Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin bacci Fauziyya takejin ciwon ciki, ahankali tabud'e idonta ta saukesu kan agogon bangon d'akin 'karfe 12 da rabi na dare, batayi niyyar tada Salim ba Amma sai taji ciwon sai Kara gaba yakeyi har abun nanema ya girmi tunaninta. Taba Salim tayi tace "hubby, hubby cikina" saurin bude Ido Salim yayi yace meyasameki, "cikina ke ciwo tafad'a tana ciccije baki saboda tsananin azabar ciwon dake addabarta. "Subhanallah, yafad'a yatashi yacanja Kaya itama ya taimakamata ta canja yace Zaki iya hawa mashin muje asibiti?" d'agamashi kai tayi Alamar e, Haka suka fito unguwar tsit bakowa, Salim yatada mashin Fauziyya tahau suka d'au hanyar zuwa asibiti Fauziyya na kwance bayan Salim, idan cikin ya murdamata saita kan'kameshi har suka iso wani asibitin kudi dake nan kusada unguwarsu, Sunyi rashin sa'a babu likita sai wasu nurse suka karbeta sukayimata allurar rage radadin ciwon tareda sanyamata 'karin ruwa, cikin ikon Allah kuwa saitaji sauki, Nan suka tabbatar ma Salim Akan dasafe likita zaidubata yaga miye matsalar. Nurse dinne suka umarci Salim daya koma gida dasafe yadawo, sune zasu rika kula da Fauziyyar. Washe gari 'karfe bakwai asibitin tayima Salim, dakinda Fauziyya take yanufa Kai tsaye, bacci ya iske tanayi, yayi kusan minti goma dashiga kafin tafarka bakinta d'auke da salati, taimakamata yayi tashiga toilet tayo Alwala tazo tayi sallah, sannan yatambayeta karfin jikinta "da sauki sosai tabashi amsa" wayarta yamik'amata "ga wayarki natahomaki da ita Koda Zaki nemi wani kokuma anemeki" "Nagode hubby" tafad'a tareda karbar wayar. *Dan Allah kurika ahkuri da duk yanda kuka samu wlh abubuwa sunayimin yawa ga hidimar gida, gana yara, Amma duk sanda nake free ai sau 2 nakemaku post ko* *Mmn khady ce* ðŸĨ° [8/20, 7:24 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* ðŸĪĶðŸŧ‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* ðŸĨ° *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇ðŸŧ *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 9 *Alhmdlh mundawo hutun sallah, my fans Happy Eid Elkabir, Ina mi'ka sa'kon barka da sallah ga 'yan'uwana da Kuma masoyana da kannena, Ina godiya ga irin soda 'kauna dakuke nunamin Nagode* *Gaisuwa gareku kannena na kaina* *Halimatu Elkasim* *Hauwa'u Elkasim* *Nasibat Elkasim* & *Amratu friend din Hauwa'u inayinki 100% Allah yabar zumunci* Da misalin karfe takwas na safe likita yazo d'akinda aka kwantar da Fauziyya, da sallama yashigo tare da wasu nurses su biyu wadanda suka karbi Fauziyyar a jiya, already dama sunyimashi bayanin matsalarta tunda yashigo asibitin, umarni yabada da ayima Fauziyya awon jini Dana fitsari sannan yaturasu d'akin scanning Dan Kara duba lafiyarta. Bayani yayima Salim yace "zamuyi wannan gwaje-gwaje dakuma hoton cikin nata inshaAllah zamu gano kowace irin matsalace ke damunta". "To Doctor nagode" Salim yafad'a, Nan aka dibi jinin Fauziyya, dakuma fitsari sannan sukaje akayimata scanning, Dawowa sukayi d'akin suka zauna suna jiran sakamako. Bangaren sani Kuma, kamar yanda yasaba karfe takwas yake zuwa aikinsa gidan Fauziyya, sai dai yau Yana zuwa ya tararda 'kofar gidan gar'kame, tsayawa yayi Yana mamakin Ina Fauziyya tatafi, haka tunda safe, iya saninshi da tsawon zaman dayayi agidan Fauziyya bata tafiya unguwa bata gayamashiba Dan