Zaria
Allah sai ya tada sumamıne". Ta kyalkale da
dariya tace,
"Kai Isah don Allah ka bar zuga ni, kada kasa
kaina ya fashe, wannan irinwashi. Na gama
koma, dama yanzu zan dau tukunya in kaiwa
Adda Fadima, ta gama tuwon ne?"yace,
"Nashigo yanzu na iske ta gama,Adda
Zuwairana taya ta suna kwashewa a food flask
din abinci".
Ta dauka miyar kacokan a tukunya ta
kawo musu, tana yi musu sannu da aiki su ma
suna yi mata, Adda Fadima sai da tayi mata
Korafin kamshin ya cika gida duk sun kosa a
kawo miyar su ci tuwo.
Adda Fadima tace Munceba ta kawo guri
a zuba mata ita da mijinta ita kuma Munecba
tace shi dai a zuba zuba masa amma ita tare da
su zata ci.
Duk wanda ya ci tuwon nan sai yayaba
dadın miyar Munceba hatta Zuwaira ta yabawa
Munecba a wajen iyagirki har Adda Fadima na
cewa "Lallai kwannan nan zan ga kanina da
Timbin ciki,don iya girki mai dadi shike sa miji
ya saki jiki yaci abincin matarsa har agaya yi
bul6ul". Ita dai Goggo duk tana jins batace
musu uffanba, dukda yake itama a ranta ta yaba
dadın miyar da Munceban ta yi,sai dai ba za ta
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yaba mataba tunda bata ga dalilin yabawar ta ta
don Munceban ta ji dadi ba.
Wajen karfe biyu saura na rana ne Isah ya
shigo gidan da jakar kayan Mujeeb, ya shigo
dakin Inna yana gaya musu ga Mujecb nan
yadawo', 'yan uwan duksuka dau murna ga ango
yazo, ga ango ya dawo, 'ya'yansu sukafella
kofar gida suna murnadaoyoyokawu oyoyo
kawu. Goggo tadubi Isah tace, "Ina kake neman
aje masa jaka?" ka kai masa dakin matarsa
mana", Isah ya dauki jakar ya wuce da ita sasan
Munccba.
Ita kam tana zaunc tamkar mutum
mutumi ta kasa motsi, in banda faduwar gaba da
ta dinga ji, tun da Ish ya shigo yace Mujcebun ya
dawo jikinta yayi mata sanyida bata san dalilin
hakan ba.
Ya yi sallama ya shigo dakin yana rike da
hannun yaran da suka je taransa ya risina ya
gaida Goggo yayi mata ya gajiya da hidima
sannan ya gaida Yayayinsa, ita kam Munccba da
kyar ta iya yimasa sannu da zuwa, sai a lokaçin
ne ta iya hada ido da shi yana sanayc da shir
maidogon hannu da wandon jeans, yayi kyau
sosai gashinsa na filanin Gombe ya sha gyara ya
kwanta luf a fatar kansa tamakar yayi masa
shamfo. Ya yi kusan mintuna goma yana hira da
105
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Yayyinsa tare da tambayarsu gajiyar hidimar
taro sun tabbatar masa koimai lafiya, basu san ya
riga ya sami labarin abinda mahaifiyarsa ta yi
ba,kasancewar dukansu bamai iya tada maganar
a gaban Goggon shi yasa ma Babu wanda zai yi
gangancin shaida masa anyi hatsaniya cikin
'ya'yanta, in dai a gaban ta ne, gara ma a bayan
idonta za su iya tattauna maganar sujajantawa
junansu, sabida suna takaicin wadannnan halaye
da mahaifiyarsu ke nunawa a bayanan nasu ga
duk wandaba takauna, ita sam babu ruwanta.
Mujecb ya mike sama ya dubi yayyinsa
yace, "Adda bari in shiga in dan huta kana kira
la'asar, amma bayanzu zaku tafiba?" Adda
Fadima tace, "Ana yin la'asar zamu tafian gama
taro me zamu tsaya yi kuma, ai gara mu koma
mun bar yara". Yace, "Shike nan kafin ku tafi
zanzo in ganku". Ya dubi Goggo yace,
"Goggonmu bari in dan huta sai na fito", tabishi
da kallo kawai tana girgiza kai har ya fice a
dakin..
Ko kwakwaran motsi Munceba takasa yi
tun shigowan Mujeeb har ya fita da kusan
mintuna uku bata motsaba balle ta yi alamun bin
sawun mijinta Adda Fadima ce ta dube ta tace,
"Ke banson jan aji irin naku na amare tashi ki
je ki ba mijinki abinci, muma da ba muyi bokoba
106
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ba zamu yi wannan kauyancinba balleke 'yar
boko, tashi ki tafi,bana son ana yiwa Kanina
wasarere". Ita dai saimurmushi take yi amma ta
kasa tashi, tana tsoron kada Goggo tace tayi
rashin kunya. Har sai da Goggon tayi mata
magana tunda ta lura nauyinta take ji, sannan fa
ta tashi sumi-sumi takammarwata munafuka ta
shiga 6angarenta.
Tana shiga taga bata ganshi ba sai taji
alamun shi a bayi don ga saukar ruwa nan
tabbacin yana ciki. yana wanka kenan. Ta nemi
kan kujera ta zuna a darare tamakar za a ce ke ta
arce, har ya fito wankan sanye yake da gajcran
wando sai tawul babba da ya rufo kansa yana
goge jikinsa da shi, kallo daya tayi masa tayi
surin rintse idanunta ta sunkuyar da kanta a kasa,
ganin haka da tayi shimasai yaji kunya ta
kamashi yayi saurin shigewa daki ya saka
jallabiya mai gajaren hannu sannan ya fito. Tana
gaisheshi, yayi murmushi yana amsawa, ya kara
da cewa,
"Ai min gaisa, ko da yake bahaushe yace
yawan gaisuwa yafi yawan fada". ta zauna kan
kujera suna fuskantar juna, yace,
"Kaqo mini manki in shafa". Tayi hanzari ta
shiga dakinta ta dauko masa daya ciki mayukan
da aka zubo mata a akwati ta kawo masa, tace;
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Wai da ruwan sanyi kayi wanka ne?" da ka
jira na zo na dafa maka", yace,
"Kada ki damu kanki, na riga na saba da
wanka da ruwan sanyi, duk wanda yayi
makarantar kwana ai ya saba ko ke ba kya yi da
ruwansanyi a makaranta?" tacc, "Ina yi tun ban
sababa ina yawan yin mura har na saba,murarma
na daina yi", yana gama shafa man ya shiga ya
sa kaya, yadi ne yasa amma dinkin karamar
rigace yayi kyau sosai ita daisai kallonsa take yi,
shi dai ko wane irin kaya yasa sai sunyi masa
kyau, tamkar jikin mace haka kaya suke masa
kyau.
Ta dubeshi tace "Ga abicni kazo kaci
tunda ka shirya", ta nuna masa kayan abincin da
ta shirya akan teburin tsakiyar dakinta, yace,
"Sauko su Kasa sai mu ci ko banda ke?" ta
girgiza kai tace, "Munci abinci tun dazu, na
koshi", ta sauko da kayan abincin bisa chinis
kafet din da ke tsakiyar dakin, ya zauna ta
mikamasa ruwa a roba ya wanke hannunsa,
itama ta zauna suna fuskantar juna abicnin na
tsakiyarsu, ta zuba masa a filet ya soma ci
sannanyace,
"Yanzu ba zaki taya ni ci ba? Ko kunya ta
kikeji?" ta girgiza kai ta yi murmushi yace,
"daga yau ki sani tare zamu dinga cin abinci aim
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
un zama daya, sai dai idan bana gari", ta yi
magana cikc da jin kunya tace,
"ta gaskiya bazan iya ba, ka yi hakuri kawai",
ya gyada kai yace "lallai Muneeba dasauranki".
Suna hirarsu har ya gama ta zuba masa
ruwa ya wanke hannu, ta zuba masa ruwa ya
wanke hannu, ta kwashe kayan ta fita da su ta
dawo, suka koma kan kujera suka zauna, amma
fa sam bata yarda ta zauna kusa da shi, ya dube
ta yace, "Girkin nan yayi dadi sosai waya yi?"
tace, "Adda Fadima tace inyi miya, su suka yi
tuwon", ya gyada kai yace, "Na yaba kwarai
miyarki tayi dadi ashe kin iya girki", ta yi
murmushi tace, "Ina dai koyo, ni me na iya ku da
kuka saba cin abincin 'yan gayu a Gombe mu
anan me muka iya",,yace,
"Wayace baku iya ba? Ke ai tudu biyu kika iya,
kin iya na gargajiiya a Dukku, sannan kin koyi
na zamani a Gombe gidan Mama Amina ko
bahaka ba?" ta ce "Eh haka ne na iya ba laifi".
Haka suka yi ta hira mai dadi suna kara
fahimtar junansu. Abinda Mujeeb ya lura
Munecba yarinya ce mai ladabi da biyayya gashi
ya lura ba zai sha wahala wajen fahimatar da ita
al'amuran da suka danganci zamansu na
auratayya ba. Kiran sallar la'asar ne ya katse
musu hirar da suke yi mai dadi, Mujeeb yayi
109
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
alwala ya fita masallaci, ita ma Muneeba taje ta
yo alwala tayi sallar la'asar.
Mujeeb tare suka shigo da Adda Fadima,
saboda za su tafi gidan mazajensu Munecba ta
cc, "Adda wallahi kamar kada ku tafi gidan zaiyi
tsit! Babu dadi, ko zaki barmin yaran gobe sai a
dawo da su", Adda Fadima tace, "Rufa min asiri,
wadannan rigimammun ai ba za su barku sakat
ba, nan gaba sa zo su yi muku kwana biyu", tacc,
"Shike nan Adda Allah ya kaimu. Har da Adda
Zuwaira tare zaku tafi", tace
"Eh, duk yanzu zamu tafi, amma ita ga mijinta
nan zuwa zasu tafi a mashin dinsa".
Muneeba ta shiga cikin kuryar dakinta
tayi tsam da ranta tana tunanin me ya kamata ta
ba Yayyin mijinta. Akwatin kayan shafanta ta
ciro sabulai da wasu kananan mayuka da su jan
baki da gazal da man le6e ta zuba a leda biyu, ta
fito ta mika wa Adda Fadima tacc, "Gashi a
kaima 'yan mata su Dija, wannan ki ba Adda
Zuwaira ta kaiwa su Hindu", Adda Fadima ta
amsa tana ccwa, "Kai Munceba har da
dawainiya, to an gode", ta leka cikin ledar tace
"Kai! Kai! Lalali yau kin birge 'yan mata akwai
tsallcn murnaan sami kayan kwalliya".
Adda Fadim tayiwa Munceba nasiha
sosai ita da Mujccb akan su zauna lafiya, su
110
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tabbata biyayyar da suka yi har zuciyarsusuka yi,
kuma domin Allah suka yi, saisu ga zamantakewar aurensu tayi aminci da nagarta. Ta kara
da cewa, "Don. Allah Muneeba ki kara hakuri
kan hakuri a zaman takewar ki da Goggo, ke ba
bakuwa bace a gidan nan kin riga kin san halin
Goggo, basai an sake karanta miki ba, to don
Allah ki ci maganin zama da ita tamkar yadda
Innarki take hakuri da ita, Gogga na son
Mujeebu sosai kada ki sake a gabanta ki nuna
kina sonsa sosai, kada kuma ki nuna masa rashin
kulawa duk ba zata dauke suba, ki yi
al'amuranki da mijinki sosai sosai, kuma ki bita
sau da kafa sai ku zauna lafiya, kaima ka kiyayc,
ka dai riga kasan irin matsayar da aka yi
auranku, ka san a wace turba Goggo take, to sai
ku lallabata don a sami zaman lafiya Allah ya
kade fitina ya hada kawunanku, mu zomu sha
suna kafin shekara ta zagayo" dukkansu
murmushin jin kunya suka yi, ita kam Muneeba
ma kara risinar da kanta ta yi kasa, dama ta san
Adda Fadima akawai zolaya da barkwanci ita
babu ruwanta har kannenta idan an hadu da wasa
da dariya ake rabuwa.
