ya hadiye wani miyau, kamar wani tsohon maye yace Dan wani mugun kyau yaga takara kwana biyun dayayi Bai gantaba, takara fari sai dai Kuma tarame "aunty Ina kwana" "lpy lao" ta amsa batareda tadago ta kalleshiba.
Matsowa yayi kusa da ita yaduka yasa hannu yari'ke tsintsiyar har Yana had'awa da hannunta, yace "haba aunty saboda me zaki wahalar da kanki bazaki Bari inzo in shareba"
Kallonshi Fauziyya tayi, sannan ta sakarmashi tsintsiyar batareda tayi maganaba, aranta Kuma tana yabonshi saboda sani akwai kirki da sanin yakamata.
Cigaba sani yayi da sharar itakuma takoma kitchen Dan hada abun Kari, Yana gamawa yahau wanke-wanke shima ba Bata lokaci yagama saboda bawasu kwanuka bane masu yawa.
Toilet Fauziyya tashiga tashe'ko wanka tafito, yauma kamar kullum wani shu'umin kallo sani yarikayimata wanda batasan yanayiba.
D'aki tawuce tashafa mai da kwalli sannan tasaka wata doguwar riga marar nauyi, tafito tanufi kitchen, tea tahada 2cups taba sani daya ta d'auki daya, tazumabashi doya data soya da kwai tabashi sannan tadauki nata tawuce d'aki.
Kallonta sani yayi azuciyarshi yace " waini Kam miye ke damun aunty, tunda nadawo gidannan nalura Bata cikin nutsuwa, ga wata irin rama datayi, to kodai tasake samun wani cikinne.
Kai beyiyuwa, aiko indai tunanina yazama gaskiya dole nasake d'aukar mataki, muddin Ina numfashi Fauziyya bazata haihu a gidannan ba, Kuma idan na tabbatar da cikine da ita saina zubardashi Koda yakai wata tara.
Wannan mugun tunanin da Sani keyi yasa yaji tea din da doyar duka sunfice aranshi, tashi yayi rai abace yabar gidan batareda sanin Fauziyya ba.
Saida Fauziyya tagama tafito taga sani bayanan, ga Kuma tea da doya yabari, dauka tayi cikeda mamaki takai kitchen tace ko lafiya Sani yabar tea dinanan, Almajiri taji yayi bara takirashi ta juyemashi, yayi godiya yafita Yana murna.
Sani Kuma gindin wata bishiya ya zauna yanata tunani aranshi, tun yanayi azuciyarshi haryafito fili "Fauziyya yazakiyimin haka, yaushe Zaki yarda ki Kuma samun wani cikin tareda Salim, haba Fauziyya, miyasa kikemin haka, nine yakamata ace kinsake d'aukar cikina bana Salim ba"
Wani shu'umin murmushi yayi yace Fauziyya kin tafka babban kuskure, amma zakiji ajikinki, dan wlh wannan karonma sainayi sanadiyyar zubewar wannan tsinannen cikin naki.
Kamar Wanda aka tsikara yatashi, komawa yayi gidan Fauziyya.
*"Kuyi manage da wannan kunsan jikin nawa sai a slow"*
*Mmn khady ce*
Mmn khady ce 😘
*Mmn khady ce* 🥰
[8/31, 8:03 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 18
Kamar Wanda aka tsikara yatashizumbur.
Hanyar gidan Fauziyya yanufa yanata surutai kamar wani mahaukaci sabon kamu, "to wlh bazan taba yarda haka ta kasanceba, ciki....ciki Fauziyya nizakiyima haka, wlh kind'ebo ruwan dafa kanki dan wlh bazanbarki ki haife abinda ke cikinkiba, dole inyo waje dashi tunkafin lokaci yakuremin"...... Haka yayita surutai Yana tafiya baisan inda yake jefa k'afarshiba, bayama kallon gabanshi harya iso gidan.
