musu don kada ina nan ina
yada manufata ban sani ba kawai in ji ance anba
wani kato a can Dukku, da anyi yaki na kin
karawa don bazan yardaba, don 'yan gidansu irin
auren da ake musu kenan a hade-hade". ita dai
Muneeba barinsu ta yi a falen ta je duba girkin
da ta dora.
Tana kammalawa ta sl irya masa a babban
tire ta dora ruwa da juice dak da ta san akwai
ruwan da juice a dakinsa hak an bai hana ta hada
44
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
da su. Tana fitowa falo ta aje tana jiran wani
cikin yara ya shigo ta bashi ya kai masa. Khausar
tadubeta tace,
"Amma ba ke zaki kai masa ba?" tace,
"Haba dai tunda Mama tace yanzu mun fara
girma mu daina shiga dakunan Yayyinmu maza
ai na dauki maganarta". Khausar ta ce, "Ranar
baki ji surutan da Yaya Sadiq ya dinga yi ba, wai
an hana mu zuwa gyara masa daki ko kai masa
wani abu me ake nufi da haka, ba a yarda da
tarbiyyar da aka yi masaba ne ko mene, shine
Mama tace ai duk gidan anan babu yaron da ta
yarda da nagartar tarbiyyyar zuciyarsa irin sa, sai
dai bata isa ta hana sharrin shaidan yayi tasiri a
zuciyarsa ba, saboda alkawarin da shaidan yayi
na yin galaba gurin cusawa 'yan adam duk irin
abubuwan da yake so don su sabawa Allah”.
Munecba ta ce,
"Allah dai ya tsare zuciyar mu daga afkawa
sharrin shaidan, amma mutane nawa ne
nagartattu masu riko da adddini irin Yaya Sadiq,
la'ananne shaidan yake yin nasarar gurfata musu
zuciya har su afka cikin tarkonsa, shi yasa idan
Allah yayi hani da abu to ko kusa da shi kada ka
kai kanka, ka nisanci abin sai Allah ya kiyayeka,
sannan yin addu'a babban abu ne Allah dai ya
45
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tsare dukkae musulmi, ya bamu ikon bin
dokokinsa
Sai da hutunsu Muneeba ya saura sati
daya aunan ta je Dukku, tayi sati daya sannan
suka koia makaranta suka kama karatu gadangadan babu kama hannun yaro a dalilin zasu
sa ajuuku na karamar sakandare.
***
vunecba don Allah ki ware kafa kiyi tafiya
vonnan irin lakai-lakai tafiyarmu sama ta ki
sa ri", Murja ke wa Muneeban korafi, unguwan
zasu je kusancewar duk hutu in dai Munecba na
gari o tare zaka gansu. Munceban ta harari
Murja tacе,
"Wallahi baki isa ki sani tafiya ina sassarfa ba
ina haki ki barni inyi tafiyata yadda na iya ke ma
saan na dole kike saboda Yaya Mustaha yace
yaua jiranki, ni kam tunda ba mai jirana sai a
kyaleni in yi lakai-lakai dina". Murja taja tsaki
tace,
Ai gashı nan kin ja maza sai kallonmu suke yi”.
"To ke yanzu ina ruwanki da kallon da suke
mana, sun dade basu kallemu ba".
Dai dai kofar gidan Hakimi suke hangi
dandanzon amari a zaune ana ta hira, ai ba bu
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
arziki Munecba ta ware kafa ta soma sauri saboda ji da tayi wani cikin samain nen yace, "Kai!Kai! yau ga mutuniyarka a gari ashc ta dawo, walalhi wannan karon kada ka yarda ta sille maka baka gabatarda kanka garcta ba idan kuma ka tsaya kallon ruwa to kwado zai yi maka kafa wallahi". Wadannan kalmanne suka sa
Muneeba karawa kafarta kaimi tana ji Murja na tsokanarta
"Kinji ko Muneeba da ke suke gasu nan ma
sun biyo mu". Ashe kuwa da gaske sun biyo su,
sai takun sawunsu ta ji a bayansu suna magana.
