Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fita direct dakinsa ya wuce ya na shiga ya wuce bathroom se da ya
watsa ruwa ya fito , ya sanya kayan Shan iska ya zube akan gado yana tunanin
maganar da Abba ya mai ta aure

Tunani yake shi da ko budurwa ba yada ake ma zancan aure ba Wai beda 'yan mata masu
hauka akansa ba , kawai dai wadda yake so ne be da ita a yanzu,

Kuma yasan halin mahaifin nasa tsayayyan mutum ne tunda har yayi masa maganar ya na
nufin auren yake so yayi ,kuma matukar yayi wasa shi me iya aura masa duk wadda ta
masa zeyi. Addu'arsa daya Allah ya taimake sa cikin masu son nashi ya bincika ko ze
daidai ta da daya daga ciki kafin a masa auren dole๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€

________________________________________

Tun safe ummah ta tashi ta tashi su Ramla su rika mata wasu kana nan ayyuka ita
kuma ta shiga kitchen ta fara daura girkin tarbar Baki se kusan Sha daya na safe
aka kammala komai har tsaftace gidan da komai , umma tace to kuje kuyi wanka ki
shirya kafin su iso

Dakin su suka shige ,Ramla ta tube ta shiga wankan Amal kam zubewa tayi kan gado
Tana fadar "wash! Allah duk bayana ciwo ma yake min duk na gaji tun safe mutum na
tsaye "ta murguda Baki

Nace Koda ita da wa๐Ÿ˜ƒ


Se kuma gabanta ya fadi da ta tuna bakin da za su zo
Fatan ta daya Allah yasa kar yaya Sadiq din ya biyo su
Tana nan kwance Ramla ta fito ita ma tashi tayi ta shiga wankan Tana fitowa ta
tarar da Ramla har ta kimtsa ta sa Atamfar ta kallon ta tayi tace "Aunty Ramla
kinyi kyau Masha'Allah"
Murmushi ta mata tace "na kai ki kyau autar Abba"
Ita ma dariya tayi tace "ai ban kai ki ba"
Tace "to naji yi sauri ki shirya bari naje waje "ok kawai ta ce mata
Zaunawa tayi kan stool din mirror na dakin tayi 'yan shafe shafen ta ,light make up
tayi ta dauko wata doguwar rigar material Baki ta saka ,
Masha'Allah ta yi kyau sosai ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป

Amal fara ce kyakyawar gaske duk mahaifiyar ta biyo kasancewar ta bafulatanar
asali, ta na da dogon hanci da idanuwanta kamar na kyanwa da Dan karamin
bakinta ,lips dinta sun kasance jajir da su , doguwa ce marar kiba , yanayin
jikinta yanayin na fulani, se dai Allah ya hore mata manya manyan dukiyar fulani
duk shekarun 16 idan ka dubi yana yin jikin se a dauka 'yar 20years ce
ba ta da kiba sosai , se dai baza'a kirata siririya Kai tsaye ba ,so tari idan
bata buda Baki tayi magana ba wasu daukar suke bata jin hausa wannan kenan

Ita ma fitar tayi ta tarar Abba shima ya dawo an shimfida tabarma a tsakar gidan
nasu da yayi fes da shi ta zauna itama

Tsayuwar motar da suka ji ne yasa su kayi shiru daga firar da suke , sallamar ummah
ce da husna yasa da gudu su Ramla suka je suka rungume su , Suma se murmushi suke
saki duk suka nufi tabarmar suka zauna ana ta gaisawa, har da kawu lawan aka zo
Ruwa su Ramla suka fara gabatar musu

Abba ne yace "Ina dandana ban gan sa ba shi"?

Ai ko Amal ta yamutsa fuska

Kawu lawan yace"tare muke ai shi ya aje mu ya juya akwai wani meeting na 'yan sanda
da suke da a garin nan yau shiyasa ai kaga munzo da wuri, yace da sun gama ze
karaso nan"

Abba murmushi yayi yace "Allah sarki sadiq ba dai kokarin aiki ba, to Allah ya kawo
shi lafiya"
Duk suka ce Ameen Amma banda Amal da Tasha jinin jikinta

Abinci suka ci duk suka gabatar da sallar Azahar sannan suka sake. Zama suna hirar
yaushe gamo

Abba ne ya yafito Ramla da hannu tazo yace "je ki sake gyara dakinnan na zaure a
can yayanku ze sauka har abinci nai da komai ku Kai masa kafin ya iso "

Tace to taja su Amal suka tayata daukar kwanukan abinci

Koda biyu na Rana tayi duk sun gama gyaran dakin se tashin kamshi yake
Suka juyo cikin gidan
Suna shigowa ummah na fitowa daga cikin da spoons da suka manta Amal ce gefenta ta
Mika mata tace "ungo tai kikai kun manta da wannan ta wuce

Dan Jim Amal tayi ta na Dan kunkunin ta cikin Rai

Takun da ta jiyo daga zauren ne yasa ta dakata bata tafi fa ta tsaya gefen kitchen
din

Yana tafe cikin takunsa na jaruman maza ya na sanye cikin uniform dinsa da suka
masa matukar kyau yana rike da bindigar sa irin wadda suke ratayawa a kafada ya
shigo da sallamarsa

Dago kan da Amal tayi caraf idanunsu suka sarke da juna wata irin kuwa ta kwalla!!!
Tana zare ido da sauri uwayen suka taso suna nufo hanyar

Se nuna sa da hannu take Tana hawaye!
Shi kam mamakinta ne ya kamashi se ya fara takowa kusa da ita
Ai kuwa ta lumshe. ido ta zube a wurin.........................

*Aysha galadima ce*
Comment
Share
[8/15, 9:33 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*



*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna sayar da Dubai gowns, laces ,shoes, bags and kitchen utensils_
_Ga masu bukata zaku iya tuntubar wannan number_ (08064933819)




*PG 9-10*



________________________________________


Umman su husna da isowar su kenan a wurin ta saki salati Tana kallon Amal da ke
zube a kasa, da sauri ta Kara sa ta dago ta su Abba duk tsaye sukayi suna mamakin
me ya faru

Kawu lawan ne ya juya yana kallon Sadiq da yayi tsaye yana kallon umma yace "Kai
Abubakar me ya faru ne?"

"Abba nima ban sani ba ta na ganina Naga ta fara kuka se kuma ta fadi"
Sadiq ya fada

Ruwan da husna ta kawo ne umman su ta karba ta shafa mata a fuska ,sannan fa ta
sauke wata irin Ajiyar zuciya Tana bude idonta a hankali, se da ta fara bin
mutanen dake zagaye da ita da kallo daya bayan daya ta na zuwa kansa ta saki wata
Kara! ta boye fuskarta a jikin ummah Tana cewa"ummah Dan Allah kuce ya fita ,se
kuka take!

Kawu lawan ne ya dubi Sadiq yace "kaje dakin zaure abincinka na can"

Juyawa kawai yayi al'amarin duk ya daure masa Kai dagata umman su husna tayi sukayi
cikin gida ,su Ramla da husna na biye da su ,dama ita umma tuni ta wucewarta Tana
me jin haushin abunda Amal din ta aikata.
Daki ta shigar da ita ta ce mata "kwanta ki futa kinji"
Daga mata Kai, kawai tayi

Ita ma fita tayi ta shiga dakin ummah

Kawu lawan ne ya ja Abba da jikinsa yayi sanyi suka fita kofar gida suka zauna kan
dakali
Ya kalli Abba yace "Isma'il Wai me ke damun Amal ne ko wata rashin lafiya ta same
ta ba muda labari?"

Shiru Abba yayi sannan fa ya shiga bama kawu lawan halin da husna ke shiga duk taga
Dan sanda ko masu wani kaki da suke rike bindiga

Abun ya girgiza kawu lawan sosai
Ya jima yana nazari sannan yace" Ai ko akwai matsala in har haka ne ,dole alkawarin
Dana yi na warware shi na zancen aurenta da Abubakar ,Dan wannan in muka takura
zata iya rasa ranta ma in har ta aure sa, tunda yanzu ma da ganin sa kawai tayi har
da Suma fa tayi"

Abba yace"yaya ayi haka kuwa tunda kasan Sadiq fa yasan da maganar nan"

Kawu lawan yace "ai wannan me sauki ne ban son abunda za muyi muzo mu bata zumunci
mu"

Shi dai Abba duk jikinsa yayi sanyi akan wannan lamari

Umman su husna ma se da ta tambayi umma meke damun Amal nan ta fada mata duk abunda
ke faruwa shiru tayi ta kasa cew komai..
________________________________________


Yana dinning yana breakfast Kiran Khalil ya shigo wayar sa dauka yayi ya Kara a
kunne daga can Khalil yace " hello kana Ina gani a kofar gidan ka Amma a rufe"

"Eh bani jaji Ina gida , kamar kasan nemanka nake kuwa"
Cewar Sadiq

Daga can Khalil yace"Allah ya sa ta samu ne, yanzu da na shirya Zan zo gidan"

"Ok seka zo"
Ya sauke wayar a kunnen sa ci gaba da latsa wayarsa

Befi 30 minutes ba se ga shi ya shigo gidan , hango sa da yayi ne yasa ya tashi
daga kan dinning ya ja hannun sa suka fita zuwa wani wurin shan iska dake
gidan ,anyi masa irin bukkar nan da ake yi an zagaye suka ne mi kujeru suka zauna


Tun lokacin da ya jawo hannun khaleel , khaleel din ke ta kallon sa da mamaki yadda
ya jawo sa kamar wani yaro

se da suka zauna kuma yayi shiru ,se da khaleel ya ji shirun yayi yawa se ya kama
hannun sa cikin nasa yace. " Captain Wai lafiya kake ko wani Abu ya faru ne?"

Ajiyar zuciya ya sauke!
Sannan ya bude Baki A hankali ya fara fadar" Baka yi mamakin ganin ban kwana
barrack ba , jiya Abba ya kirani yace na same sa a gida, bayan nazo ne yake min
zancan aure fa, ya wani zare idon sa akan khaleel , kuma Kai kafi kowa sannin ban
kawo aure a raina ba yanzu, gashi ni har yanzu bani da wata budurwa da Zan nuna
wadda nake so ,sannan idan har nayi wasa Abba me iya zuwa ne can zamfara cikin
dangin sa ya laka min wata..

Shiru khaleel yayi na 'yan sakanni sannan yace maganar gaskiya fa farouk ya kama ta
kayi aure fa shekarun 32 ace baka zancan aure , koni Dana ke 30 ai kasan dai bikina
kwanannan za'a yi shi fa, sannan da kake Zan can baka da budurwa ai ko kana da su
da yawa , gama Maryam cikkakiyar mace kamar yadda kake son matarka ta kasan ce ,ga
ilimin boko Dana Islamiyya ga kuma kirar da Allah ya mata komai zam-zam kawai ka
gabatar da ita , kuma Tana matukar sonka fa

Dan duka ya Kai masa a kafada Kai fa khaleel Dan iska ne fa ,har yaushe ka kalle ta
kasan komai zam-zam ,

Yace "ai ko makaho ya ganta yasan ta isa mace "

Farouk yace"se dai ni tamin kadan ,yarinyar da iya karta 20years kake son hadani da
ita, kawai kaja min Raini Allah ya kiyaye na aureta .

Ya fada yana ya mutsa fuskarsa

Sororo khaleel yayi da kansa yana masa kallon mamaki ,

Se yace "to ai shi kenan ka tsaya neman warinka se ka aura kaga ita ba zata Raina
ka ba ko?"

Ni malam kaga tafiya ta ya Mike ya nufi wajan motar sa yana mamakin son girma Irin
na abokin na sa
Fatansa daya Allah yasa ya tsaya ruwan ido har Abban sa ya hada sa da duk wadda ya
ga dama ya ga yadda zeyi......


_____________________________________'___

Koda Sadiq ya shiga dakin kayansa ya cire ya shiga bathroom ya yi wanka ya fito ,ya
shirya cikin wani danyan voile sky blue da ya karbe sa sosai ko Dan yana farin
namiji
Kamar Atk lol๐Ÿคฃ

A cikin gida kuwa se la'asar Amal ta farko a baccin da ya dauke , bayi ta shiga
tayo Alwala tayi sallah sannan ta fito
Tsakar gidan taga su umma zaune suna hirar su ,sunku yar da Kai tayi tace"umma Ina
su husna?"

Hararar ta ummah tayi ta dauke kanta
Se umman su husna ce tace" sun shiga makwabta gidan su ko bilkisu kawar Ramla"

Koma wa tayi ta dauko hijab dinta ta sa tace "bari na bi bayan su "

Har Sadiq ya fito dakin ya hango ta zata shigo zauren komawa yayi cikin dakin seda
tazo Dab da dakin taji an fizgota da karfi

Ta bude Baki zata yi kuwa taji an rufe bakin................ .......




*Aysha galadima ce*
Comment
Share
[8/15, 7:13 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(080649333819)




_Wannan shafin na duk wani masoyin littafinnan ne Alkhairin Allah ya Kai gare ku
a duk_ inda kuke




*PG 11-12*

__________________________

Cikin dakin ya shigo da ita ya rufe kofar ,tuni hawaye sun cika mata ido yana dago
kanta su ka samu damar saukowa, kallanta yayi na 'yan sakkani sannan ya sake ta ya
koma gefen katifar dakin ya zauna yana sauke ajiyar zuciya

Dagowa yayi yaga har yanzu Tana nan tsaye a inda ya barta yace "zo nan"ya nuna
kasan carpet kusa da katifar da yake zaune, jikinta na rawa ta matsa ta tsugunna,
yace "zauna"ta zauna
Se da aka dau kusan minti biyu sannan yace "dago kanki ki kalle ni"

Ta dago kan ta suna hada ido taji gaban ta ya fadi ga jikinta ko Ina rawa yake, se
ta sauke idanunta kasa
Yace "ni dodo ne?"

Ta girgiza kanta , yace "bude Baki zakiyi ki amsa min tambaya ta"

Murya na rawa tace"A'aaa"

Yace"to ya akayi daga ganina kika fara kuka har da Suma kika yi kika nuna ni da
hannu kin taba ganina ne?"

Ta ce" A'a"

Yace to me yasa kika yi abun da kika yi din?"


Se da aka ja sakanni sannan tace "banson Dan sanda ne"

Ji yayi kamar an caka mishi mashi a zuciya, har se da ya aza hannunsa akan kirjin
nasa

"Me yasa Baki son Dan sanda?"
Ya sake fada

Tayi shiru har se da ya sake maimai tawa
Se ta fashe da kuka ta boye fuskarta a cikin kafafunta tace

"Na dai tsane su ne kawai"

Ya runtse idanunsa yana jin wani Abu na taso masa a zuciya

Yace "har ni yayanki kika tsana?"

Ta ce "eh"

Ta na Duke bata San halin da ya shiga ba, se da ta dago kanta taga idanun sa sun
kada sunyi jajir da su da gudu ta tashi ta fita a dakin

Duk jikinsa ya masa sanyi yama kasa dakatar da ita

Se ajiyar zuciya yake sauke wa!

Ita kam ai Tana fitowa waje ta wuce Tana goge fuskar ta

Ta nufi gidan dasu Ramla suke .

___________________________

Yana nan a'inda khaleel ya barsa yana latsa wayar sa har se da yaga 12pm ta kusa
ya Mike ya shiga gida ya dau car keys din sa ya fito ya ja motar sa ya fita.

Yana kan hanya ne ya tsaya, Naga ya shiga wani mall ya hadu kayan ciye ciye ya
tsaya ya Dan zazzabi abubuwan da ya San zata iya ci ,sannan ya koma gefen turare ya
zabi kala ukku ya je wurin biya har ya biya ya fito se ya ji ana "Assalamu Alaikum"
Juyowa yayi yana kallon me sallamar wata kyakyawar yarinya ce tana murmushi ta
katse masa tunani da fadar"Dan Allah in ba damuwa number ka nake so ka bani"

Wani banzan kallo ya mata ya shige mota yana fadin"stupid girl" yana tsaki,

Yana tafe ya na takaicin wasu mata da basu da aji ,da har suke iya fada ma namiji
suna sonsa tun kafin shi ya fada

Har ya iso kofar wani Dan madaidai cin gida yayi parking ya shiga da Sallamarsa
daga ciki wata farar datijuwa ta amsa Tana fadar"muryar wa nake ji kamar ta soja"
Yana murmushi ya shiga ya nemi kujera ya zauna

Ita ko tsofuwar se farin cikin ganin sa take tace"yau wace Rana soja a wurina an
tuna da matar kenan "

Yana sosa kai yace"ai Ina zuwa kece bana tararwa"

Tace ungo naka ta mai da kuwa "ni kuwa Ina zani ko lokacin da me sunan ka na duniya
banyi yawo ba se yanzu da tsufana"

Se ta fara matsar kwallah

Shi ko farouk mi ze yi in ba dariya ba harda rike ciki ,
Ni ko nace dama wannan mutumin na dariya har haka

Filon kuje ra ta dauka ta je fa masa Tana fadar ja'irin yaro Ina zaman zamana zaka
zo ka sani kuka da Rana tsaka, tashi ka fice min a gida

Shi dai dariyar shi kawai yake se can yace"ke Wai kakus har yanzu Baki manta da
tsofonnan ba ya fa dade da gangarawa Amma ke duk mutum ya zo se kin jawo masa
maganar sa "

Ai ko se hawaye kakus ta fara tace naki in manta dashi kace Aminu ya manta da
hauwa'u kaji"

Se ya Sha toka, yaji haushin sanya iyayansa da kakus tayi , be sake magana ba

Da taga yadda yayi se ta yi dariya tace"ai yanzu kaji in da dadi kaima "

Ledar hannun sa ya aje ya tashi ze fita , tashi tayi ta rike hannunsa Tana fadar"
habah Habubakar Dina ba dai fushi kayi da matar ba?"

Ji yayi wani kololo ya taso masa jin yadda ta bata masa suna ,yace
"A'a ba fushi na yi ba "

"To muje ka zauna , kamar na San zaka zo na dama fura nasan kana son ta se ka Sha,
dama yunwa yake ji se yace" to sakar min hannu , ta sake sa ya je ya zauna ta bude
firjin ta dauko furar me sanyi ta zuba a wani kofi ta basa ya fara Sha....


__________________________


To haka dai su husna suka canye weekend din da suka zo ,Amal duk bata da sukuni ko
yaushe Tana daki labe har duka ummah ta so ta mata ummansu husna ke hana ta , shima
sadiq tun ranar be sake ganin ta ba, gashi kulum sonta kamar Kara masa shi ake ,
tunda tun Tana karamar ta yake da kon so se da yayi nisa a ciki wannan matsala ta
tunkaro shi

Duk sun fito zasu tafi umma da Ramla sun yo masu rakiya Amma banda Amal ,da Ramla
tayi tayi tazo ta ki se dai husna ce tashiga ta mata sallama Tana me jin haushin
abunda Amal kema yayan nata ,Dan har aiko husna yayi ta Kira ta ,taki zuwa

Duk mota su ka shiga suna masu daga ma junansu hannu suka wuce.
Bayan wucewar su Abba kasuwa ya wuce Ramla da ummah suka shige gida Suma.

Har washe gari umma taki sakar ma Amal fuska , har se da ta bi ta dakinta bayan ta
gai data tace"ummah Dan Allah kiyi hakuri "

Tana goge kwallar da ta taru a'idonta


Shiru tayi se can ta amsa Mata tace" bani Zaki ba hakuri ba wadanda kika ma laifin
Zaki ba hakuri ,in banda rashin hankali Amal Dan gidan kawu lawal Zaki gani kiyi
shashancin da kikayi ko kunya Baki ji , duk kinsa munji kunya a gaban mutanen nan ,
har fitowa kika bar yi fa a gidannan kamar wani dodo ne a gidannan"

Tunda umma ta fara magana hawaye suka fara zubo mata , se bayan ta gama magana ne
ta kalle ta taga halin da ta shiga se kuma taji tausayin 'yar ta ta ,

Kun san da da mahaifi se Allah, se ta ce tazo ta matsa kusa gareta se ta shiga
share Mata hawayen da take

Se ta bar kukan se dai ajiyar zuciya da take saukewa , daga fuskarta ta yi ta dubi
umman tata tayi murmushi tace"ummah kiyi hakuri nima ba'a son Raina nake shiga
halin Dana ke shi ga ba Insha'Allah zan Dena"

Jawota tayi cikin jikinta tace "ko ke fa Amal "

Tana murmushi..................



*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/16, 9:02 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(080649333819)
*Dubun gaisuwa a gare ku*

*Aysha humaira*
*Precious*




*PG13_14*



____________________________


Kara rungume ta ummah tayi Tana murmushi tace "to tashi kije ku shirya kar kuyi
lattin makaranta"

Tashi tayi ta fita ta shiga dakin su Tana shiga Ramla na fitowa bayi ,tace "da
yanzu Zan kwala Miki Kira kizo kiyi wanka kar mu makara, kin San yau Monday fa"

Amal tace Insha'Allah ba zamu makara ba yau"

Ta shiga wankan ita ma , ba ta jima ba ta fito ta shirya sukai breakfast suka
wuce.......


___________________________


Haka Rayuwa ta ci gaba da gudana , tun lokacin da su kawu lawan suka dawo kaduna ya
zauna yayi nazari sosai akan zancan Auren Sadiq da Amal , se ya samu umman su husna
da zancen ya Mata bayanin komai yadda suka yi da Isma'il , ajiyar zuciya ta sauke
tace" nima abunda na ke gani a hakura da wannan hadin da'ake so ayi, kawai ya nemi
'yar uwar ta Ramla ya aura , in sun dai dai ta shike nan ,Suma in basu daidai ta
kada muce zamu takura akan lamarinnan yanzu zamani ya canza malam"

Yace "nima abunda na yanke kenan Zan zauna da sadiq din na mai bayanin komai "


Tace "to yayi Allah ya taimaka "

Yace"Ameen"


Kwana biyu da maganar ta su Abba ya nemi ganin Sadiq , bayan sun samu kebewa yake
masa bayanin komai da komai , ji yayi kamar an buga masa guduma, gashi baya da
damar yin jayayya da mahaifin nasa

Se yace"to Abba Insha'Allah duk yadda kace haka za'ayi

Koda Abba ya dubi Dan nasa se yaga duk yanayin sa ya canza, se yaji Dan nasa ya
bashi tausayi , se dai baya da ba abunda ze masa
Danshi kawu lawan duk da be yi wani karatun boko me tsayi ba ya san yanzu an bar
yayin auren dole

Sannan yanzu auren Ina so , kana so ya yakaya ballantana auran dole, shiyasa yake
ganin baza ya takura kowa akan wannan zancen daga cikin su biyun nan ba

A haka Sadiq dai ya ma mahaifin nasa sallama ya fita , dakin sa ya wuce ya kwanta,
take yaji wani zazzabi ya ta so masa ya rufe jikinsa da bargo

Har se da husna ta shigo kawo masa abinci ta tarar da halin da yake ciki taje ta
fada wa ummansu , tasowa tayi ta biyo bayanta suka shigo dakin

Husna ce ta kama bargon Tana Kiran "yaya Sadiq ka tashi "
Tana matsar kwallah Dan Tana matukar kaunar yayan nata duk da zafin da yake da
shi ,bata so taga abunda ya same sa


Daurewa yayi ya Mike zaune , idanun sa sun kada ga jijiyoyin kansa duk sun fito
Alamun yana jin ciwon Kai sosai

Ummansu ce ta katse shirun da cewa"dama baka da lafiya shine kazo ka kwanta a
daki , to
Kasha magani?"

Da kyar ya girgiza kansa Alamar a'a

Abincin da husna ta kawo tace ta zuba masa yaci kafin ya Sha magani

Ita kuma ta fita ta nemo mai magani

Da kyar ya danyi Loma biyar ya aje

Husna ce ta dawo da maganin da ummah ta bata,Dan ita bata dawo ba karba yayi ya
Sha sannan ya kwanta

Husna na ci gaba da jera mai sannu

Ummah ko da taje, daki ta zauna tasan wannan zazzabin nasa ba ya rasa nasaba da
maganar da Abba ya masa na zancen janye maganar aurensa da Amal da'a kayi

Fatan ta daya Allah ya cire masa ita a zuciya ya zaba masa wadda ta fita


___________________________

Farouk ma a daddafe yayi weekend din a gida ya tattara ya koma barrack , saboda
duk lokacin da ya hadu da Abba se ya tuna maganar da su kayi


Shi kam dai be sake bi ta kan maganar ba saboda har yanzu be ga wadda ta masa
ba ,lokaci bayan lokaci maganar na fado masa a Rai

Yau ma yana zaune a cikin office din sa se yaji an kwankwasa kofar duk zatonsa
khaleel ne se ya bada umarnin a shigo


Kamshin da yaji ya tabbatar masa da ba khaleel bane Amma be dago Kai ba yaci gaba
da abunda yake
Ji yayi ance " well done sir"

Ya dago kansa ya kalle ta , wata 'yar kabilar ibo ce tsaye taci kitson attach ,fara
ce har wani doruwa-doruwa take Wanda ke nuna har da mai take shafawa, Tana sanye
cikin uniform dinsu na sojoji

Ya dau sakanni be amsa ba se can yace"thanks"

"Sir Ina son magana da Kai"
Ta fada

Yace "am busy now"

Shiru tayi ta jawo kujera ta na son zama yace "please can you excuse me"

Se ta Mike jiki a sanyaye ta fita

Shi kuma ya bita da harara da tsaki

Monica sunan ta ta dade Tana mutuwar son farouk tun Tana boyewa ,har ta fada ma
khaleel ta ce ya fada masa ,lokacin da khaleel ya fada masa har fada suka tashi yi
ma

Daga lokacin khaleel be sake tayar masa da zancen ta ba , bawai Dan bata yi bane

Ita ma kyakyawa ce kunsan kabilar ibo akwai masu kyau da farar fata a cikin su

Ka Wai dai shi ya tsani macen da zata ce tana sonsa da kanta , yana daukar su Mata
marar kamun Kai, sannan uwa uba gata ba musulma ,shiyasa be taba bata fuska ba


"Hattara 'yan matan zamani Kuna ganin kamar wayewa ce kije ki ce ma wani namiji
kina sonsa , to ba wayewa bace face rashin kunya da kuma Rashi aji,. 'yan matan
hausa fulani da'aka sani da alkunya, koma bashi ba kunya adon mace, Amma ba kunya
ba komai ki tunkari namiji kice Wai kina sonsa habah sisters gaskiya ku Dena ba Abu
bane me kyau, saboda namijin nan ko ya aure ki yana Nan yana kallon ke kika ce kina
sonsa ko Abu ya hadaku tsab ze goranta maki , babban tashin hankalin ma duk macen
da ke zuwa Tana cewa Tana son namiji ana daukarsu marassa kamun Kai ko mutanen
banz, Allah yasa ku gyara"

___________________________

Yau ta kama Wednesday dai dai da antashi su Amal daga makaranta ga garin hadari ya
hadu sosai ,Wanda ko da wane lokaci Ruwa na iya saukowa

Sauri kawai suke yi kar ruwan ya dake so ai ko se ga ya an sako su

Tafe suke shida khaleel a mota tasowar su daga wurin aiki kenan

Please Login or Register in order to submit comment