Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata yi ba ta share shi (deleting) don ta san data karanta zata
samu rauni a zuciyar ta ta fasa aiwatar da kudurin ta.
Sai ta kira Hamidah ta gaya mata ta sauka lafiya da irin tarbar da Mama tayi
mata, tace I really appreciate Mamas welcome, sai naji kamar Mama na ce, kin ji
dadin ki Hamdy, mother is everything, yanzu wa ya isa ya yi miki auren dole Mama na
raye? Auren ma da bawan gidan ku. sai kuka.
Hamida ta yi maza ta ce akul Sahibah! Ki gyara kalaman ki, ta ina ya zama bawan
gidan ku? Don kawai yana ma Daddy aiki yana biyan sa albashi? Kin san bauta kuwa?
Kin san tun a wane karni aka daina bauta sai ta Ubangiji?
Tukunnama ta ina neman halal da dogaro da kai ya zama bauta? Sahibah, Ubangiji
da ya halicci dan adam ya girmama shi ya karrama shi a kan duka sauran halittu, ki
daina kaskanta dan adam ko waye shi wai don yana ci a karkashin ki, musamman shi
Mukhtar a yanzu, ki ringa sanin irin kalaman da zaki ke furtawa a kan sa yanzu,
sabida mijin ki ne, da iyaye suka daura muku aure na musulunci ke da shi. Ba ruwan
malaikun ki (Raqib da Atid) da cewa wai bakya son sa aka aura miki, dukkan furucin
ki da ayyukan ki a kan sa zasu rubuta ne kawai ga lahirar ki.
In haka ne ina amfanin kalaman batanci da kaskanci ga mijin auren ka ko yaya
yake?
Balle Mukhtar bai yi kama da yadda kike kaskanta shi ba, bai yi kama da
wulakantaccen mutum ba. Wai me kika dauki kanki ne Amani?
Inna akramakum indallahi atqaakum!

Yanzu dai ki bar komai a hannu na sai na iso, sai mu shawarta abun yi, ki
kwantar da hankalin ki kin ji Sahibah? Idan ina nan babu mai miki abinda ba kya so
in zuba ido, wallahi sai inda karfi na ya kare wajen taya ki kwatar hakkin ki, amma
banda akan mahaifin ki, ko yaushe ki dinga tuna matsayin Daddy a gare ki, da
wahalar da yayi dake da rayuwar ki, da tsayin lokacin da ya dauka yana faranta
miki, ko a cikin iyaye shi na daban ne, ya fi karfin yayi hukunci a kan rayuwar ki
ki tsallake ki zauna lafiya da Ubangijin ki.
Ko nasihar Hamida ta shige ta, to fa bata bar ta ta yi tasiri mai yawa a tare
da ita ba, duk da ta san Hamida gaskiya ta fada. Sai ta hau lullube tasirin kalaman
Hamidah da hujjoji na son zuciya, tare da cewa ko me Daddy yayi mata a rayuwa
hakkin sa ne ya yi mata tunda shi ya haife ta ya kuma raba ta da uwar ta, amma
bashi da ikon yi mata auren dole. Ta koma ta jingina bayan ta a gadon ta kwanta a
gadon Hamidah ta rufe idon ta, ta ja duvet ta lullube har saman kan ta, tana jin
duniya na kara kuntata a gare ta in ta tuna igiyoyin auren Mukhy har ukku sun hau
kan ta.

A haka Hamidah ta iso gidan ta tadda ita. Ta dauka barci ta ke yi, bata san ta
dai rufe ido bane kawai tana dandanar azabar zuciya, sai ta aje jakar hannun ta da
mayafin ta ta shiga toilet domin ta rage marar ta, kafin ta fito Mukhtar ya cigaba
da kiran layin Amani. Wayar na gefen kan ta amma ta saka ta a silent don ma kada su
cigaba da damun ta shi da Alhaji don haka bata san ma ana kiran nata ba.
Mukhtar kuwa Alhaji ne ya saka shi a gaba da magiya kan yayi ta kiran layin
nata ko Allah zai sa ta dauka, yayi mata albishir din ta dawo gida daga inda ta yi
kaura a kaita Sierra Leone har dakin mahaifiyar ta in har an same ta a raye, in dai
zata yi hakuri da mijin da ya zabar mata, ya ce,
Mukhtar ya lallashe ta kawai ta dawo, in yaso ta fadi duk abinda take so ya yi
mata, don cikin hukuncin da ya yi babu canji har abada ko bayan ran sa Mukhtar zai
cigaba da rikon igiyar auren ta.
Shi yadda Alhaji ke shagwaba Amani yana tattashin ta da gudun bacin ran ta abun
yana matukar bashi mamaki da tuajjibi, wai dama akwai irin wadannan iyayen a wannan
zamanin da muke ciki, ko a kasar shi ne kawai babu irin su? Ko a nashi lardin ne
kadai babu su?
Hamida taga wayar Amani na haske sai ta lallaba ta leka. Sunan da aka yi saving
mai kiran da shi shi ya tabbatar mata Mukhtar ne da kiran nan ba wani ba.
DIRTY HUMAN BEING!.
Dariya ce mai karfi ta ji tana son kwace mata, ta toshe bakin ta. Ta lallaba ta
dauke wayar ta fice da ita can harabar gidan su ta samu kujerar roba fara tas ta
zauna a karkashin bukkar shan iska ta gidan su, sannan ta amsa wayar Mukhtar da
sallama.
Daga jin sallamar da amon muryar da nutsuwar da ke ciki muryar kai har ma da
tarin respect ya san ba Amani bace. Ga dukkan mamakin sa, sai ya ji wani tsoro da
fargabar abinda zaa ce masa ya samu mai wayar na shigar sa, a hankali ya amsa
sallamar Hamidah, sannan duk suka yi shiru na yan dakikai irin na rashin sabo da
juna, Hamidah ce ta karya shirun da cewa.
Mr. Mukhtar ne ko?
Ya amsa mata, rather subdued, cikin sautin sa da alamar mamakin inda ta san shi
haka farat daya ta ambaci sunan shi, bai yi tunanin ma Amani ta yi ajiye numba din
sa ba balle a ce tanazancen sa da wani nata a yadda ya san bata son sa dinnan bata
kuma son zaman sa a gidan su, kuma bata so wata alaqa take hada su.

A kasaice yace mata eh, nine. Excuse me pls, Ko zan iya sanin daga ina aka amsa
wayar nan?
Hamidah tace daga garin Bauchi ne. Bauchi?! Mukhtar ya tambaya cikin mamaki, a
me ta je, kuma wa ya kai ta? Ya jerowa Hamidah tambayoyin a jere a sukwane, don
kuwa bai ga alamun ta fidda ko sisi daga account din ta ba, balle ya yi tunanin ta
hau jirgi. Hamidah ta gaya masa gaskiyar komai na yadda suka yi sabani ita da
Amanin, ta tafi Katsina wajen ta ita kuma ta taho wajen ta a Bauchi. Mukhtar har da
ajiyar zuciya da ya ji cewa a (Sharon) wato motar kasuwa ta je Bauchi ita kadai, ya
tausaya mata a ran sa, don ya san wani abu ne da bata saba ba, duk a cikin kiyayyar
sa ne ko meye ma ya san zata iya, yace,
pls my sister do me a favour, kada ki gaya mata na kira kuma kin amsa, ki bani
address din gidan naku zan zo in tafi da ita gobe, saboda a bisa umarnin mahaifinta
Sierra Leone zamu wuce daga nan gidan ku kai tsaye in sha Allah, zan canza booking
din da nayi mana ya zama daga Bauchi zamu wuce Lagos, inda zamu hau jirgin
Freetown.
Hamidah ji tayi farin ciki ya lullube ta kamar ita ce Amanin, burin kawar ta at
last zai cika. Zata ga Innar ta! Ta san kowacce irin damuwa Amani ta saka kanta a
ciki a kan auren ta da Mukhtar zata zo da sauki muddin zata ga mahaifiyar nan tata
data kallafawa rai. In ta ga dama ma tace bazata dawo ba, hakan zai fiye mata
kwanciyar hankali in har Amani tana tare da Maman ta, fiye da in ita Hamidan ta ki
bata goyon bayan bijirewa Daddy ta bar gidan su ta nausa wani wajen da bazaa gan ta
ba, don ta san halin aminiyar ta sarai ba tun yau ba, bata saba in tana son abu ko
ta saka kanta abu a hana ta ta karfi ba, tunda ta taso ya riga ya saba da yi mata
komai take so komai tsaurin sa, shi yasa yanzu Daddyn ke shan wahalar ta da ya zo
yana son tankwara ta ta karfi, bayan tun tasowar ta ba haka ya sabar mata ba.
