Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG 35-36*



________________________________


Koda suka fito ummah me kudi na zaune a daya daga cikin kujerin falon Tana kallo,
bayan matsawar da ummee ta mata akan ta fito suyi Hira ,ganin Amal din na bacci
shiya sa ta fita

Dinning ummee ta nufa ,Amal na biye da ita suna zuwa Al'amin na daya daga cikin
kujerin dinning yana cin Abinci

Juyowa ummee tayi tace "zauna to ki zuba duk abunda kike so"
Al'amin dago Kai yayi yana ma ummee nuni da Ido akan Amal ,fahimtar shi da tayi
yasa ta daga masa Kai

Da sauri ya Mike ya jama Amal din kujera yace "aunty na zauna"

Ita kunya taji ganin namiji kamar wannan yana kiranta aunty
Ummee wucewa tayi wurin ummah me kudi

Al'amin shi ya zuba Mata abincin ya tura gabanta yace "bissimillah Aunty"

Dago Kai tayi a hankali se ko suka hada Ido ,da sauri ta sake sunkuyar da Kai
Murmushi yayi yace"aunty ki saki jikinki Ni sunana Al'amin kanin mijinki ne ni,
tunda na ganki nasan yayana ya dace"


Ita dai shiru tayi Zuciyarta na bugawa jin wannan katon saurayin ne kanin
mijinta ,in haka ne to ya mijin nata ze kasance?

Motsin matsar da kujerar da yayi ne ya dawo da ita daga tunani da ta shiga

Cewa yayi "se anjima aunty"
Yawuce ,a hankali ta Dan tsakuri abincin ta Mike ta wuce dakin da aka sauke su ta
zauna Tana ta tunanin yadda Rayuwa ta juye Mata ,ita ce Wai aka ma aure bayan burin
da taci nayin karatu me zurfi
hawaye ne suka zubo Mata ,ta goge abunta ,wanin abun ai se iyaye

Nima dai nace Amal dafa kin Adana hawayen idonki da saura fa😀


A can gidan Farouk misalin karfe goma na safe masu kaya suka isa
fita ma yayi ya bar musu gidan ,dama gidan tunda na namiji ne ba komai yake da shi
ba ,duk da yana da kujerin sa

Ma'aikata kuwa sun zage dantse sun hada gidan baza ka taba yarda gidan bane saboda
har kujerin falon se da suka fitar aka kawo wasu an kawata daku nan gidan sunyi
kyau sosai
Falon wasu royal chairs aka sa kalan Royal blue and milk haka ma labulayyan royal
blue and milk

Se bedroom biyu dake gidan da nasa da nata duk an saka Kaya masu kayatarwa ,
kitchen ma ba karya komai yaji

Wannan shi ake Kira auren gata, Abba yayi kokari sosai

Ango farouk se dare ya dawo gidan yana shigowa tsaye yayi yana kallon yadda falon
ya dawo ga sanyin air conditioner na tashi ,ba Kara min burge sa falon yayi ba kome
ya tuna kuma se ya tabe Baki ya wuce nasa dakin
Ko can din ya masa kyau ainun
wanka ya shiga yana fitowa yaji kamar motsi a falo
Se da ya shirya cikin jallabiyya ya nufo falon yana shigowa yaga khaleel ne zaune
akan daya daga cikin kujerin falon, dauke Kai yayi
Ze wuce ,da sauri khaleel ya Sha gaba nai yana fadin "habah Angon Amal me yayi zafi
haka ,tun shekaranjiya nake neman ka a waya Ammah kaki dagawa?"

Rabe shi yayi ya fita zuwa massalaci
Dariya khaleel yayi sannan shima yabi bayansa


Da daddare sunyi Shirin kwanciya ummah me kudi tace"gobe warahaka kina dakin
mijinki"

Ai ko se hawaye ta fara
Ummah me kudi tace"rufe min Baki ke da abun kuka be Miki wuya"
Makurewa tayi can karshen gado
Se kuma taji ta bata tausai
Cewa tayi "matso 'yata kiji"

Matsowa Amal din tayi ta Dora kanta akan cinyar ummah me kudi

"Ki zama jaruma Mana Amal ke ce ko yaushe cikin kuka ,yanzu fa kin shigo sahun
manya ,kin zama matar aure kema"
Nasiha ta ci gaba da Mata akan zamantakewar aure
Har ta soma gyangyadi ,sannan se ta kyale ta

Washe gari ummee da kanta ta Kira wata me gyaran jiki aka yini ana dilke Amal har
da kunshi a ka Mata ja , nan take ta fara glowing kun San Abu ga farar fata aka
sa tayi wanka cikin wasu ruwan turare masu dadin kamshi

Se yammah Aka kammala komai har kwalliyya , An shirya ta cikin lifaya yellow me
kwalliyar Baki Masha'Allah tayi kyau fiye da tunani

Ummah me kudi da su husna da yake sun dawo Suma da umman su aka zo aka raka Amarya
Amal gidan mijinta
Tun a hanya take kuka
Har suka iso Husna se santin gidan take tun kafin su shiga

Tun kafin su sauko a mota ummah me kudi tace "sauka da kafar dama" da kuma
bissimillah

Haka ma wurin shiga se da tayi hakan har kuryar dakinta suka zaunar da ita bakin
gado
Sun isko matar khaleel a gidan ita ce ma ta tarbe su nan dai suka Kara yi Mata
nasiha

Suka Dan Kara zagaya gidan suna yabawa kokarin sirinkin nasu

Ba su Mata sallama ba Dan kar ta rikice suka fita khaleel ya Kai su har husna
wucewa sukayi

Shirun da ta ji ne yasa ta bude fuskarta matar khaleel ce kawai a dakin hada Ido
suka yi ta Mata murmushi tace"Amaryarmu"

Se Tai kasa da kanta da dai taji shirun yayi yawa

Se tace ma matar khaleel "Ina wadanda muka zo?"

Ce Mata tayi ai sun wuce
Ai ko ta Kara rushewa da wani kukan .

Lallashinta tayi har tayi shiru Kiran Isha'i ne da aka fara yasa suka tashi suka
yi sallah

Kira ne ya shigo wayar matar khaleel
Ganin mijinta ne yasa kawai ta daga ban San me yace Mata ba Naga ta Mike ta
fita ,Koda ta fita yana cikin motar sa budewa tayi ta shiga tace

"Honey Ina Angon na ganka Kai daya?"
Ce mata yayi shi daya ze zo gida zamu wuce muma

Shiru tayi ganin kamar ransa bace


Shiru shiru Amal bata ga ta dawo ba ta taso a hankali ta fito falon Tana leke bata
ga kowa ba

Tsoro ne ya kamata da sauri ta koma kuryar dakin ta makure har kusan 9:30pm nan ta
tabbatar da tafiyarta ita ma tayi

Hawaye take yi A hankali a hankali

Motsin takun talkami taji , nan gabanta ya ci gaba da faduwa Tana Kara matsawa
karshen gadon
Duk takun da akayi daidai yake da bugawar zuciyarta ...................✍️


*Aysha Galadima ce*


Comment
Share
[8/22, 9:31 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)

*DOMIN JIN DADINKU*

Raleeyer
Ummu Afef
Fatima shehu
Aysha humaira
Leemat
Ummu sadiq
Maman sultan
Ummu Muhammad
Aysha zannah
Zahra MD


*PG 37-38*



________________________________


Sautin Takun na matsowa Tana Kara runtse idanun ta se kuma taji kamar takun gaba
yayi ba'a kofar dakin da take ciki aka nufo ba.

Shiru gidan ya kuma dauka tamkar babu wata hallitta a cikinsa

Ita ma Amal shirun da taji yasa ta tashi taje ta sama kofar key ta dawo ko kayan
jikinta bata cire ba ta kwanta bayan ta shafa Addu'a a dukkanin jikinta, a yanzu ta
Dan samu natsuwa sanin cewa akwai wani mahaluki a kusa da ita ,ita hakan da yayi ma
shine dai dai a wajenta

Tuni bacci barawo ya dauke ta

A bangaren farouk kuwa da kyar khaleel ma ya nemo sa bayan shawo kansa da yayi akan
fushin da yake da shi ,duk se da ya fada masa shima be San komai ba

Nan yake Kara basa shawara akan yayi hakuri da zabin da iyayensa suka masa ya karbi
wannan auren hannu bibbiyu Insha'Allah ze yi Alfahari da shi

Ya ci gaba da cewa
"Kuma kasan me captain? Yarinyar ba karya akwai kyau"

Wani kallo yake bin khaleel da shi yace

"Yanzu baka ji kunyar cewa yarinya ba, ai ni duk da bani da ra'ayin auren Mata biyu
dole nayi wani auren gaskiya"

Kallon mamaki khaleel ke biyarsa da shi ,yana me tunanin wane irin tsatsauran
ra'ayi Abokin nasa yake da shi, Dan shi in shine hakuri kawai ze yi a wuce wurin

Ajiyar zuciya khaleel ya sauke yace"what ever Ni dai yanzu kazo muje na kaika Ango"

Harara ya watsawa khaleel din

Yace "look captain ya kamata ma na Kira abokanmu a raka ka, kawai dai na kyale su
ne Ni kadai ma na isa ka tashi muje

"Bazan je ba"

Amsar da ya bashi ke nan ,tashi ma yayi yaja motarsa ya barsa
Ba karamin takaici Abun ya ma khaleel ba.

Shiyasa kawai yazo ya dauki matarsa suka wuce , farouk kuwa yawon sa kawai ya ci
gaba da yi a cikin motar
Sannan ya nufi gidan nasa yana me ayyana abubuwa da yawa a ransa

Yana shiga Kai tsaye dakin sa ya nufa ,wanka yayi ya kwanta gaba daya ma ko tunanin
Amaryar tasa be yadda zuciyarsa ta bijiro masa da shi ba

Kiran sallar Asuba ne ya tada Amal daga bacci A hankali ta sauka akan gadon ta nufi
bathroom Alwala ta dauro ta fito ta gabatar da sallar Asubah bayan ta gama zama
tayi akan daddumar tayi Azkar dinta daga nan wani baccin ya dauke ta

Shima farouk massalaci yaje bayan ya dawo Kuma ya nufi dakinsa

Misalin karfe takwas na safe aka fara kwankwasa kofar shigowa falo
Cikin bacci Amal taji ana kwankwasa kofar falon

A hankali ta tashi ta nufo falon jin ta inda ake kwankwasar yasa ta nufi kofar,
budewa tayi se taga wata Mata rike da basket dake dauke da wasu kyawawan kuloli gai
sawa su ka yi sannan ta Mika Mata kwandon tace"ummee tace a kawo muku breakfast"

Karba tayi tace "angode"

Juyawa tayi cikin falon ta nufi inda ta hango dinning ta aje kwandon zata juyo taji
takun tahowar mutum tsaye kawai tayi a wurin

Farouk ne ya fito cikin kakinsa na sojoji Wanda ya karbe sa , office ya ke sauri ya
wuce akwai abunda zeyi da safen nan

Fitowa tayi dai dai da ya kawo wurin shima ai kuwa karaf suka hada Ido
Wata irin Kara Amal ta saki har se da ya dafe kunne , se Kuma tayi luuu ta fada kan
kujerar dake bayanta
Tsaye yayi kawai yana kallonta ,tunani ya fara wannan meke damunta ,har ya taka ze
wucewarsa se Kuma yaga Alamar kamar bata motsi da sauri ya dawo har ya Mika hannu
ze taba ta se Kuma ya fasa tsaye yayi na few seconds se Kuma wani tunanin ko Suma
tayi ya zo masa da sauri ya shiga kitchen fridge ya bude ya dauko Ruwa yana zuwa a
tsaye ya fara zuba Mata su gasu da matukar sanyi Numfashin da ta fara ne yasa kawai
ya nufi hanyar fita gidan...............✍️

*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/23, 7:44 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)
*PG39-40*



____________________________

Fita kawai yayi a gidan be bi ta kanta ba se dai ko da ya shiga mota fuskar ta ce
ta dawo masa a Rai yana tunanin kamar ya taba ganinta tsaki dai yayi yaja motar ya
fice a gidan

Tana farfadowa da kuka ta farfado se dai bata ga kowa a falon ba ,sannan gata jike
da ruwa da sauri ta Mike ta kwasa da gudu zuwa dakinta har da su saka key

Nace kuwa bayan hari🤣

Ta dade zaune Tana kuka Tana tunanin wanna mutumin me kayan sojoji da ta gani
kakkarfa da shi ba dai shine mijin nata ba?
ai ko in shine mutuwa zatayi kawai , Anya ma su Abbah sunsan soja suka aura Mata
ta, dade Tana kukanta se da ta gaji Dan kanta ta Dena , cikinta ne ya fara kukan
yunwa ba arziki ta bude dakin ta fita da sanda ta nufi dinning din ,kulolin abincin
ta fitar a kwando ta Dora akan table din ganin ba ko spoon yasa ta shiga neman
kitchen, shiga tayi se kuma tayi tsaye Tana kallon tsaruwar kitchen din , takawa
tayi ta shiga ciki cup da spoon da Kuma plate daya ta dauka ta fito dinning table
ta nufa ta zuba kunun gyadar data gani ,se ta zuba dankali da dan farfesu data
zuba a gefe da sauri ta suri kayan ta shiga dakin ta ta rufo kofa

_____________________________

Amarya Ramla Ana kano ana ta cin Amarci tun Tana jin kunyar Abubuwan har ta fara
sakin jikin nata,Dan yaya sadeeq be je Mata da Wasa ba,kun San Abu ga sabon shiga
Dan har ciwo na kwana biyu se da tayi kafin ta fara gogewa a yanzu ,se dai Tana
cikin kewar 'yar uwarta kamar me

Yau ma Tana zaune a falonta cikin wata Dubai gown red colour rigar ta matukar yi
Mata kyau Masha'Allah se dai ta rafka uban tagumi Tana tunani ,hannunta taji an
cire daga fuskarta , firgigit ta dawo daga tunanin da take ,yaya Sadiq ya daga
girarsa sama yana cewa"Tunanin me kike haka my happiness ,tun dazu na ke ta sallama
Baki Amsa ba"

A hankali tace "Ina kewar Amal ne "

Shiru yayi yace "Ni Baki yi kewata ba se ta Amal ?"

Rufe fuska tayi tace"A'a
Wayarshi ya Ciro yace bari na Kira Abokin mijinta Dan Na karbi number sa a lokacin
Ai ko se ta washe baki kamar gonar auduga, yana ko Kira wayar ta shiga daidai
lokacin khaleel na office din farouk, sabuwar number ya gani kamar baze dauka ba
Kuma ya dauka
Sallama Sadiq ya masa daga dayan bangaren su ka gaisa nan yama sa bayanin koshi
waye nan suka sake gaisawa, nan yake ce masa ,
"in akwai number da za'a iya samun Amal da ita ya basa , sister din ta ce duk ta
damu Tana son magana da ita ,
shiru khaleel yayi na 'yan sakanni sannan yace "ba damuwa Zan tura ma number yanzu,
Ina gaida Amarya"
Sadiq ya Amsa masa da zata ji sukayi sallama
Tunda khaleel ya fara waya hankalin farouk na kansa ,se dai be tambayesa da wa yake
wayar ba
Khaleel number farouk ya tura ma yaya sadiq ba bata lokaci wayar farouk ta fara
ringing be dauka se da aka sake Kira ya dauka
Gaisawa sukayi a mutunce nan yake masa bayanin kansa da Kuma dalilin Kiran ,ce masa
yayi baya gida yanzu se In ya koma sukayi sallama ,kallon tuhuma kawai yake bin
khaleel da shi, shi Kuma yaki kallonsa ma se can kome ya tuna yace

"Malam wa ya baka damar rarraba number ta ga mutane?"

"Su waye mutane surukan naka?"
Inji khaleel yana kallon sa

Cewa yayi" Naga Alamar ka sansu saboda shishigi irin naka"

Dariya yayi yace na dai ji

"Yawwa dama Ina so na tambayeka wannan yarinyar ta na da wani ciwo ne ?"

Juyowa khaleel yayi yana fuskantarsa da kyau yace "wace yarinya?"

Shiru yayi be bashi Amsa ba
Se can khaleel din yace "ohh Amal"

"Me ya faru ne?"
Shiru yayi be bashi Amsa ba se can da yaga dama yace
"Ina fitowa dazu falo ta kwalla min Kara kamar zata fasan dodon kunne ,har da Suma
Nike tunanin tayi"

Shiru khaleel yayi yana mamakin abunda farouk yace
Tunani ya fara se ya tuno ranar da ya fara rage musu hanya irin Abubuwan da Amal
din tayi a motar sa da Kuma bayanin da Ramla ta masa akan abunda take tsoro
Kallon farouk yayi da fuskar tausayi yace "Allah sarki Amal har ta ban tausayi "
Wani kallo farouk din ke binsa da shi ,be San me yasa ba Amma yaji haushin furucin
da khaleel din yayi

Se yace "in ze yiyu kabar shiga da uniform gida ko kabar bari Tana ganinka in ka
saka please saboda yarinyar Tana matukar tsoron masu uniform ko ba Kai ba duk taga
wani da kaki Tana iya shiga halin da kaga ta shiga dazu"

"Tana tsoron kaki kace fa ,to ita wane tsautsayin ne yasa ta yarda da aure na?"
Cewar farouk

"Ai yadda kake tunanin an matsa ma ita ma kusan hakane a wurin ta , biyyaya kawai
tama iyayenta ta aure ka ,Dan haka naso ka hakura ka rungumi aurenka"
Cewar khaleel

Wani haushi ne ma ya taso ma farouk jin Wai ta tsani me kaki sannan ma dole a ka
Mata. Ta aure sa kamar wani Wanda yayi kwantai
Ganin yadda yanayin farouk din ya canza nan take yasa khaleel yace "yadai?"

Tashi yayi yana tattara kayan gabanshi yana zubawa a wata jaka se da ya gama ya
kalli khaleel yace
"Zan tafi gida ne "

Sanin halinsa yasa khaleel da sauri ya Sha gabansa yace"friend dan Allah kabi
yarinyar nan a hankali kar kayi abunda ze sa ka dawo kana Dana sani "

"Malam ya ishe ka haka fa ,ai ba'abun da ze sa Ni da na sani ita Kuma zata yaba ma
aya zakinta ,zata San tayi auren soja, badai kaki ta tsana ba to dole ta dawo Tana
son kaki "

Fuuuuu ya rabe shi ya fita.........................✍️

*Aysha galadima ce*


Comment
Share
[8/24, 9:17 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




```Follow me on #Wattpad
@Ayshagaladima666```



```When you're down ask help from Allah
When it gets fine, don't forget to call Allah again and``` ```say```
*ALHAMDULILLAH*




*PG41-42*



_______________________________



tafe yake cikin mota yana tunanin Wai kamar shi farouk ne aka ma wata dole ta
auresa bayan shine Wanda 'yan Mata ke rububi lallai wannan yarinyar zata San ta
shigo gonar sa
Kai tsaye gidan ya nufa ya Danna hon me gadi ya wangale masa gate , da sallama ya
shigo falon direct dakinta ya nufa ya sanya Kai ciki ,dai dai da ta fito bathroom
daure da guntun towel pink colour a jikinta wurin madubi ta nufa

Tuni gogan naku yayi mutuwar tsaye ganin wannan kyakyawar fulawar a gabansa

Ba ta San da shi ba duk da kamshin turaren da taji ya gauraye dakin saman stool din
madudi ta zauna ta warware ribbon din dake kanta, gashin nan ko ya zubo
Masha'Allah ,dama Allah ya Mata baiwar gashi ,sannan kafin suje kwankiyal har
saloon se da suka je ita da Aunty Ramla


Dago kan da tayi ta cikin madubi ta hangi mutum ta cikin madu , wata irin
razananniyar kuwa tayi ,wadda ita ce ma ta dawo da farouk hayyacinsa Tana Shirin
tashi tsaye ya buga mata tsawa tare da cewa"sit down Joe"


Jiki na bari hawaye na zubar Mata ta zauna Tana kama towel din dake barazanar barin
jikinta


Matsowa ya fara yi yana tunkaro ta ganin haka ya sa gabanta ya ci gaba da faduwa ta
sunnar da Kai hawaye na zu ba

Gaban madubin ya zo ya tsaya dab da ita , ganin yadda jikinta ke rawa yasa yace
Mike tsaye

A sanyaye ta Mike ko Ina na jikinta na bari,kalon sama da kasa ya Mata ya yamutsa
fuska ,yace "dago kanki ki kallan"

Kasa dagowa tayi har se da ya sake daka Mata wata tsawa sannan ta kalle sa Tana
rufe Ido

Cewa yayi "je ki sa Kaya ki same ni falo"
Ya juya ya fita yanayin jikinsa duk ya canza se yamutsa fuska yake

Daya daga cikin kujerin falon ya zube ya na sauke ajiyar zuciya tamkar Wanda yayi
gudu


Ai Tana ganin ya fita da sauri ta nufi wadrop ta jawo wata doguwar Riga data gani a
sama ta saka ,Tana ja masa Allah ya isa,Tana Kuma kuka

Hijabin sallar ta ta saka ta nufi hanyar fita tana matsar kwallah

Koda ta fito dakin bango ta kama biya kamar marainiya

Shi Kuma idonsa a lumshe suke kamar me bacci ,a darare ta nemi nesa da shi ta zauna
akan carpet,sannan ta boye fuskarta a tsakanin kafafunta


duk abunda take yana kallonta , ganin yadda ta boye fuskarta ,wata zuciyar ta ce
masa ai Kai ne bata son gani ,tunda ta tsani masu kaki, ai ko Mike wa yayi ya nufi
dakinsa,

Lokar gefen gadon sa Naga ya bude ya dauko karamar bindiga irin ta hannu, rufe
lokar yayi ya fito dakin

jin motsi yasa ta dago kanta shine dai da sauri ta sake sunkuyar da kanta gabanta
na faduwa

Kujerar kusa da ita ya zauna yace "matso nan gabana"

Kasa take kallo ta rarrafo kusa da kafafun nashi

Ji tayi ya Kara Mata wani Abu akai
Dago fuskarta tayi kawai se taga karamar bindiga a kanta , idanunta ta fara
kyafkyaftawa bakinta na motsi tuni idanunta suka lumshe tayi baya ta zube akan
carpet
Tsaki yayi ya Mike ya nufi fridge ya dauko ruwa


Yana zuwa yau be yi da mugunta ba ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa a fuskarta ai
ko ta kawo numfashi


Komawa yayi ya zauna ita ma Tana bude Ido ta gansa ,ai se ta saki kuka

Tsawa ya Mata yace"rufemin Baki Kona sa bindiga yanzu na dauke kanki, Kuma maza
goge hawayen nan"



Da azama ko ta maza ta goge ,Tana Jan ajiyar zuciya


Kallonta yayi na 'yan sakanni ganin ta samu natsuwa se ya fara magana kamar haka
"kina jina ko idan kika sake ganina kika yi kuwa ko kika dauke numfashi to ranar
ba'abunda ze Hana nasa wannan bindigar da kike gani na harbe ki kowa ma ya huta"


Tsinto muryarta yayi Tana cewa "Dan Allah kayi hakuri kar ka kasheni"


Ba karamar dariya ta basa ba ,ya kula bakaramin tsoro ne da ita ba se dai ya kanne
beyi ba yace

"Ni wanna ba matsalata bace yanzu ya rage naki ki ,sannan kulum se kin fito
falonnan kin zauna da safe kafin na fito ,Ina fitowa ki daga kanki Kita kalo na da
murmushi Ina karasowa ki gai Dani har se na fita ,

Abu na biyu ban son kazanta dole ki fito ki dinga kula da gidannan ,abinci Kuma Zan
Nemo masuyi Dan nasan ba'abunda kika iya tatsitsiya dake


Daga yanzu ke Zaki dinga wanke min uniform dina kina jina "

da sauri murya na rawa tace "ehh"
Zanga karshen tsoron da aka ce kinayi na masu uniform , tunda da kika tashi duk
kika tsallake sauran kaki ki ka fado kan soja


"Ni nama fara zargin ke kika je kika ce kina Sona, ko ba haka bane?"


Hawayen da ke ta zubo Mata take sharewa murya na rawa tace
"A'a wallahi nima ba'a son Raina bane kaddara ce kawai Ammah me zesa na auri soja"
Wani Abu yaji yana taso masa tundaga zuciyarsa yazo kan magoransa ya tsaya be fito
ba, yana mamakin yadda har ta bude Baki a gabansa Wai bata son soja,lallai ya
kamata ya koya Mata wani hankali




Cewa yayi "zo nan"


Rarrafowa ta fara yace "Mike tsaye kizo nan yayi nuni da gabanshi "

Kafafuwanta na hardewa ta tako ta tazo fizgota yayi kamar zata fado jikinsa yayi
azamar matsawa ta fado gefen sa kafin ta daidai ta se saukar hannunsa taji Akan
bakinta

Duk da yaji labban nata akwai taushi Ammah be Hana ya fasa abunda yayi niyya
ba ,wata irin murza yake ma labban nata da zafi zafi Aiko tuni hawaye ke zuba a
fuskarta ta ta kokarin ta kwaci kanta ta kasa

Se da ya gaji Dan kansa ya saketa Aiko nan take labbanta sukayi sutum ,sutum

"Kalle Ni"


Dago rinannin idanunta tayi ta kalle sa ,se da gabanta ya fadi ganin yadda idanun
nasa ke rikitar da ita , sunkuyar da Kai take kokarin yi

"Ki kallan na ce"

Kallon sa take tana kuka ,yace "daga yau duk na sake jin kince dole aka Miki a
aurena ,ko Kuma Baki son soja ko me kaki jikin kine ze fada Miki "


Kuma masu kaki kisa a ranki daga yau kin fara sonsu kina jina ta daga Kai
Yace da Baki Zaki ban amsa

Tace "Ehh"

Tashi yayi ya dau bindigar sa ya nufi dakin sa

Ai Amal kukanta ta ci gaba dayi anan Tama kasa tashi banda azaba Babu abun da
labbanta ke Mata


Motsin fitowar sa taji da sauri ta hadiye kukan da take ,matsowa yayi ze fita
yace"ki tashi kije kiyi sallah ,Kuma alkawarin harbinki na nan matukar Baki bar
wanna sakarcin da kike ba


Yana fita ta dago Kai tace"Allah ya saka min a fili"
Tashi tayi ta nufi dakinta

Bayan ya fito daga massalaci ne yaya Sadiq ya sake kiransa be daga ba kasancewar ya
gane number ,gida kawai ya nufo yana tunanin kurciya irin ta wannnan yarinyar da
aka lakaba masa

Da ya tuno yadda take kuka,se da ya Dara
Nace to fa🤔

Yana shigowa dakinta ya nufa ko da ya shiga Tana kan daddumar da ta gama sallah

Gai da shi tayi ya Amsa ,sannan yace yawwa waye Abubakar sadiq a kano ,dago Kai
tayi se kuma ta sunkuyar da shi ganin ita yake kallo

Ta fara da"Ahm yaya nane Dan yayan Abba nane,Kuma shi yake auren yayata"

Tabe Baki yayi yace "to ya Kira suna son magana dake ,duk kika yadda kikayi magana
akai na Zan gane"

Ya aje wayar kan madubi ya fita

Ba karamin dadi taji ba jin cewa yaya Ramla ce ke son magana da ita tashi tayi ta
nufi madubin ta dau wayar Aiko se ga wani Kiran ya shigo.................✍️




*Aysha galadima ce*


Vote
Comment
Share
[8/25, 8:02 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*



```Follow me on #wattpad @Ayshagaladima666```




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)
```Ban manta daku Ba```

*JATTAKO NOVELS GROUP 2*

*ALHUBBUL AAMAH FANS GROUP*

```comments din ku na sani nishadi```




*PG43-44*



____________________________

Daga wa tayi cikin zumudi se taji muryar yaya Sadiq ce gaisawa sukayi har Yana
tsokanarta Yana cewa"kanwata ya Amarci?"


Rufe Ido tayi kamar Yana ganin ta tace "Yaya bana so"

Dariya yayi ya Mika ma Ramla wayar da kamar ta kwato a hannunsa tunda taji Amal ce
ta dauki wayar,ai ko Tana karba ta barshi Nan tsaye ta nufi bedroom,kallonta kawai
yayi ya girgiza Kai ya nemi daya daga cikin

Please Login or Register in order to submit comment