sannan suka kalli janan a tare, yadda take kallonshi tana smiling abin ya birgesu sosai, ido suka haɗa lokacin daya sauko daga kan stair, murmushi yayi mata sannan yayi mata alaman tayi kyau da yatsun hanunshi, sunnar da kai kasa tayi tana wasa da spoon na hanunta akan plate ɗin data zuba shinkafa kaɗan da stew, zama yayi yace "momy good morning"
tace "morning maheer how are you?"
yace "fine, Abba good morning"
Abba yace "morning how was your night?"
yace "fantastic"
madeena da mufeeda tare sukace "good morning ya maheer"
yace "morning"
a hankali cikin siririn muryanta tace "good morning"
a hankali yace "how are you?"
tace "fine how was your night?"
murmushi yayi me kyau ganin ta fara koyon turanci, tana da saurin fahimta, da alama batasan meta faɗa ba taji Abba ne ya faɗa, yace "fine and your's?"
shiru tayi tana kallonshi da manyan idanunta, murmushin gefen baki yayi yace "dama baki san me kika faɗa ba?"
tace "ban sani ba"
yace "to ana nufin ya darenki"
tace "to me zance idan an tambaya?"
yace "zaki ce it was fine"
tace "it was fine thank you"
yace "good"
murmushi take yi alaman taji daɗi da yace mata good, abinci ya zuba ya fara ci, Abba yace "zaka fara zuwa office ko gidansu khairat?"
yace "gidansu khairat zanje first"
momy tace "ka gaishesu sosai"
yace "zasu ji"
tashi yayi zai tafi yace "saina dawo"
duk suka amsa da "Allah ya tsare"
fita yayi sojan yake bashi tsaro ya buɗe mishi mota ya shiga, tafiya yayi zuwa gidansu khairat, ya jima a bakin get kafin suka buɗe mishi ya shiga, direct falo ɗinau ya nufa ya zauna kafin ya mata text ya shigo, babu jimawa ta shigo, tayi kyau cikin atamfa dogon riga fited gown, ya matukar kama jikinta ko mayafi babu tazo tace "me kazo kayi min maheer?"
tashi yayi yace "kiyi hakuri nasan ban kyauta ba amma ina sanki"
juya baya tayi tace "you don't love me maheer, da kana sona ba zaka taɓa yadda wani dalili ya hanaka zuwa ka haɗu da Abbana a ranan can ba, kuma na kira gidanku sunce ka fita ashe karya kayi min"
yace "ba karya nayi miki ba khairat wallahi wani babban dalili ne yasa banzo ba"
"wani irin dalili ne wanda yafi khairat muhimmanci a wajenka?"
yace "ki nutsu ki saurareni"
cikin damuwa tace "yarinyar da ka kai gidanku itace dalilin?"
da mamaki yace "eh amma..."
"amma me?"
ta faɗa cikin tsananin kishi da ɓacin rai, yace "ki nutsu mana khairat"
"babu nutsuwan da zanyi maheer baka sona"
kuka ta fashe dashi tace "Abbana ya tafi hakan yayi maka daɗi?"
hanunta ya rike ta fizge cikin ɓacin rai tace "akan mace kaki zuwa haɗuwa da Abbana ka rusa duk tanadin da muka yiwa wannan ranan? shekara nawa mukayi muna soyayya? ka rusa a rana ɗaya ka ɓata komai, ka ɓata komai, ka ɓata komai maheer, I hate you, I hate you maheer"
kalamanta suna mishi tsananin zafi da ciwo, yana son khairat kamar ya cinyeta amma wannan kalman yana mishi zafi, ko sau ɗaya ta tsaya taji uzurinshi"
juya mishi baya tayi tace "shikenan sai kaje ka aure wacce kake so har ka ɗauketa ka kaita gidanku kayi using ɗina ni kuma kayi dump....."
cikin tsawa yace "ya isa khairat, an gaya miki na ɗauke ta na kaita gidanmu ne dan wani abu? Itama ba dan sonta tazo gidanmu ba, meyasa kike gayamin wannan banzan maganan?"
juyowa tayi tana fuskantanshi tace "banzan magana? banzan magana fa kace, cikin ni da kai waye yayi banzan magana? bama banzan magana ba kai kanka banza ne yanzu mahe...."
dafe kunci tayi lokacin da taji saukan gigitaccen mari, idanu a waje ta ɗago kai tana kallonshi, mamaki ya hanata cire hanu daga fuskanta, tace "marina kayi maheer?"
yace "kwarai kuma kikaci gaba da gayamin maganganu masu ɗaci sai nayi miki abinda yafi mari"
cikin tsananin ƙuna da ɗacin rai tace "akan karuwar daka ɗauko ka kaita gidanku dan ka samu daman lalata da ita a koda yaushe shine zaka mare...."
wani marin ya kuma ɗauke ta dashi, atake fuskanta ya koma jajur, ta kasa koda kyafta ido ne, zuwa yanzu duka hannu biyu ta dafe fuskanta dasu, kanta kasa, ko a mafarki akace maheer zai mareta ba zata taɓa yadda ba, soyayyan da yake nuna mata itama take nuna mishi yafi karfin ace maheer yayi mata koda tsawa ne bale mari, da yatsa ya nuna ta
"koda wasa kika kara alakantani da zina saina miki abinda ba zaki taɓa mantawa ba harki koma gaban Allah"
cikin shocking tace "ban tsaneka ba kasan wana tsana?"
bai mata magana ba dan shima a tafarfashe yake
tace "wannan karuwar taka na tsana"
murɗa handle na kofan yayi zai fita tace "ba tsananka nayi ba kai kinka nayi, kasan gara ka tsani mutum akan ka kishi, maheer I hate you"
kalman daya faɗa mata yafi marin da yayi mata zafi yace "I hate you too khairat"
buɗe kofan yayi ya fita daga gidan ma gaba ɗaya a zuciye, faɗuwa tayi akan sofa ta rasa me zata fara yi, hanu biyu ta ɗaura akanta cikin ihu tace "wayyo wayyo wayyooooooooo"
kamar zata fasa gidan, da gudu wata kyakkyawar mace ta shigo, da alama itace mahaifiyar khairat domin kuwa suna kama, tana sanye da tsadadden leshi green, fara ce sal kamar khairat ɗin, rike khairat tayi ganin ta fara watsi da kayan ɗakin tana ihu, cikin tsoro tace "meya sameki? me kikeyi haka? kin haukace ne?"
rungumeta tayi ta fashe da kuka me cin rai tace "maheer ne ya mareni maheer ne ya mareni umma"
bubbuga bayanta take a hankali tace "mari kuma? me kikayi mishi?"
kasa magana tayi, sakinta tayi taje kan tv stand ta ɗau wayarta tana kallon hotonsu dake gaban wayar, sunyi anko da maheer na shadda brown, yana zaune akan kujera ta rungumeshi ta baya suna dariya, buga wayan tayi da kasa, atake ya tarwatse, kwanciya tayi a kasa tace "shikenan komai ya kare tsakanina da maheer umma, Abba yace ba sona yake ba, da yana sona ba zai yadda da kowani dalilin da zai hanashi zuwa ya haɗu dashi ba, sai yau na tabbatar da gaskiya Abba yake faɗamin, umma help with my broken heart"
kukan da take yi yasa jikin umma yin sanyi sosai, da kyar ta samu ta lallasheta ta daina ihun kukan, kwantar da kanta tayi a kafar umma tana hawaye, umma sai shafa kanta take tayi shiru itama, bataji daɗin wannan rushewan soyayyan ba, koma meya rusa soyayyan maheer da khairat to lalle wannan ba karamin abu bane, kuma abin ba karamin sharri bane a wajen al'umma
cewar umma a zuciyarta take magana, da kyar ta samu tayi bacci idonta ɗauke da hawaye.
maheer yana fita ya nufi gida, yana sallama janan ta taso da sauri taje inda yake "tace "kaga na fara rubutun da kaina kuma zan iya karan...."
cikin tsawa yace "matsamin na wuce!!!"
a firgice ta wurgar da takaddan hanunta, jikinta ya fara rawa idanunta suka kara girma, jingina tayi da jikin bango ta fara ɓoye kanta ta yadda ba wanda zai ganta, a hankali ta silale kasa tasa hanu duka biyu ta toshe kunnuwanta ta runtse ido, harya wuce sai kuma ya dawo da baya, ganin halin data shiga daga yi mata tsawa, ji yayi jikinshi yayi sanyi a hankali ya dawo inda take, durkusawa yayi, zuwa lokacin tasa kanta a tsakanin kafafunta tana cigaba da toshe kunne, taɓata yayi a firgice ta kalleshi shima saida yaji tsoro, baya ta fara tana cewa "kayi hakuri bazan kara ba"
girgiza mata kai yayi yana kokarin ɓoye halin da yake ciki yace "bakimin komai ba ni zan baki hakuri"
tace "kayi hakuri kaji?"
tausayi yaji ta bashi, yace "kawo takaddan naga rubutun"
a tsorace ta tashi ta ɗau takaddan, daga baya ta mika mishi, yace "zo mu karanta tare"
har yanzu jikinta bai daina rawa ba, ta zauna kusa dashi ya fara duba rubutun, tayi kokari sosai amma har yanzu da gyara, yace "good girl gaskiya kinada kokari sosai, amma sai kin kara dagewa jibi saina kaiki school ko?"
gyaɗa kai tayi' yace "good"
murmushi tayi yace "bari na shiga nazo ɗaukan abu ne yanzu zan koma"
gyaɗa mishi kai tayi yace "je kici gaba da karatu"
tashi tayi taje ta zauna a kasa kusada kujera ta fara karatun, jikinshi a mace ya shiga ɗakinshi, meya sata tsoro haka? meyasa ta firgita daga wannan tsawan da yayi mata?
dafa kanshi yayi yace "ya Allah ka taimakeni nayi abu me kyau banso rabuwa da khairat ba amma batada manners"
laptop ya ɗauka kana ya fita daga ɗakin, murmushi yayi lokacin da yaga ta ɗaura kanta a cinyar madina tana karatu, ita kuma madeena chatting take a waya, haka kawai ya fara neman kuncin da yake ciki ya rasa, madeena tace "yaya ka dawo ne?"
"Eh zan koma yanzu"
"ya unty khairat?"
shiru yayi, ganin zai fita janan tace "Allah ya bada sa'a Allah ya tsare"
"Ameen"
ranshi yaji sanyi sosai, madina tace "wannan dai watarana yana fara'a watarana kamar zaki"
dariya janan tayi.
Parking na kayansu Deen yake a babban jaka, shi kuma Abeed yana zaune akan gado yayi shiru yana kallon Deen ɗin, towel ne ɗaure a waist nashi tun ɗazu yake zaune kuma a hakan wai wanka zai shiga, ɗago kai Deen yayi ya kalleshi kana yaci gaba da shirya kayan, brush na Abeed ɗin ya ɗauka da turare da sauran kayanshi yana sawa a jakan yace "wai meyasa ka zauna shiru ne yau? me yake damunka?"
tsaki yaja kaɗan yace "jikina is so weak haka kawai naji kamar akwai abinda zan bari a garinnan babban abu kuma"
murmushi Deen yayi yace "kana nufin baka son komawa gida?"
girgiza kai yayi "inaso amma na kasa samun peace of mind kamar akwai abinda zan bari anan kano"
Deen yace "babu abinda zaka bari anan kano wanda baka dashi a Abuja, nasan Abuja ma yafi maka nan sau dubu domin acan kake cin karenka babu babbaka naga ma kwana biyun nan ka rage duk abinda kake yi marasa kyau ina fatan daga nan har mu koma gida ba zaka kara aikata komai ba"
tsaki yaja yace "kaifa wani lokaci bakada wayo Deen, saika rinƙa yin abu kamar ɗan kauye bayan ka fini wayewa da sanin komai a duniya, kaifa kayi tafiya kasashe daban daban, ni kuma kasan ai banda gida babu inda Ammi take barina ina zuwa"
yayi maganan kamar zaiyi kuka,
Deen yazo gefenshi ya zauna, ya dafashi yace "kada wannan abin ya tsaya maka a rai mana Beed, kafi kowa sanin dalilin Ammi na yin haka, kuma kasan bata jin daɗi taji kana faɗan haka please stop it, kaine da beed nawa"
yace "but..."
jan hanunshi yayi yace "but what? but kaje kayi wanka oya get up"
tashi yayi yana turashi har zuwa toilet, rufe kofan yayi bayan ya turashi ciki, jingina Deen yayi da jikin kofan yayi shiru, hawaye ya cika mishi ido da sauri ya share sannan ya koma ya gama shirya musu kayan, Beed ya fito yana ɗaure da towel wajen mirror yaje zai yaye towel ɗin Deen yace "idan baka daina wannan ɗabi'an na yaye towel ba tareda ka duba akwai mutum a ɗakin ba zaka zo ka aikata abin kunya"
baiyi magana ba, Deen ya shiga toilet ɗin kawai dan yasan halin ɗan uwanshi, koda yayi wanka ya fito yaga Abeed cikin shiga na riga da wando na shadda fari kal, yayi matukar kyau sosai ya taje gashinshi dake a harhaɗe, yasa hula ɗinkin bama fari, agogon hanunshi fari ne, haka takalmin kafarshi cover shoe ne fari, Bluetooth yasa a fari a kunne, ya fito kamar balaraben daya sa kayan hausawa, daga sama har kasa Deen ya kalleshi rabon da Abeed yayi shiga irin wannan tun ranan auren abokinsu Taheer yau shekara biyu kenan, yace "you look very very very very...."
yace "handsome"
dariya Deen yayi jin ya karasa mishi, yace "kaga yadda kayi kyau kuwa? yau me yazo kanka kayi wannan dressing ɗin ko dai ka samu ƴar hausa ne?"
ɓata rai yayi yace "dama ai inada kyau, ko banyi dressing ba i know"
rike waist Deen yayi yace "umm kaine mutum na farko me yabon kanshi kafin a yabe shi"
lumshe ido ya fara, Deen yace "bari na shirya naga ka fara lumshe ido naga so kake mu kara zama anan garin jirginmu zai tashi 12"
da sauri sauri ya fara shiri, shima irin kayan Abeed ɗin yasa harma da irin hulan, agogo da komai anko sukayi, turarensu me kamshin gaske ya buɗe ya fesa a jikinshi, kana ya fesawa Abeed, makullin motan da zasuje airport dashi ya ɗauka, sannan ya ɗau wayarshi iPhone 16 wanda yasa mishi farin cover, irin na Abeed ɗin, mikawa Abeed yayi yace "rike naja trolley mu tafi kada muyi late"
karɓa yayi yasa a aljihu, idan basu ba babu wanda zai iya cewa ga Abeed ko ga Deen, ko Ammi ba ganesu take yi ba bale mutanen waje, idan ka gansu haka inda zaka gane Beed shine baya dariya, Deen kuma yanada fara'a da yawan surutu shi kuma Beed yana haɗa rai kuma baida surutu"
amma idan suna hira a tare ba zaka iya ganesu ba, fita sukayi Deen ya rufe kofan gidan, trolley suka sa a motar sannan suka shiga Deen yace "kai zakayi driving"
girgiza kai yayi kana ya shagwaɓe fuska, taɓe ƙaramin bakinshi yayi yace "am not in the mood koda na karɓa bazan iya driving ba"
da mamaki Deen yace "kaida kake son yin driving idan zamu fita tare yau meya sameka? ko dai wani abin kake ɓoyemin, please ka faɗamin gaskiya karka ɓoyemin komai"
ganin hankalin deen ya tashi yace "relax ba komai, bani key nayi driving"
mika mishi yayi dan son tabbatar da yana lafiya ko akwai damuwa.
shiga yayi ya zauna shima deen ya zauna, tada motan yayi suka fara tafiya, a hankali yake driving saide yana jin sauyin yanayi a tare dashi, kallon agogo deen yayi yace "saika kara sauri mun kusa late"
ɗan gudu ya fara, atake yaji kanshi yana sarawa, ji yayi ana kiran sunan mama, kokarin dannewa yake yaji abin yana yawa, tuna moment ɗin da abin ya faru ya fara, sunan mama da take kira har yau ya kasa fita a kanshi, ganin zasu faɗi deen yayi sauri ya rike stairy ɗin yace "easy Beed me kake tunani haka?"
da kyar ya samu ya tsaida motan, dafa kai beed yayi, yace "me yake faruwa ne? meyasa kake ɓoyemin halin da kake ciki?"
buɗe marfin motan yayi yace "ba komai nace maka kazo kayi driving ba zan iya ba"
fitowa yayi suka canja waje, runtse ido yayi baya son tuna abinda ya faru saide har yanzu bai daina jin muryanta a tsakar kanshi ba, kwana biyu ɓoyewa Deen yake amma baya samun bacci, daya rufe ido zaiji muryanta tana kiran mama, da haka suka isa airport, har suka shiga jirgi bai nutsu ba, deen yace "dan Allah ka faɗamin gaskiya me yake damunka, ina gani da kwana biyu baka bacci Beed kanaso na mutu ne?"
da sauri ya kalleshi, baiyi zaton yasan baya bacci ba, yace "ina bacci babu komai akwai stress na wajen aikin ne yayi min yawa shine har yanzu nake ji"
yace "ka rinƙa addu'a"
karfe 12 yana cika jirginsu ya tashi daga kano zuwa Abuja.
*Jiddah Ce...✍🏻*
08144818849
🌸🌸🌸🌸🌸
*ZOBEN WUTA*
🌸🌸🌸🌸🌸
By
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 4*
~Jirginsu yana landing suka fito a tare, Abeed ya ciro bakin space yasa a idonshi, kyau ya kara sosai akan wanda yayi da farko, Deen ke rike da trolley ɗinsu, motoci manya manya masu tsananin kyau duka baƙaƙe suka jeru tun daga bakin kofa har zuwa cikin airport ɗin, wani me baƙin kaya da bindiga a hanunshi da bakin glass, ya cire bakin glass ɗin da ɗan gudu yazo inda suke tsaye kusa da jirgin, durkusawa yayi alaman respect sannan ya karɓi trolley ɗin dake hanun deen, zubawa motan dake gaba ido sukayi su duka biyu suna jiran ganin wacce zata fito, duk a zatonsu Ammi ce hakan yasa kowa ya shirya domin yimata oyoyo, kyakkyawar matashiya me kama da larabawa ce ta fito daga motan, sanye take da farin kaya net ɗinkin a buɗe yake sosai, tana kama dasu sosai ba kaɗan ba saide sun fita fari, domin su har yellow yellow suka zama, mayafi siriri ne a hanunta yayinda tasa hulan net a kanta fari, ba zata wuce shekara 17 ba, jikinta kamar madara, cikin jin daɗi ta ɗan ɗaga rigan duk da high shoe ne a kafarta rigan ya mata tsayi, faɗawa tayi jikin Abeed tace "welcome back ya Deen"
cikin rashin fara'anshi yace "thanks"
zameta yayi a jikinshi domin yaji haushi da ba ammi bace tazo ɗaukansu"
kallonshi tayi sannan ta kalli na gefenshi da sauri ta faɗa jikin Deen tace "welcome back ya Deen"
cikin sakin fuska yace "zee-zee ya kike? ina Ammi?"
tace "Ammi na gida"
ya rike hanunta yace "okay let's go and meet her, munyi missing nata sosai"
kallon uban motocin da sukazo ɗaukansu yayi, a ranshi yayi tsaki yace "duk wannan motocin sabida mutum biyu? abu mota ɗaya ma ya isa"
buɗe musu marfin motan akayi, an tsaida kowa da shiga airport har sai sun fita kafin kowa zai iya shiga, jera motocin sukayi akan titin suna tafiya, kowa saida ya tsaya da tuki akan titin saida duk suka wuce da motocin kafin aka saki hanya.
Federal lowcost unguwan manyan masu mukamai da kuma kuɗi shine unguwan da suka nufa, faɗan irin manya manyan gidajen da suke unguwan ɓata lokaci ne, a kofan wani get me yalƙi kamar da ruwan gold akayi suka tsaya, tun daga bakin titin daya kama hanyan gidan abin kallo ne bale kofan gidan, a haka ma ba'a shiga cikin gidan ba, buɗe makeken get ɗin da yake sheƙi kamar kaga fuskanka a jiki akayi, cusa hancin motocin akayi har zuwa cikin gidan, duk yawan motocin saida suka shiga gidan, gida ne me girma sosai, kofofin glass ne a jiki ko ina abin kallo ne a gidan, buɗe musu kofan akayi suka fito tare, kyakkyawar yarinyar ta tsaya a tsakiyansu suka jera suna tafiya, Deen ne ya rike hanunta shi kuma Abeed hankalinshi akan waya, ciki suka shiga har zuwa falon alfarma dake gidan
"you are welcome my twins"
Ammi ce tayi magana, Masha Allah, wannan halittan dole ta haifo kyawawa, duk da ta manyanta hakan bai hana kyawunta bayyana ba, inda ake maganan kyawawa wannan matar ta kai harta dawo, tsadadden bakin leshi ne yake wanda yaji stones yake sheƙi a jikin tsadadden skin nata, duk da ta ɗaura ɗankwali hakan bai hana gashinta zuba har gadon bayanta ba, manyan idanunta duk sune abinda ƴaƴanta suka fi yin gadonshi, sexy eye's take ɗauke dashi idanu masu kalan na mage, cikin idon maimakon baƙi brown ne ga wani sarƙan da kana gani kasan na gold ne a wuyanta, hanunta ɗauke da zobe da warwaro na gold, matar nan karshe ce a wajen ado, ganin sun ɓata rai su duka sunki yimata magana ta kalli wanda yake rike da hanun zee-zee ta rungumeshi tace "Deen kada kuyi fushi dani na tuna da mahaifinku shiyasa na zauna a gida bazan iya zuwa airport na dawo daku ba"
jikinsu yayi sanyi, deen cikin sanyin muryanshi yace "Ammi ya akayi kika ganeni yau? bacin anko mukayi nida Abeed?"
murmushi tayi bayan ta sake shi tace "sabida nasan Deen ne kaɗai zai iya rike hanun kanwarshi su shigo tare"
rungume Abeed tayi tace "kada kuyi fushi dani kaji Abeed ɗina?"
ya turo baki yace "to Ammi ina jin yunwa"
a shagwaɓe yake magana, Ammi tace "to ai na aje muku abinci me daɗi"
hanunsu ta kama tana tsakiyansu suka jera zuwa dining, manyan manyan warmer's ne farare akan dining ɗin, tace "da kaina zanyi serving ƴaƴana"
duk suna kallonta Deen yace "thank you Ammi"
shiru tayi, ta juyar da kai ta yadda ba zasu ganta ba ta share hawaye, deen ya ganta amma yayi kamar bai gani ba, yace "Ammi tare dake zamuci ko?"
gyaɗa kai tayi
yace "yawwa sabida munyi missing naki sosai, har Beed ya fara rashin lafiya"
kallon Beed tayi tace "da gaske?"
girgiza kai yayi "ni lafiyana kalau"
"wallahi Ammi karya ne sai kinga yadda ya dawo ranan kamar wanda yayi s..."
da sauri ya bige bakinshi dan wani lokaci Deen yanada suɓutan baki, kallonsu tayi su duka sannan taci gaba da serving nasu dan ta ɗago me yake shirin faɗa, wani lokacin dukansu basuda kunya basa tuna ita ɗin mamansu ce, itace ta haifesu, zee-zee tace "yaya kamar wanda yayi sesame kake son cewa? to ya fara wasan yara kenan?"
daka mata tsawa Abeed yayi ganin tana so ta janyo asirinshi ya tonu, tsit tayi bata kara koda motsi me kyau ba, Ammi ma shiru tayi ta fara cin abincin tana mamaki, Abeed ne ya fara tashi yana goge bakinshi da tissue yace "thank you Allah, thank you Ammi am full"
zai tafi tace "Beed?"
saida gabanshi ya faɗi dan yasan idan ta kirashi haka to akwai magana, yace "na'am"
idonta akan plate ɗin da take cin abinci tace "kaji tsoron Allah"
ya kai 5mins yana kallonta bata ɗago ba kuma bata daina cin abinci ba, deen ma yana kallonta, da kyar ya harhaɗa magana yace "Ammi me kuma nayi?"
tace "ba sai mutum yayi komai ba ake tuna mishi yaji tsoron Allah, ko nayi laifi ne dan na faɗi haka?"
yace "A,a bakiyi laifi ba"
ya kara minti biyu a wajen ya kasa yin komai, da kyar yaja kafa ya tafi, ɗakinsu da yake kamar a kasar turai ya shiga, akan gado ya faɗa ya janyo pillow me taushi ya rungume, lumshe ido yayi yana tuna maganan Ammi, juyi yayi akan gadon ya kwanta rub da ciki ya rufe ido
"kaji tsoron Allah"
wannan kalman yana da matukar tsayawa a rai duk wanda aka gaya mishi sai yaji wani abu a ranshi, koda bakayi komai ba bale ace ka aikata wani abin, a haka har deen ya shigo ɗakin bakinshi ɗauke da sallama, bai amsa ba kuma bai tashi ba, cire kayan jikinshi yayi yasa na zaman gida domin shan iska, kallon Beed yayi bai saba haka ba idan sun dawo, canja kaya yake ya ɗau mota ya fita, shine ba zai dawo ba sai dare lokacin bacci, daga nan idan yayi bacci kuma sai gobe da safe ya shirya domin zuwa aiki, amma wannan karon ya zama shiru, hawa gadon yayi yaja blanket shima bai mishi magana ba ya rufe ido, a hankali ya tashi ya cire kayan ya barsu a inda ya cire, riga armless yasa da wando three quarter, takalmi palms na zaman gida yasa sannan ya fita daga ɗakin, direct ɗakin ammi ya nufa, a bakin kofa ya tsaya yana knocking, babu amsa sai yayi expecting tana kasa ne, juyawa yayi zai tafi yaji shesheƙan kuka, a hankali ya tura kofan ya shiga, hankalinta da gangan jikinta duk ta mayar kan babban hoton da akayi enlargement ɗinshi, akasa a cikin glass, hawaye take yi tana shafa hoton, saide da alama bataso kowa yasan tana kukan, domin sai toshe baki take, kwalliyan dake fuskanta duk ya ɓaci, babban mutum ne sanye da babban riga da kuma hula wanda da gani kasan me tsada ne, yana dariya ya ɗaga hannu alaman gaisuwa akayi mishi hoton, yana da matukar kyau kuma yana kama dasu Abeed domin kana ganinsu zaka san sun haɗa jini, da hakorin makka maƙale a hakorinshi hakan ya kara mishi kyau sosai saide shi baƙi ne saɓanin su farare, atake Abeed ya fara zufa duk da sanyin dake cikin ɗakin na tiles da Ac, idanunshi suka rikiɗe suka koma jajur kamar gawarshin wuta, jijiyoyin kanshi suka, baisan time ɗin daya karasa ciki ya fizge hoton ba, a firgice ta tashi tana share hawayen da sauri ta kalleshi tana kakalo murmushi tace "Abeed yaushe kazo?"
cikin wani irin murya da yake nuna tsananin fushin da yake ciki yace "ina zaki san na shigo kina nan kina kallon hoton wannan tsinannen mutumin"
cikin kuka tace "Abeed shi ɗin fa mahaifinka ne...."
da wani irin tsawan da yasa upstair da suke kai ya girgiza, yace "karki kara alakantani dashi, wannan ba babana bane"
gyaɗa kai tayi a tsorace ta matso wajenshi jikinta har yana rawa tace "to Abeed ba babanka bane bani hoton kaji ɗan albarka....??"
toshe kunnuwanta tayi lokacin da taji karan buga hoton da yayi da kasa, nan take glass ɗin dake jikin hoton ya tarwatse, baya tayi tana kallon Abeed da yake huci kamar zaki, idonshi akan hoton yasa kafa ya taka, take kafanshi ya tsage ya fara jini, da gudu tazo zata rike kafanshi da yake shirin kara taka glass ɗin yace "stay away from me!!!"
bata san time