was carried away I guess shine dalilin da ya hana ki magana d'azu ko?"
Mummy ko tace"ba baki kadai ba kina bukatar wanka"
Har bakin kofa ta rakata ta shiga sanan mummy ta dawo ta zauna d'aga Kai tayi ta kalle Dr mustapha sai kawai ya Sosa kai
Murmushi tayi tace"nasan jira kake ta fito ka shafa mata mai ko son?"
Da sauri ya bar ward din cike da kunya,Yana fita tace"kayiwa kanka saheeb"
Ba a jima ba fareeda ta fito d'aure da zani a kirji
Mummy ta Mika Mata wani dogon riga tasa tace"kina ta kallona,Zaki ce waye wanan?"
Murmushi yake fareeda tayi Amma batayi magana ba
Mummy ta kama hanunta tace"ni ce mahaifiyar saheeb"ta kare magana tana kallon kwayar idon fareeda
A take fuskar fareeda ta canja babu abin da kake hangowa sai tsanan Saheeb
Mummy ma sanda ta d'anyi Jim tukkuna harga Allah taji ba dadin yanayin fareeda sai dai ya zatayi shi ya jawo
Cikin sanyi jiki tace"dear ya abin ya faru"
Jikinta ya fara ruwa ta rungume mummy tace"mummy kashe ni ya so yi yana ta dukana ya yaga min kayan jikina mummy na tuba ko wani na gan yanayiwa babba rashin kunya bazan kara cewa komai ba"cikin kuka ta kwashe labarin komai ta fad'a Mata ta kare da cewa"nidai Allah ya isana"
Mummy tace"karki damu kin ji yayiwa kanshi"
Tace"mummy su mama basu zo sun gan ni ba? Yama akayi na Kare a gidan saheeb shine fa ya sace ni kwanaki criminal ne"
Mummy tayi shiru na d'an lokaci kafin tace"an fasa aurenki ne da farouq shine akayi da saheeb bamu San abinda yake shiryawa ba kenan"
Tunawa tayi da ya fad'a Mata shi ya Kira farouq
Tace"mummy shi ya shirya komai shi ya Kira farouq ya fad'a me ni karuwa ce"
Mummy tace"ki kyaleshi Allah ya isanki"
Tace"nidai a maidani gida Ina son ganin baba"
Mummy ta zauna kusa da ita tace"ah'ah gidan mu zan kaiki kina son ciwon mama ya tashi ne jin labarin abinda ya faru dake zai iya sasu cikin damuwa and yan anguwa zasu bude shafin gulma kin San yanzu kiwon mutum akeyi ko kina son baba da mama su shiga damuwa an sakoki a daren auren ki"
Kallon mummy tayi cikin alaman tambaya mummy tace"hmmm yayi Miki saki d'aya Amma karki damu daga yau kin Zama ya'ta Amma dan girman Allah kiyi hakuri ki zauna damu karki Bari kowa yasan wanan maganar harda iyayen ki duk Wanda ya tambayeki mijin ki, ki ce ya tafi Karo ilimi a kasar waje,ke kuma za a saki a makaranta ki cigaba da karatun ki"
Tace"nidai bazan iya Zama a gidan ku ba na tuba Dan girman Allah ki barni in tafi gida ni bazan iya Zama gida d'aya da saheeb ba"
Rungumeta mummy tayi domin jikin ta har wani mugun rawa yakeyi
Tace"karki damu ya tafi inda aka haifesa bazan tab'a bari a cutar da ke ba"
Tace"toh nagode"
Tea Mai kauri ta Bata ta Sha sanan ta fara had'a kayanta
Dr musty ne ya turo kofa
Mummy ta kalleshi tace"
Kuyi hakuri yau na ce bari inje break inyi bacci
Shima Dr saheeb yace"yau in muku horo domin ba laifi ya Sha zagi jiya shiyasa yace"in huta sai ya gan ta inda za a hukunta shiπ€£ππtunda kowa gudun shi yake
Fans a gaskiya nagode da kaunar ku Ina mugun yin ku please mu hade gobe inshaallah a min uzuri yau ba haka na so ba
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 11:15 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_______________
π
Ώ4β£9β£-5β£0β£
_______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mummy tace"Dr tunda baka sallame mu ba mun sallame kanmu"
Shafa kai yayi,yayi murmushi shi Mai kyau yace"Yi hakuri na gan jikin nata da saura ne"
Hararanshi tayi tace"toh mudai mun tafi"
Itadai fareeda dukar da kai tayi domin ya zuba Mata ido
Ganin ya takurata ya sata mikewa tace"mummy Ina hijabi na?"
Mummy tace"ga wani can"
D'auka tayi tasa ta d'ago kai sai su had'a ido
Mummy tace"muje daddyn ku na waje".
Dr musty ne ya amshi kayan hanun mummy ya bi bayansu har suka Kai wajen mota ta ansa tame godiya
Daddy yaji dadin farfadowan fareeda yayi Mata ya jiki tare da niman alfarma karta sanar da iyayenta in sun tambaye ta tace"kasar waje taje amma ta dawo"
Suna kaiwa gida mummy ta kaita wani had'aden d'aki babu abinda babu komai na d'akin sea green ne"
Tace"daga yau d'akin ki ne wanan kiyi wanka ki fito ki ci abinci kafin Iman ta dawo ga akwatunan da anty samha ta kawo na lafen ki cire kaya kisa"
Tace"toh"kawai tace ta zauna bakin gado
Mummy ko taje kicin dan girka masu abinci Mai lafiya domin tun bayan abinda ya faru yau ne zasu ci abinci hankali kwance
Tashi tayi ta shige toilet tsayawa tayi gaban madubi tana kallon kanta da gashi ya fara tsirowa
Hawaye na gangarowa tace"I hate you Dr saheeb I hate you"
Kuka sosai tayi kafin ta mike tayi wankan ta,ta fito d'aure da towel
Mai da ta gani gaban madubi ta shafa ta fashe jikinta da tulare ta saka atamfa riga da zani tasa hijab ta fita
Sauka tayi nan ta gan mummy zaune a dining
Tace"mummy shine baki jirani na taya ki ba"
Mummy tace"ah'ah ke da baki da lafiya"
Tace"ai naji sauki"
Mummy tace"haba dota Nan ma fa gidan ku ne ki cire wanan hijabin"
Zatayi magana mummy ta katseta da cewa bana son musu
Murmushi tayi ta cire sanan ta zauna mummy ta zuba Mata
Daddy ne ya sauko cikin jin kunya zata mike yace"Yi zaman ki ai ke na gidane
Zama tayi sai dai a takure take
Iman ne ta shigo da gudu ta rungumeta tace"lah anty Ashe kin farka"
Murmushi tayi tace"Allah yayi "
Iman tace"iam very happy today"
Daddy yace"Iman har yanzu a na sayar da foam a school dinku ko an rufe".
Tace"eh,da last week za a kulle sai kuma suka Kara one weeek"
Yace"ok gobe ki siyowa fareeda medicine Nike son ta karanta,sanan anjima zan kawo Miki sabon waya ki kira su baba ki fad'a musu dama tafiya kikayi Amma yanzu kin dawo domin ko basu fad'a ba hankalin su a tashe yake"
Tace"toh abbana"
Yayi murmushi
Zama Iman tayi ya fara cin abinci suna gamawa ta ja hanun fareeda zuwa d'akinta
Ta kalleta cikin ido tace"fareeda!fareeda!!fareeda!!! So nawa na Kira ki?"
Fareeda ta dukar da Kai"
Tace"in nine ke zanyi amfani da wanan second chance din in gyra kuskurena ta hanya sa ido a karatu in Zama abin al'fari ga iyayena zanyi amfani da wanan daman in nunawa maza masu hali irin na Yaya cewa ni macece zan iya juya duniya inda na so,Mata ba abin rainawa bane "
Ina son kullum in kika kalli madubi kika kalli kanki sumanki da ya kwashe ya tuna Miki cewa kullum kina da task a rayuwa kina da aiki da zakiyi sanan kina da makiyi da Zaki nunawa bazakiyi give up ba"
Fareeda ta fashe da kuka ta rungumeta
Tace"faree ina son ki zama wayayya mace,wayewa baya hana
Addini,ki cire duk wani tunanin abinda ya faru a baya ki wasar sanan wanan kuka da kikeyi ki daina shi cigaba muke nima kuma shi muke so,Ina son ki daina tunanin baya gaba kawai zakiyi ta tunawa ina son abinda ya faru a baya ya zame Miki tarihi karki Kara waiwayanshi ki kasance ke tunanin gaba kikeyi ki daina tuna farouq ,ki kuma manta da saheeb da ya maiyar dake karaman bazawara only focus just focus"
Cikin kuka tace"ai ba laifin uztazuna bane Kiran shi akayi ak ......"katseta Iman tayi da cewa"har yanzu kina gani uztazun ki bashi da laifi?toh inda Yana sonki kome aka ce kinyi wallahi bazai fasa auren ki ba duk a cikin wanan lamarin nafu ganin laifinshi domin be yarda dake ba kuma ki godewa Allah da baki aureshi ba,Ina son ki sani fareeda komai ya faru da bawa toh Allah na da dalilinsa na haka "
Cikin sanyi jiki tace"haka ne"
Iman tace"yauwa ko kefa"
Tayi murmushi kuma ta d'au alkawarin mantawa da komai Amma saheeb bazata tab'a mantawa dashi ba"
Soyyayen nama taje kicin ta debo a plate ta kawo suna ci suna hira dan sosai fareeda ta saki jikinta
Har daddy ya dawo Mata da sabon waya me sadar gaske tayi murna sosai tana me godiya
Yace"karki damu ki saki jikin ki ki d'auke mu a matsayin iyayen ki"
Tace"toh a take ta Kira number mama dan tana dashi akai
Bugu biyuta d'auka tace'
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 11:15 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
______________
π
Ώ5β£1β£&5β£2β£
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mama ne ta d'auka da sallama
Fareeda tayi murmushi tace"lah mama kiyi hakuri ba Kira ku ba"
Cikin farin ciki mama tace"lah fareeda ce"
Fareeda da ta danne hawayenta tace"eh nice Mama"
Mama tace"Kai fareeda baki kyauta ba kin samu cikin tashin hankali"
Da k'yar cikin kokarin karta fashe da kuka tace"nayi kewar ku"
Baba ne ya fisge wayar yace"badai matsala ko fareeda?"
Tace"babu jiya muka dawo inshaallahu zan zo in na huta"
Yace"toh ya mijin naki baki dai Yi fushi da ni bako?"
Tace"eh baba nasan komai kayi kayi shine Dan farin cikina"
Yace"toh nagode sai kin zo"
Tace"toh baba"
Suna Gama magana ta shige d'akinta har zatayi kuka ta tuna da maganganun Iman kawai sai tayi murmushi ta kunna tv ta shige bargo tana kallo
B'angaren Saheeb ko wata d'ayan Nan a daddafe yayi shi domin in ya rufe ido babu abinda yake gani sai lokacin da yake muamula da fareeda duk ya rame yayi baki,kuma shidai yasan ba sonta yake ba toh meke faruwa dashi ne
Kawai sai ya yanke shawaran cigaba da karatunshi ya karo illimi domin ya dagana abinda ke damunshi da rashin aikinyi
Aiko ya samu aka d'aukeshi ya fara makaranta sai dai fa abin girmama yakeyi kullum Yana cikin tunanin ta balle in ya tuna ya saketa sai ya ji ba dadi domin gani yake zata kula wasu
Abin har ya Kai ga ko namiji ya gani sai ya kira da fareeda
Shidai har yanzu be yarda sonta yake ba ya d'au may be sha'awa ce kawai.
Abin takaici ko bacci baya samu da ya rufe ido sai ta zo me
_____________
Bayan wasu kwanaki fareeda ta saki jiki sosai tayi kiba tayi bulbul cikin ikon Allah suman Nan ya fara fitowa yayi kyau
Mummy na Bata kulawa kuma ta samu admission an bata 200level da result dinta na midwifery
Iman ko na kokarin mayar da ita classic lady
Shiko Dr musty ya kasa samun natsuwa tunda suka bar asibitin dan haka yau ya yanke shawaran zuwa gidan tunda yasan ba aure a kanta
Yau dai ta tashi da kewar humaira dan haka wajen mummy taje ta amshi tsohon wayarta ta dawo d'akinta ta kwashi number hummaira ta kirata
Humaira na d'agawa tace"Kai kawas baki da mutunci a ce ko Kira babu"
Humaira cikin jin dadin jin muryarta da ta dade tana son jin tace"lah shegiyar d'ari Ina kika Shiga ne?"
Murmushi fareeda tayi tace"na leka lahira ne na dawo"
Hummaira tace"ban gane ba"
Tace"ki zo please zan turo miki da address kin ji Ina jira"
Humaira tace"ki bani Nan da awa d'aya Ina da lectures '
Tace"ok"
Sauka tayi ta fad'awa mummy zatayi bakuwa
Mummy tace"toh ki shiga kicin ki dafa Mata abinda zata ci"
Tace"ok"
Zuwa tayi ta fara had'a girki"
Kafin minti 40 ta gama domin taliya ta dafa da miya
Komawa tayi d'aki tayi wanka ta saka wani riga da wando da Iman ta siyo musu anko
Tayi masifar kyau gyra guntun sumanta tayi dake kwance tayi sai ya kwanta Kamar sumanda akayiwa Jerry curl sai tayi Kama da irin classic iya muran nan
Kallon madubi tayi ta gan tayi wani kyau sai kawai tayi murmushi tace"bari inyiwa kaina selfie"
Waya ta ciro ta seta camera tayi masifar kyau a hoton a take ta sashi a screen saver
Iman ne ta turo kofa ta ganta tace"wow kin gan inda kikayi kyau kuwa ko Nima zan aske sumana ne dan inyi irin wanan kyau din"
Hararanta tayi tace"sis banson haka fa"
Tace"allah kinyi kyau Bari in Miki selfie"
Tace"ok muyi tare"
Hotuna sukeyi da wayar Iman sai fareeda ta ji sallamar humaira da gudu ta bar d'akin tana dariya
Binta Iman tayi,tana sauka ta rungume ta tace"nayi kewar ki"
Humaira da harga Allah Bata gane fareeda ba ta turata tace"nifa fareeda Nike nima ko ba Nan bane gidan alhaji al-amin ?"
Murmushi fareeda tayi tace"ke banson iskanci ba ganinan ba"
Kallonta humaira tayi da kyau kuma tabbas muryar fareeda ce tace"ke ya haka?"
Fareeda ta ja hanunta tace"muje d'aki
Iman dake gefe tana kallonsu tace"humaira meya kawo ki gidan mu?"
Kallonta humaira tayi sai kawai ta saki ihu tace"lah Iman me kike a Nan"
Tace"gidan mu ne ai"
Fareeda ta kallesu da mamaki tace"Ina kuka San juna?"
Tace"
Department dinmu d'aya kuma ko d'azun muna tare"
Tace"toh muje ciki"
Suna Shiga humaira tace"nifa ban gane ba na gan duk kin canja min kuma meyasa kika rage suman kanki?"
Murmushi fareeda tayi tace"is a long story Bari in d'auko Miki abinci sai in baki labari a lot has happened"
Tace"ok"
Abinci ta kawo duk suka had'a hannun Suka ci a tray
Humaira tace"toh Ina jin ki"
Ajiyar zuciya fareeda ta sauke ta kwashe komai ta fad'a Mata
Babu abinda humaira keyi sai kuka tana tsinewa saheeb
Iman da duk jikinta yayi sanyi Bata jin dadin maganar humaira ba
Fareeda ne ta lura da haka domin koya naka yake naka ne"
Ta kalli humaira tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 4:28 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_____________
π
Ώ5β£3β£_5β£4β£
____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ta kalli humaira tace"kedai a bar maganar kawai"
Humaira da a sane take dibewa saheeb albarka hararan Iman tayi tace"barni in fad'a karta kashe ni"
Murmushi yake iman tayi tace"ai gaskiya ta fad'a"
Hira suka cigaba dayi fareeda tace"wai har yanzu shiru ke da Umar"
Tsaki humaira tayi tace"tuni Muka rabu cewa yayi beso inyi karatu toh ni ina zan iya shiyasa nace ya nimi wata zamanin nan da tsofofi da sufar su suna niman ilimi balle ni ai karatu tayi da a ce bakiyi karatu ba wanan d'an iskan yayi Miki iskanci Nan da daga Ina zaki fara"
Fareeda tace"kedai kin fiya fad'a"
Tace"na kaiki? ai kin fini shiyasa kika shiga abinda bana naki ba ya janyo Miki matsifa tsohon na nan hankali kwance gashi an raba ki da wanan suman larabawan"tayi kwafa fad'a take sosai babu abinda ke bata haushi sai suman da ya yanke
Tun abin na bawa Iman haushi har ya fara bata dariya kallonta kawai take,in humaira tayi shiru sai ta Kara kallon fareeda tace"wai da gaske ya aske suman?"
Tashi tayi tace"bari in Yi alwala inyi sallah"
Shiga toilet tayi tayi alwala ta fito rike da d'an kwali da tulin ribborn na a cuce maza
Kallon kanta Iman tayi tace"no wonder yanzu na gane dalilin fad'an ki ashe dai babu suman ne kamar na gemu"
Hararan ta tayi ta d'aura d'an kwalita tasa hijab
Itadai fareeda dariya takeyi
Tana idar da sallah ta d'auki Jakarta tace"ni na tafi sai na sake zuwa"
Har gate suka rakata a nan take fad'a musu tayi wani saurayi sunan sa Mahmud
Murmushi fareeda tayi tace"Allah yasa shine mijinki"
Tace"amin"
Komawa gida sukayi bayan ta samu abin hawa
Fareeda ta zauna suna hira
Mummy tace"shikenan yanzu ranan Monday Zaki fara zuwa school ko?"
Tace"eh mummy"
Mummy tace"ok asa ido a karatu"
Kallon mummy tayi tace"mummy kamar kina da damuwa ko"
Tace"me kika gani?"
Farida tace"na gan cikin kwana biyunan sai kiyi zurfi cikin tunani"
Tayi murmushi tace"stress ne"
Fareeda ta kama hanunta tace"mummy nasan kina tunanin Dr ne tunda ya tafi baki ji shi ba"
Mummy zatayi magana fareeda ta katseta da cewa"ba sai kin ce komai ba nasan ke uwace ta gari kuma na dade da gane ran ki ya b'ace akan abinda saheeb yayi kuma kin d'au alkawarin koya me hankali Amma ai ke kika haife shi dole wata rana tausayin ki na mahaifiyarshi sai yafi karfin zuciyarki but ya zakiyi? kin kasance mace Mai adalci Wanda take so kwato min yanci"
Rungumeta mummy tayi tace"nagode da fahimtar ki Amma wallahi duk randa saheeb ya dawo ni dashi ne"
Fareeda tace"nagode mummy Amma karkiyiwa d'ankin komai sabodani ni na fita harkanshi bana son ganin shi na tsan...."
Shiru tayi sakamakon kallon da mummy ke mata
Murmushi mummy tayi tace"ki fadi zuciyar ki bazan gan laifin ki ba sweetheart"
Tashi tayi cikin jin kunya tace"mummy ni zan Shiga ciki in huta"
Mummy tace"ok"
Da misalin karfe 8:pm
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 4:28 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_____________
π
Ώ5β£5β£_5β£6β£
_______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Da misalin karfe 8pm
Tana kwance tana posting hotuna a Instagram da charting a watsaap sai ga Iman ta shigo da sallama
Kallonta tayi tace"ana nan dai ana ta charting"
Tace"eh wallahi"
Iman tayi murmushi cikin sigar zolaya tace"mu dai Kar ayiwa Yaya mun kishiya"
Ai sai fareeda ta hade giran sama da kasa tace"gaskiya karki kara kira sunan shi a gabana bana so"
Iman ta sauke ajiyar zuciya tace"ki zo in ji mummy kin Yi bako"
Zaro ido tayi tace"bako kuma waye?"
Tace"kije zaki ganshi"
Tashi tayi tasa hijab ta sauko
Tun tana saukowa Dr musty ya gan ta wani canja ta Kara haske da kiba fatan jikinta sai kyali yake domin yana Shan hutu
Hade rai tayi domin ta lura dashi tun a asibiti yake ta wani irin kallonta
Zama tayi a kusa da mummy tace"mummy an ce nayi bako"
Mummy tayi murmushi tace"eh mustapha ne ya zo"
Turo baki tayi cikin shagwab'a da yanzu mummy ne ta shagwab'a ta
Tace"toh mummy ni miye hadi na dashi da za a kirani wajen ki ya zo"
Mummy tace"ke bana son shashanci kaishi falon baki ki bashi abin Sha"
Tashi tayi tana kunkuni ya bi ta a baya yana murmushi
Suna shiga falon ya zauna yace"haba my faree ba gaisuwa ne?"
Turo baki tayi tace"Ina wuni"
Bata jira ya amsa ba ta bar falon ta koma ta d'auko ruwa da juice sai snack ta dawo ta ajiye ta cigaba da lasar waya
Fisge wayar yayi yace"haba Mana babu kyau wulakanta mutum ai sai saurareni ko?"
Tace"toh Ina ji"
Yace"fareeda I will go straight to the point nidai na kamu da son ki tun randa aka kawo ki asibiti na please ki bani dama in nuna Miki nawa kalar soyyaya"
Tace"a gaskiya kayi hakuri yanzu bani da ra'ayin soyayyaya makaranta zan koma"
Yace"kina nufin in baki lokaci?"
Tace"no ka nimi wata saboda Kar in b'ata maka lokaci domin zan Kai 3years kafin in fara kula wani"
Yace"ko ten years ne zan jira amma taimako d'aya Zaki min ki bani number ki"
Zatayi magana yace"please"
Tace"ok"number ta kirame yayi saving sanan sukayi sallama"
Yana wucewa ta dawo falon ta gan daddy zaune
.
Murmushi tayi tace"lah Ashe ka dawo"
Yace"eh amma Ina kike na tambaya ance kinyi bako"
Tace"eh Dr mustapha ne"
Yace"me ya kawoshi"
Tace"daddy cewa yayi Yana sona zai aure ni"
Ai sai daddy ya zaro ido yace"
Maman
Noorul.hudah
Share
[1/8, 9:59 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and by expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
____________
π
Ώ5β£7β£-5β£8β£
______________
Bismillahir-Rahmnir Rahim
Yace"aure kuma?"
Tayi murmushi tace"Nima dai daddy haka nace me ya nimi wata ni karatun zanyi"
Yace"ai yafi ya nimi wata kawai"
Ba tare da ta kawo komai a ranta ba tace"ni wallahi bazan karayin aure ba"
Yayi murmushi yace"je ki kwanta gobe mayi hiran bacci Nike ji"
Tace"goodnite sweet dad"
Yace"nite my princess"
Yana Shiga d'akin shi ya tarar da hajiya kwance ta lumshe ido yasan ba bacci take ba domin kwanakin nan haka take
Yace"hajiya meyasa kike bari samari na zuwa wajen fareeda?"
Bude idonta tayi tana gyra kwanciya tace"laifi ne?"
Yace"hajiya nifa nasan komin daren dadewa yaron nan zai dawo kuma daya dawo zan sake musu aure domin ita kadai ce zata seta shi kuma hakan shine rufan asirin mu iyayenta baza su gane ba"
Tashi hajiya tayi tana kallon shi for the first time da zai gan b'acin ranta irin haka tace"wallahi alhaji baka Isa ba Koda maza sun Kare a duniya Kuma ko Kamal zai mutu wallahi farida tafi karfin shi sai dai ka nima wata matar ba fareeda ba oh saboda ita Bata da gata Yar talaka ce sai a had'ata da d'an iska toh in ma kana da wanan tunanin kayi gaggawan cire shi domin fareeda bazata kara Zama da Kamal ba"
Kallon mamaki yayi Mata cike da mamakin b'acin rai da ya gani a kwayar idonta yace"hajiya ba haka bane kema kin San bazan cuce fareeda ba saboda ita talaka bane nidai kawai Ina son had'a zuria da malam Abdallah ne na yaba da hallayensu wallahi da Ina da wani d'an bayan saheeb dana aurame fareeda dan allah ki fahimce ni"
A fusace tace"alhaji ka cire bakin ka a maganar fareeda da saheeb dan girman Allah wallahi in har ya dawo ya nuna ya tab'a saninta balle har yace"Yana sonta toh wallahi ni barrister Rukkaya zanyi shari'a da shi,kotu ne zai rabani dashi in kuma kana son in had'a da kai sai ka sanar min in bar maka gida tun yanzu"tana Gama magana ta ja bargo ta rufe har fuska
Kallonta yayi yace"ikon Allah abin ya Kai ga haka?"
Gyra kwanciya tayi ba tare da ta amsashi ba
Shiga bayi yayi ya fito yayi shirin bacci ya kwanta a gadon ya jawota jikin shi,ture me hannun tayi
Yace"haba hajiya toh miye na fushi aini tuni na janye wallahi ba ruwana Kar in rasa matata saboda shi kowa tashi ta fishe shi "
Juya me baya tayi yace"haba uwargida a gidan al-haji Musa al'amin ayiwa daddy afuwa wallahi na janye,wai dama hajiya kina da fushi haka?"
Shiru tayi shi kadai yayi ta zuba surutu itako zuciyarta tafarfasa takeyi tana jiran dawowan saheeb
Da haka daddy ya shawo kanta har ta fara bashi amsa
Itako fareeda tana shiga d'aki Dr musty ya kirata
D'agawa tayi tana jin muryarshi ta kashe wayar baki d'aya ta kwanta
Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda fareeda yanzu ta fara zuwa makaranta kuma tana koyar mota kallo d'aya zaka Mata ka gan wayyaya mace da aji zuwa yanzu sumanta ya d'an fito kuma tana zuwa ta gaida su mama sai dai har yanzu Basu San halin da ake ciki ba domin ce musu akayi mijinta yaje Karo ilimi a kasar waje
Mummy ko kullum sai dinki takeyiwa fareeda ga kayan lafe da akayi mata ta Bata abinta
B'angaren Saheeb ko
Zuwa yanzu hauka ce ya rage beyi ba domin ko abinci baya iya ci kullum cikin tunani fareeda daurewa kawai yakeyi domin karatun ma na niman gagaransa
Yanzu ma kwance yake Yana latsa waya tunanin gida ya dameshi Amma da ya tuna mummy sai ya ji bashi da kuzari
Lumshe ido yayi ko minti ashirin beyi ba bacci ya fara d'aukan shi sai dai fa ko nisa beyi ba ya fara mafalki
Zaune yake a garden sai gata ta fito sanye da riga da wando jeans da flowers a hanunta
Karasowa tayi ta rungumeshi ta baya ya lumshe ido yace"farheeb ai fushi Nike dake "
Ba tare da tayi magana ba ta hade bakin su ta fara tsoso
Lumshe ido yayi ya bude su ya jawota gabanshi ya kwantar da ita saman ciyawa Yana romancing dinta har zai shige cikin birnin dabsu ta tureshi
Cikin matukar bukatar ta yace"why?"
Tace"no"
Kokarina had'a bakinsu yake ta tureshi ta tashi
Yace"farheeb zo kiji Allah ki zo bazan Miki komai ba "
Wucewarta tayi sanda tayi nisa ta juyo tame murmushi
Firgit ya tashi daga bacci Yana mugun zufa kallon Wando shi yayi ya gan a mike take
Yace"na Shiga uku ni saheeb meyasa zuciyata zata kamu da sha'awar ta,aiko Imani ya gan ni dan wallahi nasan ban isa in koma gida da wanan maganar ba zan Bari in na Gama program dina in koma in nimi gafaran mummy da daddy ko ya Suka d'auki zance?"mikewa yayi kamar Wanda ya tuna wani abu yaje gaban wardrobe ya ciro wani waya
Numbers yake dubawa murmushi yayi yace"Iman let me call her"
Kiranta yakeyi Amma ba a d'aga ba har 4missed calls
Iman dake zaune da fareeda suna Hira,fareeda ta kalleta tace"ba wayar ki bane ki d'aga Mana"
Iman tayi tsaki tace"bansan ko waye ba international number ne"
Fareeda tace"ki d'aga may be is important"
D'agawa tayi tace*"hello"
Shiru tayi jin muryar da batayi zato ba kallon fareeda dake lasawa waya tayi
Shiko jin taki amsa me yace"
Pls comment and vote for me on watpad
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/8, 9:59 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π