da tsantsi Yana hana karyewar gashi sannan uwa uba Yana fatattakar dandruff daga cikin gashi komen dad'ewarsa,sannan Yana 'kara bakin gashi, wannan man Yanada kyau wlh duk wacce tayi amfani dashi saita Kara nemansa Kuma saitaba 'kawayenta da 'yan'uwanta labari* 👩🏻👩🏻 *Hajiya kisiya kiga yanda gashinki zaikoma abin sha'awa ke kanki sai kinji dad'i* 😘
*Idan Kuna bu'kata serious ku tuntubi wannan no*👎🏻
08166169254
Mmn khady ce
[10/3, 7:00 PM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 43
*Saboda Jin dad'in comment dinku nakaramaku wannan*👎🏻 *BONUS*
Bayan kwana biyu dayin suna Fauziyya na kwance bedroom tana bacci Yan biyu Kuma *Hanif & Hanifa* suna wurin Inna rabi, dan tunda aka haifesu Itace mai kula dasu,
Khairat na tsakar gida tana goye da Khalid tana shanya kayanshi data gama wankewa Kan igiya, Sani yashigo gidan.
Kallonshi khairat tayi tace "gaskiya Sani munyi fushi"
"Fushi Kuma nami"? yafad'a fuskarsa babu alamar fara'a Wanda ganin haka yasa khairat Shan jinin jikinta, Amma saita daure tayi tamaza tace "bakazo ganin two wins ba mana"
"To ai gani nazo yanzu"
Khairat dakanta tashiga d'akin Fauziyya, Inna rabi ta iske falo tare da two wins d'in tace "Inna dama Sani ne yazo ganin baby's"
"To yashigo Mana" Inna Rabi tafad'a tana bin khairat din da kallo...
Fita khairat din tayi minti biyu suka shigo tana gaba Sani na bayanta, Zama sukayi suduka Sani ya gaida Inna Rabi tareda yimata barka, ta amsa cikin fara'a tami'kamashi Hanif yagani sannan ta karbeshi tamaidashi takuma mi'komashi Hanifa.
Ganin yarannan ba 'karamin d'ga hankalin Sani yayiba, Amma ba yanda zeyi yariga yad'aukarma kansa Al'kawarin duk ranarda Fauziyya ta haihu yahakura da ita.
Fauziyya najin shigowar Sani Amma tayi shiru bata fitoba, ita batamaso yazo ganin baby's ba dan batasan da mugun abunda yazoba, Amma koma miye tayi tawakkali ga Allah bata cuci waniba tasan Allah bazai bari wani ya cutar da itaba.
Haka Sani yafita daga d'akin ranshi amatu'kar bace, suna fitowa tsakar gida yami'ka hannu khairat ta sauko Khalid daga baya tami'kamashi, ya rungumeshi jikinshi Yana 'karajin 'kaunarshi azuciyarshi, sannan ya sumbaceshi a goshi kamin ya mi'kamatashi yabar gidan.
*Bayan kwana biyar*
Yau an d'aura auren Sani da Zuby, anyi shagali dai-dai gwar-gwado, ango Kuma yatare gidan amaryarsa, ansha amarci dukda dai dama andad'e dashanye amarcin tun kafin auren.
Bayan sati biyu khairat tagama wanka, yanzu Khalid yanada wata biyu yayi wayo ya 'kara girma, Hanif da Hanifa Kuma sunada wata d'aya, suma sunyi wayo sosai ga wata uwar 'kiba dasukayi Kamar yan wata ukku, kyawunsu ya'kara fitowa Hanif Haskenshi yakara fitowa dan yafi Hanifa haske dama tunda aka haifesu.
Kulawa suke samu sosai daga wurin Salim, baya nuna banbanci duk abunda zai siyo Wanda ya danganci yara guda ukku yake siyowa, haka suma iyayen khairat da Fauziyya Yana kamanta Adalci tsakaninsu wuri d'ayane kawai baya adalci shine har yanzu baya iyaji zai iya kusantar khairat.
Khairat Kuma ha'kurinta yagama 'karewa, saboda haka tun kafin Salim yafita ta tambayeshi zataje gida takaima mama Khalid, bai hanataba saboda haka Yana fita tada'uko waya takira Sani.
