Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
zuciyanta yana juyawa, taji amai yana zuwa mata, da gudu ta tashi a wajen taje toilet ta fara sheƙa amai, da sauri ya tashi ya bita, harta gama aman ya bata ruwa ta wanke baki, yace "meyasa kike amai? bakida lafiya ne?" tace "lafiya ta kalau kawai naji bana son jin warin kifin" yace "sorry ban san haka ba da bazan kawo ba" tace "ba komai" koda ta dawo jikinta so weak ta kuma kwanciya kawai, yasa madina da mufida suka tafi ɗaki da kifin, momy tace "sannu bari na baki magani" girgiza kai tayi "barshi momy nasha magani acan" sannu momy take yimata. haka sukaci gaba da rayuwa kullum tare da maheer suke fita saide sun daina dafa kifi a gidan, yau da safe tana kwance a ɗaki tana karanta hausa novel data siya a kasuwa me suna AMANNA yau weekend ne babu aiki kuma babu school hakan yasa ta samu lokaci sosai, maheer ne ya kirata ta aje takaddan ta fito, ya zuba mata ido harta karaso inda yake ta zauna kusa dashi tace "ya maheer ina zakaje haka kayi kyau kamar ango" a hankali yace "kika sani ko ni ango ne yau?" dariya tayi sosai harda rike ciki tace "wace zata aureka? kana nan kamar mace abu kiris kayi kuka?" yace "ke mana ko ba zaki aureni ba" a hankali tace "me zai hana na aureka? duk wani abinda ake bukata a wajen namiji kana dashi, sannan kanada kula mutum, kai ɗin na daban ne ya maheer" zoben karamin yatsanta ya ciro yace "muga hanunki" mika mishi tayi yasa mata a ɗan yatsanta, murmushi tayi tace "yayi kyau sosai" yace "kamar yadda kike da kyau" tace "kaima ai kana da kyau" shiru yayi kamar akwai abinda yake damunshi, tace "ya maheer menene?" a hankali yace "ina sanki janan" jikinta yayi sanyi, ta sunnar da kai kasa, yace "kin taɓa soyayya?" girgiza kai tayi yace "kin taɓa jin wani a zuciyarki?" gyaɗa kai tayi a hankali, yace "wanene?" nunashi tayi da yatsa tace "kaine" a hankali yace "janan ina jinki a zuciyata a koda yaushe, ina jin kamar na haɗiyeki ko zan huta da abinda nake ji, janan will you marry me?" shiru tayi ta kura mishi manyan idanunta, ya sunkuyar da kai tace "ya maheer ina zakaje?" yace "an kirani ne a inda nake neman aiki yau sunce naje da takadduna zan samu aiki, kinga idan na samu aiki saina aureki mu zauna tare, zan baki duk wani farin ciki na rayuwa, zan kula dake sosai, zaki kara kyau akan kyawun da kike dashi, zanyi ta kallonki kullum har karshen nimfashina" karamar wayarshi ta fara ringing, tace "ka ɗauka ana kiranka" ɗauka yayi yace "ina zuwa yanzu" katse wayan yayi sannan ya tashi yace "zan tafi amma kimin alkawari zaki jirani duk daɗewan da zanyi?" tace "nayi alkwari" yace "koda ko daɗewan shekara da shekaru ne kimin alkawari zaki jirani" tace "zan jira ka" yace "bye" hanu ta ɗaga mishi, yace "ba rakiya ne?" tashi tayi ta raka shi, a bakin kofa ya tsaya yace "tsaya anan kada ki fita a ganki ina kishi sosai" murmushi tayi kana ta dukar da kai kasa, haka kawai taji yau tana jin kunyarshi sosai, yace "i love" cikin sanyin murya tace "thanks" mashin ɗin da yake jiranshi a kofa wanda masu aikin suka tura mishi ya hau, tana kallonshi har suka tafi sannan ta shiga gida. *Jiddah Ce....✍🏻* 08144818849 🌸🌸🌸🌸🌸 *ZOBEN WUTA* 🌸🌸🌸🌸🌸 By _Jiddah S Mapi_ *Chapter 8* ~Komawa ciki tayi ta fara girki dan wani irin yunwa take ji, ta jima tana girki sannan ta zuba a plate ta fara ci, abin mamaki saida ta cinye abincin duka dana su momy, a haka ma tana jin bata koshi ba, duba kitchen ɗin tayi ta dafa kai tace "Innalillahi babu komai kuma na cinye abincin?" tsaki taja kaɗan tace "ya zama dole naje na nema musu abinda zasuci" fita tayi taje ɗaki tasa hijabi, lekasu tayi taga duk sunyi bacci, murmushi tayi taje wajen momy ta shafa face nata tace "i love you so much momy" tashi tayi ta fita madeena da mufeeda suma bacci suke har yanzu, tafiya ta fara a cikin unguwan tana kallon bishiyoyi da suke a dashe, yanayin unguwan yayi mata kyau, kuɗin dake hanunta dubu biyu ne wanda ta dawo dashi daga aiki jiya, kasuwa taje ta siyo kayan abincin da zata dafa musu, neman salat ta fara domin ya kara yawan abincin, bata samu salat ba hakan yasa ta tafi wani waje da takeda tabbacin ba za'a rasa ba, sukace masu salat basu fito ba saide ta zauna ta ɗan jirasu zasu dawo, zama tayi tana jin gabanta yana faɗuwa "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" kalman da take maimaitawa kenan a bakinta, ji tayi bugun zuciyarta da faɗuwan gaba ya kara tsananta, da har masu salat suka fito, siya tayi sannan ta rike ledojin dana shinkafa dana wake saina salat, kuɗin hanunta ya kare duka hakan yasa take takawa da kafa, ga zafin rana yana haska mata fuska, sai sunkuyar da kai take domin batason zafi ko kaɗan, daga nesa ta bayanta taji ana kiran sunanta "janan janan?" juyowa tayi dan ta ɗago muryan, murmushi akan fuskanta da zufan zafin ranan ya jiƙa, ta kalli yarinyar dake zuwa, ƴar class nasu ne a school sunanta Eeshat, rungumeta tayi tace "janan ya kike? kwana biyu meyasa baki zuwa school? naje gidanku ance kun tashi kuma abbanku ya rasu, ya hakuri?" a hankali tace "Alhmdllh Eeshat school ɗin ne muna son canjawa sabida yanayin rayuwa, ina lafiya kalau ya karatu?" tace "Alhmdllh janan yanzu ina kuka koma?" kwatance tayi mata domin akwai nisa sosai tsakaninsu, tace "idan kinbi ta nan kikai senta zakiga gida da baƙin kofa to anan muke" tace "to janan naga kamar kina sauri sai nazo" kara rungumeta janan tayi tace "na gode Eeshat sai kinzo" rabuwa sukayi taci gaba da tafiya da sauri, ta jima a hanya, tun a nesa ta fara hango mutane a kofar gidansu ga maza suna alwala, wani irin jiri taji yana shirin kadata, da kyar taja kafa tana tafiya, hankalinta be gama tashi ba saida taga an ɗaga likafani an shiga dashi ciki, bata san time ɗin data zubar da ledan hanunta ba, da wani irin gudu ta shiga gidan, Momy, mufeeda, madina duk suna tsaye a cikin gidan ko kuka basu iyayi, da sauri tace "waya mutu?" wani dake gefe yace "baiwar Allah ki nutsu mana maheer daya mutu ai lokacinshi ne yayi, muma jiran lokacin mu kawai muke" zama tayi kasa tana kallonsu momy, bakinta ya kasa furta komai, idanunta a waje sun kara girma, gani tayi an fito da gawan an ɗaura akan makara akace momy suzo suyi mishi addu'a, da rarrafe ta isa inda suke tasa hanu zata yaye likafanin daya rufe mishi fuska, ji tayi an rike hanunta da karfi, a tsorace ta ɗago tana kallon waya rike mata hanu, madina ta gani tana huci, sai yanzu ta samu tace "madina meyasa zaki hanani kallon fuskan ya maheer ɗina?" wani irin hankaɗata tayi zuwa gefe, faɗuwa tayi, madina tace "janan is this your father's house?" girgiza kai tayi "no" da yatsa ta nuna mata kofa tace "then stay away" tashi tayi tace "madina kinsan me kike faɗa kuwa?" ture ta tayi taje zata buɗe gawan wannan karon da mari mufeedah ta ɗauketa dashi, dafa kunci tayi a firgice take kallonsu, cikin kuka tace "koma me nayi ku bari naga fuskan ya maheer" mufeeda tace "idan kallon fuskan ya maheer ne zaisa ki shiga aljanna Allah yasa ke ƴar wuta ce tun a duniya janan" bata jisu ba taje gaban momy ta zube akan kafanta tace "momy na yadda kumin hukunci koda banyi komai ba, amma dan girman Allah ku barni naga gawan ya maheer" juya baya momy tayi tace "tashi ki fita janan" cikin ihu tace "babu inda zanje ina nan tare daku, ko zaku kasheni sai naga gawan dan inada tabbacin ya maheer be mutu ba, yana raye domin lafiya kalau ya fita ya bar gidannan" zata buɗe taji sun riketa, iska ne ya ɗan yaye likafanin nan take fuskanshi ya bayyana goshinshi da duk jikin likafanin ya ɓaci da jini, zata rungumeshi madeena ta ɗauketa da mari mufeeda ta riketa suka fara janta zuwa waje, wani dattijo yace "haba bayin Allah me tayi muku haka kuke mata haka?" madina tace "itace ta kashe mana yaya, har ya mutu yana ambaton sunanta, bai mutu da sunan kowa ba sai janan janan janan, tunda ta shigo rayuwarmu komai ya ɓaci, ta faɗa da bakinta batada ƙaddara me kyau gashi ta shafa mana muguwa, wurgi sukayi da ita a kasa, faɗuwa tayi akan wani babban dutse ihu tayi jin cikinta ya wani murɗa mata, tana kwance a wajen cikin ruɗu har aka fito da gawan ya maheer aka tafi dashi, batada niyan tashi tana kwance a kasa har hadari ya haɗu aka fara tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, farkon haɗuwanta da maheer a cikin ruwan sama ne, haka kuma rabuwansu a cikin ruwan sama, hawaye masu ɗumi suka fara bin ruwan fuskanta, ruwa akayi sosai jikinta ya jike ga sanyi daya sauko kamar kankara, da kyar taja kafanta ta fara tafiya tana ɗingishi sosai, a hankali take tafiya tana ciza leɓe sanyi da zafin buguwan da tayi take ji, rashin sanin inda zataje yasa ta zauna a karkashin rumfan wani me shayi, jingina kanta tayi akan kujera tayi shiru tana kallon sama, da zata samu tayi kuka watakila wuta ya dena ruruwa a cikin zuciyarta, amma kukan yaki zuwa "JAAN" sunan da taji an kirata dashi kenan a cikin kunnenta, tasan duk duniya mutum ɗaya ne yake kiranta da wannan sunan ba kowa bane face ya nabeel, bata juyo ba sai ɓarin da jikinta yake, bakinshi a kunnenta cikin sassanyan murya tace "jaan mu tafi gida tunda masoyin naki ya mutu" hanunta ya rike ya fara janta, ɗayan hanun tasa a kasa ta fara laluben dutse, Allah yasa ta samu wani katon dutse, ɗauka tayi ta kwala mishi akai, rike kai yayi cikin jin zafi, idanunshi me tsananin kama da nata za waro ganin jini na bin hanunshi, kara ɗaukan wani dutsen tayi ta rotsa mishi aka, jini sosai yake zuba ya kwanta a kasa, cikin kuka tace "meyasa ka kashe shi? me yasa ka kashe ya maheer? nabeel Allah ya isa tsakanina da kai, nabeel saina kashe ka kaima" ta karasa maganan tana gunjin kuka, da kyar ya tashi zai riketa ta ɗau katako akan table ɗin me shayin, ƙwala mishi tayi saida ya faɗi ƙasa, ganin zai tashi ta kwasa da mugun gudu, binta ya fara bata tsaya ba kuma bata juyo ba, tuntuɓe tayi ta fara tangal tangal zata faɗi kasa, rike cikinta tayi jin yayi wani irin juyawa, wani gida ta gani daga nesa, jin cikinta yana kara ciwo kawai ta faɗa gidan, tana shiga ta faɗi kasa ta fara birgima, mata ne dayawa da kuma maza a cikin gidan wasu na caca wasu na shan taba, ɗakuna ne a jere, daga yanayin shigan matan zaka gane gidan karuwai ne, cikin azaba ta saki ihu "wayyo cikina ku taimakeni" taɓe baki matan sukayi suna kallonta, ganin wannan kyakkyawar ta shigo sun san zata kwace musu kasuwa, cikin birgima tana haƙi tace "ku taimakeni cikina" wata a cikinsu wacce take rike da abin cacan tazo ta durkusa tace "sannu meya samu cikin naki?" kyakkyawa ce domin tafi duk ƴammatan wajen kyau, da kyar tace "ciwo yake min" taimaka tayi ta tashi, ɗakin da yake mallakinta ne ta kaita, katifa ne shinfiɗe a tsakar ɗakin sai kayanta na sawa masu yawa cike fam da akwati, gefe guda tulin takalma da jakunkuna ne, akan katifan ta kwantar da ita, ganin kayan jikinta a jike sosai gashi tana rawan sanyi yasa ta taimaka mata ta cire mata kayan tasa mata dogon riga me ɗan nauyi, da taimakonta ta kara komawa ta kwanta, cikin raunin murya da azaba tace "zan samu ruwan zafi?" yarinyar tace "eh zaki samu me zakiyi dashi?" a hankali tace "sha zanyi" tashi tayi ta ɗibo mata ruwan zafi a flask, karɓa tayi tasha, aje cup ɗin tayi ta mike flat akan katifan ta fara birgima tana cewa "cikina" yarinyar ta tashi da sauri ta ɗau waya, ana ɗauka tace "MINAT ke magana kazo yanzu akwai marar lafiya a room ɗina please karka ɓata lokaci she is in pain" aje wayan tayi tana yi mata sannu, da haka har aka kara kiran wayar tana ɗauka tace "come in" shigowa yayi sanye da kayan likita a jikinshi, yace "wannan ce ba lafiya?" gyaɗa kai tayi, yace "what happened to her?" tace "I don't know but naga tana tasa hanu a ciki may be ciwon ciki ne" zama yayi a bakin katifan ya fara duba janan wacce ta fita a hayyacinta, ya jima yana dubata kafin yace "kamar tana cikin firgici wanda ba'a son masu ciki suna shiga, be kamata tanada ciki tana shiga irin wannan halin ba, musamman da cikin ya kai wata biyar" tashi tayi a razane tana kallon Dr, yace "madam ki daina irin wannan razanan abin cikinki ze iya samun matsala" magani ya bata yace "wannan na masu ciki ne ki rinƙa sha safe da yamma, ciwon cikin kuma is normal hakan yakan iya faruwa, amma saikin canja yanayin abincin da kikeci daso samune ki samu ganye dasu wake da sauran kayan abinci masu gina jiki kina ci, hakan zai karawa baby lafiya" har ya fita a ɗakin minat ta sallameshi da kuɗi bata ce komai ba, hanu ta ɗaura akan cikinta cikin rawan murya tace "CIKI?" sai yanzu abinda ya faru a ranan da ya maheer ya taimaketa ya fara dawo mata sabo, a haukace tace "wanene wannan? waye wannan da yamin fyaɗe ya gudu? ya Allah wannan wani irin ƙaddara ne? ya Allah ka ɗauki raina yanzu badan halina ba, Allah kada kasa naga wannan ɗan da zan haifa wanda bansan ta inda zan fara nemo ubanshi ba, ko kamannin ubanshi ban sani ba, ko muryanshi ba zan iya ganewa ba, me yake faruwa dani ne?" kuka takeyi sosai, minat ce ta shigo ta tarar da ita tana kuka, a hankali ta zauna kusa da ita tace "kukan me kike haka kamar baki san kinada ciki ba? a yadda na ganki nasan kinada ciki sabida cikinki ya girma, wannan kukan na me?" hanun minat ta rike cikin firgicin da take ciki tace "dan girman Allah kimin wani alfarma guda ɗaya" gyaɗa kai tayi "ina jinki na me?" tace "ki taimaka ki sake kiran Dr ya zubar da cikin nan" "subhanallah" ita kanta tayi mamakin kalman daya fito daga bakin minat ɗin, tace "kinsan me kike faɗa kuwa? kin san hukuncin wanda ya zubar da ciki a wajen Allah? to idan baki sani ba, duk wanda ya zubar da ciki yayi kisa ne, sannan Allah yace wannafsi binnafsi, duk wanda yayi kisa shima a kasheshi, sannan wannan yaron da kikeso ki zubar dashi kikasan dame zai zo duniya? ki kasan mutane nawa zai taimaka? kinsan ko zai zama babban malami ya bawa wasu ilimi? kika sani ko shine zai zamo sanadiyyan farin cikin ki? gaskiya banson ki kara wannan maganan" jingina tayi da jikin bango tayi shiru hawaye yana wanke mata fuska, maganganun minat sunyi tasiri a ranta, cikin tausayin kanta tace "to ai banma san wanene mahaifinshi ba" minat tace "zunubi biyu kikeso ki aikata kenan gana zina, wanda har zaki kasa tantance wanene mahaifin ɗanki ga kuma na kisa, kina ganin Allah ze barki?" a hankali ta girgiza kai, tasan koda tayi mata bayani tace fyaɗe akayi mata ba zata yadda ba, s ranan haka ta wuni ta kuma kwana cikin kuka, gashi taki cin komai har garin Allah ya waye tana cikin kuka da yunwa. minat shiri tayi cikin ɗamammun kaya ta saki gashinta zuwa bayanta sannan tasa takalmi me tsawo ta ɗau jaka tana tauna cingum tace "idan kin gama kukan naki akwai abinci a cikin wancan flask ɗin kici wanda zaki iya sauran ki fita kiba almajiri, ni zan fita may be sai gobe zan dawo, idan ba zaki iya cin abincin ba ga kayan shayi saiki sha tea" kanta haɗe da gwiwa tayi shiru, ɗago jajayen idanunta tayi wanda suka kumbura sosai fuskanta ya koma jajur tsaban kuka, tace "nima inaso na biki, ki bani kaya irin naki zansa, inaso na fara zina" "Astaghfirullah, baiwar Allah zina kikeso ki fara? amma bakisan hukuncin mazinaci ba ko? to idan baki sani ba Allah yace (wala takribuzzina) kada ku kusanci zina, bece kada ayi bafa yace kada ma a kusanta, sannan wannan shigan da nayi kinsan hukuncin masu irin wannan shigan? Allah yace idan anga masu shiga kasiyatun ariyatun a tsine musu, kuma manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace mafi yawan ƴan wuta mata ne, yace yaga ƴan wuta kuma yaga wasu mutane a tare dasu akwai bulalai kamar kunnuwan shanaye suna dukan mutane dashi da waɗansu mata da tufafinsu amma tsiraru ne kawunansu kamar tozon raƙumi, yace ba zasu shiga aljanna ba kuma ba zasuji kamshinta ba" juya baya tayi tace "wannan abinda yake kaina shine abinda manzon Allah s.a.w yace kamar tozon raƙumi, me zai miki daɗi idan kikayi abinda manzon Allah ya hana? babu komai a zina sai halaka, idan kinyi a baya ki tuba ki rinƙa istighfari ki haifi ɗanki ki kula dashi ba wai ki kara sa kanki ba, idan abinci kikeso ni nayi alkawarin baki kowane kala kikeso, idan kuma sutura ne shima zan baki duk wanda kikeso kisa" juyawa tayi zata fita janan tace "to kema bada kuɗin zinan kike siya ba?" murmushi tayi me kyau wanda ya kara kyau akan kyawun da take dashi, tazo ta zauna a gefenta tace "kinaso kema ki fara cin kuɗin zina ne? to bari na gaya miki babban illan cin kuɗin zina, akwai wata rana manzon Allah s.a.w yace yaga wani mutum da jikinshi da gizo gizo da kura, ma'ana mutumin tsoho ne kuma jikinshi da datti sosai, yace mutumin ya ɗaga hanu sama yanata roko amma Allah yaki amsawa, koda ya tambaya meyasa ba'a amsawa wannan addu'arshi? sai Allah yace shi wannan mutumin da yaketa roko mukaki amsa mishi addu'a sabida abincinshi haramun ne, abin shanshi haramun ne, guzurinshi haramun ne ma'ana ya gina jikinshi da haram, yace ta yaya zamu amsa mishi? ba zamu amsa addu'an wanda ya gina jikinshi da haram ba, to kinga shi zina kuɗin haram zai kawo maka shi kuma cin kuɗin haram yana hana Allah ya amsa addu'a" tashi tayi tace "zanyi late ana jirana a hotel" janan tace "minat zanso ki zama kanwata" murmushi tayi tace "ya sunanki?" tace "sunana janan" buɗe kofa tayi ta fita ba tareda ta bata amsa ba, kallon ɗakin tayi abin mamaki taga jakan da tasa kur'ani a gefe ta adana ta yadda babu abinda zai taɓa, a hankali ta tashi daga zaunen da take, hanunta akan cikinta tace "ba zan cutar da kai ba, domin bakasan abinda ya faru ba, amma inaso ka yafemin kafin kazo duniya, ka haɗu da uwa me mummunan ƙaddara kaima hakan ya shafeka" abincin ta ɗauka zata fara ci ta tuna da ya maheer, turewa tayi ta kifa kanta a jikin pillow ta fara sabon kuka. haka taci gaba da zama a gidan karuwai bata taɓa leka koda kofa ba, minat kuma tana kula da ita sosai domin babu abinda bata samu, duk wani abinda me ciki take buƙata minat tana bata, a yanzu cikin ya girma domin ta kai wata tara harma da sati ɗaya, saide cikin ya girma sosai, kamar kullum yauma zaune take tayi tagumi a tsakar gidan tana kallon abinda yake faruwa, kama daga kan matan da suke shigowa da kuma manya manyan mutane da suke shigowa suna ɗaukan yara ƙanana suna tafiya dasu sai kuma dare zasu dawo dawo wani ma sai sun kwana su dawo da safe, dogon riga me faɗi ne a jikinta kasancewar cikin yayi girma sosai ta yadda da kyar take tafiya, wata fitsararriya wacce tayi suna sosai a gidan tazo wucewa, tayi kyau cikin fited gown da glass ɗin data sa baƙi a idonta, dawowa tayi bayan ta wuce janan tace "naji kamar kinyi tsaki" janan ta girgiza kai tace "banyi tsaki ba wallahi" tace "dama kinyi da saina koya miki hankali dake da wannan cikin shegen da kike fama dashi, gaki da ruwan salihai amma kinje kinyi ciki tsaban barikanci" shiru tayi a lokacin minat ta shigo, tace "meke faruwa unty janan?" hanu ta mika mata tana cizan baki tace "ɗagani muje ciki ba komai" tace "karya ne akwai komai wannan marar kunyan Billy nasan halinta tsaf" billy tace "sai me? me zaki iya min?" mari ta ɗauketa dashi, ganin haka ta cire glass ɗinta ta wurgar, dambe suka fara a cikin gidan babu me niyan rabasu duk ihun da janan take yi tana kiran sunan minat taki jinta, saima kara kaimi take wajen dukan yarinyar kamar ita ta kawota duniya, janan da rarrafe taje wajensu ta fara rike minat, a wahalce tace "kanwata ki kyaleta haka ya isa kinji?" janyewa tayi ganin Janan tana kuka tace "na barki ne sabida ita wallahi badan haka ba yau sede koni ko kuma ke" yarinyar ta ɗaga waya tayi kira, nan take wani mashayi ya shigo gidan yace "wace ƴar iskan ce ta taɓaki?" nuna minat tayi tace "gata nan" cire mayafi minat tayi ta ɗaura a waist sannan ta ɗauko wani kwalba dake gefe "tace taɓani" ganin zaizo ta fasa kwalban ta nunashi dashi tace "wallahi saina kashe ka kana taɓani" janan ta fara jin jiri yana ɗibanta, tace "minat kyalesu mu tafi kinji?" yaron yace "ki aje kwalban idan kinaji kinada karfi" aje kwalban tayi tace "na aje kaima idan ka haifu kazo" zuwa yayi cikin rashin tsoro minat ta rikeshi ta fara dukanshi, shima dukanta yake bata yadda ta barshi ya daketa ba, fakan idonta yayi ya ɗau kwalban zai caka mata, janan dake rike da waist tana jin azaban saran da bayanta yake mata, ganin zai kashe minat ta bayanta tasa kafa ya faɗi ƙasa rub da ciki akan kwalban, nan take jini ya fara tsiyaya daga cikinshi zuwa kasan simintin dake gidan, manyan idanunta da suka gaji da ganin tashin hankali ta waro, ba ita kaɗai ba har minat da billy da sauran mutanen gidan sun waro ido tareda buɗe baki, hanu ta ɗaura a kanta ta fasa ihu "na shiga uku nayi kisa" kafin kace kwabo ya fara shure-shure a wajen, atake idanunshi suka kafe bai kara motsi ba, minat tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" billy ta lallaɓa ta ɗau mayafi ta fita a guje tace "saina kira police zaki kafe rayuwarki da wannan ɗan shege da zaki haifa a prison" cikin tashin hankalin da yake nema yayi ajalinta da ciwon da takeji daga kafafunta zuwa waist nata, ta riko hanun minat tace "ki taimaka min, ba zanso nasa rayuwan ɗana a prison ba, na yadda ni na shiga amma banda abinda zan haifa, bazan taɓa yafewa kaina ba idan na haifeshi a poison" minat ta kalli gawan dake kwance a gabansu sannan ta kalli agogon hanunta karfe tara na dare yayi, shiga ɗaki tayi ta ɗaga katifan ta ciro I'd card dasu abin buƙata, kuɗinta ya kare duka saura kaɗan kawai ta kwashe kaɗan ɗin ta fito, hanu ta mikawa janan tace "mu gudu unty janan" itama hanu ta mika mata saide ta kasa tashi dan wani irin azaba take ji a cikinta, tace "bazan iya ba minat" durkusawa tayi tace "kin yadda ki haifi ɗanki a prison? kin yadda kiyi life in prison? shin gama abinda kikeso ne a duniya?" girgiza kai tayi tace "na gama komai amma saura abu ɗaya" tace "menene?" cikin dauriya tace "ɗaukan fansa" minat cikin son bata karfin gwiwa ta mika mata hanu tace "idan har kinaso ki ɗau fansa nayi miki alkawari zan tayaki ɗaukan koma wani irin fansa ne, ki zama uwa wa ɗa ko ƴar dake cikinki, ki zama jaruma sannan duk abinda akayi miki ki rama" jijjiga kai tayi cikin kwarin gwiwa tace "zan fara da neman duk inda wanda yamin fyaɗe yake, daga nan saina fara da ya nabeel" tace "idan kin yadda zaki iya tashi ki daure muje" tashi tayi hanunta a cikin na minat suka fita daga gidan, a daidai lokacin motan police ya tsaya a kofar gidan, waro manyan idanunta tayi ta kalli minat wacce itama a cikin tashin hankali take, tace "ya zamuyi?" minat tace "kin shiryawa gudu?" jijjiga kai tayi, yau kawai taji tanason yin rayuwa me tsawo kodan ta rama duk wani abinda akayi mata, yau kawai taji ba zata iya mutuwa bata ɗau fansan ran maheer ba, sannan ba zata iya mutuwa bata nemi mahaifin

Chapter 7 of 9