Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace muje gidan
kaka mu Sha fura
Dariya kawai khaleel ya yi ya shiga mota suna tafe suna fira har sun gota su
khaleel ya sake yowar baya yana kallon su Amal ya gane su

Farouk yace" lafiya ka dawo?"

Yace wasu kannena nagani bari mu dauke su Naga an fara Ruwa shi dai be ce komai ba

Yana fitowa yasha gabansu yace "kanenna barka kuzo na rage muku hanya ,ga Ruwa har
ya fara sauka
Har Amal zata ce A'a
Ramla ta rigata tace
"Muje mun gode fa"

Yace "ba komai " yana murmushi

Jawo hannun Amal tayi suka nufi motar suka shiga, har sun zauna dago kan da zata yi
ta kalli madubin motar numfashinta ne ya fara sama sama da kyar ta kwato
maganar"aunty Ramla da karfi"!
.....................✍️


*Aysha galadima ce*

Comment
Share.



[8/16, 8:09 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(080649333819)




_Wannan shafin naki ne kaco kam, comment dinki yana sani Nishadi_
*Raleeyer*



*PG 15-16*


_____________________________

Ramla da sauri ta kalleta tace" Amal lafiya?"
Se nuna gaban motar take Tana boye kanta cikin jikin Ramala

Khaleel shima da sauri ya juyo yana kallon su yace
"Lafiya kuwa?"

Ramla har ta bude Baki zata bashi Amsa Idanunta suka sauka kan farouk da ke gaban
mota sanye da kayan sojoji

Tuni ta mai da maganar da ta tashi yi , tace ma khaleel ba komai

Ta dukar da Kai ta tace"ki natsu ba abunda ze Miki kinga shi ko juyowa be yi ba ,
kiyi shiru mu samu su sauke mu gida"

Daga Mata Kai tayi daga cikin hijab din Ramla da ta shige

Duk abunda ke faruwa farouk ko juyowa be yi ba, yi yayi tamkar be San hidimar da
suke ba

Kuma duk maganar da Ramla tama Amal yana ji, saboda ji ne da shi kamar me kunnen
maciji se ma lumshe idanun sa yayi

Suna tafe khaleel na tambayar Ramla inda ze Kai su

A hankali take take nuna masa hanya har suka iso kofar gidan na su yayi parking,
bude kofar Ramla tayi tace " malama daga ni mun iso ki fita"

Se da ta dago kanta a hankali ta kalli Ramla ,sannan ta kalli kofar data bude ,ai
ko da gudu ta fita ta shiga gida

Khaleel mi ze yi inba dariya ba ,ya juyo yana kallon Ramla da ta fito a motar yace
"Wai waccan kanwar taki lafiyar ta kalau kuwa?"

Se da ta kulle kofar motar ta kalle sa ta danyi murmushi ta nuna ma sa motar da
hannunta tace"mutumen ciki ta ke tsoro, mun gode fa "

Rufe bakin sa yayi yace "tasan shi ya mareta ne?"

Tace"A'a Tana tsoron masu saka uniform da masu rike bindiga "

Yace "ikon Allah daga ni har shi kuma duk sojoji ne fa, an dai yi sa'a na cire
uniform ni"

Rufe Baki Ramla tayi Tana murmushi sannan tace "mun gode "
Suka yi sallama ta shige gida

Shima mota ya shiga , Koda ya shiga ya tarar da mutumen ya cika yayi fam se huci
yake

Tada motar yayi be ce masa komai ba

"Wai Kai wane irin Dan rainin wayau ne , ka tsaya kana ta wata dariya da kananan
yara Dan na San ma kila zaka haife su ko kunya baka ji, se na fada ma Asmah kana
nan kana neman wasu Dan na tabbata wadannan baka hada komai da su ba karya kawai ka
min"
Cewar farouk

Khaleel yace "miye abun jin kunya anan ,da kake cewa na haife su ,ke nan Kai
kakansu ne kuma kaje ka fada Mata din nasan zata fahimce ni daga na taimaki yara
zaka dinga min fada , kodai akwai wadda tama cikinsu"
Wani uban tsaki farouk yaja be sake tanka ma khaleel da ke tsokanar sa ba


_____________________________


Koda Ramla ta shiga gida ta tarar har Amal ta cire kayan jikinta

Ummah ce ta shigo dakin tace "yanzu cikin ruwannan kuka fito me makon ku bari a
gama

Da sauri Ramla tace "sanda muka fito umma ba'a fara ruwan ba"

Dan tasan tsab Amal zata iya fada Mata a mota aka kawo su

Ummah tace "to yayi kuyi sauri ku canza kayan kar kuyi mura,

Ramla tace" to"


A kwana a tashi ba wuya wurin Allah har su Ramla sun gama jarabawar waec da neco
yayin da Amal ta yi j s l c


Bayan kammala
Jarabawar su da sati biyu Abba ya siya ma Ramla waya kirar Tecno L5

Ranar ba karamar murna suka Sha ba ita da Amal

Kwana biyu tsakani da yamma Tana kwance a dakin su se ga Kira ya shigo wayar ta ,
kallon wayar ta yi ta ga number ce ba suna bata dauka ba har wayar ta tsinke , aka
sake wani Kiran daga wa tayi , tayi shiru

Daga can bangaren Aka yi sallama ta Amsa

An dau sakanni ba'ayi magana ba se tace"wake magana?"

Har ta cire ran baza'ayi mayana ba

Se aka ce " aljanine "

Zaro ido tayi ta saki wayar..................✍️


*Aysha galadima ce*



Comment
Share
[8/17, 7:47 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG 17-18*




_____________________________

Ta saki wayar kan gado ta fita da sauri dakin Tana dafe kirji umma da ke zaune
tsakar gidan ta dube ta tace "lafiya kika fito kamar da gudu?"


Zare ido ta fara tace"ummah Aljani Wai ya kirani a waya"

Umma tace" ke banson shirme aljanin lafiya "

"Ummah wallahi da gaske nake"
Tana me rau rau da ido

Ummah tace "je ki dauko wayar na gani taje tadauko wayar ta bata

Se wayar ta dau Kara , umma ta daga tace "Assalamu Alaikum"
Daga jin muryar ummah ya gane ta nan ya gaishe ta ya ce "ummah sadiq ne"

Se ummah ta fadada fari'ar ta nan take tambayar sa mutanen gida yace duk lafiyar su
kalau
Sannan ta Mika ma Ramla wayar ta tace "karbi yayanku ne "
Karba tayi ta shiga daki ta gaida shi ya amsa yana me lumshe idonsa
Ji yayi muryarta na masa kama da ta Amal , nan yake taya ta murnar kammala
secondary ta ma sa godiya ,suka yi sallama

_____________________________


Abubuwa da dama sun faru har da bikin khaleel da'aka Sha ,tun da akayi bikin
khaleel Abba ya Kara yi ma farouk maganar auren sa yace masa ai ya kusa gabatar da
yarinyar basu dade da haduwa bane shiyasa

Kuji karya 😀

Yace to yayi Ina sauraron Amsar ka nan kusa bana son abun ya dau lokaci fa ya ce
"to Abbah"

A wata ranar laraba
Duk suna zaune a falo, farouk ,ummee da kuma Al'amin dake rike da laptop yana wani
assignment a ciki

Abban su ne ya shigo gidan da hanzari ,duk su ka maida hankalin su wajansa ,yace
yana da meeting a Abuja ya zo
Daukar wasu muhimman takaddune

Sama ya haura, ummee ta take masa baya domin taya sa kimtsawa

Bayan kusan 30 minutes se gasu sun sauko, ummi na rike da brief case din Abbah duk
mikewa suka yi farouk ya karbi brief case din a wurin ummee ya fita zuwa parking
space
Da sauri driver din Abba ya taso ya bude motar farouk ya saka jakar se gasu duk sun
fito har ummee sun takowa Abbah

Cikin alhini sukayi sallama da mahaifin nasu
Ya shiga mota driver ya ja suka fice daga cikin gidan

Tafiyar ta su bata yi wani nisa ba suna gab da fita garin kaduna wata babbar mota
ta Karawa motar su , motar tasu ta wani wuntsila gefen hanya

Dai dai lokacin Abba ya fito wani wuri yana kan babur din sa ya ga abunda ya faru
da sauri yayi parking ya Kara sa kusa da motar da ya hangi wasu matasa biyu har sun
bude motar sun jawo jakar Abba daya ya rataya

Yana zuwa dama be yadda da yaran ba tun da ga yanayi. Shigar su se yace 'yaro bani
jakar nan daka dauka "

Basu San da zuwan Abba ba ganin sa kawai yayi , ba kunya ba komai ya Mika jakar ,
Abba ya karba ya shiga yaga Abban su farouk da ke kwance cikin jini , ga driver
shima kwance be San inda kansa ya ke ba

Abba ne ya juyo yace ma dayan ya tare masa taxi yako tarar masa ,su suka tai
makama Abba aka dauki Abbansu Farouk da driver a taxi
Abba ya rufe motar ya dauki makullin ya juya ya kalli samarinnan ya basu dubu biyu
su raba suka karba suna godiya

Abba girgiza kansa kawai yayi saboda yaran gwanin tausayi gasu samari ammah sun
bata kan su da shaye-shaye Allah ya shirya duk masu yi
Da sauri me taxi yaja suka wuce asibiti da kyar abba ya samu aka karbesu Dan se da
ya nemo 'yan sanda

Dakin da'aka kwantar da Abban su farouk ya shiga yana kallon inda ya samu raunuka
karar waya yaji na fitowa daga jiki. Abbah zaro ta yayi

Ya Amsa daga go "ummee tace "Ina me wayar"?
Dan tunda ya tafi gabanta ke faduwa

Nan Abbah ya shiga fada mata abunda ya same shi

"Innaliahi wa'ina ilaihi raji'un "
shine abunda ta fada ta saki wayar , duk su farouk suka Mike suka zo kusa da it ,
suna tambayar
"Ummee me ya faru?"

Shiru tayi Tana nuna musu waya da sauri farouk ya dauko wayar , ya sake Kiran
number. Abbah nan shima yaji abunda ya faru
Tuni gumi ya karye masa da sauri ya dauki key din motar sa ze fita , se kuma ya
dawo yace"Al'amin daukowa ummee mayafinta"

Da sauri ya dauko Mata suka fita duk suka shiga mota ya fice gidan da sauri
Dama Abbah ya masa kwatancen asibitin da suke

Koda suka isa dakin da aka kwantar da su suka. Shiga, suka nufi gadon da Abba yake
Kai , buguwace yayi akansa an daure wurin da bandeji se a hannu da ya jimu, Allah
ya tsare da ba karaya a ko'ina

Tuni Al'amin ya fara hawaye, ummee ma idonta sun kada ammah dai bata yi kuka ba ,
farouk ne ya matso ya fara diba raunukan da ya samu da yaga ba raunuka sosai kuma
ba karaya se ya sauke ajiyar zuciya yace" ummee be ji ciwo sosai ba ku kwantar da
hankalinku ya jawo Mata kujera , ya ja hannun ta ya zaunar da ita akai , Al'amin ya
kalla da ke kuka se da ya hararesa sannan yace"Kai kuma miye da girmanka zaka zauna
kana kuka, so kake ka tayar ma ummee da hankali, hawayen da yake yi ne ya shiga
goge wa , turo kofar dakin Akayi , Abba ne ya shigo da sallamarsa
Farouk ya Amsa karasowa yayi cikin dakin , da ze musu bayani tuni farouk ya dakatar
da shi da cewa"Abba Kai kawo su asibiti ko mun gode Allah ya saka Alkhairi

Abba yace"base ka godemin ba"

Shima kujera farouk ya jawo ya Mika masa ya zauna Jim kadan ya zaro makullin motar
da jakar da ya rabe a can gefe ya ba farouk bayan ya musu bayanin yadda hadari. Ya
afku

Nan ya musu sallama yace ze je gida Amma ze dawo har da iyalinsa nan ummee suka
shiga yi mashi godiya......................✍️




*Aysha galadima ce*

Comment
Share
[8/17, 7:46 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*
*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG19-20*



________________________________


Ko da Abba ya koma gida duk su Ummah da yaranta suna zaune tsakar gida suna Shan
iska kasancewar ranar anyi zafi sosai

Da sallama ya shigo gidan suka amsa masa se dai kallonsa kawai suke ganin rigar sa
da jini gaya fararan kaya ya saka ,lura da irin kallon da suke masa se ya dubi
jikinsa nan yaga jini a tufafinsa ,wuce su yayi ya shiga daki domin yayi wanka, ita
ma ummah ta shi tayi tabi bayan mijin nata taji ko lafiya

Su Ramla Shirin suka yi sun kasa magana , se Amal da ke ta zarar ido Tana kallon
hanyar da su Abba suka bi


Ummah na zaune bakin gado Abba ya fito wankan, se da ya kimtsa sannan ya fada Mata
abunda ya faru

Ummah cikin tausayawa tace"to ya jikin mutumen Allah yasa ba mummunan rauni ya ji
ba?"

Abba yace"eh abun yazo da sauki driver ne kawai ya samu karaya"

Ummah tace"To Allah ya basu lafiya ya kuma tsare gaba"

"Ameen" Abba ya fada

Nan yake sanar da ita yana so ta shirya ko zuwa gobe ne suje su dubashi tace ba
komai Allah ya Kai mu

______________________________
A can asibiti kuwa duk suna zazzaune sunyi shiru saboda har lokacin Abba be farfado
ba Ammah likita ya tabbatar da ko yaushe yana iya farkawa

Wayar farouk ce ta shiga Kara zaro ta yayi daga aljihunsa yana diba wake kiransa
se ya ga khaleel , dagawa yayi ya fita daga dakin nan yake masa bayanin Abunda ya
faru , yace masa gashi nan zuwa suka yi sallama ya koma dakin

______________________________


Washe gari bayan Amal tayi shirin makaranta, ta wucewarta kasancewar yanzu ita dai
ke tafiyarta , tunda Ramla ta kare

Tana isa get din makarantar tasu yau kam bata tsira ba Dan ta yo latti se da aka
dake ta ,saboda Koda tazo har Assembly an gama yara duk sun shiga ajinsu

Tana tafe Tana matsar kwallah Tana gab da shiga ajinsu taji an ce Mata "hey"

Koda ta juya wani kyakyawan saurayi ne sanye da kayan N Y S C ai ko suna hada ido
da gudu ta ida shigewa Tana zuwa ta boye karkashin seat dinsu

Koda saurayinnan ya shigo ajin se ya dinga rarraba ido ko ze ganta ,Amma be ganta
ba se bayan ya wuce ne
Kawarta da suke zama kujera daya
Tace "fito kura ya tafi"

Fitowa tayi Tana hararar ta tace "Ina ruwanki da ni "

Hafsa na dariya tace "ni ko keda Ruwa dake , in bada daukan dala ba gamwo ba yanzu
har Dan bautar kasa da ko kulki basu rikewa kike ma wannan gudun ai naso ma na
tonaki nace gaki nan kasan benci"
Ta kare da tuntsire mata da dariya
Ita dai Amal shiru tayi ba bakin magana
Hafsa ta Kara cewa"kuma Naga Alamar mutuminnan sonki yake fa saboda tun ranar da
suka zo makarantar nan yake ta son ya Miki magana ke kuma da kin gansa se gudu "

Tashi Amal tayi gaba daya a kujerar ta koma gaba ko kallon hafsa bata yi ba

_________________
Bayan tafiyar Amal makaranta su Ummah suka shirya harda Ramla suka je Asibitin,da
sallama suka shiga dakin, Koda suka je Abbah ya farfado tun tsakar dare

Dakin daga Abbah dake kwance se ummah dake zaune kan kujera su farouk sun koma
gida suyi wanka kasancewar nan suka kwana


Ummee da fari'a ta tarbesu kasancewar ta gane Abba ta basu kujera suka zauna Ramla
dake tsaye rike da Dan kwandon Abincin da ummah ta danyo masu
Ummee tace" 'yata zo ki aje kwandon ga gado nan ki zauna "

Kusa da gadon Abbah akwai gadon da ba kowa , anan ta zauna

Gaisawa sukayi tare da tambayar me jiki
Ummah tace"ai yaji sauki

Nan Abban su farouk yayi ma Abbah godiyar taimakon da ya masa
Abba yace "kar ka damu zan iya ma kowane Musulmi ma idan Naga ya shiga halin da ka
shiga Alh"
Nan take Abban su farouk ya ji Abba ya kwanta masa a rai sosai

Ba su jima ba sukayi musu sallama akan zasu sake dawowa nan ummee tai ta godiyar
Abincin da ummah ta kawo sukayi sallama suka fita Ramla ce karshen fitowa Tana
fitowa suka kusa cin karo da farouk suka tsaya kallon
kallo..............................✍️



*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/18, 12:57 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




_Wannan shafin naki_ _ne_ *Ummu Muhammad*
_Nagode da Addu'arki kema Allah ya kare ki a duk inda kike_




*PG 21-22*



___________________________

Wayancewa yayi ya raba ze wuce ta gefenta se ta gaida shi ya Amsa ciki ciki ,ita
bata ma ji amsawar ta shi ba

Tana fitowa se ga khaleel kallonta yayi da mamaki yace"kanwata kun San su farouk
ne?"

Girgiza kai ta yi a takaice ta fada masa alakar ta su ta masa sallama ta wuce shima
dakin ya shiga, Koda ta tafi umma na tsaye Tana jiran isowarta, Tana ko zuwa suka
fita titi suka nemi adaidaita suka wuce gida

______________________________

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda soyayyar Ramla da yaya Sadiq,Wanda cikin
qanqanin lokaci wata shakuwa ta shiga tsakaninsu ,Wanda a yanzu ji yake kamar an
cire masa Amal a zuciya ne aka saka masa Ramla a zuciyar tasa, Wanda har uwayen
nasu sun fahimci shakuwar dake tsakanin 'ya'yan nasu , ba karamin farin ciki su
kayi ba kuwa Dan su Abbah har sun saka bikin nasu nan da wata biyu

Koda Amal ta fahimci yayarta ta fada a soyayya ba karamin farin ciki tayi ba har
take cewa "anty Ramla waye yayan nawa Wai?"

Shiru ta Mata se can tace yaya sadeeq ne fa
Dafe kirji Amal tayi tace "Dan sandan Zaki aura lallai bani ba zuwa gidanki"

Se yanayin Ramla duk ya canza Tana kallon kanwarta ta se tace"yanzu Amal saboda
kawai yana dansanda Zaki ce baza ki zo wurina ba, dama na fahimci kin gaji da
ganina shiyasa kika ce haka se kwallar da ta taru a idonta ta zubo
Take jikin Amal yayi sanyi ta matso ta rungume Ramla ita ma se hawaye Tana cewa"yi
hakuri yayata Wasa nake zan zo Allah "

Dago ta Ramla tayi ta goge Mata hawayen fuskar ta ,ita ma Amal ta goge Mata nata

Ramla tace"har kin sa naji dadi kanwata, dan Allah ki cire wannan tsoron da kike ma
'yan sanda , sufa masu kama masu laifine da kuma kula da kiyaye dukiyoyin Al'umma
bakamar yadda kika fahimce su ba ,sannan yaya sadiq Dan uwanmu ne ,shi nasan baze
iya ko kashe kiyashi ba ballantana mutum" ta kare maganar Tana kallon Amal data
natsu Tana saurarenta

Sauke ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya gani Aunty bani nasa ma kaina wannan tsoron
ba Ammah Insha'Allah zanyi amfani da maganarki zan rage tsoron sosai"

Ramla tace"yawwa ko kefa autar ummah"
Daga nan suka ci gaba da firar su gwanin sha'awa
___________________________

A bangaren gidansu farouk kam tuni Abba ya warware kamar ba shi ba Dan Asibiti ko
sati be yi ba aka sallame shi , ai ko bayan yaji sauki se da ya dauki ummee da
kansa suka je gidansu Amal ya Kara yi ma Abba godiya sosai har da bashi kyautar
kusan 1million ya ba Abba akan yaja jari ya Kara fadada sana'arsa fafur Abbah yaki
karba yace shi fa duk abunda yayi ,yayi ne saboda Allah ,ai ko nan Abbah ya Kara
kima a idanun Abban su farouk

"Hattara Mata da maza Dan Allah mu dinga hade kwadanmu ,saboda a zamaninnan kwadai
ya ma mutanen mu yawa, mussaman 'yan matan wannan zamanin Wanda kwadayi kesa suje
su zubar da kimar su Dan Allah mu gyara saboda duk Wanda ya shiga motar kwadayi to
tabbas zata ajiye shi tashar wahala

Sannan manzon Allah( s.a.w) yace in kana son kaji dadin mu'amula ko zama da mutane
to ka kiyayi Abun hannunsu .
Allah ya shiryar damu"

To kunga dai Abbah kyauta ce aka masa be karba ba Ammah kuma rashin Karbar ya jawo
masa wani mutunci a idon me kyautar
Sunyi kusan awa daya suka musu sallama Dan se ranar ma ummee taga Amal aiko taji
yarinyar ta kwanta Mata arai sosai

Ko bayan sun koma gida se da ummee ta tayar da firar gidan su Amal ta ke cema Abba
"gskya na dade banga mutumin kirki irin Abban su Amal ba ga yaran nashi masu
natsuwa da tarbiya"
Abba yace "umeen yara na rigaki a zuci ki ringani fada ,kinsan mutuminnan har
kyautar kudi na masa akan ya Kara a sana'arsa yaki ya karba, ba magiyar da ban masa
ba Amma Sam yaki karbarsu"
Murmushi ummee tayi tace ai ni naji Ina matukar kaunar wannan ahalin kar kaso kaga
yadda yaran nasa suke da tarbiya"
Se Abba yace "ba yarinyar sa daya ba wadda naji yace an kusa bikinta?"
Ummee tace su biyu ne Ramla da Amal

Babbar ce naji ance za'ama aure karamar kuma kamar s s 1 take Dan na tambayi
karatun nasu


Jim Abbah yayi yana wani tunani................✍️

*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/18, 8:45 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG 23-24*
_____________________________

Har ummee ta tambaye sa lafiya yace ba komai , tashi yayi ya hau sama ya dauro
Alwala yana saukowa Farouk na shigowa gidan ,shi ma da sauri yayi Alwalar yabi
bayan mahaifinsa, tare suka fito daga masallacin suka shigo gida tare , duk falo
suka zauna suna tattaunawa akan wani business da Abba ke so farouk ya fara bayan
sun gama tattaunawa ne ya gangaro akan maganar su 'yar Kullum wato zancen aure

Take gumi ya fara karyowa Farouk har dai da yaji Abba na cewa "idan baka samu wadda
tama a garinnan ba kawai ka shirya kaje zamfara se ka wuce maradun a can cikin
dangi ka zabo wadda ta ma ka aura"

Shiru yayi se can yace "Abbah ai na samu anan"

"To, to Alhamdulillah 'yar wane gida ce?"
Cewar Abba

Se farouk yace "ai bamu gama fahimtar juna bane "

Gani yayi Abbah ya tashi ya haye sama ya barshi a nan falon
Take yaji gabanshi na faduwa saboda ya kula Abbah fushi yayi da shi, tunda har ya
tashi ya barshi zaune,tsoron shi daya kar Abbah ya aura masa duk wadda ya samu
Se gumi ke karyo masa

Jiki ba kwari ya tashi ya nufi dakinshi
_____________________________

Su ummah nata shirye shiryen bikin Ramla Wanda yanzu sati biyu ya rage ayi bikin
Amma a can kwankiyal za'ayi daurin auren Dan ko yini duk a can za'ayi tunda abun ya
zama tuwona mai na

Ammah Anty Ramla a nan kano za'a kai ta ,duk sun bada dinkunan su na cin biki anan
kaduna yau ma sun shirya ita da Amal zasu je kasuwa daga can se su je karbar
dinkunan su

Sun shiga kasuwar sunyo siyayyar da za suyi sun fito, se suka wuce shagon dinkin,
da yake yana kusa da kasuwar ne

Sun shiga sun karbo suka fito , suka tsaya akan titin suna jiran abun hawa se ga
wata mota tazo ta faka kusa da su mutumen ciki ne ya fito ya nufo su
Ai ko suna hada ido da Amal ta koma bayan Ramla ta rike Mata hannu ta dukar da Kai

Da murmushi akan fuskar shi ya karaso suka gai sa da Ramla ,se na ga ashe malamin
makarantar su ne Dan bautar kasa

Yace "Amal Ina wuni"
Duk se taji kunya ganin ko gaida shi bata yi ba tace "malam Ina wuni "
Ya Amsa da "lafiya lau"

Ramla har ta tare Adaidaita ya ce mutumin ya wucewar sa yace ma Ramla "Aunty dan
Allah zo na mayar daku gida"
Ya wani marairaice fuska kamar karamin yaro nason kuka

Ramla ita abun nashi dariya ya bata
Sannan ganin yadda Amal Tasha jinin jikinta ,dakuma malam din da tace ya tabbatar
Mata da malamin su ne tace to mungode fa

Shi ya daukar Mata wasu ledojin suka isa yasa a mota baya Ramla ta bude ta shiga
Tana kokarin rufewa Amal ta fada da sauri
Girgiza Kai kawai yayi danshi yanzu yarinyar dariya take bashi

Tunda ya tare hafsa ya tambaye ta dalilin gudun da kawarta ke yi duk ta ganshi,
tako fada mishi dalilin

Suna tafe a motar shiru se can ya ce ma Ramla "Aunty sunana Ahmad Hashim, malamin
su Amal

Tace "Allah sarki"

Dai dai sun kawo wurin danja ta tsayar da su juyowar da Amal zata yi suka hada ido
da farouk yana cikin uniform dinsa ,motar shi ta tsaya a gefen tasu

Ai ko zaro idonta Tana kallon sa , take ya Mata wani mugun kallo tuni jikinta ya
fara rawa ta juya ta kankame Ramla da sauri Ramla ta dube ta ganin irin razanar da
tayi tace"ke lafiya?"

Se tayi shiru juyawa Ramla tayi ta kalli gefen da Amal din take dai dai an saki
danja motoci duk suka fara tafiya ,ita dai bata ga komai ba ,girgiza Kai kawai tayi
bata ce Mata komai ba har suka karaso

Aiko kamar jira take yayi parking ko takan kayansu bata yi ba ta tashi ta bude
motar tayi cikin gida se dai shi Ahmad din ne ya fito ya taimaka ma aunty Ramla da
fitowa da kayan nasu

Ramla nata zuba godiya har sunyi sallama ta juya zata shiga gida yace
"Am anty Ina da magana"

Dawo wa tayi Tana kallon sa ,Dan sosa Kai yayi sannan yace"bazan boye Miki ba tun
ranar Dana fara ganin Amal Allah ya Dora min sonta kuma ni da gaske nake aurenta
nake son yi se dai taki bani damar magana da ita ma , duk ta gani se gudu shiyasa
nayi tunanin fada Miki ko Zaki taimaka min ki shawo kanta"

Shiru Ramla tayi Tana nazari se can tace"Malam Ahmad kayi hakuri kaga Amal yarinya
ce ,ba yanzu za'a Mata aure ba sannan gidanmu ma ba'a barin mu fira ,da nace kafara
zuwa, sannan Amal nasan yanzu samari

Please Login or Register in order to submit comment