Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
sai kusan tara da rabi na dare, kowa yaje ya kwanta ransu ba daɗi. washe gari suna zaune a falo su duka harda maheer akayi knocking, janan ce ta buɗe tayi musu iso, sanye suke da bakin suit da kuma uniform na soja a jikin sauran, hanunsu rike da manyan takaddu da laptop, kowannensu yana sanye da baƙin glass a ido, saida gabansu ya faɗi ganin yadda fuskansu babu alaman murmushi ko dariya, zama sukayi akan kujera, momy taji jinin jikinta ya tsaya da aiki, a hankali tace "sannunku da zuwa, madina kawo musu ruwa da abinsha" ɗaya daga cikinsu yace "ba ruwa ko abinsha bane ya kawomu munzo ne muyi magana da ku" shiru sukayi, maheer ne ya daure yace "muna jinku" takaddun suka mika mishi sannan sukace "kafin mahaifinku ya kashe kanshi ya karɓi bashin naira biliyan uku da rabi, sannan yace zai biya kuma bai biya ba har ya kashe kanshi sabida munyi bincike sosai a motarshi munsa masu gyara sun duba kafin ya tafi, daida ya tafi mukaji yayi accident kuma kwance wani abu akayi a cikin motar, an dakatar da account nashi daga aiki sannan mun kwashe duk kuɗin account ɗin duka duka biliyan ɗaya ne da dubu ɗari tara, munyi bincike sosai mun gano yana da company ɗin gyaran takalma wanda maheer yake aiki a ciki, sannan yanada wannan gidan da kuke ciki da kuma shaguna guda biyar a bakin kasuwa sai motoci guda biyar, ɗaya nashi ɗaya na matarshi, ɗaya na maheer sai biyu na madina da mufeeda, munzo ne mu karɓi waɗannan abin duka dan mun san idan mun bari kuɗin banki ba zai fito ba, sabida haka wannan shine mutumin da zai siya gidannan akan farashin kuɗi naira miliyan ɗari shida da dubu ɗari bakwai, sannan motocin duka zai siya akan naira miliyan ɗari huɗu, sai kuma shaguna duka zai siya akan naira miliyan tamanin, sauran bashin ya zama dole mu yafe domin mun san shine iya kadaran da yake dashi" momy tace "bamu yadda ba sai munga lawyer" wani a cikinsu ya ciro I'd card nashi ya mika mata, yace "matukar baku bada wannan abin na umarnin kotu ne a kama matarshi a tafi da ita" momy tace "saide ku kamani" tashi tayi ta mika musu hannunta, ankwa zasu sa mata madeena da mufeeda suka zube a gaban maheer, cikin tashin hankali sukace "dan girman Allah yaya ka hanasu tafiya da momy mun yadda a basu komai abar mana momy" yace "ku dakata" tsayawa sukayi dasa ankwa ɗin, yace "ina zuwa" shiga cikin ɗakin Abba yayi ya tattaro duk takaddun ya kawo musu, hanu yasa sannan ya mika musu yace "gashi" kanshi kasa har suka karɓa, momy ta fashe da kuka tace "maheer kayi hauka ne? dukiyan mahaifinku gaba ɗaya zaka ɗauka ka basu? aina zaku zauna? ina zamu je?" ɗaya daga cikinsu yace "ku tattara komai naku abinda ya shafi kayan sawa banda kayan cikin gidan wanda yake mallakinshi ne ku fita yanzu domin zamu rufe gidan" momy zatayi magana maheer ya hanata, kallon janan yayi wacce ta jingina da bango, yace "jeki tattaro kayanku" ya faɗi haka ne dan yaga su madina ba zasu iya ba, yaga tsananin tashin hankali akan fuskansu, ya lura janan ta fisu karfin zuciya, zata tafi police ɗin ya fara binta, tsayawa tayi tace "meyasa kake bina?" yace "sabida kada ki aje wani abin cutarwan tunda an koreku" cikin ɓacin rai tace "na maka kama da wacce zata cutar da mutane?" yace "ni kike gayawa magana? zan wanke ki da mari anan" tace "idan ka fasa marina baka cika ɗan halak ba" maheer ne yazo cikin sanyin jiki da karaya ya rike hanunta ya jata, ɗakinsu suka shiga ya taya ta tara kayan, harda kayan momy da nashi suka kwashe, janan tana kuka suka fito, hanun momy ya rike ita kuma ta rike hanun madeena da mufeeda suka fita, shi kanshi ji yayi kamar yayi kukan daurewa kawai yake irin dauriyan namiji, duk ma'aikatan gidan ya tara su ya sallamesu, jiki a mace suka fito a gidan, suna gani aka rufe da sabon makulli, aka yar da nasu, janan tace "ina zamu je?" girgiza kai yayi alaman bai sani ba, idonta cike da hawaye tace "kasan me?" girgiza kai yayi ya kasa magana, tace "account daka buɗe min har nan Abba yasa mana kuɗi nida su mufeeda ai ni ban taɓa ba kuma na ɓoye atm ɗina sabida kar su gani" nuna mishi atm ɗin tayi tace "ka gani?" murmushi yayi yace "nawa ne a ciki?" tace "dubu ɗari biyu da hamsin duk da kuɗin daka turamin kace kamin kyauta, kaga zai kama mana haya a unguwa simple sannan zamu samu na abinci kafin Allah yasan yadda zaiyi damu ko?" momy tace "Allah miki albarka janan" tace "Ameen momy" *Jiddah Ce....✍️* 08144818849 🌸🌸🌸🌸🌸 *ZOBEN WUTA* 🌸🌸🌸🌸🌸 By _Jiddah S Mapi_ *Chapter 7* ~Janan ganin suna cikin zazzaɓi na tashin hankali tace "ku zauna anan nida ya maheer zamu je mu nemo gidan da zamu zauna" hijabinta ta ciro daga akwati sannan ta shinfiɗa musu a kasa ta rike momy ta zaunar da ita, a karkashin wani bishiya suka zauna tace "zamu je insha Allah yau zamu nemi gidan da zamu kwana a ciki kinji momy?" gyaɗa kai momy tayi, tare suka tafi, ta fara da kaisu unguwan da tasan bana masu karfi bane bale asa musu kuɗi masu yawa, har sun fara karaya da samun gida, tace "ya maheer be strong zamu samu gida insha Allah" yace "janan meke faruwa ne?" tace "ƙaddara ce kayi hakuri muci gaba da nema" zama yayi akan wani dutse yace "janan anya zan jure ganin family ɗina cikin wannan halin?" durkusawa tayi gabanshi tace "dan Allah ya maheer ka tashi, zamanka shi zai kara sasu cikin wani hali" tashi yayi suka fara tafiya, da kyar suka samu wani gida wanda mutanen gidan suka tashi satin daya wuce, janan ce ta tambaya waye me gidan, kwatance akayi mata tace "na gode" da ɗan gudu taje inda yake tsaye tace "mu karasa" wani gida suka nufa, tayi sallama, yaro ne ya fito tace "mana magana da babanka" koda ya fito ta durkusa kasa ta gaisheshi cikin girmamawa domin mutumin ya manyanta sosai, yace "tashi tashi ƴata" tashi tayi, da alama tsohon zaiyi son kuɗi sosai, domin da suka fara magana yace ko yanzu suke da dubu ɗari da hamsin su kawo su shiga, janan kallon maheer tayi tace "kaga ikon Allah ba? gashi mun samu" murmushi yayi mata kawai, gaba ɗaya dauriya yake zuciyarshi cike da tunani da sarkakiya, pos ta nema suka cire kuɗin sukazo suka danka mishi, wajensu momy suka koma, da sauri tace "momy ku tashi mun samu gida" tashi sukayi, itada maheer a gaba suna biye dasu har zuwa gidan, kallon gidan suke basu saba zama a irin wannan gidan ba, janan ce ta cire hijabinta ta ɗaura a kwankwaso ta fara share gidan, zaninta ta ciro sabo wanda momy ta siya mata sannan ta shinfiɗa musu, tace "madina mufeeda ku kwanta, momy kema kwanta" yana zaune a bakin kofan yayi