tare da tambayar iyali sannan Mama tace "Don Allah
sahiba wata 'yar matsala ke gare mu 'yata da na
ce miki tana da matsalar rashin haihuwa din nan,
to ita cc kuma mijin zai yi wa kishiya yanzu
shine na ke son gata ki bata shawarwari na gari
yadda za ta yi juriya da hakuri sannan da
shawarar yadda za ta zauna da ita kishiyar tata,
amma ina fatan kina da lokaci yanzu". Ta yi
murmushi tace,
"Haba, haba aiko bani da lokaci, zan baki aron
lokaci na in dai ba ibada na ke yi ba ko hidimar
maigida, sune kawai ba zan iya bada lokacinsu
ba, sannan wani lokacin kuma zaki ga ina
islamiyyane shi kuma malamin mu ka'idarsa
idan yana darasi bama daga waya wani lokacin
kuma ina makarantar nasara su kuma lecturers
din basa yarda mutum ya daga waya ko dai ka
kashe ko ka saka ta a silent, to ni na kan barta a
silent saboda idan malami ya fita inga wadanda
suka kira ni, don in bi bayan kiran muhimmai
cikin masu kiran, to shine fa wasu idan sun kira
ba a dauka ba suke jin haushi maimakon su yi
mana uzuri a a sai su ce an yi musu wulakanci na
kin daga waya, dole sai mun yi hakuri da juna,
ku masoyanmu ne, mu ma masoyanku ne, kinga
182
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ai ba a fushi da masoyi sai dai hakuri da juna,
yanzu ina diyar tamu bata wayar mu yi magana".
Mama ta mikawa Miniba wayar tayi
sallama sannan tace, "Antinmu ina yini?" ta ce,
"Lafiya lau uwargida don har na nada miki
sarautar uwargida sarautar mata don wannan
matsayin na ki mai muhimmanci nc, ki rike shi
sosai kada ki yarda ya kufce miki in dai kin rike
shi tsakaninki da Allah to ba ita abokiyar
zamanki ba har shi mijin sai sun dinga baki wani
muhimmin matsayi na darajaki da za su dinga yi
yin shawara da ke sannan kc ce zaki zamo ja
gaban gudanar da komai na gidanku sai sunyi
shawara da ke sannan abu na farko da nake son
in baki shawara a kansa kada ki yarda kina cewa
kishiya! kishiya! Fadin sunan nan kishiya shine
farkon abin da yake haddasawa mace tsananin
kishi a ranta idan ta ambaci kishiya! "A a ki ce
abokiyar zama zai fi sa zuciyarki a natsuwa,
sannan ki sani shi kishi ana yin sa ne FI
HUSNIL ASHIIRA, ana yin shi ne na
kyautatawa, ba na hauka ba da jahilci da rashin
wayewa saboda ba za a taba raba mace da kishi
ba tunda shi haliita ne a zuciya, kin ga ba mai
raba mutum da shi, to amma ana yinsa ne ba
yadda zuciyar ki ta raya miki ba, ai ia mace ma
idan bata kishin mijinta ba ta cika mace ba,
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
matukar irin kishin da shari'a ta yarda da shi nc,
ba ne shirme da wuce gona da iri ba.
Kishi ya kasu kashi biyu mai kyau da
mara kyau. Mai kyau shine ki bi duk hanyoyin
da shari'a ta amince miki don ganin kin sami
zaman lafiya da mijinki, da ita abokiyar zaman
ta ki idan ta zo, ki kasance mai kula da lamuran
da suka shafi mijinki, ki yi tattalin sa da yin
tsafta, iya magana iya girki da jin maganar miji,
ya masa biyayya da umarni ko hanin da miji zai
yi miki, girmama shi da kaucewa duk wani abu
da zai Gata masa rai, kuma ki kaunaci duk abinda
ya ke kauna har da ita abokiyar zaman na ki, ki
so 'ya'yan da za ta haifa tsakaninki da Allah sai
ki ga ke ma Allah ya tausaya miki ya baki naki,
kuma ki so iyayensa da yi musu biyayya ki
kyautata masu da dukkan 'yan uwansa ko da
suna munana muki babu ruwanki ke dai kike
kyauata musu, wata rana sai labari, sannan ko
shi mijin ne ya munana miki to ki biyo bayan
munanawan da kyautatawa, saboda ki saukc
nayir hakkinsa da ke kanki, babu ruwanki da
cewa zan munana masa tunda nima ba ya
kyautata min, idan ki ka yi haka ba za ki samu
mafita ba a gurin Allah ranar gobe kiyama, shi
kuma kishi mara kyau da mata ke yi idan za a yi
musu abokiyar zama ko idan an yi musu shine
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kuma wada sam! shari'a bata yarda da shi ba; shine zuwa wurin boka ko malaman tsubbu 'yan
duba don a mallake miji, ta hanyar yin tsafi da yin shirka ga Allah, ta irin wadannan hanyoyin
ne sukc korar kishiya ko su haukatar da ita su malllake mijin shike nan gida ya zama na su, idan kuma aka taki rashin sa a sai kaikayi ya koma kan mashekiya. Wasu mata saboda bakin kishi za ki ga sun rame sun kekashe saboda ba sa cin abinci duk a dalilin kishi, wata macen kuma idan miji ba a dakinta yake ba, yana dakin 'yar
uwan zamanta to sai ta ta kasa bacci saboda
tsabar kishi, ko ta kirkiri rashin lafiya na karya
ta hana su bacci don dai ta dagula musu nishadinsu na wannan daren.
Wata kuma idan mijin na gida zata yi ta
nuna halin kirki ga kishiyar, amma da zarar mijin
ya fita zata yi ta kuntatwa abokiyar zaman, ta yi ta bala'I da tijara, wannan duk rashin hankali ne da damsil basira tare da son zuciya na su matan da suke daukar abokiyar zama a matsayin abokiyar gaba, shi yasa ba a son ace kishiya gara
ace abokiyar zama, sannan ki sani Allah ne ya ba
maza damar su kara aure, duk kuwa abin da Allah ya halasta bai kamata bawa ya bijire ya ki yarda da hakan ba, kada ki zamo cikin masu bijirewa abin da Allah ya halasta, kada abokiyar
185
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
zama ta zama abar gabanki abar jin tsoron
zuwanta, da fargaba, ki sa a ranki za ta zo ne da
nufin alkhairi sai ki ga zuciyarki ta yi wasai baki
da damuwa. Idan ta zo da alkhairin shike nan da
ma zaton alkhairi ki ka yi mata sai ku zauna
lafiya hankalinku da na mijinku a kwance in
kuwa ta shigo da nufin sharri ne to kada ki biye
mata ke ki nuna mata ba ki san sharriba alkhairi
ki ka sani kuma shi za ki yi mata.
Ina son ki sani kuskure ne ga mace ta
nuna bata son abokiyar zama, ke dai idan za a yi
miki an san ba dadi, amma ki yi ta addu'a ne
akan Allah yasa gari za a kawo mai akhairi,
sannan ki sani mazon Allah (SAW) ya auri mata
fiye da daya kuma sun yi zaman kishi mai tsafta
a tsakaninsu, rashin tawakkali da rashin tauhidi
da raunin imani ga mace tace bata son abokiyar
zama domin kina yin fito na fito ne da ikon
Allah, wannan babban kuskure ne, abin da ya
kamata ki yi shine ki ba mijinki hadin kai, kada
ki bari faraka ta shiga tsakaninku balle idan ta
zo ta ga kofa kada ki nuna damuwa ko 6acin rai
ko ki ce lallai sai kin hanashi, idan kika nuna
kina taya shi farin ciki da nuna yardarki sai ki ga
ya kara kyautata miki da kara rikeki cikin so da
amana har ya kasance ke zai dinga neman
shawarwarin abinda zai gudanar na harkar bikin.
186
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Ya kasance ke zai dinga nema shawarwarin abin da zai gudanar na harkar biki. Ya kamata ki nemi tarihin nana A'isha uwar muminai matar manzon
Allah (SAW), don ki yi koyi da ita wajen kishi,
saboda ta yi kishi ne mai ma'ana da kuma tsafta,
wanda ya sa ta yi fice wajen 'yan uwanta iyayen
muninai. Ki kasance mai juriya, da tsananin hakuri da yi wa miji kissa amma ba ta mugunta ba, akwai kissa ta iya magana kawai ta wajen yin girki, akwai ta yin tafiya akwai ta kyautatawa miji, wato idan 'yar uwan zamanki ta yi abu ta kyautatawa miji to ki yi burin ranar girkinki ke
ma ki kyautata masa fiye da nata, sannan akwai
kissar kwanciya wannan ba sai na yi miki bayani ba, kin karanta a littafina DON MA'AURATA,
duk na yi bayanin irin wannan ne a littafin ba don rashin kunya ba ko fitsari na yi a dalilin la'akari da yanayin mazajen yanzu 'yan bana bakwai ne idan baki iya kisser kwanciya ba to za ki sha mamaki, mai krki ne zai iya gaya miki
baki ya ba ki koya kı ya, ko ya koya miki, wani
uwa ba zai gay 2 mici ba sai dai ya rangado
miki amarya wayayyiya ita idan ta zo ta gano
matsalarku ta yi ta mil i habaici, shi ya sa na yi filla filla a littafin. Ki kasance da kanun kai a
gidan aurenki ba ballagaza ba ke ce can gidan
makota kece can, ana shiga gidan makoci amma
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zarnia
sai larura ta auku, ba kawai don ki je hira ba, ke
kin bar na ki gidan mijin kina can kina gulma,
irin su ne ake turkesu can a makotan gurin
yawon gulma, to ki tsare mutuncinki da na
aurenki banda shashanci, kuma ki yi ta adu'ar
Allah ya zaunar da ku lafiya ke da mijinki da ita
abokiyar zaman taki, da sauran jama'a
makotanki. Sannan idan kina da zafin kishi to ki
dinga addu'a ki na rokon Allah akan ya rage
miki shi ko ya raba ki da shi.
Kuma ya kamata ki san wani misali
kamar idan mutum na da sutura masu kyau da
tsada, da zarar ya dinka sabuwa ko da bata kai
tsadar nasa na baya ba, zai yi ta doki da zumundi
hankalinsa ya karkata zuwa ga sabuwar rigar nan
na dan wani lokaci sai ya sa ta hankalinsa zai
kwanta zai bar wadancan rigunan, kafin' daga
baya ya koma ga tsofaffin nasa ya dinga
canzawa da sabuwar tunda ita ma ta shiga
sahunsu, to hakika haka namiji yake idan ya
kara aure, zai yi zumudin amaryar nan tamkar
sabuwar riga sai ya saka ta hankalinsa zai
kwanta, don haka ne ma aka umurci ya zauna a
dakin amaryar na iya kwanakin da musulunci ya
tsara idan budurwa ce kwana bakwai idan
bazawara ce kwana uku. A wannan lokacir. sai
kin kai zuciyarki nesa kin yi hakuri karla ki
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kuskura ki nuna damuwarki akan wasu al'amura
da zaki gani suna faruwa a lokacin ba ga mijinki ba ga ita amaryar ba, kuma idan kin yi hakuri
wannan zumudin na wani fan lokaci nc, zai dawo gareki za ki ga ma har ki fita in dai ba ta bashi kulawa irin yadda kika saba bashi ba, sai hakurinki ya yi miki rana.
Kuma kada ki yarda da zugar kawaye ko
wasu cikin 'yan uwa, domin kila kin yi hakuri
kin nuna rashin damuwa, sai ki ga wasu kawaye
ne za su saki cikin damuwa, har su sa ki ki aikata abinda bai dace ba, kuma da can baki yi ba sai da suka zuga ki, saboda haka sai ki kiyaye ki gane
cewa duk wanda zai zuga ki ba masoyinki bane, wannan zai lallashe ki ya baki shawarwari na gari shi ne masoyinki, duk wanda ba zaki amfana da shawararsa ba to ki yi watsi da duk abinda zai gaya miki, Allah (SWT) ya ce, HAIRUNNASI MAN ANFA"AN NAS, mafi alkhairin mutanc shine wanda mutanen suka amfana da shi kuma ki kiyaye kada zuciya ta kaiki ga aikata abinda ranki ke so, in dai ba alkhairi ba ne abin to kada ki aikata domin Annabi (SAW) yace, MAN FA"ALA ΜΑ SHA"A YALKAMAASA wanda
ya aikata abinda ya ga dama to zai ga ba daidai ba.
189
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Rayuwan nan fa ba ta da tabbas
gabadayan ta ma tana KURBIN NIHAYA ne ta
zo Karshe to me zai sa ba za mu gyara
rayuwarmu ba da al'amuranmu don lahirar mu
tayi kyau? A karshe ina kara baki shawarar ki yi
hakuri! Ki yi hakuri! Ki yi Hakuri! Domin shinc
babban jarinki a nan duniya da kuma lahira,
Allah ya baku zaman lafiya, dukkanku ya
azurtaku da 'ya'ya masu albarka, da fatan za ki
yi amfani da shawarwari na?" Tacc, "Anti na
gode! Na gode Allah ya saka miki da mafificin
alkhairi duniya da lahira bisa ga irin
shawarwarin da kike ba mu a littafinki da kuma
idan an kira ki a waya ga maman".
Mama Amina ta mashi wayar ta cс,
""Sahiba gaskiya mun gode da wadannan
shawarwari don mi ma na karu sosai tunda an sa
wayar a hands free ne, In Shaa Allah za ta yi
amfani da shawarwarinki, kuma zata cigaba da
kiranki don neman wasu shawarwarin akan
abinda ya shige mata duhu da fatan ba zaki gaji
da ita ba". Tacc, "Sam! Babu maganar gajiya
kofa ta a bude take ga kowa ba ma ita ba. Allah
dai ya yi mana jagora a al'amuranmu amin".
Suka yi sallama da juna kowa ya ajiyc wayarsa.
Mama Amina ta sauke ganinta ga
Munceba tace, "To, kin dai ji shawarwarin da
190
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
nasihohi ba ma sai na kara miki da komai ba, sai ki yi aiki da-su". Munceba tace, "Ai ni Mama
yanzu hankalina ya kwanta, In Shaa Allahu zan yi aiki da shawarwarinta ba zan bari wani abu ya bullo ta wajena ba".
Ranar yini Mama ta yi tana kara ba Muneeba shawarwari. Da Mujeeb ya zo daukanta ma Mama ta hadasu ta yi musu
nasihohi kuma ta nuna taiji dadi da bai bijirewa Umurnin mahaifiyarsa ba, don idan ya bijire Munceba abin zai shafa, gara da ya yarda tunda ya dauko Muneeba a hanya ya lura şam ba ta cikin damuwa, walwalartà ta dawo tamkar yadda ya santa, ba kamar da safcba lokacin da ya gaya mata batun aurensa.
Tun a ranar da suka koma gida, ya nemi shawarwarta, suka soma tsara yadda sha'anin bikin zai kasance, sannan ita ya dorawa ragamar komai na bikin, hatta sayan kayan akwati ita zata yi, kuma set biyu yoee, za ta saya nata da na amarya, da ta tambaye 'shi dàlili sai yace ai ita ma bai yi mata akwati ba lokacin bikinsu, wanda aka yi mata ba shiya yi ba, yanzu ko dole ne yayi mata tink li va hore mosa abin y
kayan daa don la Sad ne da sH
ma ya canza mata, amma duk da haka yace zai bata kudi isassu ta sa yi abinda take so.
191
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
*** *** ***
Tun bikin yana saura sati faya Goggo ta iso
garin Gombe, ta sauka a dakin da aka gina
dominta wanda ya kunshi komai na jin dadin
rayuwa, har da kayan kallo da AC da gadonta na
alfarma da kujeru, dakin ya ji tayals ko ina. Falo
ne babba sai dakin bacci guda daya.
Da ta zo ta ga akwatunan da Mujecbun ya
yi wa Muneeba, fada ta dinga yi, da ya ke na
amaryar can Dukku aka kai gurinta sai 'yan uwa
suka hadu suka kai a cewarta duk surutun da
Muneeban ke da su, sai yayi matą wasu
akwatuna don gata da barnatar da kudi sai ya
nuna mata to ai lokacin bikinta bai yi mata ba,
shi yasa ya hada ya yi musu tare, tace sam
wannan ba wai dole ba ne, tunda Alh. Sani ya yi
mata ai a iokacin ta yi ta fadanta yana bata
hakuri don ma bata san Munceban ba ce da
kanta ta hada akwatunan da sai ta kusa tsine
masa albarka don cewa za ta yi an dada shanyc
shi an mallake shi, abin da Munceban ta guda
kenan don bata so ya nunawa Goggo kayan ba a
dalilin abin da zai iya biyo baya ba zai yi musu
kyau ba dukansu.
Munceba ta yi tamkar ba ita ba ce ake yi
wa kishiya ba, komai da ita ake yi, to me zai
tasbi hankalinta tunda mijinta bai ragea da
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
komai ba, ita ma shi ya sa ta sha alwashin ba marada kunya, Goggo kuma ba haka ranta ya so ba, duk yadda ta so ta tinzira Muneeban don ta yi fushi ko ta nuna an yi mata ba daidai ba ta
canzawa mijnta a dalilin irin abubuwan da Goggon ke ambatawa ce wa Mujeeb din ya yi wa Suwaiba na karya don Munceba ta tinzira sai take yin sakuratin bangaro da duk wani sha ci fadin da kalaman tinzirawa da Goggon ke yi, kullum sai dai ta ganta suna raha da dariya ita da mijinta, kuma suna gudanar da harkokin bikin a
tare, don wani lokaci abubuwan da Goggon ke yi
na damunta kishi kuma yana tinkaho, amma sai ta dake ta yi saurin shigewa daki ta dauko alkur'ani ta karanta sai ta ji natsuwa ta zo wa zuciyarta.
Ana saura kwana biyu kikin Adda Fadima ta iso a dalilin Munecban ta matsa mata da waya tana son ta zo da wuri kuma ranar ne bayan isowar Adda Fadiman, masu motar kayan amarya da masu yin gyaran daki mata 'yan uwan Hajiya Harira suka iso.
An yi girki wadatacce domin zuwan nasu, ga abin sha na katan katan haka aka yi ta kai musu, duk yadda Goggo ta so aga gazawar Muneeba ace ta yi ba dai dai ba, abin ya faskara, don wani abin haushi ma da ta ji kunnenta na
193
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
jiye mata shi ne yabon Munecban da suke yi
tunda har dakin Suwaiban ta biyo su ta gaişhe su
cikin girmamawa, sannan ga tarba abinci da abin
sha masu dadi da ka yi musu, su kam ba su ga
aibun ta ba, idan Suwaiba ta so za su zauna
lafiya haka suka yi ta fada.
An gama gyaran dfakin Şuwaiba har sun
koma Dukku. Daki kan ya yi kyau sai dai bai
zarce na Munecba a komai ba illa ma na
Muneeban da ya fi yin tsari irin na 'yan boko.
Ranar bikin gida ya cika makil da jama'ar
Dukku da nan a Gombe yawanci jama'ar Inna
Amina ne, sai kawayenta Munecban na jami'a
da ta hadu da su gurin karatun da ta fara, ita kam
ba za ka ce ita kake yi wa kishiya ba saboda
kazar-kazar da walawalar da ta ke yi, sai ka
rantse itace amaryar don ko amaryar ba zata
kaita yin kyau ba.
a
Shi kanshi angon kasa tafiya gurin daura
auren ya yi, suna dakinsa yana yabawa irin kyan
da ta yi ta ce, "yanzu ni har na isa in kamo kyan
kwalliyaur ka kaifa ango nc? ya kara matseta
jikin shi yace, "Wallahi duk cikar taron bikin nan
idan aka tara matan nan za ki zamo tamkar
Zarah ne cikin taurari sannan ....". Mujecbu!
Mujecbu! Mujccbu! Wai wanc irin shirmc ne
wannan a kule a daki kabar mutane a waje su na
194
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
jiranka". Kwaratsin Goggo ne wannan lokacin da ta zo kofar falon Mujecb din tana kwarara masa kira.
