Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da ita.
Ba da sanin Amani ba, Mukhtar ya ware ido tsab yana kallon ta, kallo sosai,
irin wanda bai taba yi mata kwatankwacin sa ba. Kamar mai karewa halittar ta
kallo, koda yake hakan ne, kallon kyautar da Alhaji yayi masa yake yi a nutse, a
zaune, a tsanake, kallon da ya san a yanzu yana da hurumin yin sa ba tare da
shamaki ba ko daukar zunibi ba.
Ji yayi wani abu mai kama da shaawa na sake darsuwa a cikin ran sa, sauri ya
yi mike ya bar wurin zuwa uwar dakin, ya haye gadon ya yi light off, ya kwanta,
rokon Allah ya ke kada ya baiwa zuciyar sa ikon abinda take son darsa masa a daren
yau, don bai shirya ba, itama kuma ya tabbata bazata taba yarda ba, bai san yana da
lafiyar mazantaka ba sai yau da ya kebe da Amani, amma ya gwammace har abada ya
dawwama cikin samartakar sa, da dai ace wani abu makamancin hakan ya hada shi da
Amani.

Wani irin wahalallen barci Mukhy ya yi, da bai taba yin irin sa a wahala da
tsayi a rayuwar sa ba, shi kadai ya san yadda zai fassara shi, da izayar da ya sha
a cikin sa a dalilin yana daki daya da Amani. Da irin tsayin da daren ya yi masa,
kafin a kira assalatu. Da asubahi tunda assalatun fari ya tashi yayi wankan da ya
tabbatar ya dada kama shi karo na biyu, ba tare da ya amfana da komai daga yar
mutanen Faskari ba.
He sighed! In the toilet, saying to himself this lady is dilemma to him.
Ya fito ya tada sallah, bayan ya idar ya soma hada kayan sa da ya fidda daga
jaka. Saida ya kammala tattare kayan sa da ya zo dasu ya fahimci Amani ta tashi ta
shiga wanka itama, don yana jiyo karar saukar ruwa a shower, ya fito falon ya zauna
a kujerar da ta tashi da jakar kayan sa a gaban sa yana hada mata nata shirgin
kafin ta fito, yanzun an yi saa ta canza kayan jikin ta, ta sanya wasu wankakkun
zani da riga na atampa super holland a jikin ta, wadanda da su ta shiga toilet din
a hannun ta, fuskar nan tayi fresh da santsin sabulu mai kamshi sai daukar ido
take.
Mukhtar ya juyar da kan sa wani gefen daban, ji da yayi wani ignition irin
wanda ya kwana cikin sa na tsunkulin sa, fatar bakin ta ta yi pink shar, tayi wani
irin sumul kamar kasa hannu ka latsa don kaji irin sulbin ta, tasirin kebantuwar
mace da miji a ranar farko ya cigaba da aiki a jikin sa yana waskewa da karfin hali
irin nasa..., wadannan pinky lips din nata kawai ya ji ya ke son sumbata, musamman
da ta sunkuya don daukar gyalen ta, ya hango abinda ya firgita shi ta cikin rigar
ta, tsaye suke kyam cikin brazier, wadanda ake kira masu gindin tasa, da sauri ya
kauda kan sa ya mike tsaye, saboda gabadaya ji yayi jikin sa na vibrating, yana
amsar sakon da kwakwalwar sa ke darsawa, at the same time, ya shiga neman agajin
Ubangiji a cikin ran sa, wani bakon alamari ne ya same shi again irin wanda ya
kwana cikin sa jiya, shine ya sake ya dawo masa sabo, alamari ne mai wuyar
fassaruwa a gare shi wanda bai taba kwana cikin irin sa ba sai jiyan, dukkan
ilahirin jikin sa ke vibrating yana karbar sabon yanayin da ke sauka masa yana
kashe kuzarin sa, ta hanyar sanya masa unbearable feelings na matukar son hada jiki
da Amani. A rayuwar sa bai taba yi wa wata mace irin kallon da ya yi wa Amani jiya
da yau ba, watakila hakan ne ya janyo masa fadawa wannan masifar. Bai taba saka
idanun sa sosai a kan kowacce mace ba, don kiyaye dokar Ubangiji, sai yau a kan
Amani Usman Faskari, da yake da tabbacin a yanzu ta zama matar sa, wato halalin sa.
Mukhtar ya fahimci cigaba da zaman su wuri guda shi da Amani hatsari ne babba a
gare shi, mai barazana ga mutuncin sa da kimar sa da girman sa a idanun ta, don
Amani ba irin matan da lafiyayyen miji zai gani ya iya kauda kai bace. Sai kawai ya
mike ido jajir ba tare da ya dube ta ba ya ce,
Hajjaju, zamu wuce idan kin gama.
Amani ta dauki dan yalolon mayafin ta na raka ni gantali (cantitly) ta yafa,
sannan ta zuge jakar kayan ta, bata amsa masa ba don duk ta bi ta tsargu da kallon
da yake yi mata tun jiya kamar sabon maye, tafiyar tasu daga dakin nan zai fi bata
ventilation da sassanyar iska, domin dai tun jiya bata shakar numfashi daidai yadda
ya kamata idan ta tuna akwai Mukhtar da mayatattun idanun nan nasa a cikin dakin,
abu daya ya kwantar mata da hankali jiyan, tayi barcin ta har da munshari, da ta
fahimci ya bar mata falon ita kadai, ya shige cikin daki har ya rufo kofa da key ta
ciki, bai kuma kara fitowa ba sai dazun da ya fito don yayi sallah. Sai kawai ta yi
gaba zuwa kofa, ya janyo jakar sa ya fito shima ya rufa mata baya.
Ya bada mukullin a reception sannan mai taxi ya dauke su zuwa filin jirgin
Murtala Mohammed. Zuwan su ba jimawa suka tarar jirgin da zasu hau ya sauka.
Ethiopian Airlines ne ya daga da su birnin Freetown, wato babban birnin kasar ta
Sierra Leone.
**** **** ****

FREETOWN
S
aukar su ke da wuya suka tarar da Abdussalam Faytoory wato abokin Alhaji ya zo
daukar su daga nan filin jirgin saman Freetown, Lungi Airport. Abdussalam ya san
lokacin da suka taso da kuma na saukar su. Don haka tun kafin su sauka yana arrival
yana jiran saukar su.
Abdussalam dan asalin kasar Saliyo ne kuma lardi (province) daya suka fito da
iyayen Jalan. Ya karbi jakunkunan su yasa a bayan mota, gajiya ta gama bayyana a
fuska da jikin Amani, amma bata so ta yada zango a koina yau sai dakin mahaifiyar
ta. Son samu ta kwana a bayan ta, tana mai jin dumin ta itama. Amma Abdussalam
kamar ya san damuwar ta, suna tafe a hanya yana tuki su kuma suna ta kallon gine-
ginen birnin Freetown, wanda ya banbanta dana inda suka fito, sun shagaltu ga
kallon mutane mabanbanta a halitta da suttura da wadanda suka saba gani a arewacin
kasar Najeriya, duk da cewa suma Saliyo bakar fata ne amma yawancin su zaka samu
dogaye ne masu kyawun sura mazan su da matan su, Faytoory ya ke gaya musu cewa yau
a gidan sa zasu kwana, sai gobe in sun huta zasu wuce Eastern Province (Kenema)
kenan, wato lardin da mahaifiyar ta take zaune, ya gaya musu shima dan can ne,
kasuwancin fitar da iron ore ne ya ke kawo shi cikin Freetown.
Kenema, shine jihar su Jalan wanda ke kan boarder din kasar Guinea da ta
Liberia (Eastern Province), nanne mahadar mining din diamond industry na kasar
Saliyo bakidaya.
Ya kuma tabbatar musu Jalan tana raye ita da Yayar ta amma iyayen su sun jima
da kwantawa dama, da yayan ta biyu mace da namiji tare da ita wadanda mijin ta
Lukman ya mutu ya bar mata, amma Yayar tata bata Saliyo yanzu haka, itama aure take
yi a wata kasar daban cikin kasashen Africa.