"Salamu Alaikum, don Ailah Muneeba ki tsaya
ba wani abu ba ne izini zaku bamu sai mu iskoki
gida". Takaici ya cika cikin Muneeba na yadda
aka yi har sunanta ya zauna radam a bakin
wannar saurayin, lallai yayi bincikene akanta har
ya san sunanta. Ta juyo a fusace rantaa басе
tace,
"Don Allah Malam ka yi hakuri ba ma hira da
samari ko gidan kuka biyomu balle akan hanya".
Tana gama fadin haka ta kara sauri. Ganin Murja
zata fita sauki shi yasa suka maida akalar
maiyarsu ga Murjan yace,
"Ranki ya dade ki rokar mana ita ta dan
sauraremu, wallahi aboki na gashi nan Badaru
dan wajen Hakimi shine ke tsananin sonta
47
WATA KUSAN 1 Ranmatu Hassan Zaria
wancan karon da ya ganta kafin yaje gida aka се
ta koma makarantar kwana haka na lallashcshi
da kyar ya hakura, shine yau kwatsam muka
ganta kinga ai ba zamu yi saken da zatą sake
subuce masaba, kinga itaba zama take a garin ba,
shimaba nan yake zama ba, gara tunda yau Allah
yasa ya ganta ta dan saurareshi". Murja tace,
"Eh to żata saurareshi amma ba a titi ba hakan
ba tarbiyyarmu bace dukanku tunda kunsan gida
kuna iya zauwa anjima, ni na ari bakinta na ci
mata albasa”. Sai a lokacin Badarun da kansa
yayi magana,
""Shike nan mun gode zamu zo gidan anjima,
sai ki gaya mata, kuma don Allah a isar mini da
sakon gaisuwa kafin inzo”. Da gudu-gudu Murja
ta kamo Muneeba, saboda tafiyarta tayi ta barta.
Suna haduwa tace,
“Amma dai kin zubar da ajinki, meye na wani
tsayawa kina sauraron maza a titi kinsan kuma
an hanamu, zan gayawa Yaya Mujaheed zaki yi
masa bayani wallahi ba ruwa na”. ta riko hannun
ta ta na cewa, "Haba kawalli kada mu yi haka da
ke, nima bada son raina na tsaya ba, jin sun cе
don Allah shi yasa na sauraresu sannan ga uban
kwarjini da shi Badarun ke da shi, kema da kin
tsaya kwarjinin zaiyi miki harki saurare shi".
Tace,
48
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ni bai isa ya yaudareni da kwarjininsa ba
dama haka na ji labarinsa yaudara 'yan mata gare shi ko can inda yake aiki ance mata yake
tarawa a gidan sa". Murja tace,
"Kai Muneeba zato dai zunubi ne, sannan ba
kyau kayi mummunan zato ga dan uwanka
musulmi kuma nace idan ba zaka fadi alkhairi ba
to kayi shiru, ke kuwa duk inakika samu
wadannan labarin?"tace,
"Ai kuma na daina magana akansa kada in
hanaki sonshi, babu ruwana idan kina sonshi
kada kiji haushi na akan ina aibunta miki
masoyi". Tace,
"Kina dai aibunta masoyinki, ni 'yar aike се
zuwa gareki, yace yana nan zuwa gida anjima sai
ki san yadda zaki yi da shi idan ya zo, ni babu
ruwana". Muneeba tace,
"Za kuwa kiga na turo miki shi tunda ke kikajajibo shi".
Da ire-iren hirarrakin har suka canza
hanya don kuwa Muneeba ta ce ba zata bi hanyar ba, gara su bi hanya mai nisa, sannu ai bata hana
zuwa inda za aje sai dai a dade ba a jeba.
