Yana fita hira ta 6arke tsakanin uwa da
'yarta, cikin hirara ne Munceba cike da damuwa
146
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
take labartawa Innarsu irin gorin rashin haihuwa
da Goggo ke yi mata da abinda ya faru yau da
aka zo áka ce mata wata da aka yi aurenta а
bayan na su ta haihu. Inna ta girgiza kai tace,
"Shin sau nawa zan gaya miki ki daina
damuwa da surutan batanci irin na Goggonku,
kuma sai nawa nake miki nasiha kan ccwa ki
dauki hakuri da kaddara da ta sauka a kanki ta
rashin haihuwa? "Shi fa duk abinda kika ga
mutum ya samu a duniyar nan arzikin kudi ko
arzikin 'ya'ya to Allah ne ya nufa zai samu, idan
kuma bai nufe ka da samu ba to duk duniya nan
babu wanda ya isa ya baka", sannan idan Allah
ya baka to babu mai hanaka wannan abin da ya
baka ki sa wa zuciyarki hakuri da dangana ki yi
ta addu'a idan rashin samun haihuwarki shinc
alheri a garcki to Allah ya baki ikon cin
jarabawar da Allah ya yi miki. "Idan kuma kina
da rabon za ki haihun to Allah ya baki masu
albarka"
In banda abin mutane shin yaushe ma aka
yi daren balle gari ya wayc? Kuma haihuwar nan
ai ba ke za ki ba kanki ba, in da ke za ki ba kanki
ai da tuni kin ba kanki ko don gorin da Goggonki
ke miki ki cire damuwa a ranki, ki ci gaba da
walwallarki in ba haka ba ki je ki jawa kanki
ciwon damuwa babu gaira babu dalili, inda sabo
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ma ai ya kamata a ce kin saba da ire-iren
wadanan halayyar na Goggon, meye jiya ta yi
bare yau, ni mayye ba ta mini ba da na yi biris da
halinta me ya tsunkuni namana? "To ki ci gaba
da hakuri da zama da ita wata rana zai zamo
labarai".
"Haka innarsu ta yi ta mata nasihohi da
misalai na mata masu hakuri da kuma irin ribar
da suka samu a dalilin hakurinsu, har Mujecь
suka shiga tare da Mustapha daga gidan har
gidan Adda, Fadima suka je daga nan ta rokeshi
da ya kaita gidan kakarsu wato mahaifiyarsu
Innarta da suka ki Daddi wadda ke can a ruga, ya
dube ta yace, "Dadaren nan za ki samu shiga
daji, so kike tsofaffiin samarinki na rugar su tare
ni su kwakkwabde ni ko dan haushi na suke ji na
aurc musu buduwa". Ta yi murmushi taсс,
"waya cc maka ina da samari a rugar nana? Ni
an gaya maka ma ina kula samari nc?" Yana 'yar
dariya yace, "A dai bar kaza cikin gashinta", ya
karkata mashin dinsa zuwa rugarsu Diddi
(mashin din abokinsa nc).
A zaunc bisa katifa ta iskcta ta na
mutstsika man zafi a kafafuwanta. Munccba ta
zube wa 'yar tsohuwar a kafafu ta rungume ta, ta
soma tureta tana ccwa "Ni dagani kada ki karya
min kafa ki bar ‘ya'yana da daukan kasha don
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
dai su ne zasu yi jinya ta ke kina can gidanaki da mijinki". Duk suka yi dariya Muneeba tace,"Allah iyayena ba zasu yi jinyar kasha aba sai dai 'yar warki ta zo tayi jinyaki". Mujeeb ya
zuana daidai kafafun Diddi ya amsi mana ya lakuta sanana ya dubi Muneeba yace, "Ke daga
min kafar amarya idan kika karyata kin kwari
kanki don nana zan dawo in tare inyi jinyarta sai
dai ki biyoni manana mu zauna". Ta tashhi tana dariya tace,
"Bari in tashi kada na tun bn karyata bata
langwabe tace ta karye tudn ataji yau itace amarya".