Ya yi saurın sakin Muneba, ya gyara. hularsa da malun-malun dinsa ta asalin shaddar
gezna mai tsada fara sol da ita, ya sumbaci
labban Muneeban yace, "Shike nan mun tafi, take care". Bata iya ce masa komai ba illa hannu da ta daga ta yi masa bye-bye. Ba ta fito dakin
nasa ba sai da ta tabbatar Goggon ta dade da tafiya, sannan ta fitó. A dakintá kawayen ta na jami'a suna ta mamakin wannan hali na sirikarta,
a cewarsu meye nata na bin danta daki don ya na
tare da matarsa, to me take son ta gani in ba kwakwafba.
Taro ya watse lafiya, an kawo amarya washe gari an dada gyara mata daki sánnan kowa ya watse, sai Goggo ta řage da tace ba zata tafi ba sai ta watstsake gajiyar biki. Misalin tara na darc Mujceb ya yi sallama ya shigo dakin Muneeba ya isketa a zaune gaban madubi tana shafa mai shirin kwanciya take yi, ya zo ya sumbaci gadon bayanta sannan ya dan rage tsawo ya risina ya buba hannuwansa bisa cinyoyinta yace, "Ke shirin bacci ma ki ke yi ba zai yi cigiyar ina mijinki ya ke ba tara na darc". Ta saukc ajiyar zuciya tace,"Ya za a yi i
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
nemeka, na sani ko ka dawo ka na can dakin
Kanwata". Ya ce,
"Haba Muneeba idan na yi haka ai ban yi
adalei ba, a ce in zo ban neme ki ba in wuce
wani guri, ai ke rabin jiki na ce komai zan yi sai
da ke, yanzu ma taso ki rakani gurinta". Ta yi
murmushi tace, "haba Yayana kada mu yi haka
da kai, ba sai na raka ka ba, don ba na son yin
katsalandan a rayuwar wani, ka yi hakuri ka tafi
kai kadai za ta fi son ganinka ka je gurinta kai
kadai, ba tare da 'yar rakiya ba". Ya tubure sai
sun je tare ko ya fasa zuwa ya wuce dakinsa, da
kyar ta lallashe shi zai je shi kadai amma sai ta
rakashi bakin dakin Suwaibar in yaso sai ta
dawo
Ledojin da ya shigo da shi, ya cire mata
nata da na Goggo sannan ya dauki ra su ta raka
shi har kofar falon Suwaiba, sai da ta ga ya shiga
sannan ta jawo, karaf ta hangi Goggo na leken
wucewarsu ta labulen windon Dakinta, alhalin
gurin Goggon ya fara shiga ya yi mata sai da
safe ta, rufe kofar sannan ya shiga gurin
Muneeban shine don fitina ta tsaya tana leken ta
ga shigarsa da fitarsa.
Muneeba bacci ta yi sosai a wannan dare
wanda aka sarin mata da aka yi wa kishiya a irin
wannan daren ba sa bacci sabanin ita da ta yi
196
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
baccinta har da makara don bata tashi ba sai shida saura na safe sannan ta yi Sallah ta je ta gaida Goggo ta dawo ta shiga kiein don hada abin karyawa. Har ta yi ta gama da misalin tara
na safe ango da amarya ba su tashi ba balle su bude kofar falonsu, wannan abu ya saka Munecba cikin kokwanto ita ba abin ta je ta tambaya ba ko lafiya har yanzu ba ta ji duriyaursu ba, tuda ita dai ta saba mijina idan ya
tashi tun asuba ya je masallaci ya dawo to baya komawa bacci tarce suke shiga kicin su yi komai,
sai gashi yau daya har an fara sauya masa rayuwa. Allah sarki Munceba ai wasa farin girki kenan a al'amuran Suwaiba diyar Haj. Harira, sauran al'amura ma na can gaba na ban mamaki.
Ku biyo
Rahman zaria a littafi na biyu tare suke fito da na dayan
08068895555, 08028434948.
197
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
FILIN RAHA
LABARIN MAGIDANTA GUDA UKU
Wasu magidanta ne guda uku suke zaune a bakin
dakin haihuwa, kowa ya kawo matarsa, can sai
norse ta fito ta ce, "waye ya ke aiki a (Two
Towers)?" dayan cikinsu ya ce "Ni ne". tace ina
taya ka murna matarka ta haifi 'yan biyu" ya yi
godiya ga Allah yana murna, can ta dawo tace
ina mai aiki a (3crowns) ya ce "Ga ni" ta ce
matarka ta haifi 'yan Uku. Ta na shiga dakin
haihuwan sai fayan wanda matarsa ta rage bata
haihu baa ka ji ya saka kuka, duk suka dubeshi a
tsorace suka ce, "Lafiya malam? Ya ce, "wallahi
ni a kamfanin 7up nake aiki na san zata cc an
haifar mini 'yan bakwai!
AISHA IBRAHIM
LABARIN ‘YAN BAUTAR KASA
Wani dan bautar kasa ne yana cikin rashin kudi,
Sai aka biya masu kudin alawas dinsu naira dubu
talatin da biyar. Yana dawowa gida sai ya yi
wanka ya je ya dauki budurwar sa suka tafi super
market zai yi mata siyayya. Ta zabi mayuka da
kayan kwalliya, ashe ma su tsadane, da aka zo
198
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gurin kashiya ta yi total din kudi sai suka kama dubu talatin da hudu da dari uku (N34,300:00).
aka gaya masa ido fa ya raina fata, hakanan ya dauko kudin ya bada. Sai aka ce sunan wa za a
sa a rasit din sai yace wa kashiyar ki sa MARIGAYI.
LABARIN WASU MASALLATA
Wasu masallatane an yi Sahun Sallah da su a
Masallaci, liman ya zo ana shirin tada ikama, sai
suka ji wani daga harabar Masallacin ya na waya
yana cewa, "Eh na aje jakar tana nan a gaban
liman daga gefe, Eh, yanzu kuwa.
Liman yana kai idonsa gefe sai kuwa ya
ga jaka, ai kafa main a ci ban baki ba, ka fin ka
ce kwabo da liman da mamu sun arta waje da gudu, ana ta gwabza gudun ceton rai.
Sai a waje mutumin ke muşu bayanin ashe kudin
zakkane wani ya aiko da su ya aje a in aka idar
da Sallah ake so ayiwaliman bayani.
199
*
*
*
*
LITTAFAN MARUBUCIYAR
SANIN HALI 1,2,3
HUJJATA 1,2,3
MENE AIBUNA?
ALKAWARIN DA CIWO 1,2
NA YI BIYAYYA 1,2
WA YA CUCE NI? 1,2
BAYAN WUYA 1,2
SAIHAМ 1,2
MU YI HATTARA 1,2
AUREN MANUFA 1,2
Ana iya samun wa yannan littafai, a
SIRRIN GIRKE-GIRKE 1,2
MIJIN ARO 1,2
ILLAR KUSANCI 1,2,
DON MAʼAURATA
WATA KUSAN 1,2
MUHAMMAD SANI BOOKSHOP
CHARANCI ROAD KASUWAR BARO
080332684404,07089897389
AL-MUSTAFA BOOKSHOP
BAKIN RIMI GIDAN JUMA S/GARI ZARIA
08026570893, 08130616029
Z
RABI'U WUSE BOOKSHOP
Wuse market zone I Abuja.
08030777669, 08091331166
AL-AMIN BOOKSHОР
No Aq 1 Anguwar rimi
market Kaduna
08023607345
SPU NAFPU BOOKSHOP
Behind Kofar Doka Central Motor Park, Zaria
08028341964,
AL-AMIN BOOKSHОР
Layl Na Hudu Bayan Masallacin Abacha
A.A. Rimi Market, Kano
ABUBAKAR ABUBAKAR BOOKSHOP
Inside Club 69 Garejin Hayi-Hayl
Sheik Abubakar Gumi Central Market Kaduna 07066706030,08029646961
Designed Printed by:
ZAZZAU VENTURES
General Printing & Publishing
08028401199, 08035336868
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi