shi Mujeeb ya
rasa me zai ce wa Munceban? Yusuf sarkin
magana shine yayi magana ganin duk sun kasa
cewa junansu komaikila nauvin juna sukeji, a
84
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
dalilin wannan al'amari na bazata da ya faru
akansu yacе,
"Amarya Munccba ya hidimar biki, anyi komai
Lafiya?" fuskarta cikin lullubi tayi magana da
'yar siririyar muryarta tace,
"Alhamdulillah an yi lafiya, kuma kun iso
lafiya daga Gombe", yace,
"Lafiya lau, ai muna ta zumudin mu zo mu
yiwa su Baffa godiyar wannan muhimmin
al'amari da suka kulla, sabo da shi angon baya
garin an tura su Lagos daga Makaranta, nima
naje Bauchi, shi yasa muna dawowa muka taho
dan kada ki cinye kajin amarcin ke kadaimu ma
aci da mu". Dariya tayi bakinta tamkar a cikin
gyalenta tace,
"Sannunku da gajiya" ta dan risina gaban
Mujecb tace,
"Yaya Mujeeb ina yini, bamu gaisa ba?" yace,
"Lafiya lau, ya taro?" tace,
"Alhamdulillah, ka dawo lafiya",
"Lafiya lau nima naje (Excusion) ne jahar
Lagos ban san abinda ke faruwa ba sai- da na
dawo yau, ina fatan zamu yi wa Iyayenmu
biyayya, mu gina so da kauna a tsakaninmu,
kuma mu rike amanar juna". Tacе,
"Insha Allahu ta 6angarena ba za a sami
matsala ba. Allah ya shige mana gaba". Yace,
85
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ameen". Yusuf ma ya basu shawarwari na gari
ta yadda za su zauna lafiya tunda sun yi wa
iyayensu alkawarin yi musu biyayya. Mujecb ya
dubeta yaсс,
zamu wuce can gida, bamu je ba nan
muka la. sauka, akwai wani abu da kike so?"
tayi sauria girgiza kai tace,
"Babu abindanake so. Allah ya huta gajiya a
gaida min Goggo". Ya ciro dubu biyar ya mika
mata yace, "Ga wannan sai ki rike idan kina
bukatar wani abu, don gobe zamu wuce akwai
test da zamu yi jibi a makaranta don kun kusa
fara exaın ban sani ba ko zan sami dawowa next
weck ana goben idan zam wuce zamu biyo mu
yi sallama". Ita ta fara fita ta shige cikin gida,
nan ta ci karə da ‘yan tsegumi gidansu ana zaune
ana jiran a ga dawowarta. Su ma suka fito suka
nufi gidansu Mujeeb da ke Duggc.
Goggo na zaune fana jan casbaha, bayan
ta kida da sallar isha'i su Mujecbu suka yi
aliama suka lhiga suka zauna bisa tabarma suna
jiranta ta tagama laziun. Bata dade ba ta shafa
addu'ar da tayi sannan ta fuskancc su. Gaba daya
suka risina suka gaida Goggo ta amsa tare da
cewa,
"Saukar yaushe da daddaren nan ba kwa bari
sai da safe ku taho?", Yusuf yace,
86
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Wallahi muma mun so sai gobe mu taho
Alhaji ne yace lallai lallai ya taho yau, shinc
direba yakawomu har yakoma yanzu mai ai ya
dade da isa Gombe", Goggo tacc,
"Da zu baka biyo Alhajin ba lafiya", Yusuf
take tambaya, yace,
"Nima nayi sammakon zuwa Bauchi ne, shi yasa
ban samu zuwa ba.An daura aure Lafiya?"
