Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda kai tsaye ba sai an gaya masa ba ya gane
bazata zo su yi magana akan tafiyar su ta gobe ba.
Hamidah ta karya murya tana fadin, ka yi hakuri Mr. Mukhtar, Amani sai a
hankali, ina so in san tsarin tafiyar taku ne ta goben in mata bayani, don nayi
kokari mu taho tare yanzu ta ki.
Da fusata sosai ya ce then bani da say da ita, in har bazata zo da kan ta ba,
in baza ta je bama ni zan koma Katsina gobe, amma ki tabbatar mata kafata kafar ta,
bisa umarnnin Alhaji.
Hamida ta ce in sha Allahu ma zata je, ai tafi kowa son ganin Maman nata.
Mukhtar yace matsalar ku ce wannan, zuwan ko rashin sa, bani da asara a ciki, ki
dai gaya mata in bazata je Sierra Leone din ba ta sanar da ni a daren yau ta waya,
don in saki booking din, in kuma zata je shima ina son sani don in san ina muka
nufa goben daga nan. Ta bani amsa ta waya ya wadatar.
Zan jirata har karfe tara na safe, don booking din mu zuwa Lagos 12 na rana
ne, daga can ne zamu hau jirgin Freetown, babu jirgi mai zuwa Sierra Leone anan
Bauchi.
Hamida ta ce a ranta transit dole Sahibah! Allah ya fishsheki daga fushin
wannan Zakin.

Ta dawo dakin su shi kuma ya rufe masaukin nasa ya kwanta. Ya dauki wayar sa ya
kira Alhaji, Kamilu ne ya dauka suka gaisa ya tambaye shi ya hanya, ya gaya masa ya
isa lafiya, sannan ya hada shi da Alhajin, ya gaya masa ya sauka a Bauchi lafiya,
kawar tata Hamidah da iyayen ta mutanen kirki ne, don a gidan su ma suka bashi
masauki, sun roke shi kada ya sauka a hotel.
Alhaji ya ce ai tuntuni na san Hamida mutuniyar kirki ce ba irin Tafisu ba,
shi yasa na ke son abotar tasu, da mutum yana shirya mutum da tuni Hamida ta gyara
min halin Amani, to abotar tasu ba irin wadda ake kira ta abokin barawo- barawo
bace.
Sun dade suna tattaunawa, Mukhtar ya gayawa Alhaji dole sai sun kwana a Lagos
kafin washegari da asubah su bi jirgin Freetown. Alhaji yace ta dai yarda zata je
din ko? Mukhtar ya nisa, kafin a hankali ya ce Alhaji maganar yarda ta je ko
rashin yardar ta duk basu taso ba, abu ne dana sani ba abinda take so kuma take
buri a yanzu sama da ganin Innar tata, don haka zata bi ni ne ko bata so, donmai
binciken nata dan damfara ne kawai, alkawari ne na yi mata kuma dole in cika shi,
zan damkata gun mahaifiyar ta in yaso in ta ga dama don Allah kada ta biyo ni mu
dawo.
Ni ba a matse nake ba!.
Kunya ta kama Alhaji, sai ya hau Mukhtar da fada, na tambaye ka wannan?
Kullum ana gaya maka ka koyi lallashin mace kana kara fandarewa Mukhy, ina gaya
maka wannan ne (based on experience), da a ce na lallashi Jalan, na bi ta a
hankali, na yi hakuri da ita da shirmen ta na rashin so na, ban kuma yi zuciya ba
na saketa a asibiti wai don tana ikirarin bata so na, da na jure da har yanzu muna
tare bamu rabu ba. Da Allah kadai ya san yawan yayan mu tare.
Yau ga shi na tsufa da soyayya a kasan rai na ina ta nadama, don duk matar dana
aura na rantse maka a bayan Jalan take, kuma na kasa son ko dayan su irin son da
nake ma Jalan.
Matar fari ka tattalata Mukhy, domin bazaka samu kamar ta ba, daban Allah yake
bamu su.
Abinda ya dade bai yi ba shi ya yi yanzun wato murmushi, yace a ran sa wato
Alhaji bai sha da dadi ba a hannun soyayya shi yasa yake ji masa tsoro. Shi kam ai
mata a kasar su sai wadanda ya zaba in ya so, mata kamar hurul eeni ma, wadanda
suka fi Amani komai. Ita Amani ta ladan noma ce, kyautar ubangidan sa da ba zai iya
cewa baya so ba, ta ja zaren ta yadda take so in ta gama jan nata lokaci zai zo da
shima zai ja nasa watarana.
Haka ya kwana da sake-saken abin a ran sa. Na irin yadda zai aro kalmar hakurin
nan da kowa yake jaddada masa ya rataya a wuyan sa a kan Amani. Tunda ta zama dolen
da ba zai iya kaskantawa ba. Da asubah ya ga sakon ta a wayar sa, da sunan da yayi
saving no. dinta da shi watau AUF (AMANI Usman Faskari) mai nuna ta amince zata bi
shi Saliyo. A gajarce ga abinda Amani ta ce da mijin ta Mukhtar, ba tareda ta kara
komai a kai ba.
Yes, Im going!.
Ya dan sakawa sakon nata ido yana nazarin sa, wato bazata ko ce masa yaya ya
kwana ba, balle ya gajiyar hanya, wai miji a kewa magana haka gatsau cikin gadara,
shi ina ya san mace na ma miji magana a haka? A inda ya taso sujjada ce kadai mace
bata ma mijin ta saboda respect, soyayya, kulawa da kankan da kai.
Mukhtar ya dan kyabe baki a fili yace.
Kada ma Allah ya sa ki je!.
Yayi alwallah ya fita zuwa masallacin gidan wanda Baban Hamida ya gina like
da gidan sa.
Hamida da Amani kwanan zaune suka yi Hamida na gaya mata sai ta yi a hankali da
Mukhtar Diffa, domin maza irin sa wuyar shaani ne da su, in ba ta yi wasa ba ita
zata dawo tana cin kwakwa a hannun sa, tace Mukhtar dinnan mutum ne har mutum,
wanda ya gama sanin ciwon kan sa, ya san daraja da mutuncin kan sa bana jin zai
dauki halayen ki Amani, babu alamun wasa a tare dashi ko sakin fuskar da mace zata
raina masa hankali irin yadda kike yi.
Imagine ko sannu da zuwa babu, ko gaisuwa balle ya hanya, abinci wannan kin ki
dauka ki kai masa haba Amani! Miji duk lalacewar sa sunan sa miji balle irin naki
Amani wanda kyautar Allah ne a gareki kuma zabin mahaifin ki.
Me zai hana ki kwantar da hankalin ki ku yi zaman ku lafiya ki yi tunanin
hanyoyin mallake abin ki?
Amani ta girgiza kai cikin takaicin Hamidah, tace wai sau nawa zan gaya miki
bazan taba son mutumin nan ba? Ko da shine Hurul eenin maza bakidaya? Ni na kirawo
shi da zan masa ya gajiyar hanya? Ke da kika kirawo shi ba kin masa ba ina ce ya
wadatar? Yaron Baban nawa zan je ina ma ya gajiyar hanya? Na ce miki na shirya
zaman aure da shi ne da kike min wani fatan hanyoyin mallakar sa?
Ta yaya mutum yana aiki a karkashin iko na kuma a aura min shi? Ba don komai
Daddy ya yi haka ba sai don ya bashi lasisin cigaba da wulakanta ni, tunda tun kan
in zama karkashin sa ma yana yi min duk wani launi na wulakanci da kaskaci ga fadin
rai kamar firauna.
Na fahimci ko me zan gaya miki hujjata ta rashin kaunar Smart Ass, Bad Egg din
nan ba zaki bani goyon baya ba Habeebty, saboda kema ya asirce ki.
Hamida abun na Amani ya daina bata haushi yanzu don ta koma bata tausayi, tana
hango mata in ta bari tayi asarar Mukhtar bazata samu makwafinsa ba, wajen sanin
darajar iyayen ta, ba wai bazata samu miji ba tunda itama banda halayen ta bata da
makusa, ta yarda duk abinda take fada bilhakki take fadar sa daga kasan zuciyar ta
da gaske bata son nasa, ta sha wahala wajen lallashin Amani kan ta yi masa text
tace zata je Saliyo din.
Don Amani cewa tayi ba zata masa wani text ba dan rainin wayo kawai. Sai da
Hamida tace zata je a daren ta gayawa Hajiya Muna cewa ko abinci data ce ta kai
masa bata kai ba. Ta ce kuma wallahi in Hajiya ta ji haka a daren nan zata tasa
keyar ki dakin sa, in ya so ki je ki masa dibar albarkar a kunnen sa.
Sannan ne fa ta typer masa Yes, Im going din. Don ta san Hamidah zata aikata.
Ita kuma bata san meyasa ba duk tsiyar tata da tijarar tata tun da Kawu yace an
daura auren su ta ji kalmar ta yi mata girma a rai, aure fa! Ba karamin alaqa ne
aka kulla tsakanin su ta har abada ba, ji take bazata iya kara hada ido da shi ba
balle kuma zuwa inda yake shi kadai ba tare da kowa a tare da su ba.
Yadda Mukhtar ya kwana sake-sake a kan Amani da halayen ta, da yadda zai jure
ma zama da ita matsayin matar sa uwar yayan sa haka itama Amani ta kwana nata sake-
saken, sai dai nata sabanin nasa ne domin kuwa kwana ta yi tana saka hanyar da zata
bi ta kubutar da kan ta daga auren sa. A haka garin Allah ya waye musu
Tun asubah tayi wanka sakamakon wani irin doki da ke cin ran ta na son haduwa
da mahaifiyar ta. Ta zuba doguwar riga mai fadi na wani tattausan cotton lace ruwan
goro da aka yiwa dinki babban riga Senegalese, ta kawo wani dan mayafi cantitly
kamar abin tatar koko ta yafa a kafadar ta exactly yadda ta ke shigar ta a can
baya. Amma yau bata shafa lip stick ba ko powder bata shafa ba. Man shafawar ta
kawai ta shafa wato Elizabeth Arden Lotion. Sai ta hau hada kayan ta a trolley
dinta.
Sai lokacin Hamidah ta farka ta gan ta ta saka jaka a gaba cikin tunani, ba
komai take tunanin ba kuma sai yadda zata yi tafiya mai nisa irin haka tare da
Mukhtar Diffa. Farin Baabzinen nan da ya zo rayuwar ta rana daya ya rikita duniyar
ta. Ya canzata ya hautsina ta, ina ta taba kawowa kan ta aure nan kusa, ban da
kutsowar Mukhtar Diffa cikin rayuwar su mai tsafta ita da mahaifin ta???
Amani ta ji hawaye sun kawo wa idon ta cafka, aure na nufin karewar kuruciyar
ta kenan fa. Auren na nufin ita da Mukhy daga yanzu sun zama abu guda! Ya ilahy!
Ina zata kai wannan kayan bakin cikin da Daddy ya kunsa mata? Ai abu daya zata yi
kawai ta huce shine ta yi hakuri ta jure ta gan ta gaban Innar ta, daga nan kuwa
saidai a yi wani labarin ba dai nata da Mukhtar ba. Abun nufi, yanzu kam ta ajiye
duk wasu makaman yakin ta don ta samu ya dangana ta da Innar ta, daga nan kuwa ko
sama da kasa zata taru a kan ta ba zata dawo ba, tunda Daddy ya daina son ta.
Hamida ta tashi zaune ta gan ta ta hada kai da guiwa tana rafzar kuka har da
sheshsheka, kewar Baban ta take tun kafin ta bar shi, amma ta zabi ta bar shin,
tunda shima ya zabi Mukhtar tsintacce a kan ta.
A ran Hamida cewa ta yi Sahibah! Dadi ne yayi mata yawa". A fili kuma sai ta
tambayeta shin kin yi sallah ne da kika ci wanka da asubahin fari? Sai a lokacin ta
tuna bata yi sallar ba. Ta mike ta shiga bayi don yin alwallah.
Wajen karfe takwas nasafe Haj Muna tasa aka kaima Mukhtar karin kumallo, sannan
ta shigo dakin nasu hannun ta rike da katuwar leda, ta gan su tsaf da su duk sun
shirya don Hamidah tana so ta raka su har airport, Haj Muna ta zauna a bakin gadon
Hamidah da suke zaune kowacce hankalin ta na kan wayar ta, don hira ta ki dadi
tsakanin su, tun sanda Hamidah tace ta yi kwalliya ta gyara idon ta da ya kode
Amani ta fusata kwarai. Ta ce kada ta saka mata ido, ita ina ruwan ta da wani
Mukhtar da zata yi kwalliya domin sa? Sai Hamidah ma ran ta ya sosu, ta ce Sahibah!
Kiyi duk abinda kike so in sha Allah ba zan kara yi miki nasiha ba.
