Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
koma gidanmu da zumar zama mai tsayi. Don kuwa ina cikin jerin mutanan da aka jarraba da rashin dacen uwa. Mahaifiyata wata irin uwace mai wuyar sha'ani. Mai yada bacin rai a tsakaninmu, mai yayata kuskuren da jama'a suka yi mata. Shiyasa gabad'aya mu y'aya'nta bamu da kwarjini ko farinjini a cikin dangi. Munanan dab'iun da ta cusawa mana ya sanya ake yawan rikici da mu. Domin duk wadda ta fad'a mana ya mata kaza zamu kullece shi tare da k'ulla adawa da shi, ba tare da tunani ko shakkar komai ba. Hawaye ya silalo mini, domin ni da kaina na tabbatar muna shan zagi a idon duniya. Duk da ni kad'aice ban bi ra'ayin mahaifiyata da yan'uwana ba, amma hakan ba zai hana na shiga sahun y'aya'nta ba. Na muskuta ina jin makakin bacin rai har cikin zuciyata don kuwa ina cikin matan da basa son tuna da d'insu. Domin ni gabadaya bacin rai da kuttu yafi yawa a kafatalin rayuwata. Tun daga rayuwar gidanmu har zuwa rayuwar aurena. Amma dalilai masu yawa suka sanya na yi nufin yin bitarsu tiryan tiryan dan na lura bayar da labarin nawa na iya zama izna hadi da hannunka mai sanda ga mutanen yau, mussaman mata da sune iyayen al'umma. Ina kuma fatan duk wacce ta ji labarina zata yi duba na tsanaki ta laluba wacce irin dabia take aikatawa, shin kina cikin mutane masu manta tarin alkairai, akan kuskure guda daya tak? Ku biyo ni sannu a hankali, ta yadda zaku fahimci inda na dosa domin kuwa mai tsananin aiki da lura ne zai fahimci Dingishin K'WADO. Sunana Bilkisu Isa Funtua. Ni y'ar asalin k'aramar hukumar Funtua ce ta jihar Katsina. Ina matukar son garina, ina alfahari da kasancewata y'ar asalin Funtua. Shiyasa a duk sadda na samu sukuni na kan yi bita tare da nazarin garin namu. Dan haka kafin na kutsa cikin labarin nawa sai na fara fayyace yadda garin namu yake. K'aramar hukumar Funtua Tana daya daga cikin manyan Kananan Hukumomin Najeriya da aka samar tun bayan gyaran tsarin kananan hukumomi da akayi a shekarar 1976. Ita ce kuma hedikwatar mazabar Katsina ta Kudu, wadda ta kunshi kananan hukumomi har guda goma sha daya (11) wadanda suka hada da: Bakori, Danja, Dandume, Faskari, Sabuwa, Kankara, Malumfashi, Kafur, Musawa, Matazu da kuma ita kanta Funtua. Tana da girman murabba'i 448 km² da yawan jama'a (225,571 a bisa ƙidayar 2006) sannan kuma mutum 570,110 bisa ga ƙiyasin 2016. Shugaban shine shugaban karamar hukuma a hukumance. Mazauna karamar hukumar hausa Fulani ne akasarinsu, sana’o’insu kasuwanci, noma da kiwon dabbobi ne. Funtua tana da yanayi mai kyau yayin da take kan latitude da longitude 11°32′N da 7°19′E bi da bi. Garin yana da matsakaicin zafin jiki na 320C da zafi na 44% Funtua tana cikin iyakar kudancin jihar Katsina. Shi ne birni na biyu mafi girma a jihar bayan Katsina. Tana iyaka da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a kudu, Bakori daga gabas, Danja a kudu maso gabas, Faskari a arewa maso yamma da Dandume a yamma. Har ila yau garin namu bashi da matsalar ababen more rayuwa irinsu ruwa da wutar lantarki. Funtua tana da tashar watsa lantarki ta kasa mai karfin 132KV na National Grid da ke zuwa daga Mando tasha ta Zariya daga nan ta wuce Gusau ta tsaya a Talata Mafara. Yana da kyau a lura cewa tashar watsa wutar lantarki mai karfin 132kv/33kv da ke Funtua tana gudanar da ayyukan kananan hukumomi 9 daga cikin kananan hukumomi 11 da suka kunshi Gundumar Sanata Funtua. Yayin da rashin wutar lantarki ya zama ruwan dare gama gari a fadin kasar. Funtua ba ta da irin wannan matsalar saboda garin na samun wutar lantarki na tsawon sa'o'i 12-20 a kullum. Don haka duk mai sha'awar zuba jari zai iya zuwa ya saka hannun jari. Dangane da Samar da Ruwa; An albarkaci Funtua da madatsun ruwa guda 2, wato; Mairuwa da Gwagwaye da suke hidima da birnin da wasu sassa na majalisar Faskari da yankin Bakori. Har ila yau, akwai gonar Songhai da ake amfani da ita don horarwa da noman wasu kayayyakin gona. Haka nan Funtua ta haifi manyan mutane da suka yi shura a fannoni daban daban a jihar Katsina da k'asa gabad'aya. Bayan haka garina ne ya samar da tsohuwar marubuciya *Haj Bilkisu S Funtua.* Allah ya kara lafiya uwar marubuta da makaranta. Wannan kenan. Gidanmu na cikin unguwar low-cost wacce shiya ce ta tsofaffin y'an boko, kuma masu kumbar susa.. Katafaren gida ne da ya amsa sunan mahdi ka ture sabida k'arfin ginin. Hakanan gida ne iya ganinka domin kafin ka kai k'arshen katangar da ta kewaye gidan ma aiki ne babba. Gidan na dauke da sassa daban daban har guda biyar. Sai dai tsakanin ko wanne sashe tafiya ce mikakkiya. Ma'ana akwai tazara mai yawa ta yadda ba za'a iya yin komai tare ba. Shashen farko na Alhaji Musa ne wanda kowa a zuriarmu ke kiransa da Baba babba. Sai shashen tsakiya na mahaifiyarsu ne kafin ta rasu. Daga baya sai ya koma wajen ajiye amfanin gona domin iyayenmu manoma ne na fad'a a jarida. Sai sashen Alha Isa wanda muke kiransa da Baba k'arami. Shine kuma mahaifina. Akwai sashin ma'aikatan gidan da kuma sashe guda na baki da samarin gidan. Su biyu kacal iyayensu suka haifa sai dai mahaifinsu Malam Muhammadu d'an babban gida ne a Funtua asali yana da alak'a da gidan sarautar garin, suna da zuria mai yawa, domin y'aya'n babansu sun kai talatin, sai dai shi ya rasu tun suna k'ananu ainun. Don haka ba wani zumunci suke yi sosai ba a dalilin kishi ya rufe idonsu, sannan mijin ya rasu kowa saita ja gefe da ya'yanta. Mahaifiyarsu kakarmu kenan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu. Mahaifiyarsu kakarmu ke nan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu. Dan haka bata yi aure ba sai da suka girma suka zama samari duk da akwai tazarar shekaru biyar tsakanin Baba babba da Baba k'arami. A lokacin da suka girma kuma ta yi aure ta wuce shekarun haihuwa. Sun taso cikin wata irin soyayya da ririta junanmu don kuwa mahaifiyarsu ta yi matukar cusa soyayya da tausayi a tsakaninsu. Bayan haka kuma sun samu Ilimin addini da na boko. Baba Babba tsohon ma'aikacin gwamnati ne, haka tsohon d'an majalisar dokokin jihar katsina ne tun a jamhuriya ta biyu. Sannan mashahurin manomi ne dan kuwa sai an sako shi a cikin sahun manoma a k'asa gabad'aya ba wai jihar Katsina kawai ba. Baba Babba gabjejen attajiri ne da Ubangiji kad'ai yasan yawan arzikin da ya bashi. Dan na yi imani shi da kansa bai san adadin dukiyarsa ba. Ni bansan hekta nawa yake nomawa a shekara ba balle na hakaito. Idan na ce manomi ina nufin kololuwar manomi ne da yake noman da gaske. Dan kuwa makudan milyoyin kudi yake narkawa a gonaki. Idan kaka'a ta yi kuwa shima ba k'aramin dukiya yake cika dakuna da manyan shaguna ba. Baba k'arami kuwa likitan dabbobi ne. Shima da nasa arzikin tunda yana kasuwancin siyar da lafiyayyun dabbobi, tunda ga kan awakai, tumakai, dokuna, shanaye da rakuma. Shiyasa gidan gonar Baba Babba cike take da lafiyayyun dokuna, rakuma da kuma raguna harma da shanaye da tsuntsaye daban daban. Danginsu dawisu da tatalo, jimina, geese, agwagi, da sauransu. Gidan gonar duk fad'in Funtua da kewaye babu ta biyunta. Domin cike take ainun da dukiyar dabbobi, hatta kaji ana zuba sama da dubu ashirin na k'wai da na ci, kajin Hausa ma birjik ne iya ganinka. Tattabarun da suke ciki kuwa baza su kayyadu ba. Gidan gonar Ladi farms ta yi bunkasar da har Madara ake sarrafawa a cikinta domin shanayen waje masu bada Madara zallah ma yawansu ya kai kurewa. Kifaye kuwa ba'a magana. Baba k'arami ke kula da ita a dalilin shi din kwararren likitan dabbobi ne. Samun kulawa da kiwo na mussaman da suke samu ya sanya dabbobin suke ta bunkasa suna haihuwa akai akai. Idan ana lissafin manyan gidajen gona a Nigeria ba wai a Funtua ko arewacin Nigeria ba sai an sako gonar Ladi farms ta Baba babba. Gidanmu da muke ciki na Funtua tare suka yi ta siyan filayen suka kuma gina abunsu. Kowa zuba kudi yake yi, dan haka mallakinsu ne su biyu. Bayan haka suna da kadarori daban daban da suka yi tarayya a kai. Misali gadonsu basu raba ba. Sannan akwai wasu kadarori da suke siya tare. Amma a zahirin gaskiya Baba babba ya fi mahaifinmu dukiya nesa ba kusa ba. Duk da namu mahaifin ma attajiri ne na gaske. Ina wannan bayanin ne dan ku fahimci labarin da kyau. Iyayenmu biyu hamshakan alhazai ne, sai dai dole wani ya fi wani. Dukkan iyayenmu maza matayensu guda daya ne. Haka kuma Ubangiji ya azurtasu da haihuwa sosai. Ya'yan Baba babba guda shida ne. Wacce matarsa Hajiya Saratu ta haifa masa, muna kiranta da Momi. Ukun farko maza ne Yaya Abubakar, amma Asad ake kiransa, Yaya Umar Faruku, Yaya Usman. Sai Yaya Salaha. Daga kanta an jima sosia kafin a haifi Yaya Munira. Sai Abida da take auta, kuma ita kad'ai na girma duk da dai ba wani fiko ne mai yawa ba, tare aka yi goyonmu. Sunan mahaifiyata Haj Habiba, muna kiranta da Mami. Mu bakwai ta haifemu. Yaya Sulaiman, Yaya Hamida, sai ni Bilkisu, Ansar, Anisa sai autarmu Saddiqa. Idan aka had'amu da y'aya'n Baba babba mun zama sha biyar ke nan. Kusan kowa na da abokin haihuwarsa. Yaya Sulaiman da Yaya Usman. Yaya Hamida da Yaya Salaha. Daga nan sai abin ya juya. Gabad'aya mun taso ne bisa jagorancin Baba babba. Domin baba k'arami idan ya tafi Katsina ranar litinin sai alhamis da yamma yake dawowa. Idan ya dawo din ma mafi yawa yafi zama a Ladi farms sai dare ake samunsa. Gabad'aya mun fi shakuwa da Baba babba, akan mahaifinmu tunda yafi shi haba haba da yara, sannan shi muke ga ni kullum yaumin. Amma kuma Ya Munira tafi shakuwa da baba k'arami, matuk'ar yana gari to duk inda zaka gan shi tare da Munira a gaban motarsa ta shiga ransa ainun fiye da mu ya'yan cikinsa. Iyayenmu mata suna zaune lafiya duk da babu abin da suka had'a. Misali ko wacce bangarenta daban sannan akwai tazara mai yawa. Sai dai dukkan ahalin gidan k'wai da kwarkwata da hadiman gidan ana cin abinci ne daga tukunya guda. Domin akwia sashe guda da na y'an aiki maza masu kula da gyara harabr gidan da shuke shuken gidan, da mata masu girki da gyara cikin gidajen. Kawai umarni ake basu. Mu kuwa yaran gidan kowa na da yancin ya zauna a sashin da yake so ko dai na Baba babba ko sashen Baba k'arami. Idan an fahimce ni bamu taso mun ga banbanci ko wani rikici a tsakanin iyayenmu maza ko mata ba. Shiyasa soyayya ce mai yawa a tsakaninmu gabadaya. Bamu zama yan mata ba aka yi auren Yaya Salaha da Yaya Zainab da Kuma Yaya Hamida fiko mai yawa suka yi mana, amma da yake sai da suka yi digiri a fannoni daban daban mun data kafin a aurar da su. Amma dai ko sakandire bamu shiga ba, kawai muna ita tuna sadda aka yi auren ne. Mun taso mu uku Yaya munira da ni da kuma Abida. *Assalamualaikum barkanmu da lokaci ya hak'uri da ni?* *Ina gabatar muku da wannan labarin nawa, tare da fatan zaku karbe shi da kyau, zan yi matukar farinciki idan har kun bibiye shi cikin nutsuwa*. *Ina kuma bada hak'uri ta yadda bana iya tsallake rubuta labarin da yake d'amfare da zumunci wala na jini ko na abota ko kuma na surukunta.* *Wannan karon labarin harshe biyu gare shi don haka zaku ga ya kasu biyu* *Haka nan labaran Surayya basa nufin habaici ko shagube ga wani ko wata. Dan haka idan an ci karo da abin da ya yi dai dai da rayuwarki, ko ta waninki ba da niyya bane. Akasi ne kawai*. *Fatana dai a yi karatun cikin nutsuwa har a fahimci darasin cikin labarin.* *Surayya Dee* ✍️ [8/24, 12:52 PM] Surayya Dee: Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2347020695644 4 *Contact me 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. Ni da Yaya Munira mun taso cikin wata irin soyayya da shakuwa. Da wahalar gaske mu yi fad'a sabanin da babu jituwa ko kad'an tsakanin ta da Abida. Koda yake ita Abida da ta kasance k'aramarmu tana da wani irin hali murdadde, bata kaunar ka tab'a mata abinta ko kad'an, hakanan ta yi matukar kyamar ka kwanta mata a gadonta. Duk da dama gado uku ne a cikin dakunanmu na kowanne sashe. Bayan haka kuma tana cikin mata masu high taste bata amfani da kowanne irin garabitin abu, sai zababbe. Y'ar kwalliya ce ta sosai tun tana k'arama. A zahiri mun fita kyau, amma da yake tafi mu gayu sai ta fimu daukar ido. Kusan kullum sai ta sani kuka domin ni tun tasowa ta haka nake sanyi kalau mai matukar raunin zuciya. Yaya Munira ke k'watata a hannunta sanadin da ya ta'azzara rashin shirinsu ke nan. Amma kuma bata yarda a ci zalina a makaranta. Nan da nan Abida zata yi makarbiya ta mayar da fad'an kanta ko da kuwa bata yi mini magana. Kazalika basa shiri da Yaya Sulaiman kwata kwata basa jituwa, a cewarta shi din mai nuna son kai ne da tak'ama, a gabanta yake nunawa nice k'anwarsa alhalin yana ganin yadda Yaya Farouk yake mini alkunya fiye da ita. Shi kuma ya ce ra'ayinta da iyayyinta ne basu yi masa ba, yarinya ta yi ta juya mutane, matuk'ar yana gidan to kuwa sai an musu shari'a don sai ya yi mata abin da zata harzuk'a sai da Baba k'arami karami ya yi masa wuta wuta sannan ya daina fitinarta, don kuwa gaban Baba karami ta kai maganar tana rusa ihun ya mata iyaka da shi ko ta kira masa yan civil defence. Ba k'aramin dariya Baban ya yi ba, karshe ya wanke Sulaiman ya ce "ka fitinar mini Abida fa Sulaiman. Maimakon ka jata jikin ka, har ku k'ulla alheri sai ka dinga yi mata sheganta to ina ruwanka da bak'inta? Ina ce dakin Allah ma bak'ine ashe kuwa bak'i ba muni ba ne ba kuma tawaya ba ce! Ya ce "Na daina Baba amma lallai ka ja kunne ta akan gatsinen da take mini tare da harara ko da ban mata magana ba, sannan duk ranar da ta sake kwashe mini takalma idan na ajiye a bakin k'ofa, komai na yi mata ita ta ja". Baba ya gintse dariyarsa ya ce "Kin ji ko Abida ki daina, shima ba zai kara bata miki ba". Ta ce "Shike nan yanzu dai ka sake jaddada masa ka yi mana iyaka babu ni, babu shi har gaban abada". Baba ya kwashe da dariya ya ce "A a ba haka za'a yi ba, ba dhi ba tsokanar ki bare ya saka ki kuka, kema ba ke ba masa rashin kunya, wannan kam na shata muku layi. Duk wanda ya tsokani wani kuwa to la shakka da ni yake fad'an! Daga haka ya sallame su. Shike nan aka samu saukin rikicinsu. Ni mamakin Yaya Sulaiman nake yi idan ya sako Abida a gaba da wulak'anci don magana ma da kyar yake yin ta baya son hayaniya ko kad'an, yayin da Abida take y'ar kwarfniya ta gaske watakila wannan banbancin ya sake hab'aka yar tsamarsu. Muna kammala firamare aka kaimu Makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori(F G.C Bakori). A lokacin Yaya Munira na aji uku(J.S.3) na k'aramar sakandire a Makarantar. Tare ake yi mana komai. Kayanmu a hade suke, amma Abida bata yarda muci abinci tare. Sai dai kwanonta daban. A shekarar kuma babban wanmu Yaya Asad ya yi aure, ya wuce da amaryarsa Asaba da yake d'an sanda ne mai mukamin ASP a lokacin. Sannu a hankali rayuwa take shudewar har muka sami shiga aji uku. Yaya Munira tana aji biyar. Ta fara zama budurwa sosai. Tsayinmu d'aya da ita saboda ni din doguwa ce sosai. Amma siririya sai da ina da kugu sosai. Haka nan farare ne mu tamkar tsada sabanin Abida da take bak'a. Duk gayunta da farar fatarmu basu rudeta ta yi sha'awar sauya launin fatarta ba. Ko mai zata siya sai ta duba ingredient matukar ta ga sinadarin hydroquinone to kuwa zata ajiye shi. Tsayina da sanyin halina ya sanya dalibai suka lankaya mini Bilki sola. Matukar ka ce Bilki sola a lokacin da muke FGC Bakori kowa ya san ni. Ba ni da k'awaye, daga ta botsara Abida sai kuwa Basma Bello Maska. Kawai Ubangiji ne ya k'ulla abotarmu, don tafi dacewa da Abida, masifaffiya ce ta gaske itama. Kawarmu ce gabad'aya tunda ajinmu d'aya haka dakin kwananmu guda. Amma kawancen yafi k'arfi da ni. Da wahala mu yi fad'a sabanin ita da Abida kullum sai sun yi, wani zubin sai su yi sati basu yi magana ba domin dukkansu masu ra'ayin rukau ne, masu ji da kansu ne. Sannu a hankali Yaya Munira ta kammala ta barmu, ta yi sa'a a shekarar ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahamadu Bello ta Zaria. Kafin mu gama FGC mun zama cikakkun yan mata. Da Basma da Abida matsakaicin tsayi ne da su. Sabanin ni da nake doguwa sosai. Na keresu, a wanccan lokacin har kunyar tsayina nake ji, domin bana jin za'a samu wacce ta fini tsayi a makarantar sai dai mu yi taya. Daga sama ba ni da kiba ko kad'an, amma ina da fad'i ta kasana. Gabad'aya kirar jikina ya fi dacewa da kwalbar coca cola. Doguwar fuska gareni mai dauke da siririn dogon hanci tamkar biro. Hakanan bakina d'an tsut mai dauke da jajayen lebuna, da k'ananun hak'ora jerarru farare kal tamkar kankara. Gashin kaina baki mai sulbi har gaban goshina. Sannan a cike take ga kuma tsayi. Kallo d'aya tak zaka fahimci ni din kyakkwar mace ce lamba d'aya sabanin Basma da Abida da suke da boyayyen kyau, irin sai an kallesu da kyau kafin a fahimci kyaunsu. Mun dawo hutun zango na biyu muka yi sa'a Baba babba ya sahale mana muka tafi katsina hutu gidan Yaya Salaha wacce ma'aikaciya ce a ma'aikatar ruwa ta jihar Katsina. Bana manta ranar da muka fara haduwa. Yammacin wata juma'a bayan Yaya Salaha ta dawo daga aiki, ta aike mu, mu karbo mata sak'o a gidan iyayen mijinta a k'ofar bai. Direban mijinta ya kaimu. A k'ofar muka tarar da samari guda biyu. Tun daga nesa muke hangensu da yake fuskar gidan muke nufa. Su kuma a zaune suke kan tebirin da yake girke a k'ofar gidan. Mun fito zamu shiga gidan, idona ya fad'a cikin na dogon saurayi fari tas. Sumarsa ta tabbatar mini yana da alak'a da mutanan Habasha ko Bafulatanin usul. Faduwar da gabana ya yi, a kallon farko ya sanya ni cikin rud'u. K'afafuwana suka hau sark'ewa, da k'yar na daure na bi Abida a baya muka wuce. Zuciyata na cigaba da dokawa da tsananin gaske. Bamu wani jima ba muka fito. Muka sake tarar da su , mun gota su kad'an, kafin mu shiga mota, suka taso da azama. Wanda yafi tsayin ne ma'ana wanda na kadu da kallonsa ya yi jarumtar ce wa "Sannunku y'an mata". Zuciyata ta sake tsinkewa domin sai na ji tamkar wanda hausar tasa ma ta dabance. Ya zuba mini ido, yana son mini kallon tsanaki, gangar jikina ta taya zuciyata rawa. Na kasa amsa masa sannun da ya yi mana. Abida cikin ko d'ar ta ce "Sannunku dai Rijalu! Dariya ta k'wacewa d'ayan mai duhun fata da kuma matsakaicin tsayi. Cikin dariya ya ce "Bari na matso kusa da ke da alamu ke na dad'e ina jira". Ta rausayar da kai ta ce "A a kada ka matso, domin kuwa shekaruna sha shida, karatu zan yi, kuma na likitanci ka ga ina buk'atar nutsuwa mai yawa akan karatuna". Ya sake fadada murmushi ya ce "Nima dalibin ilimi ne, hutu na zo, ina karatun Islamic law a k'asar Sudan. Sunana Lawal ". Ta ya mutsa fuska ta ce "Idan daga Allah ne zai sake had'amu kamar yadda muka had'u yanzu babu tsammani." Ta shige mota. Yayin da na bi bayanta tamkar kazar da k'wai ya fashewa a ciki. Domin gabadaya saurayin nan ya yi matukar tafiya da zuciyata a kallon farko. Ya biyo ni yana ce wa "Saka mini lambar wayarki, mu dinga gaisawa". Murya babu amo na ce "Bama rik'e waya sai mun kammala makaranta." Ya ce "Sunana Sahal Sulaiman Mashi. Ya ciro takarda a aljihunsa ya rubuta S.S.Mashi tare da lambar wayarsa ya jefo akan cinyata tunda nice a setin da yake. Ya sanyaya murya ya ce ga lambata nan ki k'ira dan Allah da manzonsa." Kafin na ce komai direban ya ja motar mun tafi. Muna nisa da unguwar ina sake jin zakuwa da son cigaba da tattaunawa da shi. Shine saurayin da ya tab'a tunkarata kai tsaye, ba wanda zasu rubuto wasika ba. Shine kuma namijin da zuciyata ta fara bugawa a dalilin sonsa. Domin kallo d'aya na gane shi din matukar kyakkwa ne, sannan dogo ne na gaske. Bayan haka na gan shi cikin kwalliya ta burgewa. Na dauki takardar ina kallon lambobin da ya rubuta su a jere cikin wani irin salo. Ga mamakina sai na ji hatta rubutunsa ya shiga raina ko tantama bana yi yana cikin dalibai masu baiwar sarrafa rubutu babu shakka. Na shagala k'warai da gaske da kallon lambobin. Ba zato kawai Abida ta fizge, bata tsaya wata wata ba ta cukuikuiye ta yaga ta wullar ta window. Na zuba mata ido zuciyata na sake tsananta bugawa. Idona ya ciko da k'walla. Na kasa bude baki na ce mata uffan. Maimakon itama ta kama bakinta sai kawai ta ja tsaki mai tsayi tare da ce wa "Nasan kina iya buga masa waya domin na k'are miki nazari na ga ya shiga ranki. Ni kuwa ban miki sha'awarsa ba, domin idan namiji ya cika kyau had'ari ne babba a wajen mace bare ke solobiyo". Har muka isa gida bakina a dinke ruf, na shige daki na kwanta sai kawai na fashe da kuka ina yinsa k'asa kasa amma na bacin rai ainun. A haka Yaya Salaha da Abida suka tarar da ni, duk k'ok'arina na hadiyen kukan sai da Yaya ta fahimci kuka nake yi sosai. Ta rikice ta dinga tambayar ba'asun kukan, na kasa cewa komai. Abida ta ja tsaki ta ce "Wani tsalelen saurayine ya bata lambarsa akan ta nemi shi, shine ni kuma na yaga takardar kin ji sanadin kukan da take yi. Yaya Salaha ta yi jim domin bata tab'a zaton yadda nake very silent har zan fad'a tarkon soyayya tashi guda haka ba. Mussaman da ni ko karance karance bana yi. Abida ce kullum cikin fakar idonta take tana debo littafan Hausa a dakinta tana raba dare wajen karatun. Ta numfasa ta ce "Share hawayenki, Bilkisu, rabu da Abida.". Abida ta yi maza ta ce "Idan an k'addara mijinki ne zaku sake haduwa, amma ni ban miki sha'awarsa ba zubin majununai ne da shi". Yaya Salaha ta d'auki salati tana ce wa "Oh ni y'asu ke Abida wacce irin yarinya ce tun baki tafasa ba zaki kone? Har kinsan kalolin mazaje? Har kina iya banbance na gari da kuma majununi?" Ta yi dariya ta ce "Allah kuwa Yaya ina ganinsa na ji bai mini ba, da ace d'ayan da ya nuna yana sona ne yake sonta da ba zan yaga takardar ba, domin ya yi, kyaunsa kad'an ne, sannan mai wararren kai ne, haka nan bak'i ne. Amma Sallau yake ko wa? Fari ne tamkar tsada, ga kuma alamun izza tare da shi. Sam sam zuciyar Bilki bata dace da wannan ba, domin artabun da zata yi da y'an mata ba kad'an ba ne". Mamakin Abida ya sake daskarar da Yaya a tsaye. Ta ce "Ke mai ya hana ki so wanda ya nuna yana son na ki tunda kin tabbatar shi ba munafiki ne ba?" Ta yi dariya ta ce "Ban shirya aure kusa ba, dan haka bazan bada k'ofar da za'a zo gidanmu da sunan ana sona ba, hakanan ba zan yi gangancin fara soyayya a yanzu ba.". Yaya Salaha ta gwale ta da fad'in " To uwar iya. Idan ke baki shirya aure yanzu ba, kada ki sake toshewa Bilki hanyar samun samari. Ina ce bana zaku kammala sakandire, idan ta samu tsayyaye wanda ya shirya ita aurenta zata yi ba zata zauna ta tsufa

Chapter 3 of 11