Goggo taja tsaki tace,
"Sun daura lafiya ni ai fin karfi aka yi mini, da
an bi nawa ra'ayin anyi shawara da ni, inda anbi
nawa ai da ba ayi wannan hadın ba. Kun biya ta
can gidan namu ne?' Yufus yace,
"Eh, can muka fara biyawa, su Baifa sun yi
mana bayanin komai, Goggo hakuri zaki yi mu
fawwalawa Allah al'amarin tunda ya riga ya
kulla addu'a zaki bisu da shi, Allah ya basu
zama lafiya ya kauda fitina a tsakaninsu, Ai
kinyi dace da sirika Goggo yarinyar tana da
ladabi gata diyarki kinga ai ba matsala" ta ja tsaki,
"In bata da matsala ai uwarta na da shi, tunda
ta mallake mini dan uwa, shima haka za su
mallake mini shi, kuma wallahi bazaı yardaba
sai na nuna musu idan sun iya sammako to ni a
tafe nake kwana". Yusuf dai ya ta bata hakuri
yana nuna mata sam haka ba zai yiwu ba, ya
87
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Karfafa da ccwa, "Wallahi Goggo wani lokacin
ladabi da biyayya idan mace tana yiwa mijinta
shine yake sa agą tamkar ta mallake shi, saboda
miji zai kyautata mata kwatankwacin irin ladabin
da biyayyar da take masa. Wannan diyar taki a
yadda nagantą zata yi miki ladabi da bin duk
umurninki Goggon kiyi hakuri tunda Allah ya
Kulla wannan al’amarin".
Shi dai Mujeeb yana zaune tamkar
mutum mutumi, ya rasa bakin magana saboda
rudan da Goggonsa take neman jefa shi, alhalin
ya daukarwa Baffaninsa alkawarin zai yi musu
biyayya bisa hukuncin da suka zartas a kansa, sai
gashi tana nuna zahirin adawarta ga hukuncin
yayyin nata, mai makon itace mai tausarsa ko da
zai nuna bijirewa ta karfafa masa gwiwa da ya bi
umurnin 'yan uwanta sai gashi itace zata ja masa
ragama don ya bijire musu, shi kam tunda abin
da suka yi ba sabawa umurnin Allah bane sunnar
Annabi suka kula to in sha Allahu ba żai biyewa
hudubar mahaifiyarsa ya karya alkawarin
biyayyar da ya yi musu ba, sai dai zai san yadda
zai yi wajen zamansu gida daya da Goggon, zai
fifitata fiye da matarsa, zai dinga binta sauda
kafa akan duk wani umurni nata in dai ba zai
tauye hafkkin matarsa ba.
88
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo ta watsa masa idanunta cike da
tuma tacc, "Kana ji muna magana kayi mana
shiru tunda ka rigaka je Yaya Adamu sun shirya
maka kalamai masu dadisun kwakkwafcka, to ba
zance ka bjire musu ba amma ka sani, wallahi ba
zan dauki duk wani abu da bai yi mini ba a
zaman aurenku, ka sani ni mahahifiyyarka ce
babu wanda zaka so fiye da ni a duniyar
nan".Mujeeb yace.
"Wallahi ni bani da kamarki a duniyar nan, ke
kadai kika rage mini da nake kalla inji sanyi, ta
yaya za ayi in fifita wani kina rayc, ai ba zai
yiwu ba ki kwantar da hankainki in dai wannan
ne matsalarki".
Tashi tana cewa "bari in kawo muku
abinci". Yusuf tace, "Wallahi a koshe muke
Goggo, mun ci abinci a gurin Baffa zamu je mu yi sallar isha'i ne mu kwanta a gajiyc muke
sosai". Tace, "Ai dole ku gaji daga dawowarku
daga tafiya Alhaji yace sai kun taho da ya barku
sai gobe". Suka sallame Goggon suka wuce dakin Mujeeb da ke soron gidan.
Suna shiga da yake akwai bayi a dakin Yusuf ya shiga yayi alwala, sannan Mujecb yayi suka yi jam'in sallah. Bayan sun kwanta ne Mujeeb ya kasa hakuri da abinda ke mintsinin
zuciarsa yadan muskuta daga kwance yace,
89
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Yusuf ya kake ganin zanyi da al'amarin Goggo
tunda bata son auren nan?" Yusuf yace, "Ni dai
shawarata ka rike aurenka hannu bibbiyu kada
kayi sawarwarin da yarinyar nan zata subисе
maka, con wallahi komai nata yayi daga dabi'u
har yanayin ta, ita kuma Goggo tunda na lura
bata son aka so wani fiye da ita to sai ka kula
kada dadin amarci yasa wata ran ka makale ka
manta da fitowa duba lafiyarta". Mujeeb yayi
tsaki yace,
"Dadina da kaisai ka fara abu na arziki sai ka
soma slashanci, ni akwai wani dadin duniya da
zai sa in manta da Goggo? In ma akwai shi to
bana tetan yayi təsiri a kaina. In sha Allahu zan
kiyaye ka san i'a Goggon da aminiyarta suke son
hada aurenmu ni da 'yarta, goggon ace in je in
nemi yarir ar wai idan nagama karatu na fara
aiki sai ayren, a lokacın na nuna mata bana
ra'ayin yarinyar, da ta nuna min ranta ya baci sai
nace to ta cari idan nagama karatu sai in fara
zuwa gurin suwaiban don bana son hada karatu
na da komw shine fana samu ta bar maganar a
haka, shi yasa abinda su Baffa suka yi ya har
zukata tunaa ita ga shirmta 3a kuma sun yi mata
bazata, ni garama da haka ta faru don wallahi na
tsani yarinyar idanunta waje suke, ita goggon da
take ganin gara in aureta da in auri Munceba ba
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ta son ita aminiyartata itace mai cutarta ba 'yan
uwanta ba, duk san da zata yi wa Suwaiban ai na
Muneeba shine gaba, Wata Kusanai tafi gaban wata
Yusuf yacc, "amma ita ma Munecban
naga kamar ba wani sonta kake ba". Yace,
"Eh to ba zance maka bana sonta ba, sannan
bazan ce maka ina sonta, ni dai na san akwai kauna ta 'yan uwantaka a tsakaninmu amma nan gaba ina fatan kyakkyawar mu'amalar da zamu yi ta sa muso junanmu".
Da safe bayan sun yi wanka suka shirya cikin shadda Galila iri daya mai ruwan bulu ta
Mujeeb tayi duhu saboda shi fari ne ta Yusuf
kuma tayi haske sabida shi baki no amma
bakinsa mai sheki da daukar idanu a dalilin hutu
da cima mai kyau.
Dadduma suka shimfida bisa dakalin
kofar gidansu Mujeeb suka zauna suna ta hira da
abokan Mujecb dinna nan Dukku a da ilin sun
sami labarin yazo gari shine suka zo yi masa
Allah ya sanya alkhairin auren da aka daura
masa.
Kafin su Mujeeb su bar garin sai da aka
tattauna aka tsayar da cewa nan da sati biyu za ayi tarewar Munceba kuma anan gidan Inna za a
yi katanga a fitar mata da sasanta, za ayi mata
91
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
can gefe sai daki falo babba sai dakuna guda
biyu a ciki falo babba sai dakuna guda biyu a
ciki wannan gyara su kawai aka yi a fidda su
yadda ake so.
Da Mujecbun ya zo ya gani abin ya birge
shi yadda masu aikin suka tsara komai cikin tsari
da birgewa tamkar sabon gini tsari da birgewa
tamkar sabon gini haka suka maida gurin, sannan
ya yabawa Isah yadda yayi tsayin daka har sai da
ya ga komai ya kammala, Bangaren Gogon ma
tamkar sabon gida haka ya koma saboda fentin
da aka yi wa gidan duka, komai dama yana son
gyara sai dai in bai samu ba.
Tun ana gobe tarewa Inna Amina ta iso ita da
'ya'yanta, sauran jama'arta sai gobe washe gari
za suc iso. Tare suka taho da motar kaya na dakin Munceban da aka siyo su a Gombe. Innar
su Munecba ta sayar da daya daga cikin shanunta, shima Babansu Munceban kudin da 'yan uwansa suka hada suka bashi ya hada da na hannunsa duka akaba Inna Aminan shine ta yo kayan daki masu nagarta da kyau kowa ya gani sai yayaba. Ita kuma a nata guddummuwan da
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kicin da bayi duka a sasanta, diban ruwa a rijiya
ne kawai zai fito da ita tsakar gida.
Dasu Mujeeb suka koma Gombc Alhaji
ya tambaycsu me aka zartas a Dukku game da
lokacin tarewa, sai suka gaya masa an tsayar da
nan da sati biyu zata zauna a Dukku tare da
Goggo". Yace, "me zai hana ka kawota nan
Gombe sai in baku gurin zama, naga hakan zai fíi
maka sauki" Mujeeb yace,
"Furucin Goggo ya nuna min bata son in kai
Muneebar ko ina, shi yasa ban nemi izinin in
kawo ta nan ba tunda na lura ba zata yardaba,
zan barta a can in yaso na dinga zuwa week end
nan gaba idan naga yiwuwar tahowa da ita sai in
taho da ita”.Alhaji yaba Mujeeb kudi yace ya je
Dukku ya sami masu gini a sayi komai na aiki su
fidda sasan Muneeban ayi duk yadda ya kamata
ita Goggon ayi mata gyare-gyaren idan an gama
sai ayi fentin gidan duka don ya tashi bai daya.
