Reading ANYI GUDUN GARA BY Aisha Galadima Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerin falon ya zauna.



Tana shiga dakin ta Kara wayar a kunnenta tace "Amal"
Daga can bangaren tace "Aunty Ramla ya kike nayi kewar ki" se kuka ta sakar
Mata ,daurewa kawai Ramla tayi itama ,saboda tayi kewar kanwarta ga Kuma auren da
aka Mata na bazata

Da taji batada niyar yin shiru tace"Kinga in kuka Zaki yi bari na kashe wayar"

Ai da sauri tace "na Dena " Nan suka gaisa , Amal tace "Aunty kin San Wai mijin da
aka aura min sojane?"
"Eh na sani ,Kinga yadda Allah ya kaddara Miki ko shiyasa ko yaushe nake fada Miki
ki fidda wannan shirmen da kike na kin masu kaki,gashi yanzu da ubangiji ya tashi
se y hada ki da shi"
Kuka Amal din ta fara ,se kuma taji ta bata tausayi ita tasan wacece Amal

Sauke ajiyar zuciya tayi tace"yanzu abunda nake so dake ki kwantar da hankalinki
Kuma ki cire ma kanki tsoron da kika saka ,duk kin kayi sallah kiyi Addu'a Allah ya
cire Miki wannan tsoron,Dan in ya San kina wannan shirmen ban San me ze faru ba"

Se kuma tayi shiru taga Tana Shirin ballo wasu ruwan,karku manta Ramla tasan farouk
ne ya taba Marin Amal,sannan har gaida shi tayi kwanaki ya share ta


Amal ta katse Mata tunani da tace "Aunty yace se ya harbeni da bindiga ma " Tana me
ci gaba da sheshekar kukanta

Har se da Ramla ta katseta da cewa "me kika masa ne?"

Nan ta kwashe yadda suka yi ta fada Mata,ai ko Ramla dariya kamar ta karta ,shiru
kawai tayi Dan kar Amal din taji haushi
Nan dai ta bata shawarwari masu matukar Amfani ,sannan tace duk abunda farouk din
ya sata ta dinga masa,sannan tace ta diba Jakarta da ta ratayo Ashe kowacensu ciki
aka saka Mata sadakinta,tace tayi kokari tayi waya yadda zasu dinga magana tace to
Aunty nagode sukayi sallama

Tana son ta fita ta bashi wayarsa Tana tsoro,Kiran wayar Akayi taga ansa kakus akan
wayar ba shiri ta fito falon Yana zaune Yana cin Abinci a take away kasa Akan
carpet karar wayarsa ya ji juyowa yayi Yana kallon ta a darare ta iso ta Mika masa
wayar karba yayi yace "zauna"

Daga wayar yayi ya Kara a kunne yayi sallama daga can bangaren aka amsa ,sannan
taci gaba da cewa "Habubakar yanzu ka kyauta kenan daga aure har ka manta Dani ,duk
da nima daga baya nasan da maganar auren,to yanzu dai gani na shirya kazo ka kawo
Ni Naga Amarya"

Shiru yayi be bata Amsa ba har se da ta sake cewa"baka jina me?"

Sannan yace Ina jinki in na tashi da Kaina Zan kawo ki kit ya kashe wayar yaci
gaba da cin abincin sa ,Amal dai na gefe rabe

Dago Kai yayi ya kalle ta, sannan yace ga abinci Nan dauka kici,gobe Zaki fara naki
In Allah ya kaimu,da kin gama ki fito ga kayan can Dana cire ki wanke
"To tace a sanyaye ta dauki ledar da away ke ciki ta nufi dakinta


Tana shiga ta zauna ta bude ledar dama yunwa take ji , ta bude, fried rice ce da
wani naman kaza a ciki
Abincin ta saki jiki taci sosai sannan ta Mike ta fito a hankali ta nufi kitchen
fridge ta bude ta dauko Ruwa ta Sha ta fito tazo falon can nesa da shi tayi tsaye,
tafi minti biyar a tsaye

Yana kallonta ta gefen Ido yayi kamar be San da ita tsaye ba ,gajiya tayi da tsayin
ta dukar da kanta kasa tace "Ahm Ina Kayan suke"

Shiru yayi ya kyale ta , se can yace "suna dakina"

A sanyaye ta juya ta nufi dakin a hankali ta tura kofar ta shiga da sallama,
Masha'Allah tace, dakin Ya matukar yi Mata kyau ,komai na dakin Royal blue ne ,a
hankali ta karaso tsakiyar dakin ta fara raba Ido inda zata ga kayan ,idanunta ne
suka sauka akan kayan dake aje gefen gado ,runtse idanunta tayi da sauri gabanta na
faduwa,Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un ta fara fada, a hankali ta fara samun
natsuwa karasawa tayi kusa da Kayan
Hannunta na rawa ta Mika hannun bayan ta rufe idonta ta dauki Kayan ,ta juyo ta
nufo hanyar fitowa ,dai dai lokacin da ya kunno Kai ze shigo ,ganin ta dade Bata
fito ba
Yana shigowa Tana kawowa wani irin karo suka yi da har jikin su ya gamu gaba daya a
jikinsa ta fada ,daga shi har ita se da suka ji yamm a jikiinsu da sauri ya tura ta
daga jikinsa , tuni ta saki kayan jikin ta rawa ,shima a sanyaye ya wuce ya zauna
bakin gado ,ita ma da sauri ta dauki kayan ta fita,juyowa yayi ya harari hanyar
data fita, tashi yayi ya shiga bathroom

Har ta fito daga dakin Zuciyarta Bata bar bugawa ba dakinta ta shiga ta wuce ban
daki da kayan ta zuba a cikin bucket ta zuba ruwa,a daddafe ta fara wankin da kyar
take daga rigar, kunsan yadda kayan sojoji suke,dama wankinsu se maza ,Tana yi Tana
Nishi,da sabulun wanka ma take wankin ganin Bata ga klean ba ko wani sabulun ,se
bayan la'asar ta gama duk ta jikata ,sannan ta fito da bucket din ta rasa inda zata
yi shanya kitchen ta shiga inda taga wata kofa Tana ko turawa taga bayan gidan ne
akwai wani karfen tanki anan ta shanya kayan ta dawo ciki, daki ta shiga tayi
sallah ta kwanta,saboda gabobinta ciwo suke Mata wankin da tayi
Ni ko nace ko jika-jika ba🤣

Shima farouk wanka yayi ya fito yana tsaki ,saboda ya rasa dalilin da yasa har
yanzu jikinsa yaki komawa dai dai tunda yarinyar nan ta fado a jikinsa,agurguje ya
watsa ruwa ya fita gidan Baki daya


Kai tsaye gidan su ya nufa,Yana shiga falo ummee ya tarar zaune a falon sakin
fuskarsa yayi yaje kusa da ita ya gaida ta,Tana murmushi ta Amsa tace "babana Ina
diyata?"
Bata fuska yayi ya wani turo baki gaba tamkar yaro ,sannan yace "tun yanzu har kin
zabi wata akaina"
Murmushi tayi tace"kwarai kuwa"

"Ammah ummee da tsohuwar Zuma ake magani"
Cewa tayi "ai da sabuwa ma maganin yafi"

Shiru yayi ya jawo wata hirar daban sunanan zaune se ga Abbah ya dawo gaisawa suka
yi Nan yake masa maganar karatun Amal,Akan ya nema Mata wata makaranta taci
gaba,Nan yace to Insha'Allah ,nasiha da Jan kunne suka Kara masa akan ya kula da
matar sa, ya sake godiya
Abbah nata saka masa albarka da ummee ganin ya karbi auren nasa


Kuma ya samu sakin fuska fiye da kwana biyu da suka gaba ta,sallama ya masu ze fita
, ummee tace jirani na dauko ma sako kaba diyata ,tsayawa yayi
Ta shiga kitchen ta fito da wata kyakyawar kula ta bashi ,se ya fita Yana mamakin
yadda uwayen nasa ke ji da yarinyar


Kai tsaye gidansa ya nufa, Koda yaje ya shiga da sallama ba kowa a falon Ammah yaga
Alamar kamar an Kara gyara falon an saka turaren wuta tabe Baki yayi ya aje kular
Akan kujera ya nufi dakinsa Yana tsaka da cire kayan jikinsa ,se yaji sautin kuwar
Amal,da sauri ya fito ya nufi dakinta kafin ya kaima se gata ta fito da gudu tana
ganinshi jikinta ya fara rawa,saboda ba kayan Arziki ne a jikinta ba daga ita se
under skirt da 'yar shimi,har ta yi Shirin kwanciya ne ,se ta shiga ban daki tayo
fitsari ai ko Tai arba da 'yar kadangarwa



Se da ya gama kare Mata kallo sannan ya ce"Wai ke mahaukaciyar Ina ce ,da za ki
dinga yi ma mutane kuwa kamar gidan 'yan bori?"


Ita dai Tana gefe ta rabe ,se zare idanu take tace"wani Abu ne a bandaki" murya na
rawa

Yana mamakin yadda take masa wata shagwaba in Tana magana ji yayi kamar ya
maketa ,tsaki yayi ya shiga dakin ,koda ya shiga dakin bathroom din ya shiga Nan
yaga Ashe karamar kadangarwa ce ta shigo, tagar bathroom din ta can baya ya rufe
Dan ta Nan ta shigo se da ya jefar da ita sannan ya rufe tagar ya fito

Tsaye yayi cikin dakin yace "kina inane?"

A darare ta shigo ta koma can gefe ta tsaya ,kallon abunda take kawai yake yana
mamakin Abubuwan da yarinyar keyi

Cewa yayi"me na fada Miki Akan yi min kuwace kuwace a gida?"
Hawaye ta fara , sannan tace"Dan Allah kayi hakuri"

Dan tausayi ta bashi kadan shiyasa be ce Mata komai ba ya juya ze fita ai da gudu
ta karasa kan gado ta ja bargo ta rufe fuskarta

Shi dariya ma ta bashi yace"matsoraciyar banza "

Ya fita, Tana jin ya fita ta bude fuskarta Tana sauke numfashi ,se da ta Kara
Shirin bacci sannan ta kwanta


Washe gari bayan ta gama sallar Asuba Nan fa ta tuno da kayansa da ya sata wanki
fita tayi ta dauko su se da ta shigo falon sannan taga kayan duk sunyi huri irin na
sabulu , Tana Nan tsaye Tana tunanin ya zata yi taji takun saukowar sa falon Yana
ko saukowa idonsa suka fada kan kayan yaga yadda duk ta bata masa su da sabulu Nan
take ransa ya baci ,matsowa yayi kusa da ita Bata San da zuwansa ba se hucinsa taji
Tana juyowa ko ya daga hannu.............✍️




*Aysha galadima ce*



Vote
Comment
Share



*Aysha galadima ce*


Comment
Share.


[8/25, 7:52 PM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*
_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG45-46*



______________________________


Ya daga hannu ze mareta ,runtse idanun ta tayi jikinta na rawa Tana jiran saukar
Mari taji shiru , bude Ido tayi se taga ya dauki kayan ya nufi dakin sa da
su ,Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi dakinta da sauri

Yana shiga dakin cikin kayan wankinsa ya sasu , ya dauko wasu kayan ya saka ya fita
, be koma bi ta kanta ba

Jin motsin fitarsa yasa ta fito Tana cewa"Wai Allah ya so ni da mugunan ya maran
da wannan katon hannun nasa ai se Naga taurari, Allah yasa ma se dare ze dawo ,
kitchen ta nufa ta dauko plate da cup ta nufi dinning tayi breakfast ta kula shi be
ma ci komai ba ya fita


Koda farouk ya fita Kai tsaye office ya nufa ,Yana zama khaleel na shigowa sallama
yayi da kyar ya Amsa masa ,zama yayi Yana tambayarsa me ya faru Nan yake sanar masa
ai ko dariya ya shiga masa yace "ai wlh Amal ta min dai dai in ba haka Ina ita Ina
wankin kaki in Banda mugunta irin taka,ai ta biyani goro da abunda tayi

Kallonsa yayi yace haka kace ai kuwa ka ja Mata se tayi wani aikin Kuma

Ohho dai duk abunda zakayi ka dai ji tsoron Allah ,yawwa Wai yanaga ka fara wani
glowing ko har an wuce wurin?

Wani malalacin kallo farouk kema Sadiq din sannan yace"Kai fa Dan iskane in ba
rainin hankali ba wannan yarinyar da ko kwarin Kashi Bata da kake tunani Zan iya
wata mu'amula da it?"

Kallon gara khaleel din ke masa yace "a'a jaririya ce ba kwarin Kashi ne Bata da
ba,wallahi tun wuri ka shawo kanta a wuce wurin ,idan ba haka ba Ina jima tausayi
zuwa Nan gaba Dan yaran da kake rainawa sunfi wasu manyan Mata komai,sannan yanzu
ba'abunda basu sani ba"

Tashi farouk yayi ya bude kofar office dinsa yace "malam zo ka wuce ka barni nayi
aikina ,tunda Kai baka da abunyi"

Mikewa khaleel yayi Yana dariyar mugunta yace "ai Kai ne zaka zama marar aikin yi
Nan gaba kadan ,sannan ya fice daga office din,tsaki farouk yayi sannan ya rufe
kofar office din




A haka zaman nasu ya kasance kadahan madahan har aka cinye sati biyu da
bikinsu ,Wanda a lokacin Amal duk ta saki jikinta wanna tsoron da take dashi cikin
Kashi 100,zan iya cewa saura Kashi 20 ,tun lokacin abun da ya faru farouk be koma
sata wanki ba se dai ita ke gyaran dakin sa, iya karta da shi gaisuwa ,girki Kuma
tuni ya aje Mata komai na bukata ita ke dafawa da kanta


Yau Koda ta tashi taji jikinta duk ya Mata wani iri ta fara jin Alamun kamar period
dinta ne ze zo dama Tana Dan ciwon mara Ammah ba me tsanani ba daki ta shiga ta
Dan kwanta bacci ya dauke ta ,se kusan Azahar ta tashi koda ta tashi kuwa duk ta
bata bedsheet din ,ahankali ta tashi ta shiga ban daki ta wanke jikinta ta fito,
bedsheet din ta canza ,sannan ta nufi wadrop ta dauko wasu kayan ta saka se dai
Bata da pad din da zata yi amfani da ita, tunowa tayi da jakar da Anty Ramla tace
kudinta na ciki jawota tayi ta bude ,kudine da yawa a ciki Bata tsaya kirgawa ba ta
dauko 3k ,ta sa hijab dinta ta fito gate din gidan wani kurtun soja ne ya taso ya
nufota yace
"Madam me kake so?"

Shiru tayi Tana kallonsa ,Tana tunanin ai bari ma ta aike sa , kudin ta Mika masa
tace "akwai chemist Nan kusa?"

Cewa yayi "yes"

Tace to idan kaje kace a baka pad pack din gaba daya

Karba yayi ya fita,
Ita Kuma ta koma cikin gida
Iya ka minti biyar taji karar hon da'ake tayi ,Ammah Bata yi tunanin nan ake hon
din ba ta cigaba da aikinta a kitchen

Ganin shiru Emmanuel be bude masa gate ba ya sa ya fito daga mota ya nufo gate din
karamar kofar ya bude ya shigo ya bude gate din ya shigo da motar sa sannan ya rufe
,dakin Emmanuel din ya shiga ya ga ba kowa

Tunani yake to Ina ya tafi ,muryar kakus ce ta katse masa tunani da cewa" Wai
bazaka zo ka bude Ni ba kabar Ni a mota"

Juyowa yayi yazo ya bude Mata ta fito Tana kallonsa tace "lafiya kake ta dube
dube?"

"Me gadi nake nema"

Ya fada Mata a takaice ,rufe motar yayi yace muje to gaba ta shiga ya biyo bayanta
knocking ya fara da sauri ta fito ta nufo kofar ta bude ganin sa da tsofuwa yasa ta
basu hanya Tana fadar "sannunku da zuwa"

Shigowa sukayi kakus na "sannunki 'yar Nan sannan suka wuce kakus ta zauna kan
kujera shima zaman yayi ,gaisawa sukayi sannan ta Mike ta nufi kitchen ruwa da lemu
ta azo bisa try da cups ta fito a hankali ta je inda kakus take ta duka ta aje Mata
tace"babah ga ruwa"

Dagowa kakus tayi tace"wace Babar ,Ni karki sake kirana babah ,kakarki ce Ni tunda
kakar mijinki ce "to " Amal tace

Yawwa "ya bakunta Kuma 'yar Nan "
Tana murmushi ta kare maganar

A Dan sake Amal tace "lafiya Lau "

Tashi tayi ta shiga daki Tana Dan kakkame jiki gudun kar tayi staining
Duk abunda ke faruwa Yana jinsu yayi Shirunsa ,lumshe Ido yayi har se data tashi
zata shiga daki ya bi bayanta da kallo ,Yana tunanin kamar taki sakin jikinta har
yanzu ga Kuma yadda yaga Tana tafiya

Knocking da Akayi ne ya katse masa tunani tashi yayi ya nufi kofar Yana budewa yaga
Emmanuel ne ,kallon mamaki yake binsa da shi

Sosa Kai Emmanuel yayi yace"oga na madam send me"

Yana mikawa farouk leda karba yayi ,emmanuel ya tafiyar shi bude ledar yayi yaga
miye aciki idanun sa suka fada Akan VIRONY PAD

Ranshi ne ya baci Nan take ,tunani ya fara me wannan yarinyar ta dauke shi ,Dan
rashin tunani me gadi zata aika sawo pad , mi yasa ba zata fada mishi ba juyawa
yayi ya ya rufo kofar da karfi har se da kakus ta saki Baki Tana kallonsa, fuuuu ya
wuce ya nufi dakinta Yana shiga Tana kan gado da sauri ta Mike zaune

Nufota yayi ya jefa Mata ledar a jikinta yace"ke Wai wace irin marar kunya ce da
har zaki aiki me gadi ya sawo Miki wannan abun saboda Baki dauki aurena da mutunci
ba ko" ya kare maganar yana huci kamar wani Zaki

Dama kanta banye yake ,matsowa yayi ya kama gashin yaja yace "ko Baki jina ne?"
Tuni ta fara hawaye
Kofar dakin aka turo........... .✍️



*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share
[8/26, 8:44 AM] Aysha Galadima:
*ANYI GUDUN GARA*




*NA*
*AISHA GALADIMA*




*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*



```Follow me on #wattpad @Ayshagaladima666```




_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana
manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya
tuntubar wannan number_
(08064933819)



*Rayuwa ba tsere bace*, *kar ka taba damun kanka Akan se ka wuce wani*
*Duk Abunda Allah ya rubuta ma baza ka iya canza shi ba*




*PG47-48*



______________________________

Jin an turo kofar dakin cikin sauri ya maza ya zauna ya rungumota ya na fadar
"menene ya shiga idon naki ?"

Ita dai Amal tuni ta saki Baki Tana kallonsa da mamaki fal a ranta
Gyaran murya kakus tayi Tana iyar da shigowa dakin Tana cewa "me ya shiga idon nata
ne Naga fuskarta tayi shabe shabe da hawaye?"

Juyowa yayi yace
" nima haka na iskota tace min wai wani Abu ya fada Mata a ido"

Ita dai kakus kallon tuhuma take ta binsa da shi ,ganin irin kallon da take masa
yasa ya waske yace "to kije kiyi wanka , ki wanke fuskar taki Kuma"

Ya tashi ya fita ,bayansa kakus tabi da kallo ,sannan ta shigo Tana kallon Amal din
tace "ya Miki wani Abu ne"

Da sauri tace"A'a ba abunda yamin"

Tabe Baki tayi tace "to yayi ke kika sani Ni ki fito ki bani abinci ta juya ta fita
, Amal tashi tayi a hankali ta dauki ledar pad din ta bude ta dau daya ta kimtsa
kan ta ,Tana yi Tana tuna yadda ya wani rungumeta Yana shirya zance, lallai
mutumin Nan Dan duniya ne, Kiran da kakus ta Mata ne yasa ta fita da sauri

Har yanzu suna falon harshi ,kitchen ta wuce ta fito da kulolin abincin ta Dora kan
dinning seda ta gama jera komai sannan tazo wurin kakus tace
" ga abincin can na shirya"

sannu ta mata ta tashi suka nufi dinning ga mamakin Amal harshi biyo su yayi
dinning din ,shi Kuma yayi haka ne Dan kar kakus ta zargi wani Abu ,yasan tsab zata
fada ma Abbansa ,Abincin ta fara zuba ma kakus,white rice ce da miyar dage dage
data ji kaji se salad da ta yanka bayan ta zuba Mata ne

shima ta zuba masa ba sosai ba ta tura gabansa,a yadda yake ganin abincin da Kuma
kamshin da ya cika masa hanci ransa ya biya sosai Yana Kuma fatan yasa yayi dadi


Kakus ce tace"ke Amali Kara masa abincin wannan Dan tsiton abincin Zaki ba
mijinki ?"

"To Wai ke me ya dame ki da matata ne har kike wani Bata Mata suna"
Cewar farouk
Amal ji tayi abun wani banbarakwai Ammah a yadda yama kakus maganar se taji ya
burge ta🤣

Kakus tace
" nayi maganar har wani zaka nuna ma Mata bayan se da aka gaji aka ma auren tazuru
kawai"

shi dai abincinsa ya ci gaba da ci be kulata ba ,abincin ba Karamin dadi ya mai ba
Nan yake cewa Ashe dai ta iya girki har ka dama

Nace to da ya ka dauke ta🤣

Kakus yini daya ta musu ya mayar da ita Amal ko sabbin kayan da ta gani a drawer da
ba'a Dinka ba ta dau Atamfa daya da turare taba kakus ,Aiko kakus godiya Tai ta
Mata har farouk se da ta nuna ma,shima yaji dadin hakan da tayi Kuma ta Kara kima a
idonsa


______________________________

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah yanzu har sunyi wata biyu da aure ,Aunty
Ramla har an samu karuwa kasancewar cikin nata tun yana wata daya take ta laulayi
tun basu gane ba har suka shirya suka je Asibiti Nan fa aka ce ciki ne da
ita ,murna wurin yaya Sadiq ba'a magana ai ko ba kunya ya Kira gidansu ya fada,ita
Ramla kunya tai ta ji ,shi Kam ko a jikinsa ,yau suna shiri ne zasu je kaduna ta
gano gida da Kuma Amal


Da kamar ma baze barta ba yace se ta haihu.

Se da ummansa tasa Baki sannan fa ya yadda ba Dan ransa ya so ba ,dole ya
hakura,tayi shiri yau zata zo ,shi Kuma ze kawota

Washe fari da wuri. Suka taso suka zo kano ,iyayensu sun yi murna da ganinta cikin
koshin lafiya ita ma haka ,bayan sun huta ne ,washe gari yaya Sadiq ya juya bakin
aikinsa



A bangaren Amal ita ma abubuwa da yawa sun faru ,yanzu yaya farouk ya bar takura
Mata da fada ko hantara ,iya karta da shi gaisuwa da Kuma kula da gida se girki da
take masa ya ko saki jiki ya kwashi abincin sa ba kunya ba komai🤣

Har gidansu ya kai ta kwanaki Nan me ummee ke cewa ya sawo Mata waya yace to da
zasu dawo ne ya biya ya saya Mata ITEL P33PLUS ,ai ko ranar yasha godiya wurin Amal
har se da ya gaji yace ya isa hakanan ,yanzu ma Shirin shiga school take yi Dan har
ya kammala Mata komai Ammah cewa yayi ss3 zata shiga yadda ba jimawa zasuyi exam se
ta shiga jami'a
Ranar kusan raba dare tayi ta na murna har gari ya waye shima yaga canji sosai a
wurinta se fari'a take har suka zauna yin breakfast se tace

"Yaya nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi "

Dagowa yayi ya kalleta yace Amin
Kafin yace
"Naga alamar tunda Akayi zancen school dinnan kike ta farin ciki Allah yasa zakiyi
karatun ba Wasa Zaki yi
Ai Amal sake sakin jiki tayi Tana washe Baki tace" Allah yaya karatu Zan yi sosai
da ma fa Ina matukar son karatun sosai"

Kallonta yayi shima ya Dan saki fuska yace"Really"

Tace "eh"

Yace "Allah ya bada sa'a"
Tace "Amin"

To zan iya cewa shima farouk tuni ya watsar da haushin aurensa da yake ji ,Dan ya
kula yarinyar nada hankali Bata damu da shi ba ma ,sannan a Dan tsakanin Nan ya
rasa meke damunsa akanta ,duk lokacin da ya zauna baya da aiki se tunanin ta, har
khaleel ya so dago sa, ammah se yace masa Allah ya kiyaye shi Kam me ze sa ya zauna
yana tunanin Amal

Se dai khaleel yayi dariya yace "zama kazo ka fara ne"

Bayan fitarsa ne ba jimawa taji ana knocking Tana budewa taga Aunty Ramla ai kuwa
ta saki kuwa ta rungumeta ,ita ma rungumeta tayi suka shigo gidan ,bayan sun saki
juna ,Aunty Ramla ke ta kallon Amal ganin yadda cikin wata biyu ta murje ta Kara
wani fari sosai,ko ita da ke da yaron ciki jikinta be canza kamar na Amal din ba

Ganin irin kallon da Ramla ke Mata yasa tace
" aunty lafiya?"

Murmushi tayi tace kanwata Naga duk kin canza ko dai mun samu baby ne matar soja

Rufe fuska tayi Tana dariya tace a'a Aunty ba komai Allah ,tace "to naji , to ya
kike ya gidan

"Tace lafiya Lau"

Tashi tayi taje kitchen ta dauko ruwa da lemu da Kuma snacks ta gabatar ma Ramla

Ita dai Ramla se biyar Amal din take da Ido taga ta fara Hankali,tana Kuma jin
dadin yadda ta iskota lafiya Lau


Ruwa kawai Tasha ,saboda tunda ta samu cikin Nan ba komai take ci ba ,Amal din ce
ta zo tace "Aunty tashi mu shiga dakina?"


A hankali ta tashi ta bita ,suka shiga gado Amal ta nufa ta zauna , Ramla na Shirin
zama kan stool tayi sauri tace

Aunty ki zauna kan gado Mana

Harararta tayi tace "gadon mijin naki Zan hau ,Allah ya kiyaye"


"Ai ba Nan ya ke kwana ba gadonsa na dakinsa ,a can yake kwana "

Kallon tuhuma Ramla ta fara ma Amal din kafin tace
"Wai har yanzu baku shirya ke da mijinki bane?"

Murmushi Amal tayi kafin tace "ai yanzu mun shirya aunty ba kamar da ba Kinga ya
siyamin waya Kuma yanzu ya mayar da Ni school ,sannan ya ce Ni ai kanwar sa ce ,
yanzu ba ya sani aiki me wuya baya min fada Kuma duk abunda n nace Ina so Yana
siyamin"


Kallon marar wayau Ramla ke ta biyar Amal din da shi kafin tace

"Habah Amal ke Wai kamar Baki taba zuwa Islamiyya ba ,ai duk wadannan abuabuwan da
kika lissafo ban ji kince Yana sauke hakin sa na aure ba"

"Aunty nifa kanwarsa ce Baki ga yadda muke shiri ba"

Buge bakin Ramla tayi ,Amal ko ta bata fuska ,Nan Ramla ta shiga yi Mata fada sosai
,sannan ta dawo ahankali ta mata bayanin komai dalla dalla Nan fa ta dinga rufe
fuska,inda a karshe ta bata shawarar Abubuwan da zata dingayi har ta jawo
hankalinsa ,ta ce Mata Kuma"in kika yi Wasa kina Nan zakiji yayi aurensa ya barki

Ai ko Amal tace"aure Tana zare ido" dama kishi ne da ita kamar me ,Nan fa tace
Aunty Insha'Allah Zan gyara
Ramla tace da dai yafi Miki ,Nan ta bude jaka ta dauko wani littafi me suna
DON MA'AURATA
ta bata Nan ta shiga yi Mata godiya

Kusan yini Aunty Ramla tayi a gidan Dan har farouk ya isko ta a gidan ,suka gaisa
cikin sakin fuska kuwa har yake tambayarta yaya sadiq tace Yana Nan lafiya

Ganin ya dawo aunty Ramla tace zata wuce yace "ta bari yazo ya Kai ta "

Ai ko Amal Tai kwal kwal da Ido kamar zata yi kuka ganin Ramla ta fito zasu
wuce,cewa yayi je ki dauko hijab dinki mu kaita

Ai kusan da gudu ta juya ta dauko hijab dinta suka je tare Kai Aunty Ramla
gida,suna Akan hanya se da ya tsaya a wani mall yayi sayyayya sosai,sannan ya dawo
cikin motar suka ci gaba da tafiya har suka iso kofar gidan Nan Ramla ta masa
godiya zata fita kudi ya dauko ze Bata ,taki

Please Login or Register in order to submit comment