sanya ki kuka irin haka? Ta ruko hannuna na dama ta dora a saitin inda zuciyarta take. Wani irin bugu take yi fiye da kima. Ta zuba mini idanuwanta da barci da firgici suka jirgitasu. Na yi kasa da kaina ina gunjin kuka. Ta rike hannuna sosai tabbacin hakuri take ba ni duk da bata furta hakan da baki ba.
Da rawar murya na ce "Yaya Faruk ne Abida! Na furta hakan cikin rushewa da kuka fiye da wanda nake yi.
Ta zabura ta fita ko mayafi bata saka kan doguwar rigar barcinta cotton ba.
Da Yaya Sulaiman ta yi kicibis.
Ya shigo diban ruwan da lemo a fridge din momi.
A matukar razane ta ce "Me yake faruwa ne a gidan nan Yaya Sulaiman? Ina Yaya Faruku?"
Ya amsa da ce wa "Ga shi can ana masa jajjabin an kasa shi a soyayyarsa da Bilki!
Tausayinsa ya tsirgawa Abida ta sani yana son Bilki, ta kuma sani tunda ya gane Yaya Asad shima an jarrabe shi akan sonta shiyasa ya shiriritar da maganar tun kafin su fahimci Yaya Asad na sonta shi ya fahimci hakan.
Gabadaya dukkansu uku tausayinsu take ji, amma a yau na Yaya Faruk yafi tsananta.
Bilki kuwa haushin yadda ta rufe ido ta kasa zaben mutum guda a cikin yayyen nasu ya dakushe tausayinta.
Ta koma ta zauna a bakin gado tana hurar da iskar damuwa. Kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce "Bilkisu ki rufe mini baki, tun ban miki sanadin da zaki yi kuka fiye da hakan ba. Wanne irin kasafi ne haka? Menene zaki yi kuka akan Yaya Faruk alhalin ba dole aka yi miki kika zabi waninsa kika bar shi ba.
Ko makaho ya zauna da ke da Faruku sai ya gane yana tsananin sonki, amma kika runtse idanuwanki kika bar shi. Yanzu kuma ki ce zaki yi kuka dan yana bayyanawa duniya alhinin asarar rashinki da ya yi!
A matukar kufule take wannan maganar.
Tashin hankali ya yi mini kawanya. Zullumi da fargaba suka saka na yi zurzuru cikin lokaci kalilan. Na rarrafa na isa gaban gadon da take zaune na durkushe gabanta na ruko dukkan hannuwanta biyu, murya na rawa na ce "Abida ki yi mini adalci, ki ji tausayina ko iya na yau ne a rayuwata.
Na rasa gane me nake ciki, kaina na shirin fashewa, zuciyata na shirin tarwatsewa Wallahi ina jina cikin bala'in da ya yi mini dauri tamkar huhun goro!
Ta sassauta amma bata furta komai ba.
Na ce "Ki yi alkalanci na gaskiya Abida kin sani ina sonki, kin sani da ke nake son na yi sharing damuwata anan duniya dan Allah kada ki rufe mini wannan damar a wannan tsukun da nake ciki na cankacakare"
Ta cigaba da yi mini zuru hakan da na gani na alamta mini hankalinta na kaina tare da abin da zan furta.
Hawaye na zuba na ce "Abida tsakaninki da Allah Yaya Faruk ya taba tsayawa kai da fata akan yana sona, so na gaske?"
Ban jira amsarta ba na ce "Na sani kun fi kusa da shi a kaina, amma ban zaci zaki yi mini irin wannan son kan ba Abida. Ya kike so na yi? So kike na ce wa baba babba Yaya Faruk nake so ya aura masa ni alhalin shi da yake namiji bai yi hakan ba? Bayan matarsa yana da halin ya auro uku ba ni kawai ba amma tsananin tsoronta, ya hana shi kuzari akan sha'anina. Amma ke da kika fahimce ni, irin fahimtar da babu wanda ya yi mini irinta sai kuma ki hau gaba da ni akan lamarin da bani da laifi a cikinsa ko kankani! Akan me zaki rufe mini kofofin tattauna halin da nake ciki Abida? Akan me zaki yi mini irin wannan alkalancin akan lamarina da ya Faruk?"
Na fada ina rushewa da matsanancin kuka domin tsakanina da Allah gabadaya na daburce na kidime ban san ina son yaya Faruk over ba sai a ranar.
Ta sassauta kwarai da gaske ta busar da iskar damuwa ta ce "Yaya Faruk mutum ne mai matukar karamci da sadaukarwa, yana sonki, yana da burin ya aure ki, so yake ki kammala sakandire sai ya bayyana ta yadda ba zaku dade kuna dating ba zaku yi aure. Kwatsam sai aka jarrabi yayansa da sonki, irin son da ya kasa boyuwa a kirjinsa da gangar jikinsa. Hakan da Yaya Faruk ya fahimta ya sanya ya zabi ya bar lamarinki a zuciyarsa gudun kada shaidan ya kawo musu yamutsi! Amma ke gabadaya kin tattara kin rufe kofar da Yaya Asad zai same ki, kin ga ai dole Yaya Faruk ya shimfida tabarmai a yi masa jajen asarar da suka taffka ta biyu babu "
Na kasa cewa komai sai kukan da na cigaba da yinsa ainun.
Murya ba amo Abida ta sake cewa "Dole na ji babu dadi akan sha'aninki mana.
Na yarda Yaya Faruk bai zo ya nuna kansa da gaske ba. Yaya Usman fa? Yaya Asad fa? Wanne irin hannunka mai sandane bai yi miki ba? Har mai suna ya yi miki alhalin bai sanya sunana ba, kinsan kuwa na fiki cancantar ya mini cibina ba dan cikinmu guda ba sai dan tun filazal ni ce tasa ke ta Yaya Faruk ."
Na zuba mata ido hawaye na cigaba da tsere akan fuskata.
Yayin da ta numfasa ta ce "Dan haka ki rufe mini baki da wannan kukan domin dai ke kika yiwa kanki zabin da kike ganin kin gamsu da shi. Ba kuma zai yiwu ki hana zuciyata taya y'anuwana yanuwana bakin cikin asarar rasa ki da suka yi ba, hakanan ba zaki iya cire mini takaicin yadda kika zabi zumuncinmu ya yi rauni ba.
Dan kuwa da wani cikinsu kika aura zan yi mu'amala mai k'arfi da gidanki fiye da ace bare kike aure".
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: https://www.instagram.com/deenah_cakes_and_more?igsh=c2lnZjk5Z3pjYjNw&utm_source=qr
*Deenah cakes and more -Kano*
*09038055790*
*IG @Deenah cakes and more*
*Snacks such as*
*Birthday cakes*
*Cupcakes
*Samosa*
*Springrolls*
Meatpie
*Frozen snacks*
*Event snacks*
*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
12
Na sake ruko hannunta na ce "Saboda hakan sai na rasa hakkin da nake da shi na zumunci? Shike nan har kawancenmu ma sai ya shiga tasgado Abida? Yanzu ba zaki sake a gidana ba dan ban auri siblings din ki ba? Ashe haka kike da son kai mai yawa ban sani ba?"
Ta girgiza kai ta ce "Bilkisu kada ki juya mini manufata, kin sani sarai da abin da muke fata ya tabbata a tsakaninki da wani cikinsu, yadda gidanki zai zama dandali a wajena ko ban biki mun tare ba, to kuwa zan mayar da gidan ne wajen zuwana da hutawata domin dukkanku nawa ne sabanin idan ke ce tawa zan dinga yin kaffa kaffa domim ko iyayenmu ma ba zasu yarda na yi ta yi miki jele mai yawa ba."
Da rawar murya na ce "Kira Yaya Faruk na fada masa ina sonsa ya je wajen baba babba sai a mayarwa da Sahal kayansa a dawo da auren kansa".
Ta zuba mini ido ta ce "Ai hakan ba mai yiyuwa ba ne. Ban ji a jikina Yaya Faruk mijinki bane har abada kuwa. Dama Yaya Asad kika ce. Dan kuwa Yana sonki fiye da Yaya Faruk. Nima kuma ina taya shi sonki, ina matukar son a ce ya yi amarya da ke. Da bakinsa ya ce mini da ace ubangiji zai kaddara ki zama matarsa da ya tabbatar dukkan niimomi sun tabbata a gare shi. Idan har zai zauna ya fada mini hakan ni da nake kanwarsa na tabbatar son da yake yi miki mai girma ne."
Na yi kasa da kaina na kasa furta kalma ko guda domin ni kam ban taba jin sonsa ba, asalima haushinsa ne ya sake cushe mini makoshi ta yadda ya zama sanadin da yaya Faruk ya shatawa soyayyata layi. A matukar raunane na ce "Ni dai sai idan Yaya Faruk ne! Na fada zuciyata a kuntace domin har cikin kasan zuciyata nake jin sonsa.
Ta ce "ai maganarki ta yi k'arfin da ba za'a canja da wani ba. Baba babba ne ya karbi komai yanzu kuma sai ya koma ya fadawa iyayen Sahal ya fasa bashi aurenki haka siddan babu dalilinsa na yin haka. Sannan kuma a ji ya daura aurenki da wani cikin yayansa. Anya ko duniya bata yi zundensa ba, mu da kanmu ai dole mu kalubalance shi da zama dattijon kawai".
A matukar raunane na ce "To ki dawo da amincin da yake tsakaninmu Abida. Ki daina share ni. Ki daina mini fishi Ubangiji ne shaidar ina cikin takurarren yanayi a dalilin auren da zan yi da kuma fishinki!
Ta numfasa ta ce"Na huce maigado. Amma kin sani tun filazal jinina bai hadu da yaron nan ba, nima zan roke ki. Ki yiwa Allah ki yi mini adalci kada ki saka ni mu'amala da shi, kada ku samu sabani ki fada mini domin zan sake tsanarsa ba kuma zan ba ki shawara mai dadi ba a kansa. Idan kuwa hakane to kawai mu yi zumuncinmu da harkarmu a tsakaninmu amma kada na shiga cikin aurenki na roke ki, da sunan Ubangiji ki yi mini wannan alfarmar dan so nake aurenki ya yi k'arko ya kuma yi albarka". Da kuka sosai na ce "Ba zan fada miki ba, ba zan saka ki ba tunda na gane ba kya son shiga din. Amma ki sani wannan matakin zai iya zama nakasu a zuciyata, domin kinsan yadda na saba sharing damuwata da ke. "
Ta numfasa ta ce "Ina fatan matsalolin da zaki shiga a gidan aurenki su zama kadan ne kuma masu sauki sosai."
Har aka yi sallar azahar muna tare cikin wani irin yanayi mun yi jigum jigum kowa na ta sake saken zuci, ba kuma mu sanyawa cikinmu komai ba.
Taron Yaya Faruk kuma sai lokacin ya tashi bayan sun yi jam'in sallah. Kowa ya kama gabansa suna ta yi masa tsiyar ya zama ragon namiji tunda ya bari wani ya shigo har cikin gudansu ya ci shi da yaki.
Can muka jiyo shi daga falon momi yana dokawa Abida kira.
Bansan ya aka yi ta kasa amsawa ba domin da gaske jikinta ya yi sanyi irin tubus din nan.
Ba a jima ba muka ji ana kwankwasa kofar ɗakinmu. Murya a dashe ta ce "Bismillah.
Ya turo kofar ya lek'o, da kansa kadan har ya fara hargagin tana jin yadda yake kiranta amma ta yi mukus alhalin ta ji shi. Ganinmu tare a zaune ga alamun kuka nake yi sosai ya sanya ya shigo d'akin gabad'aya ba tare da ya shirya ba.
A matukar gigice ya ce "Me ya samu sarauniyar shaiba ko dai zuciyarki na taya ni alhinin da tawa zuciyar ke ciki na gagarumar asarar rashinki ?".
Yana rufe baki na sake fashewa da kuka mai sauti tamkar dai ba shafe lokaci mai tsayi na yi ina kukan ba.
Ya sake rikice wa ainun domin tunda nake da Yaya Faruk a hankalina wannan ranar ne karon farko da ya kai hannunsa jikina.
Dukkan hannuwansa ya saka ya ruko nawa hannun dake cikin na Abida.
Ya kasa cewa komai domin idanuwansa sun kada sun yi ja matuka da gaske.
Ni da shi muka tsurawa juna ido, tuni nawa idanuwan suke zubar da hawaye yayin da nasa suka cika da kwalla taf.
Soyayyata baro baro a idanuwansa da gangar jikinsa gabadaya. Domin ya yi laushi da alamun rashin kuzarin da yake zuciyarsa ya shafi gangar jikinsa gabadaya. Duk yadda yake da hayaniya da kwarafniya sai da kawo kudin aurena ya yi masa bugun da ya yi matukar kasarra shi ya zama irin yanayina na rashin hayaniya da shiru shiru.
Murya na rawa na ce "Me yasa haka Yaya Faruk? Me yasa ka mini haka? Jamila ta fini tasiri da kyallin goshi a zuciyarka da idanuwanka ko?"
Idanuwansa na cikin nawa ya shiga girgiza kai murya ba amo ya ce "Ina ko kusa, ba haka bane Bilkina. Kawai ba a kaddara mini cikin littafin kaddarata cewar ke matata ce ba. Amma Allah da ya haliccemu ya sani na soki, ina kan sonki. Ba kuma zan daina sonki ba sarauniyar shaiba muddin ina zukar numfashi".
Daga haka ya kasa jarumtar sake cewa uffan illah rungeme ni da ya yi tsamtsam. Gabadaya jikina ya hau tsuma na kasa kwacewa domin na lura gabadaya ya manta cewar ni din ba Abida ba ce da idan ya rungeme ta irin haka shaidan ba zai kawo musu caffa ba dan kuwa muharramarsa alhalin ni kuwa so da begen juna ne a tsakaninmu.
Da kyar na yi jarumtar zamewa na koma gefe ina kuka sosai, abin mamaki sai na ga shima hawaye na zubar masa haka ma Abida. Na sake kaduwa domin Abida tana da matukar taurin rai abin da zai sa zuciyarta ta karaya to kuwa lallai babba ne.
Bai ce komai ya juya ya bar dakin, da alamu ma gidan ya bari gabadaya.
Daga ni har Abida mun koma wasu iri tamkar wadda aka yi mana mutuwar kwatsam. Na kuma gane a yanzu tana tausayina, ta kuma daina jin haushina domin ta daina kyarata kullum a tausashe take yi mini magana. Har muka koma makaranta bamu wani wartsake gabadaya ba.
Sahal da kansa ya gane ina cikin takurarren yanayi. Domin gabadaya bana mararain amsa masa waya kamar yadda nake yi a lokutan baya.
Har zangon karatunmu ya fara nisa, sannan na warware na cigaba da sauraran Sahal cikin dadin rai.
Domin shima na gamsu yana sona gabadaya ya rasa sukuni a dalilin sauyin da yake ga ni a tare da ni, kullum yana zarya tsakanin Zaria da Kano.
Sannu a hankali muka kammala wannan zangon cikin nasara.
Muka koma gida muka tarar an kammala komai na siyayyar aurena wanda Yaya Asad ne ya siya kayan daki tunda ga kan gado da setin kujera na alfarma. Hatta su firij da talabijin. Ya ce lokaci ya yi da su Baba zasu fara hutawa da hidimarmu, su fara shan yayan itace da suka shuka bayan dogon kulawa da suka yi da wannan dashen.
Gidan maza sun kawo lefe da ya amsa sunan lefe domin kuwa ba karamin dukiya aka zuba ba. Ba yadda za'a yi ka ce angon bai fara aiki ko kuma ba sana'a mai k'arfi a hannunsa ba.
A bakin Ansari na ji sati uku masu zuwa ne aure. Na riga kuma na sani Zaria zan zauna domin Baban Zaria ya bashi wani karamin gida a cikin Hanwa ya zauna dan kada karatuna ya samu tasgado.
Duk yadda nake son Sahal amma na kasa jin doki da farincikin auren. Da zarar na ga giftawar Yaya Faruk da yadda ya zama sukuku sai na ji komai ya fita a kaina.
Mahaifiyata kuwa takanas ta samo mini maganin sanyi daga Kano. Itama hanyarsa aka yi mata domin daga Chad ake kawo saiwowin. Kwanaki biyu kacal da fara shan maganin na fara jin marata sakayau. A farko ban mayar da hankalina wajen shan ba, amma jin na samu sauyi a jikina nan da nan ya sanya na mayar da hankali nake sha, mussaman yadda nake jin matsalolin da sanyi ke jefa mace a ciki. Hadakar bandakin makaranta kadai ya isa ya sanya infection yi mana katutu.
Haka wani hakkin daka mai kyau kullum sai ta tsare ni na sha a cikin yogurt ko Madara. Tun a lokacin na gasgata kayan Bojuwa Herbs masu asalin kyau ne ga rahusa.
08032773332 tuntubi wannan layin don samun naki kayan gyaran na mutanen Chad.
Saiwowin dahuwar kaza ta siya ta hada ta dafa mana tare da ita. Na dinga tunanin wai har yanzu mami suna yin harkar nan ne?
Abida da Basma Maska ne kadai suka yi mini kawance, duk da Basma a kano take karatunta na jamia hakan bai sa kawancenmu ya yi rauni ba. Tare da mahaifiyarta da kanwarta suka zo. Da yamma suka koma, suka barta sai washagari zata tafi.
Ranar 15/7 aka daura aurena da Sahal Sulaiman Mashi a babban masallacin juma'a na Funtua.
Yaya Asad da dukkan iyalinsa sun zo daga Enugu.
Anty Rukayya kuwa matarsa Dispenser, oven da microwave ta kawo ban da kayan souvenirs masu uban yawa dan kuwa har da farantan tangaran da kofina mai dauke da sunana da na ango. Courtesy Mr& Mrs Asad Funtua family. Sosai bikinmu ya yi armashi. Matar Yaya Faruk kuwa tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha dan tsananin murnar da take ciki.
Lafiya lau aka yi hidimar bikina cikin walwala da nutsuwa.
Ban sake gane Abida tana sona tamkar yadda nake sonta ba sai ranar da za'a kai ni dakin aurena. Tun safiyar ranar take kuka, sai da tayarwa da dukkan wanda suke gidan hankali domin gaskiyar magana ba wanda ake so a gidanmu irin Abida. Duk yadda take a baude da kuma tsautsaren ra'ayi tana da wani iri jini mai tasiri. Kowa sonta yake yi tare da kaffa kaffa da ita, ba iyayenmu ba, ba kuma a tsakaninmu ba.
Da akace na fito za'a tafi ta rike ni gam nima kuma na riketa na ki tashi. Yaya Faruk da ya ga zamu batawa su baba babba lokaci tunda zuwa zasu yi su juyo sai ya shigo dakin namu. Ya saka hannu ya janye ta ya sakata a jikinsa yana fadin "Ai ba rabuwa kuka yi ba autar momi. Ina ce nan da sati hudu ma hutun zai kare ki koma Zaria ku hadu ku cigaba da rayuwa tare?"
Bata ce masa komai ba. Ta cire zoben hannunta wanda na gold ne ta kamo yatsana na hannun dama ta sanya mini. Ta ce forget me not Bilkina. Sannan duk ranar da na haihu to kawai ki kaddara kin sake haihuwa dan na san kafin nan, kin haifo mini nawa, hakurin da kika yi da ni a tsawon rayuwarmu ba zai tafi a banza ba, zan miki alherin da zaki tabbata kina sona. Fatan alheri mai yawa! Sai kuma kuka ya sake kwace mata.
Ina kuka sosai Yaya Faruk ya fita da ni. Domin bayan ii rabuwata da gida ba karamin raunana zuciyata ta yi da soyayyata da na gani a tare da Abida ba.
A motar baba babba C.R.V. muka tafi. Yaya Faruk ne mai tuki sai Baba babba da baba karami. Duk yadda su baba suka so Yaya Asad ya shigo a tafi da shi tunda ya riga ya dauki girma yana hurar da su dawainiya ya sanya suma suke jagorantar da shi akan sha'aninmu. Kansa a kasa ya ce "Allah ya kaiku lafiya Baba. Ga Faruku nan duk daya ne. Ya leko ya ce "Ki zama mai hakuri, ki sake ninka hakurinki. All the best maigado!
Daga haka ya matsa gefe. Cikin nutsuwa Yaya Faruk ya ja motar muka tafi.
Gidan Baba. Zaria aka kai ni. Baba babba ya rike hannuna ya damkawa wan mahaifin Sahal kuma waliyinsa amanata. Shi kuwa ya saka hannu ya rike hannuna gamgam.
Yana fadin "na karbi amaana in sha Allah y'arku tana amintaccen hannu."
Tarba ta karrmawa ya yi mana, iyalinsa kuma suka baibauemu da abinci da na sha, duk ni kaina kasa yake kuma a kunshe cikin mayafi . Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a gidan Baban Zaria. Zuciyata sai tsallen bad'ake take yi, yanzu shike nan na bar gidanmu gabadaya sai dai na je da bakunta? Iyayena da kansu suka dauko ni suka kawo ni wani gidan da nufin na zama cikin ahalinsu muddin rai. A raina na dinga jin lallai al'amarin aure ba karami bane a addini da rayuwa ba.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
*Lafazi writer's*
13
Message Amreesh spices & more on WhatsApp. https://wa.me/message/Y7KSRJ7PDQSCC1
*Fatan alheri ga*
*Haj Dr Safiya Saulawa*
*Haj Zahra Shehu*.
Sai da aka yi sallar isha sannan Baban zaria da matarsa da ake kira da Mama suka kai ni gidana da babu nisa tsakaninmu da su. Unguwar kusa ne kwarai da jamiaar.
A gidan muka tarar da shi tare da amininsa Lawal.
Addua sosai Baba ya yi mana tare da jaddawa Sahal girman hakkina da yake kansa.
Haka nima ya ta nanata mini na kulla abota da hakuri da kuma juriya, sanna na gane biyayyar da aka kallafa mini na yi masa umarnine daga Ubangiji. Dan haka duk abin da zan yi masa na hidima na yi min Allah dan kuwa shi ya shirya tsarin aure da kansa. Mama ta shigar da ni cikin dakina ta zaunar da ni akan gadona tana ta yi mini fatan Ubangiji yasa na zama tsohuwar gidan.
Basu wani jima ba suka tafi suka bar ni a sabon gidana da zan fara sabuwar rayuwa a cikinsa.
Jin ana kiran sallar magahariba ya sanya suka tafi, su Sahal suka rakasu wajen mota suna ta godiya da ban gajiya gasu Baba, sai da motarsu ta bace musu. Basu shigo ciki ba suka wuce masallaci dan sauke farali.
Bayan an idar suka shigo da ledoji da alamu sun siya tun dazu a mota suka barsu.
A guggurje ya yi barkwancinsa tare da ajiye mini bandir din yan 200 wai kudin siyen baki.
Ya yi mini sallama ya wuce, dan hanyar Katsina zai kama a daren nan.
Da kazangi ya dawo ya zauna daf da ni ya rungume ni yana shakar kamshina. Gabadaya na takura, bansan meyasa ban ji tsumin da na ji a lokacin da Yaya Faruk ya rungume ni ba a yanzu.
Tabbas jikina ya shiga bakon yanayi da bai saba ba, ban sani ba ko tsananin alhinin rabuwa da ahalina tare da fargabar yadda zan shiga cikin sabon ahali ne oho.
Cikin nutsuwa ya ware mayafin da na lulluba da shi. Ya mikar da ni ya ce "Zo mu je falo mu ci abinci. "
Tsire ne mai kyau sai yogurt da kuma ruwan roba masu sanyi.
Duk yadda nake jin yunwa ban iya cin naman ba, sai yogurt din na sha, shima ba wani mai yawa ba.
Bai wani sake ba, sai da ya dawo daga sallar isha.
Ya sake janmu sallar nafila ya yi mana adduar zaman lafiya da albarkar rayuwaa.
Da rawar Jiki ya mannu da ni ya ce "Yau ranace ta mussaman a tarihin rayuwarmu gabadaya. Ina fatan Ubangiji ya sanya albarka a dukkan zaman da zamu yi."
Murya babu amo na ce ",ameen".
Duk yadda nake jin bakunta ta kewaye ni sai da ya hilace ni ya dangana ni da lafiyayyen gadonmu da ya sha shimfida ta alfarma.
Cikin gaggawa yake yin komai, gabadaya ya dinga sarrafa ni, ya jima yana shafata tare da kissing dina. Bai samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar ya isa inda ya dade yana fatan ya isa. Bai wani jima ainun ba. Yayin da ni ban wani gane komai ba sai radadi.
Na kalle shi yana ta numfarfashi, daga haka barci ya yi awon gaba da shi. Na jima ina ta sake saken zuci ban kuma isa na hakaito mai nake sake sake a akansa ba.
Na duba wayata na ga shadayan dare. Na mike na shiga bayi dan yin wanka. Domin Mami ta ce mini kada na bari na dinga barci da janaba in ba dole ko lalura ba.
Na gasa kaina sannan na yi wanka. Har na kammala na shirya bai motsa ba. Na lallaba na kwanta a gefensa.
A haka nima barci ya yi awon gaba da ni.
Bamu makara sallar asuba ba, sai dai da muka koma din sai wajen goma muka farka a dalilin dukkanmu mun tara gajiya, na fito daga wanka ina shiryawa cikin nutsuwa, shi kuma yana daga kwance yana kallona cikin murmushi.
Daidai lokacin kuma ya fita ya karbo abin karin kumallo da aka aiko mana daga gidansu.
Funkaso ne da kunun gyada. An zuba cikin kyawawan kwanuka.
Kaitsaye dakin ya shigo da kwandon. Ya zuba mini ido ina sanye