Isah Kanin Mujeeb din shi Mujcebun a bar
komai a hannunsa na kula da aikin tunda shi ba
zama zaiyi ba.
Kafin satibiyun nan su cika har an
kammala tsara gurin yadda ake so an fidda kofa
tsakanin tsakar gidan Goggo da sasan Munecban,
kana shiga zaka iske dan madaidaicin takar gida
ga bayi guda biyu a wanka da ba haya sai kicin a
92
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
can gefe sai daki falo babba sai dakuna guda
biyu a ciki falo babba sai dakuna guda biyu а
ciki wannan gyara su kawai aka yi a fidda su
yadda ake so.
Da Mujecbun ya zo ya gani abin ya birge
shi yadda masu aikin suka tsara komai cikin tsari
da birgewa tamkar sabon gini tsari da birgewa
tamkar sabon gini haka suka maida gurin, sannan
ya yabawa Isah yadda yayi tsayin daka har sai da
ya ga komai ya kammala, Bangaren Gogon ma
tamkar sabon gida haka ya koma saboda fentin
da aka yi wa gidan duka, komai dama yana son
gyara sai dai in bai samu ba.
***
Tun ana gobe tarewa Inna Amina ta iso ita da
'ya'yanta, sauran jama'arta sai gobe washe gari
za suc iso. Tare suka taho da motar kaya na
dakin Munceban da aka siyo su a Gombe. Innar
su Muneeba ta sayar da daya daga cikin shanunta, shima Babansu Muneeban kudin da 'yan uwansa suka hada suka bashi ya hada da na hannunsa duka akaba Inna Aminan shine ta yo kayan daki masu nagarta da kyau kowa ya gani sai yayaba. Ita kuma a nata guddummuwan da
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
mijinta sukasaya T.V inci goma sha takwas da
DVD da Firiji, da kafet na tsakiyar daki sai
dangin kayan kicin na girki irin na zamani. Da
aka gyara dakin Goggon sakin baki tayi tana
kallon dakin wanda ta san ko 'yar Hajiya Harira
da take takama da ita aka auro irin kayan da za a
yi mata kenan. Nanfa ta tuma gefe ta ce sam
wannan dukiya da aka kashewa Muneeba a daki
shanu i Baban Muneeban ne aka sayar don ayiwa
Muneeban kayan garari wai duk wannan
kinibibir Innarsu ne da na 'yar uwanta Inna
Amina.
Aifa nan gida ya hautsine da rikici
tsakanin Goggo da 'yar uwar Innarsu Munecba
da suka zo gyara daki, har sai da Malam Adamu
ya zo gidan ya tsawatarwa Goggo Rahin sannan
abubuwa suka daidaita yayi mata fada da nasiha
sosai akan yarda girmanta da take yi a idon
duniya, alhalin ko 'ya'yan cikinta basa son
wannen ri halayya ta ta, su kansu ba za su iya
abinda takc yi ba.
a
Dama Mujeeb bai taho ba, yana jin
abinda ke laruwa sai yaji ba zai iya zuwa Dukku
ranar ba. saboda kuyan 'yan uwan Innarsu
Muneeba ba ma ya son su hada idanu da su, shi
yasa yayo waya yayi karyar za su yi Test a
makaranta ba zai sami zuwa ba sai washe gari.
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba dai ta cỉ kuka har ta bauku lada
sabo da abin da ya faru sannan tana tananin
yadda zamansu zai kasance tare da Gog go. tunda
bata son auren nan ita kam zata yi mata biyayya
İya biyayya, zata bi ta sau da kafa iya iyawarta ta
yadda da wuya zata ga baikenta ko da yake
wanda ya nuna baya kaunarka ko nonon uwarka
ka yanke ka gasa masaba zai ga kayi masa
gwaninta ba, gwasaleka zai yi.
