Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi. Wannan
da basarake ta aura bansan ind zata kai mulki da iyawa ba.
Shigowar Mukhtar falon aka kauraye da yi masa barka da zuwa daga bakin kannen
sa Fajur, Kamilu da sauran yayan Baba Idi dana Sahura da suka zo daga Faskari yau.
Baba Sahura na fadin ango ka sha kamshi, na Uwa farin mutum mai farar aniya alherin
Allah ya kaiwa iyayen da suka haife ka. Sahura ta fadi hakan ne don ta san duk
wannan kokarin na gyara rayuwar su data dan uwan su, kokarin sa ne bana wani ba.
Shima yau ya kasa yin rowar murmushi, sai sakin sa yake gwanin shaawa. Ya
zauna daf da Alhaji yana gaida Mammah, tace Mukhtar ya naga idanun ka sun tasa? Ina
fatan lafiya dai?
barci nayi mai yawa Mamma, da yake jiya mun kusan kwana muna meeting ta ce to
madallah, ga abinci ta soma serving din sa burabuskon shinkafa da miyar ganye da
naman tolo-tolo, ya ce Ai Mamma ban iya cin burabusko, shake ni yake yi ta mayar ta
zuba masa fried sphaghetti da romon kaza sannan ya karba ya soma ci ana ta hirar
Saliyo.
Alhaji ganin kowa ya manta da Amani shi bai manta da ita ba, yar lelen sa tana
like a ran sa. Yace Mukhy, ka gama cin abincin? Ya ce eh Alhaji. Alhaji yace yawwa,
to maza tashi ka je ka zo min da TAFISU yau labarin rayuwar ka zaka bamu dukkan mu.
Da abinda ya rabo ka da iyayen ka tun da ka ce min suna raye, da dalilin da yasa
baka ko so a yi maka zancen gida ko na kasar ku.
Amma ina so ya zama an yi komai a gaban Uwa ta (Tafisu). Don haka je ka zo min
da ita.
Kunya ta kama Mukhy, musamman da Jalan ta zuba masa ido, ta rasa mai yasa take
jin sa kamar dan cikin ta, ta yaya zai iya tsallake Uwa da uban Amani ya je inda
take a cikin gidan su?
Sai da Alhaji ya sake maimaita umarnin sa, shi ba abun yace a aika Fajur ko
Safwan ba, tunda Alhaji ne da kansa yayi magana. Da kyar ya iya mikewa ya bi
matattakala da sassarfa zuwa sama, wato bangaren Amani.
Yana zuwa kofar dakin ya ci karo da sakon ta na Do Not Disturb. A jikin marikin
kofa. Dariya ce ta kama shi, sai kace a Hotel! Ai kuwa zata ga disturbance yanzun
nan. Kofar ya hau kwankwasawa da karfin sa kuwa. Amani na tsakiyar barcin wahala
barcin da migraine ya sabbaba mata, ta ji ana mata wannan bugun na rashin tsanaki.
Ta mike cikin rangaji da sarawar kai ko kayan jikin ta da suka zo dasu a jikin ta
bata cire ba balle dogon hill shoe dake kafar ta, haka ta afka gadon duka, tana
tafe zuwa kofar a fusace, tana fadin mai raba ta da Rakiya yau sai Allah.....sai
tayi kasa-kasa da ita, sai ta ci abu kaza-kazan ta.

Tana budewa dogon baabzinen yana sako kai cikin dakin har yana kusan ture ta,
saura kadan ta fadi don dama jikin ta ba kwari. Ta yi maza ta rike marikin kofar.
Farin gilashin dake idon sa ya zare, yadda zai ji dadin kallon matar tasa
rigimammiya Amani Faskari, ta yi yar kiba kib-kib ta yi jawur ta murje abinta. Mai
nuna ta samu kwanciyar hankalin da bata taba samu ba a zaman ta a Saliyo. Ga wani
uban su kunshi mai ja da baki da Mamma tasa aka yi mata a sawayen ta da zara-zaran
tafukan hannayen ta. Ta fito a amaryar ta sosai sai rashin mutunci fal a idanun ta.
Tace a fusace.
Shin baka ga an saka do not disturb bane? Da zaka zo ka tada ni daga barci
bayan bani da lafiya?
Mukhtar ya ce do not disturb, a dakin hotel kike? Ko wata tsiya kike kullawa a
dakin banda barcin asara? Kuma na dauka a gidan mutane kike ba a gidan ki ba, da
zaki kwanta kina zuba iko?
Kallon mamaki Amani tayi masa, ta ce gidan namu ne gidan mutane? Ni da gidan
uba na? Ya ce aikin kenan! Alfahari da Uba, ko anan aka binne cibiyar ki baki da
ikon cewa kada a dame ki a gidan nan, tunda ba gidan mijin ki bane gidan Mama Jalan
ne yanzu.
Amani tayi kwafa, ta koma gefen gado ta zauna tana fadin har akwai wani gida
da ya fiyewa mace gidan uban ta? Mukhy ya ce sosai ma kuwa, gidan uban nata na
wucin gadi ne, gidan da zata je ta haifi yaya shine comfort zone din ta, shine inda
duk mulkin data zuba babu mai kalubalantar ta. Amani ta zo iya wuya, idan nace maka
ni kuma babu wani comfort zone da ya fiye min gidan uba na muhimmanci zaka yarda?
Idan nace maka baka da gidan da ya isa ka ajiye babbar yarinya iri na zaka
yarda?
Idan nace maka Alhaji ya cuce ni iya cuta da ya bada aure na gare ka
kaskantaccen bawan sa zaka yarda?
Idan nace maka kyan ka da ake fadi bai taba bugar da ni ya sa na ji ka da wani
matsayi a rai na ba saboda baka kai matsayin da zan aure ka ba zaka yarda?
Ina bakin cikin abinda ya shiga tsakanin mu ranar nan a Saliyo, saboda kai ba
aji na bane, ka yarda?
Mukhy ya juyar da idanun sa da suka canza launi, yana kokarin hadiye bacin ran
da ya taso masa, ya ce me kuwa zai hana ni yarda tunda na kwana da sanin yar Qaruna
ce, Tafisu wadda tafi sauran mata, kuma a hakan aka bani sadaqar ta, ana roko na
Allah Annabi in karba da hakuri, saboda Alhaji kan sa ya san ba yar kwarai ya haifa
ba; ballagaza ce, banza ce, mahaukaciya ce kuma jahila, wadda ta rako mata duniya!.
Amani sai ta fashe da kukan da baya mata wuya na shagwaba da sakalci, amma na
yau iya gaskiyar ta take yin sa bilhaqqi, domin Mukhy yayi mata cin mutunci da wani
dan adam bai taba yi mata ba, tun baa je koina ba, ai ga irin ta nan, Daddy ya sayo
mata gori da rashin daraja a wajen wanda bai isa komai ba, sai ta kara tsinkewa da
kuka.
Mukhy yayi kwafa, yace yarinyar nan ina tausaya miki domin baki san rayuwa ba
ko kadan, baki san Annabi ya faku ba, baki san dukkan mu darajar sa muke ci ba, duk
wani rawanin tsiya ya kare a kan ki, Ubangiji ya laanci shaidan ya kuma fitar da
shi daga Aljannah ne sabida girman kan sa da jin cewa yafi kowa.
Baki san Allah ya ce Inna akramakum indallahi Atqakum. Ubangiji yayi alkawarin
dankafar da maabota girman kai dagawa da alfahari, masu girman kai iyalen shaidan
ne, ni ina tausaya miki, ina kuma tausayawa kaina, sannan ina tausayawa yaya na
idan kika haife su baki yi hankali ba.
Ke kam ai dadi ne ya yi miki yawa, shi yasa kika kasance mara godiyar Ubangiji;
Uwa da Uban ki na son ki, suna tarairayar ki da ririta ki da son ganin kin zama
matar aure ta kwarai, wani kama na iri na bai samu wannan gatan da kika samu ba.
Don haka in kin gama ki zo suna kiran ki a kasa.
Daga haka ya juya ya fice ya koma wajen su Alhaji. Yana kokarin maida walwalar
sa ta dazu, amma hakan ya faskara, domin kullum Amani ta ci mutuncin sa fita take
kara yi a ran sa, baa jimawa kuma in ya huce zata dawo ta yi masa kaka-gida a rai,
ya manta duk wani aibun ta.
Ba jimawa sai gata ta sauko cikin shiga ta kasaita, ta ci hill shoe din ta
kamar mai shirin tafiya dinar babbar aminiya, ta kafe dauri a gaban goshi tana tana
taunar cingam rakakas-rakakas. Ita a lallai ga wadda tafi sauran mata.
Da dane, da tuni Alhaji ya fara yi mata kirarin TAFISU! Amma yanzu da yake yayi
hankali sai cewa ya yi Uwa yaya kika sakko babu mayafi? Maza koma ki yi lullubi ta
zumburo baki sannan ta koma, Jalan tayi fatan a kusa da ita take ta kaiwa bakin da
ya sha purple din jambakin Elizabeth Arden lipstick kalar material lace din dake
jikin ta kyakkyawar mahangurba. Sai Allah ya ceci Amani daga can nesa da ita kafar
bene ta tsaya.
Ta dauko mayafin wanda dashi da babu duk daya dai ta dawo. Baba Idrisu yayi
sallama ya dawo dakin don ya dan zaga toilet ne. Alhaji ya nuna mata gefen Mukhy ya
ce nan ne wajen zaman ta family meeting zasu yi.
Kallon da Mamma Jalan ke mata ne yasa ta yarda ta zauna a gefen Mukhy din, ba
tareda ta yi musu ba. Jalan ji tayi kamar ta fashe da kuka a kan irin taunar cingam
din da take yi a gaban kowa. Ta na Allah-Allah a tashi meeting din ta ci uban ta. A
Saliyo ta dan samu saiti, wato yanzu an dawo gaban Alhaji da ke daure mata gindi
shine zata koma halin ta? Ita kuwa Amani tana sane duk abinda take yi don ta kular
da Mukhy ne, wato ta rama cin mutuncin da yayi mata, ta san baya son ta da cin uwar
kwalliya irin haka. Balle daurin gaban goshi. Har taunar cingam din ma baya so ya
taba ce mata ba tarbiyya bane.
Alhaji bai san tana yi ba. Haka Mukhy bai bata hankalin sa ba balle ta kular da
shi din data ke so, ya ce Mukhtar yau ina son in san tarihin ka, abinda ya fiddo ka
daga gida, da kuma abinda yasa baka so ka koma kusan shekaru tara kenan. Lokaci
yayi da zaka je gida tunda ka fara aje iyali. Ba fata ake ba, amma akwai mutuwa
akwai kuma ciwo. Ba damuwa muka yi mu san cewa kana da asali ko baka da shi ba,
amma lallai zamu kai Amani ga iyaye da yan uwan ka don su san da zaman ta, tunda
auren sunna ne muka kulla, wanda muke fatan a samu zurria a mai albarka a cikin sa.
Mukhtar ya nutsu sosai yana sauraron ubangidan sa kuma surukin sa a halin
yanzu, ya san gaskiya ya fada, amma sabanin lokutan baya da in yayi masa maganar
gida ransa ke baci yau shi da kansa cikin nostalgia (begen gida) yake domin ya fara
gajiya da gorin Amani. Kuma ya saka a rana sa cikin satin nan in Allah ya yarda zai
koma gida ko da Amani bazata yarda ta bi shi kasar su ba.
Mukhtar ya ce.
Labari na mai tsaho ne Alhaji, and very complicated, tragic story. Wanda nafi
so in yi revealing din shi tare da ku da iyaye na a zaune gabadaya.
Abinda zan iya cewa a yanzu shine iyaye na suna raye (as far as I know), ina
kuma da labarin duk halin da suke ciki ta hanyar wani abokina na kuruciya mai suna
Ari.
Na fito daga yankin Diffa. Diffa din wani babban birni ne da ke kudu maso
gabashin jamhuriyyar Nijar. Garin na da iyaka da tarayyar Najeriya daga kudu maso
gabashin kasar.
Birnin Diffa ya samu asali tun a lokacin daular Borno (Kanem-Bornu Empire).
Wato tun lokacin 1900. Asalin mutanen da suka yi rayuwa a cikin ta a lokacin
Kanurai ne (ko kuma Barebari). Amma yanzu Diffa ta hada kabilu guda uku; Larabawan
Diffa wadanda ake kira (Diffa Arabs), Buzaye da kuma Tubawa, duka suna cakuduwa
suna rayuwa a cikin ta.
Diffa tana nesa da kimanin kilomita 1360 daga babban birni Niamey.
Iyayen mahaifi na sune asalin kabilar Diffa Arabs, watau Tubawa ne, yaya ga
Sultan Oumarou Mai Diffa, wadanda tarihi ya nuna kakannin su, su suka kafa daular
Diffa Arab. Mohammed Bazoum kan sa, wato shugaban kasar mu na yanzu dan asalin
Diffa ne daga kabilar mu ta Diffa Arabs.
Sai Mukhtar yayi murmushi ya dubi Daddy, Alhaji iya labarin da zan iya baku
kenan a kan inda na fito, maganar iyaye na ko abinda ya fiddo ni daga gida sai mun
je gaban Ummami da mahaifi na Sultan Issoufou Massaoudou, a yanzu dana yi hankali
na ga ya dace nayi exposing ciwon zuciya ta gare su, su san halin dana rayu ciki a
kan su, maimakon in yi ta rike shi a kasan rai na ina fama da shi tun daga kuruciya
ta har girma na.
Alhalin su basu san ina da shi a kasan rai na ba. Ko sun sani, ban taba
tattauna shi da su ba.
Na dade ina fama da wani dabaibayi mai fizgata ga nesanta da gida, kullum
dabaibayin nan cewa yake dani in kara nesanta kai na da Diffa, ta hakan ne kawai
zan samu nutsuwa da kwanciyar hakali, idan ba haka bazan taba zama cikin nutsuwa
ba.
Rana daya tun zuwan mu Saliyo na tashi na nemi wannan dabaibayin a tare da ni
na rasa, na nemi fargabar da ke mamayata idan na tuna Diffa na rasa, na ji komai ya
yaye daga cikin kaina duhun da ke zuciya ta ya koma haske.
Wannan alamari ya faru da ni a wannan tafiyar da muka yi zuwa Saliyo, tun daga
lokacin hankali na ya koma gida da son ganin iyaye na, kuma jin zafin su da ke
raina na samu yana decreasing gradually (raguwa a hankali), a halin yanzu ina iya
yi musu uzurin da a baya bana iya yi musu, ina shaukin ganin su, sannan a shirye
nake ga fuskantar abinda a baya nake tsoron fuskanta a gida, komai tsaurin sa.
Na shirya komawa gida a halin yanzu. Hakika Alhaji yanzu na shirya ko ba don
Amani ba zan koma gida. Lokacin tafiya ta gun Ummami yayi. Ina jin kaina a zan iya
fuskantar kowanne irin kalubale da zai iya tunkaro ni with a very big and brave
heart, wadda a baya ban mallaka ba, na rasa farin ciki tun ina yaro, na kasance
cikin kadaicin rayuwa wato solitude mai sakawa dan adam inferiority complex, a
dalilin iyaye na basu yi min abinda nake so ba.
Alhaji na karbi auren da ka bani da hannu bibbiyu, banida bakin da zan godewa
kyautatawar ka gare ni, da rikon da kayi min, na karbi Amani zan tafi da ita cikin
ahali na duk da ikirarin ta na rashin son auren mu, ni na karba na kuma gode. Na
kuma yi alkawarin rike ta da amana har karshen numfashi na.
Alhaji sai ya saki hamdalah yana fadin, na gode Mukhtar na gode Allah ya yi
maka albarka, Im the one to thank you for changing my life positively, tunda ka zo
gare ni rayuwa ta ta canza, albarka ta lullube rayuwa ta, dukiya ta ta rubanya ta
yi albarka yadda ban taba zato ba, don haka nine da godiya na kuma yarda duk
lalacewar da duniya tayi, har yanzu akwai masu mutane masu amana akwai kuma mutanen
kirki, kai dai kayi wa dan kowa alkhairi ba sai naka kadai ba. Baka san wanne zaka
ci amfanin sa ba. Kuma baka san wanne ne zai ji kan ka ba.
Sai ka shirya mana motocin da ya dace muyi tafiyar a ciki, wadanda basa
makalewa a cikin sahara. Ya ce ai Alhaji a Land-Cruiser din ka kawai zamu tafi,
tana da tsaho da fadi, a kalla zata dauke mu nida kai, Mamma da Baba Idi da Baba
Sahura, da ita wannan. Ya nuna Amani da baki.
Amani ta galla masa harara ta murguda baki cikin takaici, wai ita yake cewa ita
wannan, alhalin ya lissafa sunan kowa, wato ita bata kai matsayin da zai fadi sunan
ta ba, irin wannan rashin darajawar da yake mata shi yake sawa take kara tsanar
sa, tunda gashi ya kara fadi a gaban iyayen ta da ita kanta cewa ya gode da sadakar
ta da Alhaji ya bashi.
Hawaye ya surnano daga idon Amani Faskari, yau ita ce zata koma rayuwa a kauyen
Nijar! Wata alkarya da ko sunan ta bata taba ji ba, wai Diffa. Da sunan aure a inda
bata da kowa. Mafarkin ta na tafiya yin masters a jamiar QUEEN MARY UNIVERSITY OF
LONDON ya zama tarihi! Ya bi ruwa! Ta zama cikin Diffa Arabs, makiyayan daji da
bata san ko yaya aladu da dabiun su yake ba.
Sai gani aka yi Amani tana rafzar kuka, ita ba abun tace bazata ba, ta san ba
mai bin bayan ta, Mukhtar bayan saye Ubanta da mugun sumumu-kasau din sa, Uwar ta
ma ya saye yanzu, sai abinda ya ce. Shi kadai ne mutum a idanun su.
Ta yi magana yanzu Mamma ta kumbura mata baki, tunda kuma a kusa da ita take
zaune.
Mukhtar ya fita yasa Tajuddeen ya fido Land Cruiser din Alhaji ya ce a kai ta
service a kuma yi mata full tank, gobe asubanci zasu yi zuwa kasar sa. Kuma shi da
kan sa zai tuka motar.

Tajudden tun a lokacin ya soma kewar Mukhy, wani kwayan mutum guda daya wanda
ya zame masa tamkar dan uwa a gidan Alh. Usman Faskari, ba irin alkhairin da baya
yi masa. Ya yi wa Mukhtar fatan alkhairi, yana hawaye, tare da rokon sa ya dinga
zuwa suna ganin sa lokaci-lokaci. Ko albarkacin Amani da zai dinga kawowa ganin
gida.
Haka yai ta sallama da duk maaikatan gidan. A daren kowa ya hada kayan da zai
tafi da su banda Amani, sai Mamma ce ta zo ta hada mata da kan ta. Kwana ta yi akan
kujera tana kuka, kafin asubah bayan ta ya rike, wuyanta ya kage, kuma a haka suka
ce bazasu jira ta ta yi wanka ba ta yi sallah kawai su kama hanya, don already
Mukhy (wanda yau wata irin shiga yayi, ta asalin ainahin larabawan Diffa), in ba
har ka yi masa farin sani ba bazaka gane shi ba, ya shirya tsaf cikin kayan kasar
shi a jikin shi wato traditional attire na Diffa Arabs ya fito a ainahin kamannin
sa na Tubawa ko kuwa larabawan Diffa). Kasancewar duku-duku ne cikin su babu wanda
ya ga irin shigar da Mukhy yayi, musamman da yana cikin mota ne a zaune, ya tada
mota ya bata wuta a waje, su kawai yake jira su fito.
Mamma duk zafin ta sai da tausayin Amani ya kamata ta hada da lallashi, ta kuma
yi mata alkawarin zata kawo mata Fajur daga baya in ta gama makaranta, kuma zata
bar Baba Sahura ta zauna da ita har sai ta saba da mutanen data tarar, kuma zata
nemi Yayar ta dake Nijar ta hada su. Wannan ne ya dan sanyayawa Amani, amma in ta
tuna ta bar comfort zone din ta kenan zuwa wani kololuwar kauyen Nijar bata sanin
sanda take sake rushewa da kuka, tana laantar Mukhtar da kaddarar data yi sanadin
zuwan sa gidan su.
**** **** ****

MU BIYO JARUMAR TAMU AMINA-AMANI, UWAR BABA IDI, SANNAN TAFISU YAR GIDAN BABAN
TA… ZUWA YANKIN DIFFA A LITTAFI NA UKU DON GANIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN TA DA
MIJIN TA MUKHY’ DAN KABILAR LARABAWAN DIFFA.

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment