Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a wurin dan marinda Salim yayima Fauziyya jiyake kamar shine akayimawa, har cikin ranshi yakejin ciwon abun. Saurin kamashi khairat tayi ta fiddashi daga gidan ganin Yana neman tonamata asiri, tace "haba Sani miye haka zaka wani fad'i zaune kamar mai Shirin hawa bori, ko Kaine aka mara, iya abunda zakayi kenan, idan kuma haukanka yasa aka ganmu fa"? "Ba wanda zai ganmu, Kinsan ba abunda natsana arayuwata irin Inga abunda zai taba lafiyar Fauziyya, gaskiya ki canja wani abun banda abunda zaisa adinga dukanta, Kinga wannan kyakkyawar fuskar tata banison abunda zai tabata wlh bakijiba marinnan har cikin raina" "Naji jeka da Allah, tafad'a tana anguzaahi waje, kada kasa asamu matsala zamuyi waya anjima" Fita Sani yayi ranshi abace, khairat Kuma da sauri takoma cikin gidan tanajiyo yanda Salim keta zubama Fauziyya ruwan bala'i. Shiga d'akin khairat tayi tace "lpy dai nakejiyo hayaniya? "Lpy lao Salim yafad'a yasa Kai yafice daga d'akin zuwa d'akinshi,dan ko kad'an bayaso khairat tasan abunda ke faruwa tsakaninshi da Fauziyyar, Amma hakan bazai hanashi hukuntataba, hukunci Kuma mai tsanani, saita gane kuskurenta. Kallon Fauziyya khairat tayi tace "lafiya yanaga kina kuka wani aka aikomaki ya mutu?" Banza Fauziyya tayi da ita tatashi ta d'auke maganin da Salim ya watsamata tashige bedroom tabarta nan. Tabe baki khairat tayi tace "hmm kyaji dashi banza, nariga nasan kome, dakifad'a da karki fad'a duk d'ayane awurina Kuma zancigaba da bibiyarki har saina cimma burina. *Kuyi hakuri da duk yanda kuka samu munafama da matsalar NEPA* Mmn khady ce πŸ’ƒπŸ» 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 29 Koda Salim yakoma d'akinsa zuciyarsa tacigaba da tafar-fasa, "Wai miye ke damun Fauziyya data zabi Shan maganin Hana d'aukar ciki, bayan tasan rashin haihuwarta babbar matsalace tsakaninsu, tana ganifa yanda Mama ta tsaneta saboda rashin Haihuwa" Zama yayi gefen gadonshi ya dafe kanshi da hannu biyu "hmmm lallai biri yayi Kama da mutum, shiyasa har yanzu Fauziyya bata Kuma samun wani cikinba, bayan maganinda likita yabada yace indai tasha zata iya samun ciki kodawane lokaci" mi'kewa yayi tsaye yayi taku daya biyu zuwa ukku, "Wama yasani ko batasha maganin da likitan yabada ba tunda ba son haihuwar takeyiba. Bai ankaraba sai Jin hawaye yayi yanabin kumatunshi, Fauziyya mesa kikamin haka, miyasa Kika zabi Zama cikin 'kunci da tsangwamar mahaifiyata ta sanadiyyar hana kanki Haihuwa da kikayi" Komawa yayi kan kujera ya zauna yahade hannayensa duka biyu ya matse, jikinshi har karkarwa yake tsananin 6acin rai. "Yazama dole in d'auki mataki akanki" Tashi yayi rai 6ace yashiga toilet yashekama jikinshi ruwa ya d'auro Al'walar la'asar sannan yafito ya canja Kaya yafita zuwa masallaci. Khairat daga d'akinta tana ganin fitar Salim daga gidan tawani daka tsalle tafara rawa tana kwaso shoki, tayi tayi takumayin shaku shaku, sannan takoma zanku, saida tayi rawa tagaji sannan tanufi bedroom tanata faman Nishi kamar wacce tayi tseren gudu. Zama tayi gefen gado ta d'auko wayarta number Sani ta lalubo ta dannamashi Kira. Ringing d'aya ya d'aga dama jiran kiranta yakeyi Dan tunda yabaro gidan hankalinsa bai kwantaba ganin yanda Salim yad'auki zafi akan Fauziyya. "Hello" khairat tafad'a cikeda zumud'i. "Ina jinki" Sani yafad'a. "Kai mutumina bom d'inda na d'ana yariga yagama tarwatsewa" "Hmm khairat nidai gaskiya banji dad'in abunda yafaruba" "Kamar ya bakaji dad'iba" "Nifa banison 6acin ran Fauziyya ko kad'an"...... "Kai dallah dakatamani" tafad'a cikin fad'a _in banda iskanci yaushe anayima bakin 'ko'kari kana wani bakason haka, wlh idan ka 6atamin rai zanbaryin kome in kyaleka kaje can kamutu da son Fauziyyar Kuma kasan bazaka ta6a samuntaba........ "Ke dallah dakata, 'karamar Yar bariki, nikike gayama wannan maganar, to wlh ki kiyayeni dan koni Ina tsoron abunda ke kaina, zanshukamaki mugun rashin mutunci, haka mukayi dake cewa nayi kisa wannan kidahumin mijin naki ya d'auki wannan 'kazamin Hannun nashi yad'ora kan fuskar Fauziyya Kuma har mari biyu saboda kidahumanci, to kasani idan Kika kuskura yakara bugunta kome zai iya faruwa" Tunda Sani yafara bala'e jikin khairat ke kyarma wani irin mugun tsoron Sani ya d'arsu azuciyarta. "Haba my Sani miye abun d'aga murya Kuma, tafad'a cikin kaskantar da Kai, "kasanfa nidakai Amana ne, baikamata ace kana d'agamin muryaba, shikenan yanzu dai nayima Alkawari Salim bazai Kara Kai Hannunshi ya d'aki Fauziyya ba" "Dadai yafi" "Hmmmm" khairat tafad'a "Hmm, Kuma kifadamin idan akwai magana" "Babu magana" "To shikenan tawan dan Allah kiri'ka kiyaye abunda zai sani 6acin rai, yanzu mi kekeyi?" "Bakome" "Muhad'u gidan Zuby mana" "To shikenan muhad'u can d'in barina fito" tsinke Kiran tayi sannan tafad'a toilet tashe'ka wanka a gurguje tayi simple make up tashirya cikin wasu Riga da wando na Pakistan army green ta yafa mayafin kayan wayarta ta d'auka takira number Salim tanata ringing bai d'agaba harta tsinke, kusan sau ukku tana Kira amma no answer, massage taturamashi _Nakira wayarka baka d'aukaba dama zanje wurin kitso ne_ turamashi tayi saida ta tabbatar da massage din yashiga sannan tasaka wayar cikin porse dinta tasa Kai tabar gidan. Sanye yake cikin shirt dark blue Mai ratsin fari sai wando jeans hannunshi d'aure da fashion watch Fara 'kar, d'ayan hannun Kuma sanye da irin sarkar da maza 'yan gayu ke sanyawa a hannu, Kusan minti goma Sha biyar da zuwan Shi 'kofar gidan Zuby Yana jiran khairat Amma batazoba, ranshi yayi matukar 6aci dan amatse yake gashi itakuma tana neman ta 6atamashi lokaci, wayarshi ya fiddo daga aljihun wandonshi Yana Shirin Kiranta yaga napep ta tsaya khairat tafito kud'i tafiddo ta sallami Mai napep d'in sannan tadoshi inda sanin yake, suna had'a Ido gabanta yayi wani mummunan fad'uwa ganin yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja saboda tsabar jarabar dake cinsa. Saurin shigewa tayi gidan yarufamata baya, tana shiga gidan ta iske zuby falo ko gaisawa basuyiba ta wuce bedroom Sani yabita. Ta6e baki Zuby tayi a ranta tace "baccin ina samun kud'i wurin khairat da mi zai hana inyimata kwacen wannan guy d'in amma, duk da haka ba hakura nayiba, saina d'ana nima. (Kuji zuby Wai itama saita d'ana kamar wata mota 🀣) Khairat tana shiga d'akin ko gama cire Kaya batayiba Sani ya afkamata kamar dabba, haka yayita mid'iddikarta bai sauraramataba saida yabiya bu'katar shi. Yana gamawa yashiga toilet yasheka wanka yafito yasaka kayanshi, har lokacin khairat na kwance kan gado tana tunani "Wai yau mike damun Sani haka, gashidai yanda ya afkamata ba shiri Kuma bata gama biyan bukatartaba yabarta, gashi Kuma duk yahad'e girar sama data 'kasa, ita tsoron yimashi magana ma takeyi. Du'kowa yayi saitin fuskarta yace "nizan wuce" "To" kawai ta iya bashi amsa tajuyamashi baya. Murmushin mugunta Sani yayi Dan yasan abunda ya aikata yace "to kawai zakice bazaki bani wani abu ba"? "Bazan badaba dallah ka kyaleni, mtsww taja dogon tsaki ta gyara kwanciyarta, dariya yayi yace "ok bye" yafice daga d'akin. Harabar gidan ya iske zuby zaune kan kujera tana waya, ganin fitowar Sani yasa ta tsinke wayar ta kalleshi tace "harka fito?" "Eh" Yacemata kawai yasa Kai yafice. Murmushi tayi tace "zan kamaka a hannu, zanyima 6arin kud'i fiye da yanda khairat keyima, saina mallakeka, kamar yanda khairat ta mallakeka. 6angaren Salim Kuma tunda aka idar da sallar la'asar yakasa fita daga masallacin tunani kala-kala cunkushe a kwalwarshi. Yanzu wane mataki yakamata in d'auka akan Fauziyya, kodai inje Ingama Mama? "Kai a'a gayama mama tamkar 'kara rura wata wutar ne a gidana. "To kodai gidansu zanje inkai 'kararta?" "Bazanyi hakaba, idan nakai 'kararta bansan wane mataki zasu d'aukaba" Kawai bari inbarshi tsakanina da ita zanyi solving din kome batareda Kowa yasaniba. Wayarshi datayi ringing har sau ukku Bai d'agaba, sannan yaji shigowar massage yad'auka yaduba, ganin sakon khairat ne, Yana gama karantawa yamaida wayar Aljihu yanufi hanyar gidan dan yanasao yayi magana da Fauziyya yanzune zasuyita tunda khairat batanan. 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 30 Fauziyya kau tunda Salim yafita daga d'akinta take kuka, tunani yayimata yawa a kwalwarta, "Ina Salim yasamo wannan maganin, itadai tasan batada ala'ka da wannan maganin Amma sai gashi yana tambayarta akanshi, miye Kuma hakan ke nufi?" Tashi tayi tafara safa da marwa acikin d'akin tanaso ta tuna ala'karta da wannan magani, amma iya tunaninta da dogon nazarinta har yanzu bata iya tuna komiba. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Allah kafitar dani daga cikin wannan masifar dake nemen afkamin" Sallamar Salim tajiyo, da sauri takoma gefen gado ta zauna hankalinta tashe, wani irin tsoron salim yakamata, dan d'azun yabata tsoro sosai, tunda take dashi bata taba ganin mugun 6acin ranshiba irinna wannan lokacin. Shigowa yayi d'akin ya zauna kusa da ita sannan yakira sunanta, amsawa tayi kanta sadde tana kallon 'kasa hawaye na d'iga daga idonta. "Inaso kigayamin gaskiya, banaso ki boyemin kome kigayamin tsakaninki da Allah mi kika Sani dangane da wannan magungunan?" Cigaba da kuka Fauziyya tayi tama kasa magana. "Fauziyya tambayarki nake ba kuka nace kiyiminba, kigayamin" D'ago runannun idanunta tayi Wanda suka canja launi zuwa ja saboda tsabar kuka tace "ka yarda dani Hubby wlhy bansan kome akan wannan maganin ba" tafad'a tana Karo goge hawayen dake zarya kan kumatunta. Shiru Salim yayi na tsawon minti biyu, sannan yami'ke tsaye yafara Kai komo cikin d'akin Yama rasa ta inda zai bulloma al'amarin. Gaban Fauziyya ya tsaya idanunshi sun kad'a sunyi jajir saboda tsabar 6acin ran dayake ciki, hannuwanta yakama duka biyu yami'kar da ita tsaye ya zubamata idanunshi masu firgitarwa yace "kigayamin gaskiya Fauziyya, yaushe kika canja, kin canaja hali Fauziyya kinzama ma'karyaciya macuciya, maci amana, kin cuceni kin ha'inceni ashe dama..... Yarfar da hannuwanta yayi dayake ri'ke dasu cikin 6acin rai, yakoma ya zauna bakin gado yadafe kanshi da hannu biyu, wani bala'in ciwo yakeji kan nayimashi. Zuwa Fauziyya tayi ta durkusa gabanshi ta d'ora hannunwanta kan cinyoyinsa, lumshe idanunsa Salim yayi hawayensa na d'iga kan hannunta, bin Hannun nata tayi da kallo tanajin ciwon zubar hawayen mijinta. "Kayafemin hubby wallahi bansan komeba, tsawon shekara nawa muna tare dakai bantaba yimaka 'karyaba, baka taba samuna da wani mummunan Hali........ "Dakata Fauziyya, yafad'a cikin d'aga murya, banison Jin kome daga gareki, kije kiyi duk abunda kikaga dama Allah bazai barkiba" Ture hannunta yayi daga jikinshi yafita daga d'akin a fusace. Lokacin khairat tashigo gidan da sallama, ganin Salim datayi yasa duk ta daburce gani take kamar zaigane inda taje. Ganin ko kallonta beyiba yashige d'akinsa, yasa itama tayi saurin wucewa nata d'akin tashige bedroom ta canja Kaya dan najikinta duk sunyi squizing, Sani yagama tumurmushesu. Fitowa tayi falo ta d'auko remote dinda ta d'auko d'akin Fauziyya, tanufi d'akinta zata maidamata, sallama tayi, daga bedroom Fauziyya ta amsa mata, khairat daga falo tatsaya tace "dama remote ne dana ara d'azu shine na maidomaki" "To ajiyeminshi Nan ko kan kujera" "To" khairat tafad'a tareda ajiye remote din sannan tabar d'akin, tana kallon kofar bedroom dinda Fauziyya ke ciki. *Bayan kwana biyu* Salim fushi sosai yakeyi da Fauziyya dan ko magana bata had'asu yanzu ko gaisuwarta baya amsawa Kuma yaraba shimfida da ita, kud'in cefane ma idan zaibata sai dai ya ajiyemata, idan Kuma yanaso yayimata wata maganar sai dai yarubuta a takarda ya ajiye. Duk wannan abun dake faruwa ba wanda khairat bata saniba, dan tana biye da duk wani motsin Fauziyya da Salim, Kuma lokacin data d'ibarmasu yakusa cika. Yau khairat tashi tayi da wani irin ciwon Kai, ahaka ta d'aure tayi wanka tashiga kitchen tarasa miyema zataci, ga yunwa tanaji amma bata sha'awar cin abinci. Indomie tafara tunanin dafawa saboda itace mai saukin sarrafawa. Haka Kuma akayi indomie d'in tadafa, da kwai, tana gamawa jikinta har kyarma yake saboda yunwa ta juye a plate ko kitchen d'in bata bariba nan ta zauna tafaraci, taci kusan rabi taji zuciyarta na tashi, wani irin amai yazomata dagudu tanufi toilet tafara sheka amai ba 'ka'k'kautawa, saida ta amayar da duk abunda taci aranar, sannan ta wanke bakinta takoma bedroom ta kwanta kan gado taja bargo ta kudundune saboda wani fitinannen sanyi takeji sakamakon zazzabin daya rufeta. Wayarta taji tana ringing, Amma takasa d'auka harta tsinke aka kuma Kira nanma ta tsinke, kusan Kira biyar amma takasa d'agawa. Kira aka kumayi karar wayarma bayamata dad'i shiyasa ta lallaba ta d'auko takoma cikin bargon tana duba missed call din, duka Kiran Sani ne. Tana Shirin kiranshine wani Kiran yasake shigowa, d'agawa tayi takara a kunne murya na rawa can 'kasa-'kasa tace "Hello Sani ya akayi"? "Kina Ina haka inata faman kiranki baki d'agaba halan baccinne naki dakika Saba" "A'a wlhy Sani ganinan kwance banida lafiya" "Miye ke damunki?" "Wlh zazzabi ne da ciwon Kai" "Eyyah sorry khairina, Amma ai Zaki iya daurewa muhad'u ko, yauba gidan Zuby zamuba kawai muje hotel" "Bana iyawa Sani, ban iya zuwa ko Ina wlh banida lpy sosai" "Ok to Allah sauwake" Sani yafad'a yakashe wayar. Ranar haka khairat takwana da rashin lafiya ba Wanda yasani, dan Salim itama yadaina kulata sosai tunda suka samu sa6ani da Fauziyya. Saida gari ya waye Yana Shirin fita daga gidan yashiga d'akin khairat din zaibata kudin cefane dan yau zata 'karbi girki, isketa yayi kudundune cikin bargo, "Kekuma lpy kike kwance"? Nan take sanardashi batada lafiya tun jiya. Sannu yayimata sannan yabata kud'i yace taje asibiti. A daddafe tashirya taje asibiti gwajin farko da akayimata likita ya tabbatarmata da tana d'auke da ciki na kimanin wata d'aya da sati biyu. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, khairat tafad'a jikinta na rawa tafito daga office din doctor din da takardar gwajin a hannunta, wuri tasamu ta zauna gidin wata bishiya inda babu yawan jama'a wayarta ta fiddo takira number Sani" Ringing d'aya yad'aga cikin rud'ewa tace Sani kazo asibitin Amafin clinic inanan dan Allah kazo yanzu akwai matsala. Kafin yayi wata magana ta katse Kiran, idan hankalin khairat yayi dubu yatashi dan tunda take harka da maza bata taba ko batan wataba, barantana Kuma ayi maganar ciki, lallai yau akwai babbar matsala kenan. Minti ishirin yakawo Sani asibitin, khairat yakira tagayamashi inda take, Yana isowa tatashi a firgice tana fad'in "Nashiga ukku, yanzu yazanyi da wannan cikin?" Murmushi Sani yayi yace "bangane mi kike nufiba" Takardar hannunta tami'kamashi kagani Sani wannan sakamakon gwajin da akayimani ne Ina d'auke da ciki na wata d'aya da sati biyu" "To saime, dan kinada ciki shine zakibi kiwani d'aga hankalinki, kamar dai bakida miji" "Ko inada miji nasan ba cikinsa bane, Kuma shima yasan ba nashi bane tunda baitaba kusantataba" Shiru sani yayi nawasu mintuna sannan yace "inaga kawai muje azubardashi" A razane ta kalli Sani, "zubarwa fa kace.... "Eh inaga haka shine solution" "Gsky Sani banshirya mutuwa yanzuba, kobansan azabar da akesha wurin zubarda cikiba, dukda bansaniba inajin labari, Kuma wasu har rasa rayuwarsu sukeyi, gaskiya ni bazan iyaba... "Ke kika Sani cikin ai jikinki yake bajikinaba,... Kada kadamu Sani kabar kome a hannuna nasan yanda zan bulloma Al'amarin" "Ai dama kome a hannunki yake, yafad'a Yana wani kannemata Ido "Toya? zamu d'an shakata ne" Haba Sani ina cikin wannan masifar kake fad'in wani shakatawa kabari inyi solving wannan matsalar data dosomu" ta doso mu kodai ta dosoki yafad'a a zuciyarshi. Wucewa Sani yayi hidimar gabanshi hankalinshi kwance. Khairat Kuma daga asibitin tarasa inda zata nufa, dubara ce tafad'o mata, Mai napep ta tsaida tashiga. *Reader's dole muyi rawa mukwaso shoki, khairat ankusa zama mama, Sani Kuma za'a Zama baban baby* πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ *Bari muga yazasuyi da wannan ciki* πŸ€”πŸ€”πŸ€” [9/14, 9:03 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 31 *Game Started* ⚽ 'kofar gidansu Salim napep ya ajiye khairat, sallamarshi tayi sannan tanufi gidan, ko sallama Babu tashiga gidan, tun kafin takarasa ciki tafashe da kuka, da sauri Maman Salim tafito daga d'aki Jin kukan khairat d'in, "Subhanallah lafiya khairat miye ke faruwa, daga Ina kike haka?" Kuka khairat tacigaba dayi baji ba gani, mamar Salim Kuma sai rarrashinta takeyi tana tambayarta abunda yafaru amma taki kulata sai kuka kawai take kamar wacce aka aikoma da sa'kon mutuwar uwarta da ubanta lokaci guda. Rungumeta Mama tayi ajikinta tace "yau ni Naga ikon Allah, yanzu khairat idan kinsan bazaki gayamin abunda ke damunkiba miye amfanin zuwanki wurina, kodai baki d'aukeni amatsayin uwa ba" Jin wannan maganar ta mama yasa khairat tad'an tsagaita da kukan datake, tana share hawayenta da gefen mayafinta. "Muje daga ciki" maman Salim tafad'a, kama Hannun khairat din tayi zuwa d'aki. Zaunar da ita tayi kan kujera, sannan taje pridge ta d'aukomata ruwa Mai sanyi tasha, kafin itama tasamu wuri ta zauna tana fuskantar khairat d'in. "Inajinki d'iyata kigayamin abunda yasameki haka, ko wannan juyar matar ce tayimaki wani abu yanzu inje incimata mutunci" Girgiza Kai khairat tayi tace "a'a Mama ni Fauziyya Bata tsaremin kome ba" "To Salim ne, mi yayimaki" Wani sabon kuka khairat ta dasa, hadda sheshsheka. "Ki gayamin miye yayimaki Wanda yayi zafi haka kike wannan uban kukan, ko sakinki yayi"? Cikin kuka khairat tafara magana "Mama abunda Salim yayimani 'karama ace sakina yayi nasan inada 'yanci, zan iya zuwa in auri wani, amma wannan auren na Salim shine ake Kira *AUREN JEKA NAYIKA* kawai dai munyi aurene amma wata mu'amula ta aure bata ta6a shiga tsakanina da Salim ba" sake fashewa tayi da wani sabon kuka, sannan tacigaba da magana "mama kiduba kigani yau wata biyu da 'yan kwanaki da aurenmu, kamar ya ajiye icce, nimafa mutumce ba gunki ba, sai kullum Yana wurin wannan matar gashi itada yakebi d'in abanza tunda gashinan bata ko batan wata, nidai kawai Mama kisa yasakeni inje insamu Wanda yakesona in Aura, nagaji da wannan wula'kancin" Tunda khairat tafara korama mama bayani zuciyarta ke tafar-fasa take cika tana batsewa, "Yanzu kina nufin ba abunda yata6a shiga tsakaninki dashi?" D'aga Kai khairat tayi. "watako abunda Salim yayimani kenan, niya maida abokiyar wasanshi, hmm zanyi maganinshi yanzu" Wayarta ta d'auko ta lalubo number Salim ta dannamashi kira, ringing d'aya ya d'aga, kafin yayi magana tafara ruwan Bala'i "Salim nizakacima mutunci a garinnan, nizaka maida mutunniyar banza to wlh baka isaba, kayi maza duk abunda kakeyi kazo gida yanzu Ina nemanka" kafin yayi magana ta tsinke kiran tareda ajiye wayar tanacigaba da sababi "shashasha Wanda baisan inda duniya tadosaba, ana gwadamaka hanya kana kaucewa. Minti goma Sha ukku yakawo Salim gidan, da sallama yashigo ba Wanda ya amsamashi, Kai tsaye d'akin Mama yanufa Yana d'aga labulen yaga khairat saida gabanshi yafad'i, ahaka ya karasa shiga d'akin yasamu wuri ya zauna ya gaisheda Mama cikin girmamawa. Kasa amsa gaisuwarshi tayi saima rufeshi datayi da fad'a. "watako Salim ka gama rainani, ka maidni abokiyar wasanka, yanzu saboda Allah ace ka auri yarinyar mutane ka ajiyeta kamar ka ajiye itace, yau kimanin wata biyu da 'yan kwanaki amma babu wani abu daya ta6a shiga tsakaninka da itaba amatsayinta na matarka, sai dai kullum kana jikin wannan kod'addiyar juyar wannan matar taka wacce ba abunda aurenta ya tsinanamaka tunda gashinan har yanzu takasa ajiyema d'a a gidan. to wlh yau-yau basai gobeba Inaso inji labari ya canja idankuma ba hakaba Allah ya isa tsakanina dakai" Jin mama tana jan Allah ya isa yasa Salim saurin d'agowa ya kalli mama, Yana Shirin yin magana ta kwatsamashi tsawa "banison Jin kome daga gareka maza ka d'auki matarka kuwuce" Kallon khairat tayi tace tashi kutafi kinji 'yar Albarka Allah yayimaki Albarka, ai kinyi ha'kuri wlh, idan bakeba wacece zata iya zama da namiji baya kulata har wata biyu, nagode kinji zanzo gidan inji" "To mama" khairat tafad'a zuciyarta cikeda farinciki. Suna fita waje Salim yatada mashin d'insa tsuntsun soyayya. khairat tahau yaja mashin d'in afusace, dan ranshi yagama baci akan wannan fad'an da mama tayimashi. Cikin minti goma suka Isa gida, a 'kofar gida ya sauke khairat tashiga gidan shikuma yakoma harkokinsa dukda ranshi ajagule yake. Misalin karfe Sha d'aya na dare Salim yadawo gidan abunda baitayiba, dan duk inda yake karfe takwas yadawo gida, Amma yau saboda abunda khairat tayimashi yasa yaji bayason dawowa gidan, dama ga zafin Fauziyya akanshi sai abun yataru ya had'emashi. Duk sunyi bacci lokacin, rufe gidan yayi sannan yanufi d'akinshi yayi wanka ya canja Kaya zuwa na bacci, sannan yafito yanufi dakin khairat, zuciyarshi na tafarfasa, waishi wannan yarinyar zata Kai 'kara aiko yau zatasan takai 'kararsa, zaiyimata abunda takeso amma ba yanda takesoba. Bud'e bedroom d'in yayi ya hangota kwance kan gado tayi d'ai-d'aya tanata sharar bacci hankalinta kwance "hmm *zakisan koni waye*" Shiga yayi d'akin ya cire kayanshi gaba d'aya sannan ya afkamata, wulakance yafara murzartar ba sassauci, cikin bacci khairat taji abunda Salim din kemata hankali tashe ta bud'e Ido ta sauke kan Salim d'in, Fara tureshi tayi Amma ko motsawa bayayi saima cigaba dayake da murzarta duk abunda yayimata mai-makon taji dad'i sai wani irin zafi dan bayayimata kome da sauki, ahaka dai har Mai afkuwa ta afku. Sauka Salim yayi daga kan gadon zuciyarshi cikeda takaici da ba'kincikin yanda yasamu khairat d'in tariga tagama zubarda mutuncinta a waje. Tunda yasauka kanta take zaune bakin gado tana kuka, juyowa Salim yayi ya kalleta kukanta wani mugun haushi yakebashi, shine yakamata yayi kuka ba itaba, Kallonta yayi yace dallah malama kiyima mutane shiru, kukan ubanme kikiye abunda kike nemane Kuma kinsamu saikuma me?" "Amma wannan abun dakayimin wlh hard mugunta" fusata yayi yace "ke nikemaki mgunta, d'auketa yayi da lafiyayyan Mari, bazato ba tsammani ta dafe kuncinta kafin ta farga ya 'kara zubamata wani marin, saida yayimata Mari biyar lafiyayye, cikin muguwar Zuciya yace "kukan bura'uban me kikeyi, bayan kinriga kingama watsewa a titi, munafukar banza, wlh saikinyi nadamar kasancewa matata" 'mikewa khairat tayi azuciye tace Nika mara, to wlh baka mari banzaba dan wlh saina rama mugu azzalumi macuci, Allah ya isa..... .......ke nikeke zagi" "An zageka mugu" Sha'kota Salim yayi yafara kwallo da ita, Yana dukanta tundaga bedroom har falo, halbi Kam khairat tashashi dan Salim haukacemata yayi, Mai ha'kuri fa bai iya fushiba. Can cikin bacci Fauziyya tajiyo ihun khairat, da kamar kada tafito saikuma taga rashin dacewar hakan. Fitowa tayi tanufi d'akin khairat, ganin yanda Salim yadage yanata jibagarta yasa Fauziyya saurin Isa wurin tanabashi hakuri, dakyar tasamu yarabu da khairat, ta fiddashi daga d'akin yakoma d'akinshi yanata huci. Kallonta Fauziyya tayi tace "kekuwa miya had'aku haka har kikajama kanki wannan duka" Harararta khairat tayi tace "Ina ruwanki" taja dogon tsaki "mtswww munafincin banza kawai" Tashi tayi da kyar tanufi bedroom jikinta ko'ina ciwo. Murmushi Fauziyya tayi tace "bani nakashe zomonba rataya akabani, badan niba da bansan irin dukan dazakishaba, Allah dai wadaran mutumin dabaisan arzikiba" Komawa Fauziyya tayi d'akinta, a zuciyarta tana tunanin meye khairat tayima Salim har yakemata wannan mugun dukan. Khairat kuma kasa bacci tayi saboda yanda jikinta ke ciwo, Allah ya isa kawai takejama Salim. Wani 6angare na zuciyarta Kuma cike da farinciki tunda bu'katarta tabiya Salim ya kusanceta, dama burinta kenan. daga yauma bazai Kara samuntaba, zatacigaba da harkarta da Sani dan tamafi Jin dad'inshi. *Muje zuwa Reader's yanzu aka Fara wasan* πŸ€ΈπŸ»β€β™€ Mmn khady ce πŸ‘ŽπŸ» [9/15, 7:24 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* πŸ€¦πŸ»β€β™€ *Writing By* *Zee Elkasim (Mmn khady)* πŸ₯° *Daga Marubuciyar* πŸ“ *Siyasa ko soyayya* *Alhini* *Gidan Asali* *Halin Girma* *Autar Hajiya* *Zanen Zuciya* *Yarinyar Baba* *Auren tagwaye* *Wata Uwar mijin* *Ke Duniya* And now πŸ‘‡πŸ» *ALMAJIRIN GIDANA* 🏠 Page 32 Washe gari khairat da ciwon jiki tatashi, saida tahad'a ruwan dumi ta gasa jikin nata sosai, tanayi tanayima Salim Allah ya isa, waraka tasamu tashafe ko'ina na jikinta sannan taji sauki-sauki. Fauziyya kuwa tunda takwaci khairat hannun Salim taga irin mugun dukan dayayimata hankalinta yatashi, koda takoma d'aki bacci gagarar idonta yayi, haka tayita juyi Zuciyarta tunani barkatai "Wai miye ke damun Salim duk yabi ya canja yazama wani birkitacce, ita yajuyamata baya Yana fushi da ita, itakuma khairat yayimata mugun duka, wani irin tsorone yakamata kada itama watarana yakamata da dukan, dukda batasan laifinda khairat din tayimashiba harya daketa. Ranar haka suka tashi gidan sukuku, kowa da 'kunci da takaici a zuciyarshi, khairat Kuma wani sashen na zuciyarta cikeda farinciki Dan tasamu inda zata ma'kala cikin dake jikinta batareda wata gardamaba dole a karba, dan nanda 8month ta haihu aiba Wanda ya isa yace d'a bana Salim bane. Misalin karfe takwas Salim yafito daga d'akinshi cikin Shirin zuwa wurin aiki, baishiga d'akin khairat ba, saboda mugun haushinta yakeji, d'akin Fauziyya yanufa itama dan zaibata kud'in cefane da bazai shigaba. Bakin 'kofar yatsaya yafiddo biro da farar takarda yayi d'an shot note yahad'ata da kudin yashiga d'akin. Duk abunnan dayake khairat tana labe jikin window tana kallonshi, takasa fitowane Dan gani take kamar Yana ganinta zai Kuma rufeta da duka. Karar ruwa yajiyo daga toilet hakan ya tabbatar mashi da Fauziyya wanka takeyi, ajiye takardar yayi gefen gado tareda kud'in yafito daga d'akin. Har yanzu khairat na jikin window tana kallo harya fito yabar gidan. Sauri tayi tanufi bedroom d'inta tabud'e wata loka ta d'auko wata farar takarda tanufi d'akin Fauziyya, har lokacin Fauziyya na wanka, tura kyauren bedroom d'in tayi ahankali yanda baza'ajiba tashiga, Dube-dube tafarayi har idanunta suka sauka kan kud'i dakuma takardar da Salim ya ajiyema Fauziyya gefen gado, hannu tasa ta kwashe takardar da kudin sannan ta ajiye

Chapter 8 of 13