Su Khausar ne suka dada gyara dakin na Muneeban suka turara su da kalolir turaren
wuta, ta yadda ba ma dakin Munneban bagaba
daya gidan har sasan Inna yadauki kainshi, kai
har kamshin ya fita cikin unguwansu ti Dugge. Inna Amina ta 6alle Jakarta ta fiddo litta fai DON
MAʼAURATA tamikawa Munneba tace, "Duk wani fada da iyaye keyi mun yi miki, ga wannan littafin ki zauna a tsanake ki karanta sni, kuma ba wai ki karanta kawai ba a a kiyi anfani da abubuwan da ke cikin littafin don ki gudanar da kyakkyawar mu'amula da mijinki a rayuwar aurenku abinda baki fahimta ga nambar marubuciyar littafin nan ki kirata ki tambayeta zata yi miki bayani sosai don ina kiranta mu yi shawarwari harmun kulla amintaka sosai daita, na aminta da ita a dalilin shawarwarin da take bani, zata zo Gombe a dalili na, nima za ıje Zaria
95
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kinga zumunci mai karfi ya kullu a dalilin littafi
da kuma shawarwarin na gari da take bani, har fa
babban su Khairi ya santa suna gaisawa a waya
yayi matagodiya shawarwarin da take bani,
tunda yana jin dadin sauyc-sauycn da yake gani
a rayuwar aurenmu to ina san kiyi koyi da ni kin
zauna da ni kinga irin mu'amalar da nake yi mai
tsafta da mijina ban da kazanta banda zama ba
kwalliya ki kasancc mai iya girki nau'i-nau'l
shima ga littafin girke-girken ta da tayi mai suna
SIRRIN GIRKE-GIRKE na daya da na biyu ne,
ki dinga kwatanta duk girkin da ke ciki inda baki
gane ba ki kirata, abin da babu a garin nan ki yi
mini waya zan tado Malam Musa ya zo ya kawo
miki, sannan ki kula sosai da uwar mijiknki ki
kyautata mata, duk abinda kika girka komai
Kankantarsa ki diba ki bata, idan tana aiki ki je
ki taya ta, ki kyautatawa 'yan uwansa idan sun
zo, ki so su ki so 'yan'yansu, kiyi musu alkhairai
idan kina da hali. Allah Ya baku zaman lafiya,
ya kawo zuri'a mai albarka a tsakaninku".
Su Khausar da ke zaune sun yi tsuru suna
sauraren nasihar da ake yi wa Munceba Khairi
tace, "Mama dama ina ta son inyi miki tambaya
akan littafin nan DON MAʼAURATA mu ba
zaki siyamana ba?" ta ce, "Guda hudu nama siya
nawa daya guda uku kuma naku yanzu na ba
96
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba nata saboda lokacin in bata yayi ta
zama daya daga cikin ma'aurata ku kuma naku
yananan na 6oye sai naku lokacin yayi sannan
zan baku saboda anyi littafine domin masu aure
ko baku ga unan littafin bane DON
MAAURATA? To ba domin kowa aka yi shi ba
sai domin su, naku na nan zan baku idan lokacin
ku yayi". Khairi ta :e,
"Mama don A lah kada ki ba wata cikin
kawayenki don na sanki da kyauta, mu zo kuma
idan namu lokacin yayi ace babu a kasuwa sai an
sake bugawa, gara ki boye mana don Allah". Tace,
"Babu wandazan ba, inma na bayar na san ba
zaku rasa ba tunda zata zo ida bikin naku ya tashi, sai tazo muku da shi ko babu zata nemo ta
zo muku da shi balle ma ba zan bayar muku da shi ba tunda na san muhimmancin littafin". Ta kalli Muneeba tace,
"Kin cinye kazar da nazo maki dashi ko?" ta gyada kai tace,
"Na cinye, sauran kince a hankali zan dinga sha da nono ko madara ko yogot ko?" tace, "Eh, ki adana su inda wani ba zai gani ba, dukkuma abinda baki gane ba ki yo mini waya idan wani abu kike so shima kimin waya kada ki dinga damun mijinki idan kina son abu kin san
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
dai dalibi ne, duk da yana dan taba,kasuwanci,
amma ai bai yi karfi ba, kiyi hakuri ku lallaba
rayuwaar aurenku wata rana sai labari". Ta dubi
'yan biyunta tace,
"To 'yan matana dare yayi a tashi aje a
kwanta,kun san gobe da wuri zamu tafi saboda
shirin makaranta". Muneeba tayi karaf tace,
"Yanwa Mama banji anyi maganar ci gaban
karatu na ba". Tace, "Eh, karatu zaki ci gaba
insha Alahu duk da bamu yi maganar ba, amma
na san mijinki ba zai barki zaune haka ba, in ma
naji shinu zan neme shi yazo gida ya same ni sai
cuu yi maganar". Suka mike gaba daya zasu tafi
Muneeba tayi kwal-kwal da ido zata yi kuka..
tace.
"Yanzu Mama ba zaki barsu su kwana ba
runda ba yau zai dawo ba?" tace,
"Gara da ki fara koyon kwana ke kadai tunda
shidin ba mazauni ba ne, kuma in banda abinki
ga mutane gidan kina can kuryar gida meye
abin tsoro, kiyi aaddu'o'in tunda kina da alwala
idanna baki daia akije kiyi ga' ki rufe koina kiyi
addu'o'i ki kwanta addu'a ai garkuwa ce", tace,
"shike nan Mama na gode zai da safenku". Suka
fito ta sake rakosu har suka fita a harabar sasanta
taufe kofar ta shiga dakinta ta rufe ko ina
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
sannan ta je tayi shirin bacci tayi addu'o'i
sannan ta kwanta.
Da safe Munecba tana tashi daga baccin
da ta koma bayan tayi sallar subahi, ta bubde
sasanta tayi tun bata yi komai ba nasa sasan ba,
ta nufi gurin Goggo. A dakinta ta iske ta a zaune
da yara masu siyan kamu na yin koko, shine
sana'arta suna ta siya, da masu siyan suga.
Koda tayi sallama har ta shigo ta zauna
goggon bata dubeta ba har sai da ta gama
sallamar yaran da ke dakin sannan ne ta dubeta.
Munceba ta tashi ta risina a gaban Goggon ta gaisheta, wannan karon ta amsa bayabo ba fallasa, sabanin yadda ta amsa mata sallamar da
ta yi. Goggo ta dubeta tace,
"Ga yayyinki can cikin daki, ki shiga ku gaisa", (yayyin Mujeebu kenan mata guda biyu da ke aure a nan Dukkun). Ta mike ta shiga cikin
Dakin Goggon ta same su suna ta gyaran dakin tace, "Sannunku Adda Fadima, ashe kuna ciki,
na sha kun tafi gida ne" Fadima itace babba
kuma mai kirki irin mahaifinsu, halayyarsu daya da Mujeeb da autansu Isa, ita kuma mai bi mata Adda Zuwaira, irinta irin Goggo har kamannunta. Fadimata juyo cike da fara'arta tace, "Bamu tafi ba sai anjima, saboda saimun gyrama Goggo gida, kinsan taro akwai lalata
99
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
guri". Ta zauna bisa tabarma ta gaisliesu, ta
kamo 'ya'yansu tanamusu wasa. Sannan ta tashi
ta soma taya su gyaran dakin har suka gama,
suna yi suna hira da Fadima, ita kam Zuwaira sai
jefi-jefi take saka musu baki.
Suka dawo falon Goggon shima suka
gyara shi tastas. Munceba ta fita ta soma sharara
tsakar gidan, Fadima ta leko ta ce, "La Muneeba
shara kike yi? Don Allah ki barshi yanzu Isah zai
shigo zai share, amarya da shara da sassafe ai ba
kanta". Ta yi murmushi tace, "Bari kawai zanyi
ai ba wata wahala a sharar". Ta ci gaba da sharar
har ta gana, ta zo ta same su a dakin Goggon
suna hada abin karin kumallo koko ne da kosai.
Fadima tace, "Ki je ki kawoguri a zuba
miki, naki abin karyawan, kada ince kizo
cikinmu kunya ta hanaki sakin jiki ki ci abin
kirki". Hakan ya fi mata don ita koko bai dameta
ba gara nma kosan tana ci, amma sai bata nuna
bata ci ba ta je ta kawo jug da karamin flas din
abinci aka zuba mata, ta rike hannun filas din
abicin aka zuba mata, ta rike hannun 'ya'yansu
guda budiu ta ce su zo su je sasanta.
Da yake Inna Amina ta kawo mata
manyan gwangwanayen kayan tisai ta tafasa
ruwa ta hada ti ta sha da biskit, yaran ta raba
musus biskit amma bata ba su tin bạ don kada su
100
1
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
je su ce sun shati Goggo ta fsassara hakan da
wata manufa, zata iya cewa an bata abu bata ci
ba, sai tayi nata taci..