Mukhtar kusan ya fi Amani nuna farin cikin jin cewa Mama Jalan na raye, tsabar
yadda ta zaqu su raba hanya da Mukhtar yasa ta kasa nuna farin cikin ta da wannan
labarin da aka basu, tunda Faytoory ya ce sai ta kara kwana a Freetown kafin su
wuce Kenema wanda ke nufin sake kwana tare da Mukhtar duk walwalar ta ta kau, dan
farin cikin data samu kan ta a ciki, na jin cewa Mamanta na raye, da kasancewar ta
cikin kasar da aka haifi mahaifiyar ta ta da ya bakunceta duk sai ya bace daga kan
fuskar ta, komai ya daina burge ta, ko dama can ita bata taba sakawa a ran ta cewa
mahaifiyar ta bata raye ba, Alhaji ne kawai yake tantama, cewa da tana raye da zuwa
lokacin ko sau daya ne ta nemeta, tunda ta san garin da ta baro ta, ya bi ya take
laifin sa kullum na Jalan yake hangowa, bayan shine da laifin komai.
A kullum cikin mafarkin ta ta kan gan su tare ita da Maman nata, suna zantawa
cikin kauna da soyayya irin na zantawar nan ta Uwa da diyar ta.
Kyakkyawan dakin baki mai hade da toilet Faytoory ya basu a cikin gidan sa daga
harabar shigowa, shi kuma ya shige cikin gidan don iyalin sa na Kenema, ya shigar
musu da kayan su ya ce su kwanta da wuri don su samu hutawa sosai don gobe in sha
Allahu karfe shidda zasu dauki hanya don tafiya ce a gaban su bata wasa ba zuwa
lardin Kenema.
Ai Abdussalam na bada baya, kamar jira take, ta samu bakin kofa ta zauna ta
hada kai cikin guiwa ta soma girzawa Mukhtar kuka irin mai sosa zuciyar mutum, ya
hana shi sakat, yasa shi a damuwar da zai kasa sukuni. Kuma idan ya ce kukan da ta
soma bai bashi tsoro ba, bai taba shi ba, bai hargitsa shi ba ya yi karya, don sam
bai ga me aka yi mata na kuka ba. Ga dai ta a Saliyo, gab da haduwa da Innar ta, to
kukan na magani da menene?
Kafin wani haushi ya zo ya tsaya masa a makoshi, ganin kukan nata har da shure-
shure, na tabara da sakarci, tana yi tana fadin ita a daren nan zai dangana ta da
mahaifiyar ta, ba zata kwana a dan tsukukun dakin nan tare da shi ba, ga babu
wadatar iska da A/C, abincin da Abdussalam ya shigo musu da shi tasa kafa ta shure
ya kife, tace munafurci ne suka shirya shi da Faytoory tun a waya, cewa su kwana a
gidan sa kada su wuce a yau, don kawai ta kwana yana kare mata kallo ta wutsiyar
ido, irin kallon da ya kwana yana mata a Lagos.
Ai ta lura in tana barci sa ta yake a gaba yana kare mata kallo, har da taba
mata gashi, ina ruwan sa da ita? Ko ta gaya masa ta karbi sadakin sa da hannun ta
ne ba wajen Baba Idirisun ta baro mishi abin shi ba?
Mukhtar yayi sukuti! Yana kallon ikon Allah, domin kuka take yi sosai mai
hawaye da majina da sheshsheka. Tana fadin ko ya kai ta wurin Maman ta a daren nan,
ko ta saka kururuwar da duk makota sai an ji su, in aka zo tace sato ta yayi.
Mukhtar bai san lokacin da ya isa gaban Amani ba ya damki kullin gashin kanta
dake cikin ribbon ya mikar da ita tsaye cikin zafin nama, yace,
idan baki yi kururuwar kin gaya musu cewa na sato ki bane baki cika butulu ba,
daga abun kirki zaki yi min tukuicin tsiya? In baro komai nawa don in cika
alkawarin dana dauka don kyautata rayuwar ki, ki saka min da wannan ihun da kika
san bana so? Kin san yadda kukan mace ke kassara ni ya ji min ciwo a zuciya? Kin
san ba abinda na tsana irin kuka a kunnuwa na? Kukan ma na mace, macen kuma matar
aure na?
Budar bakin Amani sai cewa ta yi ta ina nazama matar taka? Na dauka sai na
karbi sadakin ka da hannu na da amincewa ta ne na zama matar taka? Koma ka tambayi
Malamai, sadakin ka yana gun Baba Idi sai dai in shi ka aura. Idan mafarki kake to
ka farka, ni Amani na fi karfin auren yaron gidan mu, matsiyaci irin ka kuma
faqiri, sai zuciyar firauna, me zai kai ni auren mutum mara asali da nasaba irin
ka.
