Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
ɗin data ɓuya a bayan labule ba, kallon ashanan dake saman plate dake kusa da mirror yayi, da alama maganin sauro take kunnawa dashi, zuwa yayi ya ɗauko, idanunta a waje tace "Abeed me zakayi da Ashana...?" kafin ta karasa maganan ya kyasta yasa akan hoton, kallon yadda kafanshi ke fidda jini yana ɓata tiles ɗin tayi a mugun firgice, ashanan ya kuma kyastawa yasa a jikin labulen ɗakin da suke da matukar tsayi da kyau, wuta ne ya fara ci a ɗakin cikin ihu tace "Deen!!! Deen!!! Deen!!! wuta, kazo wuta" ganin zata fita a ɗakin yayi sauri ya fara rufe kofan, janyeshi ta fara a jikin kofan tana cewa "ka bari, Abeed ka bari" ture ta yayi, ji kake tim ta faɗi kasa kusa da labulen da yake tsananin ci da wuta, rufe kofan yayi yana jin Deen yana kiran sunanshi da cewa ya buɗe kofan, makullin yasa a aljihun wandon jikinshi sannan ya jingina da jikin kofan, zee-zee da Deen har jini hanunsu yake wajen bubbuga kofan, saide babu ko alaman buɗewa a jikin kofan, deen cikin karayan zuciya yace "Abeed ka buɗe, Abeed ba zan iya rasaka ba, dan Allah ka buɗe" jin bai buɗe ba, ya kalli zee-zee wacce ta haukace wajen buga kofan tana kiran sunan Ammi, zafin wutan yasa ammi ta fara tari tana kakkare fuskanta, duk da bai taɓa ta ba amma ufti da zafi yasa ta fara fita hayyacinta, yana tsaye yana kallonta shima yana jin tsananin zafi amma wutar da zuciyanshi take yi tafi wannan zafi, a hankali Deen yace "zee-zee kice mishi na ɗau wuƙa zan kashe kaina" cikin kuka tace "to" ɗaga murya tayi tace "ya Beed? ka buɗe ya Deen ya yiwa kanshi illa da wuƙa" baisan time ɗin daya ciro makulli a aljihu ya fara buɗe kofan a rikice ba, kasa buɗewa yayi tsaban tsananin firgicin daya shiga, Ammi data fara ganin duhu duhu tana ganin haka taja da kyar taje bakin kofan, hanunta ta ɗaura akan nashi ta fara kokarin buɗe kofan, ganin baya buɗuwa yace "Ammi ki buɗemu deen zai mutu" zee-zee kara ɗaga murya tayi tace "ya Deen zai mutu Ammi" cikin kuka yace "Ammi? Deen ba zai mutu ya barni ba ko? zamu rayu tare dashi? saide na mutu na barshi ko Ammi na?" cikin azaba ta gyaɗa mishi kai, fuskanta ya riko da tafukan hanunshi tana kallonshi shima yana kallonta yace "Ammi ki amsa min ba zai mutu ba ko?" da kyar tace "eh" murmushi yayi wanda ya bayyana tsananin kyawunshi, da kyar ta buɗe kofan, zee-zee tana ganinsu ta janyo Ammi, a daidai lokacin numfashin Ammi ya tsaya cak, idanunta suka rufe bakinta kuma ya buɗe, zee-zee ta waro manyan idanunta cikin tsananin tashin hankali tace "Ammiiiiiiiiiii" Deen dake rungume da Abeed ya zaunar dashi a gefe yaje da gudu, yana tashin Ammi, bata buɗe ido ba, zee-zee dake zaune a kasa daram kan Ammi akan cinyarta, a hankali ta zame kan ammi ta kwantar da ita kasa, wajen Abeed taje idanunta a bushe tace "ka kashe ta?" bai mata magana ba sai tashi da yayi yana shirin tafiya, hanunshi ta rike da karfi tace "ka kashe ta?" fizge hanunshi yayi zai tafi ta tsaya a gabanshi tace "ka kasheta?" juyawa yayi zai canja hanya yaji ta rike hanunshi, a fusace ya juyo zai mareta ta rike hanunshi cikin zafin nama, duka ta fara kaiwa kirjinshi tana kuka tace "bazan yafe maka ba, I hate you ya Abeed I hate you so much" yana tsaye yana jinta tana duka kirjinshi harta gaji dan kanta, sai kuma ta faɗa kirjinshi ta fashe da kuka ta rungumeshi, a hankali yasa hanu yana shafa shafa bayanta da almanan lallashi, deen sai safa da marwa yake ga Ammi daya kwantar akan sofan, hanunshi rike da waya da alama ya kira doctor, jin ana knocking yaje da gudu ya buɗe kofan, doctor ne ya shigo da kayan aikinshi, deen yace "ta zauna cikin wuta shine ta suma" da sauri ya karasa ya fara duddubata, allura ya fara yimata sannan yace "karka damu ufti na wutan ne yasa ta jikkata amma garin ya haka ya faru?" kanshi kasa yace "gobara ne ya tashi a ɗakinta kafin muzo kuma yayi nisa" yace "Allah sarki Allah ya bata lafiya" Ameen, drip yasa mata kana yace "ka zauna kusa da ita zata iya farkawa a firgice domin wutan" gyaɗa kai yayi, atake security's suka kashe wutan ɗakin, bayan doctor ya tafi suka zauna shiru, deen kusa da Ammi ya zuba mata ido, itama zee-zee tana kusa da deen, shi kuma Abeed yana tsaye a gefe ya jingina bayanshi da bango ya ɗaga kanshi sama, sun jima a haka kafin Ammi ta farfaɗo, kamar yadda Doctor ya faɗa haka ta tashi a firgice da kyar deen ya kwantar da ita kafin ta gane inda take, ganin komai ya lafa zee-zee tana murmushi haɗe da kuka tana kallon Ammi, a hankali ya juya zai tafi, deen yace "karka sake kaje kasha giya" shiru yayi yabar wajen, Deen zaune yake kusa da Ammi amma hankalinshi akan Abeed da yake ɗaki, ya kalli zee-zee da tayi tagumi yace "zoki zauna kusa da ita" zuwa tayi ta zauna a inda ya tashi, cikin natsuwa yake tafiya harya isa kofan ɗakinsu, tura kofan yayi ya shiga, hamdala yayi da bai ganshi kwance yana shan giya ba, faɗawa yayi kan sofa yayi shiru yana jiran fitowanshi daga toilet, kamar da wasa ya kai awa ɗaya a wajen baiga alaman fitowa ba, zuwa yayi wajen toilet ɗin ya fara knocking, ganin bai buɗe ba ya tura kofan ya shiga, toshe hanci yayi jin warin alcohol daya buga mishi hanci, ga kuma Abeed dake kwance a kasan tile yana bacci, gefenshi kwalaben giya masu tsada da yake siya ya ɓoye ba tareda deen ya sani ba, facemask ya ɗauko ya rufe fuskanshi kafin yazo ya ɗaga Abeed, cikin maye ya buɗe ido yace "Deen ka barni mana bacci fa nake bansha komai ba, tunda baka so ai na daina sha" bai mishi magana ba ya cire mishi rigan jikinshi da kuma three quarter ya barshi boxer kawai, janshi yayi zuwa cikin bedroom ya kwantar dashi akan gado, cikin muryan maye da idanunshi wanda suka koma ciki ciki yace "deen kar kayi fushi dani kaji? you are my blood" rufashi yayi da duvet kana ya tashi ya koma cikin toilet ɗin yana jinshi yana cewa "deen idan kayi fushi dani ba zanji daɗin rayuwa ba, na dena shan giya fa tunda jimawa, duk abinda baka so na daina" shiga toilet ɗin yayi ya fara wanke rigan da wandon duka ya shanya a ciki, wanke toilet ɗin yayi gaba ɗaya ya fesa air freshener, atake warin giyan ya tafi sai kamshi, fita yayi ya kashe mishi wutan ɗakin ya tura kofan falo ya koma wajen Ammi wacce take cewa a cire mata drip zatayi fitsari, da kyar ya lallasheta ta hakura da fitsarin saida drip ɗin ya kare har bayan mangrib, duk yawan masu aikin gidan zee-zee da Deen ne sukayi girkin dare, sun jera komai akan dining har zuwa lokacin Ammi