Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata bakidaya ba tare da
ta ankara ba, sabon zautuwa ya same shi.
Sai yaji gaban sa ya fadi da wannan furucin nata, kuzarin jikin sa ya ragu, he
hate the word RAPE don haka ya rage gaggawar sa, kamar a mafarki sai taji muryar
Mukhtar yana kiran sunan ta yau cikin wani yanayi da yafi kama da lallashi na
matsananciyar soyayya, ya kankame ta iya kankamewa affectionately, yana shafa bakin
gashin kan ta cikin lallashi da neman hadin kan ta, kafin ya sanya bakin sa kasan
wuyan ta ya saki mata wani sassanyar kiss, wanda ya kusan sumar da Amani daga
kwancen da take.
Ai daga wannan lokacin komai ya sauya, domin bata kara sanin meke faruwa da ita
ba, kawai ta sakar wa Mukhy jiki ta daina kokawar kwace kan nata.
Domin abunda ta ji a tare da ita da ya yi mata wannan kiss din, ya wuce
misali. Mukhtar daya ji ya samu access tuni ya idasa sakin sauran kisses din sa a
guraben da take jiran saukar su. A hankali ya ke moving upward da tattausan lips
din sa yana sumbatar dogon wuyan nata wuri-wuri har ya isa ga bakin ta....
Amani couldnt explain whats happening from then, lokacin da Mukhy ya manne
bakin su wuri guda, ya soma ma Amani wani irin zazzafan hot kiss, a lips din ta,
kafin ya samu damar shigar da bakin sa cikin nata sosai, ta kuwa bude bakin tana
jiran isowar sa, sai da Amani ta saki numfashi mai karfi (moaning), mai nuna deep
and extreme pleasure din da Mukhtar ya sakar mata ba tare da ta sani ba.
Ta hakan ne Mukhtar ya samu access din da bai zata ba, domin Amani ta gama
sallama masa kan ta, nan ya sarke halshen su wuri guda yana sumbatar halshen nata
hungrily kamar yaron da ya samu sweet a cikin bakin sa.
Mukhtar ya gama kashe Amani a wannan lokacin ya kuma gigita kan sa ya koma
kamar ya samu hauka, a irin yadda yake sumbatar Amani da yanayin da yake ciki ya
tabbatar wa kan sa ba karamin kokari yayi ba wajen rike kan sa har zuwa wannan
lokacin da ya cika shekaru talatin da biyar, bai taba zina ba, yana adduar har ya
mutu kada ya yi, ya mayar da Amani ko dan yatsan ta bata iya motsawa domin ta hana
shi abunda yake kokarin yi din, don nemawa kan sa da ita kan ta nutsuwa, maimakon
hakan, sai ma samun kan ta da tayi tana enjoying sumbar da Mukhtar ke mata kusufa-
kusufa yadda harshen ta ko biro bazai iya bayyanawa ba, amma ilahirin jikin ta ya
karbi sakon Mukhy ta koina.
Mukhtar sai jin yatsun Amani yayi sun ratsa cikin lallausar sumar kan sa da
take cunkus, ta tura duka yatsunta cikin gashin sa tana kiran sunan sa da muryar da
bata yi kama da tata ba, wanda hakan ya kara triggering stuation din nasu beyond
expression. A wannan lokacin daga Mukhtar har Amani sun manta a duniyar da suke, ko
wata rashin jituwa ko kiyayya mai dogon zango dake tsakanin su, burin Amani shine a
kai ga babban alamarin ta gama shirya yin sallama da kuruciyar ta....
Amma sai wani tunani ya darsu a ran Mukhy, na cewa; shin ya shirya fansar da
samartakar sa ne ga Amanin da bata san darajar sa ba sam? Bata dauke shi mutum ba,
bata dauke shi komai ba banda daukar sa da take yaron gidan su? Amani har yanzu
bata son sa..... kuma ta fada har abada bazata so shi ba.
Wannan access din data sakar masa ya samu ba don SO bane, na shaawa ne da ya
taimaka wajen kimsa mata ita, ta hanyar seducing dinta da kiss, kada ya yarda...
kada ya sake, kada ya kuskura yayi saken da zai zama injin biyan bukatar gangar
jikin Amani, alhalin ba shi da gurbin so da kauna na gaskiya a zuciyar ta. Matsayin
sa da darajar da Allah yayi masa ya wuce haka!
Wannan ne ya dakatar da Mukhtar daga kokarin sa na cika sunnar aure, da
farantawa kan sa, har ma da Amanin da jira kawai take Mukhtar ya maida ita
cikakkiyar matar sa.
Ta gama sallamawa cewa a lokacin komai zai faru a shirye take, domin she cannot
resist him a yau. Amani sai ji tayi tamkar an yi ruwa an dauke Mukhtar ya mike daga
jikin ta ya koma gadon yana ta murkususun sa shi kadai. Sai a lokacin ta dawo
hayyacin ta. Kunya da haushin kanta suka zo suka lullube ta, ta hau tambayar kanta
me ya faru haka? Me ke faruwa yau kamar almara?
Ina ego din ta? Ina pride, ina class din ta, ina kuma gatan ta da dukiyar ta
data warawa Mukhtar kafa haka yau, tana jiran sa da abinda bata taba kawowa ran ta
amincewa da shi ba, gashi ya mata dandani haukaci, ya tashi ya bar ta da kunya da
takaicin kan ta.
A haka suka kwana tana kuka, kukan ta baya ta rago in ji hausawa, kukan bakin
ciki da haushi kan ta. Mukhtar kuwa falo ya koma bayan wani lokaci. A kan doguwar
kujera ya kwana cikin wani hali na kaka ni kayi. Amma kafin asubah ya samu barci
mai dadi, ko babu komai ya samu wani irin relief da bai taba samu ba.
Da assalatun fari kiran sallah ya tashe shi, yayi maza ya shiga yayi wanka da
alwallah, ya zo ya kunna fitilar dakin sai ya sameta ta hada kai da guiwa har
lokacin tana kuka kamar ta kashe kanta.
Jakar kayan sa ya bude, yau a gaban ta ya hau canza kaya. Yo kunyar ta yaushe
kuma ya ga komai itama ta ga komai, sai ita ne ta dukar da kan ta kasa don kunya.
Ya kammala shiryawa ya dube ta kan ta a kasa, tana ta hawaye, yace,
to Madam, da alkhairi, Shege yayi harama zai koma Najeriya, ya bar ki a Saliyo
ki yi yadda kike so da auren sa, a yi hutu lafiya, ko kina da sako gun Alhaji?
Amani ta mike ba tare data tanka masa ba tayi toilet. Kafin ta fito ya kammala
hada komai nasa ya na jiran fitowar ta domin Faytoory har ya iso, ya kuma kira shi
a waya ya gaya masa ya iso yana mota yana jiran sa.
Bata ce masa komai ba ta soma mayar da laffayar ta jikin ta. Mukhtar ji yayi
kamar ya kara rungume ta, ganin har lokacin kuka take yi sosai kamar ta hadiyi
zuciya, har da sheshsheka, amma ya hani kan sa da yin hakan. Ya yarda dai ta yi
nadamar maganar nan da gaske, ta kiran sa mai kama da shegu, amma shi kuma ya rike
ta bada wasa ba, har sai ta yi repenting iya repenting, yadda ya kamata, sannan zai
daina tada wannan zancen.
Ya isa inda take hannayen sa biyu zube cikin aljihun wandon Jeans baki da ke
jikin sa, kokari ya ke su hada ido amma ta ki, don yau bata da bakin rashi kunya
tunda ta gama zub da ajin ta.
Mukhtar ya ce na ce baki da sako gun Alhaji? Hawaye fal idanun ta tace inada
shi. Ka ce masa ina so ya mayar da auren sa da Mahaifiya ta, zan taya shi lallashin
ta.
Mukhtar yayi dif! Meyasa shi bai yi wannan tunanin ba tuntuni? Amma Alhaji....
ba shi da lafiya yanzu, anya Jalan din zata yarda?
Sai ya ce in har zaki lallashe ta ta yarda Alhaji ba zai ki ba, sai dai ki tuna
bashi da lafiya yanzu, bayan ta karfin jiki har da ta rashin iya aure. Amani tayi
maza ta dago tana masa kallon neman karin bayani ta hanyar zazzafar harara, abu
kazan uban sa take so ta zaga ko ta huce, wato rashin mutuncin sa bai bar kowa ba,
har Alhajin ma! Sai ya gyada kai yace eh, Im not joking, sugar ya ci karfin sa, ba
ya iya auratayya yanzu sam.
Amani ta daburce, ga kunya ga tausayin Daddy, sai ta hau masifa, ta ce kuma
aka ce kowa ne irin ka? Kowa ne yake aure don ya taba mace? Ko kuwa an ce maka kowa
ne yake aure saboda wannan rashin kunyar?
Baka san ana aure don mace ta dinga zuba ruwa a Buta tana kaiwa tsohon mijin ta
bandaki ko dafa masa ruwan wanka ba?
Dariya ce mai tsanani ta kama Mukhtar amma ya gintse, sabida ta hau kan tsini
sosai, yace,
irin naki auren ko?
Ta sa kai zata wuce ya riko gefen laffayar ta, yace Shege zai koma, sai
watarana! Idanun ta rau-rau, ta ce Allah yayi mana hisabi ni da kai, sabida yadda
kake cutar da ni da kuskure na.

