suke
cushe da jin haushin Munceba da 'yan kanninta
guda biyu da su ma duk an sa su a makarantar
bokon.
Har suna aka sa musu a gidan wai 'yan
fi'ili 'yan bokoko a wuta, tun suna kulawa har
sun daina kulawa sun maida hankali ga
karatunsu. Ita ma Innarsu ta daina doramusu
talla Muspha ya hana sai dai Innartana 'yan
kulle-kulle a zo a siya a gida, shi kuma yana yin
duk sana'ar da ta zo masa yana taimakawa
iyayensa don dai kada kannensa su yi talla.
23
WATA KL SAN 1
***
Rahmatu Hassan Zaria
*** ***
Jarabawar su Munceba ta fito, Allah cikin ikonsa
Muneeba ta sabu ci gaba da karatu a Makarantar
'yan mata ta garin Gombe. Nan ma anyi tirkatirka da iyayensu Muneeba maza kafin su yarda
suka barta ta wuce aji daya na karamar
sakandirc, su a cewarsu lalacewar ta yi yawa da
har sai ta da Murja duk sun sami gurbin karatu
zata dauki diyayrta mace ka kaita wani gari
makarantar kwana alhalin ga makaranta anan ta
sakandare a gainsu na Dukku me zai sa har sai ta
tafi cikin garin Gombe.
Mustapha ya hana kansa sakat saboda
saye-sayen da za ayi wa Muneeba na tafiya, haka
nan ma Babansu shimaba shi zaune ba shi tsaye
don ganin komai ya kammala tunda a 'yan
uwansa ba mai taimaka masa da kwandala a
cewarsu shi yasa kansa. Mutum daya tasan zai
iya taimaka musu a halin karatunta a 'yan uwa
da yana da rai Baba Aminu wato mahaifin
Mujeeb saboda shima yana bada goyon bayan
karatun 'ya'ya mata haka Muiceb da ace yagama
karatu ya fara aiki tabbas zai taimaka tunda a
cewarsa yana alfahari da kanwarsa ke karatun
boko.
24
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Ranarda za su tafi saiga Murja ta zo da safe ta iske Munecba na ta shirya kavan tafiyarta,
ta aje wata katuwar leda a gaban Mane ban tace, "Gashi nan inji Abbanmu ki Kara ba yawa. Munccba ta jawo ledar tana dubawa tacc, "Kai, kai ina Inna ta zo ta ga abin arziki". Sai
ga Innar ta shigo rikeda buta daga bayi ta fito tace, "Me ye zan gani ake kira na?" tace, "Kayan provision ne inji Hedimasta wai in Kara Inna dubi masu yawa". Inna ta kai dubanta
ga murja ta ce,
"A'a Murja ce sannu da zuwa har tafiyar ta tashi ne?" ta risina ta gaida Innar sannan ta ce,
"A'a ba yanzu zamu tafi ba, sai anyi sallar
azahar zamu biyo ta nan mu dauketa a motar
Abba, Yaya Mujahced ne zai kaimu naji yace ma har da Yaya Mustapha za su kaimu". Inna ta
zauna ta soma duba tulin kayan masarufin tana
zuba godiya da sa albarka. Da Murja zata tafi ta bata tukwici wanda da kyar ta ansa tace ta yiwa Abbansu godioya sannan ta ce itama tananan
zuwa da daddare yi masa godiya na dawainiyar
da yake yi, ban da wahalar nemo adimishon ga
kuma sayayya Allah ya bi ya shi.
Muneeba ta raka Murja, ta dawo taji
gungun matan gidan suna ya da magana
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Wannan dawainiya hala kamu yake wa dansa,
don naga shi ma dan kullum yana gidan nan sai
ya shige har kuryar faki wai abokin Mustaha".
Larai tace,
"Uhm ba dai girin girin ba ta yi mai, Allah
yasa kada ta badawa iyayenta kasa a ido sun
dage 'yarsu sai ta yi boko ta je ta dauko musu
abin kunya tunda gani suke yi 'ya'yanmu da
suke talla sune lalatattu alhalin lalacewa an ce
tana makarantar kwana", ita dai Munceba ba ta
tsaya ci gaba da sauraronsuba ta wuce dakinsu
ranta a Gace da Innarsu ta tambaycta dalilin
Gacin ranta shine ta gaya mata, Innan tacс,
"Kina son ki bata ranki a banza ne, in da sabo
ya ci ace kin riga kin saba da halin da muke ciki
a cikin gidan nan sara da sassaka kin taba ganin
ya hana gamji tifo? Ko kin isa ki hana su su fadi
abin da ransu ke so nc? to ki maida hankali ga
abinda ke gaban ki, ki bar wandaba ya gabanki,
wuce ki karasa shirinki, da izinin Allah zaku yi
karatunki, lafiya ku gama lafiya kuma bamu ba
waninmu ma sai ya amfana da iliminku in Allah
ya yarda". Munceba ta turo baki gabaki ta cc,
"Hum uh, ni Allah a matan gidan nan babu
wadda zan ba kwandalata idan nayi ilimi na
soma aiki ina samun kudi, har gara Inna Asabc
26
WATA KUSÁN 1 Rahmatu Hassan.Zaria
ban taba jin ta aibunta niba a dalilin bokon nan'. Inna ta yi murmushi ta ce,
"Yarinta manya ai a gidan an babu wanda zaki ki yiwa alheri ko ba ta dalilin boko baai duk wanda ya zalunce ka ko da da harshe ne to kada ka rama, kai ka biyo bayan zaluncin nasa da alkhairai sai ka gaya ji kunya hakan zai sa yayi
na dama ko nan gababa zai zalunci wani ba, balla kai, balle ma dukansu iyayenki ne kada ki
tsani kowa cikinsu ki kyautata musu tamkar yadda zaki kyautata mana".
Bayan sallar azahar misalin karfe biyu da
rabi motar Hedimasta fijo 504 tayi fakih a kofar
gidansu Munceba, anan suka iske Mustapha yana
tsaye da alamu isuwarsu yake jira Mujahced ya
fito daga motar yaba Mustapha hannu suka gaisa
yace,
"Hala har kun gaji ruwan kale da gajiya, ni ai
ku nake ji kada ku zo wannan ‘yar shirritar
batagama shiri ba kasan mata tun suna kanana
haka suke da nawa". Mujaheed yace,
"Allah yasa dai baka rudamini itaba da
fadanka don an san halinka, kuma ka san nima
zan iya ramawa". Yace, "Ayi hakuri tuba nake
na sanka mugu ne kai fadanka har ma da duka
kake hadawa don mugunta".Suka kyalkyale da
dariya.Gaba dayansu har da Mujaheed da Murja
27
WATA KUSAN 1 Fahmatu Hassan Zaria
suka shiga cikin gidan har dakin Inna suka
gaisheta, sannan suka fito da kayan Muneeba
suka sa a mota, Inna ta dube ta tace,
"Ki shiga kiyi wa mutan gidan nan sallama,
kowa ki bita dakinta". Haka nan tayi faki daki
tana musu sallama duk suka firfito yaransu da
manya suna "Allah ya kiyaye ya bada sa'ar
karatu", 'yan kananan yaran kuwa har jikin mota
suka raka Munceba. Inna sai dada nasiha takeyi
musu a bakin motar,
Don Allah Murja kukula da kanku kuyi abinda
ya kaiku banda wasa banda sakarci, duk wanda
kuka ga baya maida hankali gurin karatu, kada
ku rabe shi mutumin kirki da shi akc abota ba
shashasha ba, ku dage ku ba marada kunya,
Allah Ya yi muku albarka, Allah Ya kiyaye
hanya, kada ku manta ku biyata gidan ku". Duk
suka shige motar Inna tana saye har motar ta
tashi. 'yan kananan yaran gidan sai ihu suke zasu
bi Muneeba har da masu birgima sai daukansu
aka yi aka shiga da su cikin gida don kada suce
zasu bi sawun motar.
Matan gidan sai hayaniya suke basu
masan Inna ta shigo ba ita dai ta tsinkayi suna
fadin, "Wannann karfin hali har ina da zan dauki
da na in kai wani gari yin karıtu, shi karatun ma
bana Allah ba, na neman duniya".
28
4
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Yo ai abin. kama gasa ake da 'ya'yan
Hedimasta, su ai ubansu dan boko ne babu aibu
idan 'ya'yansa sun yi boko, kuma shi yana da
albashin da zai dauki nauyin karatun 'ya'yansa.
Su fa? Sai dai kame-kame da neman taimakon
'yan uwa".
Wannan karon ai ba a nemai 'yan uwa ba
bakigashi Hedimastan ba ne yayi mata hidimar
makarantar nifa ina ganin alkawarin ba dansa
aurenta suka yi shi yasa yake mata hidima ba
gajiyawa".
"Lałlai kam zamu ga inda tusa zata hura wuta,
aure ai basu ke da ikon yiwa wani alkawarin ba
'yarsu su akwai manya dole sai abinda suka ce.
Ni Allah ma yasa ta gama gwalangwason yin
bokon su Malam su hada ta aure da wanda baiyi
bokon ba sai in ga ta karyar tsiya".. ita kam Inna
tana jinsu ta yi shigewar ta daki ta kama gyaran
dakinta bayan ta kunna 'yar rediyonta tana
sauraron wa'azin da ake yi a rediyo, ya fiye mata
jin jirwayen da ake mata.
A kofar gidan Goggo Rahim Mujahced
yayi fakin din motar yace ta shiga ta fito
Mustapha ma yace ba zai shiga ba don kada su
dade. Mujceb ta fara gani a tsakar gida yana
dauraye kayan Innar yana shanyawa. Ya amsa
sallamar da tayi yacс,
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"A'a Muneeba sai Ina haka da Uniform?" Tacс,
"Kar dai kaee ka manta na gaya maka yau
zamu tafi makatrantar kwana a Gombe?" yace
"Oh wallahi shaf na manta, wa zai kaiki? Kinga
da nagama shiri da mun wace tare nima yau zan
koma". Taсe,
"Su Yaya Mustapha ne da Yaya Mujahced, sauri
muke yi shi yasa basu shigo ba".
Mujeeb ya bi bayanta suka shiga daki
gurin Guggo. Ta dubi Muneeban a yatsinc ta ce,
"Ke kuma ina zuwa haka da kayan makaranta
*yan dingıl-dingil?" ta duka gaban Innan ta fara
gaishe ta sannan tace", Na zo inyi miki sallama
ne yau z2n wuce makarantar kwana a Gombe?"
Gogga Rani ta iafa hannuwa ta ce,
"Au shine zaki tafi makarantar kwana ban taба
sani ba sai yau da zaki tafi, tunda ni talaka сe
bani da abin da zan baki amma na san ai kinje
gidan Guggonki Hinde tunda ita kunfi dasawa da
ita", (Guggo Hinde kanwa ce itama gurin Guggo
Rahin amma ha!i ya banbanta).
Munceba tace, "Wallahi banje gidan ta ba
gidanki kawai nazo". Muie b ransa baya son irin
wadannan kananan maganganu na mahfiyarsa da
irin halin da takc nunawa mahaifiyarsu
Moeban da 'ya'yanta, Mustapha ne kawai
suke dasawa, yayi saurin cewa,
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ayi hakuriGoggonmu, ke Munccba tashi ku
tafi suna jiranki a waje". Ta mikcGoggon ta ce, "Ke da wa zaku tafí makarantar?" Mujccb yayi
saurin taran numfashin Muneeba yace,
"Ita da yarinyar wajen Hedimasta ne za kaisu", tacс,
a
"Oh! Hedimasta wato har yanzu bai gama dawainiya da ke ba, hala dai so yake aba dansa
ke?" ita dai Muneeba shiru tayi, Guggo ko habar
zaninta ta kwanto kudi, ta ciro gudar dari biyu ta mikawa Munceba tana cewa,
"Gashi sai ki rike ba yawa kya sayi wani abu”..
Muneeba ta sa hannu biyu ta amsa don ta san
idan tace gogonta barshi nan ma wani kalubalen
za ta yi mata suka yi sallama, Mujecb ne ya rako
ta har jikin mota, suka gaisa da su Mustapha
sannan ya sallame su ya koma cikin gida.
Daga nan suka yada zango a kofar gidan
Goggo Hinde. Gaba dayansu suka shiga saboda
sanin halin kirki irin nata, gata da barkwanci,
idan tana wasa da su Munecba tamkar kakarsu
ba kanwar ubansu ba, shi yasa har su Mujahced
da Murja duk sun saba da ita.
Suna shiga ta tarbesu da fara'a tana cewa,
"Lale marhaban da 'ya'yana. Idan dai an ga
Zahra lalai aga wata, mu kam zamu gidan
hedimasta oyo mana musanye, a bamu muma mu
31
WATA KUSAN 1 Rhmatu Hassan Zaria
ba da wallahi hadin nan yayi ko ya kuka ce
'ya'ya nan?" dukkansu suka yi dariya don sun
gano me Goggon tasu kenufi. Mustapha yace,
"Kai Goggonmu ke dai akwai ganewa
wallahi", tace,
"Ai nituni na gane ku sannan gashi kun dace,
Allah ya tabbatar mana da alheri". Babu wanda
ya iya cewa amen cikinsu a fili, amma a
zuciyarsu duk sun amsa da amen.
Bayan sun gaishcta ne Mustapha ke gaya
mata yaune tafiyar Munceba da Murja makaranta
shinc suka zo mata sallama, tace,
"Yo tafiyar har ta zo ashe? To Allah ta bada
sa'ar abinda za a je nema, ku dage kuyi karatu
sosai banda wasa, tunda dai Allah ya taimakeku
kun sami damar da ba ko wace diya bace
iyayenta ke barinta ta yi nesa da su don zuwa
karatun boko, gara mu su Murja mahaifinki
danboko ne, ke kuwu Muneeba iyayenki a
ruwansu da bokon diya mace, sai ku dage ku ba
mara da kunya. Allah yayi muku albarka".Suka
amsa da "Ameen".Dukansu. Nan da nan ta tashi
ta dinga bankada kwanuka, ana dauko musu
abin tsarabarmakaranta irinsu garin kwaki,
dakakken kuli da yaji har da mai, daddawa na
din tuwo, da ragowar dambun nama da tayi da
sallah duk ta juye musu, tana cewa,
32
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ni wallahi ban dauka yau ne tafiyar ba, da
nayi muku tanadi sosai, da har kilishi zansa ayi
muku, amma ba komai idan za ajc y muku
ziyara zan taho muku da shi, suka mike don
tafiya suna ta yiwa guggo Hindu godiya, ha da
naira dari biyar ta kara musu tace su sayi wani
abu, cikin jimami da kewar juna suka yi sallama
da ita Mujahced ya ja motar suka dau hanyar
Gombe.
Su Mujaheed sai da suka tsaya aka yi
ivasu Muneeba komai da komai aka basu aji,
kuma ya kasance ajinsu daya dakkinsu ma daya
sannan suka yi sallama da su suka baro
makaratar ta G.G.S.S.S Doma. Amma fa sun
lallashe su sannan suka hakura da kukan sai da
suka daukar musu alkawaarin idan za a zo ziyara
(visiting) za su zo dukansu sannan suka barsu
suka tafi.
2
WATA KUSAN 1
*** ***
Rahmatu Hassan Zaria
Hutun farko da su Munecba suka dawo, sai abin
ya zama abin zunde a gidansu, a cewarsu wai ta
yi kiba tayi kyau tamkar ba karatu taje ba. Hakan
da taji ne yasa tasha alwashin idan an basu hutu
nagaba ba zata zo Dukku ba, a Gombe zata tsaya
gidan Inna Amina (Yayar Innarsu ne) ta yi
hutunta a can, ba zata zo ba balle a dinga
zundenta ana yayata tsegumminta.
Ko Innarsu ta ga canji sosai a gurin
Munceba, ta zama fes-fes da ita, ta kara kyau
kuma tunda ta dawo ta daina barin dakin Innar
su da kazanta, hatta gidansu da ke da girma haka
take yin sam nako ta share shi fes-fes sai daisu
sake fatawa ua gangan tunda suba za su share ba
kuma ba za su sa 'ya'yansu su share ba, idan ma
za s. share sai dai kowa ya kewaye harabar
dakinsa ya share itama da ta dauki jimirin
sharewa kullum sunce zatayi ta gaji ta daina don
ta shekara sharewa bata isa ta hana su 6atawa ba,
ke `ya'yansu su Gata, don woni lokacin tana
gamawa za su tsiri shan rake su da 'ya'yansu
gidan ya sake yin kaca-kaca sai dai idan sun
gama ta sake sharewa, ba ya damunta.
Haka nan bayin gidan guda biyu ne, na
wanka da na ba haya, kullum sau biyu take
wakewa, sabo da ta karanta illolin da kazantar
34
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
9
bayi take haifarwa, shi yasa ko ta wanke idan
zata yi wanka take sake wankewa. Nan ma sun
dinga tsegumi kenan wai ta je makarata ta dawo
da sabon salo da kafidiri, nan gaba idan karatun
yayi nisa basu san ya zata dauke suba, tunda
yanzu kowa kazami ne a gidan su ne kawai masu
tsafta su 'yan boko.
Su Muneeba sun shiga aji buyu a lokacin
ne Mustapha da Mujahced suka sami gurbin
karatu a jami'ar Gombe (Gombe state university.
a lokacin shi kuma Mujecb ya shiga shekara ta
biyu a (Feersl University Kashere) wadannan
samari sun shiga jami'a da kafar dama saboda
sun mida hankali sosai babu wasa. Mustapha
kam dole ya maida hankali gurin karatun domin
a hidimar karatunsa sai da babansu ya saida
sanuwarsa guda daya sannan aka yi masa rigista
da biyan kudin daki da sauran hidimu, duk dahedimasta ma ya yi musu hidima, shima wannan
karon Malam Auwalu ya taka muhimmiyar rawa gani domin ya hana hedimasta takurawa
kansayace komai sai ya yi musu tare da
Mujaheed, shima da ya sai da shanuwar sai ya
hidimta ma Mujaheed duk da ran hedimasta bai
so aka sai da shanuwar ba.
Tun hutun farko da Munecba ta zo akayi
ta mata habaici a gidansu sai ya kasance idan
35
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
anyi hutu ta daina zuwa Dukku sai tana tsayawa
a Gombe gidan Innarta har sau hutu yakusa
Karewa sai ta zo ta kwana biyu a Dukku sannan a
maida su makaranta. An ma ba ta sake zani ba
saa aka ce ilimin da ta samu yasa ta guji asalinta
ta guji iyayenta, tafi son zama gidan Inna Amina
don mijinta mai kudi ne gidansu gidan jin dadi
shi yasa take zama a gidan (kunji fa ita da gidan
'yar uwarta uwa daya uba daya, zumunci ya
zama kwadayi.
Su Mustapha a Gombe ba karatu kadai
suke yi ba har da 'yan sana'o'i su kan taбa
domin su ragewa iyayensu nauyin hidindimun da
suke yi musu, duk da daishi Muajheed ya san bai
yi sana'ar komai ba mahaifinsa zai iya daukar
nauyin karatunsa, amma hakan da yayi shima
mahaifın nasa zaiji dadi ya san cewa ya haifi dan
da zai iya tallafa ma kansa, shi kumasai ya ji da
sauran kanin Mujaheed din.
Wannan hutun ma ana yi da Mujahced
yazo daukarsu a mota ya dubi Munceba yace,
"To 'yar gidan Inna Amina, Dukkun zamu wuce
ko gidan Innar?" ta yi murm ushi tace,
"Kaima ka sani cikin gari zan fara zuwa na zo
Dukku daga baya".Ya dan rage murya cikin
marairata yana dubata yace,
36
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zara
"Ayi min alfarma wannan karon mu wuce Dukku muna bukatarki a can, ko kinfi son inyi ta kewarki?" ta sa hannu ta rufe fuska saboda
kunyar kalamansa tana dan murmushi bata iya се
masa uffan ba. ya juya bayan motar inda Mustapha da Murja suke yana duban Murja
yace,
"Kanwata please ki rokar min kawarki mu
wuce Dukku", Mustapha yayi karaf yace, "Kai ka damu sai ta zauna a Dukku tunda tafi
son zaman Gombe basai mu kaita ba", tawaigo a
marairaice tace
"Haba Yaya Mustapha kafifa kowa sanin
matsalar zama na a Dukku, nima in ba dole bana
fi son zama gani ga Inna da Baba", ya ja tsaki "Shirmen banza har sau nawa zan baki shawarar
ki fita harkar al'amuran cikin gidanmu kuyi abin
da ke gabanki". Tace,
"Shike nana mu wuce Dukkun, amma gani
nayi ku ma idan kun kaimu Gomben zaku dawo
makaranta". Yace,
"Eh, zamu dawo Gombe yau dinnan amma
zamu sami hutu zuwa next week". Tace,
"Shike nan mu wuce kawai”.
Muneeba na shiga gida da jakar kayanta
yaran gidan suka yo kanta da ihun murnar
ganinta, ko ba komai yaran gidan na kaunarta
37
WAT A KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
suna kaunar kasancewa da ita ko don koya musu
karatu da takeyi idan tana gari. Matan gidan
duka suna zaune a inuwa bishiyar mangwaron da
ke tsakar gidan suka yo mata caa da idanu suna
cewa,
"A'ah 'yan makaranta yau kuma an tuno da
mutan Dukku ne, aimun dauka boko ya sa kin
manta da asalinki". Batayi niyyar ce musu komai
ba, sai wata zuciyar ta zugata cewa wani abu
tace,
"Haba dai ai dan halas baya maya asalinsa, can
ma tasu sau na taho ba goben nan za ku gansu
sun biyo ni". Ta wuce dakinsu ta barsu suna cі
gaba da hirarsu.
Da gudu ta fada cinyar Innarsu da ke
zaune ta fada cinyar Innarsu da ke zaune, Innan
ta tureta tana cewa, "Ni matsa kada ki karya min
cinyoyi, ke sam ba kya girma da aikin shirme, ko
su Maimuna (kanwarta ba za su dinga fado min
a cinya ii haka ba". Ta jingina kanata a kafar
Inna ta
"Haba na wata hodu aban ganki ba dole inyi
murna a tunda ke keziyara idan za a zo
baky. bivo su, haba Inna kamar ba kya sona,
Murja fa duk zuwa Mamansu sai ta zo".
Inna ta ce; "Ita kika ce ni daban ita daban,
kuma ai jama'a na zuwa miki, ko zuwan da Yaya
38
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Amina daiyalantakeyibakigodebane?" ta
yisaurincewa,
"Wallahina gode ni dai ina so ko su daya i zo
kinji Innanmu?" tacc,
"Zanzo wataran insha Allahu". Ta raba da jikin
Innan ta rusuna ta gaisheta, sannan take tabayar
Babansu tace, "Yanzu ya fita, ba a kofar gida da
kun hadu". Mustapha yayi sallama ya shigo rike
da hannun Kanensa Maimuna a autansu Baffa ya
risina gaban Innarsu yagaisheta tace,
a
"Ku ma kun sani hutun kirismetin ne? yace,
"Sai sati mai zuwa zamu samu, Malam ne yayi
waya yace idan anyi musu hutu yau mu dauko su
motar haya shine wani aboin mu ya bamu aron
motarsa yace mu yi amfani da ita damu yi
wahalar shiga motar haya, shine nake gaya miki
muna dan taba kasuwanci da shi, amma shi
iyayensa masu hali ne". Inna tace,
"To Allah ya taimaka sai ku yi taka tsantsan da
duniyar mutane, ku ci halas din da kuka samu
kun nisanci haramun sai ku ga nemanku yayi
albarka", yace,
"Insha Allahu muna wannan kokarin", tace,
"To Allah ya taimaka ya rufa mana asiri
duniya da lahira", yace,
"Ameen". Ya dubi Munecba ya dubi Innarsu
yace, "Baki tambayi ya aka yi 'yar gidan Inna
39
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Amina ta fara zuwa muku hutu ba wannan
karon?" tace, "Na san ai ba zai wuce ku kuka sa
ta ba. tunda na san ta fi son yin hutunta a
Gombe, can ga 'yan mata sa'o'inta 'yan biyu
Khausar da Khairi, kuma ka san in basa a ba
gobe zaka ga aiken Yaya Amina tun da ita ma ta
fi son Muneeban ta je matahutu".
Ilai kuwa washe gari misalin karfe goma
na safe sai ga direba da su Khausar sun zo tafiya
da Muneeba. Suna shigwa suka ganta a tsakar
gidatana wanke-wanke. Khairi ta soma balla
mata harara tana murmushi, sannan suka gaida
matan gidan da ke ta aikace-aikacensu, suna isa
gurin Muneeba Khair ta duma mata dundu tace,
"Ai kin kyauta muna ta murnar dawowar ki
jiya kawia sai muka ji shiru sai Yaya Mustapha
ne ya bigo da yama yake gayawa Mama wai sun
wuro dake gida, da ta ce a barki k fara yin hutun
a anan in yaso sai ki karashe a Gombe mu muka
ce bamu yardaba yau zamu zo nu dauko ki".
Khairi tace,
"Bari mu gaida Inna muzo mu taya ki aikin ko
kya gama da wuri mu wuce".
Suna gaida Inna suka aje gyaluluwansu
duk da gayun da suka yona wani matiriyal ja mai
kwalliyar goldin, sun yi kyau sosai, amma haka
suka fita suka tayata wankc-wanke suna
40
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gamawa, suka taya ta ta share tsakar gidan tas
sannan suka shige ſakin Inna don ta hado
kayanta, Inna ta ha fo musu dangin tsarabar yara
su goruba, magarya, kurna da aduwa cike da
babbar leda ta basu tace su kaiwa kannansu,
Khairi taсс,
"Inna muma fa muna sha za dai mu sammusu,
Muma fa yaran ne Inna". Tace,
"Shike nan tunda kun maida kanku yara, da-za
a yi wata maganar kuma kuyi tsalle kuce ku ba
yara ba ne tunda kun shiga ajin sakandire". Suka
yi dariya. Ta sake miko musu wata ledar tace,
"Ga wannan na 'ya'ya ne kuka ce da kubewa da
daddawa". Khairi tayi saurin. mikawaKhausar
ledar tace, "Allah ke zaki rike wannan daddawar,
ni na rike tsarabar yara". Ita ma Khausar tacс
"Ai baki isaba ni da ke waye babba?" Inna tace
"Ka ga min yara da tsiya daddawar ba za ku rike
ba, ina ce a but zeku saka, gayun banza da na
wofi da zaayi miya 'da daddawar dukanku ci
zaku yi ku arta na gayawa Yaya Aminan kwahadu da ita". Munceba ta sa hannu ta dau
ledar ta сс,
"Barni da su zamu je gaban maman za su yi mata bayani".Suka yi sallama da Innan suka fito suka
yi sallama da mutanen gidan sannan suka tafi.
41
WTA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Yaran gidan Inna Amina suna ganin anzo
da Munceba suka cika falon gidan da ihu da
tsallen marna. Inna Aamina da ke dakin baccinta
ta fito doa ganin me ake yiwa murna sai tagansu
Kankame da Muneeba suna murna tace,
"liaba ko da naji wannan irin ihun murna, KiriKiri dai mun kwace musu 'ya ba dama taje gida
sai ar. bi sawunta, to da malam yace shima yana
son ganirta a kusa da shi ya zakuyi?" ta dubi su
Khairi tana maganar, Khausar tace,
"Ai mun san va zai hana mu tahowa da ita ba,
da ya hara ma zamu ceke kika turo mu, ko yanzu
ba mu iske shi a gida ba, amma Inna tace ba
komai mu taho zata gaya masa idan ya dawo.
Babban dan Inna Amina ya shigo Khairi
da Khausar suka hada baki wajen gaisheshi "Ina
kwana Yaya Sadiq?" yace,
"Lafiya wai har kun dawo daga Dukkan? Ina
Munceban?" "Gata nan a bayanka tana boycwa"
ya juyo yan Harararta cikin sigar wasa yace,
"Kc ko! Ke ko! Zan damke ki. Mun sakankance
nan zaki fara zuwa shine kika gudu jiya na ci
burin da kinzo zaki yi mini irin dambun nah sai
haka na kwana da yunwa" ta marairaice murya
tacc
"Ayya Yayana kayi hakuri, yanzu sai in yi
maka". Khairi tayi karaf tace, idan kin gama
42
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zara
masa muma fan waken nan kin tuna? Inna
Amina da ke gefe tana jinsu ace,
"O.K wato kunje kun dauko tanesaboda kudinga damunta da yin girke-girke, ku ba za ku koya ba sai ku dameta, to ba zata yi banutu ta zo yi kada ki sake'in ganki a kicin duk wanda ya
matsu da cinabinda ransa ke so to ya shiga kicin
da kansa ko ku sa Laminde ta yi maku". Sadiq
yace,
"Mama kiyi hakuri ni nata nake so irin na
Innarsu ne na mutan Dukku na Fulani, na
Laminde kuwa bairin nasu ba ne shi yasa", Inna
Amina taсс,
"Allah dai yasa ka sam mata da ta ya girkegirken gargajiya, gaka dan boko amma bakacin
cimar 'yan boko", yace,
"Ai Mama a kauye zanje in auro mata wanda
ta kware wajen iya dambu da tuwo, da bira bisko, ba ruwa na da cimar da bazata cika mini ciki ba, ni ban yarda da wannan gayun ba". Inna Amina tayi dariya ta wuce ta barsu:
Ko hutawa bai bari Munceba ta yi baya jata kicin ta fara hada masa dambun. Su biyu a
kicin yana taya ta aikin suna hira har ta kammala ta dora a wuta sannan suka dawo falo. Khausar da Khairi suka dube su suka yi dariya amma
suna 6oye dariyar Sadiq yace,
43
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ku kuma wa kukewa dariva kamar taба66u?"
Khairi ta gimtse dariyarta tace,
"Khausar ce fa da ta dubeku waitace kamår
mata da miji, yace.
"Au kama ce ma aimun wace kama, gara tun
yanzu ku aje girmanta da kuka yi matar yayanku
ee. ku farace mata Yaya ko anti". Suka yi dariya
har da tafawa. Khairi tace,
"Bari inje in yadawaMma wannan farin
labarin, dama Mama bata sani ba". Munecba ta
yi farat tacе,
"Don Allah Khairi kadaki je, in kuma kika je
yau dinnan zan koma Dukku". Khausar tace,
"Kin gani zaki ja mana ta gudu, ina ruwanki
aka ce miki Maman bata gano su bane?"
kallonsu kawai takcyi, Sadiq yace,
"Yauwa ai na fi son Maman ta sani saboda ta
je Dukku ta sanar