Dukkan su suka fito zuwa dakin Goggo
suka iske nar mijin Zuwaira ya zo tana haramar
fita su tafi Goggo taсс,
111
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Daga shiga sallama kinje kin shantake dakin
sirika, ke wai wace irin Yayar kwabo ce?" tace,
"Kai Goggonmu, ni fa Munecba ba sirika ta
bace, kanwatace, babu wata kunya a
tsakaninmu", ta nunawa Goggon abinda
Munecba ta bayar su kaiwa yaransu sannan ta
mikawa Zuwaira tayi mata bayani.
Zuwaira ta dubi Muneeba tayi mata
godiya.Gaba daya suka fito don tafiya. Zuwaira
ta hau mashin din mijinta suka tafi ita kuma
Adda Fadima sai Mujeebu ya rike mata jakar
kayanta ya rakata bakin hanya ya samar mata
mai mashin suka yi tsada ya bashi kudin suka
hau suka tafi tasu unguwar a nan Yelwa.
Saida Mujceb yayi sallar magriba ya
tsaya yayi isaha'i a masallaci, sannan ya dawo
gida, duk daya yi wa Muneebanwaya ya gaya
mata inda ya tsaya, amma sai yaji ya kosa
yadawo gida kila tana can a sasanta itakadai.
Akan sallaya ya samcta ta idar da
sallointa tana ta lazimi, sai ya nemi gefen gado
ya zauna har ta idar da lazimin, ta shafa addu'a
sannan ta dube shi tace, "Sannanu da dawowa",
yace, "Yauwa, da har zana tsaya hira sai na tuna
zaki zauna ke kadai, shi yasa na daw in tayaki
hira", tacc, "Ka kyauta, yanzu me zaka ci
Goggo ta ce kada ayi girki tunda akawaı sauran
112
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
abinci a food flask da yawa", yace, "Ai ni ban
cika cin abinci mai nauyi da dare ba, kuma ai
ban dadade da cin abicniba, idan zan kwanta
zanasha ruwan ti". Tacc, "nima shi nake sha idan
zan kwanta, damana zuba ruwan zafi a filas, ga
kayan ti can su Madara da suga da lipton da
biskita Inna Amina ta zo min da su", yace,
"Ai ke 'yar gatan Inna Aminace, na san ma zata
so ace a Gombe kika zuana, gaki ga tada kulawar
sai tafi haka", ta murmusa tace,
"Ai Inna Amina tayi zarra akan son 'ya'yan
'yan uwa da kyautata zumunci, gaskiya samun
irinta sai an tona, tana iya bakin kokarinta don
ganin tayi zumunci da kowa, kuma Jakarta da
hannunta basa gajiya gurin yin alheri ko hidima
da 'yan uwa hatta makotan ta na can Gombe
masu karamin karfi tana kokarin taimaka musu,
shi yasa take samun yabo sosai", ya jinjina kai
yace,"Shi yasa ni tana birgeni sosai babu
ruwanta idan ta zi garin nan kowa nata ne, sai
kuyi kokari ku yo koyin halayyarta", tace,
"Insha Allahu zamu kwatanta".
Sun kai kusan sha daya na dare suna hira
har sai da ya lura ta soma doka hamma sannan
ya tsayar da hirar tasu ta hanyar yi mata umurni
da ta je ta kwanta, ganin ta noke sai shima yaсс
baccin yakeji su je sukwanta.
