Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC YouTube channel domin samun littattafai na Hausa don't forget please like and subscribe , Thank you. https://youtu.be/6-Jrkc2kmmE FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI 08101235739 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE ONE Ƙarar ruwan sama ya ƙara karfi. Gajimare sun cika sararin gidan, kamar sama na kukan wata muguwar saƙo da duniya ta ƙi karɓa ana iya jin ƙaramin igiyar ruwan da ke gangarowa ta sama — amma abin da yafi damun mutum ba ruwan sama bane — azaba ce, da kuma ɓacin rai da ake sakawa a matsayin “tarbiyya.” KALTUME ta durƙusa gindin murhu, hannu na famar busa wuta, idanunta cike da hawayen da basu da alaƙa da ƙanshin hayaki. Ita da kanta ba ta san me ya fi nauyi ba: yunwar da ke jikinta ko ciwon zuciyar da ke cike da ƙiyayya busa wutar takiye bakin ta da hannun ta iya ƙarfin da Allah ya bata ganin lokacin dawowar Malam ya kawo kai ga talken towo akan wuta ga rashin isasshen wutar . Ƙara hura iskar bakinta taye akasar murhur a banza, kanta ta ƙara ɗagowa sama, ganin gagarumin haɗarin yana ƙara haɓɓaka. Take hawaye suka malallo kan kyakkyawar fuskar nata, ƙara durƙusawa taye da gaske, ganin ta ƙara himma gun zuga wutar ittacen, ko zai kammala kafin Mallam Audu ya dawo daga gona... Dariya da shewa daga bayanta, a hankali Kaltume ta juyo tana ganin Baaba dake tsaye da buta zuwa bayingida ( toilet ) ta ƙara da cewa, "Ye dai mugani, ko tusa zai hura wuta?" Ta shiga ƙaramin bayangida dake maƙale a barandar da ake kewo akuya — ko nace akuyoyyin gidan. Kaltume ba ta tsaya binta da kallo ba, ta ci gaba da duba wutar girken ta, har lokacin da Baaba ta fito tana ɗaga butar sama da niyyar ta watsa mata ruwa a murhur da take famar ganin yana aiki. Aikuwa, taye nasarar, zuba mata ruwan taye ya watse akan ittacen. Kaltume ba ta san lokacin da ta runtuma ihu mai kama da kuka ba, ganin wutar ta mutu murguz, kamar ba ta ye wahalar awwani a ƙasar ittacen ba kafin ta buɗe baki taye magana, sai ga ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya nan da nan. Hawayen da ruwan suka mamaye fuskar ta cikin azaba. Ta fara ƙoƙarin mikewa daga durgushen, sai dai kash guiwarta bai amince ba, sakamakon wane azaba da ƙafar take mata tumbin nata ta ƙara himma gun tashi, ga talken masarar yana huce, gaba ɗaya ruwan sama ya shigi ciki, ya zama kunu sai zubewa yakiye inda Baaba ta barta tana dariyar mugunta. Ba zato ko tsammani Kaltume ta tsinci kanta a mugun yanayi, ihu kawai ta yi, tana neman taimako "Har yanzu bakiye hankali ba! Ashe mahaukaciyar! Ina ce ke abincin nawa ke zuba a ƙasa? Wawiya karuwar banza!" Yana duka, yana ihu da surutu a ihun neman ceto, duk suka fito daga dakunan su ba wanda ya je balle ya karɓe ta daga azabtar da yake mata. "Kaltume, nasha wahalar noma, na kawo abinci ki ci! kiye kashi shine za ki min asarar tukunya gida!"yar da sandar hannunsa yayi, ya ɗauko tukunyar, ya kwara mata a jikin ta. Inda taye sauri kifewa domin ta kare cikin ta daga azabar wuta, duk da cewa ruwan sama yasa ya huce, amma har yanzu akai bala’e zafi wanda yayi sillar tarwatsewar dukkan jiyoyin jikinta. Ihu ta buga don wani bakin azabar da ya shiga sassan jikinta... Kamar yadda zai dinga karɓan tuwo daga tulu, haka ya ɗauki sanda ya dinga zuba mata da sukar magana "Wawiya! Ashe ke har yanzu baki yi hankali ba! Abinci nawa kike zubarwa wai ke wacce irin sakaryar ce mata hankali da gumi na kike wasa don ubanki ?" Inna ce ta ga abun ya wuce misali, ganin azaba da wuta, da sauri ta baro nata guntun ɗakin taɓon ta iso tana faman janye sa da cewa: "Kai Audu, zakaye kisan kai! Shikkinan ka kashe ta!" Ganin lallai Kaltume bata numfashi sai yanzu ya lura da mugun ɓarna da yakiye, ganin fatar jikinta na suɓukewa daga ruɓaɓɓon kayan ta... "Ke Ma’u tahu nan!" ta faɗi tana kallon Baaba da take zabga murmushinta hankali kwance. "Allah yasa shegiyar ta mutu na huta da ganin baƙinciki." Wutar murhun da ya dade yana so ya hura ya hana fitowa daga hanyar jikin sa. Kaltume ba ta da iko — jikinta ya saki. Amma zuciyarta tana kuka, tana kuka da Allah... "Ka bar ɗana ya rayu kayi masa jagora... ka sa kada ya zama kamar ni wallahi bada niyya na aikata ba ." zuba mata ido a makance ihu ta buga " Nashiga Ukku uwata na tuba Allah ka gafarta min , cikin ihun azaba ta yanke. numfashi rayuwa ta ɗauke babu kukan da ya isa ya hana mutuwa. Babu idon da ya isa ya ɗaga murya kowa shiru Sai ihu. Ihu daga ciki... ihu daga sabuwar rai da ke ƙoƙarin shigowa duniya...Kai Audu, kamata muyi ɗaki da ita, suna ƙoƙarin ɗaukar ta, sai ga kan jariri na ƙoƙarin fitowa daga cikin mahaifiyar sa da sauri suka ƙarasa da ita ciki. Duk sun yi cirko-cirko suna ganin haihuwar Kaltume da bata numfashi, amma ga yunkurin haihuwa. Tun suna ƙoƙarin tayar da ita, amma Kaltume rai yayi halin sa ba alamar numfashi a jikin ta. Inna ce ta fita zuwa maƙobtan su har ruwan sama ya ɗauke, ba alamar fitowar yaro ga kai ya maƙale. Ganin ba kowa a ɗakin, Baaba ta juya gabas da yamma, hannu tasa ta tura kan yaro da ƙarfin tsiya masifa don ya kuma cikin mahaifiyar sa dake kwance a matsayin gawa mai tururren wutar talken tuwo... Cikin hanzari, Inna ta shigo da maƙobtan su ihu Sallame ta tsala: "Kaltume ta mutu, waiyoo! Allah na mutu, na lallace, shikkinan sun kashe