Da daddare bayan sallar isha kawai sai ga dan aike yayi sallama a tsakar gidansu Muneeba,
abinka ga lokaci na zafi duk jama'ar gidan suna
49
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tsakar gida wasu akwanece bisa tabarma wasu a
zazzaune ana hira. Yaron yace,
"Anee ana kiran Munceba a kofargida". Matan
gidan sukanuna masa kofar dakinsu Munceba
inda take zaune kan tabarma da fitilla a gabanta
tanakarat Yaron ya sake maimaita mata aiken
da aka yo nasa tace,
"Kaje kace tayi bacci".Yaron ya juya ya tafi.
Matan gidan sai aka soma 'yan tsegungumi su a
tunaninsu bataji yo hirarasu,
"Af ai daman a san za a rina, yarinya na
tinkahon da ilimin boko ne zata saurari samarin
garin nan, ai wuce nan miji sa a garin Gombe ko
Bauchi ko Yola". Abokiyar hirar ta ce,
"Su ma samarin basu da zuciya ne, yarinyar
nan duk zuwa sai sun aiko don kiranta bata taba
fiita gurin kowa ba amma basa dandara gobe ma
zaki jı kirar wani, wahala bata ishe suba tunda
tta natsu" Sai ga yaron ya sake dawowa
wann karon da Katuwar leda a hannunsa fara
sol riai tambarin shagunan kas ashen ketare, kai
tsayə inda aka nuna masa dazu ya zuce bayań
saliama da yayi. ya aje kayan a gaban Muneeba
yace,
"Wa gashi iden ta tahi baccin a bata akwai
takarla a ciki wai ta karanta". Munecha ta ja
tsaki tace, "dauka ka mayar masa ka ce wai ya
50
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zara
rike abinsa ta gode". Matan gidan kwa duk sun
zuba idanu suna son ganin ko M.uneeba za ta
amshi kayan alhalin ta ki fito sai suka ji taсс
amayar, har yaron ya dauki ledar sai mariya ta yi
karaf ta ce,
"Idan baki so mu ki bamu, wa ke maida alheri
in ba shaidan ba, in banda abinki wannan da gani
ko wanene dan boko ne irinki kuma yana da
maiko ko da ganin wannan ledar kasan ta fito ne
daga gidan mala'u. kai ajc ka tafi ka ce angode"
Yaro ya aje ka ledar a gaban Muneeba ya wuce
ya tafi abinsa. Innarsu Munecba tana daga daki
tana jin wainar da ake toyawa. Larai ta gaza
hakuri ganin Munneeba tayi biris da kayan bata
ko kallesu ba balle ta taba. tace,
"Muneeba ki duba abin da ke ciki mana idan
akwai na lasawa a bamu namu rabon dama muna
zaune baki yayi tsami kwadayi ya addabemu,
mun rasa abin lasawa sai ga tsuntsu daga sama
gasasshe kinga ai ba maki ci ba". Abin yaba
Muneeba takaici da dariya, a zuciyarta tana ta
addu'ar Allah yasa babu abin ci a ledar ta ga ta
karyar kwadayi.
Ranta baisoba ta taba ledar tunda ita bata
yiniyar ta6aledar tunda itaba tayi niyyar taba
komai nasa ba don ba sonsa take yi ba, idan ya
dawo maida masa kayansa zata yi. Ta duba
51
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kayan shafa ne sai wasu biskita da chakulet masu
tsada su ta diba ta kai musu suna amsa suka
soma kasafi, nan da nan kika ji santi na tashi. Ita
dai Muneeba ta wuce daki da ledar, ta zayyana
wa Innarsu wanda ya aiko mata da su kuma ta
bayyana mata ita fa bata sonsa sai Innan tace to
aje kayan har babansu ya shigo sai suyi masa
bayani
Sai da safe sannan Innarsu ta yi wa
Babansu bayanin komai. Shima tunda yaji
bayanin Muneeba da dalilinta sai shima ya goya
mata baya don ba zai matsa mata don ta so
Badaru ba duk da irin dukiyar da suke da ita,
kuma yace tun kafin maganar ta girmama zai yi
nasa bincinken akan Badarun.
Kwana biyu tsakani Badarun bai sake
zuwa ba tunda aka yi haka, sai ga dan aike daga
gidan hakimi wai yana neman Mahaifin
Muneeba. Sakon na isa gareshi yasan neman ba
akan komai bane sai akan maganar Badaru da
Muneeba, shi kuma tunda yarinya tace ba ta so
to ba zai yi mata dole ba, kuma ko zaiyi mata
auren son ransa ko ta so hakika zai duba miji na
gari ne ya bata shi ba irin Badaru ba wanda ya
rayu a turai yana karatu idanunsa a bude suke,
sannan yayi tsananin bincike ya gano a can
Kadunan ma da yake aiki banda neman mata har
52
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ruwan barasa an tabbatar masa yana slaa, shi yasa
ya sha alwashin dukiya da girmar, hakimi da yake gani ba zai rude shi ya kai diyarsa inda
zaman aure ba zai yi mata dadi ba, in da za a
wulakanta rayuwarta, dama dein uwansa ne
Adnan kowa yanayabon halay'ensa zahiri da badini, toko da shine zai iya tirsasa Muneeba ta
amince da auransa tunda ya sami shaida ta gari
kuma mutum na gari shi ake ba aure.
Baiyi kasa a gwiwa ba ya isa gidan
Hakimi, aka yi masa iso gurin hakimi suka keбс
su biyu a babban falonsa na shakatawa inda yake
saukar muhimman bakinsa. Bayan gaishe-gaishe
da tambaye-tambaye akan hidimar iyali da aikin
gona sai hakimi ya aika kiran Malam Auwalu.
"Daman na kiraka ne akan wani muhimmin
al'amari da ya taso dangane da 'ya'yanmu, shì dana ne yaga diyarka yace yana so kuma so bana
wasaba aurenta zaiyi, nayi murna kwarai da ya
nemi aure a gidan dadttako gidan mutunci da ya gayamini shine nace to ya dakata bana son rawar
jiki ya bari in nemi iyayenta inji in basu yi mata mijiba, don kada ayi nema cikin nema".
Ganin girma ta martaba hakimi da jama'a
keyi yasa Mal. Auwalu sai da ya yi dan jinkiri yana nazarin irin kyawawan kalaman da zai
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gayawa hakimi ba tare da ya ji zafin ya nemawar
dansa aure ba a bashiba. Ya gyara zamansa yace,
"Gaskiya naji dadi da har babban mutúm da
ake ganin Kimarsa mai nagarta irinka zainemi
hada zuri'a da mu, wannan abin farin ciki ne,
sai dai wani hanzari ba gudu ba 'yan uwana suu
riga sun shaida mini sun fidda mata miji, ża ayi
bikin sauran 'yan uwanta to har da nata za a
hada amma Allah ya sani zan so mu kulla
zumuncin auratayya a tsakanin 'ya'yanmú, sai
dai hakan ba zai yiwu ba a dalilin alkawarin da
'yan uwana suka yina aurar da ita, ni kuma binsu
nake sau da kafa, amma zan turo Malam Adamu
ya zo yayi maka karin bayani tun da komai su kė
zartarswa magana tana hannunsu". Hakimi yace,
"To shike nan ka turo mini shi, zamu tattauna,
babu matsala da ma abinda nake gudu kenan
kada yaie y. nemeta alhalin anyi mata miji kaga
an aka shari'ar Allah anyi ba dai-dai ba, shi yasa
za a nemi aure ya kamata a fara sanar da
iyzyen yarinya ga den jin ko anyi mata mji, idan
ba a yi mataba saisu ba da izinin a ci gaba da
nema,haka ake so". Sun karasa tattaunawa
sannan suka sallami juna Mal. Auwalu ya koma
gida yana komawayasami 'yan uwansa guda
biyua shaida musu halin da ake ciki, sannan ya
54
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gaya musu abinda ya riga ya gayawa hakimi.
Malam Adamu yace,
Kayi dai dai abin da ka fada nima idan naje haka zan gaya masa, don ba zamu dauki 'yarmu
mu ba dansa ba tunda mun san halayensa sarai jama'ar gari má saisu zage mu ace kwadayi ne
yasa muka ba yaron aure alhali kowa ya san
halinsa, idan aka yi auren kuma wani abu ya faru
da ita ayi ta yo mana Allah ya kara, tomaganin
kada a yi ma kada a fara. Bari ma inje gidan hakimin".Ya shura takalmansa ya fice daga
zaurcn.
Maganar dai gudadayace hakimi yaji anyiwa yarinya miji kuma dan uwanta ne, jin haka yasa hakimi ya cc babu komai zaiyiwa dansa bayani tunda anyi wa yarinya miji sai yayi hakuri ya nemi wata.
Sun sakc zama 'yan uwan guda uku malamAuwalu, Malam Audu da Malam Adamu
suna sake tatatunawa Malam Adam yace, "To yanzu an gama da maganar dan wajen hakimi saboda haka aurensu Lawisa da za ayi to
za a hada da nata ayi". Mal. Auwalu yacc, "Har da nata?" to karatunta fa? Da wa za a hada ta?" duk suka zuba masa ido sabɔda jin wadannan tambayoyi da ya jero musu guda uku,
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zeria
wadanda yanzu kuwa zai ji amsar su. Malam
Adamu yасe,
"Kwarai da nata za a hada, karatu kuma tunda
kana so itama tana so to zata ci gaba, shi yasa mа
wanda zamu hada ta da shi dan boko ne irinta
kuma dan uwanta ne dan wajen Goggonta
Kanwarmu Rahin wato Mujcebu, hadın ya yi
maka ko kana da ja?" ya girgiza kai yaçç, anlsil
"Wallahi ni bani da ja a duk hukunci da zaku
yanke a kan iyalaina Allah ya sanya albarka yasa
ayi da mu". Suka amsa da Ameen Malam Audu
yacc.
SSIHLCD
"Abin da yasamuka zaba mata Mujcebu sabida
mun ga dacewar hadin nasu ne, tunda tayi ilimin
boko ba zamu tauyc ta mu bata mijin da baiyi
boko ba sannan kowa ya sani Mujccbu ya ro ne
na kwarai mai kyakkywan dabi'u ga natsuwa
uwa uba yana riko da addininsa sosai ga
girmama nagaba da shi, ita kanta Munceban mun
tabbata ba zata ki wannan hafin ba kumainsha
Allahu aurensu zai zamo mai albarka". Mal.
Adamu yaсс,
"Yanuzu ma abari in tashi yaro yaje ya kira
mana Rahin din, don mu shaida mata shima
Mujccb zanje Gombe da kaina gobe in sanar
masa ya fara ji daga bakina, a matsayi nana wan
mahaifiyarsa uwa daya uba daya kuma kani da
56
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
muke 'ya'ya maza da ubansa kuma nine jagoran
wannan aure haka duk zan karanta masa don ya
Kara sanin muhimmancinmu a rayuwarsa
Dunsu sun bada goyon baya fari bias dari.
Malam Auwalu yana shiga gida ya kira Mahaifiyar Muneeba can uwan daki don kada
suyi magana ajisu a tsakar gida tunda bai san a
yadda zaa dauki al'amarinba, ya bayyana mata
yadda sukayi da 'yan uwansa har da auren
Munceban da za a hada da na 'yan uwanta da za
ayi nan da kwana biyar masu zuwa.
Inna ta jinjina kai cike da alhani ta ce
"Amma kana ganin Yaya Rahin ba zata kawo
matsalaa maganar auren nan ba, ka dai san niba
dasawa muke ba, haka Munceba kullum cikin
kyararta take yi wai ta dauko halin miskilanci
irin nawa niban san me na tsarewa Yaya Rahin
ba ko da yake ta ce na mallake mata dan uwa, ni
kam banga mallakar da nayi maka ba tunda kai
ke sani kai ke hana ni kuma in yi yadda kace,
amma matar da ta mallake miji ai itace ke sa shi
ya yi kuma dole sannan ta hana shi kumaya hanu
dole, ni na san matsala ta a gurinta ba a jin
fadanmu ni da kai bana yamadidi da kai in ce ka
yi min kaza kayi min kaza, bata taba jin rigima
ta kunnu a tsakanina da kai bashi yasa za a ce na
mallake ka”. Ya yi ajiyar zuciiya yace,
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ki yi hakuri kuma ki kwantar da hankalinki,
ki natsar wa da Munecba hankali kada ta sa
damuwa ko da lana da wanda take so, tayi hakuri
in sha Allah aurenta da Mujeebu ina hango
alkhairi, Mujecbu halinsa mai kyau ne, kuma ya
banbanta da sauran yara halinsa kyakkyawa ne
abin son ko wace yarinya, ga tsafta gailimi duka
guda biyu to meye matsalar aurensa?"tace,
"Ni ban ce maka Mujeebu na da matsala, ni
dama Yaya Rahin kawai nake ji, amma ba komai
zamu mikawa Allah al'amarinmu ya kawo mana
mafita mai kyau, kuma yasa hakan da ka kulla
ya zaio alkhairi".
Da yamma sai ga Goggo Rahin ta zo
kiran da Yayanta Mal. Adamu yayi mata suka
kebe su hudu a turakar Mal. Adamu, bayan
gaishe-gaishe ne ya koro mata jawabi tun daga
nemanwa Badaru aurenta da hakimi yayi da
inats lar da yasa suka ki bada goyon bayan suba
Kadurun aure itama tace sam ba zai yiwu a ba
Badaru aure baya tafi da ita yayi ta wulakanta
rayuwaita, gara da suka yi hikimar hana shi:
Daga Karshe suka zayyane mata hukuncin da
suka yanke wanda kuma babu mai tada wannan
hadi da suka yina hada auren Mujeeb da
Munecoa, ai kuwa Rahin ta tuma tayi tsallen
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
albarka tace sama bata san wannan hadi ba ta
yarda da shi ba.
Wallahi Yaya ban amince ba, kuma ba ku yi
min adalci ba, ai kafin ku zartar da hukunci sai a
nemi shawarata, bazan yardaba uwarta ta
mallake mini dan uwa gashi nan bashi da
katabus sai abin da ta gindaya masa sannan ace
Munceba mai hali iri na uwarta ta auri Mujecbu
shike nan burin ta a kansa ya tarwatse shima
mallake shi za ayi". Malam Adamu ransa ya 6aci
yace,
"Kinga Rahin ba neman yardarki muke yi ba,
mun kira ki ne kawai don mu sanar da ke kuma
mu fita hakkin ki kada ki ji daura aure kice anyi
miki ba daidai ba, kuma maganar mallaka da
kike yi, mu dai ke muke jin kina kuzuzuzta an
mallake Auwalu ke da ba kya zaune tare da shi,
amma mu da muke zaune da shi ai mun san irin
ladabi da biyayyar da matarsa keyi masa, matan
rufin asiri ai itace mata, to ita ma 'yarmu haka
muke fatan tazamo a gidan mijinta, ko kinaso ko
bakya so nan da kwana biyar za ayi bikinsu". Таce,
"Gaskiya ba zai yiwu ba, kun dai san yaron nan
karatu yake yi, da wane zaiji da kujiba kujiban
karatu ko da nauyin iyali da za a dora masa. Ni
burina sai yagama karatu ya sami aiki sannan zai
59
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yi aure kuma ni da 'yar aminiyata Hajiya Harirа
zan hadasu tun tuni muka yi magana da ita
yarinya an gaya mata ita ma karatu take yi shima
an gaya masa to na mene ne za a gwada mini fin
Karti a rusa mini nawa tsarin da nayi". Mal.
Audu ya harzuka yace,
"Isa da mallaka kyauta da dan kishiya, shi yasa
muka yi miki haka, saboda mun isa da ke a
matsayin yayyinki uwa daya nba daya, shi kuma
da naki ne ke kika haifi abinki amma baki isa
muna raye kiyi iko da shi ba mu ne dai kuma
'yan uwan ubansa 'ya'ya maza muke sai ki gaya
mana wanda ya isa yayi mana iko da dan dan
uwanmu. Aurc ne mun kulla babu mai tada shi,
'ya'yanmu muna shaidar dabi'unsu duka su
biyun babu wanda zaiyi mana musu ko tawaye
kuma da kike maganar zaku hada auren su shi da
'yar aminiyarki Hajiya Harira ai Wata Kusan,
tafi wata duk amintarki da ta bata yi ya dan
uwanki da kika sha nono dan uwa ba, kuma duk
tsiyarki da amintar da kukewa juna idan aka
tsaga jikinki ba aza ga jinin Harira ba, haka nan
idan aka tsaga jikinta ba za ga jininki ba, kc
kuwa da dan uwan ki da 'y'yanku jininku iri
daya ne kinga kuwa ruwa bii isa yace ya kai
kaurin jini ba balle yayi takara da shi su yi
gogayya. Jinin dan uwanki Auwalu wato
60
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Muneeba ta fi diyar aminiyarki Harira ko kinki
ko kinso shasha wadda ba ta san dadin zumunci
basai son ranta".
Nan da nan Rahin taballe da kuka ta shiga
hayagaga bufan kan karya abinda ya janyo
hankalin duk jama'ar gidan suka yi cirki-cirko a
tsakar gida suna jin abin da take fada. Larai ta
dubi Mariya tace,
"Kinji wata sabuwa kuma auren Munceba da
Mujceb 'yar boko da dan boko, sannan nan da
kwana biyar za a hada da aurensu Lawisa ba
shiri ba sanarwa". Mariya ta cc,
"Sai a kaita da biro da littafai da ba tsiyar da
uwar ta tanada ai kinga yau sai boko yayi musu rana". Asabe ta tsoma musu baki duk da ba ta
shiga shirgin gulmace-gulmacensu ta ce,
"Ai kuma kun san 'yan uwanta masu zuciyar yi
ne kun san tuwon dan dangi baya ruwa wannan
ya miko gari wannan ya miko sai ku gaya tuka
kákkauran tuwo". Larai ta ce,
"Sai ki fito fili ki gaya manaba mu da dangi
tunda ita tana da dangi da yawa har a birni, 'yan
birnin marowata maga uwar da za su tsinana
matahar a sammiki ke 'yar kanzagi". Mariya ma
ta mashe ta fara jero nata zafafan kalaman ganin
ida ta ci gaba da tanka musu za su hautsine ga
gidan dama a hautsine yake sai ta kyale su ta
61
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
wuoe dasinta ta barsu suka ci gaba da raddi akan
maganar da ta aje musu.
Iaka aka rabu baram-baram dutse a
hananun riga tsakanin Rahin da 'yan uwanta.
Muneeba ma tana daki tana aikin kuka a dalilin
a da ta yi Gagonta tace, sam bata yarda da
aurenba seine itama take kuka akan bata so
nama gara a hakura da wannan hadi, amma da
farko da aka gaya mata tare da nasihar da Innarta
tay mata ya natsar da mata da zuciya ta yi na'am
da hadir iyayen nata amma yanzu jin kalaman
Guggo yasa ta ji sam bata son hadin auren nasu.
Babanta ya shigo shima ya dasa nasa lallashin ya
totsirayeta da bata tabbacin idan an sami matsala
aa Guggonta to tabbaci hakika ba za asami
matsala da Mujeebu ba din ba ya iya mušu da
suba, ba zai taba kyamatár hadin auren suba
Washe gari saura kwana hudu daura
auren, Mal. Adamu ya shirya ya tafi Gombe
gidan da Mecb ke zama daga nan yake tafiya
makaran, guan aninir mahaifinsa ne, da suka
taso ture a yara a Duk harkar kasuwanci ta
dawo da shi Gombe har yayı gidan kansa yake
zaunc da iyaiansa.
A bakin Alh. Sani (maigidan) ya sami
labarin Mujecbu sun tafi (excusion can jahar
Lagos da oyo yau kyannansu daya da tafiya za
52
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
su yi kwana biyar. da Mal. Adamu yayi tunani
sai ya ga sai ranar daura auren zai dawo. Ya bayyanawa Alh. Sani abinda ke faruwa ya Kara
da cewa, "Shine na zo in sanar masa da kaina
inyi masa bayaniyadda zaiyi kyakkyawar
fahimta ga faruwar al'amarin sabanin yadda idan
ya je yiwa al'amarin bahaguwar fahimta muddin
uwarsa ta fara shaida masa al'amarin tundata
nuna rashin amincewarta ita tafi son ya auri bare
'yar aminiyarta, ni ban taba gani inda ka so na
waje fiye da dan uwanka ba duk kuwa irin
amintar da kake da mutum ai Wata Kusan tafi
wata ko yaya ne balle kusan jini ai ba wasa ba
ne". Alh. Sani yace,
"Ai su mata al'amarinsu yana da bar. mamaki
suna da zumunta ta ziyarar dan uwa, am ma rikon
amanar zumunta har cikin cuci ai sai namiji, in
banda abin Rahin ai jini ya daranma ruwa nesa
ba kusa ba, ni ma nan ai na so hada shi da diyata
ban gaya wa kowa ba a zuciyata kawai nake
wannan sake-saken saboda kyawawan halayen Mujcebun, yaro ne na gari mai addini gashi da
neman na kansa, yanzu haka duk da karatu yake
yi amma bai hana shi neman kudi ba, sana'a
yake yi a garin nan ni na kara masa karfin gwiwa don ya tallafi kansa da mahaifinyarsa da
kannensa tunda shine na miji babba. Allah ya
63
WATA KUSAN 1 Rehmatu Hassan Zaria
sanya alheri zanyi Kokarin inzo in halarei faura
auren shi kuma da ya dawo zan turo shi nima
anan zan fara yi masa bayani. Alh. Sani ya tashi
ya shiga can eikin dakinsaba jimawakadan ya
fito da kudi a hannunsa ya mikawa Mal. Adamu
sannan yаce,
"Gawannan na biya wa dana sadaki duk da ban
san me kuka yanke ba, naira dubu talatin ne".
malamAdamu ya shiga zuba godiya yace,
"Mun gode Alhaji Allah ya saka da alkhairi ya
Kara budi. sadaki dama mu ne zamu ba da, kuma
idan aka daura aure ba a lokacin za a tare ba
tunda abin ya zo a kurarren, lokaci, zamu gyara
masa nan cikin gidan da mahaifinyarsa takc, mu
fidda masa sasansa a cikin gidan su fara zama
tudan shi ba zama yake ba nan gaba sai ayi
tunanin abin yi". Alh. Sani yace, "Wannan duk
babu matsala, Allah dai ya dawo da shi lafiya".
Yacc "Amcen amen.
Mustapha yana zuwa ya sami labarin
abinda ke faruwa, ya yimurna