"saida safe"
bai amsa mata ba, tayi shiru a bayan momy, momy taji son yarinyar ya kara shiga ranta, tana rungume da ita har bacci ya ɗauke ta.
ɗakinshi ya koma ya kwanta, tunani ya fara saide duk tunanin akan janan ne, duk yadda yaso ya kawar da tunaninta ya kasa, da kyar ya samu bacci ya ɗaukeshi, a cikin baccin ma mafarkinta yake.
washe gari weekend ne, dama ranan weekend yana kaisu shopping, yadda ya fito bai shirya ba kawai jallabiya a jikinshi momy tace "meya faru bakayi bacci bane?"
yace "nayi amma ba sosai ba inaso idan nayi breakfast na koma nayi kaɗan, kunyi waya da Abba?"
tace "wallahi munyi waya amma yana sauri zasu shiga aiki"
yace "okay Allah yasa ya dawo gobe"
tace "insha Allah gobe ɗin nema"
zama yayi ya zuba tea me zafi, lemon tsami ya matsa a ciki dayawa momy ta kalleshi bataso tana yawan mishi tambaya hakan yasa tayi shiru, madina ce ta kasa yin shiru tace "yaya kaida baka son lemon tsami yau kaine da zubawa dayawa a tea?"
lumshe ido yayi a wahalce yace "haka naga dama yau ko zaki hanani sha?"
tsit tayi, janan tayi shiru tana shan shayi, kallonta yayi suna haɗa ido ta sakar mishi murmushin data saba, murtuƙe fuska yayi yace "baki iya gaisuwa bane?"
da sauri tace "laa yaya good morning"
bai amsa ba yaci gaba da shan tea, saida ya shanye tas ya tashi yayi mika yace "momy zan koma na kwanta su shirya kafin 11 zanzo na kaisu shopping"
janan tace "hadda ni?"
gyaɗa mata kai yayi, cikin jin daɗi tace "na gode"
komawa yayi ya kamata, tunda yasha shayin yaji sauƙin abinda yake damumshi, bacci me daɗi ya dauke shi, shine bai tashi ba sai karfe sha ɗaya da rabi, da sauri ya shiga yayi wanka yasa kananan kaya sabida bayason taƙura, yayi kyau sosai yana zuba kamshi ya fito, tunda taji kamshin turarenshi ta ɗago kai tana kallon inda tasan zai fito, a ranshi yace "masha Allah"
kyau tayi sosai cikin bakin dress ɗin da momy ta zaɓa mata, tashi tayi momy tana gyara mata zip ɗin rigan, tace "momy thank you"
momy tace "kinyi kyau sosai ƴata"
rigan yana jan kasa, daga sama kuma kitson da tayi mata ta kame mata sannan tasa mayafin ta ɗan ja gaban ta yadda kitson zai bayyana, kwalliya tayi mata me kyau tasa takalmi me tsayi kaɗan sannan ta bata jaka, turare ta fesa mata me kamshi, momy tana kallon maheer wanda ya kasa ɗauke idonshi akan janan, madeena da mufeeda sunyi ankon atamfa ɗinkin dogon riga me kyau, sunyi kyau sosai suma, momy tace "masha Allah ku siya min abu me daɗi"
janan tace "to momy me kikeso? inada dubu biyar saina siya miki"
murmushi momy tayi tace "koma me kika siyamin janan zan karɓa"
tace "momy inaso naga kina farin ciki"
momy ta rike hanunta tace "janan kimin alkawari ba zaki bar family ɗinmu ba, zaki zauna damu har a bada"
a hankali tace "insha Allah"
yace "muje"
mufeeda tayi saurin rike hanun madeena suka jera suna tafiya, shi kuma yana tsaye a baya da janan ya kasa rikewa a ranshi yace "kinyi kyau"
tace "sosai?"
a hankali yace "eh mana sosai ma kamar sarauniya"
tace "ko ɓarauniya ba?"
dariya yayi yace "me kika sace?"
tace "na sace kyawunka"
yace "umm na yadda ke SARAUNIYA KO ƁARAUNIYA duk biyu, kin sace momy a wajena kuma kinyi kyau kamar sarauniya"
tace "ni dai ban sace ta ba"
yace "kin sace"
shagwaɓe fuska tayi tace "um um"
wannan shagwaɓa a jininta yake bata ma sanin tayi, shiga mota sukayi taga fadeela da mufeeda a baya alama sun bar mata gaba ta zauna, zama tayi ta juyo ta kallesu duk hankalinsu akan waya, shiru tayi har suka fita, a hanya ganin tayi shiru ba waya a hanunta yace "kinason waƙa?"
da sauri tace "eh"
yace "wani kala?"
tace "na soyayya"
murmushi yayi sannan yace "kinason soyayya ne?"
rufe fuska tayi alaman taji kunya, ya kunna mata wakan umar m sharif"
a hankali ya lumshe ido ya fara bin wakan "nayi gamo da soyayya ce, da wata ɗiya me kyau ce"
har zuwa inda ake cewa "masoyiyata kyakkyawa ce, sannan a fuska me yawan fara'a ce"
wani smiling da tayi daidai wannan lokacin saida yaji kamar ya tsaida motan yayi ta kallonta, itama ji yayi ta fara bin wakan a hankali, rage muryan yayi yana saurarenta, baisan time ɗin da yace muryanki da daɗi ba
madeena da take cikin watsapp ta turawa mufeeda text
"ke kinga wani soyayya kamar a Indian film?"
mufeedah tana karantawa ta tura mata "aiko ina gani sufa yanzu basu san soyayya suke ba, ya maheer fa ya shiga hannu"
dariya tayi sai a sannan janan ta juyo tace "madina nima ki nuna min abinda kike kallo kikayi dariya"
aikinta kenan idan sunyi dariya a waya tace su nuna mata abinda suka kalla, ko kuma ta kwanta kusa da madina tana kallon chat nata, madina tace "ai na riga na wuce"
mufeeda tayi shiru kamar bata san komai ba, turo baki tayi taci gaba da bin wakan, a kofan babban ShopRite ys tsaya da motar, tare suka fito su duka, shiga sukayi ta rinƙa bin wajen da kallo, ya mata kyau sosai, maheer yace "ƴammata muje mana kin tsaya kina kallo"
tace "wajen yamin kyau"
yace "zaki sha ice cream?"
tace "eh"
madina da mufida har sun shiga sun fara ɗaukan abinda suke so, wajen saida ice cream ya kaita aka bata akan tsinke tana murna ta karɓa tana sha, ganin yana kallonta baya sha ta mika mishi nata tace "gashi"
buɗe baki yayi, tasa mishi tana murmushinta me sanyi, saida yasha yace "thank you"
yace "muje mu samu su mufida"
tafiya zasuyi tace "wait saura na momy"
yana kallonta har taje ta siya na momy aka sa mata a leda, ji yayi ta kara shiga ranshi domin ko shi dasu madina basa tuna siyawa momy ice cream Idan sunzo, tazo tace "muje"
shiga ciki sukayi mufida ta cika basket, madina kuma tana tura musu, can ta hango katon teddy tana tsoron teddy sosai hakan yasa tayi gefe tana kallon madina da mufida suna zaɓa, a cikin kunnuwanta taji ance "JAAN"
a mugun firgice ta juyo idanunta suka kara girma, wani kyakkyawan saurayi me tsananin kama da ita ne yake tsaye a gabanta yana mata murmushi sak yadda take murmushi haka shima yake yi, atake ta fara ja da baya bakinta yana rawa, matsowa ya fara kusa da ita yana cigaba da murmushi, saida ta mannu da bango tasa hanu tana kare fuskanta daga kallonshi, matsowa yayi sosai yace "jaan nayi kewarki bakiyi kewan yayanki bane?"
a mugun firgice tace "help!!! help!!! help please"
maheer dake tsaye a gefe yana kallonsu da mamaki akan fuskanshi, tunda yaga yaron farkon shigowansu yaga sunyi kama da janan kamar an tsaga kara, yana shirin faɗa mata sai kuma ya juya bai ganshi ba, a yanzu daya gansu tare yayi zaton zatayi farin ciki da murna sai kuma yaga saɓanin haka, a ruɗe take sosai, bai taɓa ganinta cikin wannan ruɗewan ba sai ranan da yayi mata tsawa, hanu yasa ya cire hanunta da take kare fuskanta dashi yace "tsoron me kike?"
tureshi ta fara tana cewa "taimako jama'a"
da sauri maheer yazo ya tsaya a gabanshi ya cire hanunshi daga nata, wani irin kankame maheer tayi ta baya ta ɗaura fuskanta a bayanshi, ganin yadda ta rike cikinshi kamar zata shiga jikinshi, ya kalli wanda yake tsaye a gabansu yace "waye kai?"
kallon rainin hankali yayi mishi kana yace "kana ganina ai kasan waye ni, kaine dai zan tambaya waye kai sabida na ganka da kanwata"
gaba ɗaya maheer ya rasa abin cewa domin kuwa gaskiya yake faɗa kana ganin wannan kasan jinin janan ne, yace "matsa zan tafi da kanwata"
cikin tsananin tsoro ta kuma kankame maheer tana girgiza kai, rawan da jikinta yake yi kaɗai ya isa ya tabbatar da halin da take ciki, maheer yace "janan zaki bishi?"
girgiza kai tayi cikin muryanta daya gama cika da tsoro tace "ka taimakamin kasheni zaiyi wallahi yana kisa"
gabanshi yayi mummunan faɗuwa jin abinda ya faɗa, yace "kin sanshi ne?"
da kyar tace "ya NABEEL ne, ka fita dani anan"
ganin zai taɓata maheer ya dakatar dashi yace "karka sake kasa hanunka a jikinta"
yace "ko kuma me zakayi?"
buɗe murya yayi yace "security? security?"
baya yayi yace "yau ta tsira amma ka sani kaima ka shiga gonan da ba naka bane kuma zakayi nadama"
tafiya yayi yabar wajen, a hankali yace "Janan? janan?"
jin tayi shiru kuma tayi nauyi a bayanshi ya juyo da ita, ganin wuyanta ya faɗi yace "janan buɗe ido"
madina dake tsaye ledan hanunta ya jima da faɗuwa tace "ta suma"
ɗaga ta yayi yace "mu tafi"
tare suka tafi, ya sata a mota duk suka shiga, direct gida ya nufa, da sauri ya fito da ita ya shiga ciki, momy dake kallo a falo ta tashi da sauri tace "meya faru?"
kwantar da ita yayi akan sofa yace "suma tayi"
tace "meya sameta?"
madina zatayi magana yayi sauri yace "haka kawai ta faɗi a ShopRite"
kallonshi sukayi jin yayi karya, daga nan sukayi shiru, ruwa ya ɗibo ya fara shafa mata a fuska, da kyar ya samu ta farfaɗo.
*Jiddah Ce...✍🏻*
08144818849
🌸🌸🌸🌸🌸
*ZOBEN WUTA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 6*
~A ruɗe yace "kin tashi? please karki kara suma ki barni kinji?"
a hankali ta gyaɗa kai, saide har yanzu kamar bata hayyacinta dan kuwa sai kalle kalle take kuma duk abinda ya taɓa ta saita tsorata, addu'a yayi mata sannan ya shafa mata a fuska, momy tace "ka kaita ɗakinsu ta samu bacci"
riketa yayi ya kaita ɗaki ya taimaka mata ta zauna a bakin bed, shima zama yayi a gefenta yace "meyasa kike tsorata idan kin ganshi haka?"
tace "dan Allah ka daina min maganan ya nabeel, idan zakamin maganan to na yadda zan bar gidanku, wallahi ko yanzu kace na bar gidanku zan bari"
tashi tayi tasa takalmi tace "ka gani ba na shirya zan tafi, bazan kara dawowa ba kuma na maka alkawari kaji?"
hanunta ya rike karo na farko daya janyo ta jikinshi, luf tayi a kirjinshi tayi shiru shima yayi shiru, yace "bazan kara miki magananshi ba kinji?"
cikin kuka tace "to na gode"
yace "amma inaso ki bani amsa ɗaya"
tace "to"
yace "mamanku ɗaya babanku ɗaya?"
gyaɗa kai tayi tace "uwa ɗaya uba ɗaya muke dashi"
shiru yayi, yanada tarin tambayoyi amma baison tace zata bar gidansu, yace "amma mama na raye?"
girgiza kai tayi tace "mama ta mutu Baba ma ya mutu"
yace "shiiii ya isa daina kukan haka"
bata daina hawaye ba amma ta daina shesheƙa, mufida tace "meyasa ya ɓoyema momy?"
madina tace "nima ban sani ba, amma fa yayanta ɗinnan wallahi ya haɗu, kinga jikinshi kuwa? Allah yayi halitta wallahi"
mufeeda tace "gaskiya wanda yace baida kyau ma yayi karya ko makiyi ba zaice baida kyau ba"
tace "amma meyasa ta haukace haka data ganshi?"
"to nima madeena ina zan sani?"
"muje mu duba ta"
tafiya sukayi zuwa ɗakinsu, har lokacin tana jikinshi yana cewa "ya isa haka stop crying"
shiru mufida sukayi suna jin tausayinta, a hankali ta fara bacci a jikinshi jin tayi nauyi ya duba yaga tayi bacci, kwantar da ita yayi sannan yace "ku kula da ita"
shiru suka zauna kusa da ita, sun saba da ita sosai, sunfi son ganinta kullum cikin dariya da fara'a kamar yadda ta saba, idan ta zama shiru sai gidan duk yayi shiru, text ya gani a wayarshi da sabon number
"mahaifinka yana dawowa gobe daga Abuja zuwa kano"
sam bai ɗau text ɗin da wani muhimmanci ba yayi zaton ma ƴan wajen aikinsu Abba ne.
a ranan bata sake ba haka ta wuni, har zuwa washe gari bata saki jiki ba, saide ta zauna tayi shiru, kamar yadda ta saba haka yau ma ta tashi da wuri ta fara aiki, saida ta gama aikin komai ta goge ko ina, sannan ta shiga kitchen ta fara breakfast, rigan baccin ne a jikinta har yanzu ash color da hulan net ta cusa gashinta ciki, tsayawa yayi a jikin kofa ya harɗe hanu a kirji yana kallonta, sanye yake da jallabiya ash color, yayi kyau sosai, batama san yana nan ba tana soya kwai tace "Allah yasa kafin momy ta tashi a bacci na gama"
shigowa yayi ya tsaya kusa da ita, albasa ya fara yanka mata, ta ɗago kai tana murmushi tace "good morning ya maheer"
kwaikwayon muryanta yayi yace "good morning ya janan"
dariya tayi tace "daka bari zaisa hanunka yayi warin albasa"
yace "a,a barshi zanyi"
tare suka gama aikin, ta tattara ta kai dining, ta dawo zata fara wanke wanke, ya fara nannaɗe hanun riga, tace "me zaka yi?
bai mata magana ba, murmushi tayi ta fara wankewa, karɓa yake yana ɗaurayewa, saida ta gama tasa hanu a ruwan, ɗiba tayi ta watsa mishi a fuska, runtse ido yayi, sannan ya buɗe ya murtuƙe fuska kamar bai taɓa dariya ba, a tsorace tasha jinin jikinta, tace "kayi hakuri"
kallonta yayi duk a tsorace take, a yadda ya fahimta tanada son wasa, domin koda su madina suke zaune saita rinƙa tsokanansu, ba tareda ta sani ba ya ɗibo ruwa a hanu, ta dukar da kanta kasa jikinta yayi sanyi sosai, watsa mata yayi, da sauri ta ɗago tana dariya, tashi tayi zata gudu ya watsa mata dayawa, itama ɗiba tayi ta fara watsa mishi, jika kitchen ɗin sukayi, ganin kayan jikinshi ya jike sosai ya ɗau roban ruwan duka zai juye mata a jiki ta kwala ihu zata gudu sukaci karo da momy, kallonsu tayi duk suka sunkuyar da kai, tace "ku yara ne? maheer kana biye mata kalli yadda kuka jiƙa kitchen?"
shiru sukayi, tafiya zatayi janan wacce jikinta yake yoyon ruwa tace "momy kiyi hakuri"
tace "wuce muje"
wucewa tayi tana gaba momy na baya har zuwa falo, rigan ya kama jikinta sosai sabida ruwan daya jikata, momy a ranta tace "ya zama dole na rinƙa nuna mata ta daina sakin jiki sosai dashi, ita batasan halittanta ba duk wani tsalle tana iya yi a gabanshi, tana iya sa kaya ko wani iri sabida ta ɗau maganan da suke faɗa mata na cewar ita dasu mufeeda duk ɗaya duke a wajenshi, da alama batada wayo sosai har yanzu yaranta dayawa akanta"
cikin zaƙin muryanta tace "momy tunanin me kike?"
tace "ba komai tsaya anan"
tsayawa tayi momy ta ɗauko hand dryer ta busar mata da kanta wanda ya jike, towel ta ɗauko ta goge mata jikinta saida ya daina yoyon ruwa tace "muje"
ɗakinsu suka shiga momy da kanta ta buɗe drower ta ciro mata dogon riga me ɗan nauyi ta miƙa mata, tace "maza canja"
a gaban momy ta zame rigan da wandon, rufe ido momy tayi tace "janan ki rinƙa jin kunya mana"
tace "momy ba kince ku iyayena bane?"
tace "eh"
rigan yayi mata kyau army green ne, tasa hulan dake haɗe da rigan, momy tace "kinyi kyau ƴata"
murmushi tayi ta kalli madubi, gaskiya tayi kyau ita kanta ta sani, ga wani cika da takeyi tana kara yin haske, ta zama kamar ba ƴar nan ba, tace "muje muyi breakfast"
tare suka fita, yana zaune akan dining tareda su fadeela ya canja kaya zuwa shadda ruwan kasa da hula ɗinkin irin shaddan, sai kamshi yake, ya gyara sajenshi kamar baƙin balarabe, zama tayi tana facing nashi, ɗago kai yayi daga cin abincin da yake, ido suka haɗa ta kashe mishi ido tareda ɗaga mishi gira, shima gira ya ɗaga mata alaman menene?
yatsa ɗaya ta ɗaga tayi mishi alaman kayi kyau, murmushi yayi ya dukar da kai yaci gaba da cin abinci, itama ci ta fara, shiru wajen yayi sai karan cokala akeji, da ya ɗago kai sai yaga tana kallonshi, sai kuma ta kashe mishi ido tayi murmushi, gaba ɗaya yana neman rasa nutsuwanshi, kallon madina tayi, kamar batada lafiya sai lumshe ido take, janye plate ɗinta tayi tana dariya, madina tasan tsokana ne hakan yasa bata kulata ba ta kara zuba wani tana ci, janyewa ta kuma yi ta kawo gabanta, madina tace "please ki daina bana jin daɗi"
da sauri tace "sorry"
mayar mata abincin tayi, ta kalli mufeeda wacce take latsa waya, fizge wayan tayi cikin wasa ta ɓoye a bayanta, mufeeda itama kamar batada lafiya tace "ki bani please jikina so weak nake ji"
taɓa wuyanta tayi taji zafi, tace "sorry mufee"
bata wayan tayi, itama sai taji ba daɗi, ya gane idan ba tsokana tayi ba bata jin daɗin zama, a hankali yasa kafanshi ya shafa nata, ɗagowa tayi sukayi ido huɗu, murza yatsunta yayi da nashi, zata janye ya danne kafarta da nashi, cin abinci ta fara tana jin kafarshi a nata, kara danna ƙafan yayi tace "wayyo ka daina please"
duk suka kalleta daga momy harsu madeena, saurin bige bakinta tayi, shi kuma yayi kamar bai san abinda ya faru ba, momy ta tashi domin duk abinda sukayi akan idonta, tace "Alhmdllh"
ɗakinta ta shiga ta kira numbern Abba domin akwai magana da take so suyi me matukar muhimmanci"
ta kira sau uku bai ɗauka ba, ta kara kira bai ɗauka ba, hakan bai taɓa faruwa ba, idan yayi tafiya baya barin wayarshi a buɗe matukar yasan za'a kirashi be ɗauka ba, kuma bata taɓa kiranshi sau biyu be ɗauka ba, tashi tayi da sauri ta fita tace "maheer kira Abbanku na kirashi bai amsa ba"
wayarshi ya ciro daga aljihu ya kira numbern Abba, yana shiga ba'a ɗaga ba, kallon momy yayi yaga har hankalinta ya fara tashi, da sauri yace "momy ba komai fa may be yana aiki ne"
shiru tayi, tace "mufeedah kira shi"
mufeeda ta kira numbern yana shiga ba'a ɗauka ba, hankalin momy ya kara tashi, ganin haka janan ta riketa tace "momy ba komai fa zai kira ki mishi uzuri"
girgiza kai tayi
"janan bai taɓa yin hakan ba, baya taɓa kin amsa kira koda me yake yi"
wayar maheer ya fara ringing da sauri ya ɗaga, ganin numbern Abba ne yayi saurin receive yasa a handsfree sabida momy taji hakalinta ya kwanta, muryan wani daban yaji yana cewa "ina magana ne da maheer? babban taron general Ahmad?"
da sauri ya tashi daga zaunen da yake yace "eh nine lafiya?"
yace "idan kana tuki please ka samu waje tsaya, idan kuma kana tsaye ka zauna"
zama yayi yace "na zauna meya faru?"
yace "maheer mahaifinka yayi accident ga gawanshi nan zamu kawo gida yanzu domin Allah ya mishi rasuwa, saide wani hanzari ba gudu ba, accident ɗin shiryawa akayi"
maheer hanunshi ne ya fara rawa jikinshi ma gaba ɗaya ya ɗau rawa, ko kalma ɗaya bai iya kara faɗa ba, wayar ne ya faɗi ƙasa, daidai lokacin momy ta silale kasa a sume, madeena da mufeeda wani irin ihu suka fara kamar zasu tada gidan, mufeedah ta tashi da gudu zata fita a haukace, janan ta bita da gudu ta rike ta, Allah yasa tana da karfi ta iya ta kamata ta hanata fita, cikin kuka tace "janan ki sakeni Abba ya mutu?"
kin sakinta tayi sai rungumeta da tayi da karfi tana lallashinta, da kyar ta samu ta nutsu, a wajen ta zauna kasa dirshan tana rusa kuka, madina kam hawaye yaki fitowa sai ihu take, da gudu taje ta buɗe frij ta ɗau ruwa me sanyi, zuwa tayi ta zubawa momy, buɗe ido tayi tace "janan Ahmad ya mutu ya barni?"
rungumeta janan tayi tace "momy banda kuka ki daure, ki danne zuciyarki"
kallon maheer tayi har yanzu yana zaune a inda yake baida niyan tashi, ba zata iya fahimtar halin da yake ciki ba, jiniya ne ya karaɗe unguwan, motoci ne manya manya na sojoji ansa gawanshi a babban motan da suke da gawan kowane me muƙami a soja, momy tana jin tsayuwan motoci a cikin gidansu da jiniya ta kara suma a jikin janan, knocking akayi janan ta zubawa momy ruwa ta kara farfaɗowa, tashi tayi ta buɗe kofan, gani tayi manyan sojoji sanye da uniform sun shigo da akwati a hanunsu alaman gawa ne a ciki, jikinta yana rawa tace "ku shigo"
shiga sukayi suka aje a tsakar falon, kafin kace kwabo mutane sun cika gidan da ƴan uwa da abokan arziƙi, momy dasu madeena sukayi kan gawan suna kuka da ihu, janan ta jingina da jikin kofan ta ɗaga kai sama hawaye na bin fuskanta har zuwa wuyanta, sai a lokacin ta kalli inda maheer yake taga baya nan, sojojin ne sukayi mishi wankan gawa aka sashi a likafani sannan aka kawoshi tsakar falon aka kira su madeen su zo suyi mishi addu'a, momy kam ko magana bata iyawa sai kuka, tun tana kukan da murya har muryanta ya tafi sai hawaye, janan taga babu maheer a wajen, kallon kofan ɗakinshi tayi taga a buɗe, da sauri ta nufi ɗakin tayi sallama, da sauri ta juya zata koma ganin khairat rungume dashi tana lallashinshi, cikin raunin murya yace "Janan?"
tsayawa tayi bata juyo ba, batasan khairat tana nan ba da ba zata shigo ba, yace "kizo"
a hankali ta juyo tana share hawaye ta tsaya nesa dasu tana ɗauke kai ganin khairat ta cusa yatsunta a gashin kanshi, yace "matso"
A hankali ta matso ba dan taso ba, ji tayi ya rike hanunta ya gama juyowa da ita, janyewa yayi daga jikin khairat ya kankame janan sai yanzu ya samu ya fashe da wani irin ɗan marayan kuka, itama hawaye take yi, amma ta kasa taɓa shi ganin kallon da khairat take aika mata, cikin kuka yace "Abba ya tafi ya barni janan, Abba ya tafi"
itama kuka ta fashe dashi, yace "ki lallasheni ke kaɗai nake son na jini a jikinki a duk lokacin da nake cikin kunci, ki rungumeni"
cikin kuka tace "maheer kaje kaga gawan Abba, kaje ka sashi a kabari maheer, kaine babba ya kamata ka kwantarwa da momy hankali kayi jarumta, idan kana kuka su madina me kake so suyi?"
yace "ki rungumeni"
a hankali ta ɗauke kai daga kallon khairat, rungumeshi tayi tsam, a hankali kukanshi ya fara raguwa, saida taji ya lafa kafin ta janyeshi a jikinta ta rike hanunshi tace "muje Abba yana ta so a kaishi makwancinshi, faɗin Allah ne duk wani ɗan aljanna idan ya mutu yana Allah Allah a kaishi makwancinshi"
tafiya suka fara khairat tana kallonsu har suka fita, wani irin jaa idanunta yayi ji tayi tana tasa duk wani control nata, a gaban gawan suka tsaya, momy da muryanta daya dishe tace "maheer abbanku ya mutu"
rungume momy yayi yana kuka, da kyar janan ta lallasu, lokacin da za'a fita da gawan momy dasu mufeeda suka rike makaran suna ihu, janan ce ta raba hankali gida uku tana lallashinsu da haka har aka fita da gawan, zama sukayi a kasa suna rusa kuka, da alama akwai matukar shaƙuwa da kuma soyayya tsakaninsu da Abba, janan itace shaida, har aka binneshi babu wanda ya gane kanshi a gidan duk sun fita hayyacinsu, janan ta ɗauko dogon hijabi tasa sabida mutane da suke shigowa, yawanci sai kallonta suke ita kuma bata son hakan, maheer yana dawowa daga makabarta ya koma ɗakinshi ya kwanta, ya rufe ya hana kowa shigowa.
a haka har akayi kwana uku, baya yadda da abinci sede yasha tea kawai ya kwanta, momy ta rame su mufeeda ma haka, janan ma ta zama shiru shiru, ana gama sadaka mutane suka watse gidan ya dawo ba kowa, janan ce ta fara share share da mopping, jikinta sanye da hijabi dogo har kasa pink, ta faɗa sosai domin tayi kuka itama, saida ta share komai ta goge gidan ya dawo tsaf, turare tasa me kamshi kana ta shiga kitchen ta fara musu girki dan tasan duk cikinsu babu wanda yake a koshe, sai mangrib ta gama ta zuba a plate ta kaiwa su momy da madeena, mufeeda tace "bazan iya cin abinci ba janan"
cikin kuka tayi maganan, murmushi tayi tace "baki yadda da ƙaddara bane?"
tace "na yadda"
tace "to meyasa kike haka? duk cikinku kun san kowa zai mutu babu wanda zai tsallake rananshi, me zai hana mu daina wannan kukan muyi mishi addu'a?"
hanun momy ta rike tace "a duk lokacin da uwa ta kasance da rauni to ƴaƴanta zasu sha wahala, idan uwa bata kasance jajirtacciya ba to za'a samu matsala sosai a rayuwar ƴaƴanta, uwa......"
kuka ne ya kufce mata ta fara kamar zata shiɗe, momy ce ta riketa da alama akwai abinda yake cimata rai idan rana maganan daya shafi uwa, lallashinta momy ta fara tace "ki daina kuka janan insha Allah na daina nima"
tace "momy kada kisa kanki a damuwa ƴaƴanki zasu sha wahala idan bakya raye, rashin uwa babu daɗi, nasha wahala nasha wahala sosai"
momy lallashinta take da kyar ta samu tayi shiru abincin da basu ci ba