Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karba har se da yayi muryar Amal yace
"habah Aunty Ramla"
Duk dariya suka saki sannan fa ta karba ta sake to masa godiya sosai

Tana fita Ramla da sauri ta juya Tana kokarin bude kofar da take zaune ,ji tayi an
riko dayan Hanunta Tana juyowa se taga shine yake binta da wani mayen kallo ,sannan
idanunsa sun wani Kara girma,gira ya daga Mata yace "Ina Zaki "?

Marairaicewa tayi tace "yaya gaisawa za muyi da su Ummah na fito mu tafi"

Se ya sake cewa "nifa a wurin wa Zaki barni"

Gabanta taji Yana faduwa ganin irin Abubuwan da yake Mata ,sannan ga wata kunya da
take ji ,katse Mata tunani yayi yace to kimin iso nima Zan shigo mu gaisa ,ya Bata
ledojin da yayo sayayya yace "gashi kiba ummah"

Godiya ta masa ta fita a motar,cikin gidan ta shiga

Tana fita ya dafe kansa ,ya rasa me yake damunsa Akan yarinyar Nan
yanzu..................✍️



*Aysha galadima ce*
Vote
Comment
Share
[8/27, 9:28 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)


*DUBUN GAISUWA A* *GARE KU*

_Nazeefi yarima_
_Aunty hassy Atk_




*PG49-50*




______________________________


Bata wani jima ba a ciki ta fito tace ka shigo, tsaye tayi har ya fito daga motar
suka shiga cikin gidan, ko da suka shiga ummah na zaune tsakar gida akan babbar ta
barma da suke shimfidawa Tana sanye da hijab dinta

Da sallama ya shigo gidan ,Amal dai wucewa tayi wurin Anty Ramla da ta shiga daki
Durkusawa yayi ya gaida ummah ,ta Amsa a kunyace Nan yake cewa Abbah fa tace be
dawo ba , shiru su ka danyi na minti biyu ,saboda rashin sabo ,kudi ya Ciro be San
ko nawa bane ya aje da sauri yace ummah se da safe,cewa tayi ka dauki kudin ka
Allah
Yace A'a ummah wadannan ma ba yawa ai,godiya ta mishi ,ya fita gidan
Amal ta kwalawa Kira se gata ta fito Nan ummah tace "wuce Yana can Yana jiranki,
Kuma ki masa godiya wannan hidimar tayi yawa ma ga kayan da ya siyo ga kudi Kuma ya
bayar ,ita dai Amal tuni ta turo Baki saboda Bata so tafiya yanzu ba ko Abbanta
Bata gani ba

Lura da yadda ta Bata fuskarta yasa ummah ta dauko talkamen da ke gefenta ,ai da
gudu Amal ta nufi hanyar fita ,ummah tace ja'ira da ki tsaya Mana

Koda ta fita Yana cikin mota ,zagayowa tayi ta shiga dayan bangaren ta zauna sannan
ta rufo kofar waya yake koda ta shigo katse wayar yayi ya juyo Yana kallonta duk ta
wani hade Rai,cewa yayi

"Lafiya kika fito Rai bace?"

Cike da shagwaba Amal tace "to ba ummah ce ta koro Ni ba bayan ko Abbah ban gani
ba"

Gani yayi shagwabar ta Bata kyau sosai har yaso ya saki murmushi ganin Tana kallon
sa sai ya kanne be yi ba , se cewa yayi

"Shine kike wannan fushin ,ai kuwa kinja ma kanki da Zan kawo ki kafin Ramla ta
koma Ammah na fasa "

Da sauri ta wani rike mai hannu tace

"Dan Allah yaya kayi hakuri na Dena fushin ma"
Tunda ta rike mai hannu ya jisa wani iri, itama ganin yayi shiru se ta dago taga
yadda ta wani rike masa hannu se ta saki hannun ta gyara zamanta a kan
kujerar,shima daidaita kansa yayi yaja motar suka nufi gida Koda suka je gida kowa
dakinsa ya nufa kasancewar tun kafin Anty Ramla ta tafi sukayi dinner..

Haka dai zaman nasu ya ci gaba da kasancewa ,a yanzu dai Amal Bata da wata damuwa ,
kasancewar yanzu Tana da waya Tana debe Mata kewa sosai,shima farouk tun Yana
karyata kansa har yazo ya yadda da ya fada son matar sa se dai har yanzu ya kasa
fada Mata,
A ganin sa har yanzu yarinya ce Bata gama mallakar hankalin kanta ba, Ana cikin
haka ne kuwa tafiyar shi zuwa Cairo yin wani Kos na dabarun yaki ta taso ,Allah da
ikonsa a lokacin har ya nemar ma Amal wata makaranta da ake Kira *BETTER QUEEN
INTERNATIONAL SCHOOL*.
Anan sardauna creasent , kasancewar Basu da nisa da gidan mahaifansa duk wani
Shirin school babu Wanda be Mata Dan har ta fara zuwa ma


Ita dai Amal taga shige da fice da yake yau a gidan yayi yawa,Ashe Yana ta kokarin
daidaita abubuwa ne yau jirgin karfe Tara ze bi ,Ammah har zuwa wannan lokacin
Amal Bata San bidirin da ake ba ,ta na zaune bayan tayi sallar la'asar a falo se
gashi ya fito ya nemi kujera ya zauna ya tsura Mata Ido Yana ta kallo , ta kasan
Ido taga Yana kallonta Dan haka taki kallon sashin da yake,saboda ta lura a 'yan
kwanakin Nan da sun hadu wani mayen kallo yake binta da shi


Gyaran murya yayi ta dago Tana kallonshi cewa yayi "taho Nan kiji "
Ya nuna gefen kujera jiki a sanyaye ta tashi ta tafi ta zauna kallonta yayi na
dakiku kafin yace "Zan yi tafiya yau Wanda zata dauke Ni tsawon wata takwas kafin
na dawo,Ina so kafin na dawo ki kula da kanki ki Kuma maida hankalinki Akan karatun
ki kinji"

Shiru yaji se yasa hannu ya dago fuskarta ,hawaye yaga Tana yi ,Nan take yaji ta
bashi tausayi se cewa yayi
"Kanwata har kin fara kewata ne"

Se tace"A'a tsoron kwana nake a wannan gidan Ni daya"

Haushin amsar da ta bayar yaji sosai har fuskar sa se da ta canza ,tashi yayi ma ya
shiga dakinsa ya shiga hada takkadunsa masu muhimmanci a cikin jakar hannu


Shiru tayi Tana mamakin me ya canza sa Nan take ,Bata gano komai ba, knocking din
da'aka fara ne yasa ta tashi ta nufi kofar Tana budewa taga Al'amin ne murmushi
suka sakarwa juna,sannan ta bashi hanya ya shigo,bayan ya zauna ne suka
gaisa,tambayarta yayi Ina yayansa tace Yana daki ,cewa yayi ta Kira masa shi,tashi
tayi ta nufi dakin nasa,shiga tayi da sallama ,ciki ciki ya Amsa ya cigaba da
abunda yake ,shiru tayi a sanyaye Bata ce komai ba, juyowa yayi ya kalleta da sauri
ta sunkuyar da fuskarta ganin ya koma asalin farouk dinsa cewa yayi

"Lafiya?"

Tace"yaya Al'amin ne yana falo Yana jiranka"

Cewa yayi "kice ya shigo"

Fita tayi daga dakin ta sanar masa ,ita Kuma ta wuce dakinta,idan tace Bata ji wani
Abu ba Akan tafiyar da zeyi tayi karya,kawai dai Bata son nuna ta damu ne tunda
shi da yake namiji ma har yanzu ganin take kamar be dauke ta a matsayin mace ba ,ta
Yaya zata yarda har ta nuna ta damu da shi ya dauka sonsa take ,shima da yake
namiji be nuna ba se ita, ai ko mi take ji daurewa zata yi har se ranar da ya nuna
Tana da muhimmanci a wurinsa

Duk da Amal ta kasance yarinya ba wata babba ba to Tana cikin Mata masu aji ko nace
kamewa ,wannan ke Nan

Bayan Al'amin ya shiga dakin tayasa aikin gyaran kayansa yayi har se da suka hada
komai,sannan Al'amin din ke fada masa sakon ummee Akan cewa Amal ta hada kayanta
ta koma can gidan da zama tunda ba nisa da makarantar da take

Shiru yayi Yana nazari,se ya ga ma ai zamanta gidan nasu za'afi kulawa da ita sosai
Dan yaga alamar har yanzu kanta na Mata rawa,cewa yayi ba komai in kun rakani se ka
dawo ka dauketa kuje can din, to yace masa


Koda Akayi maghrib har khaleel da matar sa sunzo Dan haka suka je gidan su Farouk
gaba daya Dan ya sake sallama da iyayensa ,Koda suka je har Abbah sun isko Nan ya
Kara sallama da iyayen nasa ,suna ta sa Mai Albarka da fatan Alkhairi takwas nayi
duk suka nufi airport ,mota daya suka shiga wani soja ke Jan motar, khaleel Yana
tasa da Matarsa ,se Al'amin a tasa

Suna tsaka da tafiya taji Numfashin mutum a gefenta ko da ta juyo shine ya matso
sosai kusa da ita , sunkuyar da kanta tayi ,hannunta ya kama ya rike a cikin na sa
Yana murzawa ,daga shi har ita wani yanayi suka shiga duk da tayi kokarin zare
hannunta ammah ta kasa har suka iso airport din,driver na parking ya fita a
motar ,juyo da ita yayi kamar wata 'yar tsana ita dai runtse idanunta tayi
Kallon ta yake sosai ,har ya kawo kan lips dinta da so tari har dai in ta sa
lipstick suke daukar hankalinsa ,a hankali ya Dora bakinsa ya fara sumbatar bakinta
,
Daga shi har ita jikinsu rawa yake ,saboda tsawon shekaru talatin da biyu da yayi a
duniya wannan shine karon sa na farko da ya taba sumbatar mace ,ita Kuma Amal tsoro
ne fal cikinta ,gaba daya kokarin dawo da ita yake jikinsa yaji ana knocking glass
din ba shiri ya sake ta ya jingina da kujera Yana Maida numfashi se da ya natsu ya
dago Yana kallonta da ta dukar da Kai Tana kuka
Dago kanta yayi yace"lafiya kike kuka?"

Cewa tayi a ranta lallai wannan mutumin Dan duniya ne,share shi tayi ta juyar da
kanta, sake juyo da ita yayi kafin yace

"Ki kula da kanki kafin na dawo ,ki maida hankali kiyi karatu Kinga ba dadewa
zakuyi exam,sannan ban da kula maza a school Kinga ke matar aure ce ,kudi ya dauko
bandir ukku na 1k ya Dora Mata a kan cinya ,ga wadannan ko kina bukatar wasu
abubuwa ,na fadawa Al'amin kuje tare a bude Miki bank account ko da kin karar da
wadannan Zan iya tura Miki ta can

A hankali tace nagode ,kallonta ya ci gaba da yi kafin ya dago hannunta ya sunbaci
yatsunta ,sannan ya bude kofar ya fita ,itama fitowa tayi , khaleel na ganin yadda
idanun mutumin suka canza ,ai se ya shiga dariyar keta har se da farouk din yace
"malam lafiya Wai?"

Matsowa yayi kusa da shi yace "Wai me ka tsaya yi a mota ne?"

Hararsa yayi yace "ban sani ba"
"Ba wani ka tsaya kana latsa karamar yarinya ko kunya ba ka ji, har ka fara kewarta
ne" cewar khaleel

"Allah ya tsare ka dauka kowa irin ka ne sannan Ni ba abunda zanyi kewa har naje na
dawo ,ai ko se a kunnen Amal da ke tsaye tare da matar khaleel Tana Kuma juyowa
suka hada Ido da sauri ta dauke kanta ,kiransu aka fara yi ya tashi Nan ya sake
sallama da su ,duk yadda yaso su hada Ido da Amal taki kallonsa ,har kiranta yayi
suka fara ta kawa ta inda ze shiga jirgi shiru yayi ita ma shiru tayi har suka zo
wurin tsayawa yace "Baki da wani Abu da Zaki ce"

Tace "A'a babu Allah ya kiyaye ta juyowarta ko kallonsa Bata sake
yiba....................✍️


*Aysha galadima ce*

.
Vote
Comment
Share

[8/27, 8:25 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*
_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG51-52*




________________________________


Bayanta ya bi da kallo har ta isa inda su khaleel suke tsaye,a sanyaye shima ya
juya ya tafi.

Tana zuwa suka shiga mota suka nufo gidansu suna kan hanya ne Al'amin ke fada Mata
ai da ita ze wuce gidan ummee
Ba karamin dadi taji ba da jin wannan maganar ,shi ya sa ma ta saki ranta ,saboda
maganar da farouk yayi ta matukar Bata Mata Rai,tuni ta saki ranta ta hada kayanta
cikin babban akwati , Al'amin ne ya jawo akwatin ya saka a mota ,Nan ya rufe ko Ina
a gidan ,sannan suka nufi gidan ummee

______________________________

A bangaren Ramla kuwa Tana can suna ta kula da cikinta ,Wanda yanzu kwata kwata ba
ta son yaya Sadiq ko kadan ma ya matso kusa da ita,lura da hakan da yayi yasa shima
ya janye jikinsa a wurinta iya karsa da ita gaisuwa kowa dakinsa yake kwana ,likita
ma ya Hana ta aikin komai acewar sa mahaifarta bata da kwari,ba'a so Tana aikin
wahala ,idan ba haka ba za'a iya rasa cikin,har yaya Sadiq se da ya jama kunne akan
kar ya takura Mata sosai,shiyasa yanzu husna ma ta dawo gidan ita ke girki Tana
kula da gidan

Yau kasancewar husna zata je school bayan ta gama komai ta Mata sallama ta
wuce ,Tana zaune a daki taji ba'abunda ta ke so se Dan wake ,ai ko tashi tayi
ahankali ta shiga kitchen,fulawa ta kwaba ta shiga hadin Dan wakenta har ta gama
zata soya Mai kenan taji ana kiranta a falo Tana fitowa taga Yaya Sadiq ne

Kallonta yake da mamaki ganin ta fito daga kitchen
Kafin yace
"Me kike a kitchen?"

"Dan wake" ta bashi Amsa

Rufe Ido yayi ya shiga Mata fada Akan Bata jin magana bayan tasan lalurar da take
dauke da ita da Kuma abunda likita yace shine zata shiga kitchen Tana girki

Neman daya daga cikin kujerin falon tayi ta zauna ,Kuka ta fara masa ,dole yayi
shiru Yana Mata kallon da mamaki

Kafin ya dawo gefen kujerar yace" yanzu Honey miye abun kuka daga na Miki magana"
Kukanta taci gaba da yi kafin taja numfashi tace"to Ni na dorawa kaina da zaka zo
Kai ta min fada " taci gaba da kukanta ,ba shiri ya ci gaba da lallashinta har ya
samu tayi shiru

A karshe dai shine ya shiga kitchen din ya soya man ya hado Mata Dan waken ya kawo
Mata ta ci .

______________________________


A bangaren Amal kuwa yanzu rayuwar ta na Mata yadda take so ,Tana jin dadin zama da
ummee kasancewarta wayayyar mace ta ja Amal sosai a jiki kamar ba surukarta ba daki
guda aka Bata a gidan,sannan ga lesson teacher ummee tasa Al'amin ya samo Mata ,shi
yasa take jin dadin karatunta

Da farko makarantar tayi tunani Tasha wuya ganin ba ta jin turanci sosai a yanzu
Kam Zan iya cewa turanci ya zauna a bakinta

Shiyasa karatun na su ba ya Bata wahala sosai ,ga Kuma kawa da ta samu me suna
Yasmin a makarantar wadda tasu tazo daya da Amal sosai ,se dai Yasmin Yar gayu ce
ta gaske tana son Abubuwan kwalliyya sosai ,sanna gata wayayya ,Dan babanta
hamshakin me kudi ne a kaduna .

Kimanin wata biyu da tafiyar Yaya farouk tunda ya tafi ba suyi waya da Amal
ba ,shima kansa se da yayi nesa da Amal din yasan ba karamin sonta yake ba ,saboda
duk ya zauna ba ya da aiki se tunaninta gaya duk lokacin da ze Kira gida Tana
makaranta ,yau dai ya na matukar son yaji muryarta sosai

Anci sa'a Koda ya kira Tana gidan Al'amin ne ya dau wayar bayan sun gaisa yace ya
bawa Amal,dama duk suna zaune falon

Bata yayi yace" ga Yaya"
Karba tayi ta nufi dakinta dagawa tayi tace"Assalamu Alaikum "
Daga can bangaren se da ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,sannan ya Amsa,gaida
say tayi ya Amsa yace"ya karatu?"
Tace"Alhamdulillah"
"Kina dai maida hankali ko"
Tace "eh"
Daga Nan shiru tayi Bata sake cewa komai ba shima haka,jin kusan minti daya ba'ayi
magana ba yasa ta katse wayar ,se da ya runtse idonsa jin ta katse wayar

Tashi yayi zaune Yana yamutsa sumar kansa kafin cikinn ransa yace
ba dai yarinyar Nan Ni ta katse ma waya ba,ko Tana nufin har yanzu bata yi kewa ta
ba, tabdi ai dole ma ki Soni yanzu yarinya

A bangaren Amal kuwa Koda ta sauke wayar ta dade zaune a wurin Tana tunani tunda ya
tafi fa se yanzu ya kirata ,Koda yake yace baze yi kewar kowa ba ko ya tafi,to ko
me yasa yakira yanzu ,Tana wani yamutsa fuska ,mikewa tayi ta shiga wanka dama ta
tambayi ummee Tana son taje gidan su Yasmin ana walimar yayanta da ya kammala
karatunsa


Bayan ta fito daga wankan zama tayi ta shirya kanta cikin wata Dubai gown black ,
sannan tayi rolling mayafin ba karamin kyau Amal tayi ba kamar ka sace ta,rigar ta
matukar yi Mata kyau ko Dan Tana farar fata ga Kuma kyau da take da shi ,zaka dauka
kamar wata balarabiya ce ta shigo kasar.
Tana fitowa se da ummee ta yaba kwalliyyar tata ,se dai ta rufe fuska Tana me jin
kunya

Al'amin ne ya fito dama shi ze Kai ta
Yana ganin ta yace"Ahh matar Yaya wannan gayu fa ,ko dai ki fasa zuwa" cikin
zolaya ya kare maganar

Hararar Wasa ta masa tace "ummee kin gansa ko"

Ita ma ummeen murmushi tayi tace"kaje ka kaita ban son tsokana"

Kudi ummee ta dauko ta Bata Wai ta siyi wani gift ta ba ma Yasmeen
Bata karba ba tace"ummee akwai kudi a hannuna ,Kuma ko Basu isa ba ga Yaya Al'amin
Nan Zan karba a hannunsa" ta juyo Tana kallonsa cewa yayi "dama kin karbi kudin ki
"Yana dariya

Sallama suka ma ummee suka fita suka shiga mota ya ja, wani mall suka tsaya ta yi
shiru Tana tunanin abunda zata siya ,se ta tambayi Al'amin me ya kamata ta Bata Nan
yace wa ya gama karatun a gidan tace yayanta ne shiru yayi shima Yana nazari

Se can yace ko ki sayi turare,Nan ta diba wasu masu kyau ta siya aka samata cikin
wata jaka me kyau

kasancewar a gidan su Yasmin za'ayi walimar da ke unguwar Rimi

Can ta masa kwatance har suka isa, Koda suka je a cikin gate din gidan ake walimar
ga mutane an taru sosai

Amal cewa tayi se Al'amin ya fito ya rakota cikin gate din kafin ya wuce ba yada ya
iya fitowa yayi suka jero suka shigo

Kasancewar an dade da fara walimar,suna shigowa idanu suka koma kansu ,Yasmin data
hango kawarta tasowa tayi ta tarbeta Nan suka gaisa da Al'amin ya wuce ,tunda suka
shigo idon Yaya Nasir ke kan Amal ko kyaftawa babu har se da abokinsa ya dafa masa
hannu............✍️



*Aysha galadima ce*



Vote
Comment
Share
[8/28, 1:41 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG 53-54*




________________________________


Sannan ya dawo hayyacinsa, juyowa yayi Yana kallonsa
Shima kallon sa yake kafin yace "Nas Wai me kake kallo Ina ta magana kayi shiru,
murmushi yayi yace masa "ba komai"

Yasmin janta tayi suka samu kujeri suka zauna ba jimawa aka tashi walimar janta
tayi suka shiga cikin gidan nasu


Tunda Akayi Addu'a,Nasir yake baza Ido yaga ta inda Amal zata bullo masa be gani ba
,tuno cewa yaga Yasmin ta tarbeta ya tabbatar masa da kawarta ce Dan haka a
gaggauce ya sallami Abokansa Yana fatan Allah yasa Amal Bata wuce ba


Suna shiga cikin gidan dakin Yasmin suka shiga Nan Amal ta dauko kyautar da ta sawo
ta Bata Nan ta shiga yi Mata godiya,taji dadi sosai da kyautar kawar tata,Abinci da
snacks ta kawo Mata ,duk da tace ta koshi Ammah se da Yasmin ta matsa Mata Akan se
taci,
Kadan ta tsakura ,se ga Kiran Al'amin ya shigo wayarta,dagawa tayi yace Mata Yana
waje


Nan take Yasmin tace ta bari tazo dakin mahaifiyar ta taje ta hado Mata kayan
walima har jaka biyu,ta Bata tace daya na Yaya Al'amin ne godiya ta Mata suka fito
tare


Sun fito filin gate din kenan Nasir ya hango su da sauri ya karaso wurin Yasmin
Tayi saurin cewa "Amal ga yayana ,yaya Nasir shine ake ma walima Nan Amal ta
gaidasa da masa fatan Alkhairi Akan karatunsa godiya ya Mata ,yace "ko wucewa Zaki
yi?"

Tace "eh"

"Ok bari na dauko mota na kaiki"
Ita dai Yasmin mamakin Yaya Nasir ya kamata ganin irin kallon Yasmin din da yake da
Kuma cewar da yayi Bari yazo kaita shida keda Baki

Amal din ce tace"A'a Yaya anzo dauka ta ma "

Ta mishi sallama suka ci gaba da tafiya Ammah se da ya biyo bayansu suna fitowa
Al'amin ne ya fito yana cewa

"Da yanzu Zan sake kiranki naji ki shiru"
Murmushi ta masa tace "ka ga wadda ta tsaidani Nan "
Tana nuna Yasmin

Se yanzu Al'amin ya kula da Nasir ma ,gaisawa suka yi suka musu sallama

Suka shiga mota suka nufi gida

Suna wucewa Nasir ke cema Yasmin
"Wanene yazo daukarta?"


"Yayanta ne"
Ta bashi Amsa
Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi gida ita ko se mamakin sa take can Kuma tayi
murmushi ta juya cikin gida


Ana magariba suka Isa gida Al'amin massalaci ya wuce ita Kuma ta shiga gida,Tana
shiga Bata isko ummee falon ba,aje kayan walimar tayi a kujera ta shiga cikin
dakinta sallah tayi bayan ta gama ,ta dauko wayarta data manta da ita a gida Miss
call biyar taga an mata da wata number ta kasashen waje Nan tayi tunanin ko farouk
ne ,Dan haka se ta sake kiransa ba'a daga ba har ta tsinke ,jiki a sanyaye ta aje
wayar ta cire hijabi kenan taji karar wayar ,dauka tayi ta zauna bakin gado ta daga
wayar tace"Assalamu Alaikum"

Daga dayan bangaren ya Amsa murya a cunkushe zata gaida sa katseta yayi da cewa

"kina Ina ,Ina ta Kira Baki dauka"

Cewa tayi "bani Nan na je wurin walima"

"Kin fita da izinin wa kenan" yace

Shiru tayi ta rasa abun cewa se can tace "na fadawa ummee"

"Ni me yasa Baki kirani kin fada min ba,wato yawo kike zuwa ko?"

Shiru tayi jin fadan da ya soma Mata kafin tace "yi hakuri"

Kit taji ya kashe wayarsa ,shiru tayi Tana kallon wayar kamar zata ganshi a ciki,to
ita Bata ga abun fada anan ba ,da har yake ta fada a waya,da yake cewa yawo take
zuwa ai ba ta ma zuwa ko Ina da ya wuce makaranta ko gidansu ba ta je ba tunda ya
tafi


To ita gaskiya Bata son a ta Mata fada barin ma nashi da bayada dalili ,bangarar da
wayar tayi ta tashi ta fita daga dakin zuwa falo
A haka Rayuwa ta ci gaba da tafiya Wanda a yanzu idan ba ka ma Amal farin sani
ba ,ka ganta a yanzu bazaka gane ta ba ,komai nata ya canja tunda daga cikar data
Kara da Kuma dabi'u da yawa da ta canja, sannan ga ilimin boko da ya ratsata,

Ummee har wurin koyon kwalliyar zamani da girki ta sakata ,yanzu Amal anzama irin
'yan matannan da ake Kira first class ita kanta ummee a yanzu ta tabbatar da danta
ba karamin Dace yayi ba.




A bangaren farouk kuwa watanni takwas da ze yi a Cairo gani yake kamar shekara
takwas ze yi , ba karamin kewar gida yayi ba mussaman matar sa Amal da yake kwana
da ita a Ranshi duk da har yanzu ba wata wayar kirki suke yi ba , sannan Babu wani
sabon Abu a tsakanin su

So tari Amal takan danyi tunanin farouk a ranta kadan ba sosai ba ,saboda har yanzu
maganar da yayi da ze tafi Bata bace Mata akai ba, A yanzu ma yadda take ji ko ya
dawo duk zaman da yake so suyi shi zasu yi ,saboda Amal din da ya sani da ba ita ce
a yanzu ba


A yanzu haka jarrabawar kare secondary suke ita da kawarta Yasmin ,se dai har yanzu
bata fadawa Yasmin cewar Tana da aure ba,ga Kuma Yaya Nasir da ya taso ta a gaba
duk ya ganta ,ze ci gaba da kallonta ne har ta bace duk da be fadi ba ,ita tagano
kamar sonta yake Dan haka ta rage zuwa gidansu Yasmin din sosai .


Ba dadewa suka gama jarabawar su ,sati daya tsakani aka bugo waya anty Ramla ta
haihu ,Dan Alokacin tafiyar farouk wata takwas cif se dai har lokacin be dawo ba

Nan Amal ta shiga dokin haihuwar Anty Ramla,Rana daya suka shirya ita da ummee suka
je kano ,Al'amin ne ya kaisu, ummee dai ta dawo Amal Kam kirjin biki se anyi suna
zata dawo

Al'amin nata tsokanar ta Yana cewa"ummee kice ta dauko mayafinta ta mu wuce gida"

Amal se marairaice wa take , ummee dai murmushi tayi tace ma Al'amin "naki na ce
din ka wuce mu tafi kar muyi dare a hanya "

Fita sukayi Amal ta rakosu har wurin mota Tana ta ma ummee godiya,har se data ga
tafiyar su


Koda ta dawo gida Anty Ramla kallonta tayi tace "kanwata miye sirrin kodai soja
yayi ajiya ne"

Rufe fuska tayi

Ramla dariya tayi kafin tace "Amal gaskiya ummee mutumiyar kirki ce Kinga abun
arzikin data kawo ma baby Tana nuna wata jaka cike da kayan baby data kawo

Amal cewa tayi "ai Anty banta ba ganin mace me mutunci irin ummee ba Nan ta shiga
Bata labarin irin yadda take kula da ita ,da abubuwa da yawa data ke koya Mata
kamar ba surukar ta ba


Nan Anty Ramla ta shiga sa ma ummee Albarka Nan take cewa"yaushe mijin naki ze
dawo?"
Tabe Baki tayi tace "nima ban sani ba"


Wani mugun kallo Ramla ke bin Amal din dashi kafin tace "Baki sani ba fa kika ce?"

"Eh " tace ,tashi ma tayi ta bar Ramla sake da Baki Tana kallonta har ta shiga
bedroom dinta

A haka sukayi kwana biyu ana jego ,baby Masha'Allah dashi yaron duk Yaya Sadiq ya
biyo ,Ramla na ta son su kebi tayi magana da Amal din Dan ta kula yanzu kanta har
wani rawa yake Mata,se dai Baki da akeyi a gidan akai akai ke hanata mata magana

Wata tsohuwa ummansu Sadiq ta turo ita ke kula da Anty Ramla,husna ma tuni ta dawo
gidan da zama

Ana saura kwana ukku biki suka je kasuwa suka sayo Abubuwan da za'a ba 'yan biki
daga Nan Amal ta bayar da wani dinkin lace dinta da zata saka ranar biki


Tafe yake Akan matattakalar jirgi Yana saukowa se da ya sauko ya ja numfashi Yana
shakar iskar kasarsa ,ji yake kamar yayi wasu shekaru ba'a Nigeria ba,ya Kara wani
irin

Please Login or Register in order to submit comment