An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ο»Ώ[12/30/2019, 3:51 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
DR SAHEEB
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Gaskiya nagode da kaunar ku da adduoin ku gare ni Allah ya bar zumunci haka DR SAHEEB yake da fans tun a page 1 toh ni sai na gan kamar ya shafe duk littafaina na baya domin na gan ruwan comment da sharhi gaskiya naji dadi a cigaba da gashi
Wanan littafin sadaukarwa ce ga KAUNA CE fans group paid
&
Nida mijina fans group paid
&
Mai Mata biyu fans group paid thank you very much for your patronage iam gratefull
_______________
π
Ώ3β£_4β£
Wani irin taurari yake gani da kuma hoton mutane biyu_biyu da ya hanashi tantance ainihin Wanda ya mare shi har zare ido yake kamar a mafarki
Fareeda ce a gaban shi tana huci tace"how dare you?zaka wulakanta tsohon mutane wanan ai Ko ba kai ba ya haifi mahaifinka a matsayin Kaka yake gunka shine dan sabar rashin kunya zaka yi kwallo dashi dan kawai ya roki abinda be fi karfin ka ba"magana take tana nuna shi da yatsa
Karasawa tayi ta d'anga tsohon dake kwance a kasa
Tace"Sannu baba Dan girman ka yi hakuri"
Murmushi yayi yace"babu komai ya'ta duniya ce ta ishe kowa riga da wando Wanda Bata shigo ba ma tana jiranta"
Shidai SAHEEB ko kwakwaran motsi ya kasa yi domin gani yake mafalki yakeyi
Incharge ma mutuwar tsaye yayi domin yafi kowa sanin halin SAHEEB yasan bashi da mutunci tun kan ma yaje turai
Dr Dauda ko rike kumatu yayi kamar shi aka mara jikin shi rawa yake yama rasa daga ina zai fara
Su habiba ko mamaki da tsoro ya mamaye zuciyar su domin abinda suke gani a kwayar idon SAHEEB is not encoraging because idonshi ya kad'an ne yayi ja kamar garwashi ga wani numfashi da yake fitarwa
Itako fareeda ko kallon inda yake Bata karayi ba saima karasawa da tayi ta d'auko gadon d'aukan marasa lafiya tasa aka kwantar da yariyar
Da yike kwarariyar nurse ce midwife tuni ta fara bata taimakon gaggawa a receptionist,ta kalli tsohon tace"baba karka damu zata samu lafiya ka ji zazzabi ne da yawan zafin jikine yasa ta sume but na mata allura yanzu zata farfado"
Yace"nagode"
.tace"karka damu"
Incharge yace"fareeda ki bar asibitin nan tun kafin ranki ya b'ace wallahi wanan shirun da yayi yana nufin you are in trouble'
Tsaki tayi tace"babu inda zani Ina nan"
Dr Dauda ne yace"is like oga is in stage of shock ina ganin kila a rayuwar shi babu Wanda ya tab'a Marin shi baku gani ko motsawa ya kasayi?"
Dr salma tace"you are right"
Fareeda tace"hmmm his in shock ai taimaka me zakuyi ya dawo reality bawai ku tsaya Kuna kallonshi ba"ta kare magana cikin ko a jikinta
Dr dauda yace"wallahi tsoro Nike ji"
Incharge yace"Nima haka"
Kallon Dr salma tayi sai tace"count me out"
Tace"ok then let me help badan halin shi ba"
Ai waje taje wajen wani gindin fanfo bucket ta d'auka Wanda cleaners ke aiki dashi
Cikawa tayi dam da ruwa ta kawo ciki a gabanshi ta tsaya ai sai ta
Pls sai next yearπtalla nayi kuma an hanani sakat by next year yana nufin ko jibi ne Kar a haumin kai,wallahi a gajiye Nike typing dinma wahala yake min but from next year zaku samu posting inda ya kamata
Tanks my fans
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[12/31/2019, 10:02 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
DR SAHEEB
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous, interllingent, and expert writers,we are the best among the rest.
Wanan littafin kagagen labari ne banyi shi dan cin zarafin kowa ba
Note:ban yarda wani ko wata ya canjamin labari ko a min editing ba please a kiyaye
Wanan littafi sadaukarwa ne ga fans dina masu patronizing littatafaina Ina godiya domin tabbas kun nuna min kauna ubangiji ya baku abinda yafi Wanda kuka bani
Note:littafin Free ne
Dedicated to hajiya Aisah Bashir d'anguguwa Ina Mika gaisuwata gare ki
________________
π
Ώ1β£_2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
SAHEEB specialist hospital asibiti ne babba Wanda da ka shiga zaka San ba any how hospital bane domin duk wani na'ura na duba jikin da gane cutar dake tattare a jikin dan adam toh akwai shi a cikin asibitin, environment din yayi ne kuma akwai likitoci masu illimi Wanda suka San aikin su
Wata nurse ce tsaye a receptionist sai kwaliya take ta shafa wanan ta shafa wancan ta dage Kamar her life depend on that make up
Wata kyakyawar budurwace ta fito daga wani ward tsanye da Kayan nurses tsayawa tayi tana kallon colleague dinta
Murmushi tayi tace"habiba wai kwalliyar bata Isa ba haka kin gan inda kika Zama kuwa kamar zombi"
Murmushi habiba tayi tare da kallon fareeda tace"fareeda please nayi kyau Ina son da munyi ido biyu da shi ya nuna Yana sona kawai ya ji sai ni"kallon bangon asibitin nayi sai na gan hoton wani hadeden Gaye a kasa an rubuta Dr SAHEEB
Murmushi fareeda tayi ta tabe baki ta kalli hoton tace"hmmm iska na wahalal da me kayan Kara ke bazaki shafawa kanki lafiya ba ki nimi dai_dai ke,ke kanki kin San Dr SAHEEB yafi karfin ki"
Tsaki habiba tayi tace"please let me try my luck jo,there is no harm in trying "
Fareeda tace"I see,ke baki da tunani mutumin da baki tab'a gani ba sai a hoto be masan kinayi ba what makes you think be da budurwa?"
Habiba tayi tsaki tace"you always speak rubbish "
Fareeda tace"ni fa kin gan ni Nan a rayuwata bana son raini kuma irin maza Kamar Dr SAHEEB da gani yan rainin hankaline "
Kafin habiba tayi magana Aisha ta karaso itama fuskar nan taji foundation ga baki na kyali
Hararan habiba tayi,dariya ma suka bawa farida tace"kema Dr kike so?"
Aisha tace"ai nasan inda nike farar nan ourstory will be love at first site
Dariya fareeda tayi zatayi magana sai ga in charge dinsu ya shigo yace"pls Aisha ki kira sauran staff din ga Dr ya shigo
Dafe kirji habiba tayi
_____________
Wani hadaden motar ne ya sauke shi kafarshi ne ya fara fitowa kafin jikin shi hadaden Gaye ne son kowa kin Wanda ya rasa domin fari ne sol kamar balarabe
Suit ne jikin shi baki yayi bala'in amsarshi
Inchage ne ya karaso da gudu jiki na rawa
Yace"barka da zuwa yallabai"ko kallonshi beyi ba ya dinga tafiya incharge na binshi a baya
Shiga asibinti yayi sai yatsina fuska yake
A ranshi yace"wanan karamin asibitin ne dad ya dinga damuna wai ya gina min asibiti kamar wani abin arziki and duk tarkace"
Karasawa sukayi inda staff ke tsaye matan ko ji suke kamar su rungumeshi shiko ya hade rai
Tabe baki fareeda tayi tace"can ta matse maka idonshi ne ya sauka kanta da Jan flat shoe dake kafarta yace"what in my hopital?"
Zaiyi magana sai ga wani tsoho ya shigo da gudu babu takalmi kallo d'aya zakayiwa tsohon ka gane talakane sosai
Karasawa yayi ya sunguna yace"dan girman Allah ku taimakeni ku ceto rayuwar ya'ta "
Wani wulakatancece kallo SAHEEB yayi me kafin yace"tsoho ka tafi domin bazaka iya biyan hospital bills din ba"
Tsohon ya zube a kasa dai_dai kafarshi yace"d'an na ka taimaka ga tanan"ya Kare magana da kallon d'anshi dake tsaye rike da kanwarshi rai a hanun Allah
SAHEEB yace"ok Amma kafin mu dubata sai ka ajiye dubu hamsin"
D'ari biyar tsohon ya fito dashi yace"gashi d'ana wanan ne gareni ka taimaka"
Ai wani kwallo dashi SAHEEB yayi yace"ni mabaraci ne da zaka bani kudi kamar almaji...."
Maganar makalewa yayi sakamakon wani mahaukaci Mari da ya ji da yayi sanadiyan d'aukewar jinshi da ganin shi na wucin gadi
Toh fans wa yayi wanan Mari???
In na gan comment zan cigaba but in babu sai in huta
Don't 4get Dr SAHEEB is free
Coming soon
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/1, 7:41 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
DR SAHEEB
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_________________
π
Ώ5β£_6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tana kaiwa gabanshi ta kwara me ruwa firgit ya razana jikin shi na rawa har yanzu ya d'au mafalki yakeyi kallonta yayi da jajjayen idonshi sai ta d'aga me gira
Tace" wake up"ta kare magana da me waving
Da k'yar yaja kafarshi da yayi me nauyi ya shige office dinshi Yana shiga ya zauna a kujera Yana wani irin numfashi jikin shi na mugun rawa
Incharge yace"ba lafiya"karasawa yayi ya je gaban kujera ya Kama hanun shi ya jashi zuwa wani d'aki dake cikin office din
D'akine hadade babu abinda babu a ciki
Kwantar dashi incharge yayi inda babu musu ya kwanta
Fita yayi ya d'auko allura yayi me ko minti uku ba ayi ba bacci yayi awon gaba dashi
Ajiyar zuciya ya sauke ya bar d'akin,wajen fareeda yaje direct yace"fareeda please ki bar asibitin Nan karki Kara dawowa na rokeki"
Hannu ta Kai kugu tace"a kanme kenan?"
Yace"fareeda ki tafi please you are fired karki Bari ya fito ya sameki fareeda kin San abinda kika jefa kanki a ciki kuwa,wanan abinda kikayi ina tabbatar Miki har iyayen ki sai ya shafa"
Murmushi tayi cikin ko in kula tace"and who are you to fire me?kasani ba Kai kayi hiring dina ba so you have no right to fire me"
Yace'i know but please a matsayina na incharge din asibitin nace ki bar nan"
Tace"toh ai mahaifin me asibitin yayi hiring dina kuma shi kadai yake da right da zaiyi firing dina ko wancan sakaren be Isa ba"
Yace"fareeda Wanan taurin Kai bazai kaiki ko Ina ba please go wallahi tausayi kike bani"
Agogo ta kalla tace"saura 20minit shift dina ya kare kuma Ina tabbatar ma gobe zan dawo babu abinda zaiyi min da yafi karfin Allah kuma kome ya faru dani toh tun farko Yana cikin kunddin kaddarata ce"ta Kare magana da duba yariyar tsohon da ta farfado ta kalleshi tace"kaka zaku iya tafiya kafin a Kuma wulakanta ku kuyi ta bata magunguna Dana bata inshaallahu zuwa jibi zata warware"
Har kasa ya tsunguna yana godiya ta d'aga shi
D'ari biyar ya bata yace"ya'ta shine gareni"
Tace"baba ka barshi ko nawa ne zasu cire a albashina"
Godiya yayi sosai yace"ya'ta Nima Allah ya kawo rananda zan taimaka Miki"
Tace"karka damu"
D'anshi ya d'auketa Suka wuce
Kallon incharge tayi tace"ni zan tafi sai gobe ku cire kudin ku a albashina
Tana Gama magana ta shige wani d'aki domin canja Kaya
B'angaren Saheeb ko be wani Yi baccin kirki ba kamar a mafarki abubuwan da suka faru suna dawo me
Zabura yayi ya tashi yace"she actually slap my face"Yana magana yana shafa kumatun shi
Kallon jikin shi yayi a jiqe cikin kankanin lokaci komai ya dawo me
Wani ihu yayi Yana rike Kai yace"she slap me in public,ta mareni ni Saheeb Al_amin a nobody slap me my employing
Ai kwallo yayi da center table d'akin shi a lokaci d'aya glass din ya fashe shima jini ya fara fita a kafar shi
Zuwa yayi ya tuge tv ya fasa a kasa komai ya gani fasawa yakeyi kamar mahaukaci
Jin karar fashe fashe yasa incharge da Dr Dauda shiga d'akin da gudu
Wani kallo yake jifan su dashi Wanda yasasu shan jinin jikinsu
Zuwa yayi gaban incharge da jikin shi babu abinda yakeyi sai rawa ji yake kamar ya saki fitsari
Kallon kwayar ido shi yayi da jajjayen idonshi
Yace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/1, 7:41 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
DR SAHEEB
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my paid groups
______________
π
Ώ7β£_8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
_________
Yace"Ina ne gidansu Kuma waye ubanta a gari nan?"
Cikin tsoro incharge yace"wallahi ban Santa ba karka damu nayi firing dinta wanan ma ya isheta"
Wanka me Mari yayi yace"ta Mari ni Dr saheeb and the only thing you do is just to fire her kana hauka ne"
Rike kumatu incharge yayi yace"Yi hakuri sir "
Yace"4hours na baka and in this 4hours Ina son ka kawu min information about her I mean everything about her me takeyi,Ina take zuwa waye iyayen ta samarin ta nawa da dai sauransu ko randa aka haifeta karka Bari"
Dr Dauda yace"yallabai da ka hakura yariyar nan ba kowa bace a Mata afuwa"
D'aga me hannun yayi yace"dama tasan ba kowa bace ita ta d'aga hannu ta mareni toh Ina tabbatar muku yau WALLAHI SAI TA YI NADAMA ABINDA ZAN MATA SAI YAYI SANADIYANTA JINYA"
Yana gama magana ya fita a hanya fita yayi Karo da wata sanye da nikab babu abinda kake gani sai kwayar idonta
Haka kawai yaji mugun fadiwar gaba
Itako ratsashi tayi ta wuce cikin nikab ko matsifa take tace"ka ji shi kamar be gani "
Binta yayi da kallo zuciyar shi na mugun bugawa
A bakin titi ta tare a daidaita ta hau ta wuce unguwan su
Tun a kofar gida take kwalawa mama Kira
Mama ta fito tace ke ko bansan Randa zakiyi hankali ba ke kenan kullum sai an ji muryar ki"
Murmushi tayi ta d'aga nikab din fuskarta ta turo baki tace"toh laifine dan mutum ya Kira maman shi?"
Baba ne ya fito yace"a'ah ba laifi bane ummata"
Murmushi tayi tace"lah baba Ashe ka dawo?"
Yace"eh nadawo Yar gidan baba"
Ajiye Jakarta tayi ta yaye babban hijabinta sai ya rage ta da uniform fari da karamin hijab
Shiga karamin kicin dinsu tayi sai gata ta fito da kulan abinci
Ta zauna kusa da baba tana ci Yana Mata hira
Mama ko shigewa tayi tace"Bari inje in kwanta domin kun fara kenan shiriritar ko Bata karewa Kaima malam sai kayi ta biye Mata
Baba yace"ba dole ba ya'daya tilo
Cigaba sukayi da hiran su har ta gama cin abinci
Tace"baba kasa na makara gashi ko wanka banyi ba"
Yace"toh Yi maza kafin humaira ta shigo"
A gurguje ta shige d'akinta ta tube kayanta tafito d'aure da zani a kirji da karamin hijab
Already baba yasa Mata ruwan wanka
Shigewa bayinsu tayi Wanda ko roofing babu
A gurguje tayi wanka tana fitowa sai ga humaira tayi sallama
Tace"kardai baki shirya ba"
Tace"Yi hakuri yanzu zan shirya wallahi yau ban dawo da wuri ba
Shigewa d'aki tayi ta shirya cikin jallabiya ta saka maroon hijab da nikab ta d'auki al_qurani ta fito
Tace"muje na shirya"
Sallamar iyayenta tayi duk suka sa Mata albarka
Islamiya sukayi direct inda Zama sukayi a aji tare da sauran d'alibai Suka fara karatu
Da misalin karfe shida na yamma Suka fito
Suna tafiya suna Hira,humaira tace"hmmm kedai kina kokari kullum cikin nikab gaskiya bazan iya ba nifa ko hijabin sai zan taho islamiya nike sawa Ina zan iya"
Murmushi fareeda tayi tace"dan dai baki Saba bane kike fadin haka wallahi in kika Saba da nikab ko kudi aka baki aka ce kiyi yawo haka bazakiyi ba
Humaira tace"gaskiya zaiyi wuya in saba"
Fareeda tayi murmushi tace"baki daiso kawai da miye a cikin nikab"
Humaira tace"yauwa fareeda ya maganar auren ku da farouq"
Murmushi fareeda tayi tace"ai manya subn shiga domin mahaifin shi da kawunan shi sun zo har gida niman aure na"
Tace"na tayaki murna domin kin samu Mai sonki"
Tace"kema ai lokacin ki na nan zuwa mu dai muyi ta addu'a Allah ya rabamu da samarin banza ya rabamu da samari irin Adnan na littafin Mai Mata biyu"
Tace"amin,Amma fareeda jiya nayi mafalki wai an fasa bikin ku da farouq kin aure wani balarabe'
Cikin ko in kula fareeda tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/1, 7:02 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
DR SAHEEB
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
______________
Littafaina
1β£EESHA
2β£IKLAS
3β£IMRANFAD
5β£MATAN GIDA
6β£ RAYUWAR NUR
7β£NIDA YAYA SUDAIS
8β£SANADIN GARKUWA
9β£MAZAN KO MATAN
1β£0β£MIYE LAIFINA (free)
1β£1β£NIDA MIJINA (na kudine)
1β£2β£KAUNA CE (na kudine)
1β£3β£SO (free)
1β£4β£MAI MATA BIYU (na kudine)
Now typin
1β£5β£ DR SAHEEB free
Ga Mai bukatar littafina na kudi zai iya yimin magana ta wanan number 09090112846 sanan kowa ya bude asusu yayi ta saka ashirin ashirin domin next novel Dina na daban ne karku Bari d'ari biyu ya hana ku karantawa novel ne me cike da nishadi kardai na cika ku da surutu domin ni kaina Ina sonshi NIDA YAYA HYDAR karki Bari a baku labariπ€£π€£π€£
____________
π
Ώ9β£_1β£0β£
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tace"ai mafalki ba gaskiya bane Allah ya zab'a Mana mafi alkhari"cikinsu babu Wanda ya Kara magana har suka Kai gida
B'angare Saheeb ko gidanshi yaje gidan da ko maigadi babu fitowa yayi ya bude gate ya Shiga
A falon ya zube zazzabi me zafi ya rufe shi da ya rufe ido babu abinda yake gani sai hoton fareeda a lokacin da ta mare shi da lokacin da ta watsa me ruwa wani numfashi yaja tare da razana Kamar Wanda yayi munmunan mafalki
Mikewa yayi ya zauna yace" hmm indai har na cika d'an halak inba wulakanta yariyar nan ba toh bani kadai ba ubana ma shege ne"kawai hawaye na gani Yana bin kuncinshi ya rike kumatu yace"I can't believe it real"
Kwanciya yayi ya lumshe ido Amma ba bacci yake ba tunanin me zai Mata yake"
Be mike ba sanda ya shafe awa hudu kiran mummy ne ma ya tada shi
D'auka yayi tace"lafiyar dai ko daga shigowa Nigeria sai yawu Ina ta jira ko har yanzu baka gama ganin asibitin bane?"
Tsaki yayi yace"mummy yanzu zan dawo"
Aijin tsakin shi yasa ranta yayi mugun b'acewa tace"Kai me yasa baka da hankali ne ni kakewa tsaki? Wallahi Saheeb zan mugun sab'a maka a ce Kai a rayuwar ka baka da tarbiya ka dawo kenan ko? Wallahi zaka ma gyru ne nonesense"
B'ata fuska yayi ya turo baki Amma yasan ko Karen Lolo ya cije shi be isa ya yanke Mata waya ba"
Cikin tsigar bada umurnin tace"Ina son ganin ka nan da minti ashirin kuma in kasan da warin tab'a zaka dawo toh karma ka shigo min gida shashasha sakare Mara hankali"
Kafin yayi magana ta katse Kira
Tsaki yayi yace"wai a ce uwar da ta kawo ka duniya ta ki ka ni na rasa meyasa mummy ta tsane ni kullum sai ta kirkiro wani abinda nayi toh miye a cikin tsaki "
Aljihushi ya saka hannu ya ciro kwalin tab'a har zai kunna kuma sai ya ajiye kamar Wanda ya tuna wani abu ya d'auki makullin mota ya fita
Gida direct ya tafi inda ya tarar da mummy da Iman zaune a falo suna kallo
Iman na ganin shi ta mike taje ta rungumeshi tace"Yaya Sannu da dawowa,ya nagan ka a haka?"
Tsaki yayi yace"Iman it a long story "
Tace"iam interested"
Zaiyi magana mummy tace"saheeb kamar baka ganin bako?"
A ranshi yace"Kai mummy ta samin ido"
Gabanta yaje har kasa ya sunguna ya gaisheta cike da ladabi
Sai d'aga hanci takeyi ko zata ji warin tab'a
Sanin abinda take son ji yasashi cewa"mummy na fad'a Miki na daina"
tace"yaro Kar Allah yasa ka daina in tama illah ai ba kai kadai na haifa ba sakare"
Turo baki yayi domin ya sani mummy tayi tame fad'a balle a gaban kanneshi
Mikewa yayi yace"ni zan Shiga mummy please a rage zagina ko zanyi kiba"
Iman tayi murmushi yace"ke zan b'ata Miki rai fa"
Hararanshi mummy tayi tace"zo Nan"
Babu musu yaje ya zauna kusa da ita sai a sanan na hango kamaninsu
Tace"meke damun ka? Kamar baka da lafiya ko?"
Yace"babu komai mummy"
Tace"karya kenan zaka min"
Yace"mummy ko na fad'a Miki Kara b'ata min rai zakiyi kawai ki barni in ji da guda d'aya"
Tace"umurni ne na baka"
Tsaki yayi domin abin a jinin shi take
Talle me keya tayi sai yayi murmushi yace"wallahi mummy mancewa nikeyi"
Cikin b'acin rai ya fad'a mata komai
Wani guda mummy tayi daya sa kallon kowa ya koma kanta harda abokin shi Mahmud da shigowar shi kenan
Yace"mummy dan an mareni shine kike irin wanan murnan"
Bud'an bakinta sai Suka ji tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/1, 7:02 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to *KAUNA CE* paid group nagode da kaunar ku
_____________
π
Ώ1β£1β£_1β£2β£
______________
BismillahirRahmanir Rahim
Ji sukayi tace"Allah yayi Mata albarka,Allah yasa ta gama da duniya lafiya ubangiji ya Bata miji nagari ya rufa Mata asiri Kai naji dadin wanan al'amari"
Baki sake yake kallonta yace"mummy baki ji me nace bane I said she slap me in public just because kawai nace tsohon ya barmin asibiti,mummy saboda kawai na d'anyi kwallo dashi ya bani d'ari biyar Kamar maroki"
Mummy tace"saheeb Ina raba ka da wulakanta mutane musamman na gaba da kai ba ka ji wallahi ka kiyaye duniya wata Rana zakayi nadama gashi tun ba a Kai ko Ina ba yariyar da bata Kai ko Ina ba ta fara seta ka tunda kaki jin maganar mu toh a waje za a ladabtar da kai shashasha kawai"
Yi yayi kamar zaiyi kuka yace"mummy ban taba sanin kiyayya da kike min ya Kai haka ba I was embarass in public and you are happy about it haba mummy"
Kallonshi tayi cikin takaici tace"nice makiyiyarka?Dan kawai ina fad'a maka gaskiya Kamal ni?"ta nuna kanta da yatsa
Tace"babu komai in baka ji nawa ba kaji na mutane waje"
Yace"wallahi mummy kinji nayi rantsuwa ko itama ba kyaleta zanyi ba sai na d'au fansa Wanda yafi Wanda tamin sai tayi nadama"
Mummy ta kalleshi tace"SAHEEB kalleni"
Kallonta yayi tace"in ni na haifa ka toh ka rabu da yar mutane karka kuskura ka tab'ata Kuma kar na samu labarin ka koreta a aiki"
A ranshi ko yace"ai sai kiyi dama aini ba korarta zanyi ba muna tare har sai na d'au fansa "
Mahmud ne ya durkusa har kasa ya gaidata
Cikin sakin fuska ta amsa ta kalleshi tace"daga yau in zaka shigo gidan Nan kayi ta gyra wandonka ko kuma kuyi ta had'uwa a waje"
Shafa kai yayi yace"Yi hakuri mummy"
Tashi SAHEEB yayi yace'mudex muje part dina"
Haurawa sukayi mummy tace"Kai musu abinci"
Iman ta mike tana turo baki tace"nifa mummy ba kaiwar bane sai na Kai Yaya yayi ta ci zalina"
Mummy tace"Yi hakuri