Bayan gashe-gaishe ne Diddi take musu fadan me yasa suka zo da daren nana ko rsoro
bas a ji, suyi su zo su tafi gashi goma ana dare ta kusa. Sun gaya mata dalilin ziwansu. Ta tashi ta dinga bubbude kwanuka da korai ta hado kaya rankatakad a babbar leda ta mikawa Muneba
tace,
"Gashi nan kyayi wa su Hajiyar tsaraba, ba kya je hannu salin alin ba, mai sonka ai ya gama maka komai. Innarku ta baki wani abu ki kai
masu ko?" ta ce "Eh itama ta bada su kuka
daddawa da kubewa da sauran tarkace a kai
musu ga su can a bayan mashin". Diddi ta ce,
"to gasu mana sai ki hada musu a gaishe su da
149
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kyau a gaida Alhajin". Suka ce "Duk za su ji da
yardan Allah".
Mujceb da zasu fafi ya laluba aljihunsa ya
ciro kudl ya mikawa Diddi yace, "Ga wannan ki
yi cefane kafin in dawo, ai zasu isheki, ko da
yake ba kya girgki". Ta amsa tayi godiya 'yar
tsohuwar nana da yake garau take jin kanta har
kofar gida ta rako su ta ga tafiyarsu sannan ta
koma cikin gida. Diddi kenan 'ya'yanta su Inna
da Inna Amina da sauransu haka suka taso suka
ji kannenta na kiranta diddi suma su sake kiranta
da hakan, suma nasu 'ya'yan wato jikokinta su
Muneeba suke kiranta da hakan, kusan kowa ma
Diddi ya ke gaya mata. Tsohuwace lafiyayya ko
da yake 'ya'yanta sun tsayu a kanta suna ginata
da kayan dadI, cima sai wadda ake so suke bata
haka ma sirikanta matan 'ya'yanta sa ji da ita, a
dalilin ita ma ta rikesu tamkar itace ta haifesu.
150
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Shckaru uku da watanni kenan da auren su
Munceba, cikin wadannan shckarun abubuwa da
dama sun faru na farin ciki da na bakin ciki, na
farin ciki da na bakin ciki, na farin cikin da ya
same su shine kammaluwar karatunsu dukansu,
ita ta gama kartunta na sakandire kuma har
sakamako ya fito ta samu mafi kyawun
sakamako har ta zana jarabawar (JAMB) shima
ta sami point din da ake so yanzu shirye-shirye
tafiya jami'ar Gombe take yi inda mijinta ya yi
Federal University Kashere shi kuma nasa abin
farincikin ya kammala bautar kasa shi da Yusuf
wani aminin Alhaji ya sami masu aiki a
mabanbantan gurare kowa cikinsu ya fara aikinsa, sannan ga katafaren shago na hadaka shi
da Yusuf da suka bude na sayar da zannuwar atamfofi da leshina da shadda a babar kasuwar
Gombe, a wannan lokacin duk sun mallaki
motocin shi Mujeebu har ya kammala kerarren
gidan sa na nan Gombe a Unguwar Buhari estate
yanzu haka ma yana shir-shiryen dawo da
Muneeba ne tunda zata fara karatunta a Gomben
don ma Goggon tana ta ja musu tsaiko ne da tuni
sun tare.
Abin bakin ciki kuma da ke damunsu
tuna ci mus tuwo a kwarya kuma ba ya wuce
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
irin gori da bita kulli da gwarza ba da Goggo ta
saka Muneeba a gaba dasu na rashin haihuwa,
babu abinda ya fi tada wa Munecba hankali irin
farin cikin da take yi na gorin rashin haihuwar
wai lallai-lallai sai Mujeebu ya kara aure tunda
yana da arzikin da zai iya aje mata hudu ma ba biyu ba, shi ya sa ta dage dole sai ya auri
Suwaiba 'yar aminiyarta Haj. Harira don yanzu
ma ya kamata ayi aurensu a cewar Haj. Hariran
tunda yana da abin hannunsa, take gayawa
diyarta anya kuwa ko anyi auren ba wata tsiya
zata tsinta ba tunda karatu yake yi, ita ma karatu
ta ke yi, yanzu kuwa ta gama shi ma ya gama
nasa har ya sami aiki, sannan ga taura biyu da ya
hada a baki yana tsotso, aikin gwabnati da
kasuwancu shi yasa farat daya arzikinsa ya
bunkasa, ko motar da yake hawa idan ka kalla
kasan ruwan arziki ya sauka a gidansa.