karyazo ya tarda batanan, "to ikon Allah" yafad'a afili, sannan yasamu wuri ya zauna kusada gidan zuciyarshi cike da tunani barkatai. Wayarshi ya fiddo yafara shafawa, hotunan Fauziyya yake kallo daya bayan daya, kan wani hoto yazo Wanda Fauziyya tayi da mini skirt da wata Yar yaloluwar riga wacce ko hannuwan kirki batadu, ga wuyan rigar Mai fadine, shara-shara rigar take, hatta kalar bireziyar datasaka ana gani, Wanda Salim ne yayimata hoton da kanshi lokacinda tayi kwalliyar yake yaba kyanta, tanayimashi musu shine yace Bari yayimata hoto taga irin kyawun datayi shinefa akayi hoton, tagani Kuma saita barshi awarta har Sani yasamu damar turashi awayarta, Kuma duk cikin hotunanta yafison wannan, idan Yana kallonshi har wani nishadi yakeyi. Zooming din hoton yarikayi Yana karema ko'ina najikinta kallo, Yana fad'in "Fauziyya Ina sonki Ina kaunarki, inason kasancewa da wannan kyakkyawar fuskar taki, da dirarriyar surar jikinki wacce bakowace mace Allah yayima irintaba, Fauziyya inaso inji fatar jikina ta hadu da lallausar fatar jikinki, Fauziyya kisoni Mana, kisoni yanda nake sonki.... Saurin fita yayi daga folder picture din Fauziyya, dan folder guda yayima hotunanta a wayarshi Wanda idan yashiga su kadai zaita gani. Contact yashiga, sunan Fauziyya ya lalubo sannan ya danna Kira, riggin 2 Fauziyya tad'aga "Hello sani" "Hellow Aunty gani nazo gidanki na iske akulle lafiya kuwa?" "Ba lafiya sani, Ina asibiti" "Asibiti Kuma aunty,miya faru, waye bashida lafiya?" "Wlh sani nice banida lpy asibiti muka kwana, tun jiya 'karfe 12 nadare mukataho" "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Aunty bakida lpy ashe, Kuna wane asibitin?" Nan Fauziyya tagayamashi asibitin dasuke, cikin zakuwa sani yace "ganinan zuwa aunty zanzo indubaki, wlh duk hankalina yatashi, bazansamu nutsuwaba sainaga yanayin jikin naki" Murmushi Fauziyya tayi tace "kada kadamu sani nasamu sauki inasaranma asallameni anjima inshaAllah, yanzuma muna jiran results ne nawasu gwaje-gwaje da akayimin" "To Aunty Allah baki lpy" "ameen" Fauziyya tace sannan takashe wayar, dukda talura da irin kallonda Salim kemata tunda tafara waya da sanin, hakan baisa ta daina wayarba saida suka gama, Salim kuwa duk yabi yahada girar sama data kasa, wani mugun takaici yakeji dangane da wayar da Fauziyya tayi da Sani, kawai kyaleta yayi Dan yasan yanzu yanamata magana zata 6ata rai, shikuma ba abunda yatsana irin fushinta, Kuma gashi batada lpy. Sani kuwa suna gama waya da Fauziyya ya tsaida mashin yafadamashi asibitin dazai kaishi, cikin mintuna goma ya isa asibitin, batare da Bata lokaciba yagano d'akinda Fauziyya take dayake tagayamashi number d'akin, Dai-dai Yana zuwa likita nashiga d'akin, lokacin Kuma maman Salim ta iso asibitin Dan itama waya Salim yayimata yagayamata rashin lafiyar Fauziyya, Kuma ya gayamata anasaran cikine gareta dukda basu tabbatarba, Amma sunanan suna jiran sakamkon gwajin da'akayi. Da sallama mama tashiga, mamar Fauziyya ce ta amsa sallamar, wacce itama bata Dade dazuwa ba, waya sukayi da Fauziyyar tagayamata tana asibiti shine tazo, gaisawa sukayi itada mamar Salim ba yabo ba fallasa, sannan likitan ya gaishesu, ya kalli Salim yace "ga sakamakon gwaje-gwajen da'akayi Nan duka, yami'kama Salim yace kabiyoni office, sai nayima bayani ko" mamar Salim ce tayi karaf tace a'a likita kafad'a anan ai Babu bare anan cikinmu, nice mahaifiyarshi, wannan Kuma mahaifiyartace, tafad'a tana nuna maman Fauziyya. Duk abunnan sani Yana bakin window d'akin Yana jiyo duk abunda ke faruwa, dan tunda yazo yaga mamar Salim da mamar Fauziyya, ga Kuma Salim adakin yasa baishigaba, dukda yasan bayada matsala dakowa acikinsu sai mamar Salim din. Murmushi likita yayi yace, "amma kunsan wani abun Yana bukatar sirri" murmushi maman Fauziyya tayi tace "kada kadamu Doctor kafad'a kawai ai duk dayane" Murmushi Salim yayi yace "fada kawai doctor Nan ai duk iyayenmu ne" "Ok" doctor din yafad'a, sannan yafiddo wani farin siririn glass yasakama idonshi yace "sakamakon gwaje-gwajen damukayi mungano Fauziyya tasamu matsala amahifarta sakamakon amafani datayi da maganin zubar daciki ba bisa ka'ida ba Wanda hakanne ke haifarmata da ciwon mara lokaci zuwa lokaci....." wani mahaukacin fad'uwar gaba Fauziyya tayi tare da mi'kewa tsaye tadafe 'kirjinta Wanda zuciyrta ke barazanar fashewa saboda tsabar firgici, bangaren Salim ma hakane, kallon-kallo sukashigayi shida Fauziyya batareda kowannensu yayi maganaba, mamar Salim da mamar Fauziyya ma mi'kewa sukayi tsaye cike da mamakin abunda doctor din yafad'a, sani kuwa dayake la6e bayan window, gumine yagama jikeshi kamar Wanda aka shekama ruwa, Shiru d'akin yayi bakajin 'karar kome saina fankar dake juyawa wacce duk tsananin juyawarta Bai hana Fauziyya hada zufa ba. doctor ne yakatsemasu shirun dasukayi yace "Amma kada kudamu Naga kamar Kun daga hankalinku sosai matsalar ba Babba bace, ga magungunan Nan sai asiya indai takikaye tanasha kan ka'ida kome zai Koma normal inshaAllah Kuma inasaran tana gama shansu zata Kuma samun wani cikin da yardar Allah. Wani irin kuka Mai 'karfine ya kwacema Fauziyya tace "karya kake Doctor, wlh 'karya kakeyi nibansha maganin zubar dacikiba akanme zansha maganin zubarda ciki, bayan abunda muka Dade muna nema kenan.... Nashiga ukku dama akwai likitoci masu jama mutum sharri, tokasani Allah bazai barkaba, inshaAllah sai kaga sakayya tun anan Duniya na wannan mummunan 'kazafin dakayim...." "Dakata Fauziyya" Salim yafad'a cikin d'aga murya "Bakida wani sauran borin kunyar dazakiyimin, Ashe dama kece musabbabin zubewar farincikina, Kika zubarmin da gudan jinina, Fauziyya baki kyautaminba" ya karasa maganar murya 'kasa-'kasa hawaye nabin kumatunsa, Maman Fauziyya tace "kada muyi saurin yarda da maganar da likitannan yafad'a...." "Ke dakata malama Babu wata magana dazaki fad'a, ai tunda likita yace maganin zubar da ciki tasha, to wlh tasha, dan wlh kozaku hadiye kur'ani keda d'iyarki kice batasha maganin zubarda cikiba bazan taba yardaba, Allah yatona asirinku, dama ansaba zubarwa tun agida shine ananma za'ayi, idan banda dabbanci, waye kezubarda cikin Sunnah, ai idan kikaga anzubarda ciki tona rariya ne. Juyawa tayi kan Salim "to kaikuma shanyayye, ga abunda nake gayamaka nan, nagayama wannan yarinyar Bata nemanka da Alkhairi, Dan duk Wanda bayason ganin kwanka duniya ai bamai kaunarka bane, saboda haka Ina umartarka daka rubuta takardar saki yanzu kabaiwa Fauziyya..." Saurin dago Kai Salim yayi ya kalli mama, yace "haba mama plz, kibari abi kome ahankali mana" Likita dai tunda suka Fara hayaniya yabar d'akin Dan Yanada aikin yi. Sani Kuma Yana Nan dai inda yake yanaji Kuma Yana ganin duk takaddamar dake faruwa, "Salim kasaketa nace, wane ahankali? Bawani ahanakli kasaketa kawai" Tashi yayi yafita daga d'akin, sani naganin haka yaruga dagudu ya boye bayan wasu flowers, Salim kuwa mashin dinsa yahau yabar asibitin Ranshi amatukar bace. Mamar Salim kuwa, kallon mamar Fauziyya tayi tace "Bari kiji ingayamaki, daga Nan kiwuce da d'iyarki gidanki za'a aikomata da takardarta" "Haba mamar Salim, idan Rai yabaci ai hankali baya gushewa, baikamata ace kinzama almakashin datse igiyar aure ba, Allah bayason haka, kibari abi kome a sannu har asamu a warware matsalar" mamar Fauziyya tafad'a asanyaye. "Bawani ahanakli daza'abi, kitafi da mayaudariyar diyarki can ku karata". Tana gama fad'in haka itama tafita daga d'akin fuuuuu tanata bambamin fada. Duk sani yaga fitowarsu jiki asanyaye yabar asibitin, duk yarasa abunda kemashi dadi, wani kunci da takaici suka ziyarci zuciyarshi Wanda shi kanshi baisan dalilin hakaba, farinciki yakamata yayi awannan lokacin ganin igiyar auren Fauziyya tana lilo, Amma Kuma saiya tsinci kanshi a Sabanin haka *to miye dalili,?* *washh gajiyar sallah Bata sakeniba wlh, Ina typing Ina Gyan-gyadi* . *Mmn khady ce* ðŸĪŠ [8/20, 7:25 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* ðŸĪĶðŸŧ‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* ðŸĨ° *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇ðŸŧ *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 10 *JINJINA GAREKU YAN GROUP DIN ALMAJIRIN GIDANA NOVEL INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN IYA WUYA ANA TARE, INA MATUKAR JIN DADIN YANDA KUKE COMMENT KUMA KUKE BANI KWARIN GWIWA AKAN WANNAN LITTAFIN NAWA* *Dukda wasu shaid'an da hassada kan rufe ganinsu su gaza gane wannan k'yautatawar taki, hakan kan faru akan surukai, dangin miji, makwafta, ke harma daga cikin danginki, wani komi zaki masa bazai fasa aibantakiba, amma wlhy watan watarana koda bayan babukene saiya ambaceki koya tunaki cikin mutane Na kwarai, shiyyasa akace muguji ranar yabo.* Tafiya sani yake Yana rangaji, duk abubuwa sun jagule mashi, wani bangaren na zuciyarshi Yana cikin farinciki saboda Yana ganin kome yazo cikin sauki, dan yasan yanzu lokacin rabuwar Salim da Fauziyya yayi, Abu dayane ke batamashi rai yakesashi takaici shine yanda Fauziyya tashiga cikin matsanancin tashin hankali, bayason ganin bacin ranta Koda dai-dai da second dayane. Ahaka ya isa gidan kwanansu na Almajirai, gogaggiyar katifarka ya haye ya kwanta rigingine ya kurama rufin dakin ido, tunani barkatai acikin kwalwarshi. Bangaren Fauziyya Kuma kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita, tashin hankali tashi marar misaltuwa, wanda tunda take arayuwa ta Bata taba tunanin zata shiga irinsaba, kallin mamanta tayi da runannun idanuwata Wanda suka kumbura saboda tsabar kuka tace "nashiga ukku Mama, wlhy tallahi narantse harda Allah bansha maganin zubarda cikiba, kawai wannan likitan dai Yanada wata manufa tayimin wannan kazafin". Hararta mamar tayi fuskarta a d'aure ba Alamar wasa, tace "wace manufa gareshi dazai kagamaki sharri, mutumin dabai sankiba bai taba ganinkiba miye ribarsa idan yajamaki sharri, Fauziyya inaso kigayamin gaskiya tsakaninki da Allah miye yafaru akan zubewar cikinnan naki?" "Ki yarda dani mama, wlh bansan komeba akai, Allah shine shaidata" tafad'a tana Kara