Ta sake dafa ruwan wanka da yake yaran
kanana ne, duk ta yi musu wanka ta aje ta amso
kayansu ta sa musu. Matan guda biyu tayi musu
kwalliyaa fuska suka dinga murna an sa musu
janbaki da abin ido. Itama wankan ta yi ta shirya
cikin wata doguwar rigar (bu berry) mai
tsukakken hannu kalarta ja, ta nada gyalan rigar
a kanta zuwa kafadanta, sai zahirin kyanta ya
fito ita kanta da ta duba kanta a madubi tayi
mamakin irin kyan da ta yi. Ta kama hannun
yaran suka koma sasan Goggo.
Ta tambayi Adda Fadima tace, ko akwai
wani aiki da za ayi yanzu. Fadima tace "Babu
wani aiki da za a yi yanzu ai duk kin gama,
wannan uban aiki dakikasha, tunda kika tashi
bakihuta ba, idan ma akwai wani aikin zamu yi
abinmu kada ki bata kwalliyarki kanina ya dawo
ya ganki butu-butu, gara ma ki tashi kije ki
shirya masa abin da zaki tarbe shi don yanzu
muka yi waya yace yana nan a hanya, ko ya kira
ki?" tayi karyar bai kira ta ba,duk da dai ya turo
mata text a wayauarta cewar yana hanya wai me
ta tanadar masa tana ganin text din, girgiza kai
kawai tayi cikin jin nauyin kalmar da ya yi,
101
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kawai saita bashi amsa, Allah ya kawoka lafiya
tace Fadima,
"Ni babu abindazan shirya masa, wanda za a yi
anan ai ya wadatar ko?" Fadima tace,
a
"To ki ne 'yan boko ke kikasan abinda za a yin
tarbanshi a matsayisa na ango, sai ki fadi
abinda za ayi in yaso sai Isah ya je ya siyo kayan
yin girkin". Таce,
"Adda ni kam da kunyi abinda kuka yi niyya, ko
tuwo kuka yi ai zai сỉ”.
Adda Fadima ta ce "Tunda kin ambaci
tuwu to bari ayi tuwon, amma na shinkafa ba na
hado komai sai kiyi mana miyar tunda kina da
risho, sai kiyi a sasanki mu kuma anan saimu yi
tuwon, bamu takuraki ba ko?" tace, "Haba Adda
ko duka kika ce inyi ai bazan takura ba", Adda ta
ce :"Ai ni wannan kwalliyarce bana so ta baci
kanina bai zo ya gani bashi yasa kika ga ina
kaffa-kaffa da duk wani abu da zai 6ata miki
kwalliyar". Munecba ta yi murmushi cike da jin
kunyar kalaman Adda Fadima, Goggo tacе,
"Ke kambaki da girma kannankima ba ki jin
nauyin fadin abinda zaki sa su jin kunya, wannan
dai sirikarki ce yanzu sai a kama girma", Adda
tace,
"Goggo inaban yi raha da kanina na basu
shawara ta gari ba da wa zanyi, ni kam har yanzu
102
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba Kanwata ce ba ruwana da wani
sarakuta, gara ma ki saki jiki da ni kamar irin da,
mu yi hirar mu cikin raha, kin san sanni duk
Kannena ina raha da su kuma hakan bai sa wani
ya raina niba". ta kare maganar tana kallon
Munceba.
Adda Fadima ta sa aka nemo mata Isah ta
bashi sakon cefanen da zaiyo mata harda nama ta
ce ya siyo yau zasu ci girkin amarya. Isah yaje
ya sayo komai ya kawo, Adda ta damka a
hannun Munecba, ita kuma ta wuce sasanta don
yin aikin da aka bata.
Cikin irc-iren miyar da Inna Amina ke
koya musu a Gombe, irinta ta zauna ta shirya
lafiyayyar miyar alayayyahu da gyada, wanda ta
nama sannan ta sa kori mai dadin kamshi,
kuma ta yi amfani da magi kusan kala goma, duk
cikin irin sayayyar kayan girki (spices) da Inna
Amina ta taho mata da su ne.
ji
Nan da nan gidan ya dauki kamshi har sai
da Isah ya leko sasan nata yana tsokanarta, "Wai
Amaryar Yaya har yanzu miyar nan bata
kammalu ba ne, kamshi ya cika gida, yawuce ya
fita har. waje ya cika unguwa, kowa miyansa ya
tsinke, ni dai nawa har zubowa yayi saboda
kosawa yau jama'ar unguwar nan ma sun son an
kawo amaryar da ta iya girki, wannan kamshi
163
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan