Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
tsafff sun cimma dubu goma nan aka fitar da Mallam Audu Bayan dawowarsa gida a cikin damuwa da bakin cikim haihuwar Kaltume " akan wanan yaron aka rufe ne a police station don kutumar " ..... kafin ya gama sai ga sallama liman a kofar gida cewa a fito da gawar Kaltume domin a mata wanka da sutura akai ta makwancin ta haka ya kasance Mallam Sambo yayi jagora a inda aka nema Audu aka rasa shi mutane nata tsigume a ƙauye cewar matar sa ta mutu a sanadin sa kuma bai sallar gawar ta ba balle ya Kaita kabarin ta .. 🌾 KAƊANGAREN ƘAUYE Suna: Bashir Ma’ana: Mai bishara, mai kawo haske Halinsa: Jarumi ne mai dogon juriya. Rayuwarsa cike da gwagwarmaya, amma yana da zuciyar son gaskiya da kare talaka. Wanan kinan .. ABUJA Kallon da yayi wa Zulaihah kamar ya fi kisa: “Ina matata?! Ina Maijidda?!” Ummee ta miƙa jariran biyu da hawaye, ta ce: Ta haihu biyu ita kuma ta mutu cikin azaba Minista ya ɗauki numfashi da ɓacin rai — sannan ya juya. Shigowar Zulaihahr cikin dakin ta ta rufe windows nata zuciyar ta sai bugawa yakiye akai akai ta daura hannun ta akan ta "Wayooo Allah na na mutu na lallace nayi kissar sauran ƙirris a kaine gidan Yari na shiga ukku ya zanyi " firgitt ta tashe ta buɗe wardrop nata nan ta zaro wani ƙaramin akwati ta fito da wani abu da aka zagaye da jan ƙyale tashi tsaye taye ta kashe hasken ɗakin gaba daya ta fito da wanan abun tama ɗagawa sama sai ga madubi ya bayyana a cikin sa nan ta ajiye yana kallon kudu ta shaffa da hannun ta guda biyu , akai ta fara wasu sambatu da ba'a ganewa kwatsam sai dakin ta fara girgiza kamar za'ayi ruwan sama " hhhhhhhhhhhhhhh wani murya mai amo da ƙaraji ya ƙauraye ɗakin da wani sautin mara daɗi. sauraro man madubin yayi duhu ita kanta ta tsira matukar gaske nan zufa ta fara kwatanta daga kanta har izuwa tafin kafuffunta ....... "Kinye saki kinye gaggawa kina bachi domin an haifo KAƊANGAREN BAKIN TULU alƙawarin Ubangiji ya cika tabbas bazaki iya komai ba " ya faɗa cikin sarƙaƙiyar Muryar sa mara sa daɗi.. cikin hawaye tana na shiga ukku na lallace me za ayi ka taimake ne banson Yaron nan ya rayu a doron duniya " dariya ya sake ƙyalƙyalewa dashi Yana cewa alƙalamin ya bushe KAƊANGAREN ya fitoo sai dai ita maccen zamu iya kashe ta kafin akaita asibitin Amman wanan yaron bamu isa mu taɓa shi ba " nan ta durgusa taye wani ihu mai bakin ciki yanzu ne za'ayi ka nunamin hanya kaine Ubangiji na .... " Ka duba min kar asiri na ya tuno akaine gidan yari "..Babo wanda zai ye maganar mutuwar ta kowa zai manta da asalin mutuwar ta Amman da sharaɗin cewa dole watarana zamu tambayi ke ladar aikin mu cikin gaggawa tace ta yarda kafin ya saurarre abinda zaice nan ya Kuma da dariya ya ɓace ɓatttt Isowar sa asibiti da yara biyu har na maccen ta mutu nan aka sata a kwali saiga hawaye a idon sa ya share ya ɗaga yaron yana mai cewa " nayi maka suna Rayyan Ubangiji Allah ya kare min kai a gaban ido na da bayan numfashi na Allah ya daukaka darajar ka ya sanya sallama a cikin zuciyar ka da juriya da haƙurin rayuwa da zaka fuskanta ina sonka domin Allah .kuma Allah ya jiƙan mahaifiyar ka RAYYAN 🌆 KAƊANGAREN BIRNI Suna: Rayyan Ma’ana: Kyakkyawa kuma mai albarka Halinsa: Ya taso cikin duhun wulaƙanci da cin zarafin uwar sa, amma ya zama jarumi mai ɗokin kare 'yancin mata da yara. Hankali da ilimi ne makaman sa. Narnah ƙanwar soja ✍️✍️✍️ 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE 7 300 only FREE PAGE 08101235739 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) PAGE 7 ( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕). GARGAƊI Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba , GAISUWA Gaisuwa na musamman ga masoyyiya ta a bar alhafari na sister Habiba Ubangiji na tare dake a dukkanin motsin ke da shirun ke.. SUMMARY 🌾 KAƊANGAREN ƘAUYE Suna: Bashir Ma’ana: Mai bishara, mai kawo haske Halinsa: Jarumi ne mai dogon juriya. Rayuwarsa cike da gwagwarmaya, amma yana da zuciyar son gaskiya da kare talaka. Shine yaron da baban sa yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar sa ta hanyar duka da zuba mata ruwan talken towo sanan aka so a kashe she sai dai Allah ya nufa sai yazo duniya . Shin ya rayuwar Bashir zai kasance a wanan ƙauyen da uƙubar cikin gidan su? 🌊 KAƊANGAREN TSIBIRI Suna: Suhayl Ma’ana: Tauraro mai haske daga cikin duhu Halinsa: Rayuwarsa cike da asiri da wahala. An haife shi a bakin kogi, mahaifiyarsa ta faɗa ruwa bayan an harbe ta. Zai zama ɗan jarida mai zamewa murya ga marasa murya, kuma zai tunkari masarauta da kalmar gaskiya. 🌆 KAƊANGAREN BIRNI Suna: Rayyan Ma’ana: Kyakkyawa kuma mai albarka Halinsa: Ya taso cikin duhun wulaƙanci da cin zarafin uwar sa, amma ya zama jarumi mai ɗokin kare 'yancin mata da yara. Hankali da ilimi ne makaman sa. Ya rayuwar sa zata kasance a cikin gidan da Hajiya Zulaihah take zuba capacity? Wanan ba dogon tunani ko nazari bane labarin ne na jarumai guda ukku wanda akaso a hallaka tun suna cikin mahaifiyar su sai dai sun zama KAƊANGAREN BAKIN TULU a barsu su lallata ruwan ciki . a kore su a fasa tulu ko biyo ne ku chigaba da kasance wa da wanan ƙaramar marubuchiyar domin shiga cikin sabon chakwakiya da tunani mai zurfin gaske Amman wanan tafiya ta sauya salon domin wanan littafin anan zai dakata sai wanda suka biya 300 su ne zasu chigaba da samun update akan update ta private nasu . shin ka shirya ? ko kin shirya shiga cikin asalin labarin 08101235739 kai tsaye a wanan number amin magana ina godiya mai tarin yawa *Littattafan da Narnah Kanwar Soja ta rubuta:* *✓ An kammala su:* 1. *Duhu Cikin Haske* *Labari mai taɓa zuciya kan soyayya, iyali, da dangantaka.* 2. *Bayan Wata* *Tarihin abokai da suka fuskanci ƙalubale a wata tafiya mai cike da ƙarfi da bege.* 3. *Farashin So* *Gajeren labari na soyayya, ɓacin rai, da raɗaɗin zuciya.* 4. *Mijin Mage* *Labarin soyayya da rikice-rikicen iyali wanda ke jan hankalin mai karatu.* 5. *Rayuwar Ummah* *Labari mai taƙaitaccen bayani kan sadaukarwa, iyali, da juriyar rayuwa.* 6. *Biyayya Ga Uwa* *Gaskiyar labari mai haɗa farin ciki, baƙin ciki, soyayya, tausayi, da haƙuri.* 7. *Ruhi Biyu* *(Labarin da ya kasance a matsayin ban tsoro da fargabar ruhi ?)* 8. * Hanyar Ruwa* ( Fyaɗe da cin zarafin yara mata ) 9* Ahlin Laashkar* (, Hargitsin sarauta da jarumta na yara mata ). 10* Princess Rahilat * ( Adventure story da ya shiga gidan masarautar na gargajiya salon mulki da bajinta ). 11* MAI CIKI CE ,* ( Nishaɗi salo na musamman ma masoya tare da rikicin masu rikicin) 12* Zaɓin zuciya* ( Soyayya, tausayi , mai karya zuciya ). 13 * Madobin ido * ( Just romance and drama , ga masu lesbian da kwaɗayin duniya). 14* KAƊANGAREN BAKIN TULU* ( Labari na musamman wanda aka fara shi yanzu ). 08101235739 NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️ 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE 8 300 only 08101235739 KANO (ƘAUYEN RIMI) BAYAN WANI LOKACI ...Suratul Mulk... Bashir na durƙushe gefen rijiya, hannunsa cikin ruwa, yana wanke kayayyaki. Muryarsa ta mamaye sararin ƙauyen, yana maimaita ayoyin Suratul Mulk da nutsuwa irin wadda take saka zuciya ta lafa. A hankali kukan saƙa ya shiga cikin karatun—ba kuka na rauni ba, kuka ne na wanda ya haɗiye damuwa da fata ɗaya: samun rahamar Ubangiji. Kamar wanda aka ɗora masa nauyin duniya, bai ma ji motsin da ke bayan sa ba har sai da wata murya mai cike da ƙiyayya ta katse shi: > “Wai kai! Wani irin mahaukacin yaro ne? Wawa ɗan iska! Mu za ka ishe mu da shegen muryarka? Ina bacci kana damuna da karatu? Wa zaka gaya wa cewa kai mai karatu ne?” Ba tare da ta tsaya ba, sai ta bugo shi da dundun a baya. Bashir ya saba da duka tun yana ƙarami—mai zafi da mara zafi—don haka ya ce cikin ladabi: “Yi haƙuri, Baaba. Ban sani ba kina bacci.” Bai ɗaga kansa ba, ya ci gaba da karatu a hankali. Amma sai warash!—sandarta ta sauka a bayansa. “Don uwarka na hakanaka karatun ne zaka yi?!” Zafin ya ratsa jikinsa ya kai har kwakwalwarsa. A wannan lokacin ya ɗago, idanuwansa jajjir, amma kyawunsu ya fi duka fuskar sa. Idanunsa farare, tamkar an hura haske a cikinsu, sai ƙasan idanun da yake baƙi kamar an zana masa kwalliya da ƙyalli. Baaba ta ce da tsaki “Shegen idonka nan da kake kallo na dashi... wata rana sai na zubar maka dasu.” Bashir ya yi murmushi kaɗan—murmushin da ke da ɗan ɗaci. Duk da rashin ƙiba, yana da wani ƙefin da baya iya ɓoye. Abin mamaki, duk lokacin da Baaba ta kalli idanunsa, sai ta kawar da nata cikin hanzari, kamar tana gudun wani abu da take ji a zuciya. “Allah, ka ba ni mafita,” Bashir ya furta a ransa, yana ɗaure kayan mata da yake wankewa. A nan ne Inna Uwaliya ta fito daga ɗaki, tana tura baki, duk haƙoranta sun zube. Tana riƙe da sanda a hannunta tana mai magana da muryar da take cike da hukunci: “Bashir! Bashir!! Bashir!!!”Da sauri ya amsa, cikin ladabi “Na’am, Inna, gani nan zuwa.” yana rarrafe ya durƙusa a gabanta “Gani, Inna. Kina da wani aiki ne?” kamar wanda ke tsoron kallonta, ya tsaya shiru yana sauraren abin da zata ce a dai dai lokacin da ya gama tambayarta, "Ko kina da wani aiki ne da zan yi miki?" Ta kalle shi da wani irin murmushi mara annuri, sannan ta ce: "Ka tafi bakin rafi ka gama wankinka. Kuma daga yau na sa maka doka — kar ka ƙara mana wanki a gida duk abin da ka ke yi, ka yi shi a bakin rafi." Kalmomin sun zame masa ƙamshi mai ɗaci. bai iya cewa uffan ba, ya kama hanyar fita sai hawaye suka fara taruwa a idanunsa, zuciyarsa na cike da wani nauyi da shi kaɗai ya san yawan sa. Maganganunta sun buga masa zuciya kamar wuka. Kafin ya samu damar cewa komai, ta juya ta bar shi, ta bar masa ƙura da ƙuncin rai. Ya tattara rigunan da ya gama wanke, ya ajiye a gefe, ya kama hanyar bakin rafi. Kowane mataki da yake ɗauka yana jin zuciyarsa na nauyi. Ya kwashe kayan kafarsa, ya ɗora a kafaɗa. Hanya mai nisa, mai sanyi amma a gare shi ta zama hanyar azaba. Yana tafiya yana sheshsheƙar kuka, yana maimaita a ransa: "Wai Mama na... me yasa kika mutu kika bar ni? ne yasa kika tafi kika bar ni cikin wannan duniya babu wanda zai rufa min asiri?" A cikin wannan tafiya, kowace ƙafa da ya ɗaga kamar ta ɗauke wani ɓangare na ƙarfinsa, amma zuciyarsa tana ƙara nutsewa cikin wani daki mai duhu — dakin rashin uwa. Hawayen ba su jira ya isa wurin rafi ba — suka gangaro daga idanunsa cikin sauƙi, suka haɗu da ƙura a fuskarsa ya zauna a bakin rafi, yana jin ƙarar ruwan da yake gudu tamkar yana yi masa waƙar baƙin ciki. Sai ya furta cikin murya mai rauni, wadda da kyar za a ji: "Wai Mama na… me yasa kika mutu kika bar ni? Waye yanzu zai rike ni kamar yadda zaki rigi ne ?Waye zai yi min dariya idan nayi kuskure? Mama… yaushe zan sake ganinki?" Kamar wani yaro ƙanana da aka tsinci a cikin duniyar da babu tausayawa, ya runtse idonsa yana jin sanyi na ruwan rafi a hannunsa, amma zafin rashi a zuciyarsa ya fi kowanne sanyi ƙonewa. A haka ya ci gaba da tafiya, zuciyarsa cike da raɗaɗin zafin rashin uwa, hawaye na zubo masa kamar ruwan sama. Kamar dai duniyar gaba ɗaya ta ɗauke masa ƙauna ta maye gurbin ta da shiru da kunci. Kwatsam, ba tare da ya lura ba, ƙafarsa ta bugu da wani abu — ashe ƙafar mutum ce! A cikin ɗan kankanin lokaci jikinsa ya yi sanyi, ƙafafunsa suka yi laushi kamar za su saki, ya fara faɗuwa ƙasa a hankali, “laauuuu…” Kafin ya kai ƙasa, sai kawai ya ji an ɗan tsinke iska a bayan sa — wifff! — wata hannu ta kama rigarsa ta baya da ƙarfin da bai zata ba. Kamun ya tsaya masa tamkar an dasa shi a wurin, zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya tsaya cak, idonsa ya lumshe, zuciyarsa ta fara tunanin ko wannan shi ne farkon wani sabon labari… ko kuma wata sabuwar ƙaddara. ***************************** ABUJA Fitsari ne ya kuɓuce masa ba tare da ya ankara ba, sai ka ji zulllll yana zuba a ƙasa, yana ƙara tsananta kunya da raunin da ke cike da zuciyarsa. Kafin ya iya share hawayen da suka gangaro masa, wata jabbar bulala ta tsinke a bayansa, ta shigar masa da zafi mai tsanani har sai da ya yi wani irin tsalle ya sulale ƙasa kamar ruwan kankara da aka zuba wa wuta. A can ƙasa yake kwance yana rawar zafi, hawaye suna cika idonsa, yana kallon sama da idanu masu taɓarɓarewa. Wannan yaron — kyakkyawan yaro ne, fari sol kamar hasken alfijir, fuska mai santsi wadda da ta dace ta kasance cikin farin ciki da kulawar uwa. amma yau, babu mai rungumar shi, babu mai share masa hawaye — sai duka da zagi da zafi. Hawaye suka ci gaba da zuba kamar ruwan damina, zuciyarsa na amsa masa tambaya ɗaya: “Wai Mama na… me yasa kika mutu kika bar ni a cikin wannan rayuwa…?” Fitsari ne ya kwance masa bai sani ba, sai zulllll… fitsari yana tsalle kwaɗo kamar ruwan sama daga bututun da ya fashe. Kafin ya ankara, wani jabgiggin bulalla ta tsula masa a baya — ƙarar ta cika kunne, jininta ya cunkushe, ƙashin bayansa ya amsa. A zabure ya runtse idanu, ya furzar da numfashi mai zafi, amma kafin ya sami damar tsayawa, gwiwowinsa suka yi rauni suka sulale ƙasa. Rayyan kyakkyawan yaro ne fari sol, fuskarsa tana da ɗan zagaye da ke sa idanunsa su fito fili, manya kuma masu sheƙin ƙwalla. Hawaye suka haɗu da zufa a kumatunsa, suna bin fuskarsa kamar zaren lu’ulu’u. Bakin sa ya ɗan buɗe yana neman iska, amma muryarsa ta kulle cikin kirji, sai kawai jijiyoyin wuyansa suka fito saboda tsananin zafin bulallar da ta ratsa har ƙirjinsa. BORNO 🌙 Suhyayl A tsakiyar dajin Borno, a bakin wani babban kogi mai kaurin iska da hayaniyar tsuntsaye, can nesa daga birnin da jama’a ke cike, akwai wani ƙaramar tsibiri. Tsibiri ce da namun daji ke yawo, kuma baƙon dan adam idan ya shigo, sai ya fuskanci ko dai rahama ko hallaka. A gefen wani dutse mai kaifi, yaro ne ke durƙushe — ba wanda ya isa ya ga fuskar sa ya manta da ita. Fatar jikinsa ta launin chocolate mai sheƙi, idanunsa manya, suna kaɗaɗe da hawaye amma yanayin fuskarsa ya nuna tamkar mai ɗauke da shekaru na wahala. A gabansa tsohuwa ce ta kwanta tana shirin barin duniya, hannunta yana rawar sanyi. Sai ta ce da shi cikin muryar da take dushewa: "Suhyayl... anan ne mahaifiyarka ta zo ta haife ka. Ka sani, yanzu zan bar ka, amma ka ɗauki wannan zobe... Zoben mahaifiyarka ne. Idan ka shiga birni, ka zama ɗan jarida mai gaskiya. Wannan ce wasiyyata… ka rayu da kalmar shahada." Kafin ya iya cewa komai, numfashinta ya tsaya. Suhyayl ya kalli gawar, hawaye na zubo masa tamkar ruwan sama. Ya rik'e hannunta yana girgiza shi: "Waiyooo Mama na! Me yasa aka kashe ki, ban mutu ba? Ina zan tafi yanzu?" Kukan ya ratsa dajin, ya sa tsuntsaye suka tashi. sai zuciyarsa ta lulluɓe da tausayin wannan ƙaramin yaro mai asalin gaskiya amma rayuwa ta fara gwada shi tun yana ɗan ƙarami. Narnah ƙanwar soja ✍️✍️ 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE 9 300 only 08101235739 KANO – ƘAUYEN RIMI Bashir ya tsaya cak kamar mutum da aka zuba a cikin hoda. Idonsa ya rufe na ‘yan daƙiƙu, zuciyarsa ta buga da sauri kamar ta ji wani sabon saƙo daga sama. A zuciyarsa yana tambayar kansa, "Shin wannan ne farkon wani sabon labari? Ko wata sabuwar ƙaddara ce da zata canja rayuwata?" Kafin ma ya gama wannan tunanin, sai ga Haule — yarinyar da kowa a ƙauyen ya sani da halin tsiya — ta tintsire da dariyar mugunta, tana riƙe ciki kamar mai jin daɗin cin nasara. “Kai! Allah ya kama ka,” ta furta da murya mai ɗauke da jin daɗi. A gefensa, ƙawayen Haule suka zagaye shi kamar ‘yan kallo a wasa, suka zura masa ido suna jiran ganin abin da zai faru. Amma kafin su kai ga wani abu, sai Noor ta taso daga bayan su kamar iska, ta riƙe Hannun Bashir da ƙarfi tana janye shi baya, tana kare shi daga zagayen Haule. Numfashi ya ja dogo, yana mai jin ƙamshin turaren wankan sabulu daga jikin Noor — abin da ya sa zuciyarsa ta buga karo na biyu. Haule kuwa ta harare Noor, idonta cike da fushi da ƙyashi. “Wai ke Noor, ina ruwanki? Ai wannan ɗan uwana ne, . Ki daina shishigi cikin lamarin gida, kin ji ko?” Noor ta tsaya tana kallon Haule, ta na shiru amma idonta na nuna ba zata ja da baya ba. Sai Haule ta ja zanin rigarta da ƙarfi kamar zata kama yaƙi. Amma kafin ta isa kusa, Bashir ya ja hannun Noor a hankali yana nuna mata ta yi shiru. A zuciyar Haule kuwa, ba ta buƙatar jin wani hujja. Ta yi ƙaramar tsalle, ta koma cikin ƙawayenta tana ƙwala musu kira, “Ku tashi mu tafi! Wallahi sai na gaya wa Baaba yau. Zan faɗa masa duk abinda na gani. Sai yaga irin ‘yar banzar da kuke yi a hanya!” Suka tafi suna gudu, suna shewa kamar ‘yan tsuntsu masu cin abinci, suna ɗaga ƙafafunsu da ƙura ke tashi. Bashir ya tsaya yana kallon bayan su har suka ɓace a ƙofar rafi. Ya girgiza kai da ƙaramin murmushi mai ɗauke da takaici. Noor kuwa ta turo baki kamar wacce aka ci amanarta. “Ai ka kyale ta ne kawai, ka san halinta fa? Gobe sai ta je ta ƙara daɗa labari har ta mayar ka ka ci amanar gidan ku.” Bashir ya yi dariyar ƙasa-ƙasa, yana kallonta da ido mai cike da annuri. “To Noor, me kike so in yi? In yi mata dukan tsiya a gaban ƙauyen?” Noor ta murɗa zanin rigarta tana hararar sa. “Eh, ai da ka yi mata raddi ne ko ka ja mata kunne. Ba ta da kyau ka bar ta ta raina ka haka don kawai tana ƙamwar ka kuma ɗiyar Baaba.” “Kin dai san Haule,” ya ce yana ja da baya, “idan ka yi mata raddi, gobe sai ta kawo maka gaba ɗaya ƙungiyar ‘yan ƙauye.” Noor ta yi dariyar ƙasa-ƙasa itama, tana jin wani abu mai daɗi a zuciyarta — domin da alama Bashir ya fi damuwa da haɗa kai da ita fiye da komai. WANI LOKACIN Bakin Rafin Ƙauyen Rimi Iskar safiya tana kadawa a hankali, tana ɗauke da ƙamshin ruwan rafi da aka haɗa da wari na sabulun wanki. Rana ta fara hango ƙasa, ta haska ruwa mai sheƙi kamar gwal da aka jika. Bashir yana tafiya a hankali, yana rike da ƙaramin bokitin kayan wanki, kafafunsa suna tsoma a ƙasa mai laushi. Idonsa ya yi nauyi da tunanin yau ma an ɗora masa aiki kamar kullum. Sai kawai ya ji muryar Noor daga bayan sa, mai taushi kamar sanyi a zuciya. “Ka tsaya ka jira ni mana.” Ya waiwaya. Noor ce ke tahowa, tana riƙe da zanin jikinta da hannunta guda, ɗayan kuma ɗauke da ƙaramin kasko da aka cika da kayan wanki. A fuskarta akwai murmushin rarrashi, kamar ta san zuciyarsa na cike da kunci. Bashir ya tsaya yana jiranta. Suna haduwa, sai ta ɗan yi masa dariya. “Bashir, ka sake, ai wankan ba laifi bane. Idan kana tare da ni, sai ya zama kamar wasa.” Ya kasa ɗaga ido sosai, amma a zuciyarsa ya san gaskiya take. Duk da cewa shekaru kaɗan gare shi, akwai wani irin natsuwa da yake samu idan Noor tana kusa da shi — kamar iska mai sanyi bayan ruwan sama. Suka isa bakin rafi. Ruwa yana kadawa a hankali, yana tafka ƙaramin amo da ke haɗuwa da ƙarar tsuntsaye masu shela a kan bishiyoyin kusa. Noor ta zauna kan wani dutsen da ya yi fadi, ta saka hannayenta cikin ruwa, tana ji kamar tana wanke damuwar zuciyarta ma. Ta fara zuba kayan cikin

Chapter 3 of 11