idan an sauya sau ɗaya ba'a kara sauyawa, muje kada muyi late"
hanunta cikin na kaka tana murmushi kamar ba abinda ya faru har suka shiga cikin company ɗin, wajen ba abin kallo bane saika shiga ciki zaka san akwai kuɗi a duniya, ginin kamar da ruwan gold akayi, komai na ciki kerarre ne, kama daga masu aiki duk sanye suke da uniform kala ɗaya, mata dogon riga maza kuma riga da wando, uniform ɗin pink ne da hula fari, komai a tsare yake, office office nasu yayi kyau, ga kuma inda suke aje manyan motocin da suke kerawa a gefe, sai kuma gefe inda suke aje motocin hawansu, hanunta cikin na kaka har sukaje wajen sa hannu, kaka tayi sign na cewar ta canja me aiki, itama tayi sign tana jin faɗuwan gaba sosai, koda suka fito kaka ta bata kuɗi tace "janan dan Allah kiyi hakuri da duk abinda za'ayi miki idan kuma baiyi miki ba wallahi zamu hakura da aikin"
hanu biyu tasa cikin dariya ta juya kaka tace "to tsohuwa jeki gida naji"
har waje ta fitar da ita sannan tana ɗaga mata hanu ta koma ciki, kaka ta tafi gida tana tausaya mata domin kuwa aiki anan ba abune me sauki ba, itama sabida halin yunwa data shiga yasa take aiki a wajen badan haka ba, ba zata iya juran wulakanci da yake musu ba, bata yadda ta faɗawa su janan bane amma ranan marinta yayi ba wai niyan marinta ba.
janan tana juyawa ta rasa inda zata fara zuwa, wani me aiki a wajen ta tsayar tace "please aina ake karɓan uniform?"
nuna mata wani office yayi tace "na gode"
zuwa tayi da sallama ta shiga, tace abata uniform bata akayi sannan matar ta nuna mata inda zata canja, zuwa tayi ta canja, kallon jikinta tayi rigan ya mata kyau ga kuma farin hulan da tasa akanta, takalminta tasa sannan ta fita, tana tafiya ta rasa inda zataje taji wani yace "ke?"
a tsorace ta kalleshi tace "na'am"
yace "boss yace ki wanke wancan motar"
nuna mata motan daya watsa mata ruwan dashi akayi, da sauri tace "ina yake shi boss ɗin?"
yace "shi dai yace ki wanke mota"
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ta ya zan fara?"
gani tayi mutumin ya tafi, juye juye ta fara harta hango fonfo, roba ta nemo da kanta taje ta fara ɗiba ruwan tana zubawa akan motar, sai haƙi take jikinta duk ya jike, hamdala tayi lokacin data gama, zata tafi taji wani yace "ke"
a tsorace ta kalleshi
yace "boss yace motan bai wanku ba ki sake sabon wanki kuma ki wanke sau goma"
a tsorace tace "goma?"
barin wajen yayi bai kara mata magana ba, dube dube ta fara ko zataga boss ɗin bata ganshi ba, omon daya wurga mata ta zuba a roban, ruwa ta fara ɗiba da kyar tana wanke motan, sau tara ta wanke sabida ta wanke ɗaya ɗazu kafin yazo, hakan yasa ta samu waje ta zauna tana haƙi domin ta gaji, kara zuwa yayi yace "boss yace saura ɗaya sau tara kika wanke"
wannan karon ta gama tsorata da kyar ta tashi ta ɗau roban ta ɗibo ruwa, tafiya ta fara tana tangal tangal, zafin ciwon kwankwason bai daina mata ba har yanzu domin jikinta ɗanye ne, faɗuwa tayi da roban ruwan idonta yana rufewa, bataga alaman akwai mai taimaka mata ba, da kyar ta kara ɗaukan roban da ruwan ya zube ta kara zuwa ta ɗiba a durkushe tana ciza baki ta karasa wajen motar ta wanke, kife roban tayi a kasa sannan ta kwanta a kasa itama a wahalce, yana tsaye akan stair yana kallonta har zuwa lokacin data faɗi, kunnenshi sanye da headphones sannan wayarshi a hanu, ya harɗe kafa ya jingina da karfen stair ɗin yana taunan cingum a hankali, kiran waya yayi yace "taje ta fara aikin daya kawo ta"
katsewa yayi yana kallonta har lokacin da aka sanar mata, cikin wahala ta tashi tace "ina ake cleaning ɗin?"
nuna mata yayi yace "wancan side ɗin zaki rinƙa kula dashi, shine wajen wucewan boss kafin yaje office nashi mistake ɗaya aka samu zaki bar aikin haka dokan boss yake"
jijjiga kai tayi kwanciyan da tayi a kasa yasa ta ɗan huta, da kyar ta fita zuwa inda ya nuna mata, sharewa ta kara yi sabida gudun mistake sannan ta fara gogewa, wajene me matukar kyau kofofin duk na glass ne kasan tile ɗin kamar kaga fuskanka a ciki babu kura ko kaɗan bale maganan datti, kyau wajen yayi sosai domin ita ta kware a shara da mopping ko gidansu ya maheer bata barin masu aiki suyi aikin itace take yi hakan yasa wajen yayi kyau sosai.
*Masha Allah anan na kawo karshen free pages duk me son complete ya biya naira 300 ta nan 8144818849 Hauwa shuaibu mapi opay, a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849, please idan kin san baki shirya ba kada kimin magana ki bari sai kin shirya*
*Jiddah Ce....✍🏻*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels