a dalilin dan
uwansa aka ba kunma shi shaida ne akan waye
Mujeeb, sannan ya taya amininsa bakin cikin
rasa Munceban kasancewar yasan ya kallafa
ransa a kanta, shi yasa ya garzaya yaje ya
gayawa Mujaheed tare da lallashi da ban hakuri
na ya dauki hakar a matsayin kaddarar da ko
64
135
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
bargo, sannan yahau bisa abin sallah ya soma tilawar karatun Alkur'ani mai girma.
Har takwas saura na safe Muneeba na
aikin bacci ko alamun tashi bata yi ba, ganin
hakan yasa ya tashi daga tilawar karatun da yakc
yi yaje ya leka fuskarta baccinta take lakadan
fuskarta tayi sawaitayi kyau sosai, ya kai hannu
ya shafi kumatunta masu taushi, ya shafi
la66anta masu sul6i, yayi murmushi da ya tuno
cizon da dan bakinta ya gantsara masa a daren
jiya, ya kada kai ya lull6eta sosai sannan ya fita
zuwa sasan Goggo.
Sun gaisa ne take tambayarsa Munceba, a
dalilin tasan tare suke shigowa ko kuma ta riga
shi shigowa, don taya Goggon hidimominta na
safe, ya dan shafi fuskarsa yace, "Tana can
kwance bata jin dadi kwana mukayi tana
murkususun ciwon ciki, sai asuba ta sami bacci,
shi yasa har yanzu bata tashi ba", ta dan gintse
fuska tace, "Ciwon ciki? al'ada take yi hala?" ya
girgiza kai yacc, "A'a ciwo ne dai kawai". Tạ
dube shi sosai tace, "Ba al'ada ba ne, to ciki ta
samu ko haka da wurwuri?" yayi saurin cewa,
"Gaskiya bana tsamamnin haka ciwo ne dai
daga Allah", tacc, "to, Allah ya sawake". yace,
"Amin", da ya koma daki ya iske har a lokacin
baccin take yi, sai yasa shirt da gajeren wando ya
137
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
soma gyaran dakinsu, ko ina yayi fes-fes ya tsare
ko ina gado ne kwai da take kwance bai gyara
ba, ya fita tsakar gida zuwa kicin da bayi duk ya
share ya gyara ko ina tsaf, hatta kwanuka duk ya
wanke su.
Ya ji ana buga kofar sasansu, ya je ya
bude, sai ya ga Goggo ce a tsaye, ya bata hanya
ta shigo tana cewa, "Ya mai jikin har yanzu bata
tashi ba ne?" yace, "Eh, tana kwance, shigo bari
in kirata ina jin ta farka". Yana lura da Goggo
yadda take karewa sasan nasu kallo, kila
mamakin ganin an gyara ko ina take yi kada
yake ta ga jinshi da ruwa ta san shine yayi
ayyukan gidan.
Bata zauna bashi sai ya wuce dakin
baccinsu yaje yana dan bubbuga Muneeban yana
rada mata a kunne "ki tashi ga Goggo ta zo
gaisheki". A firgice ya ga ta tashi, yace,
"Lafiya kika firgita haka?" tace,
"Dole in firgita Goggo fa kace, zuwa kayi kacе
mata bani da lafiya?" yace, "Da naje gaisheta ne
take tambayarki shinc nace mata kin kwana da
ciwon ciki bangaya mata abinda ya faru nayi ba,
wannan ai sirrinmu ne, taso ki zo tana falo".
Ta sako hijabi bisa doguwar rigar jikinta
ta biyo bayansa falon inda Goggo tak ta ganta a
tsaye ta ce "Goggo ki zauna don Ailah, ina
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yake yi ban taba lura ba,ke ma Yaya tunda kin
sani ai da kin gaya min tunda shima dan gida ne
ai da shi za ayi, amma yanzu zata shiga matsalar
Guggonsu tunda ta nuna bata sam bata yarda ba,
wai da 'yar aminiyarta tayi niyyar hadasu
aurenshi kinji fa Yaya wai har zaka so bare fiye
da naka". Inna Amina tace,
"Yanzu ita Rahin din ce tace bata san auren
Muneeba da Mujeeb din tafi son sa da 'yar
aminiyarta, lallai zumuncin zaman bai yi ba
tunda har zaka fi son 'yar aminita da 'yar dan
uwanjini. Ni da zasu kyaleta mu a bamu muna
son abarmu, zata fi jin dadin zamada mu fiyc da
Rahin, saboda Rahin fitinanniyar halittace Allah
yayi, yanzu fitinarta zata tashi a kanki ta koma
kan Munceba, balle za su zauna gida ſaya, an
hada 'ya da fitina sai dai Allah yakare mana ita"
Inna Amina ta kwalawa su Khausar kira
duka su biyun suka shigo, suka sake gaishe da
Inna a karo na biyu, Inna Amina ta dube su tace,
"Zaa daura auren 'yar uwanku nanda kwana
uku". Gaba dayansu suka waro ido waje suka ce,
"Wacce 'yar uwar tamu?" tace,
"Muneeba mana” Khausar ta dafe kirji tace,
"Mama Munecba fa kika ce? Ita da wa?" tace,
67
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ita da dan uwanta Mujeeb, ai kun san shi ko?"
Khairi tace, "Dan wajen Guggo Rahin wandake
karatu a Uninversity Kashere?" Mama tace,
"Kwarai kin gane shi, shinc nan da kwan uku".
Khausar tace,
"Mama to Yaya Sadiq fa, shima ai yana son
Muneeba ba sai a tambaye ta ba a bata wanda
take so, shi Mujeeb dindama yana sonta ne?"
Inna ta се
"Mujeebu bai taba cewa yana sonta ba can
iyayensu ne suka hada auren shi bama ya nan bai
san za a daura auren ba ance daga makaranta sun
tura su Lagos ranar daurin auron zai dawo sai ya
dawo zaiji". Khairi taja tsaki da tace,
"Ashe ma bai sani ba shine za a cusa mana 'yar
uwarmu tana tsaka da karatunta ko aure ma bata
isa ba za a ce sai anyi mata au e, ai da sai a bata
wanda takeso kawai za a cuceta". Mama tace,
"Ya isheki haka, ina ruwanki, ko kinfi iyayenta
sanin abinda ya dace da ita ne? to wallahi ki
kama bakinki in bahaka ba ba zaku Dukkun ba
don ba zaku je ku zuga ta ta bij rewa iyayenta ba,
ku da zaku je ku lallasheta ku bata shawarwari
na gari ku nuna mata yadda zata yi zaman
aurenta lafi ya, tunda kuna 'yan karancce-karance
a a sai kuma ku nemi soko soki burutu a
al'amarin to ahir dinku kada inji wata magana
68
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
mara dadi ta fito daga bakinku, ku yi mata fatan
alkhairi kawai ku taya ta addu'a shine soyayarku
a gareta a matsayii ku na 'yan uwanta". Sukacc
"Shike nan Mama Allah ya sanya alkhairi
yaushe zamu tafi IDukkun?" tace,
"Sai zuwa jibi ana gobe daura aure, amma ku
bari Abbanku ya dawo sai muji banda zai ce
tunda itaba a lokacin zata tarc ba sai sati ya
zagayo". Suka fita suna sake tattauna wannan
abin al'ajabin. Khausar tace,
"Wai wane ne Mujeeb din ban gane shi ba ke
naga har kin gane shi". Khairi tace,
"Kema kin sanshi kin dai manta shi ne. wani
dogo fari dan gayu wanda shi babansu ya rasu
muka raka Mama gaisuwa muka ganshi tare da
Yaya Mustapha, har suka zo wajen motarmu
Mama ta yi masa gaishyuwa, kin gane shi
yanzu?" Khausar ta ce,
"O.K, na gane shi, gaskiya tayi dace yana da
natsuwa sosai". Khairi tace,
"Ai gayen ya hadu yadda kika san haifaffen
cikin Gombe haka yake, gashi kyakkyawan
bafilatani ko ba komai sun dace da Munecban
dole ma ya so ta in kuma baya so wallahi a daura
da Yaya Sadiq". Khausar tace,
"Ai wannan hadin na iyayensu babu mai tada
shi sai dai wani ikon Allah ko idan dayansu
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yamutu, amma ko suna so kobasa so sai an daura
tunda sun yi niyya. Idan mun je lallashinta kawai.
zamu yi kamar yadda Mama tace".
Inna bata baro Gombe sai da suka shirya
-yadda zasu bullowa wannan biki na bagatatan,
Inna Arnina tace a bar komai ana kayan daki a
hannunta ata yo daga Gombe.
***
Ranar Juma'a itace ta kasance ranar daurin auren
Mujeeb da Muneeba. Ranar alhamis shiryeshirye duk sun kankama a gidans Muneeba gurin
iyayensı Lawisa, ita kam Innan tace ba zata yi
o ba sai idan za ayi tarewa, shi yasa bata
gayyaci kowa ba, bata kuma yi shirin komai ba.
A gidansu Muneeba ma babu wani shiri da
Guggo Rahin take yi, a hakanne kanwar
Mahaifiyarsu da tayi saliama gidan tun basu
gaisa da Guggon ba taс,
"Gob: daura aure ba a kina shirin komai
ba?" ta ce
"Dada. wane shiri zanvi tunda ba tarewa za ayi
ba kuma ni meyc nawa ko tarewar ta zo tunda
bani na kulla auren ba, su da suka kulla ai su za
70
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
su yi duk wasu hidima". Dada ta ha zuka ta kawo wuya ta ce,
"Wai ke Rahin me ke damun rayuwarki nc, kina cikin hankalinki kuwa?Kin kuwa san muhimmancin zumunci? To wallahi ki shiga
hankalinki ki bar jayayya da auren nan in bahaka ba zaki mutu kumaayi auren suyi zamansu lafiya bayan ba ranki.
Yanzu 'yar dan uwanki,'yarki ta tashin kiyama itace abin kyamar ki, kiyayyar da kike
nunawa uwarta yanzu zata tashi ta dawo akanta kenan, to ki kama mutucinki kanki tunda kafin
ya tarwatse daga gareki, ita Hajiya Hariran da kike takamar zaku kulla auren tsakanin
'ya'yanku, idan ita bata da nagaba ai ke kina da shi, in banda shirme irin naki da son zuciya
yaushe zaka yarda danka ya auro 'yar mace, ba
kya gudun ta azo ta mayar da marigayin mijinta
kafin yamutu bayan da katabus a gidansa itace
mai juya goda shima ta juya shi? Ko kin manta
da halayyar aminiyar taki ne in kara tuna maki,
don mu jama'ar garin nan ba mu manta ba, ko da
yake tsutsunda ya jawo ruwa ai shi ruwan kanwa
dukan tsiya”. Guggo Rahin dai tayi tsuru ne tana jin fadan da Dadan ke mata wanda tana sane
haka al'amarin yake ammata gwammace ya auri
'yar hajiya, ita a nata wautar ai hakan ba zai
71
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yuwu ga danta ba, saboda sanin sirrinkan juna
da suka yita da aminiyar tata wanda bata san
Hajiya Harira ta rigata yin sammako a sanin
komai na duniya, ita kanta 'yar tata mai
budadden ido cc.