Saida yazo zaure Yana gaf dashiga gidan yatsaya Yana tunani, "idan nashiga gidan haka tabbass dole Fauziyya ta fahimci Ina cikin wani hali,.... Dafe 'kirjinsa yayi na wasu Yan mintittika, sannan ya dai-daita nutsuwarshi, da sallama yashiga gidan, lokacin Fauziyya na zaune kan kujera tana wanke inners dinta Dana Salim, amsa sallamar tayi tareda juyowa ta kalli sani tayi guntun murmushi tace "Mal Sani kud'ifa sun zaunama da alama"
Shima murmushin yayi yace saboda me kikace haka aunty ?"
"Naga yau bakasha tea ba dasafe, saida nafito naganshi najuyema wani Almajiri"
"Eh wlh aunty banajin yunwane shiyasa"
"Ainasani angayamin anganka teburin Mai shayi anyima hadin kakkaura, da bread da wainar kwai......
Dariya sani yayi sosai, itama Fauziyyar dariyar take, yace "Kai aunty waya gayamaki Ni gaskiya kowaye 'karya yakemin, yoni aunty Fauzy inadake ainafi 'karfin zaman teburin Mai shayi"
"Hmm" Fauziyya tayi murmushinta Wanda yake Kara bayyana kyawunta, Wanda yakara Jan hankalin Sani gareta, jiyake kamar yaje ya rungumeta saboda wani sabon shauk'in soyayyarta daya dira a zuciyarshi.
Shiru yaratsa na kimanin minti biyar, sannan sani yakatsemasu shirun "nikam aunty intamabyeki Mana"
"Ina jinka sani Allah yasa nasani, tafad'a tanacigaba da wankinta batareda ta kalleshiba"
Shiru sani yayi Dan yarasa ta inama zaifara...
Jin yayi shiru yasa Fauziyya juyowa tazubamashi kyawawan idanunta, taga ya Lula wata duniyar yayi nisa cikin tunani,
Ruwan kumfan datake wanki tad'an d'ebo a hannu ta watsamashi afuska, wata razana Sani yayi Wanda yaba Fauziyya dariya,
Dariya take sosai, sani Kuma kallo kawai yabita dashi cikin ranshi tana matukar burgeshi.
"Wai Sani lafiya kuwa Naga kayi nisa cikin tunani kodai kasamu wacce takama zuciyarka ne?
"Sosaima Aunty, wlh wata kyakkyawar yarinyace tatafi da duka imanina, narasa tayanda zan fuskanceta da maganar soyayya.....
"Hhhhhh, wayyo cikina Fauziyya tafad'a tana dafe cikinta "ohni su sani amfada tarkon Love, wannan wace wayrinyace haka, wacce tayima zuciyarka kamun kazar kuku"
"Bakisaniba aunty nadad'e Ina dakon soyayyarta, kusan shekara biyu da wasu wattanni kenan, amma narasa taya zan tunkareta na yad'amata manufata, amma dukda Ina sonta batasan inayiba, hakan bai hanani bibiyar al'amurrantaba, dan duk wani taku nata insane dashi, yanzuma abunda yasa kikaga nafad'a tunani haka wanine yakeson yimin shigar sauri, to narasa ta inda zan bulloma al'amarin, aunty Fauzy kibani shawara mana........
Tunda yafara magana fauziyya ke kallonshi cikeda mamaki, Dan ita wlh cikin wasa tayima Sani wannan maganar Amma taga shi dagaske yake koramata bayani.
Ajiyar Zuciya tayi tace "abunda kawai nakega zaifi shine kadake amatsayinka na namiji ka fidda tsoro ka tunkareta kagayamata sirrin zuciyarka, inaji ajikina zata aminta dakai.
"Ammafa aunty kinsanfa matsayina, niba Kowa bane sai *Almajiri* kinaga zansamu soyayyarta ayanda nake"
"inshaAllah zakasamu zantayaka addu'a" "to shikenan nagode aunty, Amma aunty nikam sainaga kinrame wlh kodai bakida lafiyane?"
"Eh banajin dadi" tabashi amsa atakaice Dan surutunshi yafara isarta sakamakon ciwon mara datafaraji sama-sama.
Kallon Sani tayi tace sani kanada labarin "Salim zaikara aure kuwa?" zaro Ido sani yayi tareda dafe 'kirji Alamar razana yace "Aure Kuma aunty"
"Hmm" kawai tafad'a tad'auki buta tashige toilet Dan ciwon marar yanadan karuwa, tana shiga abunda take zato kuwa shine tagani bakon watanta ne yazo,
D'aki takoma taduba pad batada saura Ashe, rubutawa tayi atakarda sannan tafito taba sani, "Dan Allah sani kaje chemist yanzu kasiyomin wannan"
"To" kawai sani yafad'a yakarba yatafi.
Kai tsaye sani shagon kolo yanufa, yabashi takardar yace "bani wannan maganin" duba takardar kolo yayi yadauko pad din yasaka aleda yamik'ama sani yace kud'in 350 ne, juya ledar sani yashigayi, Dan yaga abun him cikin Leda kamar wani bread, kallon kolo yayi yace wannan Kuma namiye?"
Dariya kolo yayi yace "babyn Bata gayamaba tana period ne, wannan ai audigane na mata" sani bin kolo yayi da kallo danshi yakara tunzurashi a duhu, "miye Kuma period? Sani ya tambaya Kuma miye audigar mata?
Dariya kolo yayi yace "abokina duk yanda kake harka da mata amma bakasan wannan ba" danshi kolo atunaninsa sani wata mace ya ajiye suke sheke ayarsu, saboda haka zama yayi yayima sani bayani dalla-dallah harya gane kome.
Cikeda farin ciki sani yanufi gidan Fauziyya yakaimata part din Dan kolo ya gayamashi idan mace tayi period to batada ciki, idan Kuma wata yazo batayiba to tanada ciki kenan.
Godiya yayima Allah dayasa Fauziyya batada ciki.
***. ***. ***
Bangaren khairat Kuma duk wani shirye-shiryen dazasuyi sundade dagamawa ranar aure kawai suke jira tazo, khairat tadage Shan kayan mata rarumo wannan yayo wancan, duk inda taji wani maganin mata da'akace Yana maida mace kamar budurwa saita siyeshi komin tsadarshi, itadai burinta idan tashiga gidan tazama itace Yar gaban goshin Salim yazama sai abunda tace za'ayi.
Dan tanajin labarin yanda Salim d'in ke mutuwar son Fauziyya itakuma haka yasa talashi takobin shiga tafita, Koda ta kissa da kisisina har saitaga ta maida Fauziyyar Yar bayan goshin Salim ('keya).
Ana saura kwana goma bikin masu aiki sukazo cikin sati daya an canja samfarin gidan, Dan wani karamin gidane Salim yasiya kusadashi yahade danashi kowace akayimata falo da 2 bedroom kowane da toilet aciki, da kitchen, Amma tsakar gidan dayane, sai d'akin Salim din Wanda yakasnnce Yana kallon d'akunan nasu, daga can gefe Kuma kewayen tsakar gidane.
Gidafa yafito Shar gwanin sha'awa, Fauziyya daga gidansu aka kawomata sabbin set din kujeru Dana gado, saboda haka tsohon gadonta saitasashi bedroom dinta gudan,
Guda Kuma tasanya sabon, sai falonta tajera sabbin kujerun kome nata gwanin kyau kamar itace amaryar, tsoffin kujerunta Kuma d'akin salin tajerasu, shima yayi gado medium mai kyau d'akin nashi yatsaru dukda falan dayane, sai toilet dake ciki.
Khairat anyi kamu, Babu ango Dan dama tasan Salim bazaitaba zuwaba, daga ita sai abokanta da alhazanta Wanda suke sheke ayarsune sukayimata Kara sukazo, amma ta kudire aranta ran dinner kobayaso sai yaje, dan tanaso friend dinta suga handsome d'inta, dan susan itamafa babbar yarinyace, dan bakowace mace zata iya samun kalar Salim ba sai mai sa'a.
*Washe gari* ana gobe d'aurin aure akazo akayi jeren khairat, itama Alhmdlh an tsara sashenta kome yaji, bedroom dinta duka ansa gado, falontama yasha royal chairs, abun dai Shar kitchen dinta babuce kawai ba'a sakaba Dan saida ta wanki kud'ad'e wurin alhazanta sosai
tayima kanta hidima.
*My Fan's Happy juma'at*
*Mmn khady ce* 👎🏻
[9/1, 7:17 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 19
*Plz reader's inaso kurika nutsuwa Kuna fahimtar yanda labari yake tafiya, Naga jiya danayi post sai cewa kukeyi dan Allah kada sani yakumayin nasarar zubarma da Fauziyya ciki, to idan Kun fahimci page din bafa ciki nace tanadashiba, shifa sani zargi yake tanada cikin Kuma a karshe ta aikeshi siyen part tana period daganan ya tabbatar da batada ciki sai hankalinshi ya kwanta, Ina fatan kungane*
Su khairat yau ake dinner, sai shirye-shirye aketayi itada kawayenta Kowa kagani cikin nishadi da farinciki Amma Banda amarya dan tarasa wace dabara zatayi wacce Salim zai halarci wannan dinner d'in, shiru tayi na tsawon wani lokaci kafin ta kalli 'kawayenta dake zazzaune zagaye da ita anata hada-hada, tace "Ina zuwa baby's" tafad'a tana barin d'akin.
Wani 'karamin d'aki tashige Wanda ke can gefe guda ba mutane sosai kusadashi, tana shiga ta turo kyauren d'akin, zama tayi kan buhunnan shinkafa dake ajiye cikin d'akin da alama store ne, wayarta ta fiddo number maman Salim takira, ringing biyu ta d'aga takara a kunne tana fadada fara'arta "a'a amarya kinsha 'kamshi ya hidima?"
Ko amsa maganar da mama tayimata khairat batayiba, barantana Kuma tasamu arzikin gaisuwa a wurinta, sai kawai tafashe da kukan 'karya.
A kidime Mama ke tamabayarta "lafiya khairat mike faruwa, ya ana hidima Kowa cikin farinciki ke kina kuka, gayamin wani abu akayimakine, haba 'yata"
Gwalo khairat tayima wayar sannan tacigaba da rera kukan 'karyarta harda sheshsheka,
Hanakalin Mama fa idan yayi dubu yatashi tafara rarrashinta "haba kekuwa 'yata kigayamin Mike damunki, ko Salim dinne yayimaki wani abu, kigayamin wlh yanzu inkirashi incimashi mutunci shida baisan arzikiba ana nunamashi hanya Yana kaucewa, yafiso yabiyema wannan 'kodaddiyar matar tashi juya wacce Bata Haihuwa"
Wani tsalle khairat ta daka dan murna yanda Mama bazata iya ganewaba, a zuciyarta tace anzo wurin.
Sai-saita nutsuwarta tayi sannan tafara magana cikin muryar kuka "mama Salim bayasona inaga kawai 'kara afasa wannan auren....
Wata irin razana Mama tayi tare dafe kirji tace "haba khairat dan Allah kidaina fad'in wannan maganar, meyayi zafi haka Shiba wutaba idanma wani abu Salim d'in yayimaki kigayamin nizanyi maganin abun amma kada inkarajin kinyi maganar fasa aure kinji yata" ta'karashe maganar cikin sigar rarrashi.
"Mama kiduba kiga yau kwana biyar ana program ba Wanda Salim yaje, anyi *Arebian night,* anyi *water melon party* da *'kauyawa* sannan anyi *kwallo*, jiya anyi *kamu* wai dan yau nace yazo wurin dinner shine yayitamin fad'a Wai bazaizoba Kuma idan nasake nakuma kiranshi ko awayane saiya sa'bamin...... Ta 'karashe maganar cikin sheshshekar kuka.
"Yanzu Salim dinne yayi maki haka kibarni dashi, wlh zaya sani, idanma wannan munafukar matar tashice ke hanashi zuwa duka zanje inci mutuncinsu dagashi har ita, Kuma kicigaba da shirinki dinner kamar yajene yagama" godiya khairat tayima mama tareda tsinke wayar tana tsananin farinciki dan tasan tunda tasanya mama cikin wannan maganar dole yau Salim ya halarci dinner din.
Mama tana gama waya da khairat takira wayar Salim ranta amatu'kar bace, ringing daya yad'aga tun kafin yayi magana mama tarufeshi da fad'a ta inda take shiga batanan take fitaba.
"Ka saurareni dakyau Salim wlh kafita a idona inrufe, Nizaka rainama wayo, to kasani dole yau ka halarci dinner d'in, idanba hakaba saina sabama, haka kawai kasa yarinyar mutane cikin damuwa ana tsaka da farinciki, kakirata ka zazzageta Wai bazaka dinner ba, to wlh idan bakajeba Allah ya isa tsakanina dakai"
Tana kaiwa nan ta tsinke Kiran batareda Salim din yayi maganaba,
Dafe kanshi yayi Wanda yafara juyawa saboda maganar da mama tafad'a cikeda mamaki yake nazarin maganganun da mamar tafad'a cikin fad'an nata, kenan khairat tafad'amata 'karya kenan.
Lallai zanyi maganin wannan 'yar iskar yarinyar, badai tadage saitasani abunda banyi niyyaba, hmm zamu had'une wlh saita kwashe kashinta a hannu.
Cikeda bacin rai Salim yadawo gida, tarbarshi Fauziyya tayi cikin fara'a wacce batakai cikiba, dan dauriya kawai takeyi bataso tanunama Salim halinda take ciki, 'kasan zuciyarta kuwa wani mugun kishine ke addabarta.
"A'a'a yanaga kamar ranka abace ango guda, cikin farinciki yakamata aganka haba angon khairat baikamata ace naganka hakaba, gobefa kamar yanzu ....
Wata uwar harara Salim ya watsamata wacce tasa taja bakinta tayi gum.
Wucewa yayi d'akin Fauziyya kaitsaye bedroom yanufa yacire kayanshi dagashi sai boxer yafad'a toilet yasheka wanka, yafito ya zauna bakin gado Yana shafa mai, lokacin Fauziyya tashigo jikinta a sanyaye kamar kazar da kwai yafashemawa aciki, kallonta Salim yayi yace ki shirya anjima zamuje dinner.
Sani Yanada labarin dinner d'in, shima Yana so yaje danya kashe kwarkwatar Ido, sai dai baisan inda akeyiba, saboda haka ya yanke shawarar Kiran Fauziyya ya tambayeta.
Wayarshi ya d'auko daga aljihu number Fauziyya yakira tambayeta inda ake dinner d'in, gayamashi tayi,Yacemata zaije inshaAllah, Nan itama take gayamashi ai zataje.
Fauziyya zataje dinner d'in, Aiko naji dad'i Sani yafad'a Yana murmushi kamar ance zaihadu da uwarshi ta 'kauye, kodayake Koda ita zaihad'u baya wannan murnar dan da alama yamanta da ita.
*liyafa hotel* nanne wurinda aka shirya yin dinner d'in wurin yatsaru matuka decration d'in yayi matu'kar k'ayatuwa, kome na wurin blue ne da golden, mutane ancika ma'kil amarya tadad'e dazuwa zaune take kan kujerar da aka tanada domin itada angonta, sanye take cikin wata arniyar doguwar riga fitted, tayi matukar fitoda surar jikinta, rigar blue ce wacce Tasha ado da fararen flowers, sai faraen takalmi a kafarta masu mugun tsini, hannunta rikeda purse Fara wacce tasha adon duwatsu blue, wayyo yaka hango khairat amaryar salim, kanta kuwa farin head ne,
zare namujiya take tana duban ta inda Salim din zai bullo, wasu hawayene suka Fara cikamata idanu, watako Salim bazaizoba shiyasa ya'ki yarda sutaho tare, itadai ya watsama 'kasa a Ido, hmm zanshiga gidan naka salim sainayi maganinka Salim saika kwashi kashinka a hannu (Tofah khairat keda Salim waye zai Kashi kashinsa a hannu, shiyace ke kekuma kince shi) wlh saina gyarama zama duk wukakancin dakamin saina rama.
Lokacin Sani yashigo hall d'in yasha wata munafukar shadda, tad'au guga kalar ruwan 'kasa hakama takalminsa, hularshima tayi kala da shaddar, sai 'kamshin turarensa ke tashi, wow Sanifa anfaso gari shimafa yazama mutum...
Kujerar gaba yasamu ta gab da amarya ya zauna, khairat yazubama mayun idanunshi "gaskiya kyakkyawa ce, miyasa Salim Koda yaushe yake zabo kyawawa, wannan karonma yazabo wata Mai zafi, Kai kema inayinkifa Mai kyau, inayinki sosai, ammafa ba Sonki nakeba, Ni duk soyayyata nabarma aunty Fauzy.
Kallon khairat yake bayako 'kiftawa, hawaye yaga nabin kumatunta, "to itakuma wannan miye yasakata kuka? Yayima kanshi tambayar dabashida amsarta.
Duka kallon mutanen hall din Yakoma kan wasu taurari guda biyu kokuma ince wata da Zahra, Wanda haskensu ya disashe hasken fitulun dake haske a hall d'in, Salim sanye da shadda maroon colour wacce Tasha aiki da bakin zare, sai bakar hular daya d'ora akanshi, takalmin kafarshima bakine, Fauziyya Kuma Marron d'in less tasanya Mai zanen flowers golden, d'inkin Riga da siket Wanda yayi masifar yimata kyau, kafarta sanye da takalmi golden, head din kantama Golden ne.
Khairat dake zaune hawaye yagama wankmata fuska hangosu tayi suna taku cikin kasaita, hannwansu ma'kale dana juna sunata sakarma junansu wani tsadadden murmushi mi'kewa tayi tsaye tana binsu da kallo zuciyrta na 'kuna
Sani ma mi'kewa yayi yazubama Salim da Fauziyya mayun idanunshi, wani irin kishine ya turni'ke zuciyar sani ganin yanda Salim kewani rungumeta jikinshi, itakuma ganin yanda idon mutane yadawo kansu duk saita daburce santsin tiles ya d'ebeta tatafi luuuu zata fad'i da sauri Salim ya tarbota tafad'a jikinshi, riketa yayi bayada niyyar sakinta fuskarshi na kallon tata Yana sakarmata wani irin tsadadden murmushi, cikin kunar Rai sani yafigi wata kwalbar lemu dake kan teburin gabanshi yanufi inda Salim yake, dagudu itakuma khairat tanufi inda duka switch da wearing din hall d'in yake ta fizge wayoyin wani irin shock da tartsatsin wuta suka tashi, hall d'in yayi tsit Kowa ya du'ke lokacin Kuma akaji 'karar fashewar kwalba tareda fasa wani irin ihu.......
*Mmn khady ce* 💃🏻
[9/4, 7:56 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 21
Fauziyya tunda tagama sallar da asuba batakoma bacci ba, kitchen tashiga ruwan zafi tad'ora tasaka Lipton da kayan kamshi bayan yatafasa ta tace tazuba a samis, sannan ta d'ebo dankali yanda zai ishesu harda Amarya ta fere ta fasa kwai shima yanda zai Isa, bayan tagama soya dankalin tasoya wainar Kwan, sannan tajuye kome cikin kyawawan mazubi, sannan tazubama sani nashi ta ajiye gefe.
Saida tagyara kitchen din tashare tagoge ko'ina tsaf, ta fiddo kwanukan wanke-wanke sannan tashiga toilet tashe'ka wanka tafito tashafa mai, tayi simple make up, wata doguwar rigar atamfa tasaka ja Mai manyan flowers baki, bakaramin kyau kayan yayimata ba.
Salim kuwa tunda yadawo masallaci yashiga d'akinsa yad'an koma bacci na 30minute yayi yatashi yashiga toilet yayi wanka ya shirya cikin milk din shadda, yayi matukar yin kyau, sai kamshin daddan turarensa ketashi ajikinsa.
Sallama Fauziyya tayi tashiga d'akin, amsa sallamar Salim yayi, cikin nutsuwa Fauziyya ta tako tana Shirin zama kusadashi yayi saurin rungumeta ya zaunar da'ita kan cinyarshi, k'amshin turarenta ya ziyarci hancinsa, d'ora kanshi yayi saman kirjinta yayi lamo kamar yaronda yasha kuka aka rarrashesa yayi shiru ya lafe jikin uwarsa.
