Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta damu kwarai da jin wannan zance, don tana ganin rashin farfadowar sa da
safe a kan lokaci zai janyo mata tsaiko ko wani jinkirin na isa ga Kenema. Ba
lafiyar sa ce ta dameta ba.
Allah cikin ikon sa ma da Asubah da kan sa ya tashi ya shiga toilet ya yi
alwallah, sai da ya fito ya lura da ita a dai dai kafar gadon tana gyangyadi, da
alama a haka ta kwana a zaune. Ya shiga mamaki yana son tuno abubuwan da suka faru
daren jiya ganin barci take amma tana hawaye, amma kadan yake iya tunawa.
Yasa kafa ya shure ta ya ce dallah malama ki tashi ki sallah.
Amani ta bude ido a firgice, ta dube shi tana kulubi, tana kunkunin cewa in
gama jinyar ka, in kwana a zaune saboda kai, amma ka ce min Dalla Malama, wannan
rashin godiya har ina! Amma kadan da aikin dan adam, ka yi masa rana ya yi maka
dare. Ka yi da yar halak, cikin Usmanu da Jalan!.
Dan murmushi Mukhtar ya yi, ya daga hannu zai tada sallah sai ya fasa ya ce in
jira ki ki yi alwalar muyi jami tare? Ko har yanzu kina kan bakan ki na bazaki bi
limancin shege ba?
Idon ta ya firfito waje, ta dauka ya manta sakamakon jiya ya fita daga hayyacin
sa, ta dauka zancen ya wuce, ashe babu abinda ya goge daga cikin kan sa, ko da ya
kwana ba cikin hayyacin nasa ba.
Wannan karon ba musu ta dauro awallar ta fito ta bi shi jamin, don ta tsorata
da furucin sa, wanda yanzu cikin kwanciyar hankali yayi shi babu bacin rai ko
kankani a tare da shi, sai da ya fara da rakaatainil fajr, sannan suka bada faralin
asubahi tare, ya nuna mata yadda ake zaman tahiya na sosai ba irin yadda take yi ba
shakwar-kwar a kan kafar ta ba, ya kuma ce ta yi masa tahiyar ta a fili ya ji. Nan
ne Amani ta zumbura baki ta ce ai ban ga shaidar zaman ka Alaramma ba tukunna, na
dai ga shaidar karatun ka a kan kasuwanci, wadda kuma a kan sa na san ka.
Ka bar ni da sallah ta in bar ka da halin ka kai ma tunda dai ba kabarin mu
daya ba.
Mukhtar ya kasa cewa komai, don Amani ta zarce da tunanin sa a rashin hankali.
Gashi kan sa yana dan sara masa kadan-kadan, ba ya son yawan magana, sai ya
jingina da bango yana jan carbin sa, yana cewa.
Ya Allah ka taya ni, da abinda ka san bazan iya ba a kan yarinyar nan, Allah
ka shirya ta, idan mai shiryuwa ce, idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ka yi min
musanye da mace tagari mafi alkhairi a kan ta.
Ka shaida ya Ubangiji ban kasance butulu ba, mai manta alkhairi, shi yasa na ke
hakuri da halayen ta. Ka horemin duk wani naui na hakuri da fin karfin zuciya, daga
cikin wanda ka baiwa Annabawan Ka tsarkaka.
Wai sai taji adduar tasa bata yi mata dadi ba, (idan ba mai shiryuwa ba ce
Allah ya musanya masa da mafi alkhairin ta). Me Mukhtar yake nufi da wannn muguwar
adduar a gare ta?
Yana nufin Allah ya bashi wata macen data fi ki alkhairi, wadda bazata dinga
cutar da shi daga kalaman bakin ta marassa dadi ba.
Zuciyar ta tayi gaggawar bata amsa.

To ta Allah ba taka ba, in ma mutuwa kake roka min don ka auri wata, saboda
kana jin nauyin Alhaji in ina raye!.

Zai shige toilet domin yin wanka ya dan dakata jin abinda take fada, ashe kin
san da auren? Ai na dauka ko sadakina baki karba ba Baba Idi kika barwa, Baba Idi
na aura? Ta fuske kamar ba da ita yake ba, ya gyada ya shiga wankan sa.
Kafin karfe shiddan da Abdussalam ya deba musu sun kintsa suna jiran sa, ji
take kamar tayi tsuntsuwa ta bar su, don ta ga kamar su duka yanga suke mata. Ko da
Faytoori ya zo ma sai da ya bashi magani cike da kokon duma ya sha sosai, ya bashi
kullin wasu a leda ya ce ya jika kullum ya sha ya kuma yi wanka.
Da Mukhtar ya nemi baasi sai kawai ya ce masa na fahimci baka da lafiya ne,
wannan kuma ba komai bane tsari ne da dafai irin nawa na baka.
A motar Abdussalam suka wuce zuwa filin jirgin kasa, a nan ya bar motar tasa
suka hau jirgin kasa mai shiga har cikin Kenema Province.
Zuciyar Amani sai tsalle take a cikin kirjin ta tana kissima ko wacce irin
tarba Mamanta Jalan zata yi mata? Ko zata yarda cewa itama yar ta ce da ta haifa
tunda an ce ta samu wasu yayan bayan ita???
**** **** ****

KENEMA PROVINCE, SIERRA LEONE

G
idan da suka nufa matsakaicin gida ne da bai cika girma ba, akwai karamin gate
wanda mota zata iya shiga har cikin sa.
Taxi din data dauko su daga fili jirgin kasa zuwa gidan ta ajiye su a kofar
karamin gate din. Suka karasa, Faytoory ya danna kararrawa yana gaya musu nan ne
gidan da Jalan ke rayuwa, tun bayan rasuwar mijin ta uban yaranta, ta ci gadon
wannan kyakkyawan karamin gidan ita da yayan ta.
Fajur, baki ji ana danna kararrawa bane?
In ji Yayan ta Safwan wanda kan sa ke kan allon kwamfutar bisa cinya (laptop).
Rubutu nake yi, bana son tashi. Ta bashi amsa cikin hausar su da ba sosai take
fita ba, amma a junan su suna yawan yin ta, saboda yaren su na Krio da ya mamayi
harshen su wanda shine Lingua Franca na kasar, musamman a lardin su na Kenema.
Hajiya Jalan data fito daga kitchen sai kawai ta karasa ta bude kofar da kan
ta. Don ta san halin Fajur da kiwa. Tunda tace hakan bazata tashi a kan lokaci ba.
Don ta san kiwa irin ta Fajur, zata bar baki ne su yi ta tsayuwa sai ta mula don
kan ta zata tashi ta bude.

Fara, doguwa kuma siririyar yarinyar da ke tsaye a wurin ta bi da kallo, doguwa
sambaleliya mai kira da tsayin matan Saliyo, (a perfect replica of herself) idan ba
idon ta ne ke mata gizo irin wanda ya saba yi mata ba, exactly kamar yadda take a
tsaye dirarriya shekaru ashirin da daya a baya. Tana son tuno inda ta san ta amma
ta kasa. Sai dai feeling of familiarity da wani maternal sensation dake kara
mamayar ta.
Kamar ta san ta a wani wajen! Kamar ta dade da sani da sabawa da yarinyar da ke
tsayen haka ta ji a ran ta. Amma iyaka tunanin ta bata iya ta tuno a ina ta san ta
din ba.
Amani ta jingina da kofa tana kallon Maman ta da bata bukatar a yi mata karin
bayani, Jalan ce, Jalan din Daddy Usman, wadda ta hana shi iya rayuwa da kowacce
mace sabida wannan kyawu nata da haiba da ba duk mata Allah ya yi wa ba, gata nan
da kuruciyar ta har yau (at the age of fourty), wasu hawayen farin ciki suka soma
tsera a kan fararen kundukukin ta. A hankali bakin ta dake rawa ya motsa cikin
furta haruffan.
Ma.....Ma... Mama na!.

Jalan, wadda ta zama kamar an soma rewinding casette a cikin kan ta, ta soma
zaro idanun ta sosai, kafin ta mika mata hannu ita kuma ta tafi da gudu ta shige.
Suka rungume juna kamar bazasu saki ba suka saki kuka a tare mai sauti. Mukhtar da
Faytoory sai suka koma daga gefe cikin tausayawa, Mukhtar ya ji hawaye na son
tsatstsafo masa domin sai ya ji wannan rungumar inama shi Ummami ta yi wa, ya tuno
tasa Ummamin, yau shekaru kusan goma sha biyar kenan rabon sa da ita.
Yana ji Faytoory na cewa Amani ta cika ta haka a yayin da shikuma yake tsane
hawayen sa da bayan hannun sa. Mama Jalan cikin jin kunya ta janye jikin ta daga na
Amani, tace musu barka da zuwa ku shigo daga ciki.
Safwan da Fajur, suka mike suna kallon su da bakunta a idanun su, har falon ta
ta yi ma Mukhtar da Faytoory iznin shiga, jikin ta har bari yake, sam ta manta babu
mayafi a jikin ta domin jini ya gama bayyana kan sa, ya gaya mata yar ta ce ta
Alhaji Usman Faskari ta biyo ta. Dama ta riga ta sani ko ba dade ko bajima zata zo
gare ta, in har tana raye.
Shi yasa bata taba damun kanta a kan ta ba, tunda dama babu shakuwa ta
shayarwa a tsakanin su. Amma lokaci lokaci ta kan tuna cute fuskar jaririyar mai
tsananin kama da ita, wadda bata dauko munin mahaifin ta ba ko a farce, ta kuma
tambayi kan ta sau tari ko ta rayu?

Zafafan hawaye ne suka zubo mata tana kallon Amani, wadda har zuwa lokacin
kukan farin ciki take yi ta hada kai da bango.
Mukhtar ya dubi Jalan sosai da tsoro da mamaki domin yatsan ta na karshe mai
cindo da ya dauki hankalin sa a duka hannyen ta, da wasu attributes na ta da yawa,
musamman data juya baya tana tafiya takun ta a kan duga dugai irin na Ummami, duk
da kai tsaye bazaa ce tana kama da Ummami a fuska ba, amma a wulge suna kama din,
musamman idanun ta da dirin jikinta mai kauri ba irin na Amani dan shalaf ba, ga
kuma cindon nan guda biyu dake hannun Ummami a nata hannuwan duka biyu hagu da dama
itama.
He was shocked! Truely shocked! Amma wace hujja gare shi na cewa Jalan jinin
Ummami ce? Shi kan sa bai san komai akan Ummami ba, ko kasar data fito bai sani ba,
babu wannan shakuwar a tsakanin su tun yana yaro, da zata yi hira da shi balle ta
gaya masa wani abu makamancin wannan.
Ya dai san Ummami ba yar Nijar bace, ba kuma haihuwar Diffa ba, wato bakuwar
haure ce da aka auro tun ana cinikin auro matan Saliyo ga masu mulkin kasar Nijar,
amma bata taba yi masa matashiya a kan kasar data fito ba ko zancen wani nata, yo
ina ma ya gan ta ya zauna da ita? Sabida har ya bar gida ba shi da wannan alfarmar
irin ta shakuwar Da da mahaifi da ita.

Nan da nan wannan boyayyar suffar tasa ta bacin rai da rashin walwala mai
bayyana lokaci lokaci a tare da shi ta zo ta lullube yanayin sa na annuri da yake
ciki a yanzu, wato fuskar nan tasa ta bacin rai da hadewar fuska wadda da ita ya fi
kamantuwa a koda yaushe.
Faytoory kan sa sai da yayi noticing canzawar fuskar Mukhtar, a lokaci guda
yayi jazur ya hade kamar hadari, duk wata walwala da ke kan fuskar sa a baya ta
bace. A ran sa cewa ya ke Dubi dai yadda uwa ta rungume yar ta a bainar jamaa tana
kuma zaune da yayan ta biyu a falo guda, daya tana homework daya na aiki a
computer, ita kuma tana dafa musu abinci amma shi? Umh! Ummami bai taba samun zama
irin wannan da ita ba tunda ta haife shi, sai ka ce ba haihuwar sa ta yi ba, ko
kuma tana dana sanin haifar tasa.
Kada ki so ki ga yadda fuska da idanun sa suka koma a wannan lokacin.
Kafin ka ce meye wannan Jalan ta cika gaban su da kayan abinci da abin sha na
alfarma, fadi ta ke ku ci ku sha, na tabbata kun sha tafiya, na tabbata daga
Nigeria kuke. Ko daga Freetown zuwa Kenema sai mutum ya jigata a jirgin kasa.
Tana zama a kujera domin su gaisa Amani ta kara komawa jikin ta sai da ta san
yadda tayi ta kwanta a jikin ta, kunya ta kama Jalan, ita kuwa Fajur ta kasa
hakuri, ta matso tana tambayar Maman nasu Mamma wacece wannan mai kama da ke haka?
Ke! Daga mun Mamma na Safwan yace Yayar mu ce ta Nigeria ko? Sai kuka ya kwacewa
Jalan. Amani ta mika musu hannu ta jawo Fajur da Safwan jikin ta.
Jalan ta hada su su duka ta rungume a jikin ta tana cewa alhamdulillah! Jiki na
ya dade yana bani kina raye dama, ko ba dade ko baji ma kuma na san zaki zo gare mu
muddin da gaske na haife ki a duniya.
Mukhtar ya zamo kasa ya na bata hakuri cewa ta daina kuka, ga yar ta nan Alhaji
ya ce a kawo mata. Yana rokon gafarar ta, kuma yana so in babu damuwa zai kira
Alhaji a vedio call su yi magana da ita.
Ta ce babu komai amma ba yanzu ba sai ta gama ganawa da diyar ta.
Faytoory ya yi musu sallama cewa zai wuce gidan sa, ya ce ko Mukhtar ya bi shi
gidan sa ko hotel mafi kusa zai kai shi? Sai Mamma Jalan ta ce shi din Mukhtar waye
a wurin Alhaji Usman Faskari?
Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa sosai ya kasa amsawa, sai Abdussalam ne ya
gaya mata cewa mijin Amani ne. Angon ta. Alhaji ya gaya masa ya daura musu aure ko
tarewa basu kai ga yi ba, tasa fitina sai an kawo ta, shine Mukhtar din ya ce sai
an fara dangana ta da mahaifiyar ta kafin tarewar ta.
Wata irin soyayya da kaunar Mukhtar ta zo ta lullube Jalan, sai ta tsura masa
ido tana murmushi tana jin wani irin son sa a ran ta, kwatankwacin yadda ta ji
Amani yanzu a ran ta, tace da Faytoory, tunda haka ne ai ita ce da masaukin su su
duka, akwai bangaren maigidan zata bashi ya sauka, in ya so in zasu koma Katsina
sai Malam Abdussalam ya zo ya tafi da su filin jirgi.
Ai Amani da jin Jalan tace haka ta zaburo ta kuma zumburo baki tace wallahi na
zo kenan. Ni da Nigeria har abada! Daddy ya daina so na, me zan koma in yi? Shi dai
ya koma, shine dan sa yanzu ba ni ba. Ai tun baa je koina ba Jalan ta kai wa bakin
Amani mahangurba da hannun daman ta, ta kuwa same shi a daidai, tana fadin ke kuma
ashe baki da kunya? Mijin naki kike wa magana haka babu ladabi babu ganin girma?
Hausar Jalan bata da karfi sosai amma sun gane abinda take fadi din, duk da
cikin yaren Krio ta karasa fadin bazamu shirya ba ni da ke idan ba ladabi ga
babba!.
Mukhtar sai ya dago da kyar don kunya ya ce mata ai shi a gobe zai koma
Katsina, sabida ya baro ayyukan kamfani da yawa ga Alhaji ba lafiya, don ma dai
yanzu ya samu dan sa Kamilu na kula da shi. Amma Mukhtar ya zabi komawa immediately
ne don har zuwa lokacin a cike yake da Amani.
Ya san Alhaji bai da matsala yanzu tunda yana tare da dangin sa, ga kuma kanwar
sa a gidan wato Sahura. Ayyukan kamfani kuwa duk yana tafiyar da su ne ta yanar
gizo da kwamfuta, sannan yana da mataimaka na kwarai. Amma so yake yayi nisa da
Amani.
Bayan sun ci abinci Faytoory yayi musu sallama ya tafi. Mama Jalan tace bata
yarda ba sai ya yi kwana uku sun gana sosai. Tasa Safwan ya kai masa kayan sa dakin
marigayi dake harabar shigowa gidan bayan fajur taje ta share ta kunna turaren
wuta. Fajur da Safwan suna zaune manne da Amani, sun kasa matsawa ko nan da can
kada ta tafi ta bar su. Safwan zai yi shekaru sha biyar Fajur kuma goma.
Ta umarci Safwan ya raka Mukhtar ya huta, sai suka shiga daki ita da Amani da
Fajur.
Ta hada mata ruwan zafi mai kamshi tayi wanka sannan suka zauna suna kara
gaisawa. Sallah ce kawai ta tayar dasu a wannan ranar don kwana suka yi a zaune,
Amani na baiwa Maman ta labarin rayuwar ta da mahaifin ta gabadaya tun daga sanda
ta fara wayo har zuwa yanzu, da yawan matan da ya dinga aura yana saki sabida ita,
da artabun su da matar shi ta karshe Haj. Rabi, da halin da yake ciki a yanzu na
shanyewar barin jiki, ta bata labarin haduwar shi da Mukhy a Paris, da kawo shi
gidan su da yayi, ya bashi gida daura da nasu, ya kuma sakar masa ragamar
kamfanonin ta da shagunan ta, yadda ya dinga fifita alamarin sa, da irin yardar da
ke tsakanin su wadda take ganin ta rage mata daraja a gun mahaifin ta, har zuwa
aura mata Mukhtar da yayi ba tareda yardar ta ba wanda shine abinda ya kara sawa ta
tsani Mukhtar ta kuma amince Daddy yafi son sa yanzu a kan ta.
tace Mamma wallahi bana son sa, ko kadan, ko ganin sa bana son yi, kyawun sa ko
ilmi sa ko yanayin kasaitar sa dake burge Balewa bai taba ruda ta sun saka ya birge
ni ba, ban taba son sa ba, kuma har gobe bazan so shi ba, sabida yaron Daddy ne a
kasa na yake, kuma mara kirki mara dadin muamala ba ya girmama ni. Mara asali mara
nasaba gashi nan dai shi ba tsintacce ba shi ba Da ba.
Cikin halayen sa bakidaya babu guda daya da zan iya ce miki mai kyau ne. Ga
girman kai ga fadin rai, baa saka shi baa hana shi, a haka Daddy yake tunanin zan
iya zaman aure da shi? A rayuwata in ba mijin da zan juya kamar waina a tanda ba,
bazan taba yarda in aura ba.
Duk mazan duniya Daddy ya rasa wanda zai aura min sai wanda baida asali kuma a
karkashi na yake? Ai karshen kaskantawa Daddy ya gama yi min ita, shi yasa na ce ba
zan koma Katsina ba har duniya ta nade.
Ta fashe da kuka tana cewa ko sadakin su ban karba ba, don haka babu wani auren
sa a kai na ni. Baba Idin ma ya san ban karba ba shi na barwa abin sa, sai dai in
Baba Idin ya aura.
Jalan tayi taawizi. Tun baa je koina ba Mama Jalan ta gama karantar wacece
Amani, halayen ta da dabiun ta marassa kyau na girman kai, alfahari da dukiyar uban
ta, fariya da izzah na rashin sanin darajar da Allah yayi wa dan adam. Yawan
alfahari da rashin kunya na rashin mafadi ko tarbiyya mai inganci.
Tausayi mai tsanani ya kamata sai ta kasa ce mata komai. Sabida ita ta koina
Mukhtar yayi mata, har tsoron kwarjinin sa da ilhamar sa ta ji, don kwarjinin sa da
kasaitar sa cika mata ido da falo suka yi, ta yi duba don gano makusa a tare da shi
da ta sa Amani fadin abubuwan da take fada a kan sa ta rasa.
Sai kawai ta gane cewa Amani wawuya ce, doluwa, gaula kuma goyon namiji. Mai
halin yan fari, kuma wadda gata da kudi ya jika har ya yiwa yawa har ya taba
hankali da nutsuwar ta.
Bata samu tarbiyyar uwa da wadatar ilmin addini ba sai na zamani. Sanan bata
samu religious background na musulunci sosai ba.
A yanayin da take magana ma ga kowa, gatsau ba respect ba taunawa tana gatsine
baki na raini ga Mukhy ya tsorata Jalan.
Kamar Mukhtar itama nan take ta gayawa ranta cewa jan aiki ne a gaban ta jawur,
don haka zata roki Mukhy ya bar mata Amani zuwa nan da watanni biyu haka. In hakan
ba zai cutar da shi ba. Yo Allah ta tuba ina wani kwanciyar hankali da miji zai
samu a tare da Amani mai abubuwa irin na zararru? Ai gara ma ya bar ta aga abinda
zaa iya a kan ta ko kadan ne, tunda baa bari a kwashe daidai, kuma icce tun yana
danye a ke tankwara shi.
A halin yanzu tana so ta karance ta ciki da bai, don ta san ta inda zata bullo
mata, da yadda zata gyara gurbatattun dabiun ta da halayen ta ko da ba duka ba,
kafin ta shiga dakin miji ya zama ko manner of speaking ta gyara mata. Tunda an
riga an baro kari tun ran tubani.
Duk da haka zata yi iya yin ta cikin yan watannin da zasu yi tare, sauran sai
ta barwa Allah mai kowa mai komaia, ta kuma hada da addua da rokon Allah ya baiwa
Mukhtar zuciyar dauka da soyayyar da zata rufe masa ido daga ganin aibun munanan
halaye da dabiun yar ta.
Sai bata ce mata komai a kan Mukhtar ba a wannan daren, ta barwa ran ta, don so
take ta gano root causes na matsalolin sangartar Amani da rashin good upbringing
din data samu, sannan ta yi tunanin hanyoyin magance su a ilmance.
Duk da ita ma din ba wai ta samu zurfin ilmin zamani bane amma tayi sakandire
kuma tana da ilmin addini sosai, sannan ga shekaru ga kyakkyawan hankali.
Amani ta nemi ta bata nata labarin. Bayan rabuwar ta da mahaifin ta.
Nan ta gyara zama ta soma bata labari ta gaya mata cewa bayan Daddy ya sake ta
a gadon asibiti basu taho ba sai da ta warke tas, suka dawo Saliyo tare da iyayen
ta. Maman ta tayi mata jego, har ta warke. Mahaifin ta yayi fushi da ita fushi mai
tsanani a kan rashin biyayyar data yi masa na kin zama da Alhaji. Ta hana shi samun
makudan kudaden da yake samu a hannun Alhaji Usman. Yace yanzu gashi ta janyo ya
raba ta da diyar data haifa kuma babu tabbacin yarinyar zata rayu ko aah, ko zasu
sake haduwa, tunda babu wanda zai shayar da ita.
Ni kuma kullum na yi sallah sai na roki Allah ya raya abinda na haifa koda bamu
sake ganawa ba, yasa rayayye ne kuma ya amfani musulunci da alumma.
Daga baya bayan wasu watanni, Luqman tsohon saurayi na dana ke so ya dawo neman
aure na. Da kyar na samu mahaifi na ya yafe mini, yace Yaya ta Aisata tayi mishi
biyayyar da ni ban yi mishi ba, don ita kam sayar da ita ma yayi a Nijar ga wanda
bai ko sani ba, don haka kada in taba tsammanin zai barni in zauna a gidan sa, in
kawo miji kawai talakan dana ke so yayi min aure ya huta.
To dama ni da Luqman mun dade tare kuma a kan sa ne naki zama da Alhaji Usman,
da kuma nasa halayen wadanda na san ba sai na fada miki ba, tunda baban ki ne ya
kamata ace kema kin san su.
Muka yi auren kauna da soyayya ni da Luqman, wanda shine mahaifin su Fajur,
maaikacin kamfanin Tama da karafa ne (Steel Rolling Company), wannan gidan, shine
gidan da muka rayu a cikin sa tsayin shekaru goma sha tara ni da Luqman, cikin
rayuwar aure ta soyayya da fahimtar juna wadda mahaifin ki bai iya ko daya ba, shi
dai ya yarda kudin sa ne zai samo masa duk irin matar da yake so a duniya.
Shekara na zagayowa na haifi Safwan, sai bayan shekaru biyar da haihuwar sa
har mun fidda rai sannan daga baya na haifi Fajur, a shekaru ukun baya ne Allah
yayi masa rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya.
Iyayen mu kuwa sun jima basa raye, Aisata ya sayar da ita a kasar Nijar ko zuwa
Saliyo bata kara yi ba tun karbar ta da aka yi aka tafi da ita aka bashi Rakuma
masu yawa, wato shi mahaifin namu a matsayin sadakin ta, lokacin rasuwar mahaifin
namu ne ban san ya akayi ta samu labari ba ta aiko min wasika ta

Please Login or Register in order to submit comment