Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
kwanciyar hankali in ka ganta da k'yar zaka gane tana da ciki domin hijab ne jikinta always Da cikinta taje bikin humaira tare suka je da saheeb inda ana d'aura aure ya kirata Suka koma gida duk da taso wuni haka ta hakura ta bishi Bayan wata biyar ta haiho yar'ta mace shi da kanshi ya karbi haihuwar matarshi ba karamin wahala Tasha ba Sanda ya gyrata ya fara Kiransu mummy Mummy da fushi take dashi akan yaki bari farida taje gida wanka tace"bazata je ba saidai ya kawota " Aiko yace"yi hakuri mummy please" Ganin da gaske yake yasa taje ta gyra jaririya ta Mata wanka ta had'a kayanta ta dawo da ita gida shima kayan nashi ya had'a ya bisu Ranan suna anci an Sha anyi shagali Iman da tsohon cikinta wata bakwai ta zo Zumunci ne tsakani Dr musty da saheeb sun manta abinda ya faru a baya (Haka ake son mu kasance masu yafiya) Bayan shekaru uku abubuwa da dama sun faru ciki harda gamawa makarantar fareeda Kuma yar'su ta girma Rukkaya takwaran mummy Amma suna kiranta samha soyyaya take gani a gun iyayenta sai dai fa saheeb nashi ta daban ne domin ji yake bazai iya rayuwa babu ita ba har fad'a suke da fareeda wai ya fiya b'ata yara Fareeda ne zaune a falo tana kallo sai ga samha ta zo da gudu tana nuna Mata hanunta tace"ummi kin ga zafi" Kallon wurin tayi ta gan kuraje ne sunyi ja tace"Sannu ta Bata magani ta sha"(anti biotic) Hmmn abu Kamar Wasa bayan kwana uku kurajen sun mamaye ko Ina na jikin samha harta halshe da baki babu inda babu ko magana bata iyayi Hankalin saheeb ya tashi domin har allura yayi Mata ya kaita skin care a banza duk asibitin da ake sa ran samu sauki anyi ina mummy ma nimo musu take amma abin sai karuwa yake Fareeda kullum sai kuka gata da sabon ciki Da abin yayi sanani fareeda ta kaita gida baba na gani yace"ai wanan sai maganin gargajiya Kuma yasan Mai badawa" Baba yace"a Bari gobe tunda dare yayi zasu" A ranan a gidan ta kwana sai dai fa gari na wayewa ta tashi da zazzabi Baba yace"toh ta zauna a gida su tafi da saheeb" Saheeb ne ya zo da mota ya d'auke baba da samha Suka tafi barkin saleh Parking yayi ya d'auki yar'shi a hannu Domin babu hanyar mota da zaije gidan Da sallama suka Shiga sunman gidan domin d'aki d'aya ce tak a gidan Saheeb na kallon gidan inda yayi kaca-kaca da datti Yana mamaki wai yau shine ya zo neman taimako a wajen talakawa ikon Allah Wata budurwa ce ta fito ta kallesu ta gane baba dan haka ta gaishe Shi Yace"tsoho na Nan?' Tace"eh Bari in Kira shi yana ciki" Kallon saheeb nayi sai na tuna lokacin da wanan tsohon ya zo niman taimakon waje shi haka shima d'anshi ya rike yar'shi Hmmm what goes around always comes around muna rayuwa ne but at some point wallahi komin kudin mu da mulki wata rana sai mun nima taimakon na kasa damu,karki gan ko ka gan kana da kudi da mulki kace zaka wulakanta mutum ba a wulakanta mutum toh in Allah daya hallice mu be wulakantamu ba then who are we to look down on each other? Yan uwa ya kamata mu gyra zuciyoyin mu mu, sowa Yan uwanmu abinda Muka sowa kanmu,because in kayi Mai kyau zaka gan Mai kyau Allah yasa mu dace ya rufa Mana asiri duniya da lahira ya raya Mana ya'yan mu,ya raba mu da shaarin masu sharri ya tsarkake zuciyar mu ya bamu lafiya da abinda lafiya zata ci,ya Allah muna tawasali da sunayen ka tsarkaka masu Nima haihuwa Allah ya basu,Yan Mata Allah ka Baku miji na gari masu aure kuma ka Kare mazajen mu ka raba su da matan banza,ya rabbi ka raba mu da aikin dana sani,Amin ) A raina nace ikon Allah ba a raina mutum ko Yaya yake domin kowa da baiwar da Allah yayi me waya tab'a tunanin yau saheeb zai nimi taimakon tsohon daya wulakanta hmmn mu bi duniya a Sannu Maman Noorul Hudah Luv u my fans Pls share [1/13, 9:36 AM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ Dr SAHEEB πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ By maman noorul Hudah Dedicated to 80k's _____________ 9⃣9⃣-1⃣0⃣0⃣ ______________ Bismillahir Rahmanir Rahim Tsohone ya fito da murmushin shi sai dai yana ganin saheeb ya b'ata rai Shima saheeb wani kunya da dana sani ne ya lullubeshi Tsoho ya kalleshi yace"me ya kawo ka gidana Mara mutunci ko zuwa kayi ka Kara kwallo dani?" Saheeb ya duka har kasa yace"baba dan girman Allah ka yafe min na tuba wallahi na tuba" Baba ya kallesu yace"Ina kuka San juna?" Tsoho ya kalli baba yace"ai shine ya tab'a kwallo dani akan naje niman taimako asibitinshi " Saheeb ya fashe da kuka ganin samha ta fara Mika yace"baba dan girman allah ka taimakeni ka bawa ya'ta magani " Tsoho yayi dariya yace"ashe ka ji inda ake ji kenan toh ni ka nimi wani wuri ba nan ba ka tuna Nima dana kawo nawa yar'ka wulakanta ni?" Baba ne ya fara rokonshi amma tsoho ya rufe ido yace"besan zancen ba" Hankalin saheeb ya tashi yayi nadama wulakanta d'an Adam watoh Ashe kowa na da ranan shi a duniya " Duk magiyar da zaiyi tsoho kin taimakon su yayi Baba yace"saheeb muje kawai Allah ya raya ta" SAHEEB dake zaune a kasa ya rungume samha yace"baba Ina nan har sai ya taimaka min bana son ratsa ya'ta" Gajiya baba yayi ya tafi ya barshi a zaune tsohon ma shigewa yayi ya barshi Jama'a ku duba lamarin Allah yau ga medical Dr itama matar shi Dr Yana rokon Wanda beyi karatu ba magani Allah yasa mu dace Komawa gida baba yayi fareeda na ganin shi ta taso tace"baba an dace?" Baba yace"Ina kuwa tsohon yaki bayarwa a cewar shi Kamal ya tab'a wulakantashi a asibiti da ya Kai yar'shi" Farida ta fashe da kuka tace"ka kaini kila in ya ganni ya bamu taimakon" Baba yace"da kamar wuya" Labari ta bawa baba jikin baba yayi sanyi yace"shiyasa Yana da kyau mutum ya aikata alheri muje" Suna zuwa ko Suka tarar da saheeb zaune yayi tagumi Sallama fareeda tayi budurwar d'azun ta fito saf fareeda ta gane itane aka kawo asibiti Murmushi tayi tace"Ina ka'ka" Tace"Yana ciki" Tace'yi min sallama dashi" Ciki ta shiga sai gashi ya fito Yana ganinta yace"ya'ta ashe rai kan ga rai?" Tayi murmushi dole ta gaishe Shi ya amsa Dukawa tayi tace"baba ka dubi girman Allah ka taimakawa ya'ta" Yace"ina take haba ba sai kin rokeni ba ki shigo da ita" Nuna me saheeb dake kallonsu tayi tace"gata shine mijina kayi hakuri ka taimaka" Yace"ya'ta saboda ke zan dubata in ba haka ba wallahi sai dai inda Allah yayi " Tashi SAHEEB yayi da sauri Suka shiga baba ya Basu na wanka da shafawa Fareeda ta amsheta ta goya Har kasa ya sunguna ya sake niman gafara baba da k'yar yace"albarkaci fareeda ya yafe me" Abu dai kamar al'mara da suka fara mata magani ko kwana 7 ba ayi ba samhat ta fara samun lafiya tana wasan ta Nan fa darasin rayuwa ta kara shiga saheeb ya tuba sosai Komawa yayi yayiwa tsoho alkhari Kuma ya tabbatar me duk lokacin da yake niman taimako ya zo wajen shi Bayan sati biyu samhat ta dawo dai-dai Mahmud har gida ya zo da humaira Suka roke saheeb ya yafe me Bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki harda haihuwar fareeda inda yanzu yaransu hud'u Iman nada uku humaira biyu soyyaya suke nunawa juna da girmamawa yanzu saheeb har gidan marayu yake dashi ga taimakon talakawa shiko tsoho Allah yayi me rasuwa saheeb ya d'auki nauyin karatun d'anshi kuma yanzu budurwar yar'shi a gidansu fareeda take har sun Mata miji Toh fans a Nan na kawo karshe wanan labarin kuskuren dake ciki Allah ya yafe min please ayi amfani da darasin a watsar da Wanda beda amfani Nagode da kaunar ku *NIDA YAYA HYDAR* Babban gareji ne Wanda kap kauyen kwaita babu gareji daya kaishi girma Kuma gareji ne me tashe saboda kwarewar ma'aikatarsu Gareji ne da yake bakin titi garin kwaita dake under kwali area council Abuja Shiga nayi dan somo labarai domin sunan garejin ne ya ja hankalina domin a gaban garejin na gan anrubuta *MATU GARAGE* Wani bakaniki ( makaniki)na hango kwance da kayan aikinsu yellow watoh irin kayan nan biri da wando Aiki take cikin kwanciyar hankali a karkashin mota wani dattijon ne ya zo ya jingina da motar yace"matu ki fito gashi an kawo motar alhaji Kuma kin San baya so kowa yayi me gyra sai ke" Abin ya bani mamaki domin na ji yayi maganar ne kamar da mace Aiko fitowa tayi daga karkashin mota tsanye da hula baka ganin sumanta but zaka gane macece Suman tsaye nayi ganin macece Ashe Zaro ido nayi nace mace Kuma da irin wanan aikin Muryar oga sule naji yace"matu Yi sauri ki duba motar nan kafin driver ya dawo d'auka Wani kallo tayi me da yasa shi had'iye miyau cikin rashin kunya na ji tace"in anki fa?" Murmushi yayi yace"Yi hakuri matu kap garin nan kin fi kowa kirki" Ko kulashi batayi ba ta fara tafiya kamar zata tashi sama ta Isa gaban motar Burnet ta bude cikin kwarewa ta fara gyra Tana cikin gyran ne sai ga illu ya shigo da gudu Yana Kiran sunanta Kallonta yayi yace"matu ansha dake please ki zo muje da sauri ki kalli show" D'angowa tayi ta kalleshi tace"me ake kira haka?" Yace"au ni nama mance ke hamago ce ba turanci" Cikin b'acin rai ta kalleshi tace"illu karka gan Ina raga maka ka nima ka cimun fuska" Yace"Yi hakuri kedai kin fiya matsifa zuwa nayi in fad'a Miki cewa wata ce ta zo daga birni take fad'awa su Indo wai ta fiki iya rawa Kuma wai in ki Isa ki zo a gwada" Wani mugun dariya ta bushe dashi tace"ita wacece da zata ce zata gwada Dani?" Illu yace"oho ai shine nace karya take kawata ta fita iya rawa zan Kira ki shine na taho" Oga Saleh da tunda ya gan illu ranshi ya b'ace domin ya San zuwa yayi ya hana matu aiki ' Wani saurayi dake zaune a gefen yana jiran a gyra me mota tunda ya shigo garajin ya ji matu ta birgeshi tunda yake a rayuwarshi be tab'a ganin makaniki mace ba sai yau" Murmushi yayi ya karaso gabansu ya kalli matu Yace"Hy" Kallon illu tayi tace"bashi amsa kasan ni ban iya karatun arnan ba" Maganar ya matukar bawa Hafiz dariya Yace"turanci ne karatun arna?" Ko kulashi batayi ba ta cigaba da cire rigar aikinta babu kunya harta Gama cirewa ya rageta da riga da dogon wando Pakistan Hafiz yace"haha keko ya Ina Miki magana kin share ni?" Cikin kosawa tace"Kai malam ai ko bashi na ci maka ka shafamim Lafiya ko?nifa na tsane mutum me shegen iyayi da turanci harda wani ha" Yace"Allah yabaki hakuri birgeni kikayi shiyasa ni dama Zaki aureni dana ji dadi" Kallonshi tayi sama zuwa kasa tace"ni?rufa min asiri har guda nawa nike da za a wani ce za a min aure nifa barni da gyran mota" Yace"toh bani number ki" Kallon illu tayi kawai sai ta gan yana kuka tace"Kai ya haka Kuma? kodai hauka ne ya motsa?" Cikin kuka yace"ba ke bane kike kula wani ba" Tsaki tayi tace"kawai shine na kuka? kai nifa ban fiye kula irin yan birnin nan ba babu karya da turanci babu abinda suka iya haka sukeyi su narkawa yara ciki in ba iskanci ba ni yar shekara goma shabakwai wai zai aureni Kai muje kafin raina ya b'ace,yau na ji ma wai zamuyi baki daga birni" Illu yace"muje" Shidai hafix murmushi yayi sai dai fa ya d'au alkawarin dawowa dole sai ya samu abinda yake so A hanya suka had'u da wata mota da ya lume cikin laka Ganin me motar tsaye sukayi kallo d'aya matu tayi me ta d'auke Kai Shiko Yana ganin su ya kira illu da hanun Itako kau da Kai tayi,karasawa illu yayi Yana murna d'an birni ya kirashi Gyran murya yayi yace"please ka taimaka mu fitar da motar nan mana I will reward you" Kafin illu yayi magana matu ta kece da mugun dariya tace"kwaji d'an rainin hankali toh tunda turanci zakayi Mana da karya banza ai sai turanci ya taimaka maka Mara kunya banza yanzu ko kunya baka ji ba harda turanci" Kallonta *Hydar* yayi yace"amatu ni kikewa rashin kunya ko baki gane ni bane?" Tace"fes kuwa na gane ka,ko ba Hydar bane wanan d'an rainin hankalin da karya ba? toh sai mu ga Wanda zai taimaka maka" Kallon illu tayi tace"toh inka taimakame daga yau na daina kula" Illu yace"tuba Nike ranki ya dade" Tsaki tayi tace"muje ka barshi da turancin shi ya taimaka me aini tunda ka kirani da Yar kauye mara aji nasan zamana da kai" Murmushi yake yayi yace"ai zan rike ki ne" Tace"in ka kamani ka kashe ni,kazan turawa kawai,in banda baffa Ina ni Ina wanan" Cikin b'acin rai ya.... Ku biyoni a naira d'ari biyu kacal zaku Sha dramar Karki Bari a baki labari 200only Please patronize your writer domin biyan kudin karatu pls ku min magana tawanan 09090112846 Karku bari a baku labari Dan girman Allah ba dan niba in kin San zaki fitarmin da littafi ki rike kudin ki Sai naji ku mu had'u a NIDA YAYA HYDAR palaceπŸ˜€πŸ€£ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9