Wani zuwa da Mujecb ya yi ya sami
Goggon yana tuntubarta game da komawarsu
Gombe ya kara da cewa, "Kinga Goggo ko
auren zanyi ai ba nana zan aje matar ba dole
Gombe zan kaita tunda can nake aiki shi yasa
nake son mu fara komawa in yaso maganar aure
sai ta biyo baya, in ba haka ba jama'ar gari ai sai
su zage ni ace na yi gida ban saka matata 'yar
uwataba sai da zan yi aurc sannan zan ce ta
152
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
koma". Goggo ta tabe baki tace, "Zagi? Jama'a
sun dade ba su zage ka ba, kaine kake shayin
zagin jama'a nan da ka ganni da zagi yana tsiri
da yanzu ya firfito mini, amma da yake bana
shayin uban kowa me ka ga ya same ni, kawai
dai zan barka ka tare dama ai ni ina bakin cikin
ace wannan katafaren gida mace daya jallin jal
ce zata,zauna a cikinsa ba abokiyar zama ba yara
'yan bari bari ai kaga arziki baiyi ba, amma
yanzu tunda ka amince zaka kara auren to ni ka
amince zaka kara auren to ni ka gama min komai
ka faranta mini rai yanzu zan yi waya in
shaidawa Haj. Harira ta soma shiri bikin 'yar
lelenta ya zo". Ya yi saurin tarar numfashin
Goggo yace, "A'a kada fa kice mata tayi shiri
yanzu don abin ba na gaggawa ba ne, mu bi
komai a sannu gaggawa aikin shaidan ne tunda
nace zanyi ai zanyi ne", shi kam ya fadI zai yi
auren ne don Goggo ta sakar musu mara su yi fitsari, su tare a gidansu in yaso daga baya ya san zilliya-zilliyar da ya yi ya zille wa auren.
Yana shiga dakinsu ya suri Munccba
yana juyi kyalkyatar dariya. Ta kankame shi tana
cewa, "Yayana wai me ya sa ka murna ne haka,
har ka yamutsa min 'yan hanji, sauke ni jiri nake
ji". Ya direta kasa ya zauna sannan ya janyita ta
zauna a jikinsa yace,
153
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Goggo ta amince duk sanda muka gama shiri
mu koma gidanmu na Gombe". Tsallen murna ta
Kara yi sannan ta rungume shi tana tsallen murna
tana tambayarsa,
"Yaushe tace zamu koma?" yacc,
"Sai lokacin komawa tana gurinmu shine nake
son mu yi shawarar lokacin da ya dace, ni dai
kinsan na gama sa kayan falo na da bedroom
dina kece ya rage baki amso kayan gadonki da
kujeru ba". Ta ce "ai na gaya maka akwai
balance din da zan basu sai in amshi daman a
barine sai an sa ranar tarewar sai muje in anso".
Yace, "nawa ne balance din na fa manta?" tace,
"Dubu dari biyu ne ya rage", ya се,
"OK gobe sai mu je Gombe mu kai musu
cikon mu amso, duk dai wani shirye-shirye ki yi
shi cikin satin nan sati na sama sai mu tare ranar
asabar Karshen wata kenan", tace,
"Allah ya kaimu lokacin, na gode da
kulawarka a gare ni, da irin dawainiyar da kake
da ni, Allah yay budi ya tsaremin kai". Ya
janyota jikinsa ya rungume yace,
"Nima ina godiya da dawainiyar da ki ke da ni
da kulawar da ki ke bani, Allah ya barni cikin da
kaunar juna ya bamu abinda muke nema duniya
da lahira".
154
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Fadin kalmarsa ta karshe ne yasa ta fara
hawayc, ya kai hannunsa ya lakuci hawaycn
yace, "To meye abin kuka kuma?", tayi ajiyar
zuciya tace, "a kullum ina rokon Allah da ya
bani haihuwa, don duk abinda zan yi maka ka yi
farin ciki ba zai kai farin cikin in Haifa maka
'ya'ya ba, domin su ne sanyin idaniya a garemu,
sannan in huta da gorin da ake mini na rashin
haihuwa, in fita daga kangin da nake shiga idan
na ji an furta dole sai ka kara aure tunda ni har
yau ban haihu ba tsawon shekaru hudu da
aurenmu", ta ci gaba da sharen hawaye da ke
ambaliya a kuncinta. Mujeeb ya kara matseta a
jikinsa yace,
"Sau nawa zan gaya miki ki cire damuwar
rashin haihuwa a ranki, kin taba jin na yi miki
gorin baki haihu ba?" ta girgiza kai ya ci gaba
"ko a taba canza miki wani yanayin
mu'amalarmu ne, nan ma girgiza kai tayi, yace,
to ki kwantar da hankalinki tunda mu jejje asibiti
sun dubaki sun dubani sun tabbatar mana
dukkanmu lafiya kalau muke loakci ne kawia bai
yi ba da zamu haihu, idan lokaci ya yi zaamu
ganki dauke da ciki, kai wallani ko cewa suka yi
daga gare ki matsalar take ba za ki haihuba zan
zauna da ke har karshen rayuwarmu balle sunce
mahaifark: afiyarta kalau, to me zai damcki, duk
155
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
wanda zai yi miki gorin baki haihu ba ki kyale
shi, tunda ba shi zai bakiba Allah ne zai baki shi
za ki kaiwa kukanki, kuma In Shaa Allahu za ki
Haifa min 'ya'ya masu albarka"
Haka ya ci gaba da lallashinta har sai da
ya ga ta sami natsuwa, sunci gaba da shiryeshiryen suna komawa sabon gidansu a Gombe.
Washe gari suka tafi Gombe gidan
Mamam Amina suka sauka. Sai 'yan biyu ne
gida Sadiq ma yana gidan duk suna main falo har
da Mama Amina. Shigowar Muneeba falon 'yan
biyu suka hau ihun murna suka rungumeta, jin
tare da mijnta take ne yasa Sadiq ya silale daga
falon.
A gidan Muneeba da Mujeeb suka yi
Sallar azahar, suka ci abinci sannan 'yan biyu ne
suka yi musu rakiya gurin dauko furnitures din,
wai za su taya ta zabar mai kyau. Mama tace,
"Zaki je dai ku canza mata ra'ayi, wanda muka
mana zamani ne mai kyau, idan kuka za6o
wanda ya wuce kudin wanda ta zaba kwa cika
kudin, shi ya sa na yi murna ranar da za mu je da
ba kwa nan, tunda ba ku ba ku san zafin kudi ba
ganinsu kawai ku ke yi". Suka ce "Mama gara
muje mu ga wanda kuka zaba, in dai irin naki ne
an daina yayinsa yanzu, ya zama eld modern
akwai sabbin ya yi new modern masu iyau sai
156
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
mu tayi ta zaba ta canza, ga yaya Mujeeb nan shi
zai yi cikon". Mama tace,, "Ba ku isa ku sashi
abinda ya yi niyya ba, ku da za ku je ku zabo
mai tsadan ku za ku cika". Mujeeb na musu
dariya yace, "ba komai Mama gara a dauki na
zamani, ko nawa ne zan cika ba matsaka". Mama
tace,
"Ka kyale yaran nan iya yinsu ya yi yawa, idan
kuka je za ka ga gadon mai kyau ne sosai, gadon
dubu dari hudu ne za a ce baida kyau, kila a
miliyan suke son a siya". Suka cc, "Yauwa
Mama ashe kin gane". Mama ta dubi Mujcebu
tace,
"Ka ji ko yaran nan ba su da hankali kila dai
sun dauka hako kudin ake yi a rijiya kada ka
biye tasu idan kun je ko zaka canza ka zabi
wanda ya yi maka kuma daidai Karfinka kada ka
takura kanka don ka yi bajinta ka ji ko?" Ya
gyada kai yace, "ba komai mama zan yi iyakar
iyawa ta".
Sun isa gurin gadon su kansu 'yan biyu
sun yaba sosai da gadon sa su Maman suka
dauka tun farko, shi ma Mujceb ya yaba shi ya
sa ba a ćanza ba, kujeru ma an nuna musu sun
zabi masu asalin kyau, da yake akwai shagon
kayan wuta sai yace su shiga su duba, yace ta
za6i abinda take so, sun taya ta zabi TV na
157
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
bango plasma, sai Home tiyat duk na kamfanin
LG da su Fridge da deep frizer da gas cooker da
sauran tarkacen kayan girkin kicin, dama sun
shiga banki ya ciro kudl masu yawa da yake
ganin zasu ishe su siyayya. Daga nan kai tsaye
suka wuce sabon gidan dake unguwan Buhari
Estate motar da ta dauko masu kaya ta kamfanin
funitures din tana biye da su har gidan.