Ringing d'aya yad'aga "Hello"
"Hellow Sani kana inane"
"Ina gida ya akayi"
"Plz inaso dan Allah ka taimakamin yau kome kakeyi kabani lokacinka muhad'u gidan Zuby"
Shiru Sani yayi Kamar baiji abunda tafad'aba saida yaji tana fad'in Hello, sannan yace "inaji"
"Ok kaji abunda nafad'a ko"?
"Eh naji amma gaskiya bazanje gidan Zuby ba kawai muje ki Kama mana d'aki a hotel"
"Ok to idan hakan yayima badamuwa sai muhad'u a Al-bustan Hotel, misalin karfe hud'u na yamma Dan Allah kadafa inyita jiranka"
"Indan wannan kada kidamu kinsanni banida African time"
"To shikenan sai mun had'un"
Suna gama waya tashiga wanka tahau shiri, sannan tashiryama Khalid cikin wasu green d'in Kaya Riga da wando na yara yayi kyau sosai.
'karfe hud'u saura minti shabiyar tafita daga gidan, bayan tayima Inna Rabi da Fauziyya sallama akan zataje gidansu.
'karfe hud'u dai-dai napep ya sauketa hotel d'in, batayi minti ukku da zuwaba Sani yazo, tare suka jera har cikin hotel din, khairat takama masu d'aki suka kar6i key din suka wuce.
Suna shiga d'akin khairat batajira wani abuba ta sauke Khalid dake goye bayanta yanata bacci ta kwantar dashi.
Tafara cire kayanta, Sani yanata kallonta, saida tagama kaf tafad'a kanshi tafara kissing d'inshi tako'ina saida tagama cajamashi kwalwa sannan yatashi yacire kayanshi suka fara abunda suka Saba.
Haka suka ida cinye wannan lokaci suna aikata masha'a basu bar hotel d'inba sai 'karfe tara na dare, khairat tawuce gida tana shiga gidan Salim na dawowa.
Shikuma Sani daga hotel d'in gidan amaryashi zuby ya wuce.
Lokacinda yakoma tagama shiryamashi abinci lafiyayye, yazauna yakwashi gara, bayan sungama sunkoma bedroom suka kwanta,
Zuby tanuna tana bu'katarshi amma ya'ki kulata duk yanda takai da kwakwa dole tahakura amma ta dasa ayar tambaya akanshi, tasan kila yau yahad'u da khairat, Dan idanba hakaba tasan Sani kullum sai yayi, amma bawani Abu aidama tare tagansu, wannan ba abun damuwa bane.
Tundaga wannan lokacin Sani yazama tamkar Mai mata biyu, yau khairat gobe zuby.
Zuby tasan da haka amma koda wasa bata ta6a nunama Sani tasaniba,
Khairat dai batasan da wata ala'ka tsakanin Sani da Zuby ba, barantana Kuma tasan sunyi aure.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, yauda gobe asarar mai rai.
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Tsarin gidan Salim ya canja baki d'aya, sakamakon cigaba daya samu wurin aiki, kud'i sun zaunamashi sosai,
Baki d'ayan gidan an canja mashi design, kowace anyimata part d'inta
Sai motoci guda biyu da Salim yasiya, daya saboda hidimar gida, d'ayar Kuma Yana fita aiki da ita kokuma wata zuwa unguwa nafita kunya.
part d'in Fauziyya an fidda d'akin Hanif da Hanifa anzubamasu Kaya kome guda biyu abun gwanin birgewa, yaran sunyi wayo sosai idan kagansu zakayi zaton sunfi shekara biyu.
Hakama Khalid ya girma sosai kyakkyawa dashi, fari tas kallo d'aya bazakace bahaushe bane, zakayi zaton irin 'ya'yan larabawa ne.
wata irin sha'kuwa sukayi da Hanif da Hanifa, bacci kad'ai ke rabasu, wani lokacima ko baccin baya rabasu dan wurinsu Hanif yake kwana, domin yafi samun kulawa anan fiyeda wurin khairat.
Hanifa tunda tataso yarinyace Mai shegen wayo da surutun tsiya, Hanif Kuma akwai son 'ya'uwanshi yayinda Khalid ya kasance so silent magana batacika damunsaba, kullum zaka ganshi shiru kamar marar lafiya yanayinsa, idan kaganshi cikin wal-wala to Yana tare da 'yan'uwanshi Hanif da Hanifa.
Khairat tuni tabar tafiya da Khalid unguwa tunda ta yayeshi, nan take barinshi wurin Fauziyya tayi tafiyarta yawon bin hotel itada Sani.
