Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
momi na gefensa. Amma Baba k'arami kuwa shine asalin d'an gargajiya gabadaya irin wannan rayuwar bata dame shi ba. Ga shi har digirin digir gir ya yi. ** A wannan shekarar muka samu gurbin karatu. Dukkanmu a A.B.U Zaria. Abida ta samu nasarar samun MBBS din ma'ana burinta na zama likata zai tabbata. Yayin da ni na samu Nutrition and dietetics. A wanccan lokacin ban so kwas din ba, domin ba shine zabina ba, amma na hak'ura tare da fatan ya zame mini alheri, tunda ba zai yiwu na ce zan sake neman wani kwas ba. Basma ma ta samu nasarar shiga jami'ar sai dai ita jami'ar Bayero ta samu, inda zata karanci lab science. Baba k'arami tare da Baba Babba suka kaimu har cikin makaranta, bayan nasiha da jan kunne iri iri. Ba abin da ya tsaya mini irin yadda Baba k'arami ya fito da al'amarin da yake ciwa iyayen yau tuwo a kwarya. Da kakkauran murya ya ce "Tunda kuka iso duniya bamu huta da hidimarku ta kowanne bigire ba, har zuwa yau dinnan bamu huta da dawainiyarku ba, ba kuma mu tab'a gazawa ba. Bayan hidimar da muke yi muku da aljihunmu da k'arfinmu haka nan bamu tab'a gajiyawa wajen yi muku addu'ar shirya da samun nasarar rayuwa ba. A yau da zamu kai ku jami'a wajen ka zo na zo, wajen da babu kwaba. Abun da zamu fad'a muku d'aya ne tal. Ubangiji ne wakilinmu akan tarbiyar da muka wanzu muna yi muku, idan kun taimaki kanku kun k'are mana mutunci kun kare naku, to kun tsallake kalubalen rayuwa mai yawa, idan kuwa kun ha'incemu kun watsar da tarbiyar da muka d'oraku a kai, kun jefa rayuwarku cikin garari da tashin hankali hadi da bak'in ciki marar yankewa. Ubangiji kuma zai mana sakayya. Ku kiyaye, ku kiyaye, kada ku kusancin zina bare ta baku sha'awa ku afka mata, masifarta yawa ne da ita, naso take yi. Kun isa aure duk wacce ta had'u da namijin da ya yi mata, ya nuna zai aure ta ta turo mana shi, zamu aurar da ita babu jinkiri." Gabaɗaya mun yi laƙwas kunya ta dabaibaye mu domin Baba ƙarami cire kunya ya yi sosai ya ding faɗin "Mun san sha'awa halitta ce, kuma kun kai shekarun da zaku buƙaci namiji amma kuma bata gurbatacciyar hanya ba, kada ku yi sanadin da zamu kunyata mu mutu da baƙin ciki dan Allah." Nasihar ta yi matukar ratsamu, gabaɗaya kuka muke yi, har Abida da ta fini taurin zuciya. Sun jima tare da mu a makarantar tare da Yaya Munira da a lokacin ta shiga ajin ƙarshe inda take karantar (Law) shari'a kevnan. Haka suka barmu cikin jan kunne da nasiha iri iri. Ba bangarenmu ɗakunan kwananmu ɗaya da yaya Munira ba. Amma muna haduwa akai akai, yayin da muke ɗaki ɗaya da Abida haka abincinmu a haɗe tamkar muna F.G.C Bakori. Sannu a hankali muke karatun har muka cinye shekarar farko. Yaya Munira ta kammala cikin nasara. Mun yi kewar rashinta a kusa da mu, domin sosai take yi mana alheri da saka ido a kanmu. Cikin sa'a a wannan shekarar jamiar zata yi bikin yaye dubban ɗalibai(convacation). Sosai muke ɗoki da murnar yaya Munira na cikin waɗanɗa suka yi sa'a baza su yi dogon zama kafin a yi bikin ba. Kusan kowa ahalin gidanmu ya halarci bikin inka dauke Yaya Asad da bai samu sukunin zuwa ba. Domin bai ɗaɗe da komawa jihar Anambara ba, tare da ƙarin girma. Amma hatta dukkan yayunmu mata da suke da aure sun zo. Kwalliya muka yi ni da Abida sosai tamkar mune graduate ɗin. Hakanan mune mu ke kai komon hidima da ahalinmu a wajen. Su Baba sai farinciki suke yi, suna mana addu'a muma Allah yasa su ga namu bikin gamawar. Gabaɗaya aka amsa da "Ameen". Ɗiyar Yaya Zainab Anisa ta ce zata yi fitsari. Sanin da na yi Abida bata yarda ta yiwa yara tsarki ya sanya na ruƙo hannunta na yi can gefe inda babu jama'a da ita, bayan na dauki ledar pure watee guda ɗaya. Na ɗago daga sunkuyen mayar mata da pant idanuwana suka sarƙe a cikin na tsalelen saurayin da nake kwana nake tashi da tunaninsa. Sanye yake cikin graduation gown wanda hakan ya tabbatar mini shima ɗalibi ne a makarantar. Da murmushi ya ce "Duk yadda aka yi ke ce alherin da nake ta roƙa babu gajiyawa." Bugun zuciyata ya tsananta domin ban taɓa zaton zamu sake haɗuwa ba. Ya tausasa harshe ya ce "Fara faɗa mini sunanki dana garinki. Dan kada ki sake ɓace mini". Na yi ƙasa da kaina harshena ya yi mini nauyin da ban yi zaton zai yi a wannan saɗarar ba. Ya kalli Anisa ya ce "ya sunan antinki?" Ta ce "Anti Bilkisu." Ya murmusa ya kalle ni ya ce "sunan ya dace da zubin hallitar da ubangiji ya yi miki, tabbas ke ɗin sarauniyar mata ce, kuma sarauniyar zuciyar Sahal." Na kasa tanka masa, na kuma kasa tafiya na bar shi. Kamar jifa Abida ta iso, na zuba mata ido ina kallon yadda take masa wani iron kallo. Jikina ya hau ɓarin kada ta mini sanadin tsiya domin har zuciyarta na shaida bata ƙaunarsa tun hadɗuwarmu ta farko. A sanyaye ta nuna shi da yatsa ta ce "S.S.Mashi again? Da walwala ya ce "Tabbacin haɗuwarmu haɗin Allah ce. " Ta rausayar da kai ta ce "Ubangiji ya yi zaɓin alheri." Da karsashi ya ce "Ameen ƙanwar rijalu". Dukkanmu muka yi dariya domin mun gane tsokanarta ya yi da nufin raha. "Ya mayar da hankalinsa kanta ya ce baki tambayi naki masoyin ba?" Taɓe baki ya yi tare da faɗin "Na mance ma yadda yake, ban sake tuna shi ba sai yanzu daka yi maganarsa." Ya rausayar da kai ya ce "Da kin san yadda Musawa ya rikice a kanki da kin ji kunyar wai kin manta da shi". Kaitsaye ta ce "Ina abin jin kunya tunda ba dama zan ba shi ba! A sanyaye ya kalle ni ya ce "ina fatan dai Bilkisu zata ba ni dama." Ban amsa masa ba, ya juya ga ABIDA ya ce "ki taimake ni kada ki hana a ba ni dama". Ta maƙe kafada tare da ce wa "Matuƙar tana sonka ai fatan alheri ne nawa, abu da ba ni zan tayata ɗaukar jidalin ba" A matuƙar sanyaye ya ce "Wanne irin jidali kuma?" Ba fargabar komai ta ce "Tiritiri da matsalolin da ake shiga a dalilin auren namiji mai bayyananen kyau mai k'arancin shekaru. Mamaki ya sanya ya kasa magana. Da ƙyar ya ce "da alamu idanuwanki sun haska miki ni a baibai". Yana rufe baki ta ce "Ina da yaƙinin shekarar da shugaban ƙasa Wasola ya sauƙa daga mulki ka iso duniyar." Ya kaɗu da furucinta domin kuwa hasashenta gaskiya ne, tabbas a wannan shekarar aka haife shi a ƙarshen shekarar ma. Ganin ya yi turus ta ce "Ni nasan ba zaka wuce warin yaya Munira ba" Ya haɗiye bacin ransa ya ce "Amma ina ganin ke zan baki shekaru shida zuwa bakwai." Ta ƙyalkyale da dariya ta ce"Ka girme ni tabbas amma da shekaru uku da watanni, ita kuwa Bilki babu watanin ma". Daga haka kuma ta silale ta yi tafiyarta. Takaicinta ya shaƙe shi a dalilin ya gano bata maraba da soyayyarsa da ƴar'uwarta shiyasa ta shigo da wannan rainin hankalin. Ni kuwa gabaɗaya na kasa magana domin ina tsoron jidalin Abida idan mun koma hostel. Amma gabaɗaya na ji babu daɗi yadda take yi masa iyashege mai cin rai. Gefe guda ina cikin zullumin kada ta kore mini shi, ni kam ko na girme masa ina sonsa a haka bare sarkin kankanba ta ce ya ba ni shekaru uku. A matuƙar sanyaye ya ce "Dan Allah saka mini lambarki" Tare da miƙo mini wayar hannunsa. Na karba na sanya masa. Na fara tafiya ya biyo ni yana faɗin "Yayanki ne ya kammala ko Yayarki?" Cikin nutsuwa na ce Yayata ce" "Wanne course ta karanta?" Ya tambaya a gajarce. "Law". Da matuƙar mamaki ya ce "Ya sunanta?" "Munirah Musa Funtua". Na furta cike da alfahari, domin sunanta ya yi fice a department din art and social secience gabaɗaya. Da mamaki yake girgiza kansa yana faɗin "Munee sister ɗinki ce?" Na ɗaga masa kai tabbacin eh. Ya ce "Munee gifted ce ƙwarai da gaske." Kafin na amsa masa sai gata, sanye cikin irin rigarsa. Ta ce S. Mashi kai kaɗai a nan?" Tare nake da Bilkisu ƙanwarki, nifa na ga mata Munee". Ta yi dariya tare da ce wa "Idan tana sonka ai shike nan". "Idan bata sona ba zaki taya ni kamfen ba Munirah?" Kai tsaye ta ce "Ni da ba ni zan zauna mata ba, kaga bai kamata kuma na tirsasa mata ba". Ya ce "Hakane". Tare da sakin ajiyar zuciya. Tare da yaya Munira suka shige cikin taron da alamu wani abu zasu yi. Yayin da ni da Anisa muka koma cikin ahalinmu. Sai yamma lis suka ɗauki hanyar komawa gida Funtua. Yayin da Abida ta kaikaice take faɗin yau zuciyar sola sai Allah ta ga masoyinta. Ban yarda na buɗe baki na tanka mata ba. Amma matuƙar zamu zauna daga ni sai ita, zata kaikaice ta ce "Bilki yanzu sai ki amince da yaron nan? Na rantse miki fa da kad'an zai girmi yaya Munirah. Ya miki yaro da yawa, ga shi sololayi zubin makirai, kin ga Bilki ina raba ki da kisan mummuƙen namiji". Ranar da ta fara faɗa mini wannan maganar na yi dariya ƙwarai da aniya domin yadda ta yi maganar tamkar wacce tasan kuttun ya'ya maza. Shi yasa a kullum ina tuna Abida sama da sau goma a rana. Domin komai ta faɗa mini a hankali nake ganinsu a cikin rayuwata, suna tabbata. Na numfasa na fashe da kuka ainun, sosai na yi kuka. Kukan da na tabbatar ba zan daina yinsa ba ila yau mil ƙiyamati sannan na cigaba da hakaito rayuwarmu tamkar a majigi. [8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488# *Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*. *DINGISHIN KWADO* *BY* *SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA* 08 *Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *07036662633* *Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253* Cikin sanɗa da hila S.Mashi ya shiga jikina. Domin wata irin kalar soyayya yake gwada mini mai tsayawa a rai yana kirana sama da sau biyar a , kullum kuma sai ya zo ya ganni, al'amarin da nake mamakinsa, ina yawan tambayar kaina shi bai tafi gida ba ne ko kuwa? Ashe a Zaria yake zaune gidan Baffansa wan mahaifinsa wanda prof ne a jami'ar. Haka nan a cikin quarter's din makarantar suke zaune. Sanadina ya sanya bai tattara ya tafi gida Katsina ba tunda ya kammala Asalin su Sahal ƴan asalin ƙaramar hukumar Mashi ne. Mafi yawa zuri'arsu ƴan boko ne wayayyu, sun kuma watsu a sassan arewacin ƙasar. Wasu na Kano, wasu na Kaduna, wasunsu na Katsina da Zaria, wasu kuwa na Abuja da cikin Mashi. Sannan mafi rinjaye su farare ne ƙal masu zubin sadaka yalla, domin duk fadin Mashi da kewaye idan ka ce gidan jajaye yaro da babba yasan gidan ake nufi.. An tabbatar asalin tushensu na Agadaz ta ƙasar Nijr. Kakannnsu daga can suka fito, kowa kuma yasan alaƙar mutanen jihar Katsina da Nijer. Mahaifinsa na cikin waɗanda suke zaune a Katsina. Tun Abida na kushe da nuna adawarta akan S.Mashi har ta haƙura ta zuba minu ido a dalilin watarana da ta ganmu tare a Libry muna hira. Ta kasa kawaicin ɗauke kai ta iso gabanmu ta ce "Wai ko yaushe kuna tare kenan? Ya zo da safe, ya zo da rana, ya zo da yamma, yanzunma da daddaren sai kun haɗu? Amma ai kinsan ba'a barinmu hirar dare a gida ko?" Na kasa ce mata komai domin gaskiyar magana ta faɗa mini. Ta numfsa ta ce "Sahalu ta kasa faɗa maka dokokin da aka sanya mana kafin a barmu mu zo makarantar nan. Dan haka zan faɗa maka domin ni ɗin jakadiyar iyayenmu ce. Tsakanina da Allah kana ɗagawa Bilki hankali. A yanzu ne ta shiga aji biyu. Tunda ka shigo rayuwarmu gabaɗaya ka ɗauke mata hankali daga karatun da ta baro gida dominsa, alhalin kai ka kammala naka tare da Yayarmu da muke makwabtaka da ita wajen haihuwa. Kada ka kuma zuwa wajenta a ranakun litinin zuwa juma'a, sannan haramun ne zuwanka a irin wannan lokacin. Bayan haka mu dokace ta dole sai mutum ya bayyana gaban dattijaanmu ya gabatar da kansa tare da neman izinin magana da ƴarsu". Cikin takaicin yadda take nacin jingina masa fikon da ya yi mana bai kai ya kawo ba, ya ce "Na ji Abida a kuma cikin satin nan zan je Funtua na nemo iznin, na gode da tunatarwa". Daga haka ya miƙe ya tafi babu sallama. Ta zauna kusa da ni bayan ta ja ƙaramin tsaki. Tunda ta zauna ba abin da take yi sai yaɓa mini baƙaƙen kalmomi. A matuƙar tunzure take faɗin kin faɗo da yawa. "Ina rantse miki Bilki da wannan sololayin gara miki auren Yaya Faruku mai mata da yara, gara miki yaya Asad duk da yadda ya baki tazarar shekaru masu nauyi. Yaya Usman ya yi ta nuna miki soyayyar da babu algus kina tankwabewa sai kuma ki buge a auren wannan abin? Wai ko dai kina da raunin fahimtar abu mafi kwanciyar hankali da dacewa ne? Ki ture waɗannan da suke cikinmu guda ni da su, wataƙila zuciyarki ta kisima miki ina da son kai, me yasa kika ƙi bawa tarin masoyanki dama sai Sahalu da idan ya kai shekarun ganiyarsa zai ga tsufanki?" Daidai wannan gabar ma sai da na kasa riƙe hawayena. Hakikanin gaskiya Abida ta soni ta yi dukkan iyawarta ta yakice mini shi a rayuwata amma ina? Domin ya iya shirya zakakkun kalmomi, ya iya ririta zuciyar mace, bugu da ƙari kyakkyawan ne na gaske, irin wanda nake so. Jin na yi shiru ta tunzura ainun ta ce "kyawunsa ne yake rudarki, amma da ace kin kula da kyau da kin gane ba shi da kyau, domin dukkan kyawunsa irin wanda yafi zama abun burgewa ne idan mace ke da shi. Fari dogo, mai kyawun fuska. Sai dai a lankwashe yake tunda bashi da siffofin karfafan maza, na rantse miki ba zai iya yin gwagwarmayar rayuwa ba, ina jiye miki gararin rayuwa! Ni fa ko ina da rai ba zan baki kafada ki yi kukan kuttun Sahalu ba. Domin na faɗa miki tun tafiya bata yi nisa ba, amma dan jaraba kin kasa fahimtar manufata. Haka kawai na fara mata kuka ina faɗin "Ki yiwa Allah ba dan ni ba ki daina jingina masa yarinta akan idonsa, baya so, baya jin daɗin al'amarin. Dan Allah Abida kada ki sake kore mini shi ". Na ƙarasa cikin kuka na sosai. Tsawon lokaci ina mata kuka yayin da ita kuma ta kasa ko da kwakkaran motsi. Can ta numfasa ta ce "Wato duk abubuwan da na faɗa ke ko saurarensu baki yi ba, balle na saka ran zaki fahimce ni?" Ta fesar da iskar baki tare da ce wa "Well! Idan Allah ya ya yarda ba zan kuma jingina masa ƙuryciya akan idonsa ba, amma ki sani har duniya ta naɗe a idona yaro ne ƙanƙani da bai fi ki aike shi a matsayin ƙanin mijinki ba. Amma tunda bansan gaibu ba, bansan dalilin da yasa aka jefa miki sonsa ko na ce kika jefawa zuciyar ki ba, na ajiye makamaina, amma ki sani babu ke babu kawo mini matsalolinsa, ke bama za ki ga fuskar tunkarata da kalubalen Sahalu ba. Domin Allah ne shaidar yadda nake jinki a zuciyata da kuma yadda nake guje miki artabu anan gaba. Babu damuwa na daina adawa da soyayyarki da shi tunda kina cikin jerin mutane masu son mutum a kallon farko ba tare da nazari ko tsinkayen halayyarsu ba. Fatan alheri amma ki sani matuƙar kuka cigaba da hirar dare zan bugawa Baba babba waya na faɗa masa kin yi bara'a da kyawawan turbobin da suka ɗora ahalinsu a kai. Sannan tabbas idan mun koma zan siyar musu jarida mafi tsada domin kuwa zan fayyace musu gaskiya da gaskiya cewar aure kike so dan haka su aurar da ke, sai ki kammala karatun a dakinki domin ni ba zaki dinga sanya ni cikin zullumi da fargaba ba, alhalin karatuna na matuƙar buƙatar nutsuwa." Na yi shiru tare da goge hawayena domin na yi matuƙar samun nutsuwar zata daina gwanya masa, sannan ban ji damuwa ba dan ta ce zata faɗa a mini aure. Ta yi ƙwafa tare da ce wa "Kina da kayan kuttu sola! Daga haka ta buɗe tafkeken littafin gabanta wanda modern Biology ne ta hau bita cikin nutsuwa. Yayin da ni kuma na bude littafin()sai dai bana fahimtar komai. Gabaɗaya nutsuwa ta yi mini tutsu, ba dan komai ba sai dan Ubangiji ya sanya albarka a harshe Abida a gaban iyayenmu, idan ta yi shaidar abu gabaɗaya suna raja'a domin ita ɗin bata iya ƙarya ba, a tsaye take tamkar nonon maza akan komai, idan ta ce zata yi abu ko zata faɗa to tana nufin har zuciyarta hakane. Bayan haka na hango da gaske take da ta ce tana cikin zullumi akan yadda na daukaki Sahal. Gabaɗaya rauni ya kamata a dalilin kukan da na yi mata. Tunda ga wannan rana Abida bata sake tisa ni gaba tana kushe Sahal ba, sai dai kuma bata ba ni ƙofar da zamu dinga maganarsa ba, nima kuma ganin yadda ta kame daga yawan takura ni, sai na warware na daina takura kaina na rungumi karatu domin dama faragabar kada ta kore mini shi ta hanyar yi masa isgili ne yake kiɗima ni. Amma a yanzu na wartsake tunda na sani ita ɗin bata faɗar magana da zummar waƙe. Nutsuwar da na shiga da kuma takaita zuwan Sahal sai ya samar mana da daidaito a tsakaninmu. Ta daina musguna mini, ni kuma na mayar da hankali wajen karatuna. A haka muka zana jarabawar zangon ƙarshe. Muka tafi hutu gida, wanda dogon hutu ne na watanni kusan uku. A ranar da muka isa gida Abida bata bari mun kwana ba ta zayyanewa Baba babba halin da nake ciki, a kuma gabana da muka je gaishe shi. Ya nunfasa ya ce "Alamun al'amarin daga Allah ne tunda wanccan karon kin toshe hanyar da zasu haɗu amma cikin ikon Allah sai ya sake haɗasu. Dan haka ki taya ƴar-uwarki da addu'a kawai, sau tari muna ƙin abu sai abu ya zamo alheri, abinda muka raja'a akansa kuma sai ya shayar da mu mamaki." Wata irin salama ta shige ni, domin na yi zaton Baba zai ce sai mun kammala karatu ko kuma na zaba aure ko karatu. Cikin taushi ya cigaba da ce wa "Ai ya turo ƙanin mahaifinsa ya nema masa iznin magana da ita, mun kuma amince. Tare muka yi Barewa College da iyayensa. Ni ajinmu ɗaya da wan baban nasa, mahaifinsa kuwa ajinsu ɗaya da Baba ƙarami. Mutanen kirki ne zuri'arsu basu da aibun da za'a guji haɗa iri dasu. Namiji ai baya kaɗan Abidan Baba. Ta ya Bilkisu son abin da take so." Kunya ta kama ni, na yi ƙasa da kaina ina jin farin ciki na ratsa ni. A sanyaye Abida ta ce "Shike nan Allah ya tabbatar da alheri." "Ameen ameen Abida! Ke ma Allah ya fito miki da naki mijin duk sai na haɗa na aurar da ku rana ɗaya". Da azama ta ce "Na roke ka Baba ka bar maganar nan haka. Bilki ta samu miji, ta kuma amince a yi mata aure. Ni kuma ban samu ba, ko na samu ma sai na kammala karatuna, dan Allah kada maganar nan ta yi tasiri a zuciyarka, ita dai da ta ga zata iya to a yi mata auren ta, Allah ya bata sa'a". A sanyaye ya ce "Ameen". Daga haka ya sallame mu. Duk wanda ya zo gidan sai ta bashi labarin halin da ake ciki. Yaya Faruku kuwa da ta bashi labarin ya zuba mini ido ya ce "Da gaske dai kin fasa yi da ni ko Bilki? Anya alkawari ya ce haka?" Na yi murmushi tare da sunkuyar da kaina ƙasa. Yaya Munirah kuwa addu'ar fatan alheri ta yi ta kame bakinta daga tofa komai. Amma kuma bata armasa al'amarin duk da ta san Sahal sosai tunda shima law din ya karanta. Satinmu biyu da yin hutu yaya Asad ya turo da direba ya kwashemu zuwa Anambara dukkanmu uku. A wannan lokacin matarsa na da tsohon ciki. Mace mai kirki da haba haba da mutane. A wannan lokacin haihuwarta hudu duk mata zata yi ta biyar sai ta daya ta raayi bara. *Na ce Duk masu son oriflame products kowanne iri ku tuntubi Aisha Lame zaku samuna sassuakan Farashin da ya Dara na saura rahusa*. *07036662633* Yaransu kyawawa kana ganinsu ka ga jinin gidanmu. Ni da yaya Munirah muke yin komai na hidimar gidan domin mun lura sassafe yake tashi ya hau hidimar shirya yaran nasu tare da rage mata ayyukan gidan, domin iyayen ƴar aikinsu basu yarda ta biyosu kudu ba. Shiyasa yake taya ta aiyukkan da cikinta ya yi nauyi. Ganin haka ya sanya muka daina komawa barcin safe muna gama azkar zamu fice mu hau hidimar gyaran gidan da abun da zai ci tare da yara. Sai sun tafi sai ku koma mu kwanta idan mun tashi sai muyi abin da zamu ci. Ba ƙaramin daɗin zuwanmu suka yi ba. Duk da yadda Abida bata sanya kanta a hidimar da muke yi ba, daga matar gidan har maigidan tattalinta suke yi tamkar ƙanwar momi ce. Na riga da na gane yadda Baba babba ke son Abida haka yaya Asad ma aka jarrabe shi da sonta. Shiyasa idan tana gabansa take baje dukkan wants ɗinta shi kuma yana yi mata yadda take so. Bansan me yasa har muka yi kwanaki bata fesa musu na sake haɗuwa da Sahalu ba ta bakin nata. A wannan zaman na ɗan fara sakewa da yaya Asad har ina iya zama tare da shi mu yi hira gabaɗayanmu. Wani dare muna zaune a falo ni da Abida muna kallon wani Nigerian fim (The wold apart). Jaruma Ini Edo ta yi matuƙar ba ni tausayin yadda ta faɗa tarkon son ɗan sarki. Domin nasan zafin soyayya. Tausayin da na shiga na yadda iyayen yaro suke ƙyamar haɗa iri da talakawa makaskanta. Tuni barci Mai nauyi ya yi awon gaba da Abida, yayin da yaya Munirah da matar gidan sun jima da shigewa dakunan barci tare da yara. Ni kaɗaice idona biyu. Daidai lokacin kuma na ji alamun dawowar maigidan. Ya shigo sanye da kakinsa da suke matukar yi masa kyau. Yana nan cak a tsaye tamkar saurayi. Ga shi sun fara tara yara. Duk da dai babu tazara a tsakanin yaran nasu. A zamana na fahimci shi ɗin mai son ƴaƴane bai ɗauki ɗabiar yin tazara ba, har ita matar ko dan lokacin duniyar bata waye irin yanzu ba ne, ko dan rayuwar cike take da aminci da sauƙin rayuwa? A kasalance ya shigo jikinsa babu kuzari ya zube a kan kujerar da take maƙwabtaka da wacce Abida take kai. A hankali na ce "Sannu da dawowa yaya". Ya amsa da faɗin "sannu Sarauniyar shaibah. Kallo kuke yi ne har barci ya sure wannan?" Kaina na ƙasa na ce "eh. Ya taya ni mayar da hankali kan allon talabijin din. Murya babu amo na ce "Na yi maka abinci?" Da mamaki ya ce "A wannan daren zaki iya yin girki?" A sanyaye na ce "Ai akwai komai da za'a buƙata indai zaka ci, sai na dafa maka". Ya ce "idan baki takura ba, dafa yunwa nake ji sosai". Na miƙe da hanzari, na nufi kicin ina tunanin mai kuma zan dafa ne? Wanne iyayyin ne ya jani yi masa tayin girki? Ina ma na bar shi ya ɗauko cake ɗin da ya saba ci da shayi ya ci abinsa. Na fi mintina goma ina tsaye a jikin freezer ina nazarin me zan yi masa mai sauƙin sarrafuwa kuma wanda ba zai dame shi ba tunda kwanciya zai yi. Take na yanke shawarar na yi masa jollof din patateo. Sai da na kammala yanka albasa na yi jajjaga tattasai da attaruhu sannan na ɗora na tsayar da ruwan sanwa ƙadan tunda dankalin turawa baya karban ruwa da yawa sannan na fara feraye dankalin. Na buɗe firij na ga ragowar papper fish ɗin da muka ci da rana. Na fito da wanda

Chapter 6 of 11