Yanayin tsarin gidan Mujeeb ya yi kyau
sosai, falonsa ne a gaban gidan mai dauke da
dakin bacci bubba da bayi da wani karamin daki
shima na baccin ne, ta nan zaka iya shiga cikin
gidan mai dauke da filat guda biyu iri dayah aka
dauke da haka Goggo tace ayi na Munceba da
na matar da zai kara nan gaba. Muneeba ta
razana da wannan tsari amma sia Mujecb ya
kwantar mata da ahanka cewaar yin goinin ba
shine aurensa ba, ya dai zamar masu dole ne ya
yi yadda Goggon tace don ya aranta mata rai a
zauna lafiya, amma shi ba maganar kara aure a
tsarinsa yanzu, a wancan lokacin da zai fara
ginin kenan, sai gashi yanzu Goggon ta sami
galaba a kansa har ya amsa mata cewa zai kara
aure, shi a ganinsa zai iya shshantar da maganar,
bai sani baa she Goggon ta dau maganar da
muhimmanci har ta labartawa aminiyarta sun ma
fara shirya yadda bikin 'ya'yan nasu zai kasance,
158
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ba tare da Mujeeb din ya sani ba har da shirinsu
na boye wanda sai nan gaba za su fallasa
Sannan ga fakin Goggo a gidan, babban
daki ne guda daya, sai bayi a ciki, ita tace dole a
fidda mata dakinta daban duk lokacin da ta zo
Gombe a nan zata sauka ba a dakin bakin da akа
yi ba tunda ita ba bakuwa bace, idan tag a dama
ma nan zata dawo da zama gabakidaya ma ta
gani inda mai koranta ita da gidan danta da ta
sha wahalar daukan cikinsa ta Haifa ta raini
abinda tayi fadi tashi don ganin rayuwarsa ta
inganta, ya yi ilimi har ya samu aikin yi sannan
ace wani ya more shi ba ita ba wannan ma karya
ne a cewarta ita dai Muneeba dan Goggo na
wadannan surutan shiru take yi don ta san da ita
da iyayenta takc yi saboda hidimta musu da ya
ke yi, in banda abun Goggo kaninta fa ya ke wa baffan shi kuma sirikinsa, ita kuma Inna ko ba
sarakuta ai matar baffansa ce idan ya kyautatawa
baffansa ai zai yi mata itama in har da matar
sanin ya kamata to balle yana auren 'yarta ai ta
gama masa komai.
Shi Mujeeb har ba ya son ya nuna mata
wani abin arziki ya ce zai kai gidansu Munceba
yanzu zata hau korafi ko kuma tace sai ya sayo
kwatankwacin abin an kai gidan Hajiya Harira ai
itama sirikarsa ce kuma aminiyar uwarsa dole
159
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yayi mata, idan yana son tabo Goggon sai yace
"In banda abinki Goggo Wata kusan ai tafi
gaban wata, Muneeba' fa jininmu daya babanta
sirrikina ne kuma Baffa na, Innarta sirikata ce
kuma Innata ita fa suwaiban uwarta ce fa
aminiyarki shi ke nan alakarmu". Habawa ina
wuta Goggo ta sakashi anna żata hau kansa da
sababi, "In kana da mutunci aminiyata ta kowace
irice zata zamo uwa gareka, balle tana shirin
wanke diyarta ta baka ai kuwa ta wuce wargi a
gurinka".
ta Gagarumar walima aka shirya
komawar su sabon gida wadda za a gudanr a can
gidan na Gombe illahirin 'yan uwa da abokan
arziki duk sun sami harta a bangaren Goggo har
da aminiyarta Hajiya Harira taje Gombe nan ta
kwana ma tare da Goggo, idan ta dada ba idonta
abinci, ta kuma jinjina kokarin Mujeeb saboda
wannan kerarran gida da ya gida mata na dada
tabbatarwa da cewa lallai ba kananan kudi ba ne
Mujeeb din ya yi da har ya iya "kera wannan
tsalelen gida.
Ganin irin kayan alatun da ya zuba a
dakinsa da na Munceba ne yasa Hajiya.Harira ta
sha alwashin ko ana ha maza ha mata kota halin
yaya sai Suwaibanta ta shigo gidan nan ita ma ta
shiga cikin daula a dama da ita, balle idan ta
160
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
shigo da kafar dama ta sami zazzaga 'ya'ya
kinga shikenan mai gida ya zama nata, su
fantama yadda suke so.
Komawarsu dukku da kwana biyu ne Hаj.
Harira ta zo gidan Goggo Rahin akan wani sirri
da suka kulla tun a can Gombe, tana rigan gero a
tsakar gida tace, "Au bai shirya ba ke da nace da
na zo za mu tafi da wuri sabida kada mu tadda
layin mütane". Tace, "Shiga ciki gani nan geron
nan kawai zan wanke a kai mini nika, na yi
gudun kada in yafi ban bayar ba mu dade a can,
kin san yanzu gidan ni kadaice bani da ma ani,
ya daduke abarsa da tana nan wannan duk
aikinya ne". Hajiya Harira ta ja tsaki tace "Tini
na dauka kin daina yin kamun tinda yace ki
daina, bata a ju daua tunda 'yar botin taki ta sami
'yancin kanta, kuma Mujeebu ai ya tsaya miki
komai yana miki me kike nema a duniya kin
sami da mai ladabi da yi miki biyayya, komai
waja-waja in ni ce ke ai ko nawa zanyi in zauna
ina cin arzikin haihuwa tuda ta yi miki rana".
Tace, "Lallai kam haihuwa mai dadi shi
yasa nake tausayinsa, yadda yake bauta mini shi
a ce bashi da mai yi masa ai dole in tashi tsaye in
ga ya yi aure ko da zan kauce hanya ne in ya so
na tuba daga baya amma in da zan yarda da dan
da na kallafa rai a kansa ace bashi da 'ya'ya,
161
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
sannan mace ta kanainaye mini shi bashi da wani
katabus, ba ya son a fadl aibinta, ai in dai asiri
ne mu zuba ni da uwarta shege ka fasa za su ha
irin nawa da ya fi nasu wallahi sai ta gudu a
gidan ta bar ladarta". Haj. Harira tace. "yi ki taso
mu tafi ai da zafi zafi ake bugun karfe, kuma da
sanyin safiya ake kama fara, idan takamarsu
sammako to mu a tafe muke kwana za mu kara
sai a ga wanda zai sha kaye".
Sun iso tashar Dukku suka shiga motar
kaltungo a can wani dan kauye dake kaltungon
ne za su je gurin wani boka ita Haj. Hariran ce ta
sanshi shine ta ce su je don ya yi musu aiki a
shawo kan Mujeeb ai ance da auren Suwaiban da
wurwuri ya daina jan ransu.
Sun sauka a kaltungo suka nemi mashin
da zai kaisu can kauyen kuma cikin daji boka
tsidugu ya ce sunan bokan kenan. Da kyar aka
samu masu mashin zasu kaisu a dari biyar-biyar
sabida sunce hanyar babu kyau. Da yake sanyin
safiyane ba su iske jama'a sosai ba shi ya sa ba
su dade ba aka ce su shigo. Hajiya Harira ita
tayi wa boka tsidugu bayanin komai da abin da
suke so ayi musu, boka ya kece da dariyar
mugunita yace, "Ai kinku mai sauki ne, tunda
hada aure ne mu kan raba aure cikin 'yan
dakikai balle hadawa, in dai mutun zai bi
162
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
umurninmu ba miskila to zai ga aiki babu tangarda", ya daga wani koko sama ya yi
sirkulle daga saman dakin sai ga wasu kwalalan
turare daga saman dakin sun fado cikin kokon
guda biyu rakwacam! Har Goggon su ka firgita
ya yi dariyarsa da ya saba ya ce, “Kada ku
tsorata taimako ne daga aljani tsinkau uban tsidudu yace a baku bukatarku ta riga ta biya an yi aure an gama har ma yace ayi muku bishara
da samun haihuwa a wannan aure abinda zai
biyo baya kuma sai a hankali za ku ji".ya
mikawa Haj. Harira kwalaben guda biyu yace, "Dauki farar ki bata bakar". Ta rike farar
kwalbar ta ba Goggo bakar kwalbar ta sannan ya
soma kora musu bayani kamar haka.
"Ranar da kika tabbatar danki