girl"
cikin sanyin muryanta tace "banji me kikace ba"
kallonta mufeeda tayi tace "girl this one no sabi English"
tace "I see"
ya daɗe da barin wajen, madina ta rike hanunta tace "ya sunanki?"
tace "sunana JANAN"
atare sukace "wow janan nice name, muje ciki kiyi wanka kinji?"
a hankali tace "to na gode"
suna tafiya tana bin ko ina da kallo, ba karamin gida bane a wajen, duk furnitures ɗin fari kal, ɗakinsu suka kaita ɗaki ne me kyau wanda aka ƙawata musu da kayan more rayuwa, gadonsu kamar gadon sarauta ga kuma sofan dake gefe me taushi da kyau, towel madina ta bata tace "ɗaura ki shiga wanka"
karɓa tayi cikin tsoro take kallon kan gadonsu, madeena ta ɗau teddy ɗaya ta mika mata ganin tana kallo tace "ga wannan na bar miki shine naki kinga mufeeda tana kwacemin sabbin teddy's ɗina"
baya baya take yi idanunta da alaman tsoro, wurga mata tayi ta zaci ko wankan zata shiga shiyasa take yin baya, ihu tayi lokacin da teddy ya taɓa mata jiki, da mamaki madina tace "kina tsoron teddy?"
jijjiga kai tayi cikin tsananin tsoro, dariya tayi sannan ta ɗauke tace "ok sorry"
shiga buɗe mata toilet ɗin tayi ta shiga, ɗaura towel ɗin tayi sannan ta tsaya a gefe tayi shiru, ta rasa ta yadda zata fara wankan, madina bataji karan ruwa ba tace "baki fara bane?"
a hankali tace "ban iya ba"
tashi tayi ta shiga ciki ta fara nuna mata yadda zatayi, cikin sanyin ta tace "na gode"
momy ta kasa daurewa ta nufi ɗakinshi, tura kofan tayi yana shirin shiga wanka tace "i don't understand meke faruwa ina khairat? meyasa kazo da wannan?"
yace "momy bara nayi wanka zan fito"
tace "yanzu nake so ka gayamin, khairat tace bakaje gidansu ba kuma baka ɗaukan kiranta"
yace "momy accident nayi kuma wannan yarinyar na bige mun kwana a hospital"
tace "subhanalla ina fatan bataji ciwo ba"
yace "bataji ba sosai amma jikinta yana ciwo sosai"
tace "Allah sarki bari naje nace tayi wanka da ruwan zafi sosai"
yace "ok momy thanks"
momy zuwa tayi tace "mufida ki haɗa mata ruwan zafi sosai tayi wankan dashi"
ta amsa da "ok momy"
knocking na kofan toilet ɗin tayi tace "ɗaura towel ki buɗemin momy tace nasa miki ruwan zafi sosai"
gabanta ne yayi mummunan faɗuwa karfa ya faɗawa momy abinda ya sameta, ɗaura towel ɗin tayi tazo ta buɗe, ɓoɓɓoye jikinta take ta rakuɓe a bayan kofan, ruwan zafi sosai ta haɗa mata sannan tace "yawwa shikenan"
fita tayi ita kuma janan ta tura kofan, taɓa ruwan tayi taji da zafi sosai a hankali ta shiga ta zauna, ihu ne yazo mata da sauri tasa hanu ta rufe bakinta, sai wasu zafafan hawaye yake wanke mata fuska, zafi take ji sosai, runtse ido tayi ko a mafarki batason tuna abinda ya faru, a duk lokacin data tuna sai taji bugun zuciyarta yana karuwa sosai, da kyar tayi wankan ta fito, duk yadda taso ta daure ta kasa tana shiga ta faɗa kan gadon data gani badan taso ba ta janyo blanket ɗin dake kai me taushi, rufe jikinta tayi tana jin zazzaɓi yana rufeta sosai, kuka ta fashe dashi ta cusa kanta cikin blanket ɗin sabida bataso kowa yaji sautin kukanta, madina ce ta turo kofan hanunta rike da plate na ruwan zafi da kayan tea sai gefe snacks da ruwa, ajewa tayi tace "kin fito?"
jin tayi shiru ta yaye bargon tana kallon ta, ganin tana kuka tace "me mukayi miki kike kuka?"
ta girgiza kai kawai batayi magana ba, tace "ya MAHEER ne yayi miki wani abin?"
da sauri tace "A,a"
matsowa tayi kusa da ita, riketa tayi ta tashi, taɓa jikinta tayi da sauri tace "your temperature is high bakida lafiya"
plate ɗin tazo dashi ta fara bata ruwan zafin kafin ta bata snacks ta haɗa mata tea me kauri, tana da bukata hakan yasa ta karɓa tasha sosai, saida ta koshi tace "na gode"
murmushi tayi mata tace "don't mention"
wardrobe ta buɗe ta ciro mata kaya me kyau rigan material pink, tace "gashi kisa"
karɓa tayi tace "na gode"
da kyar ta daure tasa rigan, komawa tayi ta kwanta tana maimaita sunan "maheer"
da haka har tayi bacci, ita kuma madina ta fita, da alama madeena ce karama domin mufeeda ta fita shiru shiru da rashin sakewa, ita madina tanada saurin sabo, kyawawa ne sosai suna kama da yayansu amma su farare ne, saɓanin shi chocolate, da ganin gidansu ba sai an faɗa mata ba tasan yaran masu mukami ne....
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
🌸🌸🌸🌸🌸
*ZOBEN WUTA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 2*
~Tafiya yake a cikin motan yana jin kanshi yayi nauyi fiye da yadda yake ji ɗazu, lips na kasa a cikin bakinshi, kamar zai bige mutane akan titin shi kanshi bai san inda yake ba, da kyar ya samu ya isa unguwansu, a kofan tamfatsetsen gidansu ya tsaya, kanshi ya ɗaura akan sitiyarin motar, ji ana cewa "mama" a cikin kunnuwanshi, sa hanu yayi ya toshe kunne yana runtse ido, da kyar ya latsa hon, wani ne ya leko da alama shine me gadi, buɗe get ɗin yayi, shiga yayi da motar, bai karasa ciki ba yayi parking, fitowa yayi har yanzu haunshi a kunnuwanshi yana jin amon sautin kiran sunan mama, da hanu ya yiwa driver alaman ya shigo ciki da motar, har yanzu bai daina layi ba, saide yanzu ba kamar ɗazu bane, tura kofan falon yayi kana ya shiga ciki, faɗiwa yayi a kasa ya kwanta, girgiza kai ya fara jin sautin yana cigaba da yawo a kunnenshi, da kyar ya iya buɗe baki yace "DEEN? DEEN? DEEN?"
sau uku yake kiran sunan kafin daga sama wani ya amsa da "yes ka dawo ne?"
cikin rawan ɗari yace "kazo ka taimakeni deen"
wanda aka kira da deen yana kwance akan gado sanye da singlet da gajeren wando fari kal, yayi kwanciyan rub da ciki yana kallo a laptop nashi, jin abinda ɗan uwanshi ya faɗa ya tashi da sauri ya ture laptop ɗin, saukowa yayi akan makeken kyakkyawan gadon da yake kamar na sarauta, komai na ɗakin fari ne kal kama daga sofa zuwa wardrobe da sauran kayan buƙatu, ɗakin kamar na turawa, kaykkaywan matashi ne sosai yake da kyau, suna tsananin kama da wanda ya shigo ɗin, babu abinda ya bambanta su sai gashin kansu, shi na wajen gashinshi a harhaɗe shi kuma wannan gashinshi a kwance, fitowa yayi yana cewa "meya sameka?"
da sauri yaje ya rikeshi yana ɗagashi yace "meya sameka?"
idanunshi suna rufewa yace "kaine kan bed"
rikeshi yayi suna tafiya yace "sorry"
kan gado ya kaishi ya taimaka mishi ya kwanta, pillow yasa mishi a kashi, taɓa jikinshi yayi yaji da zafi, da sauri yace "temperature ɗinka is high what happened to you ABEED?"
idonshi a rufe yace "wayyo deen ka bani magani zan mutu"
jin kalman mutuwa daya ambata yasa deen rikicewa da sauri ya sauka akan gadon ya fara buɗe drowers ɗin dake ɗakin, paracetamol ya ɗauko, ya ɗauko ruwan gora, da sauri yake yin komai, dawowa yayi ya ɗago kanshi yace "gashi take it"
a hankali ya buɗe ɗan karamin bakinshi, sa mishi yayi tareda ruwan, zubarwa yake shirin yi deen yace "haba abeed so kake kasa twin brother ɗinka a cikin damuwa? meyasa ba zaka sha maganin ba? kanaso nima na fara rashin lafiya ne?"
yana magana ne cikin sanyin murya da alama baida yawan magana sosai, kuma kamar shine babba, sai a lokacin ya buɗe baki ya shanye maganin bayan ya runtse ido, komawa yayi ya kwanta, deen ya rufashi da blanket sannan ya zauna a gefenshi yasa hanu a kanshi gashinshi dake da laushi yake shafawa a hankali har saida yaji ya fara bacci kafin yayi tagumi ya zuba mishi ido
"ko kaɗan bayason abinda zai taɓa mishi twin brother ɗinshi, bayason ganin Abeed cikin rashin lafiya bale yayi maganan magani, sai yaji ya rasa nutsuwanshi har sai ya samu sauki kafin yake dawowa hayyacinshi, kwanciya yayi a gefenshi shima ya rufu da blanket ɗin ya riko hanun abeed yayi shiru jin jikinshi da zafi, laptop ɗinshi ya ɗauko yayi playing film ɗin da yake kallo, ɗaura laptop ɗin yayi a kirjinshi hanunshi ɗaya ya rike dashi ɗayan hanun kuma ya rike hanun abeed, yayi nisa da kallo yaji numfashin Abeed yana yin sama, da sauri ya juyo yana kallanshi, birgima ya fara akan gadon ɗan karamin bakinshi yana rawa, jikinshi ma gaba ɗaya ya fara rawa, atake zazzafan zazzaɓi ya rufeshi, ture laptop yayi gefe ya rungumeshi ganin yana birgima sosai, yace "beed what is this? me kakeyi haka?"
da kyar ya iya cewa "help me deen"
sosai ya kalleshi a hankali yace "I get the sense that you're intimate with someone"
duk da yana cikin ciwo saida ya kalli deen yace "no"
yana mamakin yadda akayi ya gane, yace "beed you are my best friend ba wai kawai kanina ba, kayi s*x"
girgiza kai yayi "no zazzaɓi kawai ya kamani trust me"
yace "i trust you beed but nasan idan kasha giya ba abinda ba zaka iya yi ba"
yace "deen ka bani magani zan mutu"
wayarshi ya ɗauka ya kira numbern Doctor, yace "kazo yanzu please beed ba lafiya"
aje wayan yayi, ya shiga toilet ya ɗauko towel ɗan karami da wani ƙaramin bowl, zama yayi ya yaye blanket ɗin ya jiƙa towel ɗin a ruwan sanyin, shafa mishi ya fara a jiki, ji yayi temperature ya fara zama normal, a haka Doctor ya shigo, ya saba shigowa kai tsaye idan sun kirashi, deen cikin rashin kuzari da jin zafin ganin ɗan uwanshi cikin ciwo yace "please ka duba shi da kyau jikinshi zafi"
Doctor ya fara duba shi, allura yayi mishi, yasan baya son magani shiyasa ya mishi alluran duk magunan da zai bashi, tun a lokacin ya fara bacci, tattara kayan aikin yayi yace "Deen you love your twin brother so much"
yace "ya zama min dole na soshi, tare aka haifemu tare muka tashi tare muke yin komai, Bama rabuwa koda na kwana ɗaya ne, sannan Abeed yana da rauni sosai idan ban kula dashi ba bazan yafewa kaina ba"
Doctor yace "karka damu babu komai yana lafiya kawai zazzaɓi ne"
yace "okay na gode"
tafiya yayi shi kuma ya zauna yayi shiru, tashi yayi yaje kitchen, kitchen ne me kyau me ɗauke da kayan buƙatu, kitchen ɗin kaɗai abin kallo ne, girki ya fara, ya dafa jallof na macaroni da alot of spice, ganye ya yanka da green beans ya zuba a ciki, kamshin girkin ya fara sosai, yasan beed na son macaroni, yafi son natural drink hakan yasa ya haɗa musu soɓo yasa a frij, share kitchen ɗin yayi sannan ya goge ko ina yayi wanke wanke, jin wayar Abeed yana ringing ya fita da sauri ya ɗauka, ganin sunan dake yawo na AMMI da alaman love ya sashi saurin ɗauka
"Hi Ammi"
tace "waye wannan Deen ko Abeed?"
yace "Abeed ne"
shiru tayi tana nazarin ko waye ne a cikinsu, cikin san sanin waye tace "ya meeting ɗin me kace a wajen meeting? kaci kwai?"
da sauri yace "no...no..no banci ba"
dariya tayi tace "wannan Deen ne"
shima cikin dariyanshi me kyau da kewan Ammin ya zauna akan gadon gefen Abeed yace "Ammi kede sai kin ganoni koda yaushe"
tace "kun gama meeting lafiya?"
a hankali yace "lafiya lau ammi ba nine naje ba Abeed ne yaje"
tace "okay bashi wayar inata kiranshi bai ɗauka ba bashi mu gaisa nasan yana jina raini yasa bai ɗauka ba"
shafa kan Abeed yayi a hankali yace "yana bacci"
tace "bacci kuma baida lafiya ne?"
da sauri yace "no lafiyanshi kalau ya gaji ne kawai a wajen aiki"
tayi shiru kana tace "Deen nasan halinka da ɓoye-ɓoye da zurfin ciki, na sanka da rashin magana da rashin faɗan damuwanka, ina fatan ba wani abinda yake faruwa?"
yace "ammi relax ba abinda yake faruwa Beed is fine and I promise to take care of him"
Ammi tace "kaine babba kuma ka ɗau girman Allah maka albarka"
yace "ameen ammi"
tace yaushe "zaku dawo?"
"tomorrow insha Allah"
tace "okay me zan aje muku?"
yace "anything ammi*
tace "okay bye"
yace "love you Ammi"
"love you too"
aje wayan yayi yaci gaba da kallonshi, saida Abeed yayi bacci sosai kafin ya tashi yana murza ido, ji yayi ya warke fayau, ya kalli deen da yake kallo, zame laptop ɗin yayi ya wurga a baya, juyowa deen yayi yace "me hakan? bani laptop ɗina"
yana cire rigan jikinshi da yake warin giya yace "ba zan bayar ba"
ɓata rai yayi yace "ka bani nace"
"bazan bayar ba"
deen yace "dan me?"
yace "dan ubanka"
pillow ya ɗauka ya kai mishi duka, kaucewa yayi ya sauka a gadon bai wuce ko ina ba sai toilet, wanka ya fara saida yayi wanka me kyau kafin ya fito ɗaure da towel a waist nashi, gashin kanshi a jike yake hakan yasa ya kara yin wani irin kyau, faffaɗan kirjinshi kwance da gashi luf-luf, hand dryer ya jona sannan ya fara busar da kanshi, mai ya shafa me kamshi akanshi da fatar jikinshi, riga black marar nauyi yasa da gajeren wando, ta cikin rigan kana iya ganin fatar jikinshi, riga ne me zip amma ya bar zip ɗin a buɗe, hakan ya bayyana kwantaccen gashin dake kirjinshi, cikin natsuwa yake taku har zuwa babban falon gidan, kallon dining yayi, cikin jin yunwa ya nufi dining ɗin ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun masu tsananin kyau kamar na sarauta, abincin ya buɗe yaji wani sanyi a ranshi ya lumshe ido kana ya janyo plate zai fara serving, yaji an warce plate ɗin, yasan Deen ne, baiyi magana ba kuma bai kalleshi ba ya janyo food flask ɗin yasa spoon zai fara ci, ɗaukewa flask ɗin yayi, shiru yayi kamar zaiyi kuka yace "Deen banason haka ka bani abinci naci ina jin yunwa"
yace "saide ka kwace"
tashi yayi a zuciye zai bar wajen ya rike hanunshi, yace "sorry da wasa nake maka dawo kaci"
cikin ɓacin rai yace "no shikenan"
Deen cikin kulawa yace "dan Allah kayi hakuri wasa nake maka"
dawowa yayi ya zauna amma yaki dariya, fuska a haɗe, zuba mishi yayi sannan ya zauna, ganin ya ɓata rai yaji jikinshi yayi sanyi, yace "sorry kaji?"
baiyi magana ba, abincin ya ɗiba ya kai bakinshi, a hankali ya buɗe bakin ya fara ci, ɗauke kai yayi alaman ya koshi, soɓo ya zuba mishi ya kai cup ɗin bakinshi, karɓa yayi yace "zansha da kaina"
yace "am sorry beed banason ganinka cikin ɓacin rai ka sani abin yana damina it hurts"
ganin yadda ya marairaice yana magana kawai ya fara dariya, yace "shikenan ya wuce"
yace "to sha"
sha ya fara a hankali saida ya shanye ya rike hanunshi yace "thank you Deen"
gyaɗa kai yayi, yace "gobe zamu tafi"
yace "yes insha Allah"
yace "Abbi ya kira ka?"
girgiza kai yayi "Ammi ce ta kirani"
yace "okay"
hira suka fara ya fara bashi labarin meeting, har zuwa lokacin da aka gama meeting da abinda suka tattauna akai, da yadda zasu fara shigo da sabbin motoci, shiru yayi lokacin da yace "munsha...."
deen sexy eye's nashi me kama dana turawa ya zuba mishi kana yace "kunsha me?"
shima idanunshi masu tsananin kama dana Deen ɗin ya zuba mishi, yace "munsha ruwa da drinks"
murmushin gefen baki yayi kana yace "kunsha giya dai Beed ba abinda zaka ɓoyemin a kanka a bige ka dawo gidannan kullum ina faɗa stop drinking alcohol kada wata rana ya zame mana matsala a rayuwa, in guje maka sharrin giya zai iya zame maka babban matsala a rayuwarka, zaka iya aikata abinda zai damemu daga baya, zaka iya aikata abinda ba zaka taɓa yafewa kanka ba a gaba, zaka iya yin abinda zai tarwatsa duk wani farin cikin da muke ciki"
muryanshi ya fara rawa, yace "zaka iya aikata abinda zai iya rabani da kai, wanda shine kullum abinda yake bani tsoro idan na tuna da sharrin giya, banason koda wasa mu rabu bale da gaske"
idonshi cike da hawaye yace "beed ina sanka banason ka aikata abinda zai tarwatsa rayuwarka"
share hawaye yayi yace "amma ba komai bazan daina yimika addu'a ba"
jikinshi yayi matukar sanyi, a hankali yace "bayan na tashi daga meeting saina fara tafiya bansan inda nake zuwa ba, amma ina jin kamar ana kiran sunan wata"
da mamaki yace "sunan wata kuma? wacece?"
dafa kanshi yayi yana kokarin tuna abinda ya faru, ji yayi kanshi ya fara ciwo, rufe ido yayi yace "Deen kamar wata tana kuka a cikin kunnena tana kiran wani suna"
yanayinshi ya fara canjawa kanshi yayi nauyi da sauri Deen yace "me yake faruwa?"
yace "kaina"
rikeshi yayi yace "wai meyake faruwa ne?"
rufe ido yayi yace "mama!!!"
deen cikin tsoro yace "mama kuma? wacece mama?"
yace "shine sunan da take kira"
rike kanshi yayi da hanu bibbiyu yace "tana cewa mama"
addu'a Deen ya fara tofa mishi, yace "ko dai aljana ce ta shafe ka?"
ganin yana silalewa kasa ya rungume kanshi a kirjinshi, shafa gashinshi yake yana cigaba da karanta mishi addu'a.
"Janan bakici komai ba kin aje abinci a gaba kinyi tagumi"
a hankali ta ɗago manyan idanunta ta kalli madina wacce tayi kyau cikin riga da wando na pakistan, ta ɗaura kanta da mayafi sannan tasa farin sirrin glass a idonta, takadda ne a hannunta english novel na amina the pampered girl, murmushi tayi mata tace "kinyi kyau"
tace "na gode amma ai ke saide kicewa mutum yayi kyau sabida yaji daɗi duk inda kyau yake ai janan kinje har kin dawo"
murmushi tayi ta sunkuyar da kai, tayi matukar kyau cikin kwana biyu data zauna a gidan, duk wani kulawa suna bata saide bata samun sakewa har yanzu a takure take zama da alama ta saba da taƙura, maheer yana kokarin ya jata a jiki ta sake amma sam bata sake wa, riga ne fited gown madina ta bata sabo wanda bata taɓa sawa ba, baƙi ne rigan da hanunshi a yayyanke, kamar ka sace ta ka gudu, kanta tasa mayafi ɗan karami na rigan, abincin ta fara ci, kaɗan taci tace "na koshi"
madina tace "gaskiya ban yadda ba wannan abincin kice kin koshi?"
tace "Allah na koshi"
"gaskiya sai kinci"
gyaran murya yayi jin suna jayayya, madina ce ta kalleshi yace "tashi kije"
tashi tayi ya zauna kusa da Janan ɗin yana kallonta, taki yadda ta ɗago su haɗa ido, yace "kalleni mana"
a hankali ta kalleshi sannan ta maida kanta kasa, yace "kinason kiji daɗi a rayuwarki?"
gyaɗa kai tayi, yace "to ki manta da baya, ki fuskanci gaba, nasan da ciwo a zuciyarki amma hakan ba zai hana kici abinci ki saki jiki a cikin mutane ba, janan ki godewa Allah daya baki lafiya wasu ma suna neman lafiyan babu, meyasa kikesa kanki cikin damuwa?"
hawaye ne yake bin fuskanta tace "kasan meya sameni a rayuwa kuwa ya maheer?"
girgiza kai yayi "ban sani ba kuma ba zanso na sani na har sai ranan da kikaga zaki iya gayamin"
tace "ya maheer nasha wahala ban taɓa zaton zanyi rai ba, na mutu ya kai sau ishirin, ya maheer bansan me nayi ba"
yace "ba abinda kikayi janan"
abincin ya fara bata, tana kuka tace "zanci da kaina"
girgiza kai yayi "buɗe baki"
tana hawaye tana cin abincin har saida yaga ta koshi sannan yace "good girl cinye wannan cokali ɗayan"
tace "na koshi"
yace "no cinye"
momy ce ta tsaya tana kallonshi da mugun mamaki a fuskanta, karasowa tayi inda suke tace "maheer khairat tana kiranka baka ɗaka ko meyasa?"
da sauri janan tace "ina wuni momy"
tace "lafiya"
sannan ta kalli maheer tace "meyasa baka ɗauka?"
yace "sorry momy zan kirata"
tafiya tayi tana cike da mamaki, janan tace "wacece khairat?"
yace "wacce zan aura"
murmushi tayi tace "kenan ka kusa aure?"
gyaɗa kai yayi
tace "kenan zaka barni Idan kayi aure ba zaka rinƙa zuwa muna hira kana koyamin karatu ɗin ba?"
yace "zan saki a school nasu madeena"
tace "to na gode naga hoton matarka"
buɗe wayarshi yayi ya nuna mata hoton khairat
"masha Allah" ta faɗa tana kara kallon hoton, khairat akwai kyau da alama kuma akwai class, wani irin gayu taci a cikin hoton ba kaɗan ba, ta kalleshi shima yana kallonta tace "ya maheer amma budurwarka kyakkyawa kuma ƴar gayu ce sosai kuma tanada ilimi ko?"
yadda take tambayanshi kai kace ƴar shekara uku ce, murmushi kawai yayi mata, tace "ko yaya?"
yace "eh"
tana murmushi sosai tace "nima inaso na zama me ilimi inaso na iya turanci zaka koyamin?"
yace "zan koya miki tun daga yau ma idan kina so"
tace "yeeee na gode yaya"
matsowa tayi kusa dashi sosai tace "ga takaddan madina ka fara koyamin"
ganin yana kallonta baima ji abinda tace ba, tayi tafi kusa da face nashi tace "hello"
firgigit yayi yace "kinada kyau"
tace "kaima haka"
murmushi yayi yace "kin iya rubutu?"
girgiza kai tayi ta turo ɗan karamin bakinta cikin shagwaɓan da alama ta saba da hakan tace "ban iya ba dama farhat ce take koyamin amma mun rabu bama tare yanzu"
tunda ta fara magana ya zuba mata ido har zuwa lokacin da tayi shiru, da alama abin yana cin ranta domin kuwa hawaye take yi, yace "ina mama?"
shiru tayi
*Jiddah Ce...✍️*
08144818849
🌸🌸🌸🌸🌸
*ZOBEN WUTA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 3*
~Da alama bataso anayi mata maganan, kawar da zancen yayi yace "zan saki a school ranan monday zanyi miki register, tareda su madeena da mufeeda zaku rinƙa tafiya, cikin farin ciki tace "na gode sosai ya maheer Allah ya saka maka da Alkhairi"
a hankali yace "ameen"
takaddan dake hanunta yace "kin iya rubutu?"
girgiza kai tayi "ban iya ba amma inaso na koya"
yace "to matso ki fara daga ABCD"
matsowa tayi kusa sosai, yace "rubuta A"
kasa rubutawa tayi, ya rike hanunta ya rubuta A daga nan ya fara rubuta mata yana faɗa mata sunan duk abinda ya rubuta, farin ciki ƙarara akan fuskanta sai wani irin smiling take tana jin daɗi, da alama tana son karatu bata samu dama bane kawai, yace "yawwa anan zamu tsaya sai gobe kuma muci gaba wannan zakije kiyi ta maimaitawa a ɗaki kinji?"
tashi tayi ta daka tsalle sannan tace "yeeee yau zanyi karatu"
tana tsalle tana tafiya harta shiga ɗaki bai daina kallonta ba, mamaki ne sosai akan fuskanshi da alama akwai yaranta da tsananin taƙura a tare da ita, tana shiga ta zauna a kasa ta fara maimaita karatun, madina dake karatu tace "to janan wannan duk karatu ne?"
jijjiga kai tayi tace "eh nima zan iya rubutu da karatu"
tace "umm amma da alama kinason karatu, ko primary baki yi kenan dan naga daga ABCD kike farawa"
shiru tayi bata amsa ba, itama bata taƙura saita bata amsan ba, momy ce ta fito daga kitchen taji duk abinda suke faɗa har lokacin da janan ta shiga ɗaki bata daina kallon maheer ba, zama tayi kusa dashi tace "maheer inaso muyi wata magana da kai"
ya nutsu sosai kanshi kasa yace "ina jinki momy"
ta rasa ta inda zata fara, shiru tayi, sun jima a haka sannan tace "maheer bansan wannan yarinyar wacece ba, kuma bansan daga ina take ba, amma naji ta kwanta min arai, haka kawai naji tana bani tausayi domin kuwa alamu sun nuna ta taso cikin wahala da firgici, to amma wani hanzari ba gudu ba, shin kasan dalilin barinta gidansu? kuma kasan cewa zaka auri khairat? kada fa garin taimako kasa kanka cikin matsala ba fata nake maka ba"
a hankali yace "momy ban san dalilin ba, amma koma menene an zalinci wannan yarinyar, da kinsan halin dana ganta a ciki ba zaki tambayeta daga ina take ba, kuma da alama iyayenta basa raye"
momy tace "ba cewa kayi ka bigeta da mota ba?"
ya manta ne yayi wannan maganan ya manta ya ɓoyewa momy, yace "haka ne bigeta nayi"
momy tace "sau da yawa kyawawan mata babu Alkhairi a zama dasu, kyawunsu yakan iya zama jarabtansu, ina fatam Allah ya baka ladan taimakonta da kayi, sannan abbanku yace a sata a school su rinƙa tafiya tareda su madeena kuma ya tambayeni ya magananka da khairat?"
yace "zanje gidansu anjima"
tace "to Allah ya bada Sa'a"
"Ameen"
washe gari yayi shiri me kyau cikin tsadadden yadi sky blue, yayi matukar kyau sosai yana kamshi me daɗi, hanunshi rike da car key da wayarshi, tun daga sama ta zuba mishi ido harya sauko, waya yake har yanzu baisan tana kallonshi ba, smiling take yi wanda yake kara mata kyau, hijab ne a jikinta baƙi tasa hulan net, ba karamin kyau tayi ba kamar ka sace ka gudu, zaune take akan dining kusa dasu mufeeda suna cin abinci, tareda su momy, kwana biyu da tayi a gidan tayi kyau sosai ta kara yin haske, kuma Alhmdllh ta fara koyon abubuwa dayawa na rayuwa, mufeeda ce ta taɓa madeena