Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng AMANI

2

Littafin

SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com




THE AMINA-BRIDE
A
can cikin gida Amani ce sunkuye tana jan ruwa a rijiya domin tayi wanka, sai ta ji
muryar Kawun ta Malam Idrisu daga zaure yana fadin a shigo da goron da alewa a kai
dakin Talatu ta raba ta baiwa kowa. Sannan ya shiga kwalawa matar sa Baba Talatu
kira yana cewa kina ina ne Talatu? An daura auren UWA da wannan yaron (Mukhtar)
yanzun nan, turo min ita, ga nan sadakin ta in bata a hannun ta.
Talatu ta fito daga dakin ta tana daura kallabi ta dubi inda Amani ke tsaye a
gindin rijiya wadda a lokacin ta dakata da jan ruwan kadan, tana sauraron me Kawun
ta Baba Idi ke cewa, Talatu ta ce ai gata nan a tsaye, tana jin ka.
Kawu Idrisu yace au to! Banza kika yi da ni kenan Uwa? To bar jan ruwan ki same
ni a daki in baki sadakin ki Amani ta cigaba da jan ruwan ta wani malolon bakin
ciki ya zo ya tsaya a makogaron ta, ya ki wucewa ya tokare numfashin ta, ta ma kasa
fahimtar me Kawun ta ke nufi data same shi a daki. Kawai sai gani suka yi ta saki
gugan a cikin rijiyar ji kake cundum! Ta wuce dakin da aka sauke ta.
Kayan ta ta hau tattarawa tana dannawa a jakar da tazo da ita. Baba Idi na can
yana jiran zuwan ta ya bata sadakin ta, ta sulale ta fice daga gidan ba tare da
kowa ya ankara da fitar ta ba. don Talatu ta koma daki tana shiri don fita ta
gayawa yan uwa da abokan arzikin su daurin auren da aka yi yau dinnan da gayyatar
su wunin biki a gobe.
Daddy da Mukhtar suna dakin da aka sauki Daddy din, suna tattauanawa bayan
daurin aure, kan Mukhtar a sunkuye yana jin yadda Hon. Usman ke masa magana cikin
tsananin raunin murya, wadda babu komai a cikin ta sai kauna da tausayin diyar sa
Amani, wadda a yau ya danka amanar ta a hannun mijin aure mafi soyuwa a zuciyar sa.
A daidai lokacin Amani ta fice daga gidan ba tare da sun sani ba, dan acaba ta
tare ta ce ya kai ta tasha. Tunda take a rayuwar ta bata taba hawa acaba ba sai
yau. Da ya fizgi babur din saura kadan ta wuntsilo kasa, ta kama rigar dan acaban
nan ta damke tana salati, nan tsamin hammatar dan Acaba ya kusa sumar da ita. A
haka ya fizge ta zuwa tasha yana fadin Hajiya sakar ni don Allah kada kisa duk mu
kifa, in baki iya hawa ba ki taka sayyadar ki mana?
A can dakin Baba Idi, Hon. Usman ya cigaba da cewa Mukhtar wanda a yanzu ya
tashi daga yaron sa ya koma surukin sa.
Mukhtar bana neman komai daga gare ka sai tausayi da kyautatawa ga Amani, bata
san kowacce irin wahalar rayuwa ba kada ka bar ta ta sha wahala, amma na yarda duk
inda zaka shiga a duniya ka tafi tare da ita, ka tausaya mata, ka kasance mai
hakuri da halayen ta, na san zaka iya shi yasa na baka, da na san bazaka iya da ita
ba ko kusa ba zan fara tunnanin hada ku aure ba.
Na lamunce maka kuyi amfani da duk abinda ta mallaka tare, ka taimaka mata ta
cigaba da juya dukiyar ta ko bayan rai na.
Sannan Baban ku Idi yayi magana a kan cewa yana son muje ga dangin ka mu kai
musu matar ka idan iyayen ka basa raye. Yace hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in
ba ya ga asali da tushen ka ba, ka yi hakuri da abinda ya ce dinnan, ba rashin
kauna bace gaskiyar aure kenan, ta fanni na bani da matsala da wannan, ka sani ko
ba ka da kowa a duniya na riga na amince ka zama suruki a gare ni.
To amma nima inada na gaba da ni wanda shine waliyi a gare ta, kamar yadda na
zama waliyin ka, dole a yi masa uzurin da yake so na dangana ta da iyayen ka.

Mukhtar ya yi shiru, kansa na kasa, sai kara dukar da kan nasa kasa yake yi
yana jin faruwar komai kamar a mafarki. Wai Amani ta zama matar sa ta sunnah daga
yau. Wannan alamari sounds unbelievable! Amma baa mamaki da ikon Allah. Zuwa yanzu
ba zai ce ga gurbin da ya ajiye Amani a zuciyar sa ba, da wannan sabon matsayin
nata na mata a gare shi. Illa iyaka ya san zuciyar sa bata kin auren.
Amma kuma maganar da Alhaji ke yi yanzu a bar dubawa ce, Alhaji yayi kokari
matuka da ya bashi auren yar sa ba tare da ya san kowa nasa ba, ba kuma tare da ya
san wani abu akan sa ba (asali, tushe da nasaba). Sai ya shiga tambayar kan sa ko
shi a karan kan sa ya shirya komawa gida din? Idan bai shirya ba sai yaushe? Mutuwa
bata sallama, duk da cewa har yanzu zuciyar sa bata huce ba, bata shirya komawa ga
iyayen sa ba, amma hakika yana son ganin Ummami. Ko da ba don mahaifin sa ba zai
koma saboda ita, ta kasance mace mai rauni karkashin ikon mahaifin sa wasu abubuwan
da yawa da yake zarginta da su ya kamata ya yi mata uzuri a kan su, cewa ba ta da
karfi a kan rayuwar sa sai abinda mijin ta da kuma aladar su ta wanzar a kan ta,
wato tana bin norms, culture and tradition ne na daular su. Me yasa tuntuni bai yi
wa Ummami wannan uzurin ba?
Da Daddy ya ga Mukhtar ya yi zurfi a tunani, sai yace Mukhy, in fa baka son
komawa ni ba zan takura maka ba, amma ya kamata kayi tunanin cewa yanzu yaya zaka
tara wadanda dole wataran zasu bukaci sani ko ganin dangin su, na fahimci akwai
abunda kake boye mini, ko ince yake damun ka da baka so in sani, amma ina ganin mun
wuce wannan stage din yanzu, mun zama daya fa Mukhy, feel free with me ka gaya min
damuwar ka da abinda ya rabo ka da gida don Allah.
Mukhtar ya muskuta sannan yayi ajiyar zuciya, a hankali ya soma baiwa Alhaji
amsa duk da cewa bai shirya bashi amsar ba.
Alhaji ka yi hakuri ka bar maganar zuwa Diffa zuwa nan gaba kadan, ka bani dama
in fara cikawa Amani alkawarin dana daukar mata first, na kai ta ga mahaifiyar ta
bisa amincewar ka.
Nayi maka alkawarin bayan wannan in muka dawo zan dauke ku duka har Baba Idrisu
da Baba Sahura mu tafi Diffa ku ga asali na mu kuma gabatar da Amani ga mahaifa na.
Im very sorry Alhaji, da na boye maka cewa iyaye na suna nan a raye, koda yake
da baki na ban taba furta maka cewa basa raye ba, kai ne kake tsammanin hakan.
Hon. Usman ya shiga Hamdala yana fadin masha Allah, to shikenan Mukhtar, take
your time. Na amince ka dauki Amani ku tafi Sierra Leone daga nan ku nemi
mahaifiyar ta.
Zan baka adireshin gidan iyayen mahaifiyar ta a rubuce. Sai kayi muku booking
jirgi gobe in Allah ya kai mu sai ku wuce, na so in yi muku biki na alfarma kafin
tarewa amma yanzu ina ganin ku fara isa ga mahaifiyar ta ko hankalin ta ya kwanta,
in yaso ayi komai tare da dangin ta na Uwa dana uba zai fi sa ta farin ciki har ta
karbi auren da sauki, ka san halin mutuniyar taka har yanzu ba wai ta amince bane,
nayi gaban kai na ne na abinda addini ya ce in yi, wato a matsayin ta na budurwa in
zaba mata miji nagari, ba tare da na bi raayin ta ba.
To amma na amince sai in ba Da na Mukhtar bane mijin Amani, in shi ne kuwa bani
da haufin nan bada jimawa ba zai sarrafa min Amani zuwa yadda nake burin ku zauna
tare cikin kauna da soyayya mai yawa.
Ina kara cewa ka yi hakuri da Amani, hakuri ba dan kadan ba, har ka aro wani ka
kara a kan wanda kake da shi, mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa.
Ina mata kwadayin samun tarbiyya wadda ta dace daga gareka.
Daga nan Alhaji ya ce ya gyara masa shimfida yana so zai kwanta ya huta, ya
jaddada masa cewa ya yi booking masu jirgin tafiya Saliyo tun a daren yau, ya kuma
shiga cikin gidan ya gayawa Amani yanzu idan ya fita cewa ta shirya gobe zai cika
mata burin ta. shi kuma Mukhy zai cika mata alkawarin ta.
Bayan ya bar dakin da Alhajin yake dakin da aka sauke shi ya nufa wato dakin
Kamilu, sai ya tsaya daga zaure ya kira Isyaka da ke wucewa ya ce in ka shiga ciki
ka turo min Amani, kace sakon Alhaji zan bata. Kunya ta sa ya kasa shiga gidan
kamar yadda Alhaji ya umarce shi.
Yaro Isyaka ya je cikin gidan ya duba har dakin Laure ya duba da na Baba Talatu
amma bai gan ta ba, ya tambayi Laure ko tana ina? Tace nima tun dazu ban ganta ba.
naje makaranta yanzu na dawo. Ya koma ya gayawa Mukhtar bata nan. Mukhtar ya ce ya
koma ya tambayo Baba Talatu, ko ta gaya mata zata wani wuri, Talatu ta ce rabo na
da ita tun da na gan ta a gindin rijiya bayan daurin aure, kafin in fita zuwa
makwabta, Kawun ta ya yi mata kiran duniyar nan ta karbi sadakin ta amma yarinyar
nan tayi funfurus ta yi banza da shi bata je ba har ya gaji ya fita masallaci.
Mukhtar bai san sanda ya baro zauren ya tako ya shigo gidan ba, har da shi aka
caje gidan kaf babu Amani babu ko tsinken ta.
Daga baya kwakwalwar sa ta gaya masa babu shakka Amani ta samu labarin daurin
auren su ne daga bakin Baba Idi, ta kuma yanke hukuncin gudu. Da dai ta bi umarnin
mahaifin ta a kan sa.
Zuciyar sa tayi bakikkirin, ran sa yayi mummunan baci da Amani, yana mamakin
kafiya da taurin kan ta, wai shi mace ke gudu! Macen ma wadda in ba don darajar
mahaifin ta ba ko kallo bata ishe shi ba, bai ji ya damu da inda ta tafi ba don ya
san dai ba zata yi nisa ba, tunda bata da adireshin Maman nata, yana ji a jikin sa
Balogun Sunday yaudarar ta kawai yayi, yafi damuwa da halin da Alhaji zai shiga in
aka gaya masa cewa ta gudu!
Ya dade tsaye cikin kunan rai, ya tambayi kan sa ko meye aibun sa haka da Amani
ke masa irin wannan kiyayyar, bayan na kasancewar sa yaron Baban ta kamar yadda
take yawan ikirari???
**** **** ****

“THE RUNAWAY BRIDE”
A
mani Faskari, jingine jikin tagar motar haya ta Sharon mai tafiya garin Bauchi, ta
yi kuka tayi kuka a cikin mota har ta godewa Allah. Da wuya wani abu ya sanya Amani
kuka, mace ce mai dakakkiyar zuciya kuma jajirtacciya mai jin cewa ko me namiji zai
iya itama zata iya, amma yau da ta tabbatar da igiyar auren Mukhtar ta hau kan ta,
daga bakin da ba zai mata karya ba, igiyar kuma ba ta kowa ba ta Mukhtar Diffa,
babu shakka an shammace ta, domin bata taba kawowa haka da wurwuri Daddy zai yi
wanan danyen hukuncin ba, ta dauka ko zai yin sai ya nemo dangin Mukhtar tukunna
wanda kafin nan ita ta yi kokari ta gudu gun Innar ta.
A wannan lokacin she cannot control her tears domin ji tayi tagama faduwa kasa
warwas! Babu class dinnan, ta kare mata, kuma yanzu bata fi sauran mata ba tunda ta
kare a yaron Baban ta.
Kenan sunan TAFISU ya bar ta yanzu, bai dace da ita ba yanzu, duk sauran mata
sun fi ta aji, ajin ta ya fadi! Tunda a karshe duk gatan nata da ego din ta da
Daddy ke fadi ta kare a bada sadakar auren ta ga mijin da zata kira yaron gidan su,
mara asali mara nasaba da ko tushen sa baa sani ba.
Tana da tabbacin Daddy sadakar ta ya baiwa Mukhy, tana da tabbacin sadakin ta
ma Daddy ne ya biya, don Mukhy ta tabbata ba zai taba cewa yana son ta ba ko da
yana son ta din, balle zata iya rantsuwa ta ci laya kan cewa yadda bata kaunar sa
haka shima baya kaunar ta, ko magana da yake mata a kan dole ne bisa tirsasawar
Daddy da ko kallo bazata ishe shi ba a dai wannan girman kan nasa da rashin son
raini, kamar yadda itama koda kuskure bata taba jin son sa a ranta ba sai jin
zafin sa, na kwace mata soyayyar mahaifin ta da yayi, tana bakin cikin wannan abu,
tana kishin Mukhy for that, tana jin haushin wannan matsayi da yake da shi a gun
Alhaji mai girman da ya kamo nata ko tace ya zarta nata yanzu a wurin mahaifin ta
Hon. Usman.
Babban abunda ke sa ta kara tsanar Mukhy shi ne rashin walwalar sa, kamewar sa
mai hanawa ka tunkare shi da maganar da ka yi niyya, ko ta shirya ci masa mutunci
ko rama rashin mutuncin da yake mata kallo daya zai yi mata ta ji bazata iya ba, a
takaice yanayin rayuwar sa mai matukar aji da yanayin halittar sa na rashin daukar
wargi ko raini yana ci mata tuwo a kwarya, yana hanawa ta taka shi a duk sanda ta
so.
A wurin ta wadannan halaye ne da bata so a Da namiji, domin zasu hana ta jan
zaren ta yadda take so a gun mijin auren ta.
Allah da ya halicce ta yayi ta mutum ce mai tsananin izzah da fadin rai, wato
mai tsananin son a bata girma, mai son mulkar mutane a karkashin ta, ta yadda in
sun ganta har suyi ta bare-baren jiki don cika umarnin ta, a duniyar ta mutum ce
ita mai son kowa ya zauna a kasan ta, tana juyawa tana mulki yadda take so, tana
kuma taka duk wanda ya shiga hancinta. Tun tasowar ta a haka ta taso da wannan
mummunar dabia, tunda a kan ta Daddyn ta ya raine ta, cewa ta fi kowa gata, ta fi
kowa iko, wato ta riga ta taso a matsayin mutum mai juya mutane a karkashin ta da
basu order su bi, sai ta ke fatan hakan ya dore har a gidan auren ta, har kuma
karshen rayuwar ta wato shima mijin duk da ta aura ya ya zama tana juya shi kamar
hakan.
Amma auren Mukhtar ta tabbata babu shakka sai dai ita ta koma kasan sa, a irin
halaye da dabiun sa da ta dade da sani, wanda wannan wani abu ne da bazata taba
yarda da shi ba.
Daddy ya gama kaskanta ta, don haka ta yanke shawarar barin su shi da Mukhtar
din nasa, ta bar musu gidan ta bar musu garin, in ya so Daddy yayi zuciya ya
haifawa Mukhtar din sa wata yar a gobe ya aura masa. Tunda ya asirce shi har yana
fadin bai iya surukuntaka da kowa sai shi.
Ita wallahi sau dubu gara mata Alhaji Sadi akan Mukhy, ko babu komai zata juya
shi yadda take so, musamman data fahimci yadda ya gama macewa a son ta, zai yi wuya
tasa kara ya tsallake duk yawan shekarun nan nasa. Sannan zai yi ta tarairayar ta
ne irin na tsohon da ya dau yarinya, amma Mukhtar???
Wani kukan ya kara kwace ma Amani, ta kifa kai a kan tafukan ta tana ta yi ba
kakkautawa.
Wato duk wasu plans din ta na gidan aure Daddy ya rusa mata su, ta hanyar aura
mata wanda ya fita izza. Mujin da yake da tabbacin bazata iya mulka ba.
Iyaka tunanin ta bata ga ina ya dace ta je ba, in ta shiga duniya saboda bakin
cikin Mukhtar ita tayi asara domin kuwa sunan ta ne zai koma karuwa hakan kuma ba
zai hana Mukhy rayuwar sa cikin sukuni da sakewa tare da mahaifin ta ba, kamar
yadda yake yi tana nan, watakila ma har Daddy ya nema masa wata yar mutuncin ya
aura masa, ita su manta da ita da rayuwar ta gabadaya, su shafe babin ta, wannan
itace babbar nasarar da Mukhtar zai yi a kan ta da zata dauwama tana haunting din
ta, ta dauwama cikin cizon yatsa ba tare da ta iya ramawa ba.
Don haka ta yanke shawarar tafiya Bauchi gun Hamidah. Kafin ta samu damar da
zata wuce Sierra Leone daga Bauchin, ko a kafa ko a kan fiffiken ta, zata nemo
Innar ta. Duk da ta san Hamida bazata taba bin bayan ta ba, cewa zata yi a nemi
zabin Allah a yi wa iyaye biyayya. Ta tabbata wadannan sune kalaman Hamidah da basa
taba canzawa daga haka. Tuni ta haddace su har bata son kari.
Zata iya yi wa Daddy kowacce irin biyayya amma banda ta auren kaskanci irin
wannan da ya yi mata, babu kaskacin daya wuce mata wannan a duniya, duk mazan
duniya a ce ta rasa miji na kece raini kamar yadda take macen kece raini sai Mukhy,
wato yaron sa da tafi tsana a duniya a bisa dalilai da hujjojin ta wadanda take
ganin sun isa hana ta karbar wannan auren ko me Daddy zai yi mata a kan sa kuwa.
Sai da tafiya ta mika sosai, suka yi wa shiyyar garin Katsina fintinkau sannan
ta gaji da kukan, ta fiddo hankaci ta share fuskar ta, ta fyace hancin ta sannan ta
dauko wayar ta data kashe ta kunna.
Kamar jira wayar take a kunna ta, sai ga kiran Hamida Balewa ya shigo. Ta yi
ajiyar zuciya, ta sani Hamidah is always there for her whenever she needs her, duk
da basu da raayi guda a kan komai, amma a kalla tana sauraron ta attentively tana
taya ta damuwa da damuwar ta, in abin kuka ya sameta suna kokawa tare, in na bakin
ciki ne ma suna yi tare, kuma tana bata shelter a gidan su a duk sanda ta bukata,
da shawarwari masu inganci duk da ba duka take dauka ba, kafin ta daga wayar muryar
ta duk ta dusashe don kuka.
Hamidah tace Sahibah kina ina? Gani a gidan ku, maigadin ku na fadin baku nan
duka gidan kun yi tafiya, yanzu ina zan same ki?
Da dusashshiyar muryar ta data ci kuka ta koshi ta ce, Hamdy, mun yi sabani
toh, ina hanyar Bauchi yanzu haka nima, wajen ki na nufa, don bani da wajen zuwa.
Ta fashe da kuka. Hamidah na jin haka ta fahimci komai, ko dai an daura, ko ana
gab da daurawa shine ta gudo.
Alright Sahibah, ki isa Bauchi lafiya, zan yi waya da Mama yanzu a gyara miki
daki na don watakila ki rigani isa, zan sa direba ya juyo da ni Bauchi nima yanzu
duk da na gaji, amma ba zan kwana a koina ba tunda ba kya nan gara in juyo, tafiyar
dare ce dai na san ta same mu.
Suka aje wayar a tare. Sannan Hamida ta kira Mahaifiyar ta Hajiya Muna ta gaya
mata batun zuwan Amani, amma bata gaya mata ko a kan menene ba, mutum ce mai kiyaye
sirrin wanda ya amince mata kwarai da gaske, ta roki Maman ta Haj. Muna kan ta
lallashi Amani ta ci abinci tayi wanka ta kwanta ta huta kan ta iso. Ta kuma ce,
don Allah Mama a nemi Panadol a bata ta sha kafin ta kwanta.
Sai dare suka shiga Bauchi, suna ta waya da Hamida, ita tasa direban Baban ta
ya zo tasha ya dauki Amani zuwa gidan su dake unguwar Fati Muazu. Har dakin Hamidah
mai aiki ta shiga da kayan Amani bisa umarin Hajiyar Hamidah. Sannan aka kaita
falon Haj. Muna.

Hajiya Muna ba tun yau ta san Amani ba, da irin amintakar da ke tsakanin ta da
Hamidah tun suna sakadire a Ulul Albaab Science Secondary School Katsina suke tare,
ta dubi kyakkyawar fuskar Amani ta ga duk ta yi zuru-zuru idon ta ya kode don kuka
tayi wujiga wujiga da wahalar zaman motar haya don bata saba ba, nan take ta gane
ba zuwan arziki Amani ta yi ba wannan karon kamar yadda ta saba, don duk zuwan da
take yi Bauchi a jirgi take zuwa har wani lokacin da rakiyar yar aikin ta Rakiya
wadda ke daukar mata jaka.
Yau kuma ta gan ta helter-skelter daga ita sai jakar kayan ta babu alamun tun
wayewar garin yau ta yi wanka. Amma tunda basu gaya mata me ya faru da ita ba da
yasa ta irin wannan balaguron wahalar sai itama bata tambaya ba, tace a ran ta in
ta yi wari zata ji ne.
Ta sa aka shiryo abinci mai rai da motsi ta saka ta a gaba da lallashi da ban
baki irin na uwa har sai da ta yarda ta ci kadan, amma jin abincin nan Amani ke yi
tamkar dussa sabida yadda zuciyar ta ke cunkushe da bacin ran Daddy da abinda yayi
mata. Ba don mahaifi mahaifi bane kotu zata yi karar su su biyun alkali ya bi mata
hakkin ta.
Amma me? Ta sani duk tsiya tana jin Daddy a ran ta, tana son Baban ta wani
irin so, ba zata so ya tsaya a mumbarin shariah da yar sa ta cikin sa ba ko da kuwa
ace ta samu tabin hankali ne.
Amma Mukhtar kam will pay for that, btunda ya amince aka yi mata auren dole da
shi bazata taba yarda ta zama matar sa ba, bai isa ba bai kai wannan matsayin ba,
bari Hamidah ta zo su nemi mafita, tana tunanin tafiya Saliyo a cikin satin nan
kawai in ta je kuma ta tafi kenan, ko a gidan talbijin da radio ne zata nemo Maman
ta mai suna Jalan, tunda Daddy ya ce suna kama sak, kuma sanda ta haife ta kamar
girman ta take in ji Daddy. In ya so sai ta yi amfani da hoton kanta da kanta ta
nemi Maman nata da shi (a wautar ta). Duk da dai ko hoton ta bai taba nuna mata ba.
Amma dai zata je Saliyo kota halin kaka, ko da zata bi lungu-lungu layi-layi ne
tana tambayar mai suna Jalan mai kama da ita. Abu daya kenan da zata iya fadi a kan
Maman nata watau sunan ta.
Haka tayi ta tunani irin na soki burutsu da rashin madafa. Ta yi wanka a dakin
Hamida ta yi sallolin da ke kan ta. Tana cikin sallah tana kallon kiran Mukhtar na
shigowa wayar ta da sunan da tayi saving lambar sa da shi. Ya kira sau biyu bata
daga ba sai bai kara ba. Don shi mutum ne mara jure wulakanci.
Can kuma sai ga na Daddy. A lokacin ta idar da sallah. Amma daga Mukhtar din
har Daddy din sai ta rufe ido taki amsawa, babu wanda ta amsawa don a ganin ta basu
da abinda zasu gaya mata ta yafe wannan laifin da Daddy yayi mata.
Ta bar su suka yi ta kira har suka gaji suka saurara mata.
Daddy ya mata dogon text wanda a ciki yayi ta lallashin ta abun tausayi, yana
tambayar inda ta shiga? Yace tana so hawan jinin sa ya tashi ko? Tana so rabin
jikin da yake motsawa shima ya karasa mutuwa saboda damuwar rashin ta ko? Amma ko
karantawa Tafisu

Please Login or Register in order to submit comment