da Abeed suna bacci, shi giyan ne ya sashi bacci ita kuma allura da drip, sai bayan Isha ya fara murza ido, a hankali ya tashi yana salati tareda yin hamma, ya manta duk wani abinda ya faru ya kalli jikinshi yaga babu kaya sai boxer, da sauri ya kalli agogo yaga karfe 8 na dare, dafe kai yayi a hankali komai daya faru ya fara dawo mishi, cikin sanyin jiki da gajiya ya tashi akan gadon ya shiga toilet, wanka yayi me kyau yana kallon kayan da Deen ya wanke mishi, fitowa yayi yana ɗaure da towel bai damu ya shafa mai ba kawai yasa jallabiya coffee, duk sallan da ake binshi saida ya idar, deen ya shigo domin ya duba shi, ganin yana zaune akan sallaya yana addu'a ya juya ya koma, saida ya gama addu'a ya tashi ya fita, duka suna kan dining suna cin abinci saide fuskansu babu walwala, a hankali ya zauna kujeran dake facing na deen, saide Deen bai kalleshi Bama abincinsa kawai yake ci, itama zee-zee abinci take ci bata ko kalleshi ba, shima bai damu ba ya fara zuba nashi, ci ya fara wajen yayi shiru sai karan haɗuwan spoon da plate kawai akeji, Ammi wacce ta idar da salla da kyar ta tashi, already tayi wanka kafin tayi sallan, night cream nata me kamshi ta shafa sannan ta buɗe wardrobe ta ciro riga silk baƙi, da net net a jikin hanun da kuma wuyan, kasancewar tana jin zafi har yanzu ta buɗe kanta tareda cire ribbon ɗin data kame tulin gashinta dashi, gashin ne ya zubo zuwa gadon bayanta, flat shoe tasa sannan ta fita daga ɗakin domin yunwa take ji sosai kamar taci babu, so take ko tea ta haɗa tasha ko zataji sauƙi, da sauri ta koma da baya lokacin data gansu duka a zaune suna dinner, komawa tayi yace "Ammi" tsayawa tayi domin bata san waye ya kirata cikinsu ba, daga deen har zee zee suka kalleshi, yace "Ammi kizo muci abinci tare" sai yanzu ta fahimci Abeed ne domin kwai ta gani akan abincinshi, a hankali ta karasa ta zauna, abincin dake gabanshi ya fara bata, taunawa take a hankali tana kallonshi, yace "na baki ruwa?" gyaɗa kai tayi, ya tsiyaya ruwa a glass cup ya kai bakinta, sha tayi tace "na gode Abeed" bai amsa mata ba yaci gaba da bata harta koshi. *Jiddah Ce...✍️* 08144818849 🌸🌸🌸🌸🌸 *ZOBEN WUTA* 🌸🌸🌸🌸🌸 By _Jiddah S Mapi_ *Chapter 5* ~Few days later madina ce a cikin mota tana sanye da uniform na school nasu wando blue da riga daidai gwiwa da blue dark sai hijabi fari guntu "janan!! janan!! ki fito mana zamuyi late fa" janan daga ciki tana shiri cikin sauri, mufeeda taɗau jaka ta fita da gudu tana cewa "idan baki fito da wuri mu mun san halin sani driver wallahi tafiya yake ya barmu kuma saide muyi tafiya da kafa dan Abba ya hanamu driving" da gudu ta fita, janan idonta ya cika da hawaye tasa riga da wando duka amma gashinta yaki kamuwa kuma school ɗin basa son suga alaman acuci a kan mutum, ko ribbon kwacewa suke sabida akwai boko akwai kuma Arabic duk a haɗe, jakanta na baya fari me kyau ta ɗauka sannan tasa canvas ɗinta ta ɗau hijabin har yanzu hanunta a kanta ta fita, zuwa yanzu hawayen ya fara wanke mata fuska, ko kaɗan bataso ta rasa zuwa school koda na kwana ɗaya ne, domin karatun da ake musu yana shiga kanta sosai, dana boko dana kur'ani yanzu hadda suke na izu biyar yau zasu shiga izu goma, tun daga kan stair yake kallonta ta juya baya batasan yana gida bama, yayi matukar kyau cikin orange na riga da wando jinx da polo, yasa picap orange, yana kamshin turare me daɗi da sanyaya zuciya, har ya sauko bata sani ba, kuka take tana cigaba da kame tulin gashin kanta me tsantsi da tsayi gashi baƙi ƙirin, yarinyar nan da alama ta haɗa jini da larabawa ko kuma mamanta India ko babanta akwai ɗaya, haka ya faɗa a ranshi, gyaran murya yayi da sauri ta juyo ta zuba mishi manya manyan idanunta da suke tsuma zuƙatan duk wani namiji daya kallesu, bama namiji ba har mace idan taga idon janan saita kara kallo sau biyu, share mata hawayen yayi da tafin hanunshi kana yace "kukan me?" taɓe baki tayi cikin shagwaɓan daya zame mata jiki tace "gashin yaki kamuwa" dariya yayi dan yadda tayi magana zaka san tana cikin damuwa, jin karan hon da sani yake mata kamar zai fasa musu kunne tace "zan tafi kawai haka amma zasu dakeni a school kuma banason bulala" yace "sojoji ne suke bulalan?" girgiza kai tayi yace "to me na tsoro ni kinsan lokacin da nake zuwa school idan nayi laifi Abba sawa yake sojoji sumin duka?" da sauri ta kalleshi da mamaki tace "meyasa?" yace "sabida shi soja ne" tace "sorry kaji?" yace "juya na kama miki gashin" tace "zasu tafi su barni" ganin zata kwasa da gudu yace "wait barsu su tafi zan kaiki" wani murmushin da yake burin gani a koda yaushe kan fuskarta shi tayi mishi, a duk lokacin da tayi wannan murmushin sai yaji wani sanyi a ranshi, yatsa yasa ya lakace dimple nata sannan yace "kinada kyau" tace "ban kaika kyau ba" yace "kin fini" tace "A,a sabida ni fara ce shiyasa zaka ga na fika amma kai ba karamin kyakkyawa bane dama ace an bani skin ɗinka kai kuma an baka nawa zanso" "to sannu me wayo, juya na gyara miki" juyawa tayi ya kame mata gida biyu, kallon yadda gashin ya sauka har zuwa hips nata yayi, a hankali ya janye idanunshi daga hips nata yace "Auzubillahi minashaiɗanirrajeem" tace "laa ya maheer ka iya kama kai" gira ɗaya ya ɗaga mata yace "yes ina kamawa su mufeeda muje kar muyi late" momy saida taga zasu fita tace "janan tsaya" tsayawa tayi tanasa hijabinta, bayan tasa ta kalli momy wacce take rike da leda tace "gashi wannan banaso kina zama da yunwa" karɓa tayi ta buɗe ledan, ganin cake ta daka tsalle ta rungume momy, kiss tayi mata a gefen kumatu tace "thank you momy I love you" momy haka kawai take jin yarinyar har cikin ranta, tace "i love you too" yana kallonsu har tace "muje ya maheer" jerawa sukayi har suka fita tana murna, motarshi kiran benz ya shiga itama ta shiga, jan motar yayi suka fita, saida suka hau titi tace "ya maheer na tambayeka?" gyaɗa kai yayi tace "ba zaka min faɗa ba?" girgiza kai yayi, ba zato ba tsammani yaji tace "meyasa ake yin s*x?" saida yaji kan motan yana neman kwace mishi daga hanu, da sauri ya kalleta, sannan ya kuma kallonta, da kyar ya saita kan motar yaci gaba da tafiya akan titi, bai bata amsa ba itama bata kara tambayanshi ba, har suka isa kofan school nasu, school ne me kyau wanda alama yaran masu hanu da shuni ne a ciki, a hankali ta ɗau ledanta dake kan cinyarta tasa a jaka, buɗe marfin motan tayi zata fita, juyawa tayi ta saci kallonshi, kallonta shima yake da sauri ta dukar da kai ta fita, rufe motan tayi yana kallonta harta shiga school, meyasa tayi mishi wannan tambayan? ko lokacin da akayi mata fyaɗe batayi mishi wannan tambayan ba sai yanzu, ko dai batasan meya faru da ita bane a lokacin? to me ya kawo wannan maganan? me take tunawa harta tambaye shi?" driving ya fara jikinshi a sanyaye, ita kuma tana shiga school taji dama batayi mishi wannan tambayan ba, yau duk karatun da akayi baya shiga kanta sosai, kunyan haɗuwa da maheer take, koda aka tashi madina tace "meyasa bakizo class namu a break ba?" cikin sanyin jiki kamar me zazzaɓi tace "babu kawai" mufeeda tace "kawai me? yawwa ya maheer ne ya kawoki ɗazu?" gyaɗa kai tayi "shine" "kinji daɗi mukam barinmu yake mu taka da kafa idan sani driver ya tafi" murmushi kawai tayi, sun kyaleta sabida basason taƙura mata da surutu, da haka suka koma gida tunda sukaci abinci ta shiga ɗaki bata kara yadda ta fito ba, har mangrib har Isha tana kunshe a ɗaki batason haɗuwa da maheer, koda ya dawo a gajiye yaje ya canja kaya, fitowa yayi yaga kowa a zaune hadda Abba suna dinner amma babu Janan, yace "madina where...." tace "tana ɗaki tun ɗazu taki fitowa" ya gane meyasa taki fitowa kawai yayi murmushi ya ɗau plate zaisa abinci yace "tafi abinci?" girgiza kai madina tayi tace "bataci ba na rana ma kaɗan taci cake da momy ta bata ma kaɗan taci tabar sauran a jaka" ya ɗau plate me ɗan faɗi yasa abincin dayawa akai, spoon biyu ya ɗauka da cup biyu da ruwan gora, ɗakinsu ya nufa madina ta kalli mufeeda itama ta kalleta, rufe baki mufeeda tayi madina ta kauda kai, momy na kallonsu batace komai ba, knocking yayi cikin sanyin murya tace "yees" dariya yaji amma ya dake baiyi ba, shiga yayi batasan shi bane, tana kwance rub da ciki tayi shiru, riga da wando ne a jikinta wandon gajere sosai sai rigan shima ba tsayi har cibiyanta a waje, gashinta ne ya rufe bayanta da yake a bayyane musamman hips nata da wandon ya bayyana juya baya yayi sannan yayi gyaran murya, da sauri taja bargo ta rufa har kanta, saida ya ɗan jima kafin ya juyo, ganin ta rufe kanta a bargo yace "tashi muci abinci" kamar zatayi kuka tace "na koshi" yace "me kikaci kika koshi?" tace "babu" yace "before I count three ki tashi, one....two" tashi tayi ta yaye bargon, sauka tayi a gadon ya ɗauke kai, yace "sa dogon riga" kallon jikinta tayi tabbas wannan ya kama jikinta amma ai shi yayanta ne kuma shi yace duk abinda su mufeeda zasuyi itama zata iya yi sabida itama kanwarshi ce, wandon da kaɗan ya wuce cinyarta, rigan kuma cibiyanta a waje, bata musa ba taje ta ɗau dogon riga after dress tasa, batasa bottle ɗin ba ta zauna a gabanshi kanta a kasa tayi shiru tana wasa da yatsunta, abincin ya matso dashi gabanta, yace "oya ci" ci ta fara shima yana ci saide hawaye take yi, ganin tana hawaye yace "na kara miki?" gyaɗa kai tayi cikin kukan tace "eh" dariya yayi wallahi janan idan tayi wani abin kamar karamar yarinya, yace "to" kara mata yaje yayi sannan ya dawo, taci ta koshi kafin tace "na gode" ido ya zuba mata, tasan ita yake kallo shiyasa taki kallonshi, a hankali yace "meyasa kike jin kunya na?" girgiza kai tayi alaman ba komai, yace "haka kawai kike jin kunya na?" ta gyaɗa kai, yace "ko dan tambayan da kimanin ɗazu?" shiru tayi, yace "kinsan meyasa ban baki amsa ba?" girgiza kai tayi, yace "sabida nima inaso na tambayeki" shiru tayi, yace "kin san meyasa mutum yake zama da ilimi sosai?" girgiza kai ta kuma yace "sabida yawan tambaya, duk me yawan tambaya yana zama da ilimi, to amma meyasa kikamin wannan tambayan?" shiru tayi, ganin batada alaman magana yace "kin ɗauke ni matsayin yayan da kuka fito ciki ɗaya?" jijjiga kai tayi yace "to ki ɗago ki kalleni kimin magana idan ba haka ba raina zai ɓaci kuma zan daina miki magana" da sauri ta ɗago tace "dan Allah kada ka daina min magana" yace "to ki bani amsa meyasa kika tambayeni?" murza yatsun hanunta tayi a hankali cikin muryanta me daɗin sauraro tace "naji ana magananshi ne" yace "Aina kika ji?" cikin sanyin murya tace "a wajen ƴan class namu shine na tambayesu suka ki bani amsa" yace "okay shekarunki nawa?" a hankali tace "goma sha tara" yace "to ki bari sai kin kai 20 zan faɗa miki kinji?" a hankali tace "to" yace "kuma kimin alkawari ba zaki kara yin irin wannan tambayan wa kowa ba, daga ni sai ni" tace "nayi alkawari" yace "good girl yanzu ki daina jin kunya mu dawo kamar da" tace "toh" yace "ya karatun me akayi muku yau?" nan ta saki jiki ta fara bashi labarin karatun da sukayi a school yau, ya rinƙa gyara mata inda akwai gyara, saida yaga ta sake dashi kafin yace "zanje nayi aikina saida safe" tashi tayi tace "zanje wajen momy" yace "okay" tare suka fita, tana rike da plate ɗin da sukaci abincin, tana zuwa taga momy akan sofa da sauri ta faɗa kanta, momy tace "zaki karasa ni" dariya tayi ta kwantar da kanta jikin momy tace "momy cake naki yayi daɗi nima na fara koyan yadda akeyi" momy tace "ai cake sai lokacin da nake barrack kinsan abbanku shine babban soja a cikin barikin hakan yasa duk suke zuwa siyan cake a wajena, duk sun sanshi kuma yana da sakin fuska da son mutane, duk masu birthday a wajena suke zuwa ina musu cake, tace "nima shaida ce Abba baida matsala da wani ne nazo gidannan ba zai yadda na zauna ba, amma shi ba damu yasan daga ina nake ba, baiji tsoron ko zan iya cutar dashi ba.." momy tace "kinga zaki fara kukan naki ko? get up nayi miki kitso" tashi tayi ta zauna a gaban momy ta kwantar da kanta akan cinyarta, momy tace "madina ɗauko man kitso" turo baki tayi tace "haba momy itace fa za'awa kitson kuma nice zan ɗauko mai? bacin ni ko zan mutu ba yadda kike kimin ba" momy tace "zaki tashi ne ko saina saɓa miki?" tashi tayi suka haɗa ido da janan, gwalo tayi mata, cikin masifa tace "momy kinga tana min gwalo ba?" momy tace "karka kike janan ba zata miki gwalo ba neman rikici kawai kike" kamar zatayi kuka taje ta ɗauko man ta dire a gefen momy, yana kallonta har time data yiwa madina gwalo ya ganta, yayi shiru a bakin kofarshi ya kasa ɗauke idonshi a kanta, mufeeda ce tazo wucewa ganin ya zubawa waje ɗaya ido ta kalli wajen, da sauri tace "yaya me kake kallo?" hararanta yayi sannan ya basar ya shiga ɗaki, taga janan yake kallo sauda dama tana kamashi yana kallonta shine bai sani ba, momy tana mata kitso tana bata labarin zamansu da sukayi a barrack, na dariya tayi dariya na bakin ciki kuma ta taya momy, da haka har suka gama kitson, godiya tayi ta kalli mufeeda da madeena sai bacci suke, sun saba bacci da wuri, tashinsu tayi tace "ku tashi mu tafi ɗaki" dukkansu baccin yayi nisa, momy tace "nikam saida safe" tace "good night momy" momy tace "good night my daughter" tafiya momy tayi, rike kwankwaso tayi tana kallon sama tana tuna abinda zatayi musu su tashi, dariya tayi ta zauna tayi kallon wani film da yake mata daɗi saida aka gama na yau kafin ta kashe tv, tashi tayi taje wajen frij ta buɗe, ruwa me sanyi ta ɗauko ta tsitsaya dayawa a cup, a hankali take tafiya sabida kada ruwan ya zube, jikinsu dake sanye da rigan bacci ta ɗaga cup ɗin ta watsa musu, atare suka tashi a firgice "waye?" cewar madina, rike ciki tayi tana dariya kamar zata faɗi kasa, madeena dirowa tayi daga kan kujeran taje frij ta ɗau goran ruwa, da gudu tabi bayanta itama gudun take tana cewa "dan Allah karki watsamin please and please" sanin cewar madina batada hakuri kawai tayi ɗakin maheer da gudu ta faɗa kan gadonshi da yake kwance yana bacci, shiga cikin blanket nashi tayi ta kankameshi tana "dan Allah, dan Allah" cikin bacci yaji muryanta kuma yaji an rikeshi, da sauri ya tashi yana kwacewa yace "janan meya sameki? waya shigo gidan?" a tsorace yake tambaya, janye blanket ɗin tayi a hankali take leka madina, ganin tana tsaye har yanzu a bakin kofa da roban ruwa tace "madina ce zata watsamin ruwan sanyi" tsaki yaja yace "kunada hankali kuwa? kunsan karfe nawa yanzu?" a hankali ta fito daga blanket ɗin ta sauka a gadon tace "kayi hakuri" yace "oya jeki kwanta dare yayi" fita tayi tana lekawa, tana fita ta kuma dawowa a guje ta faɗa gadon, runtse ido yayi sam bayason bacci ya yanke mishi, yace "madina idan baki kyaleta ba na fita zan ɓata miki rai" jin tayi shiru ya rike hanun janan yace "muje" tana rakuɓe a bayanshi har zuwa ɗakinsu, ruwan madina ta watsa ta zaci janan ce a farko, da sauri ta waro ido tace "yaya dan girman Allah kayi hakuri ban san kai bane" yace "shikenan kin rama?" tace "kayi hakuri" yace "tunda kin rama ki barta ta kwanta kada na kara jin komai idan kika kara saina saɓa miki wallahi" jin ya rantse tace "to ba zan kara ba" hawa gadon janan tayi yana kallonta ta rungume mufeeda wacce tun ɗazu take bacci, tace "saida safe" yace "Allah kaimu" madina a cike fam ta kwanta, saida ta kashe wuta janan tace "good night" jin batayi magana ba tace "good night unty madina mara hakuri" shiru tayi mata, ganin haka ta tashi cikin sanɗa ta cakuli madina, nanfa madina ta danneta akan gadon tace "wallahi saina rama" ihu ta fara tana kiran Ammi, kallon agogo yayi, jin bata daina ihun ba ya tashi ya tafi ɗakinsu, kunna wutan yayi nan yaga madina ta danneta ita kuma sai harba kafa take, yace "madeena wai kunsan karfe nawa ne yanzu?" sauka madina tayi daga kanta tace "wallahi itace ta tsokaneni yaya" yana ganin idon janan yasa batada gaskiya, yace "sauko" saukowa tayi ya rike hanunta suka fita, ɗakin momy yaje da ita yayi knocking kafin ya shiga, momy cikin bacci tace "maya faru?" yace "momy ta kwana anan itada madina basa sanin dare yayi" nuna mata gefen momy yayi yace "saura naji kin koma can" da sauri ta hau gadon ta rungume momy dama abinda take so kenan, ya lura da hakan, ji yayi tace

Chapter 4 of 9