Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sady tayi tace "Fauziyya dama har yanzu akwai *ALMAJIRI GIDANKI*? murmushi Fauziyya tayi tace "Wai Sani, dama sani ai yananan, yaufa Salim saboda ya kuntatamin har korarshi yayi" Sadiya tace "shine Kuma yadawo saboda tsabar rashin Zuciya" Fauziyya tace "nice nace yadawo saboda idan yatafi waye zaiyimani aikin dayakemin, maganar yo cefane, ko nice zanrika fita dakaina Ina siyowa" "Hmm kawata kidaiyi tunani mai kyau, wlh zama da Almajiri ba karamin hadari bane Koda kuwa yarone, barantana Kuma wannan kasurgumin 'katon, yazo yayimaka zaune cikin gida, wlh akwai matsala" "Bawata matsala kawata, sani bayada matsala ko kad'an" Fauziyya tafad'a tana murmushi. _niko nace sani kau shikeda manyan matsaloli, bama matsala dayaba_ 😡 Da haka sukayi sallama Sadiya tatafi, Fauziyya takoma ciki, Tunda tagayama Sadiya matsalarta yau saitaji kamar an saukemata wasu manyan Kaya data dade tana dakonsu akanta, saitaji duk wani 'kunci da damuwa dake cikin zuciyarta yaragu da kaso sittin bisa dari. Mmn khady ce 👌🏻 [8/24, 9:29 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰 *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇🏻 *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 page 14 Bayan kwana biyu, Fauziyya tasamu saukin damuwar data sanya aranta, tunda sady tabata shwara, dan harta dan fara murmujewa, bakaramin jin dadin haka Sani yayi ba, dan ko kad'an bayaso abinda zai taba ran Fauziyya. Yauma kamar kullum Sani ne zaune kan kujera wacce ake Kira tayani gulma, Fauziyya na nesa dashi suna fuskantar juna, fira sukeyi cikin jin dadi, Babu abunda yadamesu, kwata-kwata Fauziyya tamanta da zancen Salim yakori sani daga gidan itace ta maidoshi, ko d'ar bataji a zuciyarta dangane da abunda tayi. Ada Sanin shima yanadan jin tsoro, Amma yanzu ya sake baya tunanin kome, aishi bayada matsala tunda matar gidance tanemi yadawo bashine yamaido kanshiba. Fad'owa tayi tsakar gidan bako sallama kamar wadda aka jeho, zumbur Fauziyya da sani suka mi'ke tsaye afirgice kamar wadanda aka Kama suna aikata wani mummunan laifi. Jiki na bari Fauziyya tadurkusa gabanta "Sannu da zuwa mama, Ina wuni.... "Daban wuniba kinganni, nace daban wuniba kin ganni, sakarai shashasha, wacce batasan annabi ya faku ba, zuwa nayi inji yaya, kinsake samun wani cikin kokouwa har yanzu babu wani labari" Shiru Fauziyya tayi kanta sadde, hawaye na diga daga idanunta, Sani Kuma dake tsaye gefe guda kurama Fauziyya Ido yayi Yana jiran amsar dazata bada dan shima Yana matukar bukatar jin amsar dazata bada. Girgiza Kai tayi tace "kiyi hakuri Mama, komi lokacine, idan Allah yakawo lokacin sai kome yazama tarihi.... "Tariho, nace tariho, ni zaki gayama lokaci, ai lokacin yadad'e dayi, tun yaushema ya wuce, kinriga kinyi watsi da damarki, kinsamu ciki, kinje kinsa likita ya markadeshi yabi rariya, yaushe Kuma zakisa ran samun wani, Allah aiba abokin wasankibane dazaya baki kyautarda bamai iya bada irinta saishi Kuma kisa kafa ki Shure." Wani irin kallo sani yayima Mama, jiyake kamar yarufeta da bugu, a rayuwarshi daka batama Fauziyya rai 'kara kakamashi kayimashi mahaukacin bugu. Cigaba da ruwan bala'i mama tayi, "to zuwa nayi in gayamaki d'ana yasamu cigaba, Kuma yakara samun budi wlh dole ki sakarmashi mara yayi fitsari, Yana dawowa zai sallameki kisan inda dare yayimaki, sabon aure zai sake budurwa zai aura danya sharaf, wacce tasan arziki Yar gidan mutunci ba irinkiba mai yima arziki kulli" Kuka Fauziyya keyi tana ba mamar Salim hakuri, Hannu tasa ta hankadeta tafad'i zaune tace "tafi can sha_sha_sha Munafika kawai..... Haba Babaa, idan anayin Abu ari'ka Sara ana dubar bakin gatari, iya biyayya Aunty nayimaki, amma baki gani, bakyau cin mutunci..... "Kai dakata, kai-kuma uban waye Kai, miye matsayinka a gidannan Wanda yawuce *ALMAJIRIN GIDAN* to katsaya iya matsayinka idan Kuma kanemi ka wuce wlh zakaci kwal ubanka, shege mai idanu kamar na mujiya" tana gama cin uban sani tafita daga gidan tana gyara zaman mayafinta Wanda yake sauka saboda tsabar bala'i. Daga Nan gidan aminiyarta tawuce, Hajiya Habi, da sallama tashiga gidan, Hajiya Habi ta amsa, "a'ah kaji manyan mata, daga Ina Kuma haka?" Murmushi maman Salim tayi tace daga gidan Salim nake, naje wurin wacce marar mutuncin matar, maiyima arziki kulli" D'aure fuska Hajiya Habi tayi, tace "kada ki Kuma yimin maganar Nan, tun yaushe nakemaki tayin diyata khairat akan ahad'a aurensu da Salim Amma kika watsamin kasa a ido" "bahaka bane, Hajiya wlh yaran yanzune ka haifesu baka haife halinsuba, kafin khairat saida nanemama Salim auren wata yarinya Nan kusadamu amma yaki ko saurarena barantana yajema yaga yarinyar, Amma yanzu nayimaki Al'kawarin koyanaso kobayaso saiya auri khairat indai nice na haifeshi. *(Tofah reader's ana wata gawata)* A 6angaren Salim Kuma tunda yatafi wurin aikinsa, hankalinshi bai kwantaba da halinda yabar Fauziyya, kullum daya kwanta da dare ba abunda yake sai tunaninta, anya yayimata adalci kuwa, gaskiya Bai kyautamataba, kowane irin laifi tayimashi yakamata ya hakura yabarta haka, ai tagane kuskurenta Kuma yasan bazata Kara gigin aikata laifi makamincin irin Wanda ta aikataba, da wannan tunanin ya yanke shawarar zaikoma gida yaga ya Fauziyyar take, Dan bazai iya hakurin zuwa wani weekend ba. Washe gari tunda safe Salim yadauko hanya, dan yamatsu yaga halinda Fauziyya take ciki, haka kawai yakejin rashin kyautawarshi akan abunda yayimata. Kamar yanda Sani yasaba yauma yayi wanke, wankensa yagama zuwa yayi bakin 'kofar d'akin Fauziyya yace "nagama abada kud'in cefanen" "Shigo ka karba mana" ba musu Sani yacire takalminshi yashiga d'akin, dama abunda yake nema, barantana yasamu, mi'kamashi kudin tayi tana lissafamashi abubuwan dazai siyomata, bazato ba tsammani sai ganin Salim sukayi a gabansu, bakaramin razana sukayiba suduka, Salim kuwa wata irin Zuciya ta kuloshi wani mahaukacin Mari ya d'auke sani dashi, sannan yakaimashi naushi a hanci, Nan take hancinsa yafara zubarda jini, jikinsa har tsuma yake saboda tsabar bala'i cikin d'aga murya yace "ubanwa yamaidoka gidannan bayan nakoreka" cin kwalarshi Salim yayi yace yau sainasan kowaye abanka a 'kasar nan dahar zanyima iyaka da gidana saboda ka rainani kakiji, to idan kakiji ai bakaki ganiba" hannu yasa cikin Aljihu ya fiddo wayarshi yanacewa "Dan ubanka yau hukumace kawai zata rabani dakai" Ai sani najin anyi maganar "yan'sanda Hantar cikinsa takad'a kad'an yahana yasaki fitsari a wando, hakuri yafara baiwa Salim Yana kuka, "Dan Allah kayi hakuri, karufamin asiri wlh bazankara zuwaba, dan Allah kada kahadani da police wlh banida Kowa a garinnan saiku, Koda wani nayima laifi ya kulleni ku kadai nakesaran zaku tsayamin, Dan Allah ka taimakmin kada kahadani da hukuma" Sanyi jikin Salim yayi yasaki sani, ya zauna kan kujera yahada hannuwanshi duka biyu ya rike kanshi. Fauziyya Kuma kuka take, tarasa me zatayi, itakau yau tabani, yazatayi da rayuwarta. Abubuwa duk sunbi sun rincabemata daga wannan sai wannan, Tasowa tayi tazo gaban Salim ta durkusa "Hubby Dan Allah kayi hakuri kada kahada sani da hukuma, nayima Alkawari tunda bakason aikinsa agidannan nahakura, zan sanya asamomin wani Almajirin, amma dan Allah ka kyaleshi yatafi, dukan dakayimashima kadai ya isa. Shiru Salim yayi baitankaba, kusan mintuna goma sannan ya kalli sani cikin tsawa yace "ficemin daga gida" da sauri Sani yatashi ya dauki takalminshi a hannu yafita daga gidan, ga gaban rigarshi duk ya baci da jini. *Hhhh su sani antabo ran maza yabaci* 🤣🤣🤣 Kai tsaye sansaninsu na Almajirai ya nufa, Yana zuwa yanufi dakinsu, yakoyi sa'a bakowa duk suntafi karatu Wanda shi yama manta rabon dayaje. Ruwa yazuba abuta ya wanke jikinshi, acire rigarshi wacce tabaci da jini ya wanke, sannan yayi wanka yadanji karfin jikinshi, dawowa yayi kan gurzajjiyar katifarshi ya kwanta, ya kalli sama, Azuciyarshi yace lallai Salim kadebo ruwan dafa kanka, wlh Kowa yaci tuwo dani Miya yasha, wlh tallahi sainasaka kuka da idanunka, sainasaka zubarda hawayenka, tashi yayi zaune yasa hannunshi yadafe kanshi daketa faman yimashi ciwo. Fauziyya Kuma saida, iyaye suka shiga cikin maganar sannan kome ya dai-daita Kuma Salim dakanshi yaje wata makarntar yasamoma Fauziyya wani Almajirin yarone Dan shekara Sha biyu. *Wannan kenan* [8/25, 7:55 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰 *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇🏻 *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 15 Shehu shine almajirin da Fauziyya ta canja, tun karfe bakwai na safe yazo gidan ko bud'e gida basuyiba yahau bugun 'kofa, cikin bacci Fauziyya tajiyo bugun 'kofa kamar za'a balla kyauren. Sallim ta kalla Wanda ke bacci cikin kwanciyar hankali, tabashi tayi tace "Hubby naji kamar ana bugun kofa" Saurarawa yayi yace "bari nafita nagani waye haka da wannan safiyar" Fauziyya tace "Allah sa dai lafiya" Salim yace "Ameen" jallabiya yasanya sannan yanufi zaure yabude, shehu yagani tsaye rike da robarshi irinta almajirai, ga wasu dangalalllun Kaya dayasa, sunyi muguwar dauda har wani maiko suke, gashi duk sun gama yayyagewa. Kallonshi Salim yayi a kyamace yace "lpy kake bugamana gida da wannan farar safiyar" majinar data leko daga hancin shehu ya janye sannan yace "aiki nazoyi" "what" Salim yafad'a da karfi har saida shehu ya razana, yace "kaine dama *ALMAJIRIN GIDANA*" daga Kai shehu yayi tareda sa bayan hannunshi ya goge sauran majinar dake hancinsa" A matukar kyamace Salim yace "kaje kaji munsamu wani Almajirin, dama namu yaje ganin gidane tokuma jiya da yamma yadawo" "to" shehu yafad'a Yana kokarin barin 'kofar gidan, kauda Kai Salim yayi Dan wani mugun zaurin fitsari daya ziyarci hancinsa. "Dan dakata Ina zuwa" Salim yafad'a tareda komawa cikin gida, d'aki yanufa ya tarar da Fauziyya harta dawo falo, tarbar Salim din tayi tace "Hubby lafiya, waye Kuma haka tunda safe?' "Ina zuwa Salim yace, wucewa yayi bedroom ya d'auko dari biyu sannan yanufi kitchen ya dauko wani sauran bread yafita, inda yabar shehu Nan yatarar dashi mi'kamashi bread din yayi yace "amshi wannan" jiki na kyarma shehu ya amsa, sannan Salim yamikamashi dari biyu yace "wannan kasiyi omo da sabulu kari'ka yin wanka da wanki" godiya shehu yayi yatafi Yana waiwayen gidan, Yana takaici dabaiyyi aiki cikinsaba, dan da alama za'a samu abun arziki a gidan. Komawa Salim yayi duk a kyamace, zuciyarshi sai tashi take, dan Salim mutum ne Mai tsananin kyankwami, inda yabar Fauziyya Nan yatarar da ita zama yayi kusada ita, tareda jawota jikinshi ya rungumeta. Shagwabewa Fauziyya takarayi jikin Salim tace "Hubby Wai waye dan Allah" Hannunshi yakai kanta Yana shafa lallausar gashin kanta yace "Almajirinkine" dago Kai tayi ta kalleshi tace "Yana ina?" Salim yace "Nakoreshi" zumbur Fauziyya tayi tazauna tace "kakoreshifa kace, habba Hubby to waye zairika yimani wanke-wanke da shara, gakuma yo cefane kasuwa, haba Hubby dan Allah ka tausayamin, so kake aiki yakasheni" Kallonta Salim yayi Yana jin matu'kar kaunarta a zuciyarshi, gsky Yana matukar 'kaunar Fauziyya, bayason abunda zai taba zuciyarta, mace ce managarciya, Mai hakuri, sannan uwa uba tana bashi hakkinsa na aure yanda yakamata, ga tsantsar juriya da...... 'kara jawota yayi jikinshi yace "look my wife, kada kisa damuwa aranki zanje da kaina nasake duba wani Almajirin, Amma wannan 'kazantarshi tayi yawa, na tabbatar Koda kece Kika ganshi wlh bazakiso yayimaki aikiba, dan Koda yayi hankalinki bazai kwantaba, ke kibarma batun wannan, Bari ingayamaki gaskiya muddin wannan Almajirin zaiyi aiki gidannan nagama cin abincin gidan" Zaro Ido Fauziyya tayi, arazane tace "Amma Hubby Mai zai hana uhm....umm "Fad'a mana my wife minene kiketa wani in-ina" "Kamin Al'kawarin idan nafad'a bazakace a'a ba" "Namiki Al'kawarin matata, farincikinki shine farincikina, kome kikeso inaso Wanda bakiso Kuma kome sonda nakemashi zan iya hakura dashi" Cikin fargaba da inda-inda Fauziyya tace "Hubby mai zai hana mu maido sani tunda kagashi da hankalinsa, Kuma Yanada tsafta, Kuma kaga munsaba dashi shekara nawa muna tar......... "Ke......dakata, yafad'a a tswace yace Fauziyya Ina gargadinki da... Wata irin Zuciya ta 'kuloshi yatashi fuuuu yashige bedroom, zama Fauziyya tayi falo tarasa miyema zatayi tashawo kan Salim. ***. ***. *** Zaune yake kan d'aya daga kujerun d'akin yayi shiru Yana sauraren sababinda mama kemashi. "Salim ka saurareni, wannan umarni nake baka ba shawara ba, kaje gidan Hajiya Habi, ku gaisa da khairat" arazane Salim ya dago ya kalli mama, Dan yasan khairat kamar yunwar cikinsa batada kamun Kai, tasha kawo tallar kanta gareshi rashin samun fuska yasa tashafamashi lafiya, watako yanzu tanan ta bullo, "aiko zanyi maganinta" yafad'a aranshi. Cigaba tayi da magana, "inaso ku dai-daita kanku sonike ayi auren Nanda wata daya" Wata irin fad'uwar gaba Salim yayi, yace "Amma mama... "Dakata banison wani dogon bayani, amma me? nagayama umarni nakebaka Kuma dole kabi, Kuma wlh idan kaje naji labarin kayimata wani mugun kallo ko kagayamata wata magana marar dadi wlh Allah ya'isa tsakanina dakai" dafe Kai Salim yayi da hannu biyu yace "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, mama.... ***. ***. *** . Hajiya Habi gogaggiyar Yar duniyace, tayi zaman saudiyya (kano to jidda) daga can ta haifi khairat, ubanta balarabe ne Yana can 'kasar saudiyya, rabuwar wulakanci sukayi da Hajiya Habi, saboda yakamata da maigadin gidanshi sunacin amanarshi. Dukda haka yaso tabarmashi khairat amma takiya, haka yabari tataho da ita badan ranshi yasoba, Yana masifar son khairat saboda ita kadaice diya mace cikin yayanshi. Tunda Hajiya Habi tadawo Nigeria tasayi gida tana zaman kanta, gidanta babu control banza da wofi dashara da bola Kowa shiga yake gidanta, khairat Kuma haka tataso ba tarbiyya, sai yawon gidan party, da bin maza, dan farkon wandayafara lalatamata rayuwa shine Alhji shitu bazawarin Hajiya Habi ne wand suke sheke ayarsu shine Kuma ya lallaba ta bayan kasa ya yaudari khairat din, dayimata ruwan kudi. *Reader's kuyi hakuri wlh banida lafiya ina fama da masassara da ciwon Kai Dan Allah kusanyani addu'a Idan naji sauki zakujini idan Kuma akasin haka to sai dai yanda yakama.* Mmn khady ce 🙏🏻 [8/26, 7:34 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰 *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇🏻 *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 16 "Hubby kada kasama ranka tunanin wani abu, wlh sani bayada matsala, kaga gashi da tsafta da sanin yakamata, babu wani abun 'ki tattare dashi, wlh duk wani Almajiri dazamuyi bazayakai Sani ba" Shiru Salim yayi na tsawon wani lokaci, sannan yace shikenan yadawo d'in, Amma da sharadin Koda wasa kada inga kafarshi cikin dakinki, ya tsaya iyakar aikinsa" "Kada kadamu Hubby, indai wannan ne inshaAllah zan kiyaye" "to shikenan, akiyaye" 6angaren sani Kuma tunda Salim ya koreshi daga gidanshi yarasa mikemashi dad'i, abubuwa duk sunbi sun jagulemashi, ga missing din Fauziyya da yayi, idanuwanshi na mararin ganinta, kunnuwanshi na tsananin son jin zazzakar sautin muryarta. "Yanzu yazanyi" yafad'a Yana share hawayen dasuka gangaro kan fuskarshi, "yazanyi da rashinki Fauziyya, kitaimakeni nashiga wani hali sakamakon yin nesa dake" wayarshi ya fiddo, hotunanta yafara kallo d'aya bayan d'aya, baya gajiya da kallon hotunan kullum sabbi suke koma mashi idan yana kallonsu. Yakai kimanin awa daya darabi yana kallon hotunan, saida wayarshi tabuga low battery sannan yamaidata aljihu. Tashi yayi jiki a sanyaye yafito wurin abokaninsa Almajirai daketa hidimar gabansu a harabar gidan nasu. Basiru ya hango can zaune bisa wani dutsi Yana wanki, karasowa yayi wurinsa ya zauna gefensa. kallonshi Basiru yayi yace "abokina narasa mike damunka nayi juyin duniyarnan kaki gayamin damuwarka Kuma naga kwana biyu bakaje gidan Fauziyya ba ko lafiya?" "Lafiya kau" sani yafad'a dan bayaso Kowa yasan maganar korar da Salim yayimashi, shiyasa ko maganar bayaso. "Ba dai lafiya ba abokina, dan nasan lafiya-lafiya hakanan bazakabar aiki gidan Fauziyya ba, kadai gayamin gaskiya" Basar da zancen Sani yayi yace "nifa ba wannan maganarce takawoniba, dama wata shawara nazo muyi nidakai muduka nasan zata amafanemu" "Ina jinka" Basiru yafad'a tareda maida hankalinshi kan sanin Dan sauraran abunda zaifada. Kaga jiya naduba kudina Wanda nake tarawa, yanzu sunkai kimanin naira dubu ishirin da shidda, shine nace mai zai hana muhada nidakai musamu wani karamin shago mufara siyarda kayan kwalliya, idan Allah yasanya Mana Albarka saikaga muna samun wani abu. Shiru Basiru yayi na wasu mintittika sannan yadafa kafad'ar Sani yayi dariya yace "abokina kace kadawo daga rakiyar shiririta, kagane gaskiya kenan, shikenan ba matsala kasan dama akwai wani d'an karamin shago dana kama dubu bakawaine kud'in dana biya na haya, shikenan saimuyi amfani dashi, yanzu kabada dubu ishirin da biyar Nima inbada ishirin da biyar, saimu Fara mugani" "To shikenan Allah yashigemana gaba" "Ameen" Wayar Sani ce tafara tsuwwa da sauri yafiddo daga Aljihu yaduba, sunan Fauziyya yagani, wani mummunan fad'uwar gaba yaji, dai baisan dalilin dayasa takirashiba. saurin tashi yayi daga wurin yakoma gefe nesa kad'an da inda Basiru yake sannan yad'aga wayar yakara a kunne, shiru yayi Yana jiran abunda zata fada. "Hellow sani, ya kake ya kwana biyu" shiru sani yayi yakasa magana, "Hello.....hello....... Sani kanajina kuwa?" Inajinki aunty "Ina wuni" "lpy lao" "Dama Kira nayi ingayama, Salim yace inbaka hakuri akan abunda yafaru Kuma yace kadawo kacigaba dayimani aiki" Wayyo Allah dad'i, saboda murna Sani rasa inda zaisa kanshi yayi, koba komai zaicigaba da kallon kyakkyawar fuskar Fauziyya yanajin dad'i. ***. ***. *** Kallon khairat Hajiya Habi tayi tace "Kai amma kinyi kyau wannan kwalliya haka, Ni nasan dole Salim ya amince da soyayyarki a wannan karon, Kinga kuwa yanda kikayi kyau kamar wata India" Wani kallo khairat tawatsama Hajiya Habi tace "kinmanta Hajiya aini nafi India, kohar kinmanta waye babana" "Ban mantaba khairat, watarana ai zankaiki saudia kigano babanki da 'yan'uwanki" Wayar khairat dake ajiye kan mirror kirar camon 11, ce tayi ringing, da sauri ta dauka ta kalli Hajiya Habi tace "Salim ne" dagawa tayi takara a kunnenta tace "eh kashigo kawai Jiki a sanyaye Salim yashiga gidan, gawani mugun bacin rai dake addabarshi, Hajiya Habi da kanta ta tarbeshi tayimashi iso awani madai-daicin d'aki Wanda yasha kujeru masu kyau da carpet tsakiyar d'akin sai karamin center table na glass, zama yayi sannan suka gaisa da Hajiya Habi din, Nan take tambayarshi mamarshi yace tana lfy. Komawa Hajiya Habi tayi wurin khairat tace kiyi sauri kije kina batamashi lokaci, ni bari infita Nan gidan Hajiya Asabe muje wurin maganar kayan damukayi da ita" "to saikin dawo" Feshi jikinta tayi da kalaluwan turare, sannan tanufi fridge ta dauko ruwan roba da lemu tadora kan tire da cup din glass tanufi d'akin da Salim din yake. Ajiye tire din tayi kan table dinda ke gaban Salim din sanan tamatso kan kujerar dayake zaune two seater zata zauna gaf dashi idan kaganima saikace kan cinyarshi tayi niyyar zama. Mi'kewa Salim yayi da sauri yace "ke miye haka, bakida hankaline" Cikin nuna rashin jin haushin abinda Salim din yayimata tayi murmushi tace "nice ko keda hankali, ai natabbata da banida hankali bazaka amince da aurenaba" "Wayagayamki amincewa nayi da aurenki, kawai zan aurekine dan bin umarnin mahaifiyata Amma banisonki, ko kad'an bani kaunar mace marar kamun Kai, khairat bakida tarbiyya ko kad'an babu namijin dazaiso ki kasance uwar yayanshi" Tunda yafara magana khairat ke kallonshi tana wani lumshe Ido yanda kasan Yana zubamata wasu kalaman soyayya, ko kad'an bai bata haushiba, saima burgeta dayakeyi, tadade tana son Salim, amma ya'ki saurarenta, yanzu Kuma tunda tasamu wannan damar bazatayi wasa da itaba, Koda Salim duk zuwa zai kamata yayimata duka bazata nuna taji haushiba barantana har yakawo rugujewar maganar auren nasu. Wani matsiyacin kallo Salim ya watsamata ganin yanda taketa wannan karairaya a gabanshi kamar macijiya, kasancewarta batada jiki ko kad'an kamar tsinke haka take Babu wata kwana single tatafi sai dai akwai tsananin kyawun fuska Mai d'aukar hankali, ga gashin kanta na asalin larabawa. Wani dogon tsaki Salim yaja, sannan yafice daga gidan, ko sallama basuyiba. Kai tsaye masallaci Salim yanufa yagabatarda sallar isha'i sannan yawuce gida, ranshi amatu'kar bace, Wai ace mama da kanta takeso tahad'shi aure da khairat kawai saboda tsanar dayayima Fauziyya, Tunda yashigo Fauziyya takula da halinda yake ciki, haka tafara kokarin kwantarmashi da hankali dukda batasan miye musabbabin bacin ran nashiba, Shiru Salim din yayimata, hakan ba karamin dagamata hankali yayiba, kuka tafashe dashi tace "shikenan Hubby nasan banida matsayinda zanbaka hakuri akan bacin ranka ka hakura, kanuna damuwarka ba dakuwata bace, nagode Hubby" mi'kewa tayi tana goge hawayen idonta, Wani irin tausayi tabashi, jawota yayi tafad'a jikinshi ya rungumeta tsam ajikinshi, tunaninshi daya shine yanda zai tunkareta da maganar aurenshi, gaskiya mama batayimashi adalciba. *Alhmdlh naji sauki, nagode da adu'oinku gareni, Naga dumbun masoya masu kirana a waya damasu yimin text massage damasu mun magana a chat duka Ina godiya, sai dai har yanzu jikina ba karfi,* Mmn khady ce 🤩 [8/28, 6:43 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰 *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇🏻 *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 17 Dare mahutar bawa inji Hausawa, kowace rai tanason hutu, Amma lokacin wasu ke cikin kunci da tashin hankali, kamar yanda Fauziyya ta kasance a wannan daren, misalin karfe 1:37am Fauziyya kwance gefen gado, ajiyar Zuciya kawai taketa saukewa saboda kukan datasha tun lokacinda Salim yagayamata maganar 'karin auren dazaiyi. Cikin bacci Salim yake jiyo sheshshekar kukanta, ahankali yabude idonshi ya saukesu kan Fauziyyar wacce takoma can karshe gado nesa dashi, tashi yayi zaune, jiki a sanyaye ya iso inda take yadafata, "kiyi hakuri Fauziyya, nagayamaki wannan auren wallahi bada son Raina zanyishiba, mamace ta tilastamin, Kuma wlh yarinyar nan banisonta ko kad'an, nifa duk wata mace indai bake bace wlh daya take da namiji a wurina, Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ni Ina tare dake kome wuya kome tsanani" Bayan hannu Fauziyya tasa ta goge hawayen dake bin kumatunta tace "Salim ba wannan bane damuwata, bansan yanda zamana zai kasance a gidannan ba idan ka Kara aure, nasan watarana mama saita watsamin kayana waje takoreni..... Hannu yasa yarufemata baki "dan Allah kada kisa wannan tunanin aranki, Fauziyya Ina sonki bazan iya rabuwa dakeba, babu kuma Wanda ya isa yarabani dake, mutuwace kawai zata rabamu" Ahakadai Salim yasamu yashawo kan Fauziyya, rungumeta tsam yayi ajikinshi suka kwanta, kowane zuciyarshi cike da tunani barkatai. Bangaren sani kuma sun bud'e shago shida Basiru, anzuba Kaya, Kuma alhmdlh suna samun ciniki sosai, bakaramin dad'i sani yajiba Dan Yana ganin tanan zaitara kudinda zaisamu ya auri Fauziyya, tunda amatsayin zawara zai aureta bawai wani makudan kud'i ake kashewaba, dan koda yaushe jikinshi na gayamashi Fauziyya saitazama mallakishi komin daren dadewa. Bangaren khairat da Hajiya Habi shirye-shiryen biki sukeyi sosai, dan anriga an sanya rana yau saura sati biyu bikin. Salim Kuma tun zuwan dayayi wurin khairat bai'kara zuwaba, Amma wannan bai dametaba itada Hajiya Habi sudai burinsu ayi auren Koda bayaso daga baya sun San yanda zasu bulloma al'amarin. Ko kad'an Salim Bai d'auki hidima yadorama kanshiba, bama zaka ganshi kace Yanada wata hidima gabanshiba, kullum dai Yana kan hanyar zuwa wurin aikinsa Yana fafutukar yanda za'a Kuma maidoshi wurin aikinsa, dan ko kad'an bayajin dadin kauyen dasuka maidashi. Sati daya yanata shige da fice, cikin ikon Allah yau dai yasamu abuda yake nema an maidoshi garinshi. Hakan bakaramin dad'i yayimashiba, Dan zai kasance da Fauziyyar shi Koda yaushe, zai Rika rarrashinta Yana kwantarmata da hankali Dan har yanzu tana cikin damuwa sosai. Maman Salim dakanta ta tsare Salim ta amshi kud'i masu yawa taje kasuwa tahado kayan lefe set din akwati, tacika kowane da Kaya bayabo ba fallasa, kayan sunyi bakin gwargwado. Salim Kuma dakanshi yashiga kasuwa yasiyoma Fauziyya tsaddaun Kaya less guda ukku, sai shadda guda biyu, sai atamafa kala biyar, sai dogayen riguna Dubai, suma kala hud'u, jikka da takalimi set hud'u, sai sauran tarkacen kayan make'up da turarruka, da sauran abubuwan dayakamata irinsu sarka passion da Yan hannu da sauransu. Hidima dai yinta akeyi ba Kama Hannun yaro, Maman Salim itace ke karbar kudi wurin Salim ko ransa besoba tayima khairat duk abunda akeyi, dan yauma khairat din tazo amsar kudin dinkunan data Kai Wanda zatasanya wurin bikin, dubu goma mamar Salim tabata ta amsa a wulakance Dan khairat ta bala'in raina mamar Salim. Salim kuma hidimar Shi kan Fauziyya yakeyinta dan itace damuwarshi, bayaso taga rashin adalcinsa. Fauziyya Kuma kallo d'aya zakayimata kasan tana cikin damuwa, amma haka take daurewa dan tana samun tsananin kulawa wurin Salim, shiyasa batason nuna damuwarta afili. Yau tun 'karfe bakwai Salim yabar gida saboda neman da akemasu wurin aikinsu sakamakon wani aiki da za'a turasu awata jiha, Wanda federal government ke neman hazikan malamai, na makarantun secondary shine makarantarsu tabada Salim saboda kwazonshi da Kuma jajircewa a wurin aiki, baya fashi saida wani kwakkwaran dalili, kuma Yana koyawa yanda za'a Gane sosai dalibai kejin dadinsa. tunda yafita Fauziyya tatashi tashiga kitchen ta fiddo duk kayan wanke-wanke, tashare kitchen din, sannan tafera doya tasa atukunya tadora a wuta, sannan takoma d'aki tagyara ko'ina tsaf tashare ta goge, tafesa freshner, tsakar gida tafito ta dauki tsintsiya tafara sharewa, Lokacin Sani yashigo da sallama, amsa sallamar tayi batare data dagoba, kallonta sani yayi

Chapter 4 of 13