Reading Amani 2 by SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taaziyya ta gaya
min watarana zata aiko a kaini inda take aure a Nijar, kuma tun daga wannan lokacin
ne ta soma yi min aiken kudi lokaci-lokaci duk da bana cikin bukatar komai, ina
tare da miji na cikin kwanciyar hankali da rufin asiri lokacin, bayan rasuwar Baban
su Fajur na aika mata ta hanyar dan aiken da ke kawo wasika a tsakanin mu wanda dan
kasar nan ne mai kasuwancin Rakuma a Nijar, shine fa ta bude min asusu, wanda kai
tsaye duk wata take turomin kudade na Saifa masu kauri, wadanda da su ne na cigaba
da daukar nauyin karatun yaran nan, muke kuma cin abinci, na kuma soma sanaar kiwo,
ga abinda mahaifin su ya mutu ya bar mana muna juyawa a gona, muna samun amfani
daga noma da kiwon kaji da kiwon shanu. A takaice kin ji wannan itace rayuwar da
muke yi a halin yanzu. Safwan yana rubuta jarrabawar kammala sakandire yanzu a nan
makwabtan mu wato Gambia, ya zo hutu ne, Fajur tana karatu anan wata karamar
sakandire ta kudi a bayan gidan nan, kullum da kanta take zuwa ta dawo ta huta ta
wuce Islamiyya.
**** **** ****


MOTHERHOOD
Z
uwa washegarin ranar, hatta makwabtan Jalan bakidaya sun san da zuwan yar ta dake
Najeriya aka shigo ana yi mata barka, wasu na aiko abinciccikan kwadayi wa Amani,
kasancewar Jalan ta mutane ce mai yawan kyauta da kyautatawa ga makwabtan ta, anata
mamakin kamannin su ita da Amani in ka dauke cewa Jalan mai jiki ce Amani siririya.
Duk abokan arzikin iyayen su dake raye sai da ta kai Amani a washegari suka gan ta.
Basu dawo gidan ba sai da yamma lis.
Shima Mukhatr baya gidan tun safe Faytoory ya zo ya dauke shi, sun shiga gari
yana nuna masa wurare masu tsohon tarihi na Kenema, da inda ake Mining din Diamond.
Daga can suka wuce gidan Faytoory suka ci abinci da iyalin sa sai lokacin suka dawo
gidan su Amani.
Faytoory ya ajiye Mukhtar kenan suna sallama da cewa gobe in sha Allah da wuri
zai zo ya tafi dashi Freetown, inda daga can zai hau jirgin Lagos.
Mama Jalan ta aiko Safwan ya kira shi su ci abincin dare yadda suke yi kullum,
a lokacin yana hada kayan sa a jaka yana tunanin tunda su ka zo rabon sa da kebewa
da Amani ko da da sunan su gaisa, wato ya gama mata amfanin da zai mata, tunda ta
dafe uwar ta a gefen ta shikenan. Sai ya shiga tambayar kan sa na me zai yi wannan
tunanin ma? Amani ce fa! Wadda ya sani ba tun yanzu ba. Ai ya dade da sanin Amani
ba yar goyo bace shakiyya ce ya sani dama, kuma ta fada ta kara haduwar su ta kan
hanya ce da zarar ta ga uwar ta babu ita babu shi.
Ya tuna cin mutuncin data yi masa sa Freetown da zagin fitar hankali na
sheganta shi, sai ya ji zuciyar sa na kara tafarfasa, Amani na kara fita a ran sa.
Amma mutuncin iyayen ta a zuciyar sa na kara ninkuwa.
A ladabce Safwan ya shigo ya gaida shi, sannan ya gaya masa sakon Mamma na ya
fito su ci dinner tare.
Ba tare da ya dago ya dubi yaron ba don baya so ya ga idanun sa, a dai yanayin
da suke ciki yanzu na tsananin bacin ran Amani. Ya ce ya je ya gayawa Mamma cewa a
koshe yake, ya ci abinci a gidan Faytoory kuma yana so zai shigo yayi mata sallama
don gobe in sha Allah zai koma Katsina.
Safwan ya je ya dawo ya ce Mamma ta ce ya shigo, a gaskiya a lokacin baya son
shiga cikin gidan a yanayin da fuskar sa ta koma yanzu, wato boyayyen yanayin nan
nasa da ba kowa ya san yana da shi ba ya bayyana, domin baya so Hajiya Jalan ta ga
hidden side din sa na rashin walwalar nan. Gashi idan ya zo baya iya controlling
din sa har sai ya bace don kan sa.
Sannan haka kawai yake jin muryar Mamma Jalan da accent din ta kamar yadda yake
jin tashin muryar Ummami, wanda hakan ke kara tono bacin ran dake kasan zuciyar sa
na kewar Ummami da jin zafin ta (as well), yana kara bayyana a kan fuskar sa.
Ba yadda ya iya dole bayan yayi wanka ya canza kayan jikin sa zuwa farar
jallabiyya kal kirar Dammam, ya yi sallah a masallacin kofar gidan sannan ya shiga
cikin gidan da karamar tazbaha mai kyau a hannun sa. Nan ya gan su complete family
a kan teburin cin abinci abin gwanin ban shaawa. Amani ta sha ado da laffaya koriya
sharr da irin matsatsiyar rigar nan ta roba mai dogon hannu daga cikin laffayar
light green itama. An yi mata wai irin setting din gashi wanda ya zubo a saman
goshin ta ya zarce har bayan kunnen ta. Bakin nan sai shining yake da Elizabeth
Arden Lip gloss kamar ka sace ta ka gudu (looking takeaway), idon nan nata mai kama
da kwan zabo ya sha mascara gashin idon ya fito gazar-gazar.
Rabon ta da yin ado irin wannnan bazata iya tunawa ba. Sai ko yanzu da take
jin kanta a daidai wato bata da damuwar komai, tunda rayuwa ta koma mata daidai, ga
ta ga uwar ta a duniya, ga kanne, sosai take cikin nishadi, barin ma data ji Safwan
ya zo ya fadi sakon Mukhy na cewa gobe zai koma Katsina.
Ai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, yi ta yi kamar ta tashi ta ka rawa, murnar
tata har kasa boyuwa ta yi sai da Mamma ta gane bakin ta ya ki rufuwa don Mukhy ya
ce gobe zai koma ya bar ta a nan. A cikin zuciyar ta Jalan tana mamaki, ko meye
aibun Mukhtar haka da matar sa ta kasa son sa? Mutum son kowa da shi a halitta da
dabia, abun alfaharin kowacce mace wajen kamun kai da kamewa da girmama iyayen ta,
amma Amani na neman maraba da shi irin haka bata ko jin zata yi kewar sa don ko a
waya bata ga sun gaisa ba balle text din soyayya. Kwata-kwata ta gama lura Mukhy
baya ran ta, kamar kishin sa take akan Baban ta kamar kuma zuciyar ta bata taba
kimsa mata soyayya a kan sa ba.
Ta riga ta dauke shi rival a zuciyar ta, ko kuwa wani wanda ya tare mata gaba
ya hanata rawar gaban hantsi. Sai Jalan ta shiga tambayar kan ta ko yar tata bata
da lafiya ne irin ta yaya mata ko kuma tana da shafar jinnu. Ta lura bayan dolonci,
rashin kunya, rashin ilmin addini, rashin cikakkiyar tarbiyya har da rashin sanin
muhimmancin da Allah ya baiwa miji a kan ta, da rashin sanin hakkin aure.
Kada dai tarihi ne yake maimaita kan sa, tunda itama abunda ta yiwa Uban ta
Alh. Usman kenan, kusan tsayin shekaru biyu tana wahalar da shi a dalilin bata son
sa.
Tunda ya aure ta sau daya ya taba samun saar ta, shima ta karfi, wanda daga
baya ta gane rabon Amani ne ya rantse.
Tana kuma lura da cewa tunda suka zo Amani bata je inda yake ba, bata kara bi
ta kan sa ba, bata kara yin zancen sa ko kula da alamarin sa ba a matsayin su na
sabon aure, balle ta damu da sanin halin da yake ciki a masaukin nasa, ko ta
tambaya an kai masa abinci ko aah? Don in an kira shi ya ci ma baya zuwa.
Sai ta ji tausayin Mukhy mai tsanani da kaunar sa kamar dan cikin ta ya kamata,
bata san dalili ba amma jin sa tayi ya kwanta a ranta kamar dan ta Safwan, ba
banbanci, don in ba kuskure idanun ta suka yi mata ba ita ta hango kwantacciyar
soyayyar Amani maras misaltuwa a can kasan kasaitattun idanun sa masu sheki da
sparkling a duk sanda ya juya su a kan Amani. Ita a wurin ta Alhaji Usman ya kware
shi, da ya hada shi da auren Amani, hakika ya so kan sa, domin Mukhy data ke faman
kira yaron Baban ta ita sai taga ajin sa da kasaitar sa sun dame na Amani.
Gashi ya san irin tarbiyyar da yayi mata amma ya hada dan mutane nagartacce,
kamamme mai alkunya da wahala, don ya gan shi mai hakuri da biyayya. Ga wata irin
nutsuwa da kamala a tare da shi irin wanda tsayar da addini da kula da sallah ke
haifarwa namiji, wanda bata taba gani a matasa kamar sa ba.
Ta shiga hangowa kan ta irin asarar surukin kwarai da zata yi, idan shashashar
diyar nan tata tayi masa rikon sakainar kashin da zai gaji ya yakice ta.
Sai ta yi maza ta mike tana tunanin abun yi na gaggawa, don kankarowa Amani
mutunci ka idon Mukhtar kafin ya karasa zirarewa.

Mukhtar yayi sallama duk suka amsa banda Amani, wadda a lokacin ta kai fork da
ta cokalo dankalin turawa a jikin sa bakin ta, tana wata tauna a yangace kamar
bata so. Jalan ta nuna masa kujerar da zai zauna mai fuskantar ta Amani ya tsugunna
har kasa ya gaishe ta, yana ta kokarin kin dagowa ta ga fuskar sa, amma a kulawa
irin ta Jalan, sai da ta hango yanayin da yake boye mata din, kuma a matsayin ta
na babba ai ta san dalilin sa.
Amma sai tace lafiya Mukhtar na gan ka haka babu walwala?
Mukhtar ya ki zama a kujerar don ba zai iya tana kujera shima yana kan kujera
ba, sai ya ce mata Mamma zan koma Freetown gobe da sassafe, daga can zan tashi
Nigeria in sha Allah.
Ta kusa ce masa Amani fa?
Don sai ta ji kamar bata kyauta ba in ta rike masa mata har tsayin watanni biyu
nan gaba, bayan bashi da wata matar a can gida Katsinan. Kamar Mukhy ya san me
Jalan take tunani sai yace,
ita Amina Alhaji ya ce ta zauna da ke na dan wani lokaci, ta saba da nan din
Jalan ta soma lalubo idon sa da yake boyewa da nata wayayyun idon na iyaye, ta ce.
Are sure you are okay with her stay here? Cewa nake daurin aure kawai aka yi
muku baku tare ba ko sau daya?
In don ta ni ce ba abunda zata yi min alhalin tana da miji a gefe, gara ta
wuce ku koma tare, zai fi min kwanciyar hankali da kai kan ka.
Ai jin haka Amani ta soma buga kafa irin wanda takewa Alhaji, tana fadin ita ta
zo kenan, ba inda zata sake zuwa. Alhaji ne yasa take zaune a Katsina kuma ita kam
yanzu ta barwa Mukhy shi halak malak. Sai ji kike gwajab! Mamma Jalan ta gwabje
bakin da ya sha lip gloss, tace,
Amina!
Ashe baki da daa baki da ta ido? A gaban kannen ki kikewa mijin ki wannan diban
rashin albarka? Tashi ku je ki bashi hakuri, na ce ki bashi hakuri har sai ya huce,
ku yi sallama cikakkiya, kada in ganki a cikin gidannan sai da safe!.
Tuni Mukhtar ya kai bakin kofa don in ya cigaba da zama a wajen nan Amani ta
kara magana ta rashin amincewa da umarnin ta, ko ta kara furta wani abu akan hakan
ya san Mamma Jalan zata kara kai duka, da alama mai saurin hannu ce.
Sosai dukan Jalan ya samu bakin Amani, tuni leben sama ya kumburo. Zata yi
magana ta ji bakin ta ya mata nauyi, sai ta fara hawayen da baya yi mata wuya, a
ranta ta ce shikenan itama uwa ta yayi sumumu-kasau dinsa na munafurci ya raba mu,
Mamma kuma ta yi rantsuwa ta kara ta tashi ta tafi wajen mijin ta ko ta sassaba
mata kamanni yanzun nan.
Ko me ta tuna? Ta ja hannun Amani zuwa dakin ta da zafin nama saboda idanun su
Fajur da suka bubbude suna kallon su, suna shiga ta rufo kofar da mukulli, ta dube
ta da tausayi, don ta ga tsanar Mukhtar tsantsa a cikin idon ta. Ita victim ce ta
kiyayyar auren dole ta san me Amani ke ji. Ta ce.
Amina, bana so ki zamo daya daga cikin matan da aure da hakkin sa ke kai su
wuta. Ba sai ya ce bai yafe miki ba Allah zai dubi hakkin sa a kan ki ya fidda
masa, na san a shekarun ki kin san aure, kin san maanar sa, amma a dolancin ki kina
sa kafa kina takewa.
Shin ya ta ko kin san irin kyautar darajar da Allah yayi miki kuwa da wannan
salihin mijin da ya baki? Ina jiye miki ranar dana sani.... wadda aka ce ..... keya
ce, tun da sauran mutuncin ki ki kankaro shi a idon Mukhtar, kafin ranar da zaki yi
nadama mu kuma bama tare da ku.
Jalan ta cigaba da yi mata nasiha iri-iri mai kashe jiki amma banda jiki mai
kunnen kashi irin na Amani. Don nasihar da waazin wani na shiga ne wani na fita ta
daya kunnen. Ta kawo wasu kwayoyin magani ta bata ta ce ta hadiya yanzu tana gani
kuma a gaban ta. Sai Amani ta tuno Haj. Muna, itama hakika ta bata irin wadannan
kwayoyin kuma bata yarda ta sha ba, yanzun ma da Mamma Jalan ta dage sai ta sha a
gaban ta, can kasan harshen ta ta kai su ta danne su da harshen ta ta kora ruwa.
Mamma Jalan ta hada garwashin lantarki (burner) nan da nan ta zuba wani turare irin
nasu na musamman tace ta tube ta turara jikin ta. Wanna ba musu ta yi, tunda turare
ne kawai, sannan Jalan ta raka ta har kofar entrance na masaukin Mukhtar, tace ta
wuce ciki tana kallon ta.

Haka ta tsaya daga nesa sai da ta tabbatar Amani ta buga kofar, ta ga sanda
Mukhy ya zo ya bude, da farko kamar ba zai bata hanya ta shiga ciki ba, don ta ga
kamar jayayya suke, bata dai jin me suke fadi sosai kasancewar (by nature) din sa,
Mukhy bai da daga murya wannan sai Amani idan ta so yin rashin kunya.
Mukhtar yana bude kofar ya ga Amani ce, sai ya ki bata hanya, cewa yayi lafiya?
Me kika zo yi wajen dan shege?
Idanun ta suka yi rau-rau, a rayuwar ta bata taba yin maganar katobara ta yi
nadama irin wannan maganar ba.
Da ana amai a lashe da tuni ta lashe ta, ta maida ita cikin ta.
Banda Mamma ta sako ta gaba me zai kawo ta dakin sa da daren Allahn nan har ya
gaya mata bakar magana?
Sunkuyar da kai tayi tana hura hanci da wasa da yatsun ta, sannan ta juya ta
tofar da kwayoyin maganin da ke bakin ta, Mukhtar ya bi abinda ta tofar da kallo
amma bai san mene ba, ta ce ai da gani na ka san nima takura ni a ka yi na zo, ka
san da bazan zo ba, don bani da bukatar komai a wurin ka ya ce sai ki juya ji koma,
shege baya bukatar komai a wurin ki shima.
Ta daga idanun ta cike da hawaye ta ce a rayuwa ta ban taba bada hakuri ga
kowa ba, ban taba yin magana nayi nadamar ta ba, amma wannan na yi, na maida wannan
kalamin ciki na, na kora su da ruwa nayi flushing din su tun daren dana furta su.
Ina baka hakuri a kan su, don nima na san basu dace ba, sharrin zuciya ne da
fushi, amma idan ka cigaba da maimaita min su da rike ni da su a ran ka, hakika ka
cutar da ni Mukhtar!.
Mukhtar sai ya juya ya shige ciki ba tare da ya iya ce mata komai ba, don (hes
cool and shocked) da sunan sa data ambata yau, ya kuma san da gaske take bata taba
baiwa kowa hakuri ba sai yau. Tabbas UWA daban ce, kuma uwa ta yi a rayuwar diya
mace. Wadda ta rasa UWA ayi mata jajen rashin da bazata mayar ba, har abada!!!

(Allah ka yi wa iyayen mu gafara ba don sun mutu ba, wadanda suka rasa nasu
Allah ka kai rahma da haske da kamshi kabarin su- Takori).

Ba don Mammah ta yi rantsuwa sai ta kwana a dakin ba, da daga nan zata juya ta
koma, ai dai ta yi masa sallamar data dace, kuma da ya bata hanya bai ce ta shigo
ba, itada kan ta data gaji da tsayuwa ta shiga dakin a fusace, amma bata rufe kofar
ba ta bar ta a bude fayau.
Sai shi ne da ya ga sauro zai cika dakin, ya mike ya rufe ya wuce ya koma ya
cigaba da abinda ta tarar yake yi kafin ta shigo wato booking din jirgin Lagos
online, ta cikin system din sa.
Da shigowar ta dakin atmosphere din dakin gabadaya ya canza da wani irin
sihirtacccen kamshi irin na turaren da ake yiwa amaren kasar Saliyo, wanda a
makwabtan su wato kasar Gambia kawai ake samun shi.
Yana tambayar kan sa wane irin fitinannen turare ne haka Amani ta fesa, mai
barazanar daga masa hankali? Ga gashin nan ya sha wani irin setting an kanannnade
shi ya zubo a gaban goshin ta ya zagaya ta bayan kunnen ta, ya kwanta akan wuyan
ta, kasancewar laffaya ce a jikin ta sosai gashin ya fito ya kwanta a kan dogon
wuyan ta.
Yana aikin amma hankalin sa ya rabu biyu, neman shidewa yake yi. Allah kadai ya
san wane irin turare Jalan ta turarawa yar ta. Domin dai a karshe Mukhtar sai kashe
kwamfutar sa yayi ba tare da ya san takamaimai ya gama booking din ko bai gama ba?.
Sai ga vedio call din Alhaji ya shigo masa ta whtsp dinsa, alamar yana son
magana da shi. Kasa daga wayar yayi ya dai zuba ma kiran ido, sakamakon yadda
kasala mai yawa ta rufe shi kuma baya cikin irin mood din da zai iya magana da
Alhaji.
Tana kallon sa ya mika hannu ya kashe wayar bakidaya, ta tsaya taki motsawa
daga inda take tsaye, ta harde dogayen kafafun ta ta kuma nade hannun ta a kirjin
ta tana harare-harare, ita bata zauna ba ita bata rage laffayar jikinta ta kwanta
ba.
Mukhtar da kyar ya iya mikewa ya rage fitilar dakin mai haske ya bar shudiya
mai rangwamen haske, wadda a turance ake kira dim light daga nan ya lallaba ya haye
gadon sa ya ja bargo har kan sa ya kudundune, ya bar ta a nan tsaye don ya fahimci
neman rigima take yi da shi.
Amani ta yi kwafa, miskilancin sa ya kara fusata ta, sai ta karasa gadon ta
dauki filo daya ta jefa a kasa, ta warware laffayar ta ninka ta biyu sannan ta rufu
da ita, ta kwanta akan kafet mai laushi tana cewa a ranta me zai kaita hawa gadon
nan ko da ya kula ta? Balle yayi wannan shakulatin bangaron da ita? Ai ko gadon
zinare ne ta bar masa.
To amma ta kasa barci bayan ta kwanta din, jin numfashin Mukhtar ya sauya
kasancewar dakin yayi tsit, babu komai sai bugun numfashin su da sururun iya
kwandishan, yadda numfashin sa ke sauka da sauri da sauri a kunnen ta, tamkar
zazzabi da masassara irin wanda ya same shi a Freetown ya ci karfin sa.
Tana jin sanda ya dauko filon sa ya dawo kasa shima, zazzabi sosai da sanyi
yake ji, dumin jikin mace kawai yake bukata a wannan lokacin, ya fahimci cigaba da
kwanciyar sa shi kadai a gadon daidai yake da ya haka rami ya kashe kan sa... akan
matar da addini ya riga ya bashi damar komai yake so a kan ta. Akan me zai yi ta
cutar da kan sa har haka?
Shi ya san matsayin sa na namiji kuma matashi mai jini a jika, sannan jinin
Issouffou Masaoudou, yayi matukar hakurin da ba kowanne namiji kamar sa ne zai iya
ba a kan mace. Ya san yana da hanyar da zai samu kan Amani ko da bada yardar ta ba,
amma kasaitar sa bazata bari ba, yana ji a ran sa yafi karfin ya yi forcing mace ta
kwanta da shi (by force). A yanzun da tura ta kai bango, kuma Jalan ta warware ego
din sa, ta hanyar wannan kamshi na jikin Amani da su kadai matan Saliyo suka san
sirrin da ke cikin sa, a yanayin da yake ciki yanzu, sai ya manta ko waye shi, da
wannan pride din nasa, sabida ba shi ke sarrafa jikin sa a yanzu ba.
Hakanan ya tabbata suka kwana a haka Allah ma sai ya tambaye shi dalilin cutar
da gangar jikin sa, alhalin jikin sa ma da kowacce gaba ta jikin sa na da hakki mai
girma a kan sa, bai kamata yayi ta biyewa Amani yana cutar kan sa ba, yarinyar da
kullum sai ta saka shi a tashin hankali da wankan janabar babu gaira babu dalili.
Yaya akayi yaya akayi Amani bata sani ba don ta soma samun barci, sai kawai
taji Mukhtar ya bi ya kwanta a gadon bayan ta, yana sakin ajiyar zuciya. Domin a
yau dauriya da jarumtakar sa sun idasa karewa. Koko in ce, Mama Jalan ta karar da
su da sirrin ta.
Hannayen sa ya saka ya riko hannun Amani dasu, cikin siga ta nuna bukatuwar
miji zuwa ga matar sa, matar ma wadda yake tsananin so, ya ratsa yatsun sa sosai
cikin nata, sannan ya damke su da karfi, kwanciyar sa a gadon bayan ta da yanayin
rikon da yayi wa hannun ta a bazata, ya tsorata ta, domin bata zata ba ko da wasa,
a tunanin ta Mukhtar ba zai taba iya hada jiki da ita ba, don yadda bata son sa ta
tabbata haka shima baya son ta, kuma wannan alamari ta san cewa baya faruwa sai da
soyayyah, daga haka ta ji Mukhtar ya janye laffayar jikin ta data rufu da ita, da
zafin nama ya janye laffayar, ya saura Amani da tiny rigar robar jikin ta, Mukhtar
ya ga body structure din Amani ta cikin hasken dim light wanda hakika Allah ya yi
wa Amani halitta wadda ta kasance daya cikin dubu, a cikin na mata dubu kafin a
samu irin na matan Saliyo sai an tona, bai taba zaton haka Allah ya kera Amani ba,
wanda hakan ya karasa susuta komai nasa, ya birkita dan mutanen Diffa. Kafin ayi
haka Amani ta ji Mukhy ya rungumeta ta baya sosai, da wata irin tight hug (runguma
tsatstsaura), ya manne ta a jikin sa yana sauke numfashi mai matukar wahalar fita
daga huhun sa.
Tana iya jin yadda jikin sa ke shaking, jijiyoyin jikin sa ke vibrating, yana
kara shigewa sosai cikin jikin ta da kadan kadan har ya shige jikin ta bakidaya,
wanda hakan ya gama tsorata ta, ta soma mutsu-mutsu na nuna rashin yarda da son ta
kwaci kan ta, amma karfin ba daya ba, nan ta fahimci mai raba ta da Mukhtar yau sai
Allah da ya halatta masa ita. Sai kawai ta soma hawaye masu zafi na tausayin kai,
tana hango ego din ta yau ya tsiyaye a kasa..., tana hango budurcin ta zai kare yau
a arha, ga wanda bai isa ba, mijin da aka baiwa sadakar ta ba don ya isa ba, bai
kuma dauke ta da daraja ba duk da haka, kuma baya son ta kamar yadda bata son shi
itama.
Ba kowa ya janyo mata ba sai Maman ta Jalan, cikin kuka-kuka ta ce Mukhtar,
are you trying to rape me? Kamar a mafarki Mukhy ya ji Amani ta fada cikin muryar
kuka don ta rasa karfin da zata yi kokawa da shi, kamar itama sakon Mamma na aiki a
jikin ta, don a lokacin ya gama sabule rigar robar jikin

Please Login or Register in order to submit comment