takardar hannunta tayi saurin fita daga d'akin.
Komawa tayi d'akinta, bedroom tawuce da gudu-gudu kan gado ta zauna tana maida numfashi kusan minti biyar sannan tabud'e takardar.
_"fatan kintashi lafiya, ga kudin cefane nan kiyimin tuwon shinkafa miyar d'anyar kubewa_
Dariya khairat tayi tace "tuwon shinkafa miyar kubewa, hhhhhh sai dai kaci na gidan uwarka Salim amma bana Fauziyya ba"
Sallamar Sani khairat tajiyo, amsawa tayi tareda fitowa daga d'akin.
Gaisheta Sani yayi cikin girmamawa ta amsa, already dama kayan wanke-wanke killace suke farawa kawai zaiyi.
Matsowa khairat tayi tad'an du'ko saitin kunnen Sani tace "akwai labari, sannan Kuma inamaka congrats dan yau Fauziyya zatabar gidannan"
Zare Ido sani yayi cikeda mamaki yace "haba dan Allah"
"Wlh kuwa Kai dai kazuba Ido kaga ikon Allah"......
Jin 'karar tafiya yasa khairat saurin matsawa daga inda Sani yake tana cewa "gaskiya Sani yanzu kadaina wanke kwanoni su fita, Ni narasa miye ke damunka, kusan kullum yanzu idan kayi wanke-wanke idan zanyi amfani da kwano saina Kuma wankewa"
Murmushi Sani yayi ya kalli Fauziyya dake tahowa wurinshi hannuwanta d'auke da wasu plate, yace "aunty Fauzy ai kece shedar yanda nake wanke-wanke na, yoni idan nayi wanke wanke har she'ki zakiga kwanuka nayi saboda tsabar fita dasukayi"
Guntun murmushi Fauziyya tayi batareda tace komiba ta ajiye plates d'in hannunta tabar wurin, dan tasan yanzu tana iya yin magana khairat tagayamata marar dad'i, shiyasa koda yaushe take ri'ke girmanta dan batason raini.
Nan khairat ta zauna tana taya Sani fira harya gama wanke-wanke, kitchen tashiga tahad'a mashi breakfast tea da bread, Zama yayi yagama sha ya wanke cup din ya ajiye.
Bakin 'kofar d'akin Fauziyya ya tsaya yad'an d'aga murya yanda zata jiyoshi yace "Aunty abada kud'in cefane"
Tunda aka kawo khairat gidan Sani baitaba shiga d'akin Fauziyya ba, iyakarshi ya tsaya bakin 'kofa idanma zai 'karbi kud'in cefane kenan, idan Kuma ba wurinta zai karba ba ko kofar d'akin baya zuwa.
Dubawa Fauziyya tafarayi dan tasan Salim ya ajiyemata kamar yanda yasaba, hango takarda tayi kan gado sai dai ba kud'in, d'aukar takardar tayi azuciyarta tace "yaukuma ba kud'in, bari induba Inga miye ya rubuta"
Bud'e takardar tayi tafara karantawa tun kafin ta'karasa karantawa jikinta yafara kyarma tana gamawa tafashe da kuka tana mai-maita kalmar "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"
Tashi tayi jikinta na kyarma, kanta yad'au zafi, zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri, hawaye nacigaba da ambaliya a fuskarta,
Yanzu Ashe dama Salim zai iya d'aukar wannan mummunan matakin akaina, akan laifinda banjiba banganiba, yanzu dama ashe zanga ba'kar rana mai d'auke da mummunan tarihi a rayuwata "Allahuma ajirni fi masibati wa khalibli khairan minha" nayi tawakkali gareka Allah nasan kowane mutum Yanada irin tashi 'kaddarar na yarda ni wannan itace tawa, Allah kabani ikon cinye wannan jarabawa dakayimin, Allah sa hakan yazama Alkhairi arayuwata"
Daya daga cikin trolley dinta ta d'auko tafara had'a kayanta da duk abunda tasan zata bu'kata, irin 'kananun kayan bu'kata tazuba cikin hand bag d'inta ta rataya sannan ta d'auko hijab d'inta tasaka tajawo trolley d'inta tafito tasa key tarufe d'akin tana share hawaye tasaka key d'in a bag d'inta.
Sani da khairat dake tsaye Sani Yana jiran abashi kud'in cefane, khairat Kuma tana jiran ganin abunda zaifaru sai ganin Fauziyya sukayi Jaye da trolley tabi hanyar barin gidan.
Saurin Shan gabanta sukayi har suna had'a baki "lafiya Fauziyya meya faru"
Shiru Fauziyya tayimasu da kamar kada tafad'a saikuma taga idanma bata fad'aba dole su sani domin Hausawa nacewa idan andafa boye ba'aci boye.
Handbag d'inta tabud'e ta fiddo takarda tami'kama khairat, amsa tayi tana tambayar "na miye wannan"?
Goge hawaye Fauziyya tayi tace "kiduba mana Zaki gani"
Bud'e takardar khairat tayi tana gama karantawa taja wani dogon salati, "shiko Salim meya kaishi yanke wannan mummunan hukunci"
amsar takardar Sani yayi yaduba "ya subhanallah" yafad'a tareda dafe kanshi da hannu biyu
"Amma Ina hankalin oga Salim yatafi haka, me yayi zafi Shiba wutaba"
Dafa kafadar Fauziyya khairat tayi tace "yanzu Ina zakije"
"Ina zanje Wanda yawuce gidan iyayena ai banida inda yafi can"
"Hakane bakida inda yafi gidan iyayenki, amma dazakibi shawarata kije gidansu Salim kigayama Mama, maybe tasa yajanye wannan matakin daya d'auka"
Kallo Fauziyya tabita dashi batare datace komiba, amsar takardar tayi daga Hannun khairat ta linke ta maida jikka taja trolley dinta tabar gidan.
Tana fita cikin sa'a tasamu napep tasauke wata mata Nan kusa dasu tashige tagayamashi inda zai kaita, mintuna ishirin da wani abu sun kaita gidansu, bayan ta sallami mai napep tashiga gidan, ko sallama batayiba tana shiga ta saki trolley din tsakar gida ta dur'kusa anan tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Da sauri mamarta ta fito daga d'akin jin kukanta tsakar gida dan bataji lokacinda tashigo gidanba.
"Ke Fauziyya lafiya meya faru" kasa magana tayi sai kuka kawai takeyi kamar zata si'ke.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un" mama tafad'a "yau Naga ikon Allah tashi mushiga ciki" kamata tayi suka shiga ciki sannan tadawo ta d'auki trolley d'in.
"Fauziyya kigayamin abunda ke damunki, kintsaya kinata kuka wannan kukan bayada amfani agareki"
Takarda tami'kamata tanacigaba da share hawaye.
Amsar takardar Mama tayi ajikinta na kyarma takaranta, tana gamawa ta rafka dogon salati, "garin ya haka yafaru nashiga ukku"
Tashi tayi ta d'auko wayarta number baban Fauziyya takira bugu d'aya yad'aga "sallama tayimashi Yana amsawa tace "Alhaji kazo gida yanzu ba lafiya.
Babn Fauziyya Wanda ko minti goma baiyi da barin gidanba, yadawo hankali tashe.
Khairat da Sani kuwa Fauziyya nabarin gidan suka fashe da dariya suka tafa, Sani yace "gaskiya khairat ke shu'uma ce ko alahira wutarki dabance"
Hararshi khairat tayi tace "idan 6era nada sata daddawa ma da wari, kin wutar Kai kana 'kasana"
"Mubar wannan maganar dai yanzu nidake duk biyan bukatarmuce, Wai ya abun yafaru"
Saitin kunnenshi khairat takai bakinta ta rad'amashi, dariya sukayi suduka.
Sani yace "amma baki tunanin za'a iya agane ba rubutun Salim bane"
"Bani wannan tunanin haka, dan wanda yayi rubutun ya kware a wannan harkar, dan wlh ko sign d'in mutum yakalla yayi irinsa anyi kad'an ace ba maishi yayishiba"
*To waini miye khairat tarubuta jikin wannan takardar, kudai kubiyoni dan jin yanda zan war-ware maku zare da abawa*
*Kuyi manage da wannan, maybe gobe bazakujiniba saboda inada wata 'yar hidima, amma idan Naga da Hali zanyimaku koyaya yasamu*
Mmn khady ce 😩
Mmn khady ce 👎🏻
Mmn khady ce 🙏🏻
🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 33
Baban Fauziyya hankali tashe yashigo gidan, dan dagajin kiran da akayimashi yasan bana lafiya bane.
Ganin Fauziyya dayayi ga idanunta sun kumbura sunyi suntum, bayan canja launi dasukayi zuwa ja, gabanshi yafad'i yasan ba lafiya.
Karasowa yayi inda suke yace "lpy mike faruwa haka?"
"Inafa Lpy Alhj, kaduba kaga yaronnan saida yasaki Fauziyya baccin duk irin zaman hakurin datake a gidanshi" tafad'a tana mi'kmashi takardar, karba yayi yaduba "gurgiza Kai yayi Zuciyarshi cike da takaici yace "Allah sa haka shine yafi zama Alkhairi" dukda hakan baimashi dad'iba ko kad'an.
"Ameen" maman Fauziyya ta amsa sannan tace "Amma Alhj inada wata shawara, tunda dai haka yariga ya kasance Kuma kaga duk halinda yarinyar nan take a gidanta Babu Wanda bamu saniba, tundaga tsangwamar da mahaifiyar yaronnan kemata har zuwa 'karin auren dayayi, mai zai hana tad'anyi nesa da garinnan Kota samu tahuta.
Shiru baban Fauziyya yayi sannan yace "Ina kike ganin zata tafi?"
Mai zai hana tatafi Abuja gidan 'yar'uwarta kafin muga abunda hali zaiyi"
"To shikenan saiku kirata kuyimata bayani kafin tatafi ko"
Bayan fitar baban Fauziyya, mama takira Aunty safiya yayar Fauziyya wacce ke aure Abuja tagayamata abunda ke faruwa da 'yar'uwarta a gurguje tace yanzu zata taho nan, idan tazo zakiji sauran bayani daga wurinta.
"To saitazo, da haka sukayi sallama, kallonta mama tayi tace maza tashi kid'au hanya baniso ki Kara awa daya a cikin garinnan.
Tashi Fauziyya tayi jiki a sanyaye ko kad'an bataso tayi nesa da Salim, Amma bazata iya tsallake maganar iyayentaba, Kuma tunda shi Salim din bai San darajartaba har ya iya rabuwa da ita dole itama zata daure tarabu dashi komin irin tsananin sonda takemashi.
Tana kuka tafita gidan, napep ta tsaida yakaita tasha, cikin sa'a kuwa ta tarar saura mutum d'aya golf din tacika, tana shiga suka d'au hanya sai birnin tarayya (Abuja).
Bangaren Salim kuwa tunda yaje wurin aiki haka kawai Yana zaune sai yaji gabanshi na fad'uwa.
Salati kawai yakeyi duk lokacinda yaji faduwar gaban, ranar haka ya wuni sukuku baiyi wani aikiba har lokacin tashi yayi, haka ya tattara iyayen takardun dake gabanshi yabar office d'in.
Tafiya yake kan mashin dinsa, tunda yadoso gidan yakejin fad'uwar gabanshi na tsananta yarasa dalilin.
Ahaka ya isa gidan da sallama yashiga, khairat na zaune kan kujera ta ca6a wata irin kwalliya kamar mai Shirin zuwa biki, tasaka wata matsiyaciyar doguwar riga ta wani tsadadden less takashe d'aurin d'ankwali kamar mai Shirin zuwa gasar zaben sarauniyar kyau
hankalinta kwance
Tanajin sallamar Salim ko kallon inda yake batayiba barantana ta amsa sallamar, saima cigaba datayi da taunar cingum dinta tana wani 'kas 'kas dashi abaki.
Wani mugun kallo Salim ya watsamata sannan yawuce d'akinshi, baima lura da d'akin Fauziyya dake rufeba.
Saida yasheka wanka ya canja kaya, kusan minti goma Yana jiran shigowar Fauziyya yaji shiru.
Wayarshi ya d'auko yaruba Text massage yaturama, shiru kusan minti ishirin da tura massage din amma baiga tazoba.
Tunani yafara a zuciyarshi kodai Fauziyya tagaji da yanda yake shareta itama tayi wuri ta ajiyeshi, idanko hakane baiji dad'iba dole yau su sasanta kansu ya nunamata kome yawuce Amma yajamata kunne akan kada takuma yarda ta aikata makamacin laifinda ta aikata.
Kara d'auko wayarshi yayi yaduba massage din yaga tabbass yashiga amma ya'akayi bata amsa kiranshiba.
Dialing d'in number ta yayi, tadad'e shiru kafin agayamashi inda take ba service, Kara Kira yayi hakan dai suka 'kara mai-maita mashi, kusan sau hud'u Yana Kira amma duk amsar d'ayace cewa inda take ba service.
Tashi yayi yanufi d'akinta, turus yaja yatsaya ganin d'akin rufe, daurewa yayi ya ida isa yakama handle d'in 'kofar ya murd'a nan ya tabbatar da da key aka rufe 'kofar.
Juyowa yayi ya kalli khairat wacce har yanzu tananan zaune inda take tunda yashigo tanata taunar cingum dinta kamar wata tsohuwar karuwa yace "ke Ina Fauziyya tatafi"?
Wani irin kallon ukku saura khairat tayimashi tajuya tacigaba da cin cingum dinta 'kas 'kas 'karas.
Wata irin Zuciya ta 'kuleshi yace "ke ba tambayarki nikeba"? Cikin d'aga murya yake mata maganar kamar zai rufeta da duka.
Juyowa tayi ta kalleshi she'ke'ke tace "kada ka tambayi kaza Hanyar rafi ka tambayi agwagwa kasha labari"
A kufule Salim yanufi inda take da niyyar cin ubanta, dagudu taranta ana kare tashige d'aki tarufe, tana maida numfashi tale'ko ta window taga yanda Salim yake cika Yana batsewa idanunshi sun canja launi zuwa ja, ranshi amatu'kar bace.
Ta tsorata da ganinshi haka, azuciyarta tace mugu ainagama Zama ka dokeni, kamar kasamu jakka.
Daga cikin d'aki tad'aga murya yanda zai jiyota tace "bani nakashe zomon ba rataya aka bani, Kuma dazaka tambayeni Fauziyya ajiyarta kabani dahar kake Shirin buguna, kaje can kanemi matarka"
Cikin 6acin rai yakoma d'akinshi ya zauna yadafe kanshi da hannu biyu yafara tunanin Ina Fauziyya tatafi batareda izininshiba, abunda bata tabayiba iya tsawon zaman dasukayi da ita, gashi yakira number ta anacewa inda take ba service.
Wayar ya d'auko yasake Kira, yanzu Kuma switch off akacemashi. "Oh my God" yafad'a tareda dafe kanshi, Ina tashiga haka?
Wata zuciyar tace "akan me zandamu dan banga Fauziyya ba, ai ita ba 'karamar yarinya bace, duk inda taje zatadawo ta iskeni.
Fita yayi yahau mashin dinsa yabar gidan.
Yana fita Sani yashigo yanata kwad'a sallama, bud'e d'aki khairat tayi tafito tana 'yan waige-waige.
Kallonta sani yayi cikin mamaki yace "yanaga kinata waige-waige kamar wata marar gaskiya"
Kai dole inyi waige-waige Dan yau kad'an yarage inkumashan duka wurin Salim danyazo yatarar matarshi batanan kamar nice na koreta, yatambayeni nace ajiyarta yabani"
"Yo waye yakoreta idanba keba" dariya tayi tace "au ashefa hakane kaga nifa harna manta"
"Dole kike mantawa tunda kingama da wannan babin, Kinga yanzu hankalinmu kwance ciki yazama na Salim Fauziyya Kuma tazama ta Sani" dariya sukayi suduka sannan yace "kawomin abinci yunwa nakeji"
"To acici" tafad'a tana nufar kitchen, fitowa tayi da plate sha'ke da abinci sai ruwa pure water mai sanyi guda biyu kan plate ta ajiye gabanshi.
Haka yafara kwasar girki suna fira hankalulinsu kwance dan yanzu basuda sauran matsala.
*Birnin tarayya (Abuja)*
Misalin karfe hud'u da minti hamsin da shidda motar su Fauziyya tasauka garin Abuja, tun amota kanta ke masifar ciwo ga wani irin tashin Zuciya datakeji, tana sauka daga mota takira Aunty safiya tagayamata motarsu ta sauka, cewa tayi tajira ga driver Nan zaizo ya d'aukota.
Minti Sha biyar tana jira kafin driver d'in yazo, wata had'addiyar mota 'kirar 4matic black colour tayi parking gabanta, driver yabud'e yafito yanamata sannu dazuwa, amsawa tayi duk ta makure jikinta cikin hijab sakamakon wani mugun sanyi datakeji.
Daukar trolley d'in yayi yasaka a but sannan yabudemata bayan motar tashiga yamaida yarufe, sannan shima yashiga mazaunin driver suka d'au hanya.
Suna Isa gidan yaran aunty Safiya su ukku Ahmed da Walid sai karamar su walida, suka fito da gudu suna "oyoyo ga aunty Fauziyya" da kyar ta 'ka'karo murmushi tayimasu tana rungumesu jikinta d'aya bayan d'aya.
Walida uwar surutu da shegen wayo tace "Aunty jikinki da zafi bakida lafiya ne?"
"Shuru Fauziyya tayimata suka nufi 'kofar dazata sadaka da cikin falon.
Lokacin har maigadin yashigar mata da trolley dinta.
Tana shiga Aunty safiya tarugo tanamata oyoyo, Nan suka rungume juna d'an'uwa yaga d'an'uwa, jin jikinta da zafi rau yasa Aunty Safiya saurin rabata da jikinta tace "dama bakida lafiya Kika taho"
Girgiza Kai Fauziyya tayi tace "lpy lao nataho ahanya zazzabi yarufeni, inaga harda gajiyar zaman mota"
"Eyyah sannu muje ciki kihuta kafin baban Walid yadawo sai mukaiki hospital zuwa dare"
Kama hannunta tayi takaita d'akinda akayimata masauki, d'akine had'adde babu abunda Babu cikinsa na more rayuwa, sai sanyin AC daya gauraye d'akin da 'kamshin feshner.
Kashemata Ac din Aunty safiya tayi dan taga tanata rawar d'ari.
Kitchen tanufa tahad'a mata ruwan tea da milk da Milo takawomata, dakyar tasha rabin cup sannan Tasha paracetamol takwanta kan gado taja bargo.
Fidda su walida tayi dasuketa wasa suna hayaniyar muranar ganin Fauziyya tace "muje aba Aunty wuri tahuta kunga batada lpy"
Fita sukayi sukajamata d'akin, bacci ya kwasheta itace bata farkaba sai bayan magrib, jikinta zufa sharkaf Alamar saukar zazzabin, toilet tashiga tawatsa ruwa ta d'auro Alwala tazo ta kabbara sallolinda suka risketa kan hanya, sannan tayi ta magrib, tananan zaune kan prayer mat har akayi sallar isha'i tayi sannan tafita falo.
Zazzaune ta iske kan dining suna dinner, kujera taja ta zauna dan dama yunwa takeji, amma sai dai takasa cin abincin sosai, Aunty Safiya tana kula da duk yanda take tana tausayamata tasan zafin rabuwa da masoyi, gaskiya Salim bai kyautama autarsuba tunda yasakata wannan halin.
Kallonta tayi tace "zamuje asibitin ko?"
"A'a aunty naji sauki sosai inaga basai munjeba, dama harda gajiyar mota Kinga yanzu dana huta ya sauka"
"To Allah sauwake"
"Ameen" Fauziyya tafad'a.
Mmn khady ce 🙏🏻
🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 34
*Kunata cigiyata inaji abaya nagayamaku munada matsalar NEPA saina Kai charge nabiya kudi kafin inyi typing, to jiya mai charge din nawa bayanan shiyasa kuka jini shiru, nagode da yanda kuka damu da rashin jina dakukayi masoyana, kunata jajena musamman Yan group Dina ZEE MMN KHADY FAN'S nagode Allah bar zumunci*
Bangaren Salim tunda yafita daga gidan bai 'kara waiwayarsaba saida dare, abunda yabashi mamaki shine har yanzu Fauziyya Bata dawoba, hankalinshi ne yatashi sosai.
'dakinshi yawuce ya zauna Yana tunani kala-kala, "Ina Fauziyya tatafine haka, agogon wayarshi yaduba 'karfe tara da minti talatin da takwas, gabanshine yafad'i, ranshi yafara bashi duk inda Fauziyya take babu lafiya.
To yanzu waye zai tunkara yace Yana nemanta, ga kuma wata irin fitinanniyar yunwa dayakeji rabonshi da abinci tun na safe, gashi bayaso ya tunkari khairat tunda yaga take-takenta na rashin kunya, da rashin tarbiyya.
Mukullan d'akin Fauziyya yad'auko yanufi d'akin yabud'e kitchen yashiga yahad'a ruwan zafi yasha tea dan shikad'aine abunda zai iya had'awa Wanda zeyi saurin korar yunwar dake addabarsa.
Saida yagama yafito zaibar d'akin saikuma yaji Yana mararin Zama cikin d'akin, 'kakmshin dake tashi cikin d'akin yayimashi matukar dad'i.
Zuciyarshi tabashi shawarar kawai yajira anan yaga lokacinda Fauziyya zata shigo, Kuma yau saita gayamashi inda tafita takai wannan daren batareda saninshiba.
Kishingid'awa yayi kan kujera 3 seater ya fiddo wayarshi yakira number Fauziyya Amma switch off, cike da takaici ya jefar da wayar kan kujera, tsakanin lokacinda yadawo gida darana yatarar da Fauziyya batanan zuwa yanzu yakirata yakai sau talatin Amma duk amsa d'aya akebashi shine wayarta akashe yake.
Yana nan har 'karfe Sha d'aya da minti 40 yafara gyan-gyadi bacci na neman kwashe shi, tashi yayi yabud'e bedroom dinta yashiga, gabanshi ne yafad'i ganin d'akin hargitse ga Babu trolley guda cikin jerin akwatunan Fauziyyar, sannan ga Kaya duk an fiddo daga wadrope da alama an d'ebi wasu kaya, hankalinshi ne yatashi yashiga tunani kala-kala, zuciyarshi kawai tabashi yaje gidansu Fauziyya yaga ko tana can.
"Ba shakka tana can, may be, gajiya tayi da abunda nakemata tayi tafiyarta, aiko yazama wajibi agareni inje in rarrashi matata tadawo mu manta da duk wani sabani damuka samu mu zauna mucigaba da baiwa junanmu kulawa.
Tashi yayi yakoma d'akinshi yacanja Kaya, sannan yafito yahau mashin d'inshi yanufi gidansu Fauziyya baiko kula da yanda dare ya tsalaba, unguwar duk tayi tsit bakajin motsin kome sai kukan karnuka da beraye da gyare saboda su lokacinsu ne.
Yana Isa 'kofar gidan yayi tsaye kan mashin d'in bai saukaba dan yama rasa ta Ina zai bulloma al'amarin, yakai kimanin minti biyar sannan yayi tamaza yasauka a mashin d'in yafara kwan-kwasa kyauren gidan.
Maman Fauziyya ce tafara jiyo bugun kofar, tada mai gidan tayi tace "Alhaji tashi kaji jinayi kamar ana buga 'kofa"
Saurarawa sukayi suduka, tabbass nan ake bugawa tashi baban Fauziyya yayi yasaka jallabiya yazura silifas yafito, itama maman Fauziyya hijab tasaka saman doguwar rigar baccinta tabiyo bayan maigidan nata dan Jin lafiya.
Tsayawa baban Fauziyya yayi daga zaure yace "waye" saida gaban Salim yafad'i kafin ya amsa da "nine"
"Kaine wah?" Baban Fauziyya yakuma tambaya
"Salim ne"
Bud'e 'kofar baban Fauziyya yayi dan ya d'auki murya.
Durkusawa Salim yayi ya gaidashi, ya amsa a dakile, sannan yace "lafiya naga kazo cikin wannan talatainin dare haka?"
"Eh to, da sauki dai baba, dama zuwa nayi inji ko Fauziyya tazo nan?"
Shiru baban Fauziyya yayi jin tamabayar rainin hankalinda Salim kemashi, tunda in banda rainin hankali yaushe zaka rubuta takardar saki kaba yarinya Kuma kazo gidansu kari'ka tambayar Wai tananan" to idan batanan gidan waye zata.
Mamar Fauziyya dake bayan maigidan nata jin yayi shiru baiba Salim amsaba yasa tace "Kai Salim amma bakada kunya wlh" arazane yakalli inda Mama take danshi baimasan tana wurinba saida tayi magana.
"In banda tsabar rashin ta ido yaushe zaka koro Mana yarinya harda shedar takardar saki sannan kadawo kace Wai tazo Nan, to batazoba batanan Kuma bamusan inda takeba" tana gama fad'in haka tamaida kyaure tarufe taja Hannun mijinta suka koma ciki tanata sababi, "idan Banda yaronnan ya raina mutane yaushe zaizo neman Fauziyya bayan yasan mugun abunda ya aikata"
"Saki......saki....kalmar da Salim keta mai-maitawa kenan, "ni Salim nine na saki Fauziyya, Kai baya yiyuwa yaushe nasaketa bansaniba"
Tsayawa yayi Nan yanata tunani, shidai iya zamanshi da Fauziyya baitaba tunanin yasaketaba barantana Kuma harma ace ya saketa, Kai akwai dai abunda ke faruwa amma banda saki'
Yakusa awa biyu tsaye Yana sa'ka da war-wara, ganin tsayuwar batayimashi yasa yahau mashin dinsa yakara gaba.
Duk abunnan da Salim keyi khairat naji Kuma tana ganinshi dan falo ta zauna tana le'kensa ta window, tunda yafita gidan taketa tunanin Ina zaije saida taga dawowarsa batareda Fauziyya ba sannan hankalinta ya kwanta.
*(Niko nace khairat kenan ai duk yaron daya hana uwarshi bacci shima baya rumtsa ba)*
Tunda gashi Salim baiyi bacciba saboda neman inda matarshi take, kema gashi bacci ya gagareki saboda tsabar tsoro da fargabar kada asirinki ya tonu.
6angaren Fauziyya Kuma itama tunda ta kwanta da dare take juyi kewar Salim ta addabeta, ga wata irin sabuwar soyayyarshi dake 'kara Kama zuciyarta, tun tana kwance harta tashi zaune hawaye yafara ambaliya a fuskarta "Salim meyasa ka yankemani wannan hukunci, wannan hukuncin yayimin tsauri, na yarda ka hukuntani kota wane hanya Amma kada ka yanke alakar aurena dakai"
Kuka take sosai, tanason Jin wane hali Salim yake ciki, tasan duk yanda akayi shima Yana cikin irin halinda take ciki koma nashi yafi nata, dukda dai koma miye shine yajawomasu.
Jikkarta tafara dubawa tana neman wayarta danta Kira Salim d'in bata ganiba, sai lokacin ta tuna da ashefa tunda tazo Aunty Safiya ta karbe wayar daga hannunta, dan dama gudun irin haka.
Aranar dai Babu Wanda bacci 6arawo yayi gigin sacewa tsakanin Salim da Fauziyya dakuma Mai gayya Mai aiki khairat.
Washe gari'karfe bakwai nasafe Salim yabar gidan.
Gidansu Fauziyya yayima tsinke, sallama yasa akayimashi da Baban Fauziyya, Yana fitowa Salim ya durkusa har 'kasa ya gaidashi, amsawa yayi bayabo ba fallasa,
Shiru sukayi nad'an wani lokaci kafin Salim yafara magana "Baba dama zuwa nayi kan maganar danaji mama tafad'a jiya na cewa nasaki Fauziyya, wlh tlh baba bansaketaba, Kuma banida masaniya akan sakinda tazo tacemaku nayimata,
Kuma baba wace shaida Fauziyya tanunamaku tacewa nasaketa nidai nasan dabakina ban furta kalmar saki gareta ba"
"To kamar dai yanda kasani saki ba abun wasa bane, saki dai kariga kasaki Fauziyya, sheda Kuma dakake magana abunefa Wanda kayi arubuce, idankuma kanada ja bari kagani"
Shiga yayi cikin gida, badad'ewa yafito yami'kama Salim takarda yace "wannan itace shedar saki dakiyima Fauziyya"
Amsar takardar Salim yayi jikinshi na kyarma yabud'e yafara karantawa "_Ni Salim nasaki matata Fauziyya saki d'aya sakamakon kamata danayi da laifin Shan maganin zubarda ciki datakeyi dakuma na hana d'aukar ciki idan tasamu miji tayi aure dan banida ra'ayin sake zama da ita_"
Abunda aka rubuta a takardar kenan daga 'kasa Kuma ga sign d'inshi.
Abunfa yagama d'arema Salim Kai, tabbass wannan rubutunshine babu ko tantama, Amma Kuma baisan lokacinda yayi rubutun ba.
Kuma iya saninshi Babu Wanda yagayama matsalar dake tsakaninshi da Fauziyyar barantana yace wanine yayimashi wannan rubutun.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, yacigaba da mai-maitawa, kallon baban Fauziyya yayi Wanda yazubamashi Ido Yana jiran abunda zaifada yace "wlh baba banibane, bansaki Fauziyya ba, akwai dai yanda akayi"
"Wane yanda akayi, ai babu yanda za'ayi wani yasakarmaka mata, koma miye dai aikaga sheda saboda haka kabacemin dagani kana batamin lokaci yafad'a tareda amsar takardar yana shirin shigewa gida.
Saurin Shan gabanshi Salim yayi ya durkusa yace "dan Allah Baba kayimin alfarma d'aya inyi magana da Fauziyya"
Murmushin takaici baban Fauziyya yayi yace "ai Salim Fauziyya tayi nisa da garinnan tun ranarda kasaketa bata kwana cikin jihar nan ba"
Yana gama fad'i yashige gida.
Dafe Kai Salim yayi yace ya "ya Salam, Wai miye ke Shirin faruwa dani, kodai aljanune keson wasa da kwalwata da tunanina dakuma hankalina.....
Hawan mashin dinsa yayi Bai zame ko'inaba sai gidan mamarshi.
Fauziyya Kuma tunda tatashi Aunty Safiya talura da yanda idanunta suka kumbura koba tambaya tasan jiya kuka tasha, saida suka gama break baban Walid yatafi wirin aiki yara Kuma duk suntafi makaranta Aunty Safiya ta zaunarda Fauziyya tafarayimata nasiha "Kinga Fauziyya kiyi ha'kuri da 'kaddarar data sameki, kisama ranki dangana kinsan kowane musulmi akwai nashi kalar kaddarar toke wannan itace 'kaddararki, Kuma imanin mutum baya cika sai yayi Imani da kaddara Mai kyau da marar kyau, Kinga wannan Salim d'in dakikabi Kika damu akanshi kilama ya manta dake yanacan Yana rayuwa da amaryar shi, abunda zakiyi yanzu kema kiyi addu'a Allah zabamaki miji nagari"
Shiru Fauziyya tayi nasihar Aunty Safiya tasa jikinta yayi sanyi, Kuma saitaji tafara ha'kura da Salim din.
"To miye abun damuwa anan, zakazo katasani gaba kana bani labari, ai godiya yakamata kayima Allah daya rabaka da 'karfen 'kafa, miye dama amfanin Zama da matarda bata Haihuwa juya, ai kamanta da al'amarinta kawai. karungumi khairat kucigaba da zamanku dama tun farko itace matarda tadace dakai ba wannan kod'addiyar ba"
Shiru Salim yayi Jin irin maganganun da mama ke fad'i, shiko yanzu Ina zaisa kanshi abubuwa sunbi duk sun jagulemashi, gashi Fauziyya tayi nesa dashi gashi baya samun wayarta, da duk matsalar tazo da sauki yasan idan yayimata bayani ba abunda zai hana ta fahimceshi, saboda Fauziyya macece mai hakuri da hangen nesa, dakuma saurin yafiya ga Wanda ya aikatamata laifi, haka yatashi yabar gidan jikinshi a sanyaye mamarshi Kuma addu'a tarikayi mashi "Allah sa haka shine mafi Alkhairi"
*Bayan wata biyu*
Yau Fauziyya tatashi da wani irin zazzabi Mai zafi, mijin Aunty Safiya ne yamatsa akan sai sunje asibiti,
Shiryawa sukayi dakanshi yakaisu wani asibitin kud'i dakenan kusa dasu,
Yan tambayoyi ta amsa daga wurin likita, tareda yimashi bayanin yanda takejin jikinta, jininta aka diba zuwa lab, gwajin farko aka tabbatar da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13