Tunda ka zo gidan mu mun taba ganin wani naka? Ko beran masallaci bai taba zuwa
wajen ka ya ce mana shi jinin ka bane ba, a hakan kake mafarkin ka aure ni? Ni da
ke da gata na da arziki na da komai? Allah ya tsare ni. In mafarki kake Mr. Mukhtar
ya kamata ka farka.
Wa ya sani ko a bola a ka tsintoka? Dama an ce shegun yaya shegen kyau ne da
su.......
Sai ya sakar mata gashin kan ta jikin sa yayi laasar bakidaya.
Yau idan da ace ya taba furta cewa yana son Amani, da ya nemo kalaman sa duk
inda suka shiga a kunne da kwakwalwar ta ya mayar da abin sa cikin cikin sa.
Madallah da bai taba furtawa ba, sai ya yiwa kan sa murna da fatan alkhairi.
Shin Alhaji ya san irin kalar gallafirar matar da ya aura masa mara ko kankanin
tunani, ko sanin ya kamata? Wadda bata san darajar dan adam ba? Wadda babu humanity
a zuciyar ta? Alhaji da kansa ya taba gaya masa Amani bata tauna magana in zata
fade ta musamman in ran ta ya baci, kuma ba ruwan ta da lahanin da kalaman ta zasu
yi wa mutum, amma duk da ya kwana da sanin hakan bai taba zaton zata iya budar baki
ta ce masa shege ba.
Ya koma gefen gado ya zauna dafe da kan sa yana maimaita inna lillahi wainna
ilaihi rajioun. Ita da kan ta data fadi kalaman sai ta ji tana son mayar da su,
ganin yadda suka taba shi sosai. To amma aka ce magana zarar bunu.... ta riga ta
fita.
Haka kawai ta dade tana kissimawa a ran ta Mukhy shege ne, shi yassa kyan sa
yayi yawa, bata san kaikayin bakin da ya kai ta furtawa yau a gaban sa ba.
Tafi alaqanta qaiqayin bakin nata da huce kan damin haushin kwana daki daya da
Abdussalam ya sake hada su.
Mukhtar ya dago idanun sa jazur, fuskar sa ma ta yi jazir abinki da farin
mutum a cikin bacin rai, ya dubi Amani dake tsaye duk guilty ya lullube ta, zuwa
yanzu ta daina kukan tabarar data ke yi masa. Ta kama bakin ta. Shi kam da son samu
ne ya furta mata saki uku shine kawai zai huce. Amma sai ya tuno fuskar Alhaji
Usman wadda rabin ta baya aiki, da jikin sa cikin wheelchair, da rokon da ya rika
yi masa a kan yayi hakuri da Amani, abu ne da zai karasa shi lahira nan take idan
ya ce masa ya saki Amani, saki har uku!.
Ya shiga tuno tarin alkhairori Alhaji gare shi sai ya zama cikin dilemma na
tunanin ya saki Amani ko aah? A lokacin ita kuma sai ta ji tana so ta bashi hakuri,
if possible, ta ce na maida kalamai na, ganin irin lahanin da suka yi masa, amma
izzar ta da ego din ta suka hana ta. Sai ma tsaki data yi ta haye gadon ta bar shi
nan zaune a gefen gadon, idanuwa sun kada, har tiriri suke, ta ja bargo abin ta har
kan ta ta dukunkune jikin ta a ciki.

A irin sake-saken da yake yi a yanzu sai ya ga ba abinda zai daidaita fushin da
ke hankoro a kirjin sa, banda kwatar hakkin sa ta karfin tsiya a jikin Amani, ta
hakan ne kadai zai huce abinda ta yi masa yanzun nan. Ya kuma goge rainin nan da
take yi masa daga zuciya da kwakwalwar ta. Sai dai kuma, sai fuskar mahaifin sa ta
gilma masa, wata kamilalliyar dattijiyar fuska mai cike da farin gemu da kamala,
nannade cikin nadin larabawan Diffa, wanda ya rufe har rabin dogon karan hancin sa,
ya tabbata mahaifin sa bai taba sakawa mace karfi a shimfida da sunan aure ba, wai
don ya huce fushin sa daga tarin akuyanci da rikicin da suke masa a gida, (shi da
ya tara su da yawa kenan ma), har ba adadi. Idan ya kasa hakuri da guda daya amanar
ubangidan sa mai dimbin karamci a gare shi, wadda dama ubanta ma ya san halin ta,
ya dauka ya bashi a haka, with good hope na zai iya taimaka masa su gyara halaye da
dabiun ta, ashe kuwa ba zai iya kara guda ukun dake jiran sa a nan gaba ba, da
kwarkwarori ma in ta kama, ya yi hakuri da su da halayen su kamar yadda mahaifin sa
Issouffou Massaoudou ke yi da iyayen su mata ba.

Yau shi Mukhtar tilon dan Issouffou Massaoudou mace mace ke ce ma shege sabida
ta gan shi yana neman abinci a karkashin mahaifin ta!!! Life is not fair for him at
all!!! Ko yace iyayen na sa su suka jawo masa!!!
Zubewa ya yi a gefen Amani cikin kasala da mutuwar jiki, wadda zuwa lokacin ita
har ta fara sakin minshari, sabida dadin barcin da ta samu nan take. Ko babu komai
ta fadawa Mukhy abinda zai hanashi nashi baccin yau, itama huce bakin cikin kwana
da shi daki guda again da suka hada baki shi da abokin Alhaji suka yi mata sanadin
sa.
Ga dakin wani dan akurki, gadon (6 by 4) wanda mutum biyu ba zasu iya kwanciya
a kai ba tare da sun mannu da juna ba. Ga rashin naurar sanyaya daki sai fanka ta
tsaye a daidai kan su.
Mukhtar ya gayawa kan sa idan Amani ta kira shi shege shi ya jawo, sai bango ya
tsage kadangare ke samun mashiga, abinda ta gani ne ko take tunani ne ta fada,
Baban ta kuma bai mata adalci ba da ya bata wanda bata san asalin sa ba. Babu wani
nasa da ya zo ya karba masa auren ta dole tayi masa gori har da mafi muni wato na
shegantawa.

Karo na farko da tunanin komawa gida ya zo wa Mukhy, ya ji ba abinda ya ke so
irin ya bude ido ya gan shi a gaban iyayen sa da yan uwan sa. Ko da basu canza daga
yadda ya san su ba. A kalla a yanzu ya san ciwon kan sa zai iya yi musu uzurin da a
baya baya iya yi musu idan ya ji uzurin su daga bakin su.
Wani irin gumi ya shiga yanko masa tun daga tsakar kan sa har zuwa yatsar
kafar sa..... sai ka dauka ruwa aka kwara masa kwanon sha guda. Jikin sa ya hau
rawa. Dai dai lokacin da maharbin ya harbi kurciyar dake kan bishiyar tsamiya,
wadda ke rataye da kankanuwar jar laya a wuyan ta.
**** ***** ****

Z
azzabi da masassara mai zafi ne ya taru ya rufe Mukhtar daga wannan lokacin,
lokacin da ya mirgine ya kwanta a gadon cikin barin jiki da karkarwar sa bai sani
ba. Sanyi ke kada shi ko ta ina, yana neman abun rufa, ga Amani ta janye bargon ita
kadai ta cukuikuiye a cikin sa. Dan karfin da ya saura masa ba zai ishe shi kwatar
bargon nan daga jikin Amani ba.
Sai kawai ya kwanta ya kama ta ya kankame jikin sa yana bari da karkarwa,
hakoran sa na haduwa da junan su, ji ka ke kaf-kaf-kaf.
Zafin zazzbin jikin sa sai da ya huda har cikin bargon nan, ya tadda fatar
Amani, bayan kamar rabin awa da kwanciyar Mukhy a jikin ta, ba tun yau ba ita mutum
ce mai nauyin barci sosai, hakan ne yasa har Mukhtar ya dade yana samun dumin jikin
ta bata sani ba, ga hucin zazzabi dake fita daga hancin sa zuwa fuskar ta da bata
rufe da bargon ba. Duk nauyin barcin da ke kan ta haka ta soma kokarin bude ido don
ji take kamar an danne ta. Kamar numfashi na mata wuyar shaqa. Ilai kuwa da idon ta
ya bude sosai, Mukhtar ne ta gani kankame da jikin ta cikin wani hali na
numfarfashi tamkar ran sa na son fita.
Idan ta ce bata tsorata ba, kuma bata wartsake nan take ba, ta san ta yi karya.
Kokarin raba shi da jikin ta ta soma nan ta ji irin zafin da jikin nasa ya
dauka. Kidimewa ta hanata daukar matakin da ya dace wato ta dauki wayar sa ta kira
Faytoory, sai ta kama rawar jiki da kaduwa itama tana tunanin maganganun ta ne suka
jefa shi a wannan halin.
Tace na shiga uku ni Amina, shegen baki na zai kashe mutum!
Sai ta fara hawaye tana fadin na mayar da kalamai na, can cikin ciki na
Mukhtar, wallahi I dont really mean it.
Ina! Mukhy, bai san tana yi ba don zuwa lokacin ya gama zama unconscious, wato
ya suma gabadaya.
Fitsari ya kwacewa Amani daga tsaye ta sake shi piiiiiii, ta nufi kofa da gudu
ta zare sakata tayi waje, sai ta rasa inda zata nufa. Kofa ta gani a rufe wadda
tayi cikin gidan ta hau bugawa da karfi. An yi saa Abdussalam idon sa biyu sallah
ma yake yi da yake Malamin addini ne sosai.
Amani saboda rudewa ce masa ta yi ka zo don Allah ba ya motsi, wallahi ba da
niyya na fada ba, ba ni na kashe shi ba, ko da bana masa so na soyayya, ba zan
kashe shi ba, ban ma san yadda ake kashe mutum ba.
Kafin ta rufe bakin ta Abdussalam ya kai kofar dakin.
Ya ciccibo Mukhtar daga gadon ya kwantar a tsakar dakin, sannan ya rike
tsintsiyar hannun sa ya tabbatar jijiyar tana motsawa. Kallo daya ya yi masa ya
gane halin da yake ciki wato; sihiri mai karfi ke fita daga jikin sa.
Ya ce da Amani ta shiga dakin da ta ga ya fito ta duba bayan kofar dakin zata
ga kwarya ta dauko masa, zata ganta da ruwan ganyen magarya a ciki, da gudu ta je
ta kawo, ya karanta wasu kebantattun surori da taawizai na karya sihiri ya tofa a
ciki, sannan ya ce ta taimaka masa ya cirewa Mukhtar riga.
In ka ga bare-bare a gurin Amani wanda hannnun ta ke yi yayin cirewa Mukhy riga
kamar tsohuwa yar shekara casain, tana kici-kicin cirewa Mukhy riga, tana kauda kai
cikin jin kunya da faduwar gaba, kamar ta ce kasar ta tsage ta shige, kafin ta
kalli kirjin sa mai cike da lallausar gargasa, baka wuluk, irin ta gashin kan sa,
haka ta cire rigar ta jefar, ta koma can gefen su ta rufe ido tana ta tuba, na tuba
ya Ubangiji na tuba! Astagfirullah kuwa a jejjere haka ta hau jero ta ta kai sau
hamsin, don ita gabadaya ta baiwa kan ta laifin ta ne, muggan maganganun ta ne suka
jefa Mukhtar a wannan halin na mutu kwakwai, rai kwakwai.
Abdussalam ya shafe duka jikin sa da ruwan maganin nan, har fuskar sa da gashin
kan sa, ya bar shi daga shi sai short nicker da ke jikin sa, sannan ya maida shi
gadon ya ja bargon ya rufe shi da shi, yana kallon yadda Mukhtar ya bude ido a
hankali ya kuma mayar ya rufe, alamar barci mai nauyi yayi gaba da shi. Fatar bakin
sa dake motsawa da ace zaka fahimta, ka kuma san abida ke zuciyar sa, zaka gane
sunan garin su yake ambata watau.
DIFFA......DIFFA.......DIFFA!,
(With extreme nostalgia).
Daga baya bakin ma ya daina motsin kiran Diffan, ya yi shiru, ya mike sosai a
cikin bargon don barcin sa yayi nisa.

Faytoory ya maida duban sa ga takurarriya mai barin jiki, Amani, yace kada ki
tashe shi sai ya tashi don kan sa, hakika akwai sammu a jikin sa wanda nake da
tabbacin yanzu, ya fita.
Amani ta dago a zabure, tana tambayar Faytoory menene sammu? Ya ce sihiri
iyakar tsorata Amani ta tsorata, don ta san ba ka da mai yi maka wannan sai makiyi,
to shi kuwa Mukhtar da ko aboki bai da shi a Katsina bayan Alhaji, wa zai yi masa
sihirin?

Please Login or Register in order to submit comment