Shikenan duk suka zama kurame a dakin kowacce ta ki kara kula yar uwar ta har
zuwa shigowar Haj. Muna. Ta zaune gefen Amani sannan ta shiga fiddo kayayyakin dake
cikin ledar data shigo da ita, tana yi ma Amani bayanin yadda zata ke shan
magungunan da ke ciki, Haj. Muna tace,
ya ta Amani, sai an gwada akan san na kwarai, ni na gaya miki da kudin ki zaki
zo neman kari, kin gan su tafiyayyu ne tun daga Nijar na yo odar su don amfanin kai
na. Wannan Uwa ce kawai zata iya baki su, yanzu nake so ki sha kowanne a gaba na
sannan ki daure sauran ki wuce da su.
Amani tayi sakatoto! Tana kallon Hajiyar da kayan hannun ta, kafin ta ce
innocently Hajiya maganin menene? Ni ai lafiya ta kalau, Sahibah ce take bata min
rai, shine kika ganni kamar mara lafiya Hajiya ta ce na sani Amani lafiyar ki
kalau, bahaushe kuma ya ce "in kana da kyau ka kara da wanka".
Dalili na anan shine. Na hango miki wani irin miji mai babban alamari irin
wadanda ke wahalar da matayen su a dalilin tarin baiwarwakin da Allah yayi musu.
Mijin ki ga dukkan alamu babban mutum ne, mai tarin ilhama, ban ga ta inda zaki
samu kan sa ba sai ta wannan hanyar kadai, don baki da wayo da kissa da su kisisina
irin na yaya mata sai dolanci. To cigaba da dolancin ki, amma ki kama shi ta nan ta
nuna can kasan Amani.
Hamida bata san sanda dariya ta kubuce mata ba don ta lura Amani kallon Haj.
Muna kawai take tana cewa toh! amma kwata-kwata bata san inda zantukan Hajiyar suka
dosa ba, ta dai karba ta aje ta kuma yi godiya. Amma ta ce ba zata iya cin komai a
ciki ba yanzu sabida tana jin yunwa.
Hajiyata sa aka kawo musu abinci suka karya amma Hajiyar na fita ta tattara
magungunan ta mayar a ledar su. Ta cewa Hamidah "in kin gama dariyar muguntar taki
sai ki je ki gaya masa na shirya. Hamida ta ce ga yar aiken ki ko? To da mecece?
Hamida sai ta dauki wayar Amani ta danna ma Mukhtar kira ta na cewa ki ji tsoron
Allah Amani, mijin naki ne Dirty Human Being? Smart Ass, Bad Egg. Ai ko karen gidan
ku bakya kira da wadannan sunan ba balle mutum dan adam.
Ita dai bata ce komai ba amma ta sa a ranta zata canza sunan koda ba da wani
sunan mai maana ba, amma dai zata canza wannan din, ganin yadda Hamidah ke Magana a
kai kamar zata yi kuka. Hakan yasa ta tabbatar bata son sunan ga Mukhtar. Ko yaya
ne tana ragawa Hamidah saboda duk tijararta ta san Hamida Balewa mai kaunar ta ce.
Mukhtar na cikin sanya links din hannun rigar da ya sanya ta ash colour getzner
ya ga AUF na kiran sa, dauke kai yayi kamar kada ya daga don ya san arziki ba zai
sa Amani kiran sa ba. Abu daya yasa shi amsawa ganin lokacin tafiyar su filin jirgi
yayi. Don haka ya amsa, amma ba tare da ya ce uffan ba. Sai ya ji Hamidah ce, ta ce
sun gama shiryawa kuma direba yana bakin entrance na masaukin sa da mota bakar land
cruiser zasu raka su har filin jirgi.
Mukhtar sai ya samu kan sa da cewa Hamidah madallah da karamcin ki. Madallah da
kawa irin ki. Allah ya baki miji na gari kema.
Ki yi min godiya wajen Hajiya mun gode sosai, da zumunci, Alhaji ya ce a yi
muku godiya".
Zuciyar Hamidah ta cika da jin dadin wadannan kalamai na Mukhtar, sai ta ji
wani karfin guiwa ya shige ta na son kara taimakawa aminiyar ta ta zauna da wannan
mutum da babu wada ya taba shiga ran ta kamar sa. Hakika Mukhtar Diffa, yana da
charisma ta farin jini a duk inda ya shiga, ba ga manya ba ba ga yara ba. Duk wanda
wata kankanuwar muamala ta hada shi da shi sai ya so shi, ya kuma bar shi da begen
son cigaba da alaqa da shi idan ya bar wajen.
Har dakin Hajiya Muna Hamida ta raka Amani ta yi mata sallama daga nan suka
wuce maadanar motocin gidan. Tana janye da jakar Amani.
Tuni Mukhtar direban ya bude masa mota ya shiga gidan gaba ya zauna yana jiran
fitowar su, yana yi yana duba agogon fatar dake daure damtsen hannun sa samfurin
RADO. Da suka karaso ta cikin farin glasses din da ke idon sa wanda ya makala shi
saman dogon karan hancin sa ya hango Amani tana tahowa, da gantalallen mayafin da
ta yafa, tafiyar nan tata kamar ta macen Dawisu bai canza ba, duk da cewa zuciyar
ta da kamannin ta sun canza zuwa na bacin rai zallah. A hakan kuma sai tayi wani
irin kyau ba dan kadan ba. amma mayafin da ta yafa wanda saman kirjin ta kawai ya
lullube ya bakanta masa rai. Haka ya shanye abin a ran sa albarkacin direba da
Hamidah. Suka shiga baya su biyun ita da Hamidah direba ya saka jakar kayan ta a
boot kusa da jakar Mukhtar, sannan ya shiga mazaunin sa ya ja motar suka fita daga
gidan su Hamidah.
Sai da suka hau kwalta sosai Hamidah ta gaida Mukhtar, kamar ba zai amsa ba sai
kuma ya amsa din, har ya ce mata "yaya fama da bakuwa?" Sai ta yi murmushi ta ce ai
na saba da wannan bakuwar tawa mai rigima, mai giggiwa. Ta mudubin motar Amani da
Mukhtar suka hada ido unexpectedly ta sakar masa harara, bai yi kasa a guiwa ba
wajen maida mata da wadda tafi tata zafi. Ya kuma maida kan sa bisa titi.
Hamida tace don Allah Mr. Mukhtar da kun sauka ku kira ni in tabbbatar kun
sauka lafiya. Ya ce "in sha Allah". Duk Amani na jin su, amma ko kallon su bata
kara yi ba. Sai haushin Hamidah da ya kara cika ta.
Sun tarar jirgin da zasu hau zuwa Lagos har ya kusa gama lodi, don haka a
gurguje suka yi sallama da Hamidah ta bashi jakar Amani a hannun sa, ya hada da
tashi yana turawa Amani na bin shi a baya, yana cewa a ran sa yau shi Mukhtar ne da
dakon kaya, Alhaji ya ce yayi komai don ya lallaba ta, amma kuwa dakon kaya ai is
frustrating, musamman ga namiji kamar sa, to amma ita yanzu din iyalin sa ce.
Annabi SAW kuma yayi umarni da a tausayawa mata, dattijai da kananan yara, a agaza
musu. But duk da haka yaji abin weird a gare shi.
Seat din shi a cikin jirgin kusa da nata ne, tana daga jikin taga a takure yana
gefen ta. Amani tana ji ana a daura belt jirgi zai tashi amma taki daurawa. Ba don
tana da burin ganin Innar ta ba, kafin Allah ya dau ran ta da ta roki Allah jirgin
ya fado duk su mace da dai ta zauna da shi har abada a matsayin mijin ta uban yayan
ta.
Jirgin Max Air ya daga da su, Mukhtar sai ya saka hannu a bayan kwibin ta yana
fastening mata belt din, ko babu komai diyar Alhaji ce shi kuma servant din Alhaji
ne, don haka ba faduwa bane don ya hidimta mata a dalilin Alhaji Usman Faskari ne,
jirgin bai dire su a ko'ina ba cikin dan kankanin lokaci sa a birnin Ikko.
Da suka sauka shi ya dauko kayan su again suka fito daga terminal, mai taxi ya
zo gaban su yana tambayar ina zasu je? Mukhtar sai yace masa any nearest good
hotel. Amani bata ji ba, don a lokacin tana waya ne da Hamidah tana gaya mata gasu
a Ikko, amma bata ga an ce a tsaya a shiga jirgin Freetown ba, Hamida ta fashe da
dariya ta ce to kika sani ko jirgin yamma ne ko na dare? Ta ce,
bar zancen wasa Hamidah, kina gani fa ya tsayar da taxi, gidan wa zamu je?"
Hamidah ta kasa tsayar da dariyar ta ta ce "ki fidda ni a lamarin ki, tunda babu
arziki a ciki, naga alama baki san Annabi ya faku ba, ina laifinsa ya baro komai
nasa da ayyukan sa da Alhajin sa, don ya dangana ki da Maman ki?" Amani ta ce "to
ni na saka shi? Ban ce a bar ni a ga iyawa ta ba? ban ce a bar ni zan kai kaina ba?
Kuma in jirgin yamma ne zamu shiga ba waiting lounge zamu je mu zauna ba?
Hamidah ta ce.
"Ki tambaye shi mana da kan ki ina zaku je din? Me yasa zaa yi transit? Ni
Hamida ina nan Bauchi ina na san me kuke ciki ke da mijin ki a birnin Ikko?
Dole ta kyale Hamidah don daga karshe ma ta kashe wayar ta daga gama fadin
hakan hakan, bata so Mukhtar ya san da ita Amani take waya kada ya dauka ko da saka
hannun ta a rashin mutuncin da Amani ke yi masa, fatan ta Allah yasa wannan tafiya
ta zama silar shiryawar su da kuma sanadin alkhairori a cikin auren su. Already mai
taxi ya saka kayan su a bayan motar, ya budewa Mukhtar gidan baya ya shiga.
Hajiyar tsayawa tayi kikam tana jiran karin bayani na inda zaa je daga gare sa.
Amma bata ga alamar Mukhy na da niyyar yi mata bayanin komai ba, sai ma wata
muguwar harara da Mukhtar din ya sakar mata, wadda ita kan ta ma amsa ce na cewa ba
bayanin da zata samu daga bakin sa. Zata yi magana ya ce a fusace,
idan kika sake kika tambaye ni ina zamu je? Zan ce miki sayar da kan ki zan yi
a Ikko malama. Don kan naki zai yi tsada, kamar yadda kike yarinya mai tsada, na
tabbata zai isheni in ja jarin da zan yi kudi, in tashi daga matsayin yaron Baban
ki, ko kya daina raina ni.
Sakatoto ta yi da baki tana kallon sa. Kafin ta yi aune taji ya fizgi hannun ta
ya saka ta a bayan motar ya rufe. Shi kuma direba bai bata lokaci ba ya ja motar.
Hotel din dake manne da Lagos International Airport ya kaisu wa to Legend
Hotel. Mukhtar ya sallame shi da kudin da suka zarta abinda ya bukata, Amani ta
zauna na tsayin lokaci a cikin motar, ta kasa fitowa daga motar nan, kai ko
kwakkwaran motsi ta kasa, ta rasa inda zata saka kan ta ta ji dadi a wannan
lokacin. Sai wani irin kokawa take da numfashin ta saboda bakin ciki. Saboda (this
will be the first day) da zata kebe da namiji, kuma mai amsa sunan mijin ta a
muhalli guda, sannan wai a ce ba kowa bane mijin face MOUKHTAR DIFFA. Wani kwayan
mutum guda daya da duk duniya babu wanda ta ke wa kallon bai isa ba, kallon
abnormal human being, kuma matsala ga farin cikin ta irin sa. Ta tsani halayyar sa,
girman kan sa da charismatic personality din sa, ta raina shi kamar yadda ta raina
Karen kofar gidan su, tana ganin sa a ba komai ba, face yaron gidan su, mai
hidimtawa Alhajin ta don samun na abinci, wanda karfi da yaji ya kwace mata
mahaifi, ya shiga tsakanin soyayyar dake tsakanin ta da mahaifin ta, soyayya mai
asali da tushe wadda Alhaji ke yi mata.
Zuwan Mukhtar cikin rayuwar su ya canza wannan. Ya sauya rayuwar gidan su
gabadaya, ya sauya mata mahaifi da dabiun sa. A dalilin shi mutum ne mai
charismatic personality da duk inda yaje sai an so shi. Ta fahimci kamar ita kadai
ke kin Mukhy a duniyar subhana, kuma kamar shi din ya zame mata dole a yanzu, aure
ba wasa bane duk da bata da ilmin sa, abinda ta sani akan aure shine mijin da
igiyoyin auren

Please Login or Register in order to submit comment