mini tare da tarairayata fiye da ƴar ɗakinsa sarkin rikici Abida.
Yana isowa na mike tsaye murya a dashe na ce "Baban Bilkisu sannu da zuwa. Ya su Nana da Anti?"
Maimakon ya amsa da baki sai ya cire hularsa tare da ƙamewa ya kuma sara mini tamkar dai yadda ya taɓa yi mana ni da Baba babba shekarun baya.
Daɗi ya ratsa ni har zuciyata domin gaisuwa ce mai ƙololuwar daraja bare kuma ace mai ɗamara ne ya yiwa farar hula irina da ba ni da wani muƙamin komai sai dan girmamawa kawai.
Murmushi ya subuce mini, na ce "Baban Bilkisu na gode da karamcinka".
Ya taya ni murmushi fararen haƙoransa suka haska baƙar fuskarsa.
Ya ce "So nake Bilki ta manta batun duniyar yaya Asad ta yi ta ganinsa a cikin mutanen da suke sonta tare da kambaba dukkan lamarinta."
Na ƙayalkyale da dariya na ce "Ai tunda ka mini takwara na yafe maka, na manta komai na gane na sha gaban Abida. Amma fa ni gaskiya har gobe yaya Faruku ne best"
Ya yi waiwaye ya ce "Idan autar momi ta ji wannan maganar ai kin kunyata ni Maigado".
Na sake yin dariya na ce "Ai gaskiya na furta".
Daidai lokacin Sahla ya gaishe shi cikin nutsuwa domin ya lura ma tamkar bai lura da shi ba, ko kuma mun manta da shi gaba-daya.
Ya amsa gaisuwar babu yabo babu fallasa sai dai ko kadan babu raha ko karramawa. Ya wuce cikin gida ya barmu.
Hirar da bata yiwu ba ke nan. Domin mintina biyar ya ƙara ya mike tare da faɗin "Zan wuce ina son na isa Zaria da wuri. Baba ya ce zan raka shi dubiya bayan maghriba".
Ban kawo komai a raina ba na ce "To"
Muka yi sallama ya tafi a sanyaye.
Na shiga falon Momi na tarar da shi tare da su Baba suna taya shi rarrashin Abida domin tunda ta gaishe shi bata sake kula shi ba, duk yadda take tatsarsa a dalilin bai mata takwara ba, sai ni ya yiwa, bai sa ta huce da shi ba har lokacin.
Na zauna na ce "Wato Allah ya so ni da ba zamu yi kishi ba Abida."
Ta galla mini harara tare da ce wa "Yo ai ke tsare mini gaban da kika yi ko kishiya sai haka. Kowa Bilkisu, kowa Maigado, duk wanda suke jama'atane a da kin kwace mini su a yanzu. Abin kaicon kuma naki mutanen kin riƙe su gam tsabar haɗama."
Gaba-daya aka kwashe da dariya, yayin da ta gintse tata dariyar da take neman ƙwace mata.
Baba ya ce "Abida ƙanwar Bilki kina sanya ni nishadi, idan kuna makaranta sai na ta jina tamkar wanda ya rasa wani abu. Domin kullum kuna ɗebe mini kewa na yi ta tuno da ƙuruciyarku."
Yaya Asad ya ce "Yaran nan kun samu duniya, Allah yasa lahirarku ta zarce hakan."
Wannan karon Abida ce ta yi dariya tare da ce wa "Kai Yaya!
Ya murmusa ya ce "To me zan ce? Gaba-daya kun tattare soyayyar ya'yan fari da ya'yan karshe ku kaɗai. Fatan Allah yasa kuna ibada tuƙuru yadda lahirarku ma zata yi muku daɗi fiye da nan"
Ya nisa ya ce "Wai ina Muni ban ji ɗuriyarta ba".
Baba ya ce "jiya ta je Katsina yayarsu bata jin daɗi shine ta je ta ɗan kula mata da yara kafin tafiyarsu Kano ta taso".
A ladabce ya ce "Allah ya bata lafiya, amma mun yi waya bata faɗa mini bata da lafiya ba".
Baba ya ce "ka manta zurfin cikinta ne? Kasan kuma ce wa zata yi, kana nesa ba zata tayar maka da hankali ba tunda ba kashirban take ba '".
Bamu tashi ba sai da aka fara kiran sallar magarib. Ni da Abida muka yi sashinmu dan bawa baba babba damar ganawa da baban Bilkisu sosai. Tunda ya mini takwara na koma ce kishi hakan a gabansa ko ba'a gabansa ba. Na kuma fahimci yana son sunan domin da karsaahi haɗi da kazangi yake amsawa.
Daren ranar shiru Sahal bai ƙira ni ba, tunda tara da rabi ta yi na shiga tunanin ko lafiya domin da zarar tara ta yi idan muka fara waya muna kaiwa goman dare ko fiye da haka tamkar da akan iska muke magana ba kuɗi ba.
Da goma ta yi sai na kasa haƙuri na buga masa, amma har ta katse bai ɗauka ba, kuma bai katse dan ya biyo baya ba. Ban shiga mamaki ba sai da aka shafe mintina talatin bai bugo ya gabatar da uzzirin baya kusa ko yana tare da iyayensa ba. Gabadaya na daburce, na sake ƙira a karo na uku sai na ji an kashe wayar ma bakiɗaya. Da yake fashin sallah nake yi, sai na takure a kan gado gaba daya na rasa jin daɗin zuciyata. Yayin da tuni Abida ta yi barcinta cikin nutsuwa. Idan akwai abin da yake burge ni da Abida to rashin sanyawa kai damuwar duniya ne. Samsam bata yarda ta yi sabo da abin da zai dame ta. Kusan kullum sai ta ce mini soyayya lalura ce kabiran. Kafin ta yi barci ma da ta lura da yanayina sai da ta ja tsaki ta ce "Ya miki sabo da kalaman da kaso saba'in cikin ɗari na daɗin baki ne ba na gaskiya ba. Da zarar an haɗaku zaman aure hirar mintina goma ma sai an wayi gari ba zai iya ware wa cikin lokacinsa ya yi da ke ba, a yanzu kuma ya yi miki sabo da doguwar hirar da idan baki ji daga gare shi ba zaki kidime ki kasa sukuni. Me za'a yi da soyayya irin taki ne Bilki?"
Da nasan gaskiya ta faɗa sai na kasa amsa mata domin ba ni da bakin yi mata musu ko raddi dan idan ta kaikaice ta fara cashe mini sai ta sanya ni kuka na gaske. Sannan zata juya ta yi kwanciyarta, cikin nutsuwa zan ga tana sauke numfashi tabbacin barci mai cike da nutsuwa take yi.
Da ƙyar na yi barci ina ta saƙesaƙe ko jinya ce ta kwantar da shi tunda a kullum sai ya ce mini ba zai iya barci bai ji muryata ba. Shiyasa ma baya ƙirana sai ya yi sallar Isha domin da zarar mun gama waya barci yake yi muryatace abu na ƙarshe da yake ji a ko wanne dare.
Ina idar da sallar asuba na sake ƙiran layinsa amma shiru kake ji a kashe take.
Na shiga damuwa duk yadda nake son komawa barci ranar ban samu sukunin komawa ba.
Sai da muka karya muka yi sashen Momi hannuna ɗauke da ledar alawa da biskit masu tsada cikin wanda Sahal yake kawo mini na ɗiba na zuba a leda da yawa da mufin na bawa baban Bilkisu ya kaiwa Hafcy. Muka tarar shi kadai yana karyawa kuma ya yi haramar komawa. Muka gaishe shi ya amsa tare da faɗin "Na shiga gaida Mami da Baba ƙarami baku tashi ba".
Abida ce ta amsa da ce wa "ki ce ban tashi ba kawai, amma ita bakam ta yi bata cikin hayyacinta saurayinta ya yi mata fushi tun daren jiya ta rasa walwala da kuzari ".
Ga mamakina sai na ga ya ɓata rai, bacin ran da ya bayyana har a fuskarsa. Da farko tamkar zai share sai kuma ya kasa hadiyewa ya ce "Har haka kika bari ya mamaye ki ne Bilki? Ni ba dan kar na zama babban kwabo ba da sai na ce miki kin fishi ƙarfi da karsashi, gabadaya fa siffar mata gare shi wannan yaron, dan dai kina sonsa ne, autar momi ta yi gaskiya zubin makirai ne da shi, kin kasa ganewa, bansan me yasa ba zaki gane gaskiyar lamari ba, yanzu saboda Allah Maigado menene aibun auren mai mata ne?"
Zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Amma saboda yadda Abida ta kasa ta tsare tana kallonmu nasan ba iya kallon kawai take yi ba, har da nazari. Domin kamewa ta yi tana kallonmu cikin tsananin nutsuwa.
Dan haka cikin rawar murya haɗi da kuka na ce "To shine ya tunkare ni da sunan soyayya ban da shi babu wani, sannan mai matar ai bai zo ba, bare ace na jingina masa aibu."
Bansan ya aka yi ba Abida ta yi fit ta ce "Sau dubu nawa zasu zo? Yaya Faruku fa?"
Takaicinta ya shake ni, na rushe da kuka sosai na ce "Da yaushe ya taba tare ni da sunan soyayya ta gaskiya ba ta wasa ba?"
Kafin ta amsa mini Baban Bilkisu ya ce "Kin fita gaskiya. Faruku bai zo da gaske ba, amma akwai wadanda suke son ki da gaske kina tankwabarwa, abokin nan nawa da gaske yake yi, bayan shi akwai wani da zaki amince ya tabbatar mini ko yaushe a shirye yake domin kin yi masa irin sosai ɗin nan".
Abida ta numfasa ta ce "oh Yaya Asad!
Ya yi biris da ita domin sosai ya ɗaure fuska dan haka dole ta kame bakinta ta tsuke.
Ya numfasa ya ce " share hawaye ki ki daina kuka kin ji, ba wacce aka yiwa auren dole a gidan nan, matukar ina raye kema ba za'a yi miki ba, ina miki fatan alheri tsakaninki da yaron".
Daga haka ya mike ya zura hannu a aljihunsa ya ciro ƙudi ya damƙawa Abida ya ce "ke da ita, ku sayi abin da kuke so idan zaku koma makaranta."
A sanyaye ta yi masa godiya. Ni kuwa na kasa yin godiyar.
Ya ce "To mu je ku raka ni mu yi sallama da su Baba."
Na miƙe na zare abin hannuna wanda na stones ne, na sake zaro ribbon din kaina na jefa a ledar alawaer na ce "ga shi ka kaiwa Hafcy, ka faɗa mata I realy miss her silly questions."
Ya murmusa ya ce "Kullum sai ta yi hirarki, kullum sai ta ce "Anty Maigado zata. Ga shi Maigado ba mai fahimta ba ce".
Zuciyar tawa ta sake karaya,.nauyi mai yawa ya kama ni. Na saci kallon Abida na ga itama kallona take da dukkan nutsuwarta.
Haka muka bi bayansa ba tare da mun iya tofawa ba.
Ya yi sallama da kowa, iyayenmu suka bishi da sanya albarka tare da nema masa tsarewar Ubangiji akan dukkan lamarinsa.
Har waje muka bishi ni da Abida.
Bana manta kallon da ya kafe ni da shi, amma bai ce ƙala ba, illah faɗin "ku kula da kanku Allah ya sake haɗamu da alheri."
Abida ta rike hannunsa ta ce"Ka kula da kanka yaya! Su Baba na buƙatarka, matarka da ƴaƴanka na buƙatarka, muma muna sonka, kada ka saka damuwa mai yawa akan lamarin wanda baya bukatarka ko ba shi da asara idan ka haɗu da jinya ".
Ya zuba mata ido irin sosai tare da ruƙo dukkan hannuwanta murya cike da rauni ya ce "Zan kiyaye autar momi! Sai dai bana son ki zama mai son kai, ko tursasawa ga rayuwar wani ta hanyar kyara da ƙaranta mu'amala. Kina da hazaƙa, kina da saurin fahimtar al'amurra. Na roki kada ki yi ƙullaci ko kushe wanda Maigado take so "
Ta amsa da ce wa "To" a takaice.
Jikina ya sake sanyi sosai domin na gaskata sona yake yi. Sai dai tabbas bai yi mini ba, duk yadda yake a tsaye kuma ƙarfaffa. Amma bana son auren zumunci, bana son auren mai mata bana son baƙin namiji.
Ya shiga motar da ta zo daukarsa suka tafi.
Abida ta yi gaba ta bar ni da sanyin jiki. Da ƙyar na ja ƙafafuwana na bi bayanta. Shariyar Abida da rashin samun wayar Sahal suka yi mini rubdugu. Yini guda ina ɗaki sai juyi nake yi na rasa sukuni a jika da zuciyata.
Da na idar da sallar la'asar na dauki wayar na sake ƙiran layinsa a karo na barkatai. Cikin sa'a ta shiga, gaba-daya na ji wani irin salama ta shige ni. Sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba. Na sauke ina sake gaskata lallai akwai matsala. Sai dai tunanina bai haƙaito mini menene dalilin faruwar haka ba.
Ina ta kokawa da zuciyata akan kada na sake ƙiransa. Ba zato sautin da na sanya masa na real love by massari ta hau tashi. Kamar zan share amma na kasa sharewar.
[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.
*DINGISHIN KWADO*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
11
Deenah cakes and more -Kano
09038055790
IG @Deenah cakes and more
Snacks such as :
Birthday cakes
Cupcakes
Samosa
Springrolls
Meatpie
Frozen snacks
Event snacks
*Lafazi writer's*
Jiki na bari na amsa kiran. Ba wani karkasashi ya ce "Na ga tarin missed call dinki, hidima ta sha kaina ban samu sukunin kiranki back ba".
Na yi sororo da waya a hannuna. Domin a yadda na dauka babu hudimar da zata hana ya nemi ji daga gare ni, mussaman wayar dare da ta zame mana kaida.
Tsawon lokacin ban samu sukunin lalubar kalma ko guda ba.
Ya numfasa ya zarce da ce wa "Bilki so nake ki bani dama na turo a tsayar da maganar aure a tsakaninmu. Don so nake yi, na takaitawa kaina zullumi da fargabar rasa ki".
Gabana ya takarkara ya fadi. Aure kuma? Ban ci karfin karatuna ba, duk yadda nake son Sahal ban hakaito na yi aure a lokacin ba, domin dukkan sisters dinmu ba a aurar da su ba sai da suka kammala digiri. Ga Yaya Munira ma bata yi a aure ba sai ni?"
Da rawar murya na ce "Aure yanzu?'
Ga mamakina sai kawai ya katse wayar gabadaya. Ba tare da ya ce uffan ba.
Na rike wayar ina kallonta tamkar wacce zata fahimtar da ni dalilin sauyin da nake ga ni a tare da Sahal.
Gabadaya na sake rikicewa, na kasa gane mai yake yi mini dadi a duniyata. Kwanakin biyun da suka biyo baya masu tsauri ne domin gabadaya Sahal ya yi watsi da ni. Na kasa tattauna halin da nake cikin da kowa. Abida ce abokiyar hirar, sai dai ban isa na tunkareta da maganarsa ba. To ban fada mata matsalata da shi ba kullum a cikin yi mini habaci da shaguben son da nake yi masa ya zarce wanda yake yi mini take. Bare yanzu da take mini fushi akan ban so brothers dinta ba.
To ina kuma ga na bude baki na tabbtar mata damuwar da nake kwana na yini a cikinta Sahal ne sababinta.
Cikin rashin karsashi nake hada kayana na komawa makaranta tunda a sati mai zuwa hutunmu zai kare.
Kwanaki biyu ke nan da nutsuwa ta yi mini tutsu sosai a dalilin kullum lamarina da Sahal na sake cakalkalewa. Na gama tunanina nasan ban yi masa komai ba. Haka kuma nasan bamu samu sabanin ra'ayi ba.
Haka siddan matsalakan ya dauki zazzafan fushi da ni, dan kawai yasan zuciyata ta shaku da shi, ta kuma kambaba sha'aninsa.
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
Ranar talata da daddare bayan Abida ta yi barci. Na lallaba na kira wayarsa domin na kai matukar gajiya wajen takura da yanayin da ya jefamu.
Bugu biyu ya dauka murya babu amo ya yi sallama.
Na amsa sai kuma na yi shiru. Na kasa ce wa kanzil.
Murya a dashen ya ce "Me ya hana ki barci Bili?"
Maimakon na amsa sai na jefa masa tambaya na ce "Ni kam mai yake faruwa ne. Tun zuwan da ka yi last gabadaya ka canja mini, na gama iya nazarina ban hango inda muka samu sabani ko na bata maka ba. Amma ina ta ganin changes masu yawa a tare da kai. Tun ina yi maka uzzirin ko yanayin rayuwa ne har na fahimci kawai dan ka ga na damu da kai ne shiyasa zaka yi amfani da hakan wajen gigita nutsuwata!
Na kammala maganata cikin yanayin damuwa ainun.
Ya numfasa ya kaurara murya ya ce *Bilkisu".*
Na kasa amsawa domin ban saba jin ya kama cikakken sunana ba, yafi ce wa Bilki ko Bily.
Ya zarce da fadin "Gaskiyar maganar ban ji dadin wulakanta ni da yayanku ya yi a gidanku ba!
Gabana ya takarkara ya tsinke. Na kasa hakaito wanne a cikin yayan nawa yake batu a kansa?
Ban kai ga ganowa ba ya ce " Bilki tuni na fahimci mafi yawa y'anuwanki basu sona tare da ke. Na gama tunanina ban samu gamshasshen dalilin da zai sa su washe ni irin haka ba. Amma daga ranar da muka yi ido hudu da Asad Funtua na gane shi suke marawa baya, haka nan muzanta ni da ya yi a gabanki ya tabbatar mini da ce wa sonki yake yi, an kuma shirya yaudarata ne shi ya sanya aka karbi iyayena da hannu bibbiyu."
Raina ya baci sosai. Da rawar murya na ce "Wa ya shirya yaudarar naka ni ko iyayena Sahal?"
Jin na harzuka da yawa sai ya yi maza ya sassauta ya ce "Ai idan muna magana a tsakaninmu iya ni da ke ta shafa, babu maganar iyayenmu a ciki don kuwa ba abokan wasanmu bane. Ke kike mini wasa da hankali. Domin yadda kika manta da ni daga isowar yayanki wajen da muke zaune ya tabbatar mini da cewar kema kina sonsa, kinsan kuwa duk yadda iyayenku zasu so ni ba kamar dansu ba ko?"
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya na ce "Ba a mini dole akan lamarinka ba, da yawuna ka turo aka tambayar maka izinin neman aurena, menene zai tayar maka hankali akan Yaya Asad?"
Da azama ya ce "Soyayyarki da na ga ni cikin idanuwansa da gangar jikinsa ce ta dame ni".
A tausashe na ce "Indai ba a nawa idanuwan ka ga soyayyarsa ba, ban ga abin damuwa ba, domin kuwa na riga na zabe ka".
Maimakon ya ji dadin kalamaina ya gasgata ni, ya huce. Sai ya numfasa ya ce "Indai nine zabinki to zan turo a yi maganar aurenmu idan ba haka ba, to kuwa sai dai idan hakan ya zama lisisin korata. Ni ba zan iya jure zullumin da nake ciki akan wannan tafkeken dansandan ba".
Na murmusa na ce "Me yasa ka karaya haka? Me yasa ka rasa jarumtar gwarazan maza?"
Murya babu amo ya ce "saboda Baba babba ne ubansa. Kin sani, na sa ni kuma still baba babban ne mai bada aurenki, idan kuwa haka ne ko ban ce komai kin san ína da hujjoji da zasu karya dukkan confidence dina."
Na numfasa na ce "Dukkan sisters dina da aka aurar sai da suka kammala jamia, ni fa yanzu ne na gama shekarar farko ma, ka yarda kai ne zabina".
Ina rufe baki ya ce " Allah ya bamu alheri! Cikin fishi ya furta hakan, sannan ya katse kiran.
Na daure ban kira shi ba . Kwanaki biyu Muna cikin takaddama. Kan dole na hakura na bi ra'ayinsa na amince mu yi auren tunda shine samun masalaaha a tsakaninmu.
Domin gabadaya ya fittitke akan ko dai mu yi auren ko kuma na ya yi gaba ba zai yarda na cigaba da yaudararsa ba.
Bamu koma makaranta ba sai da ya turo aka yi maganar aure tare da kawo dukkan abubuwan da ake yi ja al'ada. A sanya aure watanni hudu masu zuwa wanda ya yi daidai da kammala zangon farko na aji biyu.
Mahaifana duka biyu basu wani so lamarin ba, domin kowa da dalilin da ya hana shi zumudi.
Baba karami so ya yi ace a cikin yayan Baba babba ne zai aure ni, yayin da mami take kuncin ga Munira nan da kammala digiri ba a yi mata aure ba sai ni dan bakar mugunta irin ta Baba babba.
Ni dai na kame bakina ban ce mata komai ba, amma nasan koma menene nice da alhakin komai tunda sai da baba babban ya tambaye ni, na amince Sannan ya basu damar zuwa da maganar aure.
Ansar na zugata, yayin da Yaya Sulaiman ya ce "Mami huce ki daina damuwa dan ta riga Munira da Abida aure ai ba wani abin bane. Kowa da yadda aka tsara masa rayuwarsa, kawai yi hakuri ki bita da addu'ar dacewa". A lokacin ya zo hutu.
Kan dole ta hakura amma ba dan ta so ba.
Murna da zumudi da Sahal ke cikinsu ba zai yiwu na iya hakaitosu ba. Domin gabadaya ya ninka kulawar da yake yi mini, yayin da ni kuma na takura gabadaya na kasa samun nutsuwa a zuciyata. Haka siddan nake jin tamkar na yiwa kaina garaje. Na rasa da wa zan tattauna, na rasa wa zan tunkara ko na samu na fita daga takura da na samu kaina a ciki.
Ana jibi zamu koma makaranta. Da hantsi na ji ana ta kiciniya a harabar gidanmu. Da yake dakinmu na sashen baba babba muna ganin harabar ta taga. Da yake bana iya barci a dalilin nauyin da zuciyata ta yi mini a kwanakin nan. Ya sanya na sauka daga gadona na isa jikin tagar na yaye labulen kadan dan kada haske ya isa ga fuskar Abida ta tashi ta rufar mini da bala'i. Tunda aka saka ranar aurena ta sake botsare mini fiye da kwanakin baya. Ba gaba take yi da ni ba, a a kawai ta sake kamewa daga shiga dukkan shirgina, yana wahalar gaske ta yi mini magana a karan kanta, amma idan na yi mata zata amsa ko da a takaice ne. Haka nan shekaranjiya bayan an kawo kudin aurena.
Ta kalle ni jikinta a sanayaye ta ce "Ina miki fatan alheri a cikin hukuncin da kika yankewa kanki. Ina miki fatan kada ki yi kuka a hannun Sahalu"
Daga haka ta bude littafin Jiki magayi ta hau bitarsa da haka Har barci ya sure ta.
Na saki ajiyar zuciya mai nauyi ina cigaba da leken yadda ake ta daura tampol tare da shimfida tabarmai . Tsawon lokaci ina tsaye ina kallo tare da cankecanken me za'a yi haka a gidan na hidima bamu sani ba?
Na tabbatar da mutuwa ce ba zan ga ana yin aikin cikin walwala da nutsuwa ba.
Nan da nan aka kammala shimfida aka shiga ajiye kulolin abinci kalakala tare da lemounan kwalba na maltina da su coke.
Na sake shiga mamaki, sai na yi tamkar na tashi Abida sai na fasa domin tashinta a barci bata dauke shi da sauki ba. Yana cikin zunubin da idan aka yi mata sai an biya ta da wani abu, ko ku yi ta buga dabi.
Kafin ka ce kwabo kuma sai shigowa ake yi ana ta zama, na gane wasu da yawa abokan Yaya Faruk ne. Yayin da ban gane wasu da yawa ba.
Ina tsaye ina kallon ikon Allah kawai sai na ga Yaya Faruk ya shigo ya zauna cikin alhini, sai mika masa hannu ake yi ana yi masa jaje tare da fatan Allah yasa hakanne alheri.
Kaina ya sake kullewa, a fili na furta "Menene yake faruwa ne?"
Gabadaya wajen sai hada hada suke suna cin abinci ana ta hira yayin da Yaya Faruk ya tagumi cikin takurarren yanayi.
Can Kuma na ji ya hau fadin "Ba fa hira da nishadi na kiraku mu yi ba. Na gayyatoku ne ku taya ni alhinin rasa sarauniyar shaiba".
Suka dauki hayaniya kowa na fadin "Rashin rabo ya sanya bai fahimci Dingishin kwado da wuri ba.
Ni kuwa gabadaya na ji jiwa na katantawa da ni, kaina ya kulle dakin ya shiga juya mini tamkar an mayar da kasan ya koma sama.
Hawaye ya balle mini. Wani irin abu ya sake tokare mini a kirjina. Hakan ya saka damuwar da nake ciki ta rubanya tsananta. Bansan ya aka yi ba na ware baki na fashe da matsanancin kuka, hawaye da majina suka dinga sintiri a fuskata.
A kidime Abida ta tashi ta zauna a tsakiyar gadonta.
Murya a dashe kuma a firgice ta ce "Me ya faru, mutuwa aka rafkane Bilki? Hayaniya nake ji sosai".
Ta duro a gigice dan taga abin da yake wanzuwa har ya sani kuka sosai.
Bata ga komai ba, illah Yaya Faruk da jamaarsa suna ta cin abinci da alamu walima ake yi duk da shi din bata ganshi da kuzari ba.
Ta saki labulen yayin da ni kuma na yi kasa na zauna dabas a kasan tayal ina cigaba da kokawa ainun.
Ta yi shiru amma gabadaya jikinta ya saki. Ta zauna kusa da ni a tausashe tamkar ba Abida ba ta ce "Na hada ki da darajar ma'aiki ki fada mini me ya