113
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Ya yi mata umurni da su yi alawala su
gabatar da nafila tare da yin addu'o'in don Allah
ya sanya albarka aaurcnsu, kuma ya kade fitina.
Bata yi jikinri ba ta je ta yi alwala suka yi sallar
tare da addu'o'in da aka umurci ma'aurata su yi
a daren farkon aurensu.
Ya umurce tada ta hau gado takwanta,
tasoma'yan noke-noke ya dubeta yana dan
murmushi yace "kunyar kwanciya tare da ni kike
yi?ko kin manta yanzu ni mijinki ne?? ta dube
shi a kunya ce tace, "Na sani, amma gaskiya ina
jin kunya bazan iya kwanciya gado daya da kai
ba", yace, "To shike nan kwanta a gadon ni bari
in shimfida wannan bargon sai in kwanta a
kasa", ya dauko bargin da ke bisa gadon ya
shimfida tare da jefa filo yana shirin kwanciya
tace,
"ba zai yiwu ka kwanta a kasaba tunda gadon
nan dominka aka kawo shi, ni dai bari in kwanta
a kasan kai ka hau gadon tunda naka ne banawa
ba", yana 'yar dariya yace,"niba nawa ba ne ni
kadai, in dai kin yarda to namu nemu biyu har da
ke,kawai ki yarda mu kwanta tare tundayana da
girma babu wanda zai matsi wani balle ki ce zan
matse ki", ta girgiza kai tace,"Nacigirma a
matsayina na babba ni zan kwanta a kasa ke ki
114
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kwanta a gadon kada kiyi min musu oya zo ki
kwanta".
Babu yadda zata yi saboda ganin babu
wasa a fuskarsa dole ta haye gadon ta kwanta,
yana dubanta yace, "kiyi addu'a kada ki manta
kiyi bacci", ta ce "To," ya kashe fitilan dakin
sannan yayi addu'a ya kwanta.
Zaman kwana biyu da Mujeeb yayi a Dukku tare
da amaryarsa Muneeba, ya haifar musuda
shakuwa da juna sosai, a dalilin sun dan soma
fahimtar halayyar juna kuma ga dukkan alamu
kaunar da suke wa juna ta jinin 'yan uwantaka ta
soma rikidewa zuwa soyayya, wadda su kansu
basu san yaushe soyayyar ta fara ratsa zukatansu
ba, su dai sun san idan suna tare basa son daya
yayi nisa da daya tunda shi kansa Mujeeb idan
yana tare da Muneeban suna hira, sai yaji sam
baya son lekako da kofar gida ne balle yayi nisa
da gida, ita ma haka abin yake ta 6angarenta, ko
aiki zata yi a kicin ta fi son yana kusa da ita
saboda lura da tayi mijinta gwani ne wajen iya.
soyayya da tarairayar mace, sai hakan ke mata
dadi, kuma hakan na birgeta, har bata san
115
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
lokacin da ta sake kunyarsa da ta ke jiba ta soma
sakar masa jikinta sauyi wasansu na ma'aurata,
amma hakan bai saya nemi hakkinsa na aure a
gurinta ba duk kuwaiya wasan da zasu yi, sai dai
ta lura idan yana san ya canza yakan yi sauri ya
kyalcta ya shiga bayi yayi ta shckawa kansa
ruwan sanyi, sai tayi haka take ganin ya dawo
dai-dai.
Da safen ranar da Mujecb ya kwana uku a
gari, misalin sha daya na safe, suna zaune a
falonsu suna kalln wani kaset din wa'azin sheikh
Kabiru Gombe, kan Muneeba na bisa cinyar
Mujeeb yana wasa da sumar kanta yayi magana
cikinsanyin murya,
"Gobe fazan koma Gobe, muna da text, dazun
Yusuf ya kirani yake gaya mini". Tayi saurin
juyowa tanakallonsa a raunane tace,
"Ni kam wallahi bana son tafiyarką zanyikewa
sosai". Ya kamota ya riketa gam a jikinsa saboda
hawaye da ya ga idanunta ya soma fiddawa yace,
"Yi hakuri kwana biyu ko uku zanyi in dawo,
kuma ba lallai sai week end ba duk lokacin da
karatu ya tsagaita mini zaki ganni ko da yini ko
kwana daya ne zanzo in ganki". Ta langabar da
kanta a kafadarsa shi kuma sai lallashin. yake yi
ta dago ido ta dube shi ta ce". "Ni yaushe zan
koma makaranta?" yace, "Shine abin da nake
116
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tunani kila transfer za a yi miki don ba zai yiwa
ki ci gaba da makarantar kwana da aure a kanki
ba". Ta ce, "Saura fa 'yan watanni mu zana
"JSCE) ka yi hakuri ka barni in zana jarabawar
in yaso SS1 dina sai ka canza mini kamaranta".
Yace,
"Zamu yi shawara abinyi tunda hutun naku ya
kare".
Washe gari da zai tafi, tun safe take masa
kuka duk sai hankalinsa ya tashi ya rasa yadda
zaiyi da ita, tunda yayi lallashi iya lallashi abin
ya gagara, sai yace, "to shirya mu tafi sai ki je ki
gayawa Goggo zaki bini". Ta make kafada "niba
zan bika ba",, yace "to ya kike so ayi yanzu?" ta
yi shiru tana goje idanunta yace, "Ki yi hakuri ki
kwantar da hankalinki in bahaka ba zakisa nima
hankalina yaki natsuwa guri dari daya, ko kina
son in kasa tabuka abin arziki a makaranta har in
fadi gwajin da zamu yi?" tace, "na ji na hakura,
Allah ya kiyaye ya bada sa'a".
Da kanta ta gama yi masa shirin kayansa,
har yana mata tsiya tare da bata labarin irin tsiyar
da zai sha a gurin Yusuf idan ya koma a dalilin
sun yi da Yusuf din kwana daya zaiyi ko biyu
sai gashi yayi kwana har hudu kuma ba don.ya
kira shi ya gaya masa za su yi text ba da ba zai
koma ba, shine tun a waya ya fara masa tsiyar
117
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
wai tunda amarya ta rike shi yana nan zuwa masa da Karin kayan sawa tunda kala biyu ya febo shine yace masa in ka so ka debo duka ne
mara kunya yaro, suka yi ta dariya wayar. Da zai tafi ta rako shi iya bakin kofar sasanta yayi-yayi ta raka shi gurin Goggo taceba zata iyaba, ammatana labe tana kallonsa har yayi sallama da Goggo ya fita ya tafi, kawai sai taji saukan hawaye masu dumi a kuncinta ta juya ta koma daki, ta haye kan gado ta janyo bargon da suke lullubec ta shige ciki ta dukunkune tana aikin zubda hawayc a dalilin kewar mijinta da zata yi, na wasu kwanaki, gashi yayi mata sabo da kwana a jikinsa yana mata 'yan wasanni da labarai har ta yi bacci haka yake mata, cin abincinsu tare ne, wanka ne kawai bata iyayi tare da shi, amma idan zai shafa mai, zuwa sa kaya duk tana taya shi suyi tare in girki take yi tare suke yi yana taya ta, Goggo tace ita ta dinga yin girkin rana, ita Goggo take yi musu tuwon dare kasancewar Goggo tafi son tuwo da daddare, shima Muneeban bata bari ta yi itakadai zuwa take yi ta taya ta har su gama.
Ranar Juma'a da yamma lis Muneeba na
sasan Goggo tana taya ta aikin tuwon dare, bayan ta gama tace mata kullun kokon sayarwa da takc. A gaskiya ayyukan da Goggon ke loda
118
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
mata suna son su yi mata yawa, kusan ayyukan
gidan nan kaf ita takc yin su, tun safe idan ta
tashi ta zo gaida Goggo zata taya ta su hada abin
karyawa idan ma Gogon na hidimar cikinta na
safe to itace ke hada abin Karin safen, sannan ta
gyarawa Goggon daki ta share dakin zuwa tsakar
gida, itace keyin wanke-wanke, sannan a gurguje
take zuwa ta yi nata abincin rana, wani lokacin
ma gyaran dakin nata bata samun yinsa sai ta
dora girkin rana, sai fa ta gama girkin ne ta ke
samu ta yi wanka.
