Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ke hannun sa, sai yadda ya ga damar yi da rayuwar ta da gangar
jikin ta har wani lokacin, da zuciyar ta. Ya Rabbal Alamin. Wane irin balaI ne ya
tunkaro ta haka?
Saukar ta daga motar nan na nufin yau zata kwana daki daya da Mukhtar Diffa!
Matsayin miji da mata na Sunnah. Wannan wace irin bakar rana ce da bata san
kaddarar da ta yi mata sanadin ta ba? Ai ko Mukhtar bai sayar da kan nata ba kamar
yadda ya ce cikin gatse, ta tabbata sai ta gwammace bata san wani mai suna Mukhtar
ba, daga irin halayen sa da ta fuskanta na son girma da rashin daukar raini, muddin
bazata sauke kai ta yi masa irin girmamawar da yake so, ya kuma taso ya ga ana yi
masa ba, ya ga mace (wato mahaifiyar sa) na yi wa mijin ta (mahaifin sa) a gidan su
ba, wani zubin tamkar ta yi masa sujjada, to kuwa zata sha wahalar sa.
Ya riga ya san babu wannan tarbiyyar a tare da ita, to daga yau zata fara
daukan ta bisa dole, in ba haka ba bai da wani courage na kai ta gaban iyayen sa a
matsayin matar sa uwar da ya zabawa yayan sa.
Tunanin ta ya gama bata cewa Mukhtar ya tsayar da su a Lagos ne don ya samu
damar da ya dade yana neman samu a kan ta, wato damar da zai wulakantata son ran
sa, a inda bata da mai ceton ta sai Allah, shine dalilin da yasa ya shirya musu
kwana wuri guda da sunan transit, bata yi tunanin cewa Mukhtar mijin ta ne da
shariah ta halarta zaman nasu waje guda ba a yanzu.

Har Mukhy ya je ya kama masu daki ya dawo Amani na zaune cikin mota bata ko
motsa ba tana ta tunanin da bai bata mafita ko guda daya ba. Ya dauki kayan su a
booth ya kai ya dawo tana nan yadda ya bar ta; ihu ne kawai bata kurma ba. Damuwar
duniya da bacin ran da take ciki ya gama bayyana kan sa a kan kyakkyawar fuskar ta,
wadda yanzu ta hade tayi jazur idanun ma suka yi jazur abin ki da farar mace.
Mai taxi ya kunna mota ya ce ta fita shi zai wuce, sai ta juya kai ta dubi inda
Mukhtar ke tsaye, ya harde hannuwan sa a kirji yana kallon ta, yana jira ta gama
sake-saken wadda zata fishsheta, kafin ya gaya mata cewa shima bai shirya kwana
daki daya da mace ba, don bai taba ba, kuma bai shiryawa rayuwar sa hakan a nan
kusa ba, don bai shirya sallama samartakar sa ga macen da bata san darajar shi ba.
Da a ce zai iya, da ya gaya mata hakan ko don hankalin ta ya kwanta, cewa daki
ciki da falo ya kama musu; shi ciki ita falon, don ma ta daina kissima abinda take
kissimawa wanda shi bai taba kawowa ran sa ba.
Mai taxi sai ya koma masifa yana fadin ta fitar masa a mota zai tafi, haka dole
kanwar na ki, Amani ta ja dogayen kafafun ta ta fito masa daga mota, rataye da yar
farar hand bag din ta mai matukar kyau samfurin LV (Louis Vuitton), da cokalelen
takalmin ta kamar zai huda kasa, sai Mukhtar ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya
san ya yi ba. Ya juya, ita kuma ta bi shi a baya, a haka suka isa har cikin lifter,
inda suka shiga ya tashi da su ya sauke su a kofar dakin da ya shigar da kayan su.
Bata da zabi banda na bin sa ciki, tana tafiya tamkar ba ita ba, sabida yadda
tayi cooling. Kan ta yayi down, bata ko iya dago kan ta. Duk da haka ba wai ta rasa
komai bane daga izzar ta da takamar ta na halitta ba. Wadanda da su Allah Subhana
ya halicce ta. Kuma dai an ce hali zanen dutse ne amma tabbas a wannan lokacin
bakin ta kanwa yayi laasar.
Sai dai da yake an ce aure yakin mata, ni TAKORI na yarda da wannan
zaurancen, domin kuwa hakika yau naga tasirin sa a tare da jarumar mu mai kasaita
da izza wato Amina (Amani) domin tasirin sa ya kurda cikin jikin ta yana yaqar ta
ta koina ba tare da ta sani ba, dalilin da yasa tayi dan sanyi kenan, a lokacin da
Mukhtar ya sanya mukulli ya bude kofar dakin nasu, ya bata hanya ta fara shiga,
sannan ya wuce ciki ta bishi a baya, sai dai a wannan lokacin idan ka lura da kyau
zaka fahimci gab take da fashewa da kuka wanda ta san idan ta yi shi babu mai
taimakon ta!!!
**** **** ****

Suna shiga dakin Mukhy ya maida kofar ya rufe, sannan ya dau jakar kayan sa
ya wuce ciki batare da ya kara bi ta kan Amani ba. Don yunwa yake ji sosai, in yana
jin yunwa kuma (at times) zuciyar sa a kusa take.
Da ta gaji da tsayuwa dole ta nemi kujerar falon ta zauna, tana maida numfashi,
so ta ke ta yi wanka ko ta ji dadi a ran ta da jikin ta, sabida yadda jikin ta ke
mata danko danko na gajiyar tafiya, amma ta daure don tana jin nauyin shiga toilet
alhalin yana dakin. A ran ta tana jira ya zo ya ce ta shiga ciki ita ta hau gadon,
kada ta yi ciwon baya in ta kwana akan kujera, in ya so shi ya kwana a falon, amma
gogan nata sai ji ta yi yana kakkabe gadon, da alama kwanciyar sa zai yi. Ita kuwa
ko oho.
Amani ta dauki kayan wankan ta a jakar ta ta shiga toilet ta kulle da key ta
ciki, sannan ta yi wankan ta a hanzarce kuma a darare, don ji take kamar zai bude
ta a toilet din, ta samu ta ji dadin jikin ta, sai ta dauro alwallah ta zo ta bada
faralin sallar azahar ta wuce su a hanya. Mukhtar tunda ya canza kayan jikin sa
zuwa na barci yayi sallah sai ya kishingida yana hutawa a kan sofa-bed na dakin
cike da gajiya, ko ci kan ki bai ce mata ba.
Daga bisani yunwar cikin sa ta dame shi, sai ya janyo kan telfon din hotel din
ya kira restaurant din su, ya bada odar abinda yake so ya ci wato pounded-yam and
egusi soup, sai ya tuna Amani bai san favourite food din ta ba tun sanin sa da ita,
do haka ya fito ya tadda ita, da kan telfon din a hannun sa ya fito falon da ya bar
ta a zaune, ya samu ta yi wankan ta har ta shafa mai, tana sallah lokacin, daidai
ta sallame sallar ta ta mike kenan tana nade mayafin ta, ya dube ta ya ce.
Hajjaju may I know what you want to eat? Amani tayi banza da shi kamar ba ta
ji shi ba, wai ita ce Hajjaju, irin ya maida ita tsohuwa din nan, ko me yake nufi
da wannan sunan? Ko duk cikin ire-iren wulakancin sa ne zai dubi yarinya yar
kwalisa kamar ta ya ce mata Hajjaju?
Ganin ta yi kicin-kicin da fuska kuma bata amsa shi ba, yayi kasa da murya ya
ce ba da matar dakin nan nake magana bane? Ko Hajjaju bata ji na?
A fusace ta juyo, ta watsa masa manyan idanun ta da ke cike da tsana, raini da
fushi mai yawa, ta ce idan na ji, ka kuma ban ga damar amsawa bane sai me? Sai a ka
ce dole sai na amsa?
To bana cin komai, ko dole ne sai na kula ka? Ina ruwan ka da cin abinci na ko
rashin sa? Hanya ce kawai ta hada mu, zuwa Saliyo, kuma da sannu zata raba mu, so
ka tsaya iya matsayin ka na abokin kan hanyar Saliyo.
Mukhtar ya ce ni kuma na yi rantsuwa sai kin bani amsar me zaki ci, kin yi
kadan in yi miki magana ki mayar min da zancen banza, ni zaki gayawa hanya ce ta
hada mu alhalin kina matsayin matar aure na dana biya sadaki dagumi na ba na wani
ne ya biya min ba? Ya soma takowa zuwa gare ta kafin tayi aune ya saki kan telfon
din hannun sa ya yi wuf! Ya kama tsinin karan hancin ta da bakin rashin kunyar ya
murde su tare, sai da Amani ta saki kara don azaba, tana son kiran ka cece ni
Daddy! Amma Mukhy ya murde bakin da hancin ya hana sauti fita sai da wasu hawayen
azaba suka feso mata. Sannan ya sake ta yana fadin this is last warning! Kika kara
yi min rashin kunya wanda ya fi shi zan miki. Kuma duk abinda nasa a ka kawo sai
kin ci wallahi ba zan yi asara ba.
Ya zauna a kujera ya kira kitchen, ya ce su kawo masa tuwon dawa miyar shuwaka.
Shi kuma pounded-yam with egusi soup.
Ba jimawa aka kawo, tana tsaye inda ya murde mata baki tana hawaye dafe da
bakin nata wanda take ji kamar Mukhtar ya tsinke shi daga jikin ta, ya ce zauna mu
cinye shi tas tace Allah ya sauwake in ci abinci da kai, abincin ma tuwon dawa,
nayi maka kama da yar talaka ne? Ko aka ce maka kowa ma faqiri ne irin ka?
Maganganun ta sun tsorata Mukhtar don rashin tarbiyyar magana da ke cikin su ya
isa, ya ce sannu yar Qaruna, wato bakin naki har yanzu bai mutu ba ko? Yana bukatar
sabon garambawul ya mike ya doshe ta tayi maza ta haura bayan kujera kamar wata yar
wrestling. Mukhy ya ce mara kunyar karya, ki tsaya mana in ba tsoro ba? Ki gani in
ban yi reshaping bakin ba ta hanyar kara miki girman sa? In the way and manner da
gobe da kudi aka ce ki yi min rashin kunya da gorin arziki wallahi baza ki yi ba ta
ce ba tsoron ka nake ba, bana son ganin ka kusa da ni ne, balle kodaddiyar fatar ka
ta gogi tawa, don ban sani ba wannan farin naka ko ka hada dangi da zabiyu
(albinos).
Mukhtar ya hadiye zafin da maganar ta yi masa ya ce Allah ko? Su zabiyu ba
mutane bane kenan? Zaki ga zabiyu ganin idon ki, ranar da kike shayar min da
fararen yaya na masu kama da zabiyu, na lura fata ta ta tsole miki ido, don tafi
taki haske, idan ke mayya ce ki ci kan ki, ni kurwa ta kur!
Amani ta soma hawayen bakin cikin kalaman sa ta ce Kada Allah ya nuna min
wannan ranar, ko makamanciyar ta ko a cikin mafarki! Wato ranar da zan haihu da
kai.
Aka kwankwasa kofa ya je ya karbo abincin ya dawo.
Ya zauna ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa da dadin rai ya manta da ita a
tsaye, Amani na nan tsaye har zuwa lokacin kamar soja ta ki zama, don ta fara
tsorata da irin kalaman sa kamar ba Mukhtar ba, ya ce ki zauna ki ci tuwon nan ki
kuma cinye shi tas, ba zan yarda ki kwana da yunwa ba saboa hakkin ciyarwa, kin ji
ko yar Qaruna?
Idan kuma kika ki, wallahi mai raba ni da ke a dakin nan Allah ne kadai,.
Amani bata san sanda ta zauna gaban tuwo tana kuka ba, bakin ta har yanzu bai
daina radadin murdar da ya sha ba, bata so a kuma, ta ce fisabilillahi ka takura
min, ka na son matsanta min, ni bana taammali da tuwon dawa, sai ka saiwa kan ka
sakwara ni ka saya min bakin tuwo? Saboda Allah amanar da Daddy ya baka kenan?
Mukhtar ya hadiye dariyar da ta bashi ya ce to naji mu yi musanye, na gan ki
babu kumari ne, fingi fingi kamar kazar mayu, ina so kashin ki yayi kwari ne kafin
ranar amarcin mu, wato ranar saka kwallo a raga, ranar da zan yaye duk wani hijabin
raini dake tsakani na da ke, kafin zuwan ranar nake so ki yi kwari, ki yi kumari,
yadda zan ji dadin hutawa sosai a kan kowacce gaba babu fargabar zan iya ballaki,
ko kasusuwa su zo suna suka na, shi yasa nake son ki fara taammali da tuwon dawa
tun yanzu, don ki samu sinadarin carbohydrate sosai a jikin ki.
Ai jin abinda Mukhtar ke cewa sai bakin Amani ya mutu bakidaya daga nan, bata
taba zaton yana magana haka ba, balle kuma a ce ita yake gayawa, ta san dai
tsakanin su babu ragayya, amma bata san akwai sabo irin wannan ba ba da har zai iya
furta mata wadannan maganganu masu nauyi haka, ko kuwa su maza daga ranar da aka
daura musu aure shikenan kunyar su da bakunta ga diya mace ya tafi shikenan?
Amani ta tambayi kan ta, amma bata iya ta baiwa kan ta amsa ba, sabida kallon
da Mukhy ke mata
A rude ta zauna ta hau jefa loma bayan loma bayan wata hararar bakin ciki da ta
zabga masa, sai ta cigaba da jefa lomar tuwon dawa babu kakkautawa, bata ma bi ta
kan sakwarar da ya ce ya yarda su yi musanye ba, ba don komai ba sai don yadda
maganganun nasa suka kidima ta suka gigita ta, suka rikita ta duk a lokaci guda,
don bata taba zaton su daga bakin mutum kamamme irin Mukhtar ba.
Duk da a yawan shekarun ta ta san cewa shaani na aure ya fi gaban nan. Sannan
babu babba babu yaro when it comes to marital affair. Amma bata taba zaton Mukhtar
zai iya furta mata su ba, in aka yi laakari da irin personality din sa na kamewa,
fadin rai, girman kai da rike girma, da yadda ta dauka cewa kwatakwata ya tsaneta
ba ya son ta. Ba ta yi tunanin zai taba wannan hasashen na samuwar yaya a tsakanin
su ba, wanda ke nufin yana hasaso physical relationship (bodily contact) watarana a
tsakanin su.
Gara ta cinye tuwon dawa komai yawan sa a kan dai Mukhy ya kara yi mata wannan
sabon da kunnen ta ba zai iya jure ji ba, sabida nauyin da maganar ta yi mata a
kwanya, don ji ta yi tamkar Mukhtar yayi babban sabo, yo sabo mana! Tana kara
maimaitawa a zuciyar ta .... kada Allah ya nuna mata wannan ranar da yake hasashen
zuwan ta!
Sai da ya tabbatar ta cinye tuwon sannan ya kyale ta, kuma ya yi mamakin ganin
yadda ta cinye shi kamar kiftawar ido, bai san tsabar rudewar da kalaman sa suka
saka ta bane yasa ta cinyewa cikin rashin sani, ya mike ya wanko hannun sa sannan
ya fita zuwa reception don ya yi waya da Alhaji, yayi wayar wajen tsayin awa guda
kafin ya dawo dakin, nan ya ga Amani a kan doguwar kujera tayi wata irin
takurarriyar kwanciya, ta kuma kankame jikin ta cikin rawar dari sabida sanyin air
condition da rashin abun rufa. Da kyar in wuyan ta bai rike ba a irin wannan
kwanciyar da tayi a kan kujera.
Sai ya kasa wucewa toilet din da ya yi niyya domin ya yi wanka, ya koma uwar
dakin ya dauko duvet din sa da filo guda daya, yana gayawa ran sa Amani amana ce
ita a hannun sa, da mahaifin ta ya damka masa ba don ba ya so ba, ko don ya gaji da
zama da ita ba, sai don aure shine cikar rayuwar diya mace, ya rabu da ita ya bashi
ba don ya gaji da ita ba duk irin halin ta, ya bashi ne domin ya cikasa rayuwar ta
ta diya mace. Duk abinda ya yi mata dazu yana sane, so yake ta rage masa kaifin
baki amma ba shi da wata manufa a kan ta a daren yau, kai daga nan har zuwa wani
lokaci mai tsahon da ba zai iya kintatawa ba bai da wata manufa ta dabam a kan ta.
Ya zo ya rufa mata abin rufar, sannan ya soma kokarin saka mata filon a kasan
wuyan ta da ta dora a kan masangalin kujera, kayan da ta zo da su ne a jikin ta har
zuwa lokacin bata canza su ba, duk kuwa da cewa ta yi wanka, wai don kada Mukhy ya
zaci tayi kwalliya saboda shi ya kara raina ta, duk da ta yi wanka amma sai ta
mayar da kayan da ta tube. Gashin kan ta baki sidik mai laushi da tsayi ya watsu a
kan hannun kujerar da ta tada kan ta.
A hankali Mukhtar ya russuna yana kokarin saka mata filon da ya dauko a kasan
wuyan ta, faffadan kirjin sa ya yi mata rumfa, sai ya ji ya kasa dagowa daga
sunkuyon, sakamakon wani lallausar kamshi da ya shaka ta cikin gashin kanta, ya
kara kusanta hancin sa zuwa daf da gashin kan ta, wanda ke fidda kamshin tsadadden
turaren gashi na musamman, Mukhtar ya zama glued a hakan, yana ta shakar kamshin
gashin Amani. Wanda hakan ya yi sanadin da wani bakon alamari ya bakunce shi, tun
daga yatsar kafar sa ya tafi har zuwa cikin kwakwalwar sa.....
Kamar cikin mafarki Amani ta ji ta shaki sansanyar kamshin turaren maza na
Azzaro Visit, wani masculine perfume da kamshin sa ya ratsa ya tafi har cikin
ruhin ta, ya kai ziyara hancin Amani da ke barci sadidan a cikin yan dakikai, sai
ta muskuta ta gyara kwanciyar, yadda zata ji dadin cigaba da shakowa sosai, don ta
dauka cikin mafarki ne. Hakan ya bashi access na ganin kyakkyawar fuskar ta sosai.
Mukhtar ya tsura mata ido, yana kallon wannan kyakkyawar halitta ta Ubangiji, sai
ya samu zuciyar sa da cewa inama yadda ta ke da kyan nan haka halin ta ma yake da
kyau! Babu shakka shi kam da ya gama morewa.
Yana dagowa don barin wurin dan yatsan sa ya sarko silin gahin kan ta, wanda
hakan ya sa ta bude lumsassun idanun ta masu cike da barci da gajiya, da tabon
busashshen hawayen da ya saka ta, suka sauka a hankali cikin nasa, sai Mukhy ya ji
abinda bai taba ji a rayuwar sa ba. Ta mutstsike ido, ta kuma bude shi tangararau,
nan ta tabbatar wa kanta da gaske Mukhtar ne sunkuye a saman kan ta tsayin lokacin
da bata sani ba. She cant believe it, in aka ce kallon da ya dauki lokaci yana mata
ba tareda ta sani ba na soyayya ne ko makamancin ta, to kallon me yake mata haka
bayan ya gama ci mata mutunci?
Shi kuma sai kawai ya wuce toilet cikin borin kunya ba tare da yace mata komai
ba, don bai so ko kadan ta kama shi cikin wannan yanayin da ya same shi ba.
Jin dumi data yi ne yasa ta duba jikin ta, sai ta ga ashe duvet din gadon ya
dauko ya lulluba mata. Ta yi maza ta cire shi daga jikin ta ta ajiye a gefe, in ma
wani abun ya saka mata a ciki don ya cutar da ita, to ta Allah ba tashi ba.
Ya shiga toilet ne da niyyar ya dauro alwalla ya fito amma a yanayin da ya samu
kan sa ya san wanka ya gama kama shi, kunyar kan sa da haushin kan sa suka taru
suka lullube shi, yana wankan a shower yana cewa Amani masifa ce, ko kallon ta
mutum ya cika yi wato sai janaba ta kama shi. Da ya fito sai ya kasa hada ido da
ita, tana zaune tana tufke kanta da ya warware, anan falon ya shimfida darduma zai
fara sallah, sai itama ta tuna bata yi sallar ba, ta mike ta nufi toilet ta dauro
alwallah.
Sai kawai ya fasa tada sallahr har sai da ta fito. Ba tare da ya dube ta ba ya
ce mu yi jami, yin hakan sunnah ne, sannan ki bi ni muyi nafila za ta yi musu da
harare-hararen ta data saba ya ce is an option, not compulsory. Sai kawai ya tada
sallar sa ya rabu da ita.
Mukhtar da ya idar da sallah, sai ya zauna a kan kafafun sa yana lazimi, Amani
ta tada tata sallahr a gefen sa ita kadai don ta ki yarda ya limance ta, har cewa
take a ran ta haka kawai bata san asalin mutum ba zata yarda ya ja ta sallah? Da
mayafin ta mai kama da abin tatar koko ta rufa a ka ta tada sallah, ta ki yarda
suyi jamin sam, tana sallahr yana observing sallar tata, abin mamaki so many
kurakurai a cikin sallar ta, ko zaman tahiya ba daidai ta yi ba.
Data idar sai ya kasa shiru, ya ce Amani haka kike sallah a gurguje? Da wannan
mayafin mai kama da abin tatar ko....? Takaici ya hana shi karasawa yayi shiru.
Yana so ya ce ta yi masa karatun da ta ke yi a cikin sallar ya ji, sai ya ga cewa
ba wannan ne lokacin da ya dace da duk wannan ba. Lallai aiki ne jawur a gaban sa.
Yana jiran ta gaida shi, irin gaisuwar kauna da girmamawa da ya san Ummami na yi wa
mahaifin sa, a duk lokacin da suka idar da sallahr farillah ita da shi, amma shiru
kake ji wai malam ya ci shirwa, sai ma komawa data yi ta kwanta a saman kujerar
data tashi, ta dauki wayar ta ta soma shiga yanar gizo, ta ture duvet din da ya
rufa mata gefe guda don dai ta nuna masa bata bukatar komai da kowanne taimako da
ya fito daga hannun sa.
Mukhtar bai damu ba, jikin ta ko nasa? Amma ya riga ya sanyawa ran sa kin
hakuri da rashin gaisuwar nan tata, a zuciyar sa ya ji takaicin wannan rashin
tarbiyya nata, ya kuma gane ba karamin aiki ne jawur a gaban sa ba, in ya bar ta a
haka me zata koyawa yayan sa?
Murya shake, ya ce ba ki iya gaisuwar bayan idar da sallah ba ko AMINA? Baki
san gaida na gaba da ke ba? Baki san muhimmancin yin jami tsakanin mace da miji ba?
Baki san yawan ladan da ke cikin hakan ba? Gaisuwa ga miji in an idar da sallah
alada ce mai kyau ta iyayen mu da kannin mu.
Amani ta murguda baki ta kauda kai, ta ce a ran ta in Ustazu ya koma sai ya
nemo duro, zata bashi kyautar lasifika. Bata san cewa a fili maganar ta fito ba.
Mukhtar ya fusata ya ce haka kika ce? Fine. Abinda ya fi ustazu ma ki kira ni,
amma dole ki gyara dabiu da tarbiyyar ki muddin muna tare, ba zan dauki ko dayan su
ba, don ba haka na taso na ga ana yi a gidan mu ba. Oya! Ki gaishe ni ko a zuciyar
ki ne, in ba haka ba mu koma gida kawai a fasa zuwa Saliyon.
Juya kai tayi tana kunkunin fadin in dai sai ta gaida shi ne, to kuwa saidai a
koma gida din. Ya tabbatar ba zata gaishe shi din ba, takaicin ta kamar ya kashe
shi, sai aka kira shi a waya shi yasa ya rabu da ita da zancen gaisuwa ya amsa
wayar.
Tana jin sa yana waya da wani mutum, wanda ta ji ya kira Abdussalam Faytoory,
Alhaji ne ya hada su, cewa da sun sauka a Sierra Leone su kira shi, shi zai kai su
har gidan su Jalan a Kenema. Shi Abdussalam din tsohon abokin harkar sa ne a Saliyo
lokacin da yana harkar fitar da Iron ore, da Aluminium ore. Da turanci suke magana
shi da Mukhtar, ya gaya masa suna Lagos, zasu tafi Airport da asubahin washegari
daga nan su taso Sierra Leone.
Ya dubi Amani bayan ya gama waya da Faytoory, ya na so ya ce ta tashi ta yi
wankan kwanciya barci ta canza kayan jikin ta zuwa na barci su koma ciki, in ya so
ya bar mata gadon, don ya ga zaman ta a kan kujerar ya takura ta, sai ya ga cewa
wani daddadan barci irin na gajiya yayi awon

Please Login or Register in order to submit comment