Sun yi sallama da Mukhy a kan in ya sauka a Bauchi goben zai kira ta, ta bashi
lambar wayar ta, har rokon sa ta yi da kada ya kama hotel in ya iso, tace akwai
gidan saukar baki a nan cikin gidan su, tunda dole sai sun kara kwana a Bauchi kan
su wuce Lagos din.
Bayan sun gama wayada Hamidah ya gayawa Alhaji ashe wajen kawar ta ta tafi a
Bauchi. Nan dai hankalin su ya kwanta suka soma shirin komawa Katsina washegari.
Baba Idi ya ce wallahi idon sa idon Amani sai ya zane ta.
Sai da suka tsaya a Funtuwa Sahura ta yi sallama da yayanta ta dauki kayan ta
sannan suka wuce Katsina, har da Kamilu, wanda Mukhtar ya ce ya dinga kula da
Alhaji har ya dawo tunda zai yi tafiya gobe. Duk irin kulawar da yake masa ya
nunawa Kamilu, ta ci da sha da shan magani da tsaftace masa jikin sa, kuma Kamilu
yayi alkawarin kwatantawa.
Alhaji ya sa Rakiya ta kai Sahura dakin Haj. Rabi ya ce ta zauna a nan, Kamilu
ma aka bashi daki a cikin gidan daura da na Alhaji. Mukhtar ya gaya masa sai ya
dawo daga tafiyar da zaiyi zai kai su kamfani da Boutique din Amani, in yaso su
zabi in da zasu yi aiki tsakanin shop da kamfani. Sauran kannen na kamilu da Alhaji
ya baiwa aiki ba a gidan sa zasu zauna ba, duk ya basu gidan zama ne can kusa da
kamfani. Kamilu ne kawai zai zauna da su saboda kula da Alhaji da tafiyar da Mukhy
zai yi wadda shi kan sa bai san tsayin kwanaki nawa zata dauke su ba shi da Amani,
idan har ta yarda sun tafi taren kenan. Sai ko Baba Sahura da dake dakin Haj. Rabi.
Su kenan a gidan sai Rakiya mai girki. Da maigadi Malam Tajuddeen da sauran
maaikatan waje
Sai dai Mukhtar ya san mawuyaci ne duk bacin ran da Amani take ciki, da halin
kuncin da ta saka kan ta a ciki na babu gaira babu dalili sai kiyayyar auren sa a
ce mata ga ido tace doyi yake. Wato bazata iya tankwabe zuwa gun Innar ta ba,
iyakaci in aka je din ta ce ba zata dawo ba, ya riga ya san hakan ce zata faru,
kuma ya shiryawa hakan.
Karfe sha biyu na ranar washegari Mukhtar Diffa ya sauka a filin jirgin saman
Sir Abubakar Tafawa Balewa. Sanye yake da farar shadda kal Wagambari babbar, ya aza
hula zanna bukar a kan sa mai ruwan kasa-kasa ta zauna daram a cikin tarin sumar
kan sa, kamar yadda takalmin kafar sa na fata kirar Italy shima ruwan kasar ne,
haka fatar agogon rolex da ke daure a damtsen hannun sa na hagu wanda bakin
lallausar gashi ya kwanta a hannun itama brown ce. Yana takun sa cikin nutsuwa da
haiba yadda ya saba yana tura matsakaiciyar jakar matafiya. Hamidah da kan ta ta
tuko motar ta ta zo daukar sa, ta baro Amani ta shiga wanka bayan ta tashi barci ta
more ta sau nutsuwa. Ba yadda Hamida bata yi da ita kan ta karya kumallo ba amma
Amani ta ki, ta ce daga ranar yau ta daina cin komai, ta daina shan komai, ta fi
son yunwa ta yi mata illar da har har sai ta mutu, in ya so Hamidah ta kai wa
Mukhtar da Alhaji gawar ta, tunda Hamidan ta ce abinda suka yi mata din ba laifi
bane, kauna ce.
Hamida sai ta kada kai ta fita tana dan murmushi.
Har falon Haj. Muna Hamida ta yi wa Mukhtar iso, ta gaya mata angon Amani
kenan. Jiya aka daura auren, shine Amani ta taho basu sani ba. Yanzu Daddy ya ce
Mukhtar ya zo ya tafi da ita zasu wuce wajen Maman ta a Freetown.
Haj. Muna tace ikon Allah, masha Allah tabarakarrahman, dalilin tahowar ta a
motar haya babu sanin ku ranar daurin auren ta nake son sani, ko bata son auren ne
da wannan miji sardidi haka son kowa?
Kunya ta kama Mukhtar ya kara dukar da kai kasa. Shi kansa yasan Allah ya
kyautata halittar sa ko mutane basu fad aba, amma baya so ana fada sai yaji wani
iri, Hajiya ta cigaba da fada tana cewa.
Da sabon aure haka a kan ta tayi wannan kasassabar, tahowa har Bauchi babu
iznin mijin ko na Baban ta? Maza kirawo min Amanin, in wanke ta tatas, haka ta zo
tana langabe min jiya kamar mutuniyar kirkin da ke cikin matsala, ashe ashe gudun
nata na aure ne.
Hamida da Mukhtar babu wanda ya tanka, amma sun ji dadi da Hajiya zata wanke
musu Amani wankin babban bargo, illa yayi kasa da kan sa da ke duke yana danna
wayar hannun sa. Zaune yake bisa kilishi kafafun sa a tankwashe, yana fuskantar
Haj. Muna, wadda ke kan kujera tana masa nasihar yayi hakuri da Amani irin hakurin
da zai yi da kanwar sa, kasancewar bata tashi tare da mahaifiya ba wani abun sai
ana mata uzurin sa. Don dabiun ta ba irin na wadanda suka tashi da uwa da dangi
bane. Goyon namiji ce.
Shi kam Mukhtar har ya gaji da cewa da ake yayi hakuri da Amani, wai wane irin
hakuri? Ita tafi kowa shafuwa da mai ko yaya ne? A wurin sa ai saidai duk su yi
hakuri da juna don shima ba kanwar lasa bane, in ta so a zauna lafiya a zauna, in
ta zabi tsiya a tsiyace, shi duk wanda ta zaba daidai ne a gun sa. Babu diya macen
da zata daga masa hankali, don in dubu yake so a rana zai samu, bai yi raayi bane.
Koko ya ce lokaci bai zo ba.
Amani yana jin ta da matsayi na dabam ne saboda karamcin mahaifin ta gareshi da
irin kauna da yardar da ya yi masa, da tausayin halin da yake ciki na rashin
lafiya, sannan kuma yana da son rama alkhairi da alkhairi.
Ba don haka ba Amani ta yi kadan ta wahalar da shi irin haka, ko ta saka shi
yawon da bai shirya ba irin haka, yana bin ta gari-gari kamar wani jelan ta.
Yana cikin wannan mitar a ran sa ya ji kamshin turaren Amani a falon.
Ko kusa bata kawo a ran ta wanda ke duke gaban Haj. Muna Mukhtar ne ba, ta ina
ma zata yi tunanin ya san inda take? Ko ya sani tunanin ta bai taba bata zai iya
ajiye girman kan sa ya biyo ta har nan ba, balle kuma tayi tunanin Balewa zata iya
tona mata asiri ta fadawa Mukhy tana gidan su a Bauchi.
Har ta zauna a kujerar da ke fuskantar Hajiya bata gane Mukhtar ba, sabida
keyar sa ce kawai a duke, duk da hasken fatar sa daban ne dana mutane da ke saurin
fallasa shi hankalin ta bai kai kan sa ba, watakila kuma don bata taba kawowa ran
ta ganin nasa anan bane.
Mukhtar ya dago fusatattun idanun sa ya dubi Amani da su a lokacin da take zama
a kujerar kusa da shi, bayan ga Hajiyar ma na kan kujera, wato rashin tarbiyyar
nata a koina ma yin sa take yi har a bakon wuri, tunda dai gashi tana ganin daga
shi har Hamida sun zauna a kan carpet Haj. Ce kadai a kan kujera amma ta dare kan
kujera tana fuskantar Haj. Muna.
Haj. Gani, Balewa tace kina kira na.
Haj. Muna ta jefa mata harara sannan ta dunkule hannu ta mika mata ta ce ungo
naki (dakuwa) sannan ta nuna mata Mukhy da ke zaune yana hararar ta shima wata irin
sassanyar harara.
Ga mai kiran naki nan, ba ni bace, dauko mayafin ki kafin in kyafta ido na,
sawun ki a likkafa ki bi shi duk inda ya sanya kafa bisa umarnin mahaifin ki, ina
maki kallon mai wayo ashe Amani sakarai ce ke? Ki sa kafa ki taho ke kadai tun daga
Faskari ba da iznin mijin ki da sanin mahaifin ki ba? Shin kina son albarka Amani
ko kuwa kin fi mahaifin ki sanin abinda yake daidai a gare ki?
Sai a lokacin Amani ta gane Mukhtar ne, da kuma ainahin fadan da Hajiya ke yi.
A firgice ta juya ta kalle shi suka kuma hada ido, saura kadan fitsari ya kwace
mata da irin zazzafan kallon da Mukhtar ke mata. Hankalin ta in ya yi dubu to ya
tashi tsaye, nan take ta hau yi wa Haj. Kuka mara sauti tana fadin Hajiya ki yi
hakuri ni ba zan koma Katsina ba, idan kin kore ni ma gaba zan nausa Hajiya tace ki
wuce birnin Sin, amma tare da mijin ki ba da ni ba, maza Hamidah dauko mata kayan
ta kisa a bude musu guest house yanzu, su kwana gobe sai su yi sammako tunda dare
ya riga yayi yanzu.
Amani ta wuce dakin Hamida tana kuka wiwi tana tattara kayan ta. Hamidah ta
shigo dakin tana fadin da gaske Sahibah ba wanda ya isa ya gaya miki ki ji? Na
dauka Hajiya ta matsayin uwa take a gare ki, ta dauka zata yi miki fada ki ji ko ba
kya so, tunda tace ki bi shi sai ki bi shi, baki san alherin da ya zo miki da shi
ba.
Nan ta gaya mata cewa Mukhtar ya zo ne don ya kai ta Sierra Leone.
Amani tayi tsit! Kamar ruwa ya cinye ta, jikin ta yayi dan sanyi, da gaske yake
ko kuwa yaudara ce don ta yarda ta bi shin? Me ya hana tun lokacin da yayi mata
alkawarin ya cika? Sai yanzu da ta zama matar sa da bata da iko da kan ta?
Hamida ta shiga lallashin ta, tana cewa ki bashi dama Sahibah, hes a very
serious person babu batun wasa a abinda ya gayawa Mama, da gaske Sierra Leone zai
kai ki.
Amani ta rage kukan ta ce Hamida, idan da amana bazaki gaya masa inda nake ba,
daga yau na san ajin da zan ajiye ki, ya kamata tuntuni in fahimci kema kina yin
mutumin nan, in ba ke ba babu wanda zai gaya masa inda nake.
Hamida ta soma kokarin kare kan ta da cewa wallahi tausayi Daddyn ki ke bani
Amani..bashi da lafiya kuma yana cikin damuwar inda kika shiga ni bana baki tausayi
ko? Ni da a ka yi wa auren dole da wannan green snake din? Hamida ta ce wato
sunayen nasa kala-kala ne har haka, shine Dirty Human Being yanzu kuma shi ne Green
Snake, sannan Sumumu-kasau, duk shi kadai bawan Allah!
Tsaki Amani tayi tace in dai Bauchi ce yau zan bar miki kayan ku, zan shiga
duniya tunda hakan kike so, ba zaki bani refuge daga auren dole ba. Hamida ta yi
murmushi tace don Allah Mama ta ce in kin tashi shiga duniyar ki wuce har bangon ta
(birnin Sin).
Suna wannan cece-kuce din Hajiya Muna ta shigo dakin, don ta ga Amani ta bi
umarnin ta ko aah, mai aikin ta biye da ita dauke da fakadeden tray da ake jera
abinci da abin sha a kai, ta ce,
Amani ga nan abinci dauki ki kai masa da kan ki, Hamida ki raka ta masaukin
bakin, na sa Ali ya raka shi tun dazu.
Hamida ta ce da mai aikin ta wuce gaba ta kai masa abincin zasu zo yanzu. Ta
dauka Amani zata bi umarnin Hajiyar ta, amma ga mamakin ta Hajiya na bada baya
Amani ta yi rantsuwa ba inda zata je, in kuma Hamida ta takura mata sai ta fita to
kuwa ta fita kenan har abada itada sake zuwa inda Hamida take.
Hamida ta dauka wasa take yi, amma sai ta ga ta rantse ta kara rantsewa kan
cewa bazata kwana inda Mukhtar yake ba, har ta ce saboda daurewa karya gindi sai ki
sauke shi a gidan nan? Koda yake dama ai ke kika gayyato shi, don haka sai ki
karasa ladan ki ki kai masa abinci. Ki kuma kwana kina taya shi hira.