goge hawayen daketa zarya kan kumatunta. "Fauziyya banason muyita jayayya dake, kigayamin gaskiya Dan insan yanda za'a shawo kan abun tun kafin yayi nisa" "Mama kema kin yarda kenan, kin yarda da 'kazafin da'akayimin, shikenan mama, nasan duk yanda zanyi ba Wanda zai yarda dani tunda kema gashi kinki yarda dani, Allah kadaine shedata shine Kuma zai war-ware wannan matsalar" Kallonta mama tayi, "Hmm Fauziyya kituna nice mahaifiyarki, bakida tamkarni duk fadi'n Duniya, idan bakigayaminba waye Zaki gayamawa, Amma tunda kinki gayamin gaskiya bari in kyaleki, saiki tashi mutafi gida ko, ai kinsan dai bazaki koma gidankiba kina ganin wannan Uwar mijin taki yanda take cika tana batsewa itada d'an nata, na tabbatar idan kikakoma gidan Salim kome na iya faruwa, Kara mutafi gida idan zuciyarshi tayi sanyi dakanshi zai nemeki" "A'a mama kada muyi haka, idan Natafi gida kamar Karin wani laifine akan wannan da ake zargina akai, Kara inkoma gidan, zanyima Salim bayani Kuma nasan zai fahimceni" "To naji, Amma yazakiyi da mahaifiyarshi?" "Mama wannan ba matsala bace, indai Salim ya yarda ya amince ban aikata laifinda ake zarginaba wlh duk na mahaifiyarshi Mai saukine" "To shikenan Allah rufa asiri" mama tafad'a duk itama tayi sukuku jitake kamar itama tafashe dakuka ganin yanda diyarta tashiga matsanancin tashin hankali "Ameen" Fauziyya tafad'a. Tattara kaynsu sukayi suka fito harabar asibitin, saida suka Fara zuwa pharmacy suka siyo magungunan da aka rubutama Fauziyyar sannan suka tari adai-daita, har kofar gidan Fauziyya ya saukesu, saida mama tashigar da ita har gidan tayimata nasiha tare da kara bata hakuri akan duk abunda Salim din zaiyimata, Dan yanzu Yana cikin matsanancin bacin Rai zai iyayin kome, haka tatafi gidanta tabar Fauziyya cikin tsananin fargabar yanda zasu kwashe itada Salim. Maman Fauziyya tana zuwa gida ta iske maigidan, sannu da dawowa yayimata sannan yatambayeta jikin Fauziyyar, Nan takwashe duk matsalar dake faruwa tagayamashi, Yashiga cikin damuwa sosai dajin abunda yafaru, yace "wannan Al'amari akwai rud'ani aciki" "Wlh kuwa, itadai tayi rantsuwa ta mai-maita akan batasha maganin zubarda cikiba" "To Allah bayyana gaskiya" "ameen" mamar Fauziyya tafad'a. Tun bayan tafiyar mama Fauziyya tarasa inda zata sanya kanta, tsananin fargaba da fad'uwar gaba. Tun bayan azahar takesa ran shigowar Salim amma baidawoba, har la'asar shiru, ga wata irin yunwa dake addabarta, tashi tayi tanufi kitchen jikinta duk ba kwari, tattasai ta jajjaga tadora tukunya, indomie jallouf tadafa, da kwai mintuna Sha biyar tagama ta sauke, kula ta d'auko tana Shirin juyewa aciki tajiyo sallamar Sani, ansawa tayi tare dafitowa daga kitchen. Murmushi ta kakaro Wanda Bai kai cikiba tace "a'a sani Kaine" "Eh nine aunty, Ina wuni" "Lpy lao" "Yanzu daga asibiti nake akace an sallameku" "Eh wlh tun wurin azahar muka dawo" "Allah sarki, Aunty ya jikin" "Da sauki sani" "Allah karo sauki, Kinga kuwa yanda Kika rame aunty Kika Kara fari, gsky kinsha ciwo, waima miye ke damunki?" "Wlh kuwa sani, zazzabi ne da Dan ciwon Kai, Amma yanzu na warke, bari inzubama indomie ce nadafa" "Kai aunty daga dawowarki keda bakida lpy har Kika samu damar dafa wani abu" "Dole indafa sani Dan nasan duk inda Salim yake idan yadawo zai nemi abinci, kasan baisaba cin abinci awajeba" d'aure fuska Sani yayi dan Fauziyya ta ambaci sunan Salim, cikin zuciyarshi yace "akwai sauran aiki agabana dole nasaka tsanar Salim azuciyarki Fauziyya, dan Salim yanzu banida matsala dashi tunda ya yarda da kece Kika zubar masa da ciki nasan dole son dayakemaki yaragu da kaso sittin bisa dari...... "Sani... Wai tunanin me kakeyi haka... Firgici ya kalleta hannunta d'auke da plate din indomie, yace "wlh aunty rashin lafiyar kice ke damuna shiyasa duk nashiga wani hali, Allah dai yakaramaki lpy aunty" "Ameen" tace ta ajiyeminshi plate din gabanshi Wanda bayada niyyar amsa tawuce d'aki. Haka sani yafaracin indomie, Yana yaba iya girki irinna Fauziyya, Wanda komiye tadafa sai yayi dadi idan kanaci kamar kunneka zai tsinke. Daga Nan inda yake yaketa faman zubama Fauziyya surutu amma yau bai samu yanda yakesoba Dan bata biyemashi kome yace batabashi wata cikakkiyar amsa daga eh sai a'a sune kawai abunda take iya fad'a. Duk yanda sani yaso suyi fira da Fauziyya yau dai bai samuba, dan ita hankalinta nakan Salim Wanda tunda tadawo bai dawo gidanba gashi har andade dagama sallar isha'i. Mi'kewa sani yayi yace aunty Bari inwuce saida safe, Allah sauwake "ameen" ta amsa daga cikin d'aki. Sallama Salim yayi yashigo gidan, gaisheshi sani yayi sannan yayimashi sannu dazuwa, ba Wanda Salim din ya amsa sai wani mugun kallon tsana dayabi sanin dashi kafin yawuce d'akin. Tabe baki Sani yayi yace "Nina kashe zomon Kuma nine zan ratayeshi, babu yanda zakayi dani Salim, danni yanzu jina nake dai-dai dakai indai akan Fauziyya ne, da kamar ya labe yanda yasaba sai yaga koya labe bayada amafani dan bazai iya jiyo komeba tunda suna d'aki. Dole yabar gidan zuciyarshi cike da farinciki da Kuma haushin Salim, da tsantsar kaunar Fauziyya. *(Oh ni yasu, sani a daiji tsoron Allah)* ~kira garemu mata masu d'aukar 'katon Almajiri dasunan aiki wlh kalubale agaremu, Dan kwana ukku danaje gida, wani kanina yake bani labarin Almajirin gidan wata mata Wanda yayimasu asiri, saboda abun duniya, saboda haka wlh mata da maza magidanta kusan irin almajiran dazaku rika dauka sanamaku aiki agida, idanma yazama dole adauki alamajirin kenan, Amma idan sonsamune wlh sister kidaure kiyi aikinki da kanki zaifimaki kwanciyar hankali~ [8/23, 6:47 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* ðŸĪĶðŸŧ‍♀ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* ðŸĨ° *Daga Marubuciyar* 📝 *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now 👇ðŸŧ *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 13 Kuka Fauziyya tafashe dashi, kafin tatashi tafito falo, ido biyu tayi da kud'i dakuma takardar da Salim ya ajiye kan kujera, ahankali ta Isa wurin tasa hannu ta d'auki takardar, budewa tayi tafara karantawa. *Anyimani transfer wurin aiki anmaidani wani kauye, saboda haka natafi ga kudi nan nasan sun isheki har lokacinda zandawo, dan bazan rika dawowaba sai weekend* tana gama karanta takardar wasu sabbin hawaye suka ganagaro bisa kumatunta, cikin matsanancin bakin ciki tace "Haba Hubby ya isa haka, hukuncin ya isa, Koda dagaske na aikata wannan laifin ai hukuncin dakayimin ya hukuntani, yakamata kahakura mucigaba da rayuwarmu yanda muke ada. Daukar kudin tayi ta had'a da takardar ta rike tacigaba da kuka, jitake kamar tahada kudin da takardar ta 'kone, sai-dai hakan ba dacewa bane. Wayartace tayi Kara alamar shigowar Kira, amma ko kallon inda wayar take batayiba barantana ta dauka, harta tsinke aka Kara Kira nanma batada niyyar dagawa, saida aka Kuma Kira karo na ukku sannan tasa hannu ta dauka, sunan sani tagani akan wayar, saida tagoge hawayen idanunta ta dai-daita nutsuwarta sannan ta danna Alamar Kore tare da karawa a kunne, sani yace "Hello aunty ya kike" "Lpy lao sani, ya safiyar" "Safiya ba dad'i Aunty, kina ganin yanda oga Salim yayimin cin mutunci ya koreni batareda nayimashi wani laifiba" "Kayi hakuri Sani, dama kobaka kiraba inada niyyar inkiraka, ingayama kadawo dan Allah kacigaba da aikinka kayi hakuri da abunda Hubby yayima" Wani balai'itaccen kishine yatasoma sani jin fauziyya takira Salim da Hubby, jiyake kamar ya aza hannu bisa Kai yace wayyo, amma saiya daure yace "amma kina ganin hakan ba matsala, idan yaganni Kuma fa?" "Kada kadamu baya garin, an canjamashi wurin aiki yanzu idan yatafi baya dawowa sai 'karshen mako" Wani irin farincikine ya ziyarci zuciyar sani, dan yanzu yakeda damar tarewa gidan Fauziyya yaci karenshi ba babbaka. Ko mintuna goma ba'a karaba dagama wayarsu saigashi yazo gidan, cikin farinciki yashiga kitchen ya tattaro kayan wanke-wanke cikin yan mintoci ya wankesu tass, dayake dama bawani yawane dasuba. Yana gamawa Fauziyya tabashi kudin cefane yafita zuwa kasuwa, yana fita fauziyya tace "da Salim daya Kori sani nice zanrika fita inyo cefanen, Hmm ai maganar korar sanima daga nan gidanma bata tasoba". Ruwan wanka tahada tashiga toilet tasheka wanka, tafito tashafa mai batawaniyi kwalliyaba dan rabonta da kwalliya tun kafin Salim yajuyamata baya, wasu riga da zani na atamfa ta sanya, tayi mamakin yanda tasanya rigar cikin sauki Kuma batareda tazage zif ba, rigarda ta masifar matsarta Amma yanzu jinta take wata sakwa-sakwa ajikinta, me hakan ke nufi ta tambayi kanta, Wanda bata bukatar abata amsa dan tasan amsar. Kitchen tashiga ta silala indomie, tazuba nata a plate, sanan tajuyema sani nashi, tashige d'aki tana faraci sani yadawo, ajiye cefanen yayi kitchen sannan yashigo d'akin yami'kamata canjin, 'karba tayi sannan tace ya d'auki abincinsa nanan kitchen din. "To" Sani yace, tareda sha'kar 'kamshin turarenta ya sauke wata ajiyar Zuciya, sannan yafita d'akin, abincin nashi yadauka sannan ya zauna yafaraci Yana zubama Fauziyya shegen surutun daya Saba, yauma dai bata biyemashiba dan batada kwanciyar hankalin zama tayi surutu dashi. Haka Fauziyya ta zauna jugum cikin d'aki, shikuma Sani Yana tsakar gida, duk iya kokarinsa na ganin yaja Fauziyya da surutu abun yaci tura, haka yahakura yaja bakinshi yayi shiru, wayarshi ya fiddo yafara buga Game. Sallamar Sadiya tasa yad'ago kanshi tareda amsamata sallamar, wani mugun kallo sady ta watsamashi dan taganeshi shine *ALMAJIRIN GIDAN* Fauzy, kenan har yanzu bata rabu dashiba dukda girman daya karayi, gaskiya Fauziyya tanada matsala. Gaisheta Sani yayi, ko amsa gaisuwarshi batayiba tace "Fauziyya naciki?" "Tananan" yabata amsa ataikace. Sallama tayi tareda daga labulen d'akin, zaune ta hango Fauziyya tsakiyar carpet ta buga uban tagumi da hannu biyu, kallo d'aya sady tayimata tagane tana cikin matsananciyar damuwa, ga wata irin rama datayi, duk tabi ta kod'e takara fari idanunta sunfad'a, Juyowa Fauziyya tayi dan ganin waye tsaye bakin kofar, ido hud'u sukayi da sady tayi saurin tasowa tafad'a jikinta tasaki wani marayan kuka, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Fauziyya lafiya miye ke damunki, shiru Fauziyya tayi tacigaba da kuka, tambayar duniya sady tayimata amma taki bata amsa sai kuka dayaci 'karfinta, tun Sadiya na rarrashinta harta Fara bata haushi tace "wannan kuka Fauziyya bana lafiya bane, ko Salim ne yamutu? Girgiza mata Kai Sadiya tayi, to ko Mama da baba aka aikomaki basuda lpy? Nanma girgiza Kai Fauziyya tayi, "towai miye dan Allah, haba Fauziyya kefa ba karamar yarinya bace dazanta fama akanki, kigayamin abunda ke damunki idan inada maganin abun zanyimaki, idan Wanda zanbaki shawarane inbaki, idan Kuma yafi 'karfina intayaki da addu'a" goge hawayen fuskarta tafarayi Wanda basuda niyyar tsayawa, sannan ta zauna kan kujera sady ma zama tayi kusa da ita tace Ina jinki 'kawata gayamin damuwarki. Goge hawaye Fauziyya tayi tafara gayama Sadiya duk abunda ke faruwa tsakaninta da mamar Salim dakuma cikin datasamu da yanda yazube, da rashin lafiyar datayi likita ya tabbatarmasu musabbabin rashin lafiyar Wai akan tasha maganin zubarda cikine Wanda ita batasan da wannan zancenba, dakuma yanda Salim yajuyamata baya, ko magana bata had'asu yanzu sai dai yarubutamata ya ajiye, Goge hawaye Fauziyya tayi tace "yanzuma maganar damuke yau yayi tafiya wani kauye, Wanda akayimashi transfer daga wurin aikinshi, amma banci arzikin dazai gayaminba sai dai yarubutamin ya ajiye, Kuma bazai dawoba sai weekend, Kinga takardar daya rubuta" Amsar takardar sady tayi ta karanta, wata irin ajiyar Zuciya ta sauke sannan tamaida dubanta ga Fauziyya tace "kawata ki gayamin tsakaninki da Allah kece Kika zubar masa da ciki" "Haba sady kinsanni kinsan halina, kinsan abunda zan iya aikatawa da Wanda bazan iya aikatawaba, tun muna yara muke tare ba abunda ke rabamu nidake sai bacci, yakamata ace Koda wani kikaji yafad'i wannan maganar kizama mai bada kyakkyawar sheda akaina" Dafa kafadarta Sadiya tayi tace "na yarda dake kawata dari bisa dari, amma wannan al'amarin akwai rikitarwa acikinsa" Shuru sukayi suduka, kowace da abunda take ayyanawa aranta. Wani munafikin murmushi Sani yayi, dan yaji duk abubuwan da Sadiya da Fauziyya suka tattauna dukda yasan abubuwa da dama afirar tasu, Amma yasamu Karin haske sosai, Kuma yanzu burinshi yakusa cika Yana gab da mallakar Fauziyya. Sadiya ce takatse shirun tace "Fauziyya inaga yakamata su mama Susan da wannan maganar, sai asamu iyayenshi Salim din ayi magana inaga haka kad'ai shine solution, kawai ki shirya kije gida ki gayamasu" "Kina ganin hakan ba matsala" "Babu wata matsala inshaAllah" "To nagode 'kawata, amma zanbari saiya dawo sai inje yanda za'ayi maganar yana gari" "eh haka yakamata, Ni bari inwuce dama hanyace tabiyo dani wlh da kamar kada inshigo, saikuma naji kamar ana ingizoni ashe rabon inzo inji abu marar dadi" "Hmm kedai Bari kawata wlh ina cikin matsananciyar damuwa" "Aiba saikin fadaba Fauziyya, dan duk wanda yasanki ada yaganki yanzu yasan akwai matsala, kinga yanda kikayi wata muguwar rama" "Koni nasan narame wlh" "To Allah ya kyauta" Sadiya tafad'a tare da fitowa daga d'akin tasanya takalminta, idanunta kan Sani wata irin muguwar tsana takemashi Wanda ita kanta idan za'a tsareta tafad'i dalili batadashi. Rakota Fauziyya tayi har zaure, kallonta

Chapter 3 of 13