Sam bata samun sukunin hutawa shi yasa
bata yi wani kyan amarci ba, duk ta susuce cikin
'yan kwanakin da mijinta ya tafi ya barta.
Goggo ta dube ta tace, "Yau na lura tunda
mijinki yayi waya zaizo sai rawar jiki da murna
kike yi, 'ya'yan yanzu kuna ban mamaki akan
son da namiji, sai ya gunguma muku tsiyarsu ta
maza, sannan nekuke shiga taitayinku, ku zama
abin tausayi". Goggon ta numfasa bayan ta gama
gano yanayin soro da ya shigi zuciyar Muneeban
har ta bayyana karara a fuskarta ta kara da cewa,
"ina ce kwannan nan zaki koma makatanta?"
Munecba ta gyada kai tace,
"Eh, mun kusa komawa" ta ce "shine
kik shisshigewa miji, idan ya banka maki ciki
kin dai san bazasu barki a makaranta ba tunda
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
naji ance ka'idar makaranta kwana ba a yarda
aga mace da ciki ba ko da tana da miji,
hukuncinta kora ne, kinga idan korarki za suyi,
shike nan kinyi asarar karatunki, tun wuri gara ki
kama kanki shi namiji babu kiwansa idan ya
sami biyan bukatarsa me kuma ya saura? Ke
cuta shi yana nasa karatun ke ki rasa naki, kinga
wa gari ya waya in ba ke ba, nan gaba yana iya
auro 'yar boko 'yar uwarsa".
Jikin Muneeba yayi sanyi kalua, tsoron
abinda Goggo ta fada ya shigeta, nan ta shiga
taitayinta, hakika zancen Goggon hakkun
gaskiya ne, muddin ta saki jiki ta biye wasan ran
Mujeebu to zata wayi gari ta ganta dauke da ciki,
kuma tabbas haka na faruwa to karatun ta zai
salwanta kenan, ita kam duk abinda zai sa ta rasa
karatunta bata sonsa, tana son tayi ilimi sosai
tunda shine burin mahaifinta ita ma shine
burinta, saboda ta haha dole ta dauki matakin
gaggawa don hana faruwar wata miskila daga
gareta, tunda dai shima Mujeebun bai taба
marmarin neman hakinsa ba, in ma zai nema to
ba fa zata yardaba don ba zai yi mata sakiyar da
babu ruwa ba.
Har Goggo ta kare yi mata wannan
huduba da bata kamata ba, ita dai tana sauraronta
batace uffjanba illa dai tana gyada kai tabbacin
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
zancen yana shiga kwakwalwarta kuma yayi
tasiri, ita ko kallonta Goggon ta gano hakan
kuma wannan shine tarkon ta na farko da zata
fara danawa Munecba, wasu kuma zasu yi ta
biyo baya wadanda za su dasa kiyayyar
Muneeba a zuciyar Mujcebu, dama ta gayawa
iyayen Munecban da jagororin hada wannan
aure kowa ya ci tuwo da ita to miya ya sha bai ci
tuwon ba kai miyar ma bai sha ba sai daisude
kwano.
Wannan hudubar bata hana Munecba yin
wanka ta yi kwalliya cikin kanana kaya sabo da
Mujeeb ya gaya mata yafi son yaga ta sa kanana
kaya, sai kuma Allah yasa tana da su, da bikinta
ya taso ma Inna Amina musamman ta shiga da
ita kasuwa ta saya mata, saboda ta san Mujeeb
dan boko ne kuma dan gayu dole sai tana masa
gayu sosai in kuma ba haka ba to zai je ya kalla a
jami'a ko yana so ko bay a so.
Shigowar dare yayi bayan sallar isha'i shi
yasa bai iskcta a sasan Goggo ba tana nasu
sasan, ya dade a gurin Inna suna hira ya fiddo
tsarabar da ya zo musu da ita yaba Goggon duka
yace ta raba ta cirewa Munecba. Hakan yayi wa
Goggo dadi ganin irin nuna fifikon da dan nata
yayi mata. Ta dibi abinda zata diba tace ya
wucewa Muneeba da nata, kayan ciyc-ciye ne,
121
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
sai kayan masarufi. Hankalin Mujecb duk ya riga
ya tafi gurin matarsa don ya riga ya gaya mata а
waya gashi ya shigo cikin gida ammazai fara
shiga gurin Goggo, sai gashi ya shafe fiye da
minti talatin Gogon na jansa da labarai har
Muneeban tayi masa filashin, ya san ta matsu da
son ganinsa ne, ya samu dai ya shiga
bangarensu, tunda yayi sallar isha'i a masallaci
kafin ya shigo sai kawai ya maida sakatar
sasansu ya rufe, kila in ba larura ba babu abinda
zai fito dashi.
Da yake akwai wutar nepa, shi yasa yana
yin sallama ya ga Munceban bisa kujera a zaunc
tana kallon kaset din wa'azi. Sauri tayi ta taso
cike da murna da dokin ganinsa, ta amshi kayan
hannunsa, shi kuma yana kokarin ya hada ta da
jikinsa,amma sai ta kaucewa faruwar hakan
saboda ita yanzu sam tsoronsa takeji, kuma
tanatsoron duk waniabu da zai salwantar mata da
karatunta.
Bakinta ya kasa rufuwa, sai faman yi
masa sannu da zuwa take yi, ya amsa tare da
cewa, "Zan sami ruwan wanka?" tace "Eh, gashi
can bari in juye maka". Ta wuce cikin bayi, ita
kuma ta fita kicin don debo masa ruwan wankan.
Tana shiga bayin da bokitin ruwan ta iske har ya
soma tube kayansa, tayi hanzarin ajiye ruwan
122
WATA KUSAN 1 Ráhmatu Hassan Zaria
zata fita, yayi magana Ina kuma zaki je? Zo nan
ki taya ni, tayi magana fuskarta na can gefen
"Don Allahka yi hakuri wallahi bazan iyaba,
kunya nakeji". Yace
"Nikam ban taba ganin inda mata kejin kunyar
mijinta irin naki ba", tace,
"Ni dai kayi hakuri nan gabazan taya ka amma
ba yanzu ba", ta fice da sauri saboda taji
alamunsa a bayanta.
Ita ta tayashi ya shafa mai ya shirya cikin
riga da wando na bacci, sannan ta fara jero masa
kayan abinci, ya dakatar da ita, "kinga bar kayan
abincin nan kadan zanci, zo ga tsarabarki". Ya
janyo ledar da ya zo da ita ya soma fiddo kayan
ciki kayan ciyc-ciye ne, su biskit da chakulet
masu dadi sai robobin yegot, da kayan ti sai
gassassar kaza dankwaleliya, Gogo ma ya sayo
mata, duk ta cire nata,.
Sunci abincnin tare suka sha yegot suka
ci naman kazan, suna dan taba hira tana bashi
labarin abubuwanda ya faru da baya nan kamar
baki da tayi ta yi, da irin kewarsa da tayi, da
tsoron da ta dinga ji ranar da ya tafi da dadddare,
yayi ta mata dariya. Yace,
"Amma kuma me yasa ki rama, kinyi ciwo da
ba nan ne?" ta girgiza kai, sam ba zata iya gaya
inasa cewa arin ayyukan da Goggo ke lafta mata
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ne yasa tayi rama ba, saboda har zullumi take
ace gari yawaye to fa idan ta fito sasanta tun
daga zuwa gaisheda Goggo zata soma ayyuka,
kuma