Inda Allah ya cece ta daga Mukhtar shine kofa da ake bubbugawa, dole ya sakar
mata laffayan, idanun sa kamar su hadiye ta, ya karasa ya budewa Fajur data kawo
masa karin kumallo haka da wurwuri.
brother sabahul khair, an tashi lafiya? Ga nan breakfast inji Mammah.
Ya dubeta cike da kauna ya ce nagode Fajur, amma ki koma da shi ciki don na
makara, kuma ban iya karyawa da wuri ba, tuni Faytoory ya zo dauka na. Brother zan
bi ka in ji Fajur. Tana marairaicewa duk sai sai kamannnin ta da Amani suka
bayyana. Ya ce kada ki damu matas, zaku taho tare da Yayar ki in ta gama hutun ta.
Da wannan duk suka rankaya suka fito Fajur na cewa ya cika alkawari fa, ya dawo
ya tafi dasu Najeriya tana son zuwa kasar Najeriya, kullum Mamma na basu labarin
Najeriya mai GREEN WHITE GREEN flag.
A harabar gidan suka samu Mamma tayi lullubi ta fito domin su kara sallama da
Mukhtar, har kasa ya tsugunna ya gaisheta sannan ya shiga motar Faytoory. Amani ta
wuce cikin gida ba tare da ta tsaya sun kara hada ido ba, balle ta kalli shigar sa
mota, ko tace Allah ya kiyaye. Kuma a rashin tarbiyyah irin nata bata gaida abokin
Baban ta ba wato Malam Abdussalam.
Faytoory ya ja motar Mukhtar na gefen sa suka fita daga gidan, Fajur da Safwan
na masa adduar sauka lafiya. Mamma na daga masa hannu idon ta cike da kewa da kunar
sa.

