kuka
Zama kawai sukayi kowa yayi tagumi masu jaje da gulma sun sasu a tsakiya
Ba karamin kuka fareeda ta ci ba ga ciwon ciki yasata gaba ko ta kan abinci daya ajiye Bata bi ba
Shiko wajen Mahmud yaje ya bashi labari
Mahmud yayi dariya yace"ka ce zaka kwashi gara in nine Kai sati biyu zatayi kafin in saketa"
Murmushi yayi yace"ko so d'aya ya isheni nifa bawai iam interested bane na so in Sa ne but bansan abinda yasa ba Ina jin bazan iya Bari wani yayi ba"
Mahmud yace"ko za a d'an min ne"
Hararanshi yayi yace"tunda matar ka ce"
Mahmud yace"na gan kaima ba matar ka bace"
Share shi yayi ya
cigaba da latsar waya
Fareeda ko bayan ta gaji da kuka ta zauna tana salati tana Kiran sunayen Allah gashi ya rufeta a d'akin
*Wacece fareedat?*
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/3, 7:16 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my paid groups
______________
π
Ώ2β£5β£&2β£6β£
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
A gurguje please
Fareedat Abdallah shine cikekken sunanta ya'ce ga malam Abdallah da mahaifiyarta Rabiah
Malam Abdallah mutum ne me niman na kanshi domin baya son raini yana da niman na kanshi baya raina sana'a
Auren soyyaya sukayi da matar shi Rabia shekaru talatin da suka wuce sai dai Kash sanda suka shekara tara Basu ajiye kwansu a duniya ba domin Rabiah in tayi ciki zubewa yakeyi a cikin shekarun Taran nan tayi b'ari 7
A lokacin Yan uwan malam Abdallah suka tada da hauka sai ya Kara aure ko su suyi me
Aiko rufe ido yayi yace"bashi da ra'ayin yin aure kuma suna zaman lafiya da matarshi ai shi ba jahili bane da zaiyi aure dan kawai matarshi allah be kawo lokacin da zata haihu ba ai ba laifinta bane
Babu inda basuyi ba har ya Kai ga ita Rabian da kanta tace"yayi auren Amma yaki kuma maganarta ya mugun b'ata me rai kuma ya sanar da ita akan in ta Kara cewa yayi aure sai ya mugun sab'a Mata hakan yasa taja bakinta tayi shiru ta zuba me ido
Wanan dalilin yasa Yan uwan malam Abdallah suka fita harkar shi,shima be damu da ya nimi sulhu ba
A haka dai suka cigaba da rokan Allaj cikin ikon allah sa ga Rabia ta samu ciki laulayi sosai takeyi kullum suna asibiti gashi ba wani sana'ar kirki yakeyi ba gadi ne a Wani company Al-amin ventures
Aiko cikin ikon Allah cikin ya tsaya inda bayan wata tara ta haihu yar'ta mace ranan suna yariya ta ci suna fareedat sunan mahaifiyarshi
Malam Abdallah ya kwashi son duniya ya d'aurawa fareedat Yana sonta domin itace duniyar su
A haka tayi primary and secondary school har ta gama cikin ikon allah ta samu admission taje school of midwifry minna kasancewar tana da illimi ga kokari duk wani tanadi da malam abdallah keyi akan fareeda yake karewa a lokacin da take makarantahar kwana da yunwa sukeyi wata ran dan kawai ta samu tayi karatu
Bayan ta gama makaranta ta zauna babu aiki sai islamiya take zuwa nan ne Allah ya had'ata da malamin hadda su farouq har suka kulla soyayya inda yanzu ana maganar aurensu farouq shima dai ba wani kudine da shi ba Amma Yana da rufin asiri domin Yana aikine a wani company
Baba ne ya Kai takardunta wajen alhaji Musa megidanshi Aiko yayi sa'a lokacin ya budewa d'an shi dake turai asibiti suna niman ma'aikatan a take ya Bata aiki ba karamin godiya baba yame ba
Fareeda ta kasance yariya Mai tarbiya,ga girmama na gaba da ita shiyasa Bata d'aukan raini wajen kowa tana da kamun Kai ga addini domin in ba a wajen aiki da ya Zama mata dole ba da wuya ka ganta babu nikab
Fareeda bata da wata kawa da ta wuce humaira domin tare suka taso kuma tasu ta zo d'aya fareeda bata son mutum me raini
Fareeda tana da saurin hannu domin irin mutane nan ne da babu wuya sun Kai duka in rai ya b'ace domin tun tana karama ake fama da ita a anguwansu sai dai in akaji tayi fad'a toh tana da gaskiya ne
Fareeda ta tsani mutum ya raina ta
Fareedat fara ce sol tana da d'an kiba sai dai bata da tsayi
Tana da tsoro kuma ga karfin hali
Fareedat na matukar son farouq domin burinta ta auri uztaz Wanda keda addini Aiko allah ya Bata farouq
Farida na matukar tsoron first night domin ko Hira ake ko kuma tana karantawa a littatfai taji anyi zance first night jikinta rawa yakeyi
Tana da suma sosai kuma Bata son kiso ta fison tayi ta tufkesu tana matukar son inda sumanta yake shiyasa take son gyrashi domin wani tsansi ne dashi ko an kitseshi sai ya kwance
Wanan kenan sauran maji nan gaba
*Cigaban labari*
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/3, 7:16 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my paid groups
______________
π
Ώ2β£7β£-2β£8β£
_________________
Bismillahir Rahmanir Rahim
A haka bacci ya d'auketa a ranan saheeb be dawo ba sai washe gari
Tana ganinshi ta fashe da kuka tana rokon shi
Yace"wallahi kiyi shiru ki bar b'atawa kan ki lokaci domin ko talakar ubanki bazai kwace ki ba sai na d'ana ki sai nasa ke da iyayen ki kunyi nadama "
Rokonshi take tana kuka cikin kuka tace"wallahi na tuba kamin Rai ka rama Marin ka nidai Dan girman Allah ka Bari in tafi wajen iyayena"ta kare magana da sakin wani kuka"
Yace"ki bar b'atawa kanki lokaci dan wallahi sainayi mikin abinda ko kudi aka bawa namiji ya aure ki bazai aure ki ba"
Tace"wallahi karya kakeyi babu abinda zaka min da Allah beyi ba mugu kawai ka sato ni ka raba ni da iyaye na kuma da kake cewa talakar ubana ai kaine babban talaka tunda komai kudin ka baka iya taimakawa na kasa da kai"
Yace"wai ke bazakiyi shiru ki bar zagina ba kila in tausaya Miki?"
Cikin kuka tace"dan Allah kayi hakuri nidai Allah ya isa na"
Murmushi yayi yace"watoh taurin kan a jinin ki yake ko?"
Zama tayi ta ma manta babu ko d'an kwalli kanta zufa take duk da sanyi ac dake d'anki ga dogayen sumanta ya barbaje a fuskarta "
Karasawa yayi ya gyra suman,d'angowa tayi ta kalleshi
Yace"harda gashin doki kike sawa Yan iska sai ayi ta pakewa dasa hijab"
Tsaki tayi ta ture hanunshi ta turashi ta nuna shi da yatsa tace"karka Kara tab'a min suma domin Ina matukar son gashina a rayuwata Dan haka bazan bari kazami irinka ya tab'a min ba,wanan aikin uztazuna ne"
Yace"Allah ko?"mikewa yayi yace"anyways I don't have your time zan tafi,but kwana nawa kike yin period?"
Hararanshi tayi tace"ban sani ba"
Yace"ok then zan baki 1week sai Nan zan dawo nasan ko kece kamfanin manja kin gama a lokacin Zaki san koni waye bani da mutunci"
Kuka ta fashe dashi tace"nidai Allah ya isana ka barni in tafi wallahi mamana bata da isheshen lafiya na tuba"
Ko kulata beyi ba saima cewa yayi in kin ji yunwa akwai komai a kicin in kuma da yunwa zaki zauna inda kikayi jiya it your choice na tafi"Yana gama magana ya bar gidan
B'angaren su baba ko duk inda ake sa ran za a gan fareeda abin ya faskara
Mama ko sumanta biyu yanzu ma haka a kwance take da drip a jiki domin jinin ta yayi mugun hawa
Baba ma karfin hali yakeyi ga surutu ya cika anguwa
Shima farouq hankalinshi yayi mugun tashi domin already fauziya ta riga ta gurb'ata me tunani kuma ko kad'an beson yan'uwanshi su San zance balle mahaifinshi da fauziya ta fad'a maganar a gaban shi
Haka fa aka cigaba da niman fareeda inda yau kwana 6 kenan baba ya rame yayi baki alhaji al'amin kuwa har station yaje da hoton fareeda Amma ba progress
Mama ta fita haiyacinta tayi baki baba ma ko abinci be iya ci
B'angaren fareeda ko duk dabaran da zatayi Dan ta gudu tayi Amma babu hanya domin kofofin gidan securities door ne haka ta hakura ta cigaba da addu'a ganin Zama da yunwa bazai taimaketa ba yasata fara dafa abinci duk da dai badan dadi take cin shi ba
Wani tsanan Dr takeji domin ko ba a fada Mata ba tasan mahaifanta na can suna kukan rashinta bazata tab'a yafewa Wanda yayi sanadiyan zubar hawayen iyayenta ba,kuka ko tayi shi har ta gode allah
Tashi tayi bayan ta gama cin indomie da ta dafa ta haura sama ta Shiga toilet tayi alwala
Fitowa tayi ta shimfide dadduma ta tada sallah domin ita kwana uku takeyi
Bayan ta idar tayi ta addu'a
Washe gari da safe
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/4, 12:54 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_______________
π
Ώ2β£9β£_3β£0β£
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Washe gari da safe iyalan alhaji al'amin ne zaune a dining suna cin abinci
Daddy ne ya kalli mummy yace"hajiya har yanzu fa babu labarin yariyar nan fareeda na tausayawa malam Abdallah "
Mummy tace"Allah ya bayyanata gashi bikinta Nan da kwanaki kad'an ne ai irin haka sai ya haddasa zargi tsakanin mijinta"
Shidai saheeb shiru yayi Yana tunanin badai fareedar daya sace dady ke magana akai ba"
Daddy ne ya kalleshi yace"Kamal ai a asibitin ka take aiki ko kasan inda taje Kuma yaushe ne last ka ganta domin ance daga zuwa night har yau"
Kallon daddy yayi yace"asibitina kuma?nifa ban san wata fareeda ba,but daddy baka tunanin ko wajen saurayinta taje ne?"
Dakuwa mummy tame tace"gidan ku Kai meyasa babu alkhari a bakin ka ne?"
Daddy yace"nifa nasan fareeda yariyar akwai natsuwa bana jin zata aikata hakan fatan mu Allah yasa tana lafiya,zan Kara zuwa police station inji ko sun samo wani labari"
Mummy tace"Allah ya taimaka"
Yace"Amin"
Saheeb a ranshi yace"yau dai zanyi abinda zanyi kafin asirina ya tonu"
Tashi yayi mummy ta kalleshi tace"Ina zuwa?"
Yace"asibiti"
Kallon tuhuma tame tace"wai meke faruwa ne?Kai da baka son zuwa aiki suddenly yanzu kullum sai kaje,iam warning you don't act anything funny cause I won't spare you"
Gabanshi ne ya fadi Amma ta dake yace"kedai mummy babu abinda zanyi in birge ki da bana zuwa kullum kina fad'a Amma yanzu kuma ina zuwa kina magana toh ai dole zan sa ido a aiki ko"
Bata Kara magana ba ta mike tana had'a plates
Gidanshi yayi direct inda yaje ya Sami fareeda zaune ta hade Kai da guiwa tana kuka
Dariya yayi yace"tun yanzu ai banma Yi komai bako,yanzu dai karki b'ata min lokaci ki tashi ki tube da kanki I don't have time Dan na gan alamun kin yi wanka'
D'agowa tayi da jajjayen idonta tace"ai sai dai ka tsallake gawa ta kafin ka aikata Zina dani d'an iska kawai"
Karasawa yayi cikin mugunta ya mikar da ita ya wanka Mata wani Mari daya sata sakin kara ta fadi saman gado
Jan rigarta ya farayi sai ya yage
Kwantawa yayi samanta ya fara kokarin hade bakinsu ta damke nata
Aiko sai ya rufeta da duka ta saki kuka yace"Dan kawai Ina ta Miki dariya?ni ba a tab'a ni in kyale yau zan nuna Miki ke karamar Yar iska ce ke karamar Mara kunya ....."Ai maganar makalewa yayi sakamakon fashewar bedside lamb da ya ji akan shi tuni ya koma gefe wanda a take ya sume
Tsoro ne ya kamata jiki na rawa ta saka hannu a aljihun shi ta cire makulli da k'yar ta iya bude kofar ta sauka da gudu ta bude na falon
Har zata fita ta kuma dawowa ta Shiga kicin ta ciro ruwan sanyi ta haura ta zuba me a jiki
Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke ya bude ido sai dai ya kasa motsi
Kallonshi tayi tame gwalo tace"serves you right sanan ta ruga a guje ta bar gidan
Shiko kanshi ya rike ga jini na zuba ya wanke me fuska
Yace"you won't get away with this"
Hmmm
*Wanene Dr saheeb?*
Maman
Noorul
Hudah
Luv u
Pls share
[1/4, 12:54 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my family
_____________
π
Ώ3β£1β£&3β£2β£
____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kamalundeen Al'amin shine asalin sunan shi Amma ana kiranshi da saheeb saboda ya ci sunan kakanshi watoh mahaifin daddy shi
D'an ne ga alhaji Musa al'amin da mahaifiyarshi Rukayya Wanda in ka ganta sai ka rantse balarabiya ce Kuma ita fulani ce fulanin taraba
Iyayenshi auren soyyaya sukayi inda ko shekara Basu da aure basuyi ba Allah ya Basu haihuwa suka haife shi
Alhaji Musa d'an kasuwa ne Yana da kamfannoni mutum ne me son jama'a ga iya Zama da mutane
Su biyu ne a wurin iyayensu shi da kanwarshi Iman
Saheeb da Iman sun taso ne cikin so da gatan iyayen su kasancewar mahaifinsu attajiri ne Wanda yake da kamfanoni dayawa
A Niger State (Minna) suke da Zama Amma asalin mahaifinsu d'an kano ne Amma mummy taraba a makaranta Suka had'u da daddy har sukayi aure
Hajiya Rukkaya barrister ce sai dai bata aiki
A minna saheeb yayi primary da secondary dinshi inda ya gama al-amin international School Yana gamawa Daddy ya turashi kasar waje inda ya karanta likitanci ya Zama cikeken likita watoh medical doctor Wanda yasan aikin shi
Sai dai saheeb bashi da halin kirki domin tun Yana karami ya tsane talakawa ga rainin wayau da rashin girmama na gaba dashi,mummy tayi iyakar kokarinta na ganin ta seta shi Amma abin ya faskara domin ita kadai ke fama daddy be damu ba, irin mutanen Nan ne I dont care duk da shima wani lokaci ya kan me fad'a
Tun Yana turai daya kusa Gama makaranta Daddy ya fara Gina me asibiti babba me girman gaske domin ya faranta mishi
Saheeb Yana shaye-shaye tun Yana secondary school kuma iyayen shi sun sani mummy dai tana iyakar kokarinta na ganin ta gyra me rayuwa sai dai kamar a banza takeyi domin komin fad'an ta in yayi niyar yin Abu baya fasawa sai dai wani lokaci Yana mugun shakkata kasancewata no nosense ne ita"
Kamanin saheeb d'aya da mummy shiyasa mutane ke me kallon balarabe domin fari ne tas ga kyau kamar mace ga gashin kanshi kwance
Ranan daya farawa zuwa asibiti kenan ya had'u da fareeda har tame wanan Marin Wanda da tasan ko waye saheeb da Bata kuskura ta wanka me wanan Marin ba,saheeb irin mutane nan ne da basu da tunani da rashin Imani balle in yayi shaye-shaye,saheeb har wiwi yana sha,saheeb bashi da yafiya ko kadan domin ko Iman ne tame laifi sai ya rama hakan yasa shi d'aukan alkawarin b'atawa fareeda rayuwa at all cost
Shekaran saheeb 27 ita kuma Iman 23
Wanan shine kad'an daga cikin labarin saheeb sauran zaku ji Nan gaba sai dai fa kuyi hakuri da abinda zaiyi wa fareeda
Wanan kenan
Cigaban labari
Maman
Noorul
Hudah
Luv u
Pls share
[1/4, 6:51 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
___________
π
Ώ3β£3β£-3β£4β£
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Da k'yar ya jawo waya ya Kira Mahmud ko minti ashirin ba ayi ba ya zo gidan
Abu kamar Wasa sanda saheeb ya Sha ledar ruwa hakan ya kara sashi saka mugun kudiri a ranshi na ko me zai faru sai ya wulakanta fareeda tunda har tayi sanadin da yayi jinya
Fareeda ko tana fita ta tare me adaidaita gida tayi direct inda ya sauketa ta Shiga ciki domin anso me kudi
Baba dake zaune yayi tagumi Yana ganinta ya mike yace"fareeda Ina kika Shiga har tsawon kwana bakwai kuka ta fashe dashi
Tace"saceni akayi baba yanzu dai bani kudi in kaiwa me adaidaita"
Kudi ya bata ta kaiwa me a daidaita a kofar gida ko sai kallonta ake Bata kulasu ba ta shige gida
Zama tayi baba ya kalleta yace"Ina jin ki"
Kallonshi tayi tace"baba Ina mama tunda na dawo ban ganta ba"
Yace"tana d'aki an Samata ruwa hawan jini ya kamata"
Mikewa tayi ta shige d'akin ta rungume mama dake bacci bude ido tayi tana ganin fareeda ta fara kokarin tashi
Tace"mama karki damu na dawo kenan"
Mama cikin muryar marasa lafiya tace"Ina kika shiga kika barmu cikin damuwa?"
Tace"wallahi Rana nan Ina dawowa wasu Suka sace ni Suka saka ni a mota yanzu ma da k'yar na kubuta"
Baba zaiyi magana sai yaji sallama daddy
Fita yayi suka gaisa daddy yace"yanzu kenan na fito daga ofishin yan sanda Amma har yanzu shiru karka damu nasan za a dace"
Cikin ladabi baba yace"ai mun gode Allah yanzu ta dawo"
Daddy yace"ikon Allah alhamdullilah Kira ta"
Fitowa farida tayi ta durkusa har kasa ta gaisheshi
Kallonta yayi yace"fareeda ya akayi haka kuma?"
Shiru tayi a ranta tace"d'an ka shi ya saceni"Amma a fili sai tace"wallahi Abba saceni akayi aka kaini wani gida"
Yace"ikon Allah Amma waye yayi Miki wanan aikin domin nasan da kidnappers ne da sunyi demanding ransom"kallonta yayi yace"Zaki iya gane ko in ce kin San Wanda yayi Miki wanan aikin"
Shiru tayi tana tunanin ta fad'a me gaskiya ne ko ta b'oye me"
Maganar shi ce ta katseta da yace"kin Yi shiru"
Kawai sai ta yanke shawaran ta b'oye me d'anshi ne yasa aka sace ta saboda dalilai uku,na farko bata son abinda zai kawo rashin fahimta tsakanin daddy da baba domin tasan halin baba da zuciya ba karamin b'aci ranshi zaiyi ba in ya San gaskiya Kuma zaice zai Kai Kara station domin zaice dan saheeb d'an me kudine bashi zai bashi damar wulakanta yar'shi ba,dalili na biyu shine Bata son surutu yayi yawa a ce tayi rayuwa a gidan wani namiji har na tsawon sati d'aya Bata ma son uztazunta ya San gaskiya dama ta lura ya fara canja Mata tasan aikin fauziyane,dalilin na uku shine bata son ta Kara shiga harka saheeb ko aikin ta hakura tana gudun ta fadi gaskiya ya zo yayi Mata abinda yafi nada"
Kallon Abba tayi tace"ban sanshi ba"
Abba yace"ok zan Kira Yan sanda ayi bincike ai nasan kin San inda suka kaiki"
Tace"daddy a sume Suka kaini kuma da na gudu ban lura da anguwan ba saboda saurin karsu kamani bazan gane ba"
Daddi yace"Yan sanda zasuyi aikin su"
Tace"nagode"
Cikin kankanin lokaci surutai ya cika anguwa kowa na fadin albarkacin bakinshi wasu suce yawo taje wasu Kuma suce dama sun San irinsu
Bayan wasu kwanaki saheeb sanda yayi Kwana uku be koma gida ba
Ran mummy yayi mugun b'ace d'aya dawo sai ta ganshi da bandage tayi me tambayar duniya Amma yaki fadin meya sameshi da ta masa ne sai daddy yace a barshi Mana ai shi ba yaro bane"badan taso ba tayi shiru
Bayan wasu kwanaki bikin fareeda da uztazu ya rage kwana biyu tunda ta dawo Bata koma wurin aiki ba sai dai uztaz ya mugun canja Mata baya zuwa gidansu ko yaje ita kadai ke magana
Shiko SAHEEB hankalin shi a tashe yake ganin har zatayi aure be samu ya d'au fansa ba sai dai fa ya d'au alwashin baza a d'aura auren nan da farouq ba
Zuwa yayi ya d'au katin bikin da aka bawa daddy
Number dake cikin katin ya kwashe ya Kira
Yace"Dan Allah Ina magana da farouq ne"
A d'ayan b'angaren aka ceme ah'ah
Yace"pleaes number shi nake so ne domin Ina son muyi wata magana ne"
.Abbas abokin farouq ba tare da tunanin komai ba ya tura me number
Murmushi yayi a take ya Kira number
Farouq na d'agawa da sallama
Saheeb yayi murmushi yace"saurayin fareeda ne na kirane in maka kashedi ka fita hanyar karuwata in ba haka ba toh Ina tabbatar maka mu biyu zamuyi ta hawanta domin ko ka aureta bazai Hana mu had'uwa ba"
Ai wani fadiwar gaba uztaz ya ji yace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/4, 6:51 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
___________
π
Ώ3β£5β£-3β£6β£
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
cikin mugun tashin hankali farouq dake tsaye cikin d'akin shi ya zauna yace"bawan Allah karka Mata sharri fareeda ba haka take ba"
Dariyar rainin hankali saheeb yayi yace"Ashe kaima kana cikin mahaukata Wanda fareeda ke yaudara ta Sha fad'a min Kai Wawa ne shiyasa tace"muje muyi sati d'aya mu huta kafin auren Ku ta Kuma cemin indai Kaine ko wani karya ta shimfid'e maka yarda zakayi,ka tab'a tunanin meyasa da Bata night duty sanda na dawo ta fara nine Dr saheeb ai babu abinda mukeyi sai hulewa"
Hawaye ne ya fara gangara daga idon uztaz jinshi shiru yasa saheeb yin murmushi samun nasara
Yace"nidai na dai Kira kane in baka shawara ka fasa auren nan in ba haka ba fareeda matar maza biyu ne"
Yanke wayar uztaz yayi ya kwanta Yana jin wata tsanan fareeda
Shiko SAHEEB yayi dariya yace"kin Yi kuskure yariya"
Bayan kwana biyu
Yau ta kama juma'a kuma yaune d'aurin auren fareeda da farouq gidan ya cika da makota da abokan arziki
Amarya ko tayi kwaliya cikin wata atamfa Wanda ta tsaya da kudinta domin ba laifi ta dade tana tanadi su humaira ne zaune suna Mata tsiya
Bayan sallah juma'a aka cika a cikin massalacin kofar gidansu fareeda
Sai dai fa an share awa biyu ba a gan ango da walihi shi ba babu jama'arsa
Daddy daya gaji da jira yace"wai malam Abdallah meke faruwa ne?"
Baba dake kiran number farouq a Karo na ba adadi
Sai yanzu ya d'aga baba yace"ya na jiku shiru Kuma na Kira number kawunan ka akashe"
Farouq yace"fasawa mukayi "
Baba besan lokacin da yace"kun fasa Kuma?"
Tasowa saheeb daya nace sai ya biyo daddy yayi yace"baba meya ce?"
Baba da ya rike Kai idonshi ya canja kala ya kalli daddy yace"wai sun fasa"hawaye ke gangarowa a idonshi yace"sun b'atawa ya'ta rayuwa,har cemin yake wai shi bazai auri karuwar da taje karuwanci har na tsawon sati d'aya ba"
Daddy yace"karka damu za a San abinyi"
Saheeb yayi saurin cewa daddy me zai hana ni a d'aura dani?"
Baba yace"ah'ah karka damu zamu yarda da kaddara bana son ka zo daga baya ka wulakanta min ya'ta tunda a araha ka sameta ko kamata gori".
Daddy yace"karka damu na dade Ina son haka ta faru domin na yaba da hankalin fareeda"
Baba zaiyi magana daddy ya dakatar dashi
Shidai saheeb addu'a yake baba ya yarda
Daddy yace"muje ka gan ai mu bar jamma'a kuma ka hakura ayi auren Nan gashi mun tara jama'a
Yace"toh"
Suna komawa ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren
KAMALUDEEN
~Da~
FAREEDA
Akan sadaki dubu hamsin
Su dai yan cikin gida Basu San meke faruwa ba ciki kuwa harda fareeda ga Daddy ya roki alfarma Kar a sanar da ita a bari ta gani da idonta
Shiko SAHEEB ana fitowa daga d'aurin auren ya Kira wani mutm
Yace"ka min booking flight din?"
A d'ayan b'angaren akace 12:am zai tashi
Yace"good"
Kira Mahmud yayi yace"ya maganar maganin da kace zaka bani na gargajiya?"..!
Mahmud yayi dariya yace"kace plan din yayi kenan?".
Yace"eh Mana"
Mahmud yace"
Toh fans ya kuke ganin zai kasance?miye plan din saheeb nidai shawarata team fareeda a zauna da shiri karya shnmace ku
No my water inside wooo Kar a zo a ce na fiye muguntaπ€ͺ
Maman
Noorul
Hudah
Pls share
[1/5, 9:33 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to all my fans
____________
π
Ώ3β£7β£_3β£8β£
_______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mahmud yace"ok zamu had'u zan baka maganin zaka iya 4hrs kanayi zaka ajiye tarihi a rayuwarta da ko ganin ka tayi wallahi sai ta firgita balle ya Kai ga,ta d'aga hannu ta mare ka"
Yace"good Ina gamawa zan bar gari wallahi"
Mahmud yace"in kana so sai in Taya ka"
Tsaki yayi yace"kaifa d'an iska ne matar nawa"
Daddy ne ya taho inda yake yace"muje toh muyiwa mummy bayanin komai kasan ba musan da bikin ba"
Yace"toh"
Zuwa sukayi wajen baba da kwata-kwata harkan auren beyi me ba ya dai jin kunyar alhaji ne Amma shifa harga Allah baya son aje a wulakanta me ya'
Duk daddy ya lura da yanayin shi kallonshi yayi ya dafa shi yace"malam Ashe duk tsawon shekaru da muka kwashe muna tare baka yarda dani ba Kamal d'an na ne kuma ai a gaban ka ya nuna da kanshi ba dole akayi me ba Yana son auren fareeda ka kwantar da hankalin ka inshaallah za a rike ta Amana"
Baba ya kalleshi ya Kama hanunshi yace"alhaji ba haka bane Amma Ina gudun aje a wulakanta min ya'ta wallahi bazan ji dadi ba nasan ya'ta na kuma yarda da tarbiyarta shiyasa Nike