Kafin Dada ta bar gidan Goggo Rahin sai
da ta jadda mata cewa tayi abinci na masu zuwa
daura aure, sabooda abokan babansu Mujcebu da
abokan Mujeeba na nan Dukku da na Gombe da
zasu halarci daura auren duk da Mujecb din baya
nan. ta tabbatarwa da Dada zatayi komai da ake
yi sannan Dadan ta bar gidan ta nufi gidan su
Munceba.
Washe gari da safe za a daura aren ne
misalin sha daya na safe, tun wajen karfe tara
iyalan gidan Alh. Sani da shi kansa suka iso
Dukku. Matansa guda biyu be suka shi ga gidan
Guggon tare da direbansu da ke dauke da katon
akwati da wani a gannu guggo Rahin na ganinsu
ta tare su da murna saboda dama sun san junan
tun suna nan Dukku. Ta sa aka kawo musu
abinci da abin sha. Bayan sun gaisa ne suke
shaida mata tare da Alhaji suke yana kofar gida
tace,
"Shi ne tun shigowarku ba ku gaya mini ba aka
barshi a waje, bari in sa isha yabude masa dakin
Mujecbu unda an gyara dakin". Ta fita ta kira
72
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Isah tace maza ya bude dakin Mujecbu na azaure yayi wa Alh. Sa ni jagora gata nan zata zo śu gaisa.
Matan Alh. Sani suka nuna mata
akwatunda suka shigo da su. Suka ce inji Alhaji
yace a hadasu da wasu mata su kai can
gidakunsu Munecba. Guggo ta washe baki tace,
"Lallai Alhaji lar da wata dawainiyar akwati bayan kudin sadaki da ya aiko? To Allah ya saka
da alkhairi ya kara budi, an gode". Ta saka hijabi
ta sami Alhaji a ſakin Mujeeb, bayan sun gaisa
ta dinga zuba mas a godiya yace,
"Babu komai Mujecbu da na ne zan iya yi
masa fiye da wannan, don na ma abin ya zo a
kurarren lokaci shi yasa". Guggo anyi mata susa
a inda ke mata kai-kai sai ta gyara zama ta ce,
"Kai ma ka gani dai Alhaji, in banda ana son a
nuna min iyaka aa yaushe za ace za ayiwa yaro
aure cikin kwana biyar ba tare da saninsa ba bare yardarsa ai yanzu an daina irin wannan auren, wato su suna takamar Yayyi na rie su, sannan
sune kannen ubansa shi yasa za su yi gadarar
nuna iko, nima ai ina da iko a kansa basu kadai
ba". Alhaji Sani dama har da nasiha ya zi yi mata tunda ya ji tana a lawa da auren sai ya ce, "Kiyi hakuri, wannan abu da 'yan uwanki suka yi ba nuna iko ane zumunci ne suke son ya
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Kullu mai karfi, kin san babu wata mu'ammala
da ke kara karfafa dankon zumunci irin hada
auratayya a tsakanin ya'yayc, in har za ayi
hadin comin Allah ba don son raiba, ko don
wani abu na duniya da aka hanga Mujeeb yaro
ne na gari mai ladabi da biyayya, idan ya dawo
ina rokonki da ki karfafa masa gwiwa akan
wannan abin alkhairi da kawunninsa suka yi
masa, nuna kin amintan da hadin, shi zai kara
masa kaifin gwiwa ya rike amanar auren da aka
hashi".
Hana Alh. Sani ya dinga kawo mata
nassosi da nasihu akan ta yi hakuri da hukuncin
da 'yan uwanta suka zartars akan danta tunda ba
hukuncın da zai cutar da shi ba ne, ana sa ran
alkhairi su biyo bayan wannan aure, tare da
zuri'a mai albarka.
Mut ne suna ta dudduba kayan akwatuna
da aka kawo, zannuwa ne masu kyau da tsada
kala goma sha biyar da hijabai da gyalulluwa a
baban akwatin, m vinsa kuma kayan shafa ne
dankam niasu kyau da tsada. Kowa ya ga kayan
sai sun birge shi babu ma kamar takalma da
jakunkunan masu tsada ne a kamfanin (VINCI).
Guggo Rahin ta hada mata uku da matan
Ah. Sani suka tafi suka kai kayan gidansu
Munceba. A lokacin tana can dakin Inna Asabe
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ita da su Khausar da Khairi da Murja suna mata tsiyar irin kayan da tayi na kwallaiyar da suka
zauna suka cancada mata da wani leshi mai tsada
da Inna Amina ta dinko ta taho mata da shi. Tun
zuwansu Khairi a jiya suka yi mata shampoo
suka yi mata stracin kanta da (handdryer) da
suka zo da ita, aka yi mata, tun a jiyan suke aikin
gyara Munceban don har dilka da suka zo dashi
suka yi mata tayi kyau tamkar a ranar aka faro ta
a leda.
Yara suka leko dakin da gudu suna cewa
"Adda Munceba an kawo miki sabbin akwati
masu kyau, zo ki gani". Ta ballawa yaran harara
ta ce,
"Kai ku wucc ku bamu guri kafin in zane ku".
Daga baya Inna Asabe ce ta take basu labarin
akwatin da aka kawo, kaya kala sha biyar kuma
duk an dinka su, dinki kuma na gani na fada,
ance kayan daga Gombe ne gidan Uban dakinsa
don matansa ne ma suka kawo". Take gaya
musu. Khairi tace,
"Inna zamu iya zuwa mu gani?" tace,
"Mc zai hana, ku zo muje ku gani, suna dakin Larai, can aka kai". Su Murja sun ga kayan su
ma sun yaba sosai don da ganin kayar: ka san 'yan boko ne suka hada su.
75
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
An daura aure aurarrakin da misalin sha
daya da minti ashirin na safe, wanda a 6angaran
Mujeeb Alhaji Sani ya sami halarta da wasu
abokansa guda uku sai abokan Mujeeb din na
nan Dukkuhar ma da na Gombe duk sun sami
zuwa.
Mujeeb sun iso garir Gombe misalin
hudu na yamma. Daga makaranta bayan sun
gama abin da za su yi direct gidan Alh. Sani ya
iso a lokacin su kuma sun dade da dawowa don
bayan sallar azahar suka baro Dukku, gaba daya
shi da jama'arsa da iyalansa. Wani abu yake ta
daure masa kai tun yana garin Ikko da wasu
cikin abosansa suke ta kiransa suna taya shi
murna wai za ayi daurin aurensa sai dai yayi
murmushi kawai, yace, musu basu ji da kyau ba
auren kannensa ne za a yi, idan suka yi masa
musu haka nan yake hakura ya kyalesu tunda shi
bai ji wannan tatsuniyar da suke masa a bakin
wani na gidansu ba. Amma da ya dawo yaji Alh.
Sani yace yana son ganinsa sai zuyarsa ta fara
raya ko dai soki burutsun da ya dauka abonkansa
suna gaya masa gaskiya ne? to in gaskiya nc shi
kuwa da wa aka daura masa aure? Shi dai yasan
duk 'yan matan zuri'arsu babu wadda yace yana
so, to ko Goggonsu tasa an daura masa aure da
Suwaiba ne 'yar wajen aminiyarta Hajiya harira?
76
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Tunda ta taba yi masa zancen yaje ya nemi
Suwaiban, shi kum a ya nun ba ya ra'ayin da ta gaji da yi masa naci dole ta hakura ta kyalcshi,
Allah dai yasa bahaka banc.
Ya iske Alh. Sani a falonsa, ya dube shi
yana murmushi ya ce, "Da gani ko abinci baka ci
ba, wanka kawai ka yi ka zo amsa kiran
babanka?" ya gyada kai yace,
"Na kasa cinabincin nehar sai naji abinda
kirankaya kunsa, zuciyata sai dar-dar take yi
tamkar laifi nayi". Alhaji yayi dariya yace. "kwantar da hankalinka babu laifin da ka yi, abin
farin ci neta sameka iyayenka maza wato
Baffanninka sun daura maka aure da 'yar uwarka
Muneeba a yau da hantsi, mu ma dazu muka
dawo daga Dukkun". Mujeeb cike da alhinin
abin da yaji yace,
"Alhaji, aure? Me ya faru haka har aka daura mini aure bani da labari? Ita Muneebar ce masu
tayi muna soyayya da har suka yanke wannan
hukuncin?" Alhaji ya fuskanci Mujeeb sosai
sannan yace,
"Yadda baka da masaniya haka ita ma yarinyar
bata da masaniya har sai da iyayenku suka yanke
shawarar haďaku sannan ne itama aka gaya mata,
to Alhamdu lillahi tayi halacci don bata bijirema iyayenta ba ana ta yabon ta na sa mata albarka,
WATA KL SAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ak kaima ina rokonka arziki da ka yi
biyayya a garesu tunda na san ko kai mai
biyayya ne, kamar yadda aka yi ta sa mata
albarka kaima ina fatan idan ka isa can gida su yi
ta sa maka albarka a dalilin ka yi musu biyayya
kada ka irsura wani cikin 'yan uwan ko abokai
kai ko iyayenku mata wani yayi maka hudubar
iblis ka bijue wa wannan aure da aka kulla muku
addu'a kawai zaka yi Allah ya sa hakan da suka
yi ya zamo alkhairi a gare ku baki daya, ya baku
zama laf yada fahimtar juna da karuwar arziki".
Jikin Mujeb yayi sanyi kalau da wadannan
nasihohi na uban dakinsa, kwarai da zuciyarsa ta
soma kiusa masa sam kada ya yarda anyi masaba
dai dai ta an dauki karar yarinya an aura masa
yar shckara sha biyar, duk da a garinsu taisa
aure amına shi a nasa sarin ba yazu yake son
yayi aur: ba, ko da zaiyi aure a kalla sai ya
kammala karatunsa ya sami aiki, in so sarnu ne
ma sai yayı whalli sannan zai yi aure, amrna sai
gashi duk nashi tsaiin da yayi an rushe, haka
al'amarin Allah yake sai kay rayuwarka tsari
irin yadda kake so shi kuma baiyi daidai da nasa
tsari ba sai ya canza maca i lan kai mai imani ne
da yadda da hukuncin Allah a akanka sai kayi
na'am da hukuncin da yayi a kanka don hakika
hakan shine alkhairi a garcka, iuan ku aka
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
bijirewa hukuncin Allah to tabbas haliika zaka
ga ba daidai ba a rayuwarka", shi yasa Mujceь yayi saurin fatattakar sashen zuciyarsa da ke son
ingiza shi ya yiwa iyaycnsa tawaye, yavi amanna
da sashen da keyi imasa nuni da yin bivayya.
Ya risina gaban Alhaji Sani yace, "Na
gode Allah yasa hakan da suka yi shine mafi
alkhairi, kuma insha Allahu nayi biyayya bazan bijire musu ba, zan amshi auren da suka yi min
hannu bibbiyu”. Alhaji yace,
"Allah ya yi maka albarka sai kayi shiri ka isa
Dukkun yanzu tunda darc baiyi ba, sai Musa
direba yakaika sai ya dawo, kuma ka fara isagurin kawunninka ne akwai bayani da zasu yi
maka". Yace,
"Alhaji ko za a bar tafiyar sai gobe, yamma
tayi kuma wallahi a gajiye nake sosai", yacе, "Eh, na san a gajiye kake, ba kcmai kayi hakuri ka isa Dukkun yau na riga nayiva iyayen naka alkawarin da ka dawo yau zan turɔ ka bbau
komai tashi ka duba Musan a waje ku tafi". Yalaluba hannu a aljihunsa ya debo kudi dubu
goma yamika masa yace,
"Ga wannan ka rike ko zaka bukata, Allah ya kiyaye hanya". Sannin baya san idan ya bada kudI a kI karba shi yasa Mujceb yasa hannu biyu yaamshi kudin tare da yin godiya sannan yafito
79
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ya shiga cikin gidan Alhajin lon yayi sallama da
iyalansa.
A babban falon gidan ya iske matan
gidan, suna ganinsa suka soma tsikanansa da
"Ga Ango ga Ango!" yadan yi murmushi kawai
yace, "Dama nazo muku sallama ne Alhaji ya cc
lallai sai naisa Dukku yanzu, nayi nayi yabari
gobe na tafi yaki". uwargidan tace, "Gara katafi
yanzu tunda dare bai yi ba, kuma hakan zai
tabbatarwa da iyayenka kayi na'am da hadin da
suka yi maka". Nan dai matan suka yi masa
nasihohi sannan ya fito yanufi dakinsu da ke a
harabar gidan, tare suke zaune da amininsa dan
wajen Alhaji Sani tare suke karatu a jami'a,
amma kowa da fannin da yake karantawa
yasame shi kwance bisa katifa da laptop a kan
ruwan cikinsa yana sarrafatı, ya dubi Mujeeb
din yana dan murmushi yace,
"Ango ka sha kamshi, daga shigowar ka har
dakin yaamshi bakuncin kamshi, ya dan
harareshi yacc,
“Aiban san haka kake ba Vusuf sai yau, wato
har da kai za a yi mini rufa-rufa an daura min
aure ka kasa yin wayaka gaya mini, wato idan na
dawo na ji ko?" Yusuf yace,
"Mai da wukar aboki na, wallahi Alhaji ne ya
gargade kowa na gidan nan kada yaji anyi waya
80
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
an gaya maka a bari idan ka dawo shida kansa
zai gaya maka, to ya kake so inyi in karya dokar Alhaji ma ai ba zai yiwu bashi yasa". Mujecb yace,
"Ka fanshi kanka na amshi uzirinka amma da
har na farajin haushin ka sani baka gaya mini ba,
yanzu ma Dukkun Alhaji yace sai na tafi, Musazai kaini sai ya dawo". Yusuf yamike ya
kashe laptopdinsa yace,
"Ai daki ba zai tashi rayya ta zauna ba,
wannan angwanci da ni za aje asha kamshinsa,
ko rowar kamshin kake mini", yace
"Idan zaka raka ni wa zai hana ka, amma don
Allah kada muje ka saki baki gaban yarinyar nan kana sakin manyan maganganu da
kwakwalwarta ba zai iya daukaba yarinyace
karama don ina jin ko sha biyar bata cika ba, karike girmanka bana son' sakarci". Yusuf
yatafka hannuwa yana cewa,
"Ho manya amfa zama maigida anan da 'yan
watanni kuma baba, gaskiya dole ka dinga yi
mini fada tunda ni yaro ne ban shiga sahuh
manyaba. Naji zan kama baki nan a daina
bara,bata,a". Mujceb yace,
"Kai dai ka sani. Don Allah tashi mu wuce kada
dare yayi, kaga Malam Musa zaije ne ya dawo".
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Sun iso Dukku ana ta kirar sallar magriba
shi yasa Mujeeb iyace, su wuce masallaci,
hanyan sun yi sallah sannan su ka isa gidansu
Muneeba. Da Malam Musa ya sauke su sai yace
zai wucc suka ce ya isaya ya ci abicni sannan ya
tafi yace ba komai idan ya koma gida ya ci. Suna
tunanin yadda za su shiga gidan kenan a dalilin
har yanzu gidan dankam yake da jama'a 'yan
biki sai gasu Malam Adamu sun dawo daga
masallaci, ya gansu a tsaye yace, "A'a Mujeebu
mutanen Ikko, saukar yaushe" ya се,
"Wallahi dazu na dawo Baffa", suka durkusa
suka gaida su sannan Malam Adamu ya tura yara
cikin gidan yace su amso babbar tabarma da
abinci su ce ga yayansu Mujeebu yazo.Ai
kuwayar an da gudunsu suka jesuka isa da sako,
wani cikin yaran yagarzaya inda Muneeba take
yace, "Add Muneeba gasu Yaya Mujeebu nan
son zo, baki gani ba sun ci gayu shi da
abokinsa". harare yaron itace,
"Nace ne ka zo ka gaya, ko ance ne ka zo ka
gayamin? wallahi idan ana yini abu kana zuwa
kuna gava min sai na zane ka da buiala, oya
wuce ka caje ka yi wasankı". Yaron na fita su
Khairi suka hau yi mata tsiya, suka ce lallai sai ta
canza kaya tayi kwalliya don sun san za a ce ta
zo su gaisa da angor. Tace. "Haka kurum kama
اد
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
sai ace inzo mu gaisa, kunyarmu ta filani kuma
in zubda kc nan".
A kofar gida bayan sun ci abinci sun
natsa, mahaifin Munceba ma yadawo duk sun
hadu, sannan Malam Adamu ya korawa Mujecbu
bayanin duka yadda al'amari suka kasance har
aure ya tabbata da shi, ya kara ca cewa,
"Wannan abu da muka yi bamun yi da nufin
musguna maka ko takurawa rayuwarka ko da
wata manufa ba ne illa don daukaka sunnan
Manzo (S.A.W) da kuma habaka zumunci a
tsakanin zuri'ar mu, duk da yake mahailiyarka ta
nuna mun yi mataba daicai ba itaba yanzu ta ci
burin kayi aure ba sai kagama karatu ka fara aiki
ka tara abin duniya sannan zaka yi aure, kuma da 'yar aminiyarta, ina fatan kai ba zaka yi mana abinda ta yi mana ba, ba zaka tozartamu ka watsa mana kasa a ido ba tunda diyarda muka baka nagartacciyar diya ce mai addini mai ilimi duka guda biyu kuma mai biyayya don tayi mana biyayya ta yadda ko a ido baya nuna r ana bata
fatan
son hadin da muka yi muku ba, kaina muna ka yi mana biyayya ka nunakaima halas dan
Adamu
ne".
saboda
Mujecb ya risina a gaba Malam tsananin ladabi yace, "Wallahi Baffa tun kafin inzo nar, tun a
Gombe Alhaji yayi mini bayanin komai kuma
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tun a can na bashi tabbacin nayi na'am da abinda
kuka yi dari bisa dari, Allah ya saka muku da
alkhairi ya baku ladan zumunci kuma in sha
Allahu zan rike 'yar uwata da amana sai kuyi ta
mana addu'a". sauran Baffanin nasa ma suka yi
masa nasihohi tare da sanya masa a lbarka.
Turakar Mal Adamu suka koma aka kira
Munecba aka hada su akayi masu fada da
nasihohi sosai akan zamantakewar aure daga
karshe iyayen nasu suka futa suka barsu su uku
Mujeeb da Yusuf sai itakadai suka ce sudan
tattauna.
Kunya ce ta lullube Munceba, kara jan
mayafi ta rufe fuskarta ruf, Mujeeb ya dan saci
kallom Muneecban ta sha kwalliyarta sai zuba
wani ni'imtaccen kamshi takeyi mai dadi wanda
yaso ya rikitashi a dalilin shi ke zaune daf da ita.
(Aikin Inra Amina ne tun safe da kanta ta turare
jikin Muneeban da turaruka masu kyau da tsada).
Mujecb sai ya ga Muneeba ta karayi masa tsawo
da girma ta zama mace sosai sai ya ga tamkar ya
shekara ne bai ganta ba. Dakin ya yi shiru na
'yan mintuna kusan biyu, sabo da