Tunda ta shigo gida take kuka, koma me ya same ta yau ta tabbata Mama Jalan ta
jawo mata, don watakila magungunan data bata duk da ta zubar amma ai wasu sun narke
mata a baki, da turarukan data yi mata ne suka sa Mukhy ya samu damar da ya samu
yau a kan ta.
Yanzu ya tafi ya bar ta da cizon yatsa.

A haka Mamma ta zo ta sameta ta soma yi mata fada, a kan rashin gayar da
Faytoory da rashin iya tattalin miji da kula da yi masa addua. Ta ce ban taba ganin
sokuwa irin ki ba Amina, rashin tashi da Uwa hauka ne? Ai wani abun kana tsintar sa
a social environment din da kake ciki da kuma aladu masu kyau na alummar da ka taso
a cikin su.
Ke kam kin rako mata duniya!!!
Ta sake rushewa da kuka, tana son fadin Mamma taba ni yayi ta yi fa duk ya
hargitsa ni amma ga mamakin ta wannan maganar ta yi mata nauyi a baki, a ce ta
gayawa Maman ta ita. Gaar ta bar bakin cikin ya kashe ta. Sai ta yi shiru, tana jin
ciwon kalaman uwar. Da tace ta rako mata duniya wajen rashin iya tattalin miji! Da
ballagazanci!! Ta ce har da dolanci !!!

***** ***** *****

T
un daga wannan ranar Mamma Jalan ta maida hankalin ta da lokacin ta kacokam! A kan
gyaran tarbiyya da dabiu da addinin yar ta Amani.
Gashi yau har Mukhtar yayi sati biyu da komawa Katsina, Jalan har girki tare
suke yi da Amani don ta lura bata iya komai da ya shafi rayuwar mace a gidan aure
ba. Kada girki ya ji labari.
Hatta sallahr ta ta tsaya tana dubawa da gyarawa da saka Safwan ya dinga koya
mata karatun Alqur ani kullum. Ba don bata san ranar komawar ta Katsina ba da a
islamiyya zata saka ta.
A hakan ma babu laifi don tana da kwakwalwa, tana daukar kananan surorin da
Safwan ke kara mata kullum.
Shakuwa mai tasanani ta shiga tsakanin Amani da kannen ta biyu wato Fajur da
Safwan da mahaifiyar su da ke kokarin samar da kauna da shakuwa da hadin kai a
tsakanin su.
**** ***** ****

KATSINA
T
unda ya tafi bai kira Amani ba, ko sau daya, kai ko da kuskure, domin ya tarar da
very tight schedules a kamfani da shagon ta, amma tabbas ya san yana kewar ta da
rashin kunyar ta, kai har ma da fitsarar ta. Ya kan tun ranar su ta karshe with so
much adoration.

Allah yayi mana hisabi ni da kai, sabida yadda kake cutar da ni da kuskure na!

Sune kalaman ta da kullum yake yawan tunawa yayi murmushi. Masu tabbatar masa
da cewa (for the first) tima tayi maganar da ta zo ta yi nadamar ta a rayuwa.
Amma daga komawar sa Baba Idi har ma da Alhaji suka bude masa wuta kan sai sun
dangana da iyayen sa ko danginsa don shima Baba Idi ya dage a kan hakan. Mukhtar
kuma yafi son ya fara sulhunta Jalan da Alhaji tukunna kafin ya yarda su tafi
Diffa, gabadaya har Mamma Jalan don dai ya kore curiousity din sa a kan cindon ta
da na Ummami. Don haka ya gayawa Alhaji sakon Amani, na tana rokon su maida auren
su shi da Maman ta.
Alhaji Usman sai yayi dariya, yace a da can ma dana ke da cikakkiyar lafiya
Jalan bata yarda ta zauna da ni ba sai a yanzu da nake da rabin jiki shanyayye,
kuma ba zan iya sa ta haifar wasu yayan ba? Dube ni a cikin wheelchair.
Mukhtar ya ji wani iri ya ce cikin tausayawa,
ai Amani ta ce auren zuba ruwa a buta a kai bandaki da zuba ruwan wanka zaku
yi. Ba sai don wannan kawai ake aure ba Alhaji, in ji ta. Alhaji bai san sanda ya
bushe da dariya ba, ya ce ai ka sani Mukhtar ni bani da say, in dai a kan Jalan ne.
Na bar komai a hannun ku kai da Amanin, idan har ta amince a hakan da nake ni ai
zan fi kowa farin ciki.
A daren Mukhy ya yiwa Amani gajeren text messege, yana so ko yaya ya tsokane
ta, inda yace.

Shege ya zo gida lafiya, duk da baki nemi jin hakan ba.
Alhaji ya amince da bukatar ki na maida auren sa da Mamma, idan har zaki yi
masa yakin neman amincewar ta.
Su Baba Idi zasu taho a maida auren. A kasan sakon sa ya rubuta;
_Mai kama da shegu.

