Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure,bansan yadda
Zan Miki bayani bane shiyasa nayi shiru"

Kallonta Yasmin Tayi shekeke ,sannan tace to ki bani ruwa ko se na roka"

Da sauri tace "A'a"
Mikewa tayi ta nufi kitchen se da ta shige Yasmin Tayi murmushi tace miskila kawai
kallon falon ta ci gaba da yi har idanunta suka fada kan farouk Masha'Allah
tace,Ashe babban soja Amal ke aure gaskiya ta taya Aminiyar ta murna, ta fada
acikin ranta

Ruwa da lemu Amal ta kawo Mata Tasha ,sannan tace "bani labari me yasa kika kasa
fada min

Labarin yadda auren nasu yake tun farko taba yasmin,sannan ta kare da Kinga ba son
juna muke ba fa ,kila ma auren ya kusa mutuwa,da sauri Yasmin ta rufe bakinta
tace"kar kice haka ni yadda ki ka ban labari na lura ba karamin so yake Miki ba ma
kawai ki saki jikinki kusha soyayyar ku malama"

Sororo Amal tayi Tana kallon Yasmin kafin tace"dawa za'ayi soyayyar Allah ya kiyaye
,mutumin da har yanzu be ce Yana Sona ba ,Zan wani shige masa"

"To Bari kiji idan kika yi Wasa tsaf wata zata kwace maki shi in kika tsaya Jan
aji,in Zaki ji shawara ta tun da miskili ne ,to kizo ki fara Abubuwan da Zaki jawo
hankalinsa akanki Wanda Dan dole ze bude Baki yayi magana,daga Nan cikin ruwan
sanyi Zaki hukunta sa ya gano cewa Allura ma karfe ce"

Dariya Amal ta saki ,ita ma Yasmin haka ,se sallama suka ji ya shigo da sauri
Yasmin Tayi shiru ,Amal Kam ci gaba tayi da dariyarta ,tunda ya shigo idon sa na
kan Amal da yaga dariyar ta matukar yi Mata kyau har da murmushin gefen Baki
yayi,duk Yasmin na kule da shi kafin tace"Ina wuni"

Yace lafiya Lau zama yayi daya daga cikin kujerin falon ,suka Kara gaisawa da
Yasmin , ya saki jikinsa se tambayoyi yake Mata Nan ma yasan kawar Amal din ce

Amal se mamakin wanna shishigin nasa take
Yasmin ce ta mata signal da ta bashi ruwa,Bata fuska tayi se da taga Yasmin din ta
harareta sannan ta Mike ta dauko ruwa da lemu
Ta kawo gabansa dukawa tayi Tana zuba masa ,tuni idanunsa suka masa kyakyawan
gani ,lumshe idanun sa yayi ,Mika masa cup din lemu tayi se da ya hada da hannunta
ya Dan rike kafin ya sake ta

Yasmin yi tayi kamar Bata ga abunda ya faru ba, Amal ce tace Mata zo muje daki kiga
wani Abu mikewa sukayi suka shiga daki

Suna shiga mikewa yayi jiki a mace ya nufi dakin sa

Suna shiga kan stool din madubi Yasmin ta zauna kafin tace"kawata mutumin Nan fa na
lura ba karamin sonki ya ke ba wallahi Kinga kallon da yake Miki kuwa

"Kamar wani maye ,anya ba so yake kawai ya sameni a bagas kuwa ba"

Yasmin tace"to miye Dan ya same ki ba sadakin sa ya biya ba,ke dai kiyi Amfani da
shawarar da na Baki ,shi da kansa ze bude bakinsa ya fada Miki Yana sonki ko ba shi
kike son ji ba, daga Nan Kuma dole ki saki jiki ya gurji Amarcin sa "

Duka Amal ta Kai Mata ,da sauri ta goce Tana dariya tace"Ehh Mana gaskiyar ke
nan,in Kuma kika na ganin Wasa ne ki zauna Nan se dai kiji yayi auren sa ya barki "

Yawwa Ina kayanki suke na lefe na diba Miki kayan da ya Dace ki dinga sawa
Nuna Mata su tayi

Ta jawo su kuwa ta shiga budewa,har ta cimma English wears nan ta zabo Mata masu
kyau ,tace to gasu Nan se ki dinga sakawa
Kallon ta kawai Amal ke yi har ta fitar da kayan ,sannan tace "Yasmin yanzu kina
ganin ya Dace na saka kayannan karfa ya ga zakewata da yawa"

Yasmin se da ta Harare ta tace"ya gani Mana ba mijinki bane "

Shiru Amal tayi Dan ta San tsab Yasmin zata balbale ta da fada in tace ba zata saka
ba


Bayan ta gama Nan ta shiga Mata hudubobi kala kala ,Wanda ita Amal mamakin yadda
yasmin din tasan wasu Abubuwan da yawa take
Daga karshe tace"in kinyi Amfani da abunda nace kin taimaki kanki in ba haka ba
wannan basamuden mijin naki ko ta karfi se ya kwaci hakkinsa ,sannan ko soyayyar da
kike son ya bayyana Miki ya Kiya Kuma ya je yayi aurensa da ya gano Baki iya kula
da shi ba"

"Zanyi tace "kamar wata yarinya,Yasmin dariya ke cinta amma Bata yi ba ,Dan ta kula
Amal na matukar tsoron gamonta da soja ga Kuma kishi

Se dai a ganinta shawarar da taba kawarta shine daidai in ba haka ba yadda matan
yanzu suka lalace tsab wata zata kwace Mata shi ko a cikin barikinnan ma
Har dai kabilun ciki da suke shiga kamar tsirara

Ta dade se zuwa marece ta Mata sallama Akan zata dawo, Dan taji kwanakinnan exam
din su zata fito

Har kofa ta rakota
Nan take ce Mata ta gwada Abubuwan da ta fada Mata yau fa
"To" tace mata

se ga farouk ya fito shima ze fita cewa yayi muje na aje ki gida
Ba musu ta bishi ita Amal gida ta koma bayan sunyi sallama


Da Daddare bayan ta gama sallar Isha'i ta dauko kayan da Yasmin ta fitar Mata ta
kula duk ba na mutunci a ciki se wata English gown red se dai ba har kasa ta Kai
Mata ba ,sannan spaghetti hand gare ta ,ita ta saka ,ba karamin kyau ta Mata se dai
fa ta fallasa asirin jikinta Baki daya ,ita kunya ma ta fara ji Tana Shirin cirewa
taji anturo kofar dakin an shigo,shine ya shigo kuwa ,kallonta yake yi ba ko
kiftawa ,takowa yayi ya nufo inda take hijabin sallar ta ta dauko zata saka karbe
hijab din yayi ya jefa kan gado ya wani rungumota sosai,take ta fara kicikicin
kwatar kanta Ammah ta kasa ,sunbarta ta ya shiga Yi kafin Naga Yana kokarin cire
zip din rigar jikinta ya Kuma nufi bed da ita ,gaba daya ya fara fita a
hayyacinsa ,in Banda kuka babu abunda Amal take ,juyata yake yadda ransa ke so
ganin Abubuwa sun fara gudana na nufi hanyar fita
Leemat se ingizani take na koma na dauko Rahoto,Raliya da su ummu afaf na jawo
ni,muna cikin wannan jayayyar ne na jiwo karar Amal tuni Alkalamina ya fadi
kasa..................✍️




*Aysha galadima ce*


Vote
Comment
Share
[8/31, 8:54 PM] Aysha Galadima:
*AN YI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 61-62*

________________________________

Ko da na koma dakin bayan wasu awwani da suka shude,Yaya farouk na isko rungume da
Amal da ko numfashi Bata yi kamar mattaciya ,se sabbatu yake zubawa Yana
cewa"princess Allah ya saki Aljannar fiddausi,Dama ance maza ke daga kafa mace ta
shiga Aljannah to ni na daga Miki tawa princess ,Jin ko motsin fitar Numfashin ta
ba ya ji yasa hannun sa ya Kara a hancinta yaji shiru ,mikewa yayi da sauri ya aje
ta ya nufi bathroom ruwa ya debo ya fito da sauri ya zauna bakin gadon ya aza kanta
a cinyarsa ya shiga shafa Mata Ammah shiru kake ji take hankalinsa ya tashi ,da
sauri ya tashi ya mayar da kayan jikinsa ,ita Kuma wata doguwar Riga ya samo cikin
kayanta ya saka Mata,ganin yadda jini ya Bata bedsheet din ba karamin daga masa
hankali yayi ba


"Hattara 'yan matan zamani a kula da Kai a rike mutuncin Kai har aje gidan miji Dan
shine mutunci ki a idon miji,duk wadda ke cewa Wai ba'a gane wa ko kinyi
aure,wannnan karyane Dan mazan yanzu sun San komai, ki kame kanki ,ki tsarkake
zuri'ar ki duk macen da ta zubar da mutuncin ta kafin taje gidan miji,to mijin nan
baze taba ganin kimar ki ba Allah ya shiryar da mu".

Ameen


Haka Nan ya samu ya saka Mata rigar ,makullin motar sa ya fita ya dauko a daki ,se
da yaje ya bude motar da hanzari ya zo ya dauke ta ya sata bayan kujera kafin yaja
motar da wani irin gudu,lokacin da ze fita , khaleel ya ga sadda ya fita ,ganin
irin gudun da yake yasa yayi tunanin ba lafiya ba bayan sa yabi


Wata private hospital ya nufa da ita Yana zuwa emergency aka nufa da ita
Tsaye yayi a wurin ya Kai ya kawo ji yayi an dafa bayan sa Yana juyowa ya ga
khaleel ne ,kalon sa yayi yace farouk lafiya kuwa


Shiru yayi kafin yace "my wife ce Bata da lafiya"

Shiru yayi Yana kallon sa Yana tunanin yaushe farouk ya fada ciki ne har yake
kiranta wife ,bangarar da tunanin yayi yace
"Tana Ina ?"


"Sun shiga da ita ciki ne"
Farouk ya fada

Jawo sa khaleel yayi suka zauna kan wasu kujeru dake jere a wurin ,sannan ya ce "ka
kwantar da hankalinka insha'Allah zata samu sauki

Amin farouk yace

Shi dai khaleel shiru yayi Yana tunanin meke faruwa


A can ciki kuwa da farko wasu nurses ne suka fara attending dinta ganin abun yafi
karfin su jini kawai ke fito Mata yasa
suka Kira Dr Kamal ayagi dama shine on duty da sauri yazo ya fara kula da ita har
ya samu nasar tsayar da jinin ,sannan ya Mata dinki ,Alluran barci masu karfi ya
Mata yasa suka Kai ta dakin da za'a kwantar da ita


Fitowa yayi Yana goge gumin da ya tsatsafo Masa a goshi ,da sauri farouk ya nufi
doctor din Yana cewa"Doctor ya jikinta ta farfado"



Kallon sa doctor din yayi ganin sa a Riki ce yasa ya ce "eh ta farfado Ammah ka
same ni office Dina"




Ya wuce, bin bayan doctor din yayi shida khaleel ,har sun shiga sun zauna ,doctor
din ya kalle su yace"patient din da ka kawo miye alakarka da ita?"



"Matata ce"
Yace,kallon khaleel yayi yace wannan fa

"Abokina ne"

To ko zaka Dan bamu wuri doctor yace ma khaleel



Har farouk ze yi magana da sauri khaleel ya katse sa yace"Bari na fita ,ai doctor
gaskiya ya fada "


Fita yayi kafin doctor ya juyo kan khaleel yace "yawwa matar ka ce kace ko,me yasa
baka bita a hankali ba ,ba ka San irin wannan zuwan da ka Mata ze sa ta tsorata da
Kai ba har ma ta fara gudunka,kaga yanzu ba karamin rauni ta ji ba Dan har dinki se
da aka Mata

Farouk se yanzu yake Jin haushin abun da yayi na kin binta a hankali da be yi
ba,shi Kam Ina ze sa ransa in ta guje sa saboda wannan dalilin




katse masa tunani doctor yayi ganin yadda duk ya ji kunyar abunda ya faru cewa yayi
ya sunanka

"Captain farouk Bashir maradun"

"Kai soja ne"

"Eh"

Doctor murmushi yayi Dan farouk ya saki jikin sa yace"to ba filin yaki bane fa ka
dinga binta a hankali ,Mata se da lallashi,sannan yanzu mun Bata gado har se ta
fara jin sauki zamu sallameta,Kuma ko kun koma gida ka Bata lokaci har se ta warke
sosai"



"To " yace,sannan suka yi musabiha da doctor din suka fito tare ya nuna masa dakin
da'aka kwantar da ita

Shiga dakin suka yi shida khaleel Tana kwance tayi wani fayau da ita har Rama yaga
ta masa ,ganin dare yayi yasa khaleel ya Masa sallama akan gobe zasu dawo da
Matarsa ,saqo ya basa akan akawo mishi wasu kayansa da bargo sallama suka yi ya
tafi


Dawowa yayi gafen gadon ya dauki hannunta ya saka cikin nasa ji yake wata zazzafar
kaunar ta na shigar sa, dukawa yayi ya sunbaci goshinta kafin ya tashi ya nufi
bathroom din dake dakin wankan tsarki yayi ya fito,Koda ya fito ya tarar an kawo
Masa kayan daukar jallabiyya yayi yasa,ya shimfida dadduma ya tada sallah ,ya dade
Yana nafila har kusan 2:30 sannan ya kwanta


Da Asuba massalacin asibitin yaje yayi sallah sannan ya dawo ,har lokacin Bata
farka ba Dan se da ya leka ta
Zama yayi ya dauko wayar sa ya Kira ummee bayan sun gaisa ne ya ce Mata suna
Asibiti Amal Bata da lafiya
Nan ta balbale sa da fada akan me be Kira tun jiya ba ,Nan yace ai da Daddare
ne ,Nan ta tambaye shi wane Asibiti ya fada Mata sallama suka yi ya aje wayar

Har yanzu akwai bacci a idon sa Dan haka ya kwanta a dayan gadon Nan take bacci ya
dauke sa

Karfe bakwai na safe ummee ta iso Asibitin ita da Al'amin da ya dauko Mata basket
din abinci dakin suka shiga suka tarar da harshi me jinyar bacci yake
Al'amin ne ya fara taba sa yana cewa "Yaya"
Firgigit ya farka dama ba yada nauyin bacci tashi yayi ganin ummee Nan ya gaida ta
ta Amsa tambayar sa me jiki tayi yace taji sauki Ammah har yanzu bata farfado ba

Ummee ce tace "me ke damun ta ne?"

Shiru farouk yayi ya rasa me ze ce ,ganin yadda ta tsare shi da Ido ya tsinci
kansa da cew"zazzabi ke damun ta"

"Allah ya Bata lafiya" ummee tace yace Amin

Yawwa to ga breakfast Nan kayi se ka koma gida kayi baccin anjima se ka dawo "to "
yace, ya hada tea ya Dan Sha ,sannan ya masu sallama ya fita


Shima Al'amin be dade ba ya mata sallama ya fita


Tana Nan zaune ba jimawa taga hannun Amal kamar Yana motsi,can Kuma A hankali ta
fara bude idonta,dakin ta fara bi da Ido ,Nan ta gane Asibiti ne

Ummee ta karaso bed din tace"ya jikin ki 'yata ?"

Da kyar tace da "sauki"
Duk ji take jikinta kamar ba na ta bane

Nurses biyu ne suka shigo ,Nan suka ce ma ummee zasu taimaka Mata ne su gasa Mata
jikinta

Da mamaki ummee tace "gashin lafiya zaku Mata"

Nan nurse ta shiga ma ummee bayanin abunda ya same ta"

Ita dai Amal ta sunkuyar da Kai kamar kasa ta bude ta shige take ji

Nan ummee tace to su hada ruwan ita zata taimaka Mata

Cikin ranta kuwa ta shirya fadan da zata ma farouk kan wannan abun da yayi,Akan mi
baze bi matar sa ahankali ba,har se ya ji Mata ciwo............✍️




*Aysha galadima ce*




Vote
Comment
Share
[9/1, 6:12 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 63-64*

________________________________


Ummee da kanta ta tayar da Amal a hankali ta taimaka Mata suka shiga cikin bathroom
,cikin ruwan zafin tace ta zauna,zaunawa tayi tayi wata irin zabura saboda azabar
zafi,ta tashi lallashinta ummee Tai tayi har ta zauna cikin ruwan hawaye kawai take
yi ba bakin maga, ummee ba karamin tausaya Mata tayi ba sosai,har dai Tai Mata
hakan kusan so ukku sannan suka fito tare ,ba karamin Jin dadin wankan Amal taji ba
Dan ta rage Jin Abubuwan da ta ke ji sosai, doguwar Riga ummee ta bata ta
saka ,sannan ta samu ta Rama sallolin da ke kanta



Bayan ta gama tana zaune kan dadduma sallama Akayi aka turo kofar dakin , ummee ce
ta Amsa
Matar khaleel ce ta shigo Tana dauke da kwandon Abinci

Gaisawa tayi da ummee,sannan ta jiyo kan Amal ta na Mata ya jiki,da sauki tace Mata
Cup ummee ta dauka ta hada Mata tea ta Bata karba tayi Tana Sha a
hankali,Sallamarsa ce tasa duk suka dago suna kallonsa

Wata irin sarkewa Amal din tayi da tea din da take Sha da sauri ya karasa shigowa
dakin

Har ya Mika hannu ze taba ta ummee ta masa wani irin kallo tuni ya dauke hannun
sa,ita Amal Kara shigewa jikin ummee tayi ,ita Kuma ummee ta dinga bubbuga bayanta

Har tarin ya Dan lafa Mata,sannnan ta Bata ruwa ta Sha,shi dai farouk ya na gefe a
tsaye

Bayan ta gama Shan tea dinne ta Sha magungunata ta kwanta da sauri ta rufe idanunta
Dan kar ma su hada Ido


Ganin hafsa na Nan matar khaleel ,yasa ummee tace muje ka kaini gida Zan dauko wasu
Abubuwan mu dawo tare
Tuni jikin farouk yayi sanyi Dan tunda ummee ta masa wannan kallon ya tabbatar da
ta San komai

Hafsa suka Bari da Amal suka fita ,tunda suka shiga mota yaga ummee ta Sha masa
toka sosai har suka isa gida


Fita tayi ta barshi a motar ,dole ya rufe mota ya biyo bayanta ,ko da ya shigo tana
zaune a daya daga cikin kujerin falon

Shigowa yayi jiki a sanyaye ya zauna

Kallonsa tayi kafin tace"Babana miye Amfanin abun da ka aikata fissabillilahi ,me
makon kabi matar ka a hankali shine za kayi Mata wanna aika aikar ,irin wannan abun
fa ake Kira fyade,runtse idanunsa yayi Yana me takaicin abunda yayi ,ci gaba tayi
da masa fada sosai,sannan ta dawo da masa nasiha akan ya dinga bin komai a
sannu ,in ba cin ma zalamarsu ta 'ya'yan yanzu ai da mace na shekara gidan miji be
bi ta kanta ba


Shi dai farouk kansa na kasa duk kunya ta kama sa,se hakuri yake Bata Ammah ya ki
dago kansa

Ganin yadda duk ya zama wani kalan tausayi yasa ummee ta bar maganar tace to"ka
tashi kaje Kuma ka ba matar ka hakuri ,ka Kuma lallashe ta Allah ya maku
Albarka ,anjima Zan sa driver ya mayar da Ni"


"To " yace ya Mike ya fita

Bayan sa ta bi da kallo Tana me jin kaunar Dan na ta🥰


Bayan fitar su Farouk ,Amal mikewa tayi zaune dama ba bacci ta ke ji ba,suka fara
Dan firar su da hafsa,Nan hafsa ke cewa "Amal ko dai mun samu karuwa ne,Naga ummee
ma ke jinyar taki"

Rufe fuska tayi da hannu ,hafsa ce tace"miye abun jin kunya ,

Cewa tayi "ai ni yarinya ce ban Isa haihuwa ba"

"Baki Isa haihuwa ba inji wa"
Cewar farouk da ke shigowa dakin

Ai tuni Amal ta hade Rai ,hafsa me zata yi in ba dariya ba take"Nima dai shi na
gani"

Gadon ya zauna akai ,matsawa Amal din take kokarin yi,hannun ta ya kamo ya rike
Yana murzawa a hankali Yana firar sa da hafsa

Duk a takure take jinta so take ya sake ta yaki

Sallama hafsa ta musu ta tafi Tana fita kamar jira take tace"ka sakar min hannu
miye haka Wai"

Kallonta yake cikn shaukin so yace"My Princess Ki yafe min Abunda ya faru Nima ba'a
son Raina hakan ta faru ba,juyar da kanta tayi gefe ta bar kallon sa ,ba ta sarar
ba taji ya rungumota gaba daya ,kuka ta aza Masa ,dole ya sassauta rikon da ya Mata
yace "menene?"


Hararsa tayi yace "wow Kinga yadda harararnan ta Miki kyau kuwa"

Baki ta murguda Masa aiko ya cafke bakin bugun kirjin sa ta fara,Ammah ko a jikinsa
,se da ya gaji Dan kansa ya sake ta Yana Maida numfashi, kukanta taci gaba dayi har
likita ya shigo dakin ,Nan yake tambayar ko har yanzu wurin zafi yake Mata tace
"a'a ita ya sallameta kawai"

Murmushi yayi yace "ok anjima idan nurse tazo Zan sa ta sake Diba ki idan kin fara
samun sauki zamu sallame ki ki iyar da warkewa gida,Ammah ki bar wannan kukan
hakanan, "to ". Tace ya gama abun da ze yi ya fita

Shiru dakin ya dauka Dan ya tashi daga Kan gadon da take Yana dayan gadon zaune ya
na latsar wayarsa


Kamar waddda aka ma dole tace"ka aramin wayar ka Zan Kira"

Dagowa yayi yace"wa Zaki Kira "

Kyale shi tayi se shine ya tashi ya kawo Mata wayar kamar ba zata karba ba ta dai
karba

Kiranshi Akayi da dayar wayar sa ya fita a dakin

Mikewa tayi zaune ,ta sa number Yasmin ringing daya ta daga tare da cewa"Assalamu
Alaikum"

Amsawa Amal din ta yi taci gaba da cewa"muguwa gani Nan kin jazamin kwanci a
asibiti ,gaskiya Yasmin Baki kyauta min ba,a dayan bangaren dariya kawai Yasmin ke
yi ba kakkautawa ,kashe wayar Amal tayi Tana tsaki


Sake Kira tayi Bata daga ba,har farouk ya dawo dakin Kira take Ammah Amal taki daga
wayar,se shine ya daga wayar

Ta dayan bangaren Yasmin na dauka ta fara da cewa"Dan Allah Amal kiyi hakuri nifa
bada wata manufa na Baki wannan shawarar ba,tuni farouk ya dago zancen Yasmin Dan
haka yace


"Kar ki damu Yasmin Ni taimakona ma kikayi"

Duk kunya ta kama Yasmin ,gaisawa sukayi Nan yake fada Mata Asibitin da suke


Tunda ya fara wayar Amal ke Jin wani irin haushin sa,yace taimakon sa Akayi Mana
tunda yayi yanda ransa ke so ya barta da lalura

Juyawa ma tayi ta kwanta bacci ya dauke ta



Kwanan Amal ukku a asibiti aka sallame ta bayan gargadin da farouk ya Sha a gurin
doctor,da Kuma ummee Dan da har ummee zata ce ta dawo wurinta har ta warke,Abbah ya
Hana yace ta barsa da matar sa ya kula da ita,ba yadda ta iya ta barsu suka tafi
gidan su

Amal Bata yadda Farouk ya fada ma su umman ta Bata da lafiya ba Wai kunya take ji
ma aji abunda ya same ta shima kunyar surukan nasa yake ji shiyasa be fada ba

Magunguna iri iri ummee ta aikowa Amal wadanda zata yi Amfani da su har ta
warke ,sosai Amal taji dadin magungunan Dan iya karta sati daya taga har dinkin ya
warke ta koma lafiya kamar ba ita ba



Tun da suka dawo farouk ke bawa Amal wata kulawa ta mussaman duk da ita har yanzu
taki sakin jiki da shi,Dan har yanzu tun Abunnan da ya faru Bata sake yarda sun
hada makwanci ba kowa dakin sa ya ke kwana


Ba karamar azabtuwa farouk yake ba ,Kuma ya kula da ta dade da warkewa ,gashi yanzu
da gayya ma ta mayar da English wears kayan sakawarta a gidan,Kuma yama kansa
alkawarin baze Kara takura Mata ba se da yaddar ta


Tana tsaye wurin dinning Tana jera kulolin Abinci ,sallama taji anyi Tana juyawa
taga Al'amin ne sannu da zuwa ta masa

Yace "yawwa Anty na me aka shirya muna dama yunwa na kwaso "

Dariya tayi tace bissimillah kazo ga abinci se ka koshi


Cewa yayi da surprise nazo Miki fa da sauri tazo ta zauna kusa da shi tace"gani
bani Mana autan ummee "

Dariya yayi kafin ya dauko wata farar takarda ya Bata

Karba tayi ta bude

Alhamdulillah tace Tana sake kallon takardar , result dinta ne na waec ya
fito ,Kuma duk taci


Murna kawai take ko da ta dago ta masa magana ,wayam ba kowa ,juyawa tayi ta
hangesa kan dinning Yana cin abincin sa ,ta sowa tayi tace "me ummee tace ,kaji an
fara nema min jami'ar?"


"A'a Yaya aka ce ki ba danshi keda friend a school din

To kawai tace,Tana tunanin yadda zata basa takardar

Bayan tafiyar Al'amin Tana Nan falo zaune ya dawo sannu da zuwa ta masa yace
"yawwa"
Ledar da ya shigo da ita yace tazo ta dauka,tasowa tayi a hankali ta dauka,Tana
budewa taga wata hadaddiyar waya ce me kyau a kwalinta,

Cikin farin ciki tace "nagode sosai Allah ya Kara budi"

Yaji dadin Addu'ar sosai Dan harda murmushin sa ,sannan ya tashi ya nufi dakin sa
wayar ta Ciro ta sata caji
Dakin ta ta shiga ta dauko result din nata,a hankali ta nufi dakin nasa ta
kwankwasa,shigo taji ance

Shigowa tayi ,Yana zaune bakin gado da laptop a gabansa ,tsaye tayi yace "karaso
Mana"

Ya nuna Mata gefen gadon,zuwa tayi ta zauna dagowa yayi yace"ya dai akwai abunda
kike so ne?"

Takardar hannunta ta basa karba yayi ya gani yace "Ahh result yayi kyau sosai
princess"

Murmushi tayi Nan ta fada masa sakon ummee

Bata fuska yayi yace"a'a ai ba wata jami'a da Zaki je"

"Ammah me yasa"
Tace, fuska a hade


"Saboda Ni ko na secondary din ba wani canji Dana tarar a ciki"
Shiru tayi ta ma rasa me zata ce masa


Mikewa tayi zata fita taji ya rungumeta ta baya Yana shinshinar bayanta ,tuni
jikinta ya fara rawa

Magana ya fara da cewa"ke da har yanzu banga wata kulawa da kika fara bani ba, Zan
bar ki kije jami'a habah princess ba Kya tausayi na ko?"

Ya juyo da ita Yana kallon ta ,kin kallonsa tayi,ba zata kawai taji hannun sa a
kirjinta,ba shiri take son kwace kanta Amma be Bata damar hakan ba,daukarta ma yayi
ya nufi bed din da ita ganin hakan yasa ta fara kuka Tana "Dan Allah kayi hakuri"

Magana yayi Shima Yana "ki tausaya min princess"

Kuwa ta kurma ba shiri ya sake ta ya fada kan gadon Yana Maida numfashi ,tashi Amal
tayi ta dauki rigarta dake yashe kasa ta saka ta nufi hanyar fita da sauri ta nufi
dakinta tana Mai da numfashi


Ya dade wurin kwance dafe da marar shi da yaji ta wani kulle Masa ,da kyar ya samu
ya shiga Baye ya watsa ruwa


Yana fitowa bayan ya kimtsa key din motarsa ya dauka ya fita

Khaleel ya hadu da shi tsayawa yayi ya fito suka gaisa nan yake fada masa da gidan
sa ze je

Yace"gani ai se mu tafi"

Cewa yayi ya dai shigo cikin motar suyi magana


Shiga ciki yayi suka zauna,Nan yake tambayar sa "me ke sa mace na gudun mijinta ,ko
Kuma in Bata sonshi ne ya ke sa Tana gudunsa?
Kallonsa khaleel yayi Nan ya kula aminin nasa kamar ma baya cikin natsuwarsa,
numfasawa yayi yace
"To a gaskiya farouk a yadda kaje ma matarka ai dole taji tsoron haduwar ku ta
gaba,sannan Amal fa yarinya ce so dole ka dinga tarairayarta kana lallashi kana
Mata duk abunda take so ta Nan ne zata baka hadin Kai sosai


Dafe Kai farouk yayi yace "Ammah kana ganin Tana Sona kuwa?"

Dariya khaleel yayi kafin yace ai wannan me sauki ne zamu iya ganewa in mun so


"Ta Yaya"

Magana ya fada masa a kunne koni ban ji me yace ba

Nan dai khaleel ya Kara kwantar Masa da hankali da fadi Masa Abubuwan da ya Dace ya
dinga yi


Sallama sukayi,

Please Login or Register in order to submit comment