Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
ɗan dake cikin cikinta ta rama abinda yayi mata ba, zuciyar janan ya bushe gangan jikinta ya amsa, kirjinta yana bugu da karfi, idanunta sun rufe babu abinda take ji take gani sai fansa, damke hanun minat tayi tace "na shirya" minat tace "duk harbin da zasuyi kada kiji tsoro ki tsaya kisa a ranki ko mutuwa ko rayuwa" jijjiga kai tayi tace "na amsa" da wani irin gudu suka fita a gidan, billy tace "gasu nan zasu gudu" jin haka yasa police suka buɗe wuta suka fara harbinsu suna binsu, cikin tsananin duhun daya karaɗe gari sabida rashin wuta suke gudu, police na bayansu suna harbi, ji kake tau a ƙafan janan, faɗuwa tayi kasa tana rike kafa tace "wayyo Allah minat ba zan iya ba" minat cikin tashin hankali taga jini yana zuba, ɗankwalin kanta ta cire ta ɗaure mata ƙafan tace "wa zaki bari ya ɗau miki fansa idan bake ba janan" girgiza kai tayi "minat na karaya" tace "babu karaya a tareda macen da akaci zalinta, babu karaya a tare da macen da take ɗauke da cikin data kusa haihuwa, idan ba zakiyi dan ke ba kiyi dan ɗan dake cikinki" da rarrafe suka shiga har cikin dajin dake gabansu, bishiyoyi da kuma kukan dabbobi da suke ji ya kara tabbatar musu suna cikin daji ne, sun daina jin karan sautin harbi, a karkashin wani babban bishiyan mangoro suka zauna, minat ta taimaka mata ta kwanta sannan itama ta zauna a gefenta sukayi shiru sai haƙi da minat take ita kuma janan tace "kafata tana zugi ki ciremin bullet dake kafata" kwance ƙafan tayi ta kunna tocin karamar wayarta sannan ta fara dubawa, kallon janan tayi wacce take a kwance sannan tasa hanu zata zame tace "anya zan iya?" da kyar tace "zaki iya minat ina jin azaba a jikina" rufe ido tayi ta zare bullet ɗin, kara me razanarwa janan tayi, tace "sannu" ɗaure mata ta kuma yi, janan tace "bayana kimin addu'a" Addu'a ta fara mata, saide ciwon kara karuwa yake, tace "idan na mutu minat inaso kimin wani abu" tace "ki daina maganan mutuwa" tace "ya zama dole, minat duk abinda na haifa ki kula min dashi kamar kece kika haifa, sannan ki nemi yayana nabeel yadda kika ganni haka yake babu abinda ya rabani dashi, kawai de shi namiji ne ni kuma macece, inaso a duk inda kika ganshi ki kashe shi, karki barshi a raye dan girman Allah, idan kikamin haka kin gama min komai" cikin kuka tace "meyasa kike wannan maganan? meyasa zaki kashe yayanki wanda kuka fito ciki ɗaya?" hanunta ta rike ta damke ka karfi tace "inajin haihuwa zanyi minat" cikin harshen larabci take karanta mata addu'o'in samun sauki da kuma wanda zata samu ta sauka lafiya, tace "minat ruwa" tashi tayi tace "zan nemo miki duk inda ruwa yake" tafiya ta fara da tocin tana duba cikin dajin, can ta hango katon kogi cike fam da ruwa, zuwa tayi ta rasa aina zata ɗiba, ta hango wani roba da gudu taje ta ɗauko, zuwa tayi ta fara ɗiba ruwan, kukan kura taji a bayanta, a firgice ta juyo, ido huɗu sukayi da kuran, jikinta ya fara rawa saide bata yadda ta zubar da ruwan ba, dabara ne ya faɗo mata lokacin daya tunkarota, shiga ruwan tayi ta kwanta luf, mumfashinta yana katsewa kamar zata mutu, saida ta daina jiyo sautin kukanshi sannan ta fito daga ruwan, haƙi take yi sosai da alama ta iya ruwa hakan yasa bata jiggata ba, da ruwan a hanu ta fara gudu har Allah yasa ta fara hango bishiyan data bar janan, da gudu ta karasa, murmushi me haɗe da kuka ya suɓuce mata lokacin da taji kukan jariri, saide murnan ya koma ciki ganin janan bata numfashi, ruwan ta ɗiba ta watsa mata a jiki, ganin bata motsa ba, ta kwantar da kanta a jikin janan ɗin ta fashe da wani irin ɗan marayan kuka tace "nayi shekara biyar a bariki ban taɓa haɗuwa da wacce naji hankalina ya kwanta da ita ba saike unty janan, kin haifi ɗan da kullum sai kinyi mishi kuka amma meyasa zaki tafi ki barni dashi? ta yaya zan iya ɗauka miki fansa? bacin kece kikejin zafi da raɗaɗin abinda akayi miki?" jariri yana kuka sosai ta ɗaukoshi ta ɗaurashi akan cikin janan, cikin jini suke su duka tace "kiji kukan jaririnki wanda kikace baki san mahaifinshi ba, ki tashi ki nema mishi mahaifinshi ki rama duk zalincin da akayi miki" shiru bata motsa ba da alama rai yayi hali, tashi minat tayi ta rungume yaron jikinta duk ya ɓaci da jini tace "shikenan na ɗaukeki kamar wacce muka fito ciki ɗaya zan tafi nima na daina zaman bariki na tuba na koma ga Allah kuma zan koma gidan kakata, ina fatan Allah yasa tana raye, tareda jaririn da kika haifa daga yau ya zama ɗana" tafiya ta fara, baka jin komai sai sautin kuka jariri da kuma karan ganyen da take takawa, a hankali ta buɗe idonta da yayi nauyi tace "minat?" wani irin dariya da kuka minat tayi a lokaci ɗaya, juyowa tayi ta faɗa kanta ta rungumesu da yaron, cikin nauyin murya da karfin hali tace "wannan shine ɗan dana haifa?" jijjiga kai tayi tana kuka tace "shine" a hankali ta buɗe hanu tace "bani shi" a kirjinta ta manna mata yaron tace "kin samu ɗa namiji" murmushi tayi tace "ya maheer ne ya dawomin" a hankali tace "kisa mishi albarka sannan kisa mishi suna" a hankali tace "Allah ya maka albarka, na raɗa mishi suna MAHEER" *Jiddah Ce...✍️* 08144818849 🌸🌸🌸🌸🌸 *ZOBEN WUTA* 🌸🌸🌸🌸🌸 By _Jiddah S Mapi_ *Chapter 9* *Daga wannan zan rufe free pages, sabida azumi dake zuwa shiyasa ba zanyi free pages dayawa ba, duk wanda yakeso ya biya 300 ta account 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay* ~Allah ya rayashi" a hankali tace "Ameen" tace "ke ƴar asalin wani gari ne unty janan?" tace "ni ƴar asalin kano ce anan aka haifeni" tace "ni kuma a Abuja aka haifeni inada zama a wajen kakata, zanso ki biyoni mu zauna acan idan har tana raye" tace "batada lafiya ne?" hawaye yana bin kuncinta tace "tanada lafiya amma yau shekarana biyar bana gida, na tafi na barta bansan halin da take ciki ba, haɗuwa ta dake yasa naji ina kaunar komawa gida, naji bariki duk ya fitamin a rai" janan ta dafa ta tace "ki daina kuka daga ganinki ke mutuniyar kirki ce, duba da ilimin addini da kike dashi, bansan meya kawoki nan ba amma naji a jikina bada sonki kike wannan abin ba" cikin kuka tace "janan mahaifina attajirin me kuɗi ne yanada dukiya sosai, kanin mahaifina ya kasance azzalumi shine ya kashe mahaifina ya kwashe dukiyanmu ya hanamu, ya kaini wajen kakata wacce ta haifi mamana, mamana ta jima da rasuwa, ya dawo yana farautar rayuwata, da kyar na tsira daga hanunshi na tafi na bar kakata na shiga duniya yanzu bansan ya take ba, ko tana raye ko ta mutu ban sani ba, da yunwa muke kwana da yunwa muke tashi, bata sani ba WATARANA DA DADDARE na gudu na haɗu da wata kawa ta nuna min gidan karuwan da yake kano a waya, hakan yasa na bita muka zo, na fara bin maza ina samun abinda zanci hakan yasa na manta dasu kakata da halin da nake ciki, a ranan da naga kinzo gidan naji tausayinki na tuna halin dana shiga a baya, ban kara jin zafin bariki da nake yi ba saida naga kinada ciki, tsorona kada ɗan da zaki haifa yazo duniya ya kalleni ina zina, wannan ma ba ɗan cikina ba idan ɗan cikina ne ya zanyi?" rungumeta janan tayi sannan tace "tunda Allah yasa kin gane gaskiya shikenan sai ki tuba izuwa gareshi sannan saiki koma wajen kakarki ki kula da ita, ba sai da kasuwanci ake ciyar da kai ba, ga sana'a dayawa wanda zaki iya yi ki taimaki kanki harma da kakarki" cikin kuka tace "kin yadda zaki bini Abuja mu koma gidan kakata da zama? i promise you babu abinda zai sameki kuma babu abinda zai sami ɗanki" a hankali ta jijjiga kai tace "na yadda amma kimin alkawari ɗaya" tace "koma na menene nayi miki" tace "kimin alkawari babu wanda zaisan nice na haifi maheer, duk wanda ya tambayeki kice maheer kanina ne" tace "insha Allah babu wanda zan faɗawa" tace "na gode" sun kwana a cikin dajin, garin Allah yana wayewa suka tashi kogin data ɗibo ruwa jiya can sukaje suka yiwa maheer wanka sannan itama janan tayi wanka, da kyar take tafiya minat ce rike da yaron har suka fita zuwa cikin gari, mashin suka shiga da kuɗin hanun minat, tasha suka nufa amma suna ɓoye fuskokinsu sabida kada ƴan sanda su gane su, motar Abuja suka shiga saida motan ya tashi sukayi hamdala, maheer yana kuka sosai a cikin motan a hankali take jijjigashi, ganin kukan yaki tsayawa ta ɓoyeshi da mayafin jikinta ta fara bashi nono, kin karɓa yayi, da sauri ta kalli meenat tace "meenat kinga yaki yadda dani, shima kenan zai kini kamar kowa? kenan shima baya sona?" kuka take yi sosai, meenat ce ta karɓeshi tana jijjigashi atake yayi shiru, jingina tayi da motan tana kuka sosai har suka bar garin kano. basu isa Abuja ba sai yamma likis sabida motarsu ya tsaya a hanya, ana dab da mangrib suka sauka a motar, meenat ta goya maheer ita kuma janan tana fama da ciwon ciki, mashin ta tara cikin sanyin jiki da jin kunyan haɗa ido da kaka tace "maitama" shiga sukayi sai a sannan ta fara kuka me taɓa zuciya, dauriya janan tayi tana bata hakuri har suka isa unguwar, a farkon layin gidan yake tace "anan ya isa" gida ne me bakin kofa da alama kakarta batada karfi, biyan me taxi kuɗi sukayi sannan ta tsaya a bakin kofa tace "janan ki fara shiga" girgiza kai tayi tace "haba meenat ta yaya zan fara shiga nida bata sanni ba, keda ta sani ai kece zaki tsaya a farko" tace "ina jin kunyan kaka" tace "ki daure mu shiga" da kyar ta lallaɓata ta shiga gaba, sallama tayi da sauri aka amsa, wata tsohuwa ce zaune a tsakar gida kan tabarma hanunta rike da carbi tana lazimi, jin muryan meenat ta tashi tana cewa "muryan waye kamar na ameenatu?" shiru meenat tayi hawaye yana wanke mata fuska, farin ciki sosai ya bayyana a fuskan kaka tace "meenat kece kika dawo? dama nasan ba zaki tafi ki barni ba nasan zaki dawo meenat" da gudu taje ta rungume kaka, kaka tace "wannan waye a bayanki?" cikin kuka tace "kanin sabuwar kawata kuma yayata ne sunanta janan" kallon janan tayi taga ta sunkuyar da kai, tace "zo nan jikata" zuwa ta tsaya tana wasa da farcenta, kaka ta janyota ta rungumesu su duka, tace "koma wacece ke tunda meenat tana sonki nima ina sonki sosai, sannan zamu zauna dake anan kinji?" gyaɗa kai tayi tace "na gode" "ki daina kuka bari nasa muku ruwan zafi kuyi wanka kuci abinci sai kuyi salla ku zauna ku bani labari" da kanta tasa musu ruwan zafi, da alama tanada tsafta sosai domin toilet nata a wanke, ga sabulu da soso, meenat ce ta yiwa maheer wanka itama janan tayi wanka da ruwan zafi sosai, kaka tace "tunda jikin wannan ɗin naga harda ciwo bari na kara mata ruwan zafin" kara mata tayi ai kuwa taji sauki data samu ruwan, da ɗingishi ta shiga ɗakin ta kwanta, abinci ta kawo musu me zafi shinkafa da wake sannan da kunun gyaɗa me daɗi a cikin flask, janan ce tasha kunun sosai sannan taci abincin, itama meenat cikin yunwa take cin abincin saida suka koshi dam Allah yasa maheer yayi bacci hakan yasa ta kwanta itama akan gadon kaka nan take baccin gajiya ya kwashesu su duka biyu suke baccin kamar waɗanda suka suma, a lokacin daya tashi kuka yake sosai, kaka ce ta ɗaukeshi tace "Allah sarki jariri watakila mahaifiyarka mutuwa tayi, bari yayar taka ta tashi saita baka nono, ko kuma na baka madaran shanu?" jin yayi shiru tace "masha Allah ban taɓa ganin kyakkyawan jariri kosashe kamar wannan ba, wannan se kace ɗan turawa" fita tayi ta buɗe wani roba ta ciro madaran shanu ta zuba a karamin cup ta ɗau cokalin cin shinkafa ɗan karami sosai sannan ta koma ɗakin, addu'a tayi a cikin madaran daga karshe tace "Allah ya tsareka da sharrin baki da sharrin ido" bashi madaran ta fara, ya buɗe baki yana sha, saida ta tabbatar ya koshi sannan taga ya fara rufe ido alama zaiyi bacci, kwantar dashi tayi a gefen janan nan take ya fara bacci. sune basu tashi ba sai karfe ɗaya na dare nan ma janan ta kara shan kunun sannan ta kara komawa baccin ganin yaron yana bacci taji hankalinta ya kara kwanciya, kaka tayi mamakin irin baccin da sukayi. washe gari sallan asuba sukayi suka gaida kaka nan kuma wani bacci ya kara daukansu, kaka abincin karyawa tayi musu ganin sunsha kunu dayawa yasa ta kara dama musu wani, sai karfe sha ɗaya na rana janan ta tashi, maheer na hanun minat tana shafa mishi mai da alama wanka sukayi, murmushi tayi mata tace "kin tashi?" gyaɗa kai tayi ta zauna tace "wanka kuka yi?" abincin ta tura mata sannan ta cika mata cup da kunun tace "ci abinci kema ga can ruwanki akan wuta" ci tayi dan tana jin yunwa sosai, saida ta koshi ta ɗaura zanin minat ɗin ta shiga wanka, ruwan zafi sosai tayi wanka dashi, ta dawo ɗakin, kayan meenat ɗin ta kara sawa sannan ta zauna zuwa yanzu sun gama hutawa, kaka tazo ta zauna kusa dasu tayi shiru, meenat tace "ba abinda ya canja ko kaka?" tace "babu abinda ya canja saima abinda ya kara zafi meenat, tunda kika tafi wahala kawai nakesha, aiki nake zuwa kullum da safe a wani ƙaramin company ina musu goge goge da haka nake samun kuɗi ina siyan abinci, babu komai sai abinda nayi kullum ina cikin bakin ciki gashi bakya kusa dani damuwa yamin yawa" kuka take yi, meenat ma tana tayata, janan ta daure tace "yanzu tunda munzo wajenki aiki ya dawo hanunmu, daga yau kin daina goge goge a company ni janan nice zanyi kuma nayi alkawari" meenat zatayi magana ta ɗaga mata hanu tareda girgiza kai tace "no meenat kin gama kokarinki tun lokacin da kika ciyar dani kika taimakamin na dawo gidanku da zama, now is my turn, koda nisan company ya kai daga nan zuwa kano nayi alkawarin zuwa nayi aiki acan matukar zan gyara rayuwarki dana kaka da kuma maheer, zan baki amanan maheer ki kula dashi domin kece uwa yanzu a gareshi ni janan zan karɓi aikin da kaka take yi ku huta domin nasan kun gaji a rayuwa" zatayi magana tace "please banaso kice komai" shiru kaka tayi su duka sukayi shiru, kallon maheer tayi dake hanun minat, taji wani irin sanyi a ranta wanda bata taɓa jinshi ba, taji kamar ta haɗiye yaron dan so, ita kanta tasan yaron yana tsananin kama da ita, hakan yasa ya kara shiga ranta, tunawa tayi da maheer a fili ta share hawaye tace "Allah yaji kanka yasa kana gidan Aljanna, nasan da kana raye da ina tare da kai" minat tace "ki daina kuka" a hankali tace "ya zama dole minat nasa ya maheer a raina, ban taɓa jin soyayya akan kowa ba, ban taɓa sanin menene soyayya ba sai akan ya maheer ina ma Allah ya dawomin dashi duniya koda sau ɗaya ne na kara ganinshi, shine mutum na farko daya fara sa dariya akan wannan fuskan nawa, shine mutum na farko daya jani a jiki bai nuna min kyama ba, shine mutum na farko daya koyamin soyayya, shine mutum na farko daya koya min karatu da kuma turanci, sannan shine mutum na farko da zanso kuma shine mutum na farko da zan mutu dashi a cikin zuciyata, kuma shine mutum na farko da bazan taɓa mantawa dashi ba, kuma shine mutum na farko da zan riƙa yiwa addu'a babu dare babu rana, kuma shine mutum na farko da ko me kama dashi na gani zanji ina son meshi, haka zalika shine mutum na farko da za'a tambayeni in mutu a dawo dashi duniya zan amince...." kuka ne ya hanata karasa sauran maganan, meenat tace "kiyi hakuri ki daina wannan kukan janan zaki sawa kanki ciwo, kukan yayi yawa babu ranan da garin Allah zai waye bakiyi kuka ba?" cikin dauriya tace "ya zama dole na daina kuka ko dan wannan yaron me suna maheer dake hanunki" juyawa tayi ta kalli kaka sannan tace "kaka koda zamu ɓoyewa kowa ke bazan ɓoye miki ba maheer ɗana ne" murmushi kaka tayi tace "nifa ba yarinya bace jikata, tunda na ganshi kuma na ganki nasan ɗanki ne, amma bansan dalilin ɓoyewa da kukayi ba hakan yasa nima nayi shiru kuma zanci gaba da ɓoyewa kamar yadda kuke so maheer kaninki ne" murmushi tayi ta share hawayen tace "na gode, gobe akwai aiki zaki kaini company nice zan fara zuwa ba ke ba" kaka zata yi musu tace "dan girman Allah kada kice a,a" a hankali tace "to shikenan Allah ya miki albarka" a hankali tace "Ameen" wunin ranan sunyi cikin hira, kaka ce take basu labari wani suyi dariya wani kuma suyi kuka. washe gari, kaka ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani, janan ya kalleta tace "kakus wannan dressing ɗin na zuwa wajen aiki haka kikeyi?" kaka tace "wannan wajen aikin fa ba kamar kowanne bane, ina faɗa miki uniform za'a baki kisa idan kinje sannan wallahi me company ɗin baida mutunci ko kaɗan, mugu ne sosai mara imani, gashi kyakkyawa baiyi kalan mugaye ba amma wallahi ban taɓa ganin mara dariya mara fara'a irin shi ba, kinga ni wannan tsohuwan?" janan tana kallonta tace "eh" tace "akwai ranan daya kusa marina, akwai ranan daya sa wuta a company ɗin mutane suna ciki suna aiki, da kyar Allah yasa aka kashe wutan a ranan ƴan gidansu ne suka zo suka tafi dashi, to amma abinda yake ɗauremin kai kuma yake bani mamaki watarana yana zama me hankali sosai, watarana idan yazo company da kanshi yake kiranmu muyi hira, watarana har kuɗi yake bani yace na hau taxi, to gaskiya abinda ban fahimta ba shine yana iya canja hali ne? ko dai shi ɗin yanada ra'ayi guda biyu ne? ko kuma yanada hali guda biyu? shiyasa banaso kije company ɗinnan domin fa zaki iya fuskanatar matsala, zai iya miki komai idan ranshi ya ɓaci" murmushi tayi tace "kaka ba sai kayi laifi kafin za'a maka abu ba?" kaka tace "duk yadda zanyi miki bayani ba zaki fahimta ba janan amma muje nasan da kanki zaki ce kin fasa" tace "bama zance ba" riga da siket tasa na atamfa da hijabi fari sannan ta kalli meenat dake goye da maheer tana aiki tace "anyi ruwan sama nasan gari a jike yake gara ki canja hijabi kisa baki" tace "a,a barni da farin dai" zuwa tayi ta yiwa maheer kiss a goshi sannan tace "mun tafi" turo baki meenat tayi tace "ni ba zakimin ba?" murmushi tayi wanda yake kara mata kyau sannan tayi mata kiss a goshi tace "mun tafi" tace "Allah ya bada sa'a Allah yasa ki shiga company ɗinnan a sa'a Allah ya tsareki da sharrin makiya" a hankali tace "Ameen kanwata" kaka tace "fito mu tafi kada muyi late idan ya rigamu zuwa za'a kulle get" tafiya sukayi kaka na bata labari har suka samu taxi suka shiga, kaka tace "ABEEDEEN MOTORS" kasancewar babu wanda baisan sunan company ɗinba hakan yasa yace su shiga, company ne da suka kware wajen kawo motoci da mashuna, duk wani tsadadden motan da yake duniya akwaishi a wannan company, suna da hannun jari da manyan manyan masu motocin duniya, hakan yasa company ya shahara a duniya, ba wannan ba Abeedeen motors suna iya kera motoci da kansu, ba kowa bane yasan Abeedeen mutum biyu ne, kowa ya zaci abeedeen mutum ɗaya ne, Abeed shine me ƙwaƙwalwa da matukar basira shine yake kera motoci, yayinda Deen yake safa da marwa wajen shigar da motocin zuwa manyan company na duniya, a cewar mutane Abeedeen shine yake kera motoci kuma shi yake siyarwa, Ammi dasu kaɗai suka san wannan sirrin. Janan wacce gabanta yake faɗuwa tace "kaka to Abeedeen ɗin shine yake faɗa a company?" kaka tace "shi Abeedeen mutum ɗaya ne me hali biyu, watarana yazo mana a me hankali watarana kuma mahaukaci ya fishi nutsuwa, bari na gaya miki wani abu Abeedeen yana shan giya watarana a bige yake shigowa company, watarana kuma da kanshi yake yiwa masu shan giya wa'azi akan su dena" shiru tayi tana mamaki, tace "kaka to meyasa yasa wuta a company da mutane a ciki?" tace "sabida yaga wani hoto guda ɗaya kawai a hanun wani cleaner wanda ya share office ɗin daya jima ya fitar da hotona" tace "to kaka wani hoto ne yasa har yasa wuta a company?" tace "to wasu sunce wani babban mutum ne sanye da manyan kaya amma ni ban gane musu ba ni ranan ma gudu nake ina kokarin tsallake katanga" dariya ta kwashe dashi sannan tace "kaka to zaki tsallaka katanga ai da kin tsaya keda kika tsufa ai saiki taimakawa waɗanda suke da sauran shekaru ke kuma kiyi shahada" zagi ta aika mata tace "kinci gidanku nida naga wata budurwa tana gudu da yanga wai zata haura katanga na tureta nace wani ya ɗagani na dira ana wasa da rai ne?" dariya tayi, taxi ɗin ya tsaya kaka tace "lafiya ɗannan?" yace "wallahi mai ya kare" kaka tace "kai ka sani kuma bazan biyaka duka kuɗin ba rabi zan baka" yace "haba mana abinda ga can company mun iso taku nawa ya rage ku shiga?" Janan tace "kaka bashi kuɗinshi tunda ba nisa" kaka ta buga tsalle tasa kwalli a ido ta hanashi sauran kuɗin, saida janan ta bashi hakuri kafin yace ya yafe, dariya kawai take amma ba har cikin ranta ba, cike take da kewan ya maheer dasu madeena so take ta manta baya amma hakan ya gagara, tafiya suke tana kara jin bugun zuciyarta yana tsananta, daga nesa ta fara hango wani babban get ɗin da yake walƙi anyi rubutu da manyan harufa yana kawo wuta a jikin an rubuta "ABEEDEEN MOTORS" ganin sunan kaɗai yanasa gabanta yana faɗuwa, tayi tunanin kodan abinda kaka ta faɗa mata ne akanshi yasa takejin bugun zuciya, juyowa tayi zata yiwa kaka magana taji saukan ruwan taɓo a fuskanta, runtse ido tayi ganin farin hijabinta ya lalace da ruwan ya koma kalan kasa, ga fuskanta daya ɓaci da caɓi baka iya ganinta da kyau, a hankali ta fara buɗe idon ganin waye yayi mata wannan ɗanyen aiki, waye ya kara mata zafi a ranta akan zafin rabuwa da maheer da tunaninshi da take yanzu? waye ya ɓata mata kyakkyawan fuskan da idan ta gani take murmushi sabida ya maheer yace a duk sanda yaga fuskan yana samun nutsuwa a zuciyarshi, ido huɗu sukayi dashi, saida taji wani abu ya daki kirjinta ya tokare maƙogaronta, idanunshi masu kama dana mage ya zuba mata yana daga zaune a cikin motan, sanye yake da baƙin suit ya yiwa gashin kanshi style me kyau, sajenshi ya kwanta luf akan fuskarshi, ɗan karamin bakinshi ɗauke da cingum yana ci, farin mota kirarren mota yake ciki motan ma ya ɓaci da ruwan, kallon sama da kasa yayi mata sannan ya ɗaga glass ɗin daya sauke ya kara fesa mata sauran ruwan dake gefen, wannan karon ba hijabinta ba har kayan jikinta saida ya jiƙe jagab da ruwan dattin, barin wajen yayi ya shige company, zuciyanta kamar wuta haka take ji yana zafi, jikinta ya fara zafi kamar yadda kirjinta yake tafasa, kaka wacce tayi shiru a gefe sai yanzu tazo ta rike hanunta, ganin mutane suna kallonsu tace "janan mu koma gida na hakura da aikin" abin mamaki tasa hanu ta share ruwan daya ɓata mata fuska, murmushi take yi sosai har fararen hakoranta suka bayyana gefen kumatunta ya lotsa, ta riko hanun kaka tace "sabida wannan shine zaki hakura da aikin da kike ci kuma kike sha a ciki? sabida ɗan wannan ruwan daya watsa min bada saninshi ba zaki hakura kaka? nice fa janan wacce nayi miki alkawarin zan karɓi aikinki nayi da kaina to idan wannan ya ɓatamin rai na hakura kema kin hakura wani aiki zamuyi kuma a gaba? baka cin halal saika wahala" ganin tayi shiru, tasa yatsa ta lakaci kumatunta tace "kaka rakani muje ciki kisa hanu nima nasa hanu kamar yadda kikace anayi idan za'a sauya me aiki kuma kince

Chapter 8 of 9