Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu ne a gabanta ba se dai karatu ,Ammah dai
zanyi kokarin ganin ko gaisuwa ce ku na danyi "

Murmushi yayi yace nagode da kika fahimce ni kuma naji dadin bayanin da kika
min..............✍️



*Aysha galadima ce*

Comment
Share


[8/19, 9:50 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*
*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 25-26*



________________________________

Nan dai suka yi sallama da Ramla har ya karbi number wayarta , ta shiga gida inda
ta tarar da Amal ta nade kafafu Tana cin Abinci ,harara ta dalla Mata ,ai ko se ta
kyalkyace da dariya ita dai Ramla dakin ummah ta shiga ta nunnuna Mata kayan da
suka sawo da kuma dinkunan da ta karbo

Ana saura kwana biyu su wuce kwankiyal Abbah ya Kira Abbansu Farouk ya ke shaida
masa bikin da kuma tafiyar da zasu yi

Abban su farouk nata jin dadin sanar masa da Abbah yayi nan yace masa anjima ze
shigo Dan yana da muhimmiyar maganar da yake son suyi , nan dai suka yi sallama

_______________________________


A bangaren farouk kuwa yana cikin damuwa saboda gaba daya Abbah ya dauke masa
wuta ,Dan haka a gaggauce wannan weekend din yayi shi ,ranar Sunday ya tattara
kayan sa ya koma barrack ko Abbah be ma sallama ba

Ko da ya koma Kullum cikin Damuwa yake ,yau dai khaleel ya tasa shi a gaba akan se
ya fada masa damuwar sa , nan dai ya fada masa yadda sukayi da Abba
Ajiyar zuciya khaleel ya sauke, sannan yace "Captain gaskiya duk laifinka ne tun
yaushe Abba yake ma maganar aure Ammah kayi ko oho da maganar nan , sannan nayi
biyar ka ka zabi cikin masu sonka kaki yanzu ya kake so ayi?"

Farouk ya kalli khaleel yace "wallahi nima ban San ya zanyi ba ni fa na fada ma
bazan taba auren yarinyar da ita tace Tana so na ba , na fi son Naga wadda nake so
da Kai na"

Sororo khaleel yayi yana kallon shi can yayi murmushi yace "to ai shi ke nan se ka
shirya zuwa maradun ya ganmu se muje ka zaba"

Wani naushi ya kawo masa ya kauce
Nan khaleel ya ci gaba da dariyar sa se da ya gaji Dan kansa yace "to naji yanzu
dai ka shirya gobe mu fara yawo cikin garin kaduna ko za'a da ce "

Tashi yayi ya barsa falon ya shige bedroom
Mi ze yi khaleel kuwa in ba dariya ba ,se da ya gaji Dan kansa ya tashi ya fita
daga gidan


________________________________

Washe gari Abban su farouk ya je gidan su Amal yau dai har cikin gida ya shiga ,
su ka shiga daki da shi da Abbah

Sun fi awa daya suna magana ban San Abunda suka tattauna ba , Abbah ya fito suka yi
sallama ya tafi

Tun Asuba ummah ta tada yaran nata suka shirya Koda 7am tayi sun kama hanyar
kwankiyal koda 5pm na yamma tayi sun isa kasancewar garin na da nisa sosai, ko da
suka isa sallah kawai suka yi suka nemi dakunan gidan Kawu suka shige su Dan futa
saboda gajiyar tafiya da suka kwaso


Abbah ko da suka iso ya nemi kawu da kuma yayansa lawal suka kebe sun dade suna
magana Sannan suka fito Allah dai yasan abunda suka tattauna ,


naso shiga Esher maradun ta hana ni 🤣🤣


To haka dai Aka ci gaba da gudanar da shagulgulan biki
Su yaya sadiq sun Riga su Ramla zuwa kwankiyal danko da suka zo sun isko su

Ai ko dare nayi yaya Sadiq ya matsa akan Ramla ta fito yana son ya ganta ta rasa
yadda zata yi ta fita waje ita dai

Se tace "Amal muje ki rakani waje "

Sun fito ke nan suka ganshi har Amal zata juya Ramla ta rike ta. Tace "muje ki
gaisa da shi Mana"

Ranta be so ba tabi ta suna zuwa
Se da Ramla ta matsi Hanunta sannan da kyar tace "Ina wuni"

Se da ya kalle ta sannan yace "lafiya lau kanwata me tsorona "
Dan murmushi tayi tace "ai na Dena"

Yace "da ya fiki ai zamu ga karyar tsoro"

Da sauri Ramla tace "kamar ya yaya "

Ya wayance ya ce "ba komai "

ita dai Amal barin su tayi ta shige gida

Haka dai aka ci gaba da hidimar biki 'yan uwan ummah na gombe duk sunzo sunyo Mata
Sha tara ta arziki.

can a gidan wata goggonsu dake wani Dan kauye da ake Kira gangalawai aka sa
Amarya Ramla lalle ,ranar ko Tasha kuka su Amal da sauran dangi se tsokanar ta
suke

Ita ko se kuka take gwanin tausayi
Rana bata karya yau dai ake daurin Aure karfe biyu aka sa saboda Baki masu zuwa ne
sa

Na Sha mamaki Dana ga har da su khaleel da wasu abokan aikin su amma ba da farouk
ba se Abbah da Al'amin

Can cikin taron daurin naji me sanarwa yana cewa An daura auren *Abubakar sadiq
lawal da Amaryar sa Ramlatu Isma'il*

Dana kuma *Umar farouk Bashir* *maradun*
*da amaryarsa* *Amal Isma'il*
ai se na yarda Alkalamina.............✍️



*Aysha galadima ce*



Comment
Share
[8/19, 9:23 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



_Yau bana jin dadi fans ,ban yi tunanin ma zan iya typing ba,damuwar da kuka nuna
tasa_ _nayi Dan farin cikin ku
Nagode_




*PG 27-28*
________________________________




Da kyar na samu na dau Alkalamin nawa cikin mutane da ya fadi

Khaleel se kallon Abbah yake da ya fito daga massalacin da aka daura auren ,saboda
ya yi mamakin abunda yaji marokin na fada ,tun jiya yake mamakin Kiran da Abbah ya
masa akan cewa ya gayyaci wasu abokan aikun su zasu raka shi daurin Aure, shi
khaleel duk tunanin sa tare da farouk zasu zo , se da suka taso yaga bada shi ba
tun nan ya fara Shan jinin jikinsa.

Abba na dago Kai suka hada Ido yafito shi yayi da hannu , khaleel ya matsa kusa da
Abbah

Abbah yayi gyaran murya yace"khaleel kaji an daura auren abokinka ko, Khaleel ya
kalli Abbah yace "Eh Abbah Ammah banga farouk din yazo ba kuma be fada muna ba"

Jawo hannusa Abbah yayi suka fito cikin mutane ,sannan ya kalli khaleel yayi
murmushi yace" eh ai bada sanin sa ba ma na masa wannan auren , a matsayina na
mahaifinsa na zaba masa macen da na ga yafi da cewa ya aura tunda shi ya kasa nemar
wa kansa "
Cikin fushi Abbah ke maganar
khaleel dai sai cewa yayi "Abbah kayi hakuri Insha'Allah farouk ze karbi wannan
auren da ka masa da hannu biyu"

Abbah ya nisa yace "ai dolen sa ma ya karbe shi"

Wucewa Abbah yayi ya bar khaleel tsaye da jikinsa ya gama yin sanyi akan wannan
auren

Abokansu ne suka katse masa tunani, dayan ya ce "khaleel dama auren farouk za'ayi
shine ko ku sanar Mana ka kwaso mu mukazo?"


Khaleel se karya ya musu akan abun ne yazo kurkusa shiyasa be musu damar yi masu
bayani ba
Dayan ya kuma cewa"to Ina angon?"

Yace baya jin dadi ne ,Ammah yanzu zamu juya se mun Isa kd za'ayi reception


Acan cikin gida kuwa suna ta hidimar bikin su har se da wata Mata ma ta shigo gidan
take sanar da har an daura auren

Ummah ce ta fito tsakar gidan wasu Mata da suka shigo nan suke tayata murna suna
cewa"Ashe kuma matar Isma'il duk 'ya'yan naku kuka aurar to Allah ya basu zaman
lafiya"

Tace "Amin"
Yaro take nema ta tura a kirowo Mata su Amal da suke makwabta, bata so 'yar tata
taji labarin auren da aka daura Mata tafi so ta fara ji a bakinta

Dan ita ma tun lokacin da Abbah ya tare ta da zancen abunda Abban su farouk yazo da
shi ta kasa samun natsuwa Dan dai mijin nata da 'yan uwansa sun Riga sun yanke
hukuncin ne ,sannan 'yan uwanta sun taushe ta da bata yadda Anma 'yarta aure cikin
hanzari haka ba

Da kyar ta samu wata jikanyar gidan ta tura ta ta Kira Mata su Amal

Da sauri yarinyar ta fita,ita kuma ta koma dakin matar kawu

Ba jimawa ko su Amal suka fito suka nufo gidan bikin suna shigowa abokan wasan su
na ta tsokanarsu ita dai Amal bata kawo komai a ranta ba

Dakin matar kawu suka shiga inda ummah take zaune tare da 'yan uwanta na gombe da
suka zo da sallama suka shiga suka gaida su ,da fari'a duk su ka amsa

Yayar ummah ce ta yafito su da hunnu tace"kuzo nan 'ya'yana ta nuna kusa da ita
kasancewar Tana kuryar dakin

Se da suka zauna ta fara masu nasiha me ratsa jiki ,ita Amal ma mamaki take da'aka
hada da ita wurin nasihar aure se rufe fuska take , har ta Mike

Umma me kudi tace"dawo zauna ja'ira Ina Zaki kika Mike?"

Dawowa tayi ta zauna kallonta ummah me kudi tayi tace "Amal Nasan dai Kuna zuwa
Islamiyya ko sannan kunsan muhimmacin iyaye a wurin 'ya'yansu ko?"

Daga Kai tayi gabanta ya fara faduwa
Ciga ba tayi da cewa"Idan iyaye suka ba 'ya'yansu umurni me ya kama ta suyi?"

Tace "biyyaya ya kamata suyi akan umurninsu "
Cewar Amal

Ummah me kudi tace "to Iyayenki yau dai sun daura Miki aure da Wanda suke ganin ya
cancanta da fatan Zaki yi masu biyayya kamar yadda kika ce"


Amal rasa wane yanayi take ciki tayi ,se wata zufa ke karyo Mata ita kanta Ramla ta
shiga shock din Abunda ummahe kudi tace se kallonta take

Shiru dakin ya dauka

Se can ummah me kudi ta kamo hannun Amal ta rike tace " 'yata kinyi shiru"
Dukar da kanta tayi wasu hawaye na zubo mata da kyar tace " Zan musu biyayya"

Wata ajiyar zuciya ummah ta sauke ,tasowa tayi ta rungume Amal din tata ita ma Tana
goge kwallar data tarar Mata a Ido

Nima aje Alkalamin nayi nafara ta ya su kuka😭...............✍️



*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/20, 3:47 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)


*WANNAN SHAFIN NAKU NE*


*ANYI GUDUN GARA FANS GROUP*

*DUNIYAR MAKARANTA*

*ATK HAUSA NOVELS*

*FEENERH FANS GROUP*

_Ina jin dadin comments dinku_



*PG 29-30*


______________________________


Sun dauki tsawon mintuna kamin ummah ta dago kan Amal da hawaye ke ta zubo
Mata ,hannu tasa tana goge Mata su Tana cewa" ki bar kukan hakanan 'yata ,idan kika
ci gaba da yin kukannan zan dauka kamar ba kiyi na'am da zabin mu ba"

Ajiyar zuciya tayi bayan wasu sakanni tace "ummah ai nasan ba za ku zabar min
abunda ze cutar Dani ba"

Wani tausayin ta ne ya kama ummah ,se ummah me kudi ce da wata kanwar ummah suka
matso su ka shiga rarrashin Amal din har ta yi shiru , nan suka shiga Yi masu
nasiha me ratsa jiki
Har dai suka Dan saki jikinsu

Hakan ba karamin natsuwa ya Dan saukarwa ummah ba Dan tun da maganar auren nan na
Amal yazo kunnenta ta kasa samun natsuwa

Abunda ya faru kuwa shine
ranar da Abban su farouk ya je gidan Abbah a can kd , bayan sun gaisa ,nan fa ya
nemarwa Dan sa auren dai daga cikin 'ya'yan Abbah, nan Abbah ke ce masa babbar ai
aurenta za'ayi dayar kuma ko secondary school bata gama ba , nan Abban su farouk ya
shiga magiya akan Abbah ya taimaka masa saboda yana son hada iri da shi kasancewar
sa mutumin kirki , kuma yana da tabbacin 'ya'yansa duk masu tarbiya ne

Be boye masa komai akan farouk ba har da damar da ya bashi na ya fitar da matar
aure be yi ba ,shiyya sa yake ganin ya da ce a matsayin sa na mahaifinsa ya zaba
masa, a karshe yake cewa zancen karatun Amal kuwa zata ci gaba ko bayan auren na su
, nan dai ya ci gaba da yi ma Abbah magiya , Wanda hakan yasa Abbah ya kasa musanta
masa, saboda ya na jin nauyin sa da kuma girmansa Dan ko a shekaru ya fisa


Se da ya Dan yi shiru na wani lokaci ,sannnan yace"To Alh a yanzu bazan iya yanke
hukunci ni daya ba ,Ina da yaya da kawuna da yake can bauchi ,Zan fada musu duk
abunda suka yanke nima shine nawa , anan kafin Abbansu Farouk yama Abbah sallama se
da ya karbi number wayar kawu lawal a wurinsa

Dama washe gari akwai abunda ze Kai Abbansu Farouk kano ,Dan haka Koda yayi waya da
kawu lawal bayan sun gaisa nan yake ce masa gobe ze shigo kano yana son su hadu

Washe gari ko Abbah ya nemi wani Amininsa suka je kano ,tarba ta mutunci kawu lawal
ya musu ,se bayan sun zauna ne Abbah yaga Ashe yasan kawu lawal shi ma kawu lawal
nan ya gane Abbah nan suka Kara gaisawa ,

Can baya akwai wani taimako da Abbah yama kawu lawal

Bayan gaishe gaishe nan Aminin Abbah ya gabatar da bukatar da ta kawo su ,Dan Jim
Abbah yayi saboda shi ya San Alh Bashir maradun mutumin kirki ne ,ga taimakon
Al'umma dan shi shaida ne
Kuma a yadda yadda yadda sansa tsayayyan mutum ne Dan haka ko 'ya'yan sa ya San
suna da tarbiya

Murmushi yayi yace to Alhamdulillah ba laifi na amince se dai bari na Kira kawun mu
kuji ta bakinsa ,waya ya daga ya Kira kawu ya saka ta handsfree

Nan dai Aka tattauna bayan tambayoyi da kawu ya sake ma Alh Bashir.
Nan dai kawu shima ya amince

Fadar farin cikin da Abban su farouk ya shiga baze misiltu ba
Cikin farin ciki ya dawo kd ,se dare yake sanar ma ummee ita ma tayi farin ciki
sosai, se dai tana tunanin yadda farouk ze daukin auren ,se dai bata nuna ma mijin
nata ba kasancewar ta da sanin ya ka Mata
Da tayi wani tunani ma se take ganin wannan hukuncin da Abbah ya yanke ma farouk
shi ne dai dai da shi

Bayan su Amal sun Dan natsu kanwar umma ce ta tirsasa musu cin abinci sama sama
suka danci se ga kawu ya aika kiransu dakin sa , tashi sukayi suka nufi dakin nashi
, Koda suka shiga kawu ne da kawu lawal da Abbah dake gefe
Se sadiq dake kasa zaune , Suma gefe suka samu suka zauna

Nan kawu yayi gyaran murya , ya shiga yi masu nasiha me ratsa jiki , tuni su Ramla
suke ta kukan su a cikin mayafi se bayan ya gama ne yake kara Jan kunnen Sadiq akan
ya kula da 'yar uwarsa ,kasancewar a ranar za'a Kai Ramla a can kano

Nan fa Amal ta turje akan da ita za'a Kai Ramla nan fa Abban su farouk yace to tazo
a tafi da ita daga can su wuce kd , kasan cewar Abban su farouk yace baya bukatar
komai na kayan daki ko gara

Da kyar dai aka samu aka banbaro su Amal daga jikin ummah aka wuce dasu cikin
mota ,ita ma Amal tafiyar kenan daga ankai Ramla za'a wuce da ita kd
Motar da khaleel ze ja Amaren suka shiga tare da ummah me kudi

Sauran motoci kuma suka dauki mutane Ammah ba sosai aka je da mutane ba kasancewar
gari ba kusa ba

Se bayan tafiya ta fara nisa ummah me kudi tace "to ku bude fuskokin ku , kusha
Iska Mana "

A hankali suka Dan daga mayafin nasu suka yi shiru suna kallon hanya
Khaleel da ke tuki kamar Wanda aka tsikara yaji yana sha'awar ganin matar Abokin
nasa

Ta madubi ya kalli bayan motar, zaro ido yayi, in ya kalli Ramla ya kalli
Amal........................✍️

*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/20, 8:05 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 31-32*




_______________________________

Kamar ance Ramla ta dago kanta ,suka hada Ido da khaleel

Ci gaba tayi da kallonsa Tana mamakin ta in da ya fito
Shi dai mai da hankalinsa yayi wurin tuki yana tunanin to ya akai haka ta faru ,
sannan Wai ma wacece matar Abokin nasa a cikinsu

Sake dago Kai tayi suka sake hada Ido se tace mai"Ina wuni"
Yace "lafiya lau ,ya hidima"
Tace "Alhamdulillah"

Ummah me kudi ce ta kalli Ramla tace"kin San shi dama shine tun dazu Baki gaida sa
ba, ko Abokin Sadiq ne?
Ramla tace "A'a ummah na sanshi a kd ne"
Ummah me kudi tace "oho"
Nan shima khaleel ya gaida ummah me kudi
Da yake ummah me kudi wayayyiyar mace ce tako saki jikinta suka gaisa
Nan khaleel ke cewa ai shi Abokin farouk ne dayan angon
Nan ummah me kudi tace "Allah sarki mijin Amal kenan " Tana juyowa Tana kallon Amal
din data sunkuyar da kanta ,kamar ma bata a motar

Take khaleel ya fuskanci cewa Amal ai ita ce matar Abokin nasa ,aiko ba karamin
dadi yaji ba da hakan ta kasance ,dariya yake so yayi Ammah ya danne saboda ummah
me kudi , har dai in ya tuna cika bakin da farouk keyi na cewar yar 20years ta masa
yarinya , ganin wannan ma da ko 20 din bata Kai ba

To a haka dai suka isa kano cikin dare ,direct Ramla gidan mijinta a ka wuce da
ita, ummah me kudi kuma gidansu Sadiq aka wuce da ita ,Amal dai gidan amarya zata
kwana kasancewar akwai wasu bakin da zasu kwana a can
Shima khaleel se dai suka nemi hotel din da zasu kwana gobe su wuce Kd

Gidan Amarya Ramla Masha'Allah su Abbah sunyi kokari sosai an kawata gidan yadda
yadda ya kamata kasancewar ita dai akama komai ba da Amal ba
Da ka shigo falon gidan babba ne madaidai ci an kawata shi da kujeri da labulayya
har zuwa fentin falon lemongreen and orange ne se dinning area daga hannun dama se
kuma dakin Amarya Ramla,da kuma master room dake can kurya akwai kuma dakin Baki ,
kitchen na can kusa da dinning area

Dakunan gidan se sambarka komai yaji gishiri😀

Ramla dakinta suka shiga ita da Amal sauran mutane biyar din da suke tare suka
shiga dakin Baki
Suna shiga Amal se santin gidan na yayarta take , ita dai Ramla shiru tayi Tana
tausayin kanwar ta ta har dai da taga khaleel ta fara tunanin tabbas farouk shine
mijin Amal gashi soja abun da take tsoro
Lallai wannan shine *ANYI GUDUN GARA*

Tana tunanin yadda kanwar ta ta zata iya Rayuwa da farouk gashi yadda ta lura mutum
ne me saurin fushi tunda baza ta manta Marin da ya taba ma Amal din ba

Amal ce ta katse Mata tunanin da cewa "aunty ana Kiran wayarki "

Karbar wayar tayi taga yaya Sadiq ne , daga tayi taji yace"fito gani nan falo" se
da taji gabanta ya fadi

Juyowa tayi tace Amal ta rakata se taga har ta tayar da sallah ,dole bata da wani
zabi ta dauki mayafinta ta fita
Ko da ta shigo falon yana zaune akan kujera ,tunda ta fito yake binta da
kallo ,kujerar nesa da shi ta zauna da kyar tace"yaya Ina wuni "

Tashi yayi ya dawo kusa da ita , se ko jikinta ya fara rawa ,shi dariya ma ta bashi
se dai ya kanne

Kallonta yayi yace"ya gajiyar hanya beauty"
Shiru tayi Tana Wasa da yatsun hannunta se kallon yatsun nata yake lallenta ya
matukar burge sa ba zato taji yayi kissing hannun da sauri ta Mike tsaye Tana zaro
ido. Kamar wadda tayi karya

Murmushi yayi kawai ya kula ba karamin tsoron sa take ji ba
Ledar hannunsa ya Mika Mata
Ta karba yace "ki tabbatar kin ci fa kafin ki kwanta"
Se da ya sunbaci goshinta sannan ya nufi dakinsa

Da sauri Ramla ta nufi dakinta Amal ta isko har ta kwanta ta tadata tana tashi
ledar ta karba dama abincin da khaleel ya siya musu bata wani ci ba

Budewa tayi ,kaza ce a ciki taji Hadi

Irin ta yahuza suya😀


Take ko ta fara cin Naman
Ramla tashi tayi ta shiga ban daki domin ta watsa ruwa

Amal ko ba sauki take cin kazar nan

Nace a ci sannu Amaryar farouk..............✍️

*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/21, 10:47 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)
*PG 33-34*



________________________________

Washe gari da wuri suka tashi sukayi wanka,sannan duk suka yi breakfast da aka aiko
husna ta kawo daga gidansu yaya Sadiq

Bayan an gama nan suka shiga gyara Mata gidan

Ummah me kudi ce ta Dan Kara yi ma Ramla nasiha,nan ta dauko wata leda a Jakarta ta
bata tace"yadda za'ayi amfani da komai yana ciki"

Ita dai Ramla se 'yan kwallah ta ke gogewa,Amal tuni Ido ya Rena fata

Ba jimawa kusan 10am khaleel yazo gidan sadiq inda anan ne ze dauki ummah me kudi
da Amal su wuce Kd

Ai ko Amal tuni ta saki kuka har suka fito filin gate taki sake Ramla, ummah me
kudi se rarrashinta take , khaleel shima ya fito daga mota yana kallon drama da'ake
da ita ,se ya ji ta bashi tausayi

Hango Sadiq da ummah me kudi tayi yasa ta shiga mota ta zauna

Kamar daga sama suka ji ance
" ke sakar min mata"

Duk juyowa suka suka ga ashe yaya sadiq ne

Yana isowa ba kunya ya kama hannun Ramla ya rike,ita dai Ramla sunkuyar da Kai tayi
saboda khaleel na tsaye

Ai Amal ba shiri ta saki Ramla Tana kallon yaya Sadiq

Shi kallon Ramla ma yake yana cewa"ai se ki sa hawayen my wife su kare habah Amal"

Se ya dago kansa yana kallon Amal da hawaye duk suka bata Mata fuska ,se kuma yaji
ta bashi tausayi

Kama hannunta yayi ya ce"kibar kuka my sis kinji Allah ya bada Zaman lafiya Amarya"
Ya kare maganar da zolaya
Ai ko se da ta rufe fuska Tana jin kunya

Rike hannunta yayi har zuwa Motar
Ramla na gefen sa na dama

A hankali ta shiga motar se ta juyo Tana kallon Ramla
Ganin zasuyi wani kukan da sauri Sadiq ya rufe motar ya juyo yayi sallama da
khaleel da ummah me kudi


Ya ja hannun matarsa suka shige ciki

To Amarya Ramla Allah ya bada Zaman lafiya
_____________________________

Suna shigowa garin kaduna gidansu farouk ya wuce da dasu ummah me kudi,Dan wannan
umurnin Abbah ne ,akan Akawo su Amal nan gidan nasa
Tarba ta mutunci ummee tama su ummah me kudi
Daki guda ta basu, su shiga suyi sallah su huta ,har Abinci ma a can ta gabatar
musu Dan su samu sakewa

Bayan sunyi sallah ummah me kudi ta zuba abincin,tace ma Amal tazo taci
abincin ,Dan har ta kwanta,tasowa tayi Dan tasan ummah me kudi bata da Wasa ,tsab
zata iya balbale ta da fada

Tashi tayi taci Abincin bayan ta gama ta Dan kwanta


A bangaren Abbah kuwa tun jiya da ya dawo gida ,ya Kira farouk bayan sun gama
gaisawa nan Abbah ke fada masa auren da ya masa

Gumi ne ya dinga tsatsafo masa ya ma rasa abunda ze ce Banda bugawa ba'abun da
zuciyarsa ke yi


Abbah ne ya katse masa tunani da cewa "gobe in Allah ya Kai mu Zan turo masu Kaya
zasu zo su saka Kaya a gidan naka , khaleel ma yana can shi ze zo da matar taka
gobe Insha'Allah

Wani tukuki ne ya taso masa jin cewa khaleel ma ya sani har ma da shi akai komai be
fada masa ba

Ummee ce ta katse masa tunani da cewa "kayi shiru ba zaka ce komai ba?"

Wani Abu ya hade kafin yace"nagode Abbah Allah ya saka da Alkhairi"

Murmushin manya Abbah yayi ,saboda ya kula da halin da farouk ya shiga
Yace"Ameen

Nan dai iyayen nasa suka ci gaba da yi masa nasiha Wanda yasa jikinsa ya danyi
sanyi ya rage radadin da yake ji a cikin ransa

Fatansa daya ALLAH yasa ba kwaila mahaifin nasa ya aura masa ba,sannan Koma wacece
ze koya Mata hankali tunda ta shigo rayuwarsa be shirya ba

Bayan sun gama yi masa nasihar ya musu sallama ya fita

Ummee ce tace Allah ya basu zaman lafiya
Abbah yace "Ameen"

Kai tsaye gidansa ya nufa Koda yayi parking motar ya shiga gidan bathroom ya wuce
ya sakarwa kansa shower ya dauki kusan minti goma kafin ya fito

Koda ya fito wayarsa na Kara Koda ya Diba khaleel ne aje wayar yayi be dauka ba ya
kirasa ya fi a kirga Ammah be dauka ba


A can gidan su Farouk kuwa se bayan la'asar Amal ta falko tashi tayi ta shiga
bandakin wanka tayi Koda ta fito ta tarar da an aje Mata Kaya akan gado ,shadda ce
ready made doguwar Riga an Mata stone work me kyau
Saka rigar tayi, ta yi sallar la'asar Tana gamawa aka turo kofar dakin
Ummee ce ta shigo da sallamarta Amsawa Amal tayi
Sannan ta gaida ta cikin girma mawa

Amsawa tayi cikin sakin fuska tace" 'yata ya gajiyar hanya?"
Amal tace "lafiya Lau " Tana sunkuyar da kanta
Ummee ta kalle ta tace" ki saki jikinki kinji ki dauke Ni tamkar mahaifiyarki nan
gida ne a wurin ki duk abunda kike so ki fadamin kinji"

"To "
Amal tace
Ummee tace "taso muje falo kici Abinci"

A sanyaye Amal tabi bayanta
.......................✍️



[8/22, 7:45 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*






Please Login or Register in order to submit comment