Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌸🌸🌸🌸🌸 *ZOBEN WUTA* 🌸🌸🌸🌸🌸 By _Jiddah S Mapi_ *Chapter 1* ~Mama!!! Mama!!! Mama!!! muryan mace ne yake tashi a cikin ruwan sama da yake sauka, duk garin yayi duhu sosai babu abinda akeji sai karan hadari da tsawa da kuma walƙiya da yake tashi, ruwan sama sosai ake kamar da bakin kwarya, mutanen dake aiki a waje kowa ya nemi mafaka, kasancewar ruwan yana da karfi da kuma iska ba karamin duka yake yiwa mutum ba, kowa ya ɓoye amma banda wata kyakkyawar yarinya da take gudu cikin ruwan, baƙin hijabi ne a jikinta, kafarta babu takalmi, duk da duhun daya mamaye garin hakan bai hana farin fatarta fitowa sosai ba, cikin gudun take ambatan sunan mama da siririn muryanta wanda ya gama dishewa sabida ruwan daya jiƙata da kuma ihun kiran sunan maman da take, walƙiya akayi sannan akayi wani tsawa me tsananin razanarwa, toshe kunnuwa tayi da alama tanada bala'in tsoron tsawa da kuma hadari, wani lungu ta samu ta zauna tareda kankame kanta a cinyarta ta toshe kunnuwa tana kuka, cikin kuka tace "mama karki tafi ki barni, idan kin barni ina zanje? mama ina zansa kaina?" jikinta yana rawa domin sanyi take ji sosai ruwan ya shiga jikinta, hasken mota ne ya haskata da sauri ta kuma ɓoye kanta ta zaci walƙiya aka kuma yi, kara haskata akayi, cikin wani yanayi ya waro manyan idanunshi yana kallonta, matashi ne kyakkyawa ajin karshe sanye da suit baƙi, yana cikin wani tsadadden rantsatsen baƙin mota, baisan time ɗin daya karasa da motarshi wajen ba, parking yayi a gefe bai damu da ruwan da ake ba ya buɗe motan ya fito, madalla ga ubangijin da yayi wannan halitta, tsayawa nayi bayanin irin baiwan kyau da Allah ya bashi babban ɓata lokaci ne, cikin maye yake tafiya da kyar ya isa inda take, ruwan sama aka kara farawa kamar da bakin kwarya, hanu yasa ya dafa ta sannan cikin muryan maye yace "me kike anan?" a tsorace ta ɗago idanunta tana kallonshi, baya yayi da sauri yace "Aljana ce ko mutum?" cikin kuka tace "mutum ce dan Allah ka taimakeni mama na banaso na rasa ta" da sauri ya mari fuskanshi kaɗan ya kara waro ido yace "wannan ba mutum bace, wannan aljana ce babu mace me irin wannan kyawun a wannan a duniya" cikin kuka tace "ka taimaka min" tashi tayi daga zaunen da take, tana rawan ɗari hakoranta suna haɗuwa da juna tace "mama na" ji tayi ya rungumeta, a tsorace ta fara janyewa, cikin zazzaƙan muryanta tace "ka kyaleni me haka?" a hankali cikin maye yace "aljana your voice is sweet" dukan kirjinshi ta fara tana cewa "me haka? me kake cewa? ka sakeni niba aljana bace ni mutum ce" murmushi yayi kana ya kalleta da idanunshi wanda suka sauya zuwa jajur yace "cewa nake muryanki da daɗi, zanso naji ya bakinki yake" duka take kai mishi da karfi tana kuka, ihu ta fara lokacin daya fara kokarin cire bakin hijabin dake jikinta, kokawa suka fara duk da baida karfi sabida mayen da yake ciki hakan bai hanashi yaga hijabin sannan ya yaga koɗaɗɗen material ɗin dake jikinta, take kyakkyawan jikinta ya bayyana, ajiyan zuciya ya sauke lokacin daya sa hanunshi a jikinta, wani irin razanannen ihu tayi ta tureshi gefe, gudu ta fara tana kakkare jikinta har yanzu kalman mama bai daina fita daga bakinta ba, ji tayi ya riketa ya juyo da ita, da karfi ya kwantar da ita a wajen, ruwan sama na dukan bayanshi bai damu ba saida ya tabbatar ya yiwa yarinyar fyaɗe, tun tana bugunshi a baya har taji hanunta ya daina aiki, jikinta yayi nauyi, ido kawai ta zuba mishi har lokacin daya kwantar da kanshi a wuyanta yayi shiru kamar ya dawo hayyacinshi, a hankali idonta ya fara lumshewa cikin muryanta daya gama dishewa tace "mama......" daga wannan bata kara cewa komai ba, da sauri ya tashi yana gyara jikinshi, wajen motarshi yaje ya shiga harya tada zai tafi, sai kuma ya kalli gefen da take a kwance, buɗewa yayi ya ciro kuɗi masu yawa yazo inda take, hijabinta daya yaga ya ɗauko ya rufa mata jikinta dashi, har a lokacin ba'a daina ruwan sama ba, jini ya gani yana zuba daga kasanta yana bin ruwan dake wajen, tafin hanunta ya buɗe, lalle ne red me kyau a hannun, kasancewar ita farar fata ce yasa hanun yayi kyau, kallon lallen yayi sannan yasa mata kuɗin a tafin hanun ya rufe, kallon bayan hanunta yayi anyi baƙin lalle me matukar kyau, a hankali ya tashi yana cigaba da kallon kyakkyawan yatsunta da kuɗin yake ciki da kuma lallen, idonta a rufe yake da alama suma tayi, ya koma cikin mota yabar wajen da mugun gudu, a lokacin ruwan sama ya tsaya sai yayyafi da ake kaɗan kaɗan, zuwa yanzu yanayin garin ya fara dawowa daidai, iska da tsawa da walƙiya ya tsaya sai sanyi da akeyi sosai kamar anyi ruwan ƙanƙara, saida ruwa ya tsaya cak kafin mutane suka fara fitowa daga wajajen da suka ɓuya, kowa ya fara neman hanyan tafiya gida domin kuwa mangrib ya gabato, harma an fara kiraye kirayen salla. kwance take a wajen har bayan sallan Isha kasancewar lungu ne yasa mutane basu fiye bin ta wajen ba musamman da akayi ruwa. wani farin mota ne yazo wucewa, ganin ruwa ya rufe hanyan da yake bi yasa ya tsaya, buɗe marfin motan yayi ya fito yana kallon ruwan, fuskanshi a kwaɓe kamar yayi kuka, kyakkyawa ne ajin karshe a kyau, skin nashi brown ne sai glowing yake, shadda ne a jikinshi blue da hula ɗinkin Borno, sai kamshi yake zubawa kamar ka sace ka gudu, shima saide muce madalla ga ubangijin da yayi wannan halittan, cikin gajiya yace "wallahi ruwa ya rufe hanyan Abba ya zanyi?" shiru yayi yana sauraran abinda ake faɗa mishi a wayan, a hankali yake gyaɗa kai alaman yana fahimta, cikin sanyin murya yace "okay Abba yanzu zanbi amma fa lungu ne" sai kuma yace "thanks for the care abba ina rokon Allah yasa naje a sa'a Allah yasa babanta ya soni ji nake idan banje na haɗu da babanta ba yau zan iya samun heart attack" kallon wayar yayi jin Abba ya katse, sai wani kira ya fara shigo mishi, amsawa yayi yace "hello baby yau zanje na haɗu da abbanki insha Allah kin kusa zama tawa" cikin sanyin murya yace "insha Allah ba zan kara minti goma ba domin nasan idan ban haɗu dashi yau ba to na rasaki kenan har abada kuma kinsan bazan iya jurewa ba" murmushi yayi yana jin sanyin dake ratsawa yace "baby akwai sanyi sai nazo zan canja hanya ne, i love you so much" shiga motan yayi bayan ya kashe wayan, canja hanya yayi zuwa ɗayan hanyan da yafi sauki akan wannan, zaro ido yayi ganin kamar mutum ne kwance a kasa, da sauri ya fito a motan cikin tsoro ya haska tocin wayarshi, gani yayi jini a wajen ga kuma fuskan meshi a rufe "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" shine kalman daya fito daga bakinshi, cikin sauri ya kashe tocin zai koma mota domin gawa ne ya gani kwance a cikin ruwa da jini, a hankali yaji tace "mama!!" tsayawa yayi ya juyo, jin muryan mace ya kuma haska tocin, ji yayi ba zai iya tafiya ya barta ba, dawowa yayi yace "baiwar Allah?" shiru babu amsa amma yaga hanunta yana motsi, a ranshi yace "kada na taimaka mata ta mutu ace nine na kashe ta, gara na tafi" sai kuma wata zuciyar tace mishi "ka taimaka mata da kanwarka ce anan zaka iya barinta?" jikinta a bayyane yake hakan yasa ya rufe ido a hankali yasa mata rigan dake yage, hijabin ya rufa jikinta dashi sannan ya ɗauketa, gani yayi kuɗi me yawa ya faɗo daga hanunta, dubu ɗaɗɗaya ne sabbi dal suka watse a cikin ruwan, bai bi ta kan kuɗin ba ya kaita mota, sata yayi a ciki sannan ya shiga da sauri ya tada motan, ya sadaukar da komai wa Allah shiyasa ya taimaka mata, gudu ya fara sosai na ceton rai lokacin da ya hau kan titi, a hankali ta buɗe baki da alama bata cikin hayyacinta tace "mama? ki bani ruwa" ji yayi idonshi yana cika da hawaye daga jin muryanta karamar yarinya ce ba zata wuce 19years ba, yayi tafiya me nisa kafin ya isa wani hospital da aka rubuta well care hospital, har ciki ya shiga kafin yayi parking, da ɗan gudu ya zagayo ya buɗe marfin motan ya ɗauko ta, gudu yake cikin tsoro dan yaga tana shaƙuwa sosai sannan tana buɗe ido ta rufe, likitoci suna ganinshi sukazo da gudu, akan gado aka kwantar da ita, tare dashi suke tura gadon, a kofan emergency room ya saki gadon, ji yayi ta rike hannunshi, gabanshi yayi mummunan faɗuwa, yaji jikinshi yayi sanyi sosai, a hankali ya kalleta, idanunta a rufe, janye hanunshi ya fara amma ta damke gam, hawayen da yake ɓoyewa tun ɗazu su suka zubo suna bin kyakkyawan kumatunshi, janye hanunshi yayi da kyar a cikin nata, yana tsaye a wajen yana kallon fuskanta har aka shiga da ita aka rufe kofan, jingina yayi da jikin kofan yayi shiru, duk kiran da ake mishi a waya bai damu ya ɗauka ba. likitoci suna kokarin ceto ranta saide raunin yayi yawa a jikinta domin taji ciwo sosai, alluran bacci sukayi mata kafin suka fara yimata aiki, sun ɗau lokaci me tsayi kafin suka sa mata drip suka fito da ita, yana ganin sun fito yazo yana cewa "tana raye?" a tare sukace "ka kwantar da hankalinka tana raye" wani likita dake gefe yace "amma gaskiya baka da imani, kana ganin karamar yarinya haka kayi mata irin wannan abin? meyasa idan an aura muku yara ƙanana bakwa tausaya musu ne?" shiru yayi dan baisan ta yadda zai fara musu bayani ba, ɗaki aka shigar da ita sannan suka kara mata alluran pain relief, suna fifowa sukace "zaka iya shiga ka zauna kusa da ita domin zata iya farkawa a kowane lokaci" jijjiga kai yayi kana ya shiga ɗakin da take kwance jikinshi a mace ya janyo kujeran plastic dake gefe yazo ya zauna kusa da ita yana kallon fuskanta, bacci take kamar wacce bata cikin matsala, gashin idonta yake kallo yadda yake da tsayi ga kuma farin fatarta kamar ba ƴar kasar nan ba, tana kama da larabawa sosai, bakinta ɗan karami sosai pink dashi, hancinta siriri da tsawo har zuwa bakinta, farin fatarta ya fara komawa yellow yellow, kallon tafin hanunta yayi, yatsunta zara-zara ɗauke da ja da kuma baƙin lalle, kafarta ya kalla shima lalle ne me kyau, a hankali ya kalli kanta kananan kitso aka yiwa gashinta daya zubo akan farin pillow ɗin da suka ɗaura kanta akai, yanada tabbacin idan ta tashi gashin zai iya taɓo hips nata, da alama wannan amarya ce kuma yau juma'a ne yau ake ɗaura aure a mafi yawan garuruwa, to amma idan amarya ce meya kawota nan? me yasa akayi mata fyaɗe?" baida amsan wannan tambayan, tun yana kallonta har bacci ya fara fizganshi, wasa wasa bata farfaɗo ba har karfe ɗaya da minti hamsin na dare, bacci yakeyi a zaune, sai yaji motsi saiya buɗe ido, idan yaga idonta a rufe saiya koma baccin, sai karfe biyu da rabi ta fara motsa hanu a hankali tana buɗe ido, da sauri ta maida idon ta rufe sai kuma ta kara buɗewa, a firgice ta tashi zata gudu, da sauri ya buɗe ido harta zame drip ɗin da canulla dake hanunta, tasa kafafunta a kasa zata sauka ya riketa, fizgewa tayi idanunta sun kumbura sosai ta fara girgiza mishi kai tana yin baya, riketa yayi sosai yace "relax da kwai drip a jikinshi a gadon asibiti kike" kallon ɗakin tayi sannan ta kalleshi da dara daran idanunta, saida yaji gabanshi ya faɗi a zuciya yace "auzubillahi minashaiɗanirrajeem" wannan idanun kamar bana mutane ba, tace "ina mama? me kamin?" cikin son kwantar mata da hankali yace "mama zata zo anjima ki kwanta yanzu drip ɗin ya kare" cikin tsananin tsoron da take ciki tace "kayi alkawari mama zata zo? ba zata barni ba? kuma baka min komai ba?" gyaɗa kai yayi hawaye yana zuba, yace "kwanta" yana kokarin kwantar da ita, tace "no kace min kayi alkawari baka min komai ba? amma ya naji zafi a kasana? ya nake jin kamar ciwo sosai bazan iya tafiya ba" ɗauke kai yayi yana jin kuka sosai yana zuwa mishi, cikin ruwan murya yace "ban miki komai ba nayi alkawari" murmushi tayi mishi gefen kumatunta ya lotsa bai tsorata da kyawunta ba saida yaga fararen hakoranta, tace "to shikenan na yadda da kai mafarki nayi ɗazu" kwanciya tayi ya zauna a bakin gadon yayi shiru, ɗan juyowa yayi domin ganin ko tayi bacci, ido huɗu sukayi ta sakar mishi wani murmushin a hankali ya kara ɗauke kai, saida yayi 15mins bai kara kallonta ba, jin numfashinta ya fara sauka a hankali ya juyo ya kuma kallonta, dara daran idanunta masu ɗauke da zara zaran eyelashes ta zuba mishi, sannan ta kuma yin wani murmushin, a hankali yake kallonta sai yanzu ya fahimci dalilin murmushin da take, dan yace mata mama zata zo, to Aina zai fara neman mama? yace "kiyi bacci" tace "bana jin bacci sai mama tazo" a hankali ya matso kusa da ita, hanunta ya rike yace "kanwata kiyi bacci zuwa safe zata zo ki samu ki huta kinji?" jin sunan kanwata daya kirata dashi ta lumshe ido bata buɗewa ba, hanunshi cikin nata har bacci ya ɗauke ta, ya kasa ɗauke idonshi akanta, da haka ya kwana a wajen har saida aka fara kiran salla kafin ya fita, alwala yayi sannan yayi salla a mallacin dake cikin hospital ɗin ya dawo, lokacin ta tashi harma ta zauna tana ciza karamin bakinta, azaba take ji sosai a jikinta, ta cire drip ɗin da kanta, kanta tasa a gwaiwa tayi shiru, turo kofan yayi bakinshi ɗauke da sallama, ganin ta tashi ya karaso inda take zaune, zama yayi a gefenta yace "kin tashi?" bata amsa ba kuma bata ɗago kai ba, ya kuma cewa "kin tashi?" sai a lokacin ta ɗago kai ta kalleshi, cikin raunin murya tace "me nayi?" girgiza kai yayi "ba abinda kikayi" murmushin baƙin ciki tayi wanda yafi kuka ciwo kana tace "to meyasa hakan yake faruwa?" yace "haka Allah ya ƙaddara miki" tace "ka sanni ne?" girgiza kai yayi, tace "to meyasa kace ƙaddara ne? kasan meya sameni a rayuwa?" yace "ban sani ba amma koma me ya faru haka Allah ya rubuta miki" tace "wannan ba ƙaddara bane son zuciya ne kasan raɗaɗin da nake ji a zuciyata? kasan zafin da nake ji a jikina?" yace "kanwata ki daina cewa haka" da sauri tace "kasan wacece kake kira da kanwarka? kasan haɗarin dake tare dani kuwa?" yace "koma menene ke kanwata ce" girgiza kai tayi sannan tace "zan tafi" "ina zaki je?" tace "wajen mama" jikinshi yayi sanyi ya tashi ya ɗau makullin motarshi yace "muje na kaiki" girgiza kai tayi tace "karka damu da kaina zanje wajen mama" tausayi take bashi, ta tashi tana ɗingishi tasa hijabinta da yake a yage, ganin ba zata iya tafiya ita kaɗai ba yace "kiyi hakuri zan kaiki akwai mota a wajena" gani yayi ta juyo tana dariya wanda ya kara mata kyau sosai, hijabin da yake baƙi ya matukar amsan fatar jikinta, kitson da akayi mata bai hana gashin dake gaban goshinta kwanciya luf ba, tace "mama tayi nisa mota ba zaije inda take ba" a hankali yace "zan biya miki kuɗin jirgi" tace "jirgi ba zaije ba nice kaɗai zan iya zuwa" a hankali ya tako zuwa gabanta, kyakkyawan fuskanta da yake ganin tashin hankali da tsananin buƙatan mutum kusa da ita ya kalla, yace "aina take?" cikin muryanta daya fara rawa domin kukan daya suɓuce mata tace "lahira, mama tana lahira ta mutu...." kuka me tsuma zuciya ta fashe dashi, bai taɓa jin tausayin da yakeji irin na yau ba, toshe baki tayi tana kukan sosai, ba zato yaji ta faɗa jikinshi tana raira kuka me karya zuciyan mutum, bayanta ya zubawa ido yana jin sautin kukanta, a hankali yasa hanu yana taping bayanta kaɗan kaɗan alaman lallashi, saida ta samu sassauci kafin ta zame tana kawar da kai tace "zan tafi na gode da taimakon da kayi min" ji tayi ya rike mata hanu yace "ki biyoni na kaiki gidanmu zanyi kokari wajen kula dake da baki duk wani farin ciki zan zame miki yaya" ido ta zuba mishi, da mamakinshi yaga tayi murmushin gefen baki me sauti tace "kasan wacece wannan?" ta nuna kanta, baiyi magana ba tace "nida kake ganina duk wanda na shiga rayuwarshi baya taɓa jin daɗi har sai na fita, ka ganni nan daga ranan dana shiga rayuwar mutum daga ranan zai fara haɗuwa da asara da rashin kwanciyan hankali, ba zai samu natsuwa ba har sai na fita, kuskuren da mutum zai fara tafkawa a rayuwarshi to shine ya fara sani a rayuwarshi, taimakon da kayi min ina addu'a kada Allah yasa wani abin marar kyau ya shiga rayuwarka a yau, zaifi kyau kaje kayi rayuwa ka kyaleni bazan rasa wajen zuwa ba" yace "na yadda da komai da zai sameni indai zaki yadda na taimaka miki" kuka take yi sosai, tace "ba zaka fahimci abinda nake nufi ba har sai na shiga rayuwarka, zuwana gidanku kada ya zame maka..." rufe mata baki yayi, yace "idan kin ɗaukeni matsayin yayanki ki yadda da abinda nace" zatayi magana yace "dan Allah" tace "na gode" yace "kin yadda na kaiki wajen momy na?" gyaɗa kai tayi yace "good girl" yace "zauna to" zama tayi yace "lallenki yayi kyau" a hankali tace "lallen aurena ne" yace "kenan kinada aure?" girgiza kai tayi "auren ƙaddara ne kuma ba'a ɗaura ba" baison ya fiye tambaya hakan yasa yayi shiru, ganin akwai alaman tambaya a bakinshi ta ɗan janye wuyan riganta, shatin yanka ya gani a wuyanta, a firgice ya kalleta, tayi murmushi tace "karka yadda na shiga rayuwarka ina tausaya maka" yace "na yadda koma menene zai sameni ina tare dake" zatayi magana yasa yatsa a baki yayi mata alaman tayi shiru, bata kara magana ba yace "Bara na kira likita" tace "to" fita yayi tana ganin ya fita ta tashi da kyar ta sauka a gadon, babu takalmi ta fara tafiya cikin sanɗa ta yadda zata iya gudu ba tareda kowa ya ganta ba, a hankali ta buɗe kofan ta fita, dubawa tayi taga babu me kallonta, cikin azaba take tafiya sauri take ta fita, ajiyan zuciya ta sauke lokacin data fita daga hospital ɗin, juyawa tayi zata gudu sukayi ido huɗu dashi, cak ta tsaya ta dukar da kanta kasa, hanunshi rike da makullin motan ya karaso inda take tsaye, yace "so kike ki gudu?" shiru tayi, kanta a kasa, yace "ɗago ki kalleni mana" tace "kayi hakuri wallahi banason na shiga rayuwarka kowa yana cewa idan na shiga rayuwar mutum farin cikinshi tarwatsewa yake, banason tarwatsa farin cikin wanda ya taimaki rayuwata wanda ya cetoni" yace "idan kin yadda da ƙaddara ki amince ki biyoni" a hankali tace "na yadda kuma na gode" yace "kiyi alkawari koda na kaiki gidanmu ba zaki gudu ba" a hankali tace "nayi alkawari" hanu ya mika mata yace "mu zama friends" sa hanunta tayi a nashi suka gaisa tace "mun zama" yace "babu ɓoye sirri tsakaninmu" tace "insha Allah babu" yace "good girl muje ko?" a hankali ta fara binshi a baya, gefenta yazo suka jera a tare ganin a hankali take tafiya har suka isa wajen motar, buɗe mata yayi ta shiga ta zauna, ya zagayo shima ya zauna mazaunin driver, ruwa me sanyi ya mika mata a gora, karɓa tayi ta rike bata buɗe ba, jan motar yayi yana tafiya bini bini yake juyawa ya kalle ta, da alama batada yawan surutu domin kuwa sunkuyar da kai take idan sun haɗa ido, da haka har suka isa wani unguwa me matukar kyau, kallon manya manyan gidajen da suke unguwan take yi, a tsorace ta kalleshi, cikin wasa yace "kina tsoro ne? ba zan yanke miki kai ba" sunkuyar da kai tayi, ya tsaya a kofan wani tamfatsetsen get yayi hon, buɗe mishi akayi ya shiga, cikin tsoro take kallon mutanen dake cikin gidan masu sanye da baƙaƙen kaya da bindigu a hanunsu, fita yayi yace "fito muje" kin fitowa tayi idonta akansu, yace "babu abinda zasu miki security's ne" fitowa tayi tana tafiya a hankali cikin tsoro, ta rike gefen hijabinta daya yayyage tana binshi a baya, har zuwa wani babban falo yayi mata iso, koda ya shiga duk ƴan gidan suna zaune a falo sunyi tagumi da alama suna cikin tashin hankali domin fuskokinsu ya nuna, suna ganinshi duk suka tashi kowa yazo wajenshi momy itace suke tsananin kama, sai Abbanshi da kuma kanneshi mata biyu, duk suka fara tambayanshi "yaya ina ka shiga? ka barmu cikin tashin hankali" yace "ba inda na shiga" momy ta sauke ajiyan zuciya tace "Alhmdllh tunda ba abinda ya sameka" momy tace "ka shiga kayi wanka sai kazo kaci abinci" a hankali yace "to amma itama a bata abinci" sai a lokacin suka kalleta, momy tace "wacece wannan?" yace "momy dogon labari ne, mufeeda da madeena su shiga da ita su abinci tayi wanka su bata kaya ta canja" a tare suka kalli juna, ita kuma tana gefe tayi shiru tana murza gefen hijabinta kanta kasa, ɗayan yarinyar tace "masha Allah wannan kyakkyawar kamar daga India ko dai balarabiya ce?" ɗayan tace "a,a mufeeda wannan nakega bata jin hausa ma bakiga batayi magana ba?" yace "take her to ur room banason surutu" momy tayi shiru batace komai ba, madina tace "what is your name?" a hankali tace "banji me kikace ba" da alama madeena tafi yawan magana, tace "wow kina jin hausa?" gyaɗa kai tayi, tace "surprise you look like Indian

Chapter 1 of 9