Sanda sakon ya shigo wayar ta girki suke yi itada Fajur, don haka bata duba ba
duk da ta ji alamar shigowar sa sai da suka kammala.
Ta runtse idon ta kadan, a kan wannan kalma da ya kara ambata mata, ta yarda
Mukhy, mutum ne mai tsananin riko, irin wadanda da wuya a cuce su su yafe, ba tare
da sun rama fiye da abun da aka yi musu ba ko mafiyin sa, ko da zasu huce din ma
kenan.
A ranar ta nemi jin ta bakin Maman ta kan komawa mahaifin ta, ta ce for my sake
Mammah!
Ta hada hannayen su wuri guda tana rokon ta. Har da hawayen ta.
A karshe Jalan ta amince zata komawa Baban Amani, albarkacin Amani da Mukhtar
don su yi zaman aure na jinyar Alhaji, koko zaman auren zuba ruwa a buta da kai
ruwan wanka kamar yadda Amani ta kira auren.
Wata biyu bayan nan Mukhtar ya yiwa Baba Idirisu da su Kamilu da Baba Sahura
shirin tahowa Kenema, shi kadai ya tsaya tare da Alhaji da kamfani, cikin kwana uku
da zuwan su aka maida auren Ahaji da Jalan, farin cikin da Amani ke ciki ne yasa
ita da kanta ta hada musu kayan su don su taho Katsina tare da su Baba Idi, wai
biki zata yi wa Daddy da Mammah, biki na kece raini, hararar ta Jalan ta yi ta ce,
ki fara shirin naki bikin dai, ni ba saar wasan ki bace.
Baba Idi dake wurin yace ai in suka isa Katsina ba zama zasu yi ba, mika ta
wajen mijin ta zasu yi, zasu dunguma ne su wuce wajen iyayen sa a Diffa region, ta
kasar Nijar. Kuma Mukhtar yace in sun tafi bazata dawo ba, sai ko da ganin gida.
Maganar sai ta tunowa Jalan da Yayar ta Aisata dake Nijar. To ai kamar a Diffa
din ne ma dan aiken dake tsakanin su yace take aure. Tsakanin ta da Aisata sai
aike, don bata taba fita daga gidan mijin ta ba tun ranar data shige shi. Ta sa a
ranta zata nemi jin hakikanin inda take a Nijar din in sun je, bata dai tabbatar da
inda take a can din ba don taba zuwa ta yi ba, zata nemo mutumin ya bata adireshin
Aisata ko don ta yi wa Amani Uwa a can da jinin ta kuma uwar ta.
**** **** ****

B
a karamin shiri Mukhtar ke yi na isowar Maman su Jalan ba. Ya sa an fente gidan
gabadaya da sabon farin fenti mai feshi, an shirya mata dakuna na alfarma da
furnitures yan uban su. Sannan ya sa an shirya dakin Fajur kusa dana Amani, Safwan
ma yasa na fidda masa daki daga waje kusa da na Kamilu. So gida ya zama full house,
family house don hatta Baba Idrisu sun bashi dakin sauka a gidan duk lokacin da ya
zo. Gidan Hon. Usman babban gida ne da ya lamushe dukiya mai yawa wajen ginawa a
matsayin sa na Architectural Engineer, har gobe kuma kullum kara kyawun gidan ake
da gyara shi yadda zai tafi daidai da zamani da duk wani sabon abun kawata da ya
shigo da shi daga waje.
Rakiya na ta hidimar dawowar uwar dakin ta, bata sama bata kasa don tabbatar da
ta ajiye ma Amani komai na bukata, yadda suka saba. Ta ji labarin auren Amani da
Mukhy a bakin Malam Tajudden tun kafin su dawo, tayi mamakin ta ita kadai ta bari.
Yanzu kuwa Kamilu ya gaya mata har Babar Amani mahaifiya zaa dawo don haka girke-
girke na musamman ta yi musu, zuwa yamma kuwa sai taji dirin motocin da suka je
debo su sun shigo, wato dai sun iso gidan lafiya.
Gidan ya kaure da hayaniyar farin ciki, Mukhtar yana gidan sa yana barci bai
san sun iso ba, don jiya kwana yayi da maaikatan Alhaji ana meeting na amana, kan
wanda zai jagoranci kamfanin Alhaji da gaskiya a cikin su tsofaffin maaikatan
Alhaji, sabida shi zai koma gida, bada jimawa ba. Bai kuma da niyyar dawowa.
Boutique din Amani ya koma karkashin kulawar Kamilu kasancewar shima kasuwanci
ya karanta. A karshe Mukhtar ya zabi Alhaji Badaru Matawalle wani tsohon maaikacin
kamfanin da sun fi shekara Talatin suna aiki tare da Alhaji, a shirya a bata, still
dai an jure zaman tare na lokaci mai tsayi, an kuma san halin juna, Alh. Matawalle
dan asalin Bindawa ne, shi Mukhtar ya baiwa kujerar sa karkashin saka hannun
mutumin da Lauyoyin Alhaji, suka yi resolution kan zaa cigaba da gudanar da ayyukan
kamfani yadda aka saba bisa amana da gaskiya, Mukhtar ya ce ko yaya suka fahimci
wani abu ya biyo baya na rashin gaskiya a kamfani, to kuwa zasu rufe kamfanin ne
kawai.
Aka yi komai a shariance, sannan ya ce gobe zai ma Matawalle handing over na
ofishin sa. Ba shi ya tashi daga barcin gajiyar da yake yi ba sai ana gab da kiran
sallar maghriba. Don haka a gurguje ya shiga wanka yayi alwallah ya fito yana
shiryawa a gaggauce, ya san yanzu su Amani sun dade da sauka.
Ya rasa dalilin dokin da ke cin ran sa sai kace shi aka kawowa amarya ba Alhaji
ba.
Murmushi ya yiwa kan sa, wani abu da ba kasafai yake faruwa da shi ba, wato bai
da yawan murmushi, kuma in yayin, shi kan sa ya san ba karamin kyau yake kara masa
ba.
Ya ce ma kan sa in haka ne ai shima yana da amaryar, sai dai tasa fitsararriya
ce hamshakiyar shuuma mara kunya, ba irin ta Alhaji mai kirki da sanin ya kamata
ba.
Sanda yake fesa turaren sa watau Azzaro Visit bayan ya fito daga wanka, sai da
wani farin cikin son ganin Amani ya darsu a ran sa.
Yana duba wayar sa ya ga missed call din Alhaji dana Kamilu rututu, da sauri
ya saka takalmi a kafar sa ya fita, bayan ya rufo kofar dakin da mukulli ya hau
motar sa Bugatti wadda Alhaji neya bar masa ita zuwa gidan Alhajin, duk da ba nisa
da nasa gidan tafiyar kafa ce kawai, ya kuma fi zuwa a kafan a yawancin lokuta,
amma yau da yake cikin saurin isa gidan yake sai kawai ya hau motar.
Yana parking yana fitowa da Safwan ya fara tozali, yaron ya zo da gudu ya
rungume shi, bakin Mukhtar yau a bude, fararen hakoran sa a warwaje, kai ka ce shi
ya mallaki kamfanin COLGATE, abinda ya baiwa su Malam Tajudden matukar mamaki, sai
fara yake yana rike da hannun Safwan suka shiga gidan, yana ta bashi labarin zuwan
su da abubuwan da suka gani na mamaki a hanya.
Kai tsaye falon Alhaji ya nufa inda ya tadda su su duka a can, har Mamma
Jalan, sun hada kai ana cin abinci tana zubawa Alhaji ruwa a tambulan, wannan abu
yayi matukar faranta ran Mukhtar. Yau rayuwar Ubangidan sa ta koma irin wadda ya
dade yana masa fata, rayuwa mai kyau da maana wadda addinin musulunci yayi koyi da
ita, ba irin kazantacciyar rayuwar sa ta baya ba ta babu wani jinin sa da zai rabi
niimar arzikin da Allah ya yi masa. Wadda watakila ita ta jawo masa yake ta shan
wahala a rayuwar sa.
Ya duba ya hanga a cikin su bai ga yar mulkin ba. Wadda tun zuwan su gidan da
aka kauraye da hayaniya ta samu migraine wato ciwon kan barin kai guda wanda gajiya
ta haifar mata, sai ta zame jikin ta ta haye sama dakin ta, ta shige ta kulle kan
ta. Har da lika takardar data ke likawa Rakiya a jikin kofa an rubuta DO NOT
DISTURB wato kada wanda ya zo ya dame ta.
A duk sanda Rakiya taga ta lika mata wannan a jikin kofa bata kara zuwa kofar
dakin sai ta neme ta don kan ta.
To yau ma hakan, Rakiya ta zo don ta kawo mata nata abincin, don ta san bata
cin abinci da mutane, nan ta ga abinda aka lika mata tuni ta yi ta kanta. Baba
Sahura ta tambaye ta ina Uwa, ta san in ta ce UWA Amani take nufi, ta ce tana
barcin gajiya ta lika kada a dame ta. Sahura ta ce Inye! Mulki sai mai

Please Login or Register in order to submit comment