Inna Rabi Kuma ana yaye twowins takoma 'kauye sai dai tana zuwa lokaci zuwa lokaci tana dubasu, dan zamanta gidan Salim ba'karamin sha'kuwa sukayi da Fauziyya ba.
___________________________
Sani zaune tsakiyar carpet dinda ke shinfed'e tsakiyar falon, kulolin abincine gabanshi zuby Kuma tana zaune gefenshi da alama abinci suka gama ci,
Fira suke tabawa kad'an kad'an, cikin firar tasu zuby tasako maganar zuwa garinsu Sani.
"Waini baby yaushe zamuje garinnan naku naga tunda mukayi magana shekaranjiya bakacemin komeba, yakamata ace nasan 'yan'uwanka koda mutum d'ayane kodan abunda nake d'auke dashi, kaga yanzu cikinnan harya shiga wata hud'u baikamata ace na haihu babu danginkaba, Kuma kaga yakamata iyayenka Susan kayi aure tunda kaga basusan da maganar aurenmu ba".
Saida takai aya sannan yace "na mantane ban gayamakiba tun ranar dakikayimin magana natsara yanda zamuyi tafiyar, gobe zamu tafi inshaAllah saboda haka ki shirya mana kome yanda yakamata.
Wani irin dad'i zuby taji Kuma tundaga lokacin tahau Shirin tafiya.
Ranar khairat da Sani suka had'u hotel kamar yanda suka Saba, bayan sunagama she'ke ayarsu yake sanar da ita maganar zuwanshi garinsu, fatan Alkhairi tayimashi sannan tanuna irin missing d'inshi dazatayi, kud'i mai yawa tabashi tace yayima mutanen gida tsaraba.
Washe gari misalin 'karfe takwas na safe suka fito cikin motar zuby zasuyi tafiyar, tun kafin subar garin suka shiga wani 'katon super market zuby tayima iyayen Sani tsaraba saida tacika but da kayan masarufi sannan suka d'au hanya.
Tafiya suke suna labari, cikin so da 'kauna da kulawa da juna hankalinsu kwance, zuby itace ke driving saboda tafi Sani kwarewa dukda Shima ya iya ta koyamashi Amma har yanzu hannunsa bai gama fad'awa ba.
Tunda suka fita gari zuby tafara sharara uban gudu kamar zata tashi sama dan taga titin baida yawan motoci, wata mota take ko'karin wucewa, saiga wata motar tataho da gudu saitin hannunda zata hau, cikin zafin nama ta kauce sai dai akayi rashin sa'a motar takwacemata tanufi daji, 'karshe takaima wani 'katon icce Karo, kafin kace me jini yafara zuba ta wurin 'kafar motar....
Sani da Zuby Kuma duk iya hangenka baka ganinsu cikin motar.
Mmn khady ce 👎🏻
[10/3, 7:00 PM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 44
*MASU SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BAN YAFEBA, KUMA INSHAALLAH KUD'IN BAZAI MAKU ALBARKA BA*
Motar da abun yafaru Kan idonta ce tafara tsayawa kafin wasu motocin duk su tsaya domin taimakon wad'anda sukayi accident d'in.
Kafin ayi wani Abu har police sunzo, nan aka samu aka fiddo Sani Babu Rai tare dashi amma baiji ciwo ko kad'an ba.
Zuby Kuma ansha wahala kafin asamu a fiddota can 'kasan seat itama dai Babu rai amma bataji ciwoba sai Jini dake bin 'kafafunta.
Asibiti aka wuce dasu, kasancewar basuyi nisa dagariba shiyasa aka dawo dasu babban asibitin dake garin, emergency room aka nufa dasu ba Kamar zuby tana matukar bu'katar taimako.
Likitoci ne suka taru akansu domin ceto rayuwarsu, kusan awa biyu kafin asamu numfashin Sani yadawo jikinsa.
Zuby Kuma dama basu dad'e dazuwa asibitin ba ta farfad'o sai dai tayi asarar cikin dake jikinta.
Kwanan Sani da Zuby biyu a asibiti aka sallamesu suka dawo gida, bazaka kallesu kace sunyi wani accident ba, dan babu ko kwarzani a jikinsu, sai dai rashin gudan jininsu dasukayi, Wanda hakan ba'karamin ciwo yayimasuba, bama Kamar Sani Allah yasanyamashi son cikin zuby tun kafin yazo duniya, ashe dai bazai rayu ba, Amma ba yanda zasuyi dole Susama ransu hakuri Allah zai sake basu wani.
Haka suka dangana suka cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.
6anagaren khairat Kuma yau sati biyu kenan da tafiyar Sani kullum saita Kira wayarshi yafi a 'kirga Amma baya shiga, sakamakon 6acewar wayarsa lokacinda sukayi accident, hakan ba 'karamin damunta yakeba saboda haka yau ta yanke shawarar fita ko Allah zaisa taganshi kokuma taji labarinsa.
A waya takira Salim tagayamashi zataje gidan zuby, bai hanataba saboda haka tahau shiri, Khalid sai binta yake yana cewa mama Ina zuwa, Amma ko kallonsa batayiba tacigaba da shirinta.
Cikin wasu fitinannun riga da siket na wani had'adden material blue, sannan tadawo pink din gyale da pink din takalmi da jaka ta Sanya, kalaluwan turare tafeshe jikinta dashi, tafito daga sashenta Khalid sai binta yake Yana fad'in inazuwa, tureshi tayi tace "Kai kada kadameni ko kaga Ina fita dakaine, wuce can katafi wurinsu Hanif kayi wasa"
Sukuku yanufi sashen Fauziyya Yana hawaye, koda yaje baishigaba sai yatsaya 'kofar falon.
Haniface tafito daga falon taganshi, Kama Hannunshi tayi tace "Khalid waye ya bigeka? Momynka ce ko? Taho mutafi mu momynmu bata duka"
Binta yayi suka wuce d'akinsu, suka had'u da Hanif suka Fara wasa, cikin d'an lokaci Khalid ya manta da wani bacin rai.
Khairat kuma tana fita daga gidan Kai tsaye makarantar su sani tanufa gidansu na *ALMAJIRAI* ta tambaya ko yananan,
Nan suka sheda mata ai Sani yafi shekara biyu rabonsa da zama cikin wannan gidan.
Tambaya tayi ko sunsan inda yakoma, sukace gaskiya Basu saniba, da dai abokinsa Basiru nanan daya gayamata domin shine kad'ai yasani.
Haka tabar wurin ranta a dagule dan taso ace taga Sani yau, yanzu Kuma Ina zata nufa.
Napep ta tsaida tashiga bayan tagayamashi inda zai kaita suka d'au hanya.
Sani Kuma Yana tare da Zuby d'inshi dan tunda sukayi accident suka dawo baya fita ko Ina kullum Yana gida.
Zuby Kuma bata gajiya da abunda aka Saba, badare ba rana kullum aikin kenan.
Yauma Kamar kullum kwance suke Kan gado suna Raya saunnah, tunda aure ne sai dai muce raya Sunnah.
Lokacin khairat tashigo gidan tanata faman kwad'a sallama amma shiru ba'a amsaba, Zuby da Sani sunyi nisa sun Lula acikin duniyar ma'aurata.
Gajiya tayi da sallama tashiga falon bataga kowaba, bedroom tanufa batareda wani tunaniba.
Wata irin 'kara tafasa tareda dafe kanta da hannu biyu sakamakon mummunan ganin datayi tsakanin Zuby da Sani.
Baya tayi dagudu tana niyyar barin gidan, da sauri Sani yasa boxer yabiyo bayanta lokacin harta Kai bakin get tana Shirin fita yayi saurin ri'keta "khairat.... khairat.... Kitsaya mana, ki tsaya ki saurareni.
'ko'karin kwace hannunta takeyi tana kuka Kamar ranta zai fita " mezanji Sani ka cuceni ka kasheni da raina, ashe dama zuby kake nema..... innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"
Wata irin tsawa Sani yadaka mata "ke dallah kirufama mutane baki, kiwuce mushiga daga ciki muyi magana kada kitara mana mutane.
Binshi tayi ciki, zuby Kuma tunda khairat takamasu jikinta ke 6ari tana fad'in "shikenan nashiga ukku na lalace, asirina yagama tonuwa yau nabani na lalace.
Suna shigowa tayi firi-firi da ita Kamar kicemata tak ta ranta ana kare.
Zama Sani yayi kan kujera yacema zuby tami'kamashi rigarshi, jiki na kyarma taje ta d'auko takawomashi yasanya.
Khairat na tsaye tana kallonshi, zuby Kuma ta'ki yarda su had'a Ido da khairat.
Sani ya kalleta yace "ki zauna mana"
"Zama, ai banga ta zamaba cikin wannan 'kazamin gidan, yanzu Sani miye baniyima mena rageka dashi amma bazaka iya ha'kuriba ka danne kwad'ayinka saika 'kara da Zuby, tafad'a tana kuka.
Sannan tacigaba da magana cikin masifa da d'aga murya "Sani kacika munafikin Maci amana, ka cuceni ka cuci rayuwata Allah ya isa kaci amanata.......
"Tassss kakeji ya d'auketa da wani lafiyayye mari, cikin tsananin huci da 6acin rai yace "akwai babbar Maci amana irinki Mai Zina da aure, munafika annamimiya, to Bari kiji in gayamaki zuby ba nemanta nakeba aurenta nayi"
Zaro Ido khairat tayi cikin tsananin firgici tace "Aure.....aurefa kace Sani, zubyn ka aura"
"Tabbas Aure" Sani yafad'a cikin gadara.
Dariya khairat tayi Mai Kama da ta6in hankali tace "to kasani Sani ka auri mutuwarka da kanka, muna zamanmu kaje ka kwaso mana 'kamaya-maya saikutashi mu d'unguma muje asibiti likita yayita aunamu Kamar yadi"
"Mi'kewa tsaye Sani yayi yace "ke dakata khairat bangane inda maganaki ta dosaba.....
Kafin yarufe baki khairat ta kar6e "to Zuby dai 'kanjamau kegaret.......
Kafin ta ida fad'i Sani yaji kanshi na juyamashi yafara gani wani duhu-duhu kawai sai gani sukayi yafad'i sume.
Zuby naganin haka tayo Kan khairat gadan-gadan tacimata kwala, tana fad'in "wlh idan Kika kashemin miji saina kasheki, muguwa."
Itama khairat kwalar Zuby taci tace "gakinan muguwa azzaluma kinsan kinada HIV Kika aureshi danki gogamashi.......
"Na aura d'in ba son abun duniya yakawoshiba, ko kinsan tsakanin aurenmu zuwa yanzu nawa nakashemasa...
"Koma nawa Kika kashemasa Ina ruwana, Nikuma dakika gogamawa ubanme Kika bani"
"Uban mi zanbaki kuwa, sakamakon daya dace dake ne wannan, kina nufin zakiyi bariki ki wanye lapiya, harma kisamu sakamakon samun miji Kamar Salim...
Wani mugun naushi khairat tayima zuby abaki, Nan take ha'korinta guda yacire jini yafara ambaliya.
Itama zuby dukan khairat d'in take, haka sukayita danben bala'i cikin gidan Babu Mai rabasu, ga Sani kwance a sume harta kanshi sukebi suna takawa wurin fad'a.
Kafin kace mi sunyima kawunansu muguwar illah, khairat tafi zuby 'karfi saboda haka zuby tafi jin jiki, sai dai wani mugun cizo da zubyn ta labtama khairat a kafad'a Wanda saida taciro tsokar wurin.
Kayan jikinsu Kuma sun yayyage sunyi fata-fata.
Sani dai Yana kwance rai hannun Allah,
Suma dasuka gaji da damben kowace zubewa tayi tana maida numfashi Babu mai iya tada wani cikinsu.
Azabar ciwon da bakin zuby keyi sakamakon fita da ha'korinta yayi shiyafi kome addabarta, rarrafawa tayi ta d'auko wayarta takira number Alhj Haladu wani abokin tambad'ewarta ne tagayamashi sunanan gida itada mijinta ba lafiya ya taimaka yazo yakaisu asibiti.
Minti ishirin Alhj Haladu ya iso gidan, yayi mamakin yanda yasamesu Kamar wad'anda sukayi wani mummunan had'ari.
Haka ya kwashesu yazuba mota yakaisu general hospital, akace baza'a kar6esuba sai anzo da police,
Ganin suna neman su jazamashi wata fitinar yasa yakaisu wata asibitin kud'i Nan aka kar6esu aka Fara Basu taimakon gaggawa, sannan khairat taro'ki likita dayayimasu awon HIV suduka,
Jininsu aka eba akaje lab, suduka sakamakon d'ayane suna d'auke da cuta Mai karya garkuwar jiki.
Sai dare sannan Sani ya farfado, yaso a sallameshi likita yace gsky baza'a sallameahiba akwai sauran gwaje-gwaje da akeson yimashi, khairat da zuby Kuma tun ranar aka sallamesu,
Khairat tawuce gida cikin tsananin tashin hankali, Wai yanzu itace d'auke da cutar 'kanjamau, Amma Zuby tacika babbar muguwa azzaluma.
Zuby Kuma Zama tayi da niyyar jiyyar Sani, sai dai tunda yaji sakamakon da likita yafad'i na Yanada 'kanjamau yasa yaji wani mugun tsanar zuby muddin Yana ganinta gabanshi zai iya rabata da numfashinta saboda haka korata yayi yace taje gida kawai bayason ganinta.
Hankali tashe zuby tafita daga asibitin cikin tsananin rud'ewa batako kallon gabanta tahau titi tana tafiya kamar wata Zararra by mistake kuwa wata mota tayi ciki da ita, Nan take tace ga garinku Nan.
Allah sarki Zuby anrigamu gidan gaskiya, sai muce Allah ya kyauta namu zuwan.
Mmn khady ce 🤼♀
[10/3, 7:00 PM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 45
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
*Kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu hakan yasamu saboda wata Yar 'karamar matsala, bayan haka Kuma zanyi amfani da wannan damar wurin kawo 'karshen wannan labari, Amma kuyi hakuri zan takaita 'karshen labarin saboda wasu 'yan dalilai*
Bayan kwana biyu Sani kwance Kan gadon asibiti Alhmdlh yasamu sauki sosai,
Likitane yashigo d'akin hannunsa d'auke da wasu takardu,bayan sun gaisa da Sani yayimashi ya jiki Sani ya amsa "jiki Alhmdlh Babu abunda ke damuna"
Gyara zaman glass d'in fusakarshi yayi yace "sakamakon gwaje-gwajen damukayi, bayani ganowa damukayi kana d'auke da cutar 'kanjamau, sakamako na biyu Kuma ya nuna bazaka iya 'kara hauhuwa ba sakamakon buguwa dakuma tsananin razana dakayi"
"Me....." Me kake fad'i haka likita, kana nufin yanzu nida Haihuwa har abada"?
"Kwarai kuwa haka sakamakon ya nuna" likitan yafad'a tareda mi'kama Sani takardun sakamakon yafice daga d'akin.
Hankali tashe Sani yabar asibitin 'kafarsa ko takalmi Babu, tafiya yake batareda yasan inda yake saka 'kafarsaba, ikon Allah ne kawai yajaishi gidan Zuby, Yana zuwa ya tarar da mutane dankam 'kofar gidan 'yan zaman makoki, kafin ya isa wurin yaji wani dattijo na fad'in "Allah sarki zubaida anrigamu gidan gaskiya Allah jikanta da rahama" da wannan magan-ganun Sani ya tabbatarba kanshi da mutuwar zuby.
Juyawa yayi yabar wurin batareda yashiga gidanba kokuma yayima wani magana, Babu Kuma Wanda yalura dashi a wurin dukda dama bakowabane ya sanshi.
Shagonsu yanufa wurin Basiru dan yanzu Babu abunda yafi bu'kata sai kud'i, zuwa zaiyi ya 'karbi kud'insa ya tattara yanashi yanashi yaje wurin khairat ya amshi sauran farincikin daya ragemashi a rayuwa wato Khalid yawuce 'kauyensu.
Khairat tana zaune d'akinta cikin kwana biyu duk tabi ta lalace tayi ba'ki, hankalinta yagama tashi,
Ga maganin HIV din data karba asibiti amma batada kwanciyar hankalin dazatasha, dan tunda tadawo daga asibi da maganin da sakamakon gwajin da'akayimata duka tahad'a ta ajiye Kan kujera a falo Tama manta inda ta ajiyesu.
Khalid Yana d'akin Fauziyya wurin su Hanif suna wasa wani Zazzafan zazzabi ya rufeshi har Yana firgita, haniface takira Fauziyya tagwadamata Khalid d'in hankali tashe ta d'aukeshi takaishi d'akin khairat tagayamata bayada lpy, amsarshi kawai khairat tayi ta kwantar dashi dan batada nutsuwar dazata bashi wata kulawa.
Bayan azahar Salim yadawo gida kamar yanda yasaba,
Fauziyya ta gayamashi Khalid fa bayada lafiya Kuma tund'azu nakaishi wurin mamarshi Amma banga tafito takaishi asibiti ba"
'dakin khairat d'in Salim yanufa Dan ganin jikin Khalid d'in.