Hamida ta rasa yadda zata yi da Amani, ta tabbata wajen taurin kai da kafiya
babu na biyun ta duk fadin garin su Faskari tabbas ta Faskari kowa, sannan a
tarbiyyar da aka yi mata baa koya mata bin umarnin na gaba ba, sai dai ita tayi wa
wani umarnin.
Hamida zata soma yi mata waazi ta mike ta hau hada kayan ta ta soma kuka a
haukace, fadi take in dai don na zabi yin mafaka a wajen ki ne kika tona min asiri
haka bari in tafi gidan karuwai cikin daren nan, in kika takura sai na je inda
yake.
Hamida ta rike jakar kayan nata ta ce na kyale ki Amani, ba zan kara takura ki
zuwa guest house ba, amma kin manta ya ce wajen Maman ki ya zo ya kai ki? Ta ce don
wannan na yarda zan bi shi, ai zaman jirgi ne kuma babu transit, daga nan Bauchi
kai tsaye a hau jirgin da zai je Freetown, inba haka ba na hakura, wallahi bana ko
son ganinsa Hamida. Hamida ta hadiye dariya, ta soma mayar mata da kayan da take
kwasowa cikin jakar ta, tace kada ki manta hausawa dai sun ce komai wayon
amarya.?!.
Hararar da Amani tayi mata kamar idanunta zasu fado kasa tasa ta ficewa daga
dakin da sauri tana cigaba da tillika dariya. Masaukin Mukhtar din ta nufa, so take
ta ji yaya tafiyar tasu zata kasance goben, tunda ta gane transit ne Amani bata so
a yi a koina, bata kuma jin akwai jirgin Freetown daga Bauchi dole sai daga manyan
birane wato Abuja ko Lagos.
Hamidah tayi sallama a kofar guest room, daga ciki Mukhy ya amsa, bai kuma
taso ya bude ba amma don ya ji muryar Hamida ne, a hankali ta ce Hamida ce, zan iya
shigowa? Sannan ne ya taso ya bude, kallo daya Hamida tayi masa cikin kayan barci
na DKNY ta ji zuciyar ta ta tsinke, sannnan ta doka da karfi, a zuciyar ta ta shiga
neman tsari daga sharrin zuciya dana shaidan masu gaya mata tace da shi, ya kyale
Amanin da ta tabbatar bata kaunar sa ita ya zo gare ta. Ta yi maza ta yi taawizi ta
nemi tsarin Allah daga sharrin zuciya dana cin amana, ta bi bayan Mukhtar zuwa
cikin falo, suka zauna a kujerun da ke fuskantar juna a falon, har ya yi wanka ya
canza shaddar jikin sa zuwa shirt da wando marasa kauri blue samfurin DKNY. Yana
shirin taje sumar nan tasa da ta jike jagab da ruwa ta mammanne a saman fatar wuyan
sa, da alama bai kai ga taje ta ba, fitowar sa kenan daga wanka Hamida ta kwankwasa
masa kofar.
Kamshin kakkarfan turaren sa na Azzaro Visit da ya fesa yanzu-yanzu, ya mamaye
dakin, ya cakude da sanyin air conditioner ya bada wani atmosphere mai dadi a falon
da sanyaya zuciyar duk wanda ya shake shi.
Hamida ta russuna ta gaida Mukhy with much respect, kwarjinin sa na kara rikita
nutsuwar da ta shigo da ita. Shikuwa ya kara daure fuskar nan tamau kamar yadda
take as usual. Duk sai ta kara firgicewa, ga kwarjinin sa ya mamaye dakin. Yarinyar
bata yi kama da masu kawo shirme ba amma me zata gaya masa da zata biyo shi har
inda suka sauke shi a irin wannan lokacin?
Da karfin sunan Allah a bakin ta Hamida ta samu nutsuwa ta ture duk abubuwan da
shaidan ke kissima mata, ta ce.
By the way, ni ce Hamidah Balewa, ni kawar ta ce tun muna secondary school.
Mukhtar yace I can relate, tunda har zata iya gudowa wajen ki har nan tun daga
Faskari ba da izni na ko na Alhaji ba. Ya fada da dan fusata a muryar sa, na ganin
ta ita kadai ba tare da Amani ba,

Please Login or Register in order to submit comment