shiru yana kallonta, saida ta gama taje ɗakin da maheer zai zauna ta gyara mishi, zuwa tayi tace "ya maheer muje ka kwanta" binta yayi yaga ta gyara mishi wajen, kwanciya yayi ta cire hijabin data ɗaura ta rufashi dashi, tashi tayi zata tafi ya rike hanunta, shiru tayi jikinta a sanyaye tace "kayi bacci ya maheer dare yayi" yace "ki dawo janan yau kawai mu zauna tare" dawowa tayi ta zauna tace "ya maheer me kake cewa haka? ai ba zaiyi mu kwana waje ɗaya ba, da safe nayi maka alkawarin zan dawo, yanzu zanje na gama gyara cikin gidan ne" yace "janan me zaisa mu kwana waje ɗaya?" a hankali tace "ya maheer aure ne kawai zaisa hakan" a hankali yace "zaki aureni?" da mamaki ta kalleshi, sai kuma tace "baka cikin mood me daɗi shiyasa kake faɗan duk abinda yake maka, yanzu yi bacci zuwa safe sai muyi magana" zaiyi magana tace "shiiii yi bacci" tana kallonshi shima yana kallonta har bacci ya ɗaukeshi, murmushi tayi ta shafa gefen face nashi tace "Allah ya baka ikon jurewa baka saba da wahala ba" tashi tayi ta fita, saida ta gyara ko ina sannan tazo bayan momy ta kwanta ta rungumeta itama tayi shiru, ta zaci sunyi bacci sai jin muryan momy tayi tace "janan?" a hankali tace "na'am momy" tace "yau kaɗai zanyi miki wani magana" shiru tayi, momy tace "mahaifiyarki tana raye?" girgiza kai tayi, "a'a ta mutu" momy tace "zaki yadda ki zama ƴata ta har abada? da mahaifiyarki tana raye zance tayi rashin ƴa, amma tunda bata raye zan jinjina mata domin ta haifi ƴa" a hankali tace "momy ni ƴarki ce" tace "na gode" shiru sukayi su duka basu samu bacci ba a daren sai wajen asuba bacci ya ɗaukesu. Deen ne tsaye a kusa da Ammi, wacce tayi tagumi tana hawaye kamar zata shiɗe, zama yayi ya zubawa Ammi ido yace "Ammi wai kukan nan na mene? wai meke faruwa ne? kin dawo kin ɓoye takaddu kin hanani gani kuma kina rusa kuka, so kuke ku kasheni ne a gidannan?" cikin yankewan magana tace "Deen Allah ya ɗauki raina na huta, Deen ina cikin matsala, kirjina zai fashe..." kuka take sosai, rungumeta yayi yana bubbuga bayanta yace "shii it's okay ya isa haka" tace "bazan iya daina kuka ba, ina cikin tashin hankali, sai yaushe zanyi farin ciki?" hanunta ya rike yana murzawa a hankali, kanshi a kulle yake, komai na gidan ya fita mishi a rai, baya son komai na gidansu, ji yake kamar ya gudu ya bar gidan, amma son da yake yiwa Abeed ba zai barshi ya tafi ba, cikin raunin murya yace "Ammi idan baso kike zuciyata ta fashe ba ki gayamin meke faruwa?" gunjin kuka take yi ta kankameshi tace "Deen zan faɗa maka amma dan girman Allah kada ka faɗawa kowa, duk soyayyan da kake yiwa Abeed kada ka faɗa mishi wannan maganan kamin alkawari" zuwa yanzu ya gama karaya yace "ammi ki faɗamin dan Allah" cikin kuka tace "naje na samu doctor ɗin da ya yiwa Beed gwaji, result nashi ya fito" mika mishi tayi tace "Deen ƙaddaran kowa da yadda yake zuwa mishi ƙaddaran Abeed ba ƙaddara ne me kyau ba" yace "Ammi kina rabamin hankali ki faɗa min abinda yake faruwa" tace "Abeed ba zai haihu ba" a firgice ya tashi yana kallon ammi cikin shocking, jijjiga kai tayi hawaye yana cigaba da wanke mata fuska tace "kwarai Abeed ba zai haihu ba deen" kuka take yi sosai, da kyar yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" cikin gunjin kuka tace "ɗan uwanka ba zai taɓa ganin jininshi ba a duniya" shiru Deen yayi, tashin hankalin da yake ciki ya ninka wanda Ammi take ciki yace "Ammi kuma babu yadda za'ayi a gyara abin?" girgiza kai tayi tace "na cewa likita zan bashi rabin dukiyanmu ya sama mana hanyan da za'a gyara harya samu haihuwa, yace babu hanya" kuka me tsuma zuciya deen ya fashe dashi, duk yadda yaso ya rike kukan ya kasa, Ammi ta kasa lallashinshi itama kukan take babu me basu hakuri, yace "meyasa Abeed yake shiga wannan halin? meyasa bani ba sai shi?" turo kofan yayi kunnenshi ɗauke da headphones yana jin waƙan badman biladin na hello my baby, da sauri suka share hawayen, deen ya kakalo murmushi yace "ka dawo?" Ammi tace "yaushe ka shigo?" cire headphones ɗin yayi, kyau yayi sosai cikin rigan armless da purple da wando fari yace "is everything okay?" Ammi tace "yeah yeah everything is fine, ya ka samu abokin naka?" turo baki yayi kamar karamin yaro yace "he's fine amma baida lafiya" Ammi tace "Ayya sorry je kayi freshen up saika fito kaci abinci ko?" jijjiga kai yayi a shagwaɓe yace "ya deen why you look so weak?" cikin dauriya yace "am just missing you" yace "nima nayi missing naka let's go in, kaji wani labari" Ammi tace "kenan ba zakuyi maganan a wajena ba?" yace "no Ammi banda ke?" tace "shikenan kuje" ganin tayi fushi ya rungumeta yace "sorry Ammi wannan fa secret ne between me and my twin bro" tace "shikenan nima zanje ɗakin zee-zee muyi hira abinmu" yace "ummm" rike kafaɗan Deen yayi yace "meka ajemin dana tafi?" taɓe baki yayi alaman be aje komai ba, yace "um wai kai Deen har yau bakayi beb bane? ba zakayi aure bane?" yace "zanyi amma nafiso mu auri mace ɗaya, kaga zatafi baka kulawa sosai" yace "noo a time ɗin da muke yara ne muke cewa zamu auri mace ɗaya amma yanzu mun girma" Ammi tana ganin sun shiga ɗaki ta kifa kanta a jikin sofan da take kai, ta fashe da kuka me tsuma zuciya, faɗuwa yayi kan gado ya rungume pillow yace "Deen kasan me?" girgiza kai yayi "no saika faɗa" yace "deen inason yara, so nake naga na tara baby's a gabana muna wasa dasu, i love fine fine kid's shiyasa nake jin muyi aure kawai" deen da za'a yanka jikinshi jini ba zai fito ba, ya zuba mishi ido kawai yana kallonshi ko kyaftawa babu, yace "hello kana jina?" firgigit yayi, ji yayi ya rungumeshi kawai yace "Abeed har yanzu bamu kai aure ba mu kara bari wani lokacin" janyewa yayi yace "kai Deen kasan me kake cewa kuwa? bamu kai aure ba? kasan we are 29?" yace "Abeed dan Allah ka daina maganan aure yau" Abeed bai ɗago komai ba yace "okay I understand kafi son na fara yin aure na samu perfect mace kafin kaima kayi, don't worry zanyi aure soon kuma na yiwa matata ciki da wuri ta haifa min fine fine yara" da kyar ya share zufan daya keto mishi, ta yaya zai ya faɗawa Abeed ba zai haihu ba? tashi kawai yayi ya shiga toilet, a hankali yake kuka harya gode Allah yayi alwala ya fito, sallaya ya shinfiɗa ya tada salla sabida baison Abeed ya kara mishi maganan, zee-zee tana kwance a ɗaki tana karatu dabida zasu fara exams Ammi ta shigo, tace "Ammi kin dawo?" a gefenta ta zauna tace "na dawo karatu kike?" "eh Ammi gobe exams" "to Allah ya bada sa'a" "Ameen" ta faɗa ita kuma Ammi ta kwanta tareda juya baya ta rufe ido kamar me bacci, hawaye ne yake zuba, ta kasa rike shesheƙan kukan saida zee-zee ta ji, aje takaddan tayi tace "wai Ammi sai yaushe zaki daina wannan koke koken ne? wai abinda ya faru ba ya riga ya wuce bane me kuma na tuna baya?" tace "ba baya nake tunawa ba zee-zee, gaba nake tunawa, abinda yake faruwa ina ganin zaifi na baya muni" "subhanallah Ammi keda kanki kike faɗan wannan maganan? duk abinda zai faru na tashin hankali amma yafi wanda muka gani a baya ina rokon Allah ya ɗauki rayuwata kafin na ganshi, bama rayuwata ba harda rayuwar yayuna biyu Abeedeen" girgiza kai tayi "dan Allah ki daina min maganan mutuwa zee-zee, banson na rasaku koda a magana ne" idon zee-zee cike da hawaye ta tashi tace "koda bamu mutu ba ki sani a kullum kina kashemu da kalamanki kuma bazan iya jura ba, matukar na gaji da wannan abinda yake faruwa a gidannan wallahi zan gudu, zan shiga duniya kuma ba zaku sake ganina ba ammi" tashi itama Ammi tayi sannan tace "kina ganin kamar laifi nane yasa nake wannan kukan zee-zee? kina ganin kamar da gangan nake yin kuka dan nasa ku tuna baya? ko kaɗan ba haka bane, sannan matukar kika gudu kika bar gidannan ki sani nima guduwa zanyi, bama sai kin gudu ba zan tafi kafin ki gudu" ganin tana kuka tace "Ammi ko zaki iya faɗamin me yake saki kuka a yau?" tace "bazan iya ba" a tsawace zee-zee tace "baga irinta ba? ba gashi kinki faɗa ba, kin cutar da rayuwar ɗanki da kanki kuma kinzo kina kuka muguwa mara imani..." da mari ta ɗauketa, dafa kunci tayi tace "kika mareni?" cikin tsawa tace "na mareki ko zaki rama ne?" hanu ta ɗaga zata mareta sai kuma ta dunkule hanun ta ciza lips nata na kasa tace "kinsan meyasa ban rama ba?" da kanta ta kara bada amsa tace "sabida kece kika ɗauki cikina na tsawon wata tara, sannan kika haifeni kika rene ni harna kawo war haka, badan wannan abin ba wallahi saina rama marin da kikamin" idonta cike da hawaye tace "rama mana zee-zee, ki rama idan har hakan zaisa kiji sanyi a ranki" juya baya tayi tace "bazan rama ba" a tsawace ta juyo da ita tace "kinsan meyasa nake kuka?" itama da ihu tace "ban sani ba kuma bana neman na sani" cikin kuka da sanyin jiki tace "Abeed ba zai haihu ba, ba zai taɓa haihuwa ba kwata kwata zee-zee" cikin kiɗima ta kalli ammi tace "wani Abeed?" da hanu ta nuna mata hoton Abeed da Deen dake maƙale a jikin bangon ɗakin, sunsa suit kala ɗaya baki sunyi kyau, cikin kukan taje wajen hoton tana shafawa tace "a cikin waɗannan biyun ɗaya ba zai haihu ba zee-zee kuma Abeed ne ba zai haihu ba, Abeed ne...." kuka take yi sosai, zee-zee cikin shocking ta nufi wajenta ta riketa tace "Ammi meyasa kikace haka?" result ɗin data ɓoye a cikin riganta ta ciro ta nuna mata, tace "doctor ya tabbatar min da haka, yaje India shiyasa bai bamu amsa da wuri ba, ya tabbatar min Abeed ba zai taɓa haihuwa ba...." kuka take yi kamar ranta zai fita, dafa goshi zee-zee tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Ammi kina nufin maganan Abbu ya tabbata? kina nufin da gaske Abbu yake?" cikin kuka ta gyaɗa kai zuwa yanzu ta kasa magana, cikin jirin da take ji ta tashi taje cikin akwatin data ɓoye kayanta, a kasa ta ciro hoton data ɓoye, Abbu ne yayi kyau sosai cikin shadda ɗinkin babban riga tace "meyasa? me yasa hakan yake faruwa Abdussalam?" Abeed yaga sallan Deen bana karewa bane, ya tashi yace "bari naje muyi hira da Ammi dama so nake ta bani wani shawara" fita yayi daga ɗakin ya nufi ɗakin zee-zee dan yasan acan take, hanu yasa akan handle zai murɗa yaji tana cewa "Abdussalam na soka kamar na mutu, naso mu rayu tare mu kula da yaran da muka haifa meyasa kayi hakan? Abdussalam ka amsamin" shiga ɗakin yayi yana kallonta, zee-zee data ganshi ta fara kokarin kwace hoton, Ammi tace "ki barni dan Allah koda sau ɗaya ne na kara ganinshi" kwacewa tayi ta wurgar, ido huɗu Ammi sukayi da Abeed wanda ya harɗe hanu a kirji yana girgiza kafa yana kallonta, jikinta ne ya fara ɓari, da sauri ta take hoton tana dariya tace "Abeed nawa yaushe ka shigo?" baiyi magana ba, saide tana iya hango tsananin ɓacin rai akan fuskanshi ga kuma kafarshi dake rawa alaman yana son ya danne halin da yake ciki, zuwa tayi ta rike hanunshi, babu musu ya biyota har bakin gadon ta ajeshi, da hanu ta yiwa zee-zee alaman ta ɗauke hoton kada ya gani, yana ganin duk abinda take yi, da sun haɗa ido saita mishi murmushi, youghurt me sanyi ta ɗauko da cup na glass ta zuba mishi, tace "Abeed ɗina sha youghurt" ɗan bige cup ɗin yayi alaman beso, rungume kanshi tayi tace "kada kayi fushi da Amminka kaji?" a hankali yasa hanu akan nata yayi shiru, zee-zee tayi mata alaman ba matsala? a hankali ta gyaɗa kai sannan tayi mata alaman eh ba komai, yana kallonsu ta cikin madubi basu sani ba, hankalinta ya kwanta domin taga kamar baiji abinda take faɗa ba kuma baiga hoton ba. da dare zee-zee da Ammi ne suke cin abinci, cikin Deen da Abeed babu wanda ya fito, bata damu ba dan tasan suna iya bacci a wannan time ɗin, can saiga ɗaya daga cikinsu sanye da jallabiya ya zauna akan dining baiyi magana ba kawai ya fara sa abinci, Ammi tace "wannan Deen ne ko Abeed?" shiru yayi bai amsa ba, kallon zee-zee tayi sannan ta taɓe baki ta gano abeed ne domin shine baya magana idan anyi mishi wani lokacin, hankalinta ya kwanta domin shine bataso yayi nisa da ita tafi son yana kusa da ita domin tana tsoron ya aikata wani abin idan baya kusa, tace "shi deen baya jin yunwa ne?" zee zee tace "may be sai zuwa anjima zai ci" baiyi magana ba ya fara cin abincin, kwai ta ɗauka ta ɓare tasa akan abincinta, zee-zee tace "Ammi nima kisa min kwai" ɓarewa tayi ta yayyanka dayawa ta zuba mata, kallonshi tayi tasan Abeed da son kwai hakan yasa ta zuba mishi ba tareda ta tambayeshi ba, da sauri ya ture abincin daga gabanshi, tasan Deen ne baya son kwai to idan wannan Deen ne ina Abeed?" sai yanzu yayi magana yace "nima na tashi daga bacci naga baya nan" tace "what? Ina yaje?" yace "may be yana cikin gida ko garden" tace "Deen ko dai yaji abinda nake cewa ɗazu?" yace "akan me?" tace "akan Abbu" "Ammi meyasa kike haka ne?" tace "ka taimakeni kada wani abin ya sameshi" har rige rige suke wajen fita su ukun, dube dube suka fara a cikin gidan cikin tashin hankali, tambayan me gadi sukayi ya fita, yace bai fita ba, Ammi ta kara ruɗewa tace "deen ku kasheni kawai, watakila komai yazo muku da sauki, deen ina lalata komai da kaina" garden Deen ya nufa ya buɗe murya yana kiran "Beed!!! Beed!!! Beed!!! where are you?" daga nesa ya ganshi a bakin swimming pool yasa kafafunshi cikin ruwan ya ɗaga kai sama yana jin iskan bishiyoyi yana ratsashi, gefenshi tsadadden drink ne a cikin cup, ganin yadda Ammi tazo a ruɗe, ya kalleta sannan ya ɗau cup ɗin yayi sipping na drink kaɗan yaci gaba da wasa da ruwan, hamdala tayi a fili tace "thank god" Deen ya zauna a gefenshi shima yasa kafa a ruwan yayi shiru, Ammi batayi magana ba ta juya ta tafi, kallanshi Deen yayi yace "kana zaune anan kana cikin damuwa ne?" girgiza kai yayi, alaman baya cikin damuwa, waya Deen ya ciro yace "to juyo nayi maka hoto" ya juyo yana murmushi rike da cup ɗin deen yayi mishi hoto, shiru sukayi duk yadda Deen yaso ya jashi da hira ya saki jiki sam yaki yadda yau ya zama wani iri, jikin deen ya kasa sakewa yace "Abeed akwai abinda kaji ne?" tsoron shi kada ace Abeed yaji cewa ba zai haihu ba, zaiso abin ya kasance tsakaninshi ne kawai da Ammi, yace "no banji komai ba, amma kasan me?" yace "no" "naji inaso naga yaranmu muma muyi wasa dasu" gaban Deen yayi mummunan faɗuwa, yace "gobe zamu fara fita aiki" jijjiga kai yayi yace "na sani" shiru sukayi su duka. Janan ganin zamansu a gidan haka ba zaiyi ba saida sana'a ta fita domin nema aikin da zata rinƙa samun kuɗi tana siya musu abin buƙata, tasan har maheer da yake namiji bai saba da rayuwan wahala ba bale mufeedah da madina, shagon wata mata ta samu tana mata wanke wanke ita kuma tana biyanta sannan ta bata abinci, a cikin biyan da take mata take samun ta siya musu abinci sannan ta siya musu duk wani abinda suke buƙata irin kana kana ɗinnan, suna zama a gidan da hakuri domin duk cikinsu ba wanda baya kwana cikin kunci da bakin ciki, saide janan tana iya bakin kokari ganin tasa farin ciki a fuskokinsu, hakan yasa take dagewa da neman kuɗi domin ta taimaka musu kamar yadda suka taimaka mata, yauma kamar kullum dawowanta kenan daga wajen aiki ta gaji sosai, tana zuwa ta faɗa kan tabarman da momy take zaune, ta ɗaura kanta a cinyar momy, momy wacce ta rame sosai ta kara yin fari tace "janan kin gaji ko?" gyaɗa kai tayi cikin shagwaɓanta tace "na gaji momy kuma nayi missing naki, ina su mufeeda?" shigowa sukayi suna cewa "gamu nan" da murmushi akan face nata ganin sunyi kyau cikin dogayen rigan material nasu da alama unguwa suka fita, taji daɗi da suka fara sakewa, tace "kunyi kyau sosai" madina tace "janan kinga yadda kike kara cikowa kuwa? kinga fa rugannan yayi miki kaɗan da kyar kike numfashi a ciki kumburin lafiya?" momy sai yanzu itama ta zuba mata ido taga ta kara hips sosai ga kuma breast nata ya cika, tayi fara duk da wahalan da take ciki, a ranta tace "may be haka yanayinta yake bata rama" tace "ke madina ba kumburi bane haka mama take" maheer ne yayi sallama, yayi kyau cikin bakin riga da wandon da yasa, ya rame kaɗan, hanunshi rike da leda yace "wai me kokarin neman kuɗi ne ake cewa tana yin jiki?" dariya tayi tace "haka dai madina tace" yace "yau na kawo muku favorite naku musamman janan" da sauri ta tashi tace "cat fish?" jijjiga kai yayi alaman eh, sannan ya mika musu ledan, da sauri suka karɓa itada su madina, itace farko farko wajen buɗewa, tana gama buɗewa ta ɗauka zata sa a baki, wani irin wari taji yana mata, duk yadda take son catfish sai taji

Chapter 6 of 9