Itama Fauziyya'kamshin turarensa take sha'ka, cikedajin dad'i wani irin farincikine cikeda zuciyarta, ganin yanda Salim din yanuna yayi missing dinta tsakanin daren jiya zuwa yanzu dasafe,
Magana tafara cikin wata irin sassanyar murya "Hubby katashi lpy?"
"Lpy lao my wife"
Yafad'a Yana Kara jawota jikinshi Yana shafata cikin salon soyayyarshi, "Uhum Hubby dama zuwa nayi Inga idan kunshirya kaida amarya ga breakfast can nahad'amana" hancinsa yakai saitin wuyanta yakara sha'kar 'kamshin turarenta, ya sauke wata ajiyar Zuciya yace "Nashirya my soul, a Ina zamuyi break d'in muje d'akinki ko?"
"A'a Hubby, kada muyi rashin adalci mana, kariga kasan daga jiya har zuwa kwana shidda masu zuwa nan gaba duka ranar khairat ne, sai dai muje d'akinta, kokuma muzo nan d'akinka muduka"
"Ok to kikawo mana anan inaga zaifi"
"To" kawai tafad'a tamike daga kan cinyarshi tanufi kofa, hartakusa fita daga d'akin yari'ko hannunta, juwowa tayi ta kalleshi tasakarmashi wani k'ayataccen murmushi, shima murmushi yayimata can 'kasan ma'koshi yace "I miss you" "miss you too" tafad'a sannan tazare hannunta daga nashi tafita daga d'akin.
Dai dai lokacin Sani yashigo gidan da sallama, amsa sallamar Fauziyya tayi "ah Sani Kaine, Ashe zakazo ai nad'aukama bazakazoba dan naga bakada lpy, ya jikin naka?"
"Da sauki Aunty, ai bawani ciwo bane dayawa kinsan kai da jini koyaya aka tabashi" Yana maganar Yana satar kallonta dan yau wani fitinannen kyau tayimashi, kullum kyawunta Kara fitowa yakeyi, kullum ganinta yake wata sabuwa awurinshi"
Allah sarki Fauziyya batasan tunanin da Sani keyiba akanta, ta gabanshi tawuce, nanma binta yayi da kallo azuciyarshi yace "wow tahad'u.... Tahad'u, gaskiya Ina sonki Fauziyya Kuma inaga lokaci yayi dazan mallakeki, hakurinafa ya'kare,"
Yana cikin wannan tunanin Fauziyya tazo tawuce tagabanshi d'auke da tiren data jeromasu kayan breakfast akai, taku take cikin nutsuwa sautin takalminta Yana bada kwas...kwas kan tiles d'in tsakar gidan, binta da kallon sani yakarayi, wani abu yaji Yana tsirgamsahi tundaga kanshi har zuwa babbar d'an yatsar kafarshali, tabbass yasan yanayima Fauziyya sonda babu wani mahalukin dakemata kalarshi duk duniya.
Juwowa Fauziyya tayi ta kalli Sani, wani mummunan fad'uwar gaba taji dan kamashi datayi Yana kallonta, kallonma irinna maza mayun mata, wani irin fad'uwar gaba taji dan kad'an yahana tasaki tire din kayan dake hannunta.
Dakewa tayi tace "lafiya dai Sani, wannan wane irin kallone kakemin haka kamar yau kafara ganina" kame kame yafarayi dan yashagala da kallonta baisan tazo kusadashiba hartakamashi Yana kallonta, dan ya iya takunshi duk tsawon shekarun dasuka d'auka tare bata taba kamashi da laifi kodayaba cikin tarin laufuffukan dayake aikatawa sai yau.
Sosa 'keya yafarayi kamar tsohon munafiki, "a'a aunty bafa ke nake kalloba, wlh Ina wani tunanin ne daban, banma San kinzo nanba" "ok to ga kayan wanke-wanke can nafiddo saikaje kafarayi ko" tana fad'in haka tayi gaba tabarshi nan tsaye yabi bayanta da kallo Yana lashe busashshen lebensa kamar wani tsohon maye.
Tagama jera kome na breakfast din a d'akin Salim kan carpet din tsakiyar d'akin, saukowa Salim yayi daga kan kujera ya zauna kan carpet din yace "Had'amin nawa sauri nake zanfita wurin aiki Kinga nakusa makara" yafad'a Yana kallon kyakkyawar agogon dake d'aure a hannunshi.
Murmushi Fauziyya tayi tace amma kasan banice keda hakkin hadamaba, koka manta bani d'aya bace agidan yanzu, yakamata kaje kayima khairat din magana tazo muyi breakfast din, saita hadama tunda yanzu duk cikin aikintane"
Da kamar Salim din yaki zuwa Kiran khairat din, Amma saiya tashi kawai yanufi dakin khairat din dan bayaso Fauziyyar ta daukeshi marar adalci,..
Sani Kuma tun shigar Fauziyya d'akin Salim wani munafikin kishi ke d'awainiya dashi, jiyake dayanada hali daya fiddota daga d'akin Salim din, amma hakan bazai yiyuba, cigaba yayi da wanke-wankesa zuciyarshi na Kuna.
Da sallama Salim yashiga d'akin khairat, shiru yaji Bata amsaba, Kai tsaye d'akin dayasan nan takwana yanufa, tura kyauren d'akin yayi yashiga, kwance ya isketa kan gado ta baje tayi dai-dai sai bacci take, duk illahirin surar jikinta bayyane take Dan kayan baccin dake jikinta dasu da babu duk d'aya suke.
Tsayawa yayi bakin 'kofa Yana kallonta, zuciyarshi na rayamata abubuwa daban-daban, wani irin mugun haushin khairat ya dira azuciyarshi, dan daganin yanda khairat ke bacci yasan ko sallar asuba batayiba gashi yanzu har karfe tara saura batada niyyar tashi, wata irin Zuciya takuleshi a harzuke ya isa inda take kwance ya dai-daici cinyarta wacce take yashe yad'aga hannu iya 'karfinshi ya d'ad'a mata wani mugun bugu.
A firgice tatshi zaune kan gadon tafasa Kara tana Kiran "Wayyo Allah Hajiya... ganin Salim gabanta fuska ba annuri yasa tayi saurinsa hannunta tadafe bakinta batareda da karasa abunda zata fadaba, zare idanu tafarayi kamar wacce tayima sarki 'karya.
A kufule Salim yace, nanba gidanku bane dazakiyi yanda kikaga dama, da alama ko sallar asuba bakiyiba kin kwanta kina baccin asara, idan Kinga dama kitashi idan kingama abunda kike Ina jiranki dakina, Kuma banison Bata lokaci minti shabiyar nabaki" yanagama fada yafita yabar d'akin.
Tana ganin yafita tatashi tana Sosa inda ya d'ada' mata bugu a cinya tace "mugu kawai, Kuma wlh saina gyarama zama a gidannan, nan gaba ko cewa akayi kayimin kallon banza bazaka iyaba barantana ka iya daga shegen hannunka kace zaka bugeni.
Toilet tashiga tashe'ko wanka tafito tashafa mai, sannan tazauna gaban mirror tayi wani mahaukacin makeup, wadrope tanufa tadauko wasu matsiyatan Kaya English wears riga da siket, rigar karamace da kyar ta rufe cibiya Hannun rigar net ne, Wanda saika duba sosai zaka gane akwai Hannun Dan sajewa yayi da jikinta, ga wani katon wuya da rigar takedashi Wanda Rabin Brest dinta a waje yake, siket dinma ya matseta sosai, Kuma bai kai har kasaba, amma ya wuce gwiwa.
Yani yalolon mayafi ne tadaura akanta, turarurrukanta masu masifar 'kamshi tafesama jikinta sannan tafito daga d'akin tanufi d'akin Salim din, maganar sallah Kuma Babu ita sai dai Atari ta azahar Kuma.
Sani dake duke Yana share tsakar gidan 'kamshin turaren khairat ya dakarmashi hanci, mi'kewa yayi tsaye yayi yasaki baki da hanci Yana kallonta, ganin yanda Sani ke kallonta yasa takara canja tafiya hartazo tagabanshi tawuce tana juya baya yaga yanda take juya mazaunai Wanda ba wani na kirki kegaretaba amma da tsiya takoyi yanda zasu rika juyawa idan tana tafiya.
"Wowww" sani yafad'a dan khairat tagama tafiya da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13