Yana shiga idonshi ya sauka kan ledar maganin khairat dake kan kujera, har zai wuce saikuma yadawo Yana bud'awa yafara duba magungunan danshi baitaba ganin irinsuba, tunani yafarayi wannan maganin Kuma na miye haka 'kara dubawa yayi ya d'auko takarda Mai d'auke da sunan khairat dakuma sakamakon gwajin HIV tana d'auke dashi.
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafara maimaitawa, da sauri khairat tafito falo Jin yanda Salim ke rafka salati, ganin ledar maganinta gabanshi hannunshi Kuma d'auke da takardar gwajin yasa ta razana tayi hanyar waje.
Da hanzari Salim ya damkota ya wankemata fuska da lafiyayyan mari yace "khairat gayamin gidan ubanwa Kika kwaso wannan cutar?"
Zubewa khairat tayi gabanshi tana kuka, shima Zama yayi kan kujera jikinshi sai 6ari yake.
Wayarshi yafiddo yakira mamarshi yace tazo gida ba lafiya, sannan yakira Hajiya Habi mamar khairat itama yagayamata yanda yagayama mamarshi.
Ba dad'ewa suduka sun halarci taron, Fauziyya mamaki take Wai miye ke faruwa haka taga mamar Salim da mamar khairat sunzo, kodai jikin Khalid ne yayi tsanani, saboda haka itama sashen khairat tanufa Dan taji ko miye.
Ko minti goma dashigowa Fauziyya batayiba Sani yashigo gidan Babu ko sallama yayi wani wurjiga wurjiga kafa ba takalmi, kamar wani Mai tabin hankali.
Yana shigowa kallo yadawo kanshi, shima kallo yabi duka mutanen dake falon sannan yace nagodema Allah Dana iske wannan taron, saboda haka zanyi amafani da wannan damar ingayamaki irin mugun abunda muka d'auki shekara da shekaru muna aikatawa nida khairat.
Nan Sani ya zayyane masu kaf labarinshi tun kafin zuwan khairat gidan har zuwanta har Kuma zuwa lokacinda ake yanzu dayazo amsar d'anshi.
Arazane mamar Salim tace 'kanjamau" innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Salim Babu dai abunda yashiga tsakaninka da ita"
Murmushi takaici Salim yayi yace "Ina kyautata zaton haka"
Mama tace "maza ka rubuta mata takardar saki yanzu kabata sutafi can su karata tsiyarsu"
Bama saina rubutaba khairat kije na sakeki saki ukku, Kuma kije keda Allah.
Kaikuma Sani kaci amanata kaci amanar matata inshaAllah sai kaga sakamako tun aduniya.
Mamar khairat kuka kawai take sai hakuri takeba mamar Salim.
Mama tace Babu wani hakurin dazanyi ki kwashi gayyar tsiyarki kubarmin gidan d'ana.
Sani Kuma kallon khairat yayi yace kafin kitafi inaso kibani d'ana.
Sai lokacin khairat tatuna da halinda tabar Khalid ciki, da sauri tashiga d'akin.
Wata irin razannaniyar 'kara tasaki domin ganin Khalid datayi Babu Alamar rai tare dashi.
Allah yaraba gardama kenan, Khalid yarigamu gidan gaskiya bayada rabon ganin takaicin rayuwa.
Da sauri Haj Habi tanufi d'akin khairat ta iske tanata fizge kayan jikinta tana wata irin dariya, da alama dai ta haukace.
Sani Kuma Nan aka gayamashi Khalid yamutu, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafad'a baijira wani bayaniba yabar gidan.
Kai tsaye sahgon su yanufa Yana zuwa kuwa ya hango dan-dazon mutane anata zuba ruwa shagon yagama 'konewa 'kurmus.
Yana ganin haka bai Ida karasawa shagonba yayi baya yahau titi Yana tafiya tsakiyar titin, wata katuwar mota tazo tabi ta kanshi, Nan take ya margaya, wannan shine karshen masu cin Amana.
*ALHMDLH ANAN NAKAWO 'KARSHEN WANNAN LITTAFIN, SAIKUMA ALLAH YASAKE HADAMU WANI LOKACIN MAMAN KHADY KEMA MASOYA FATAN ALKHAIRI*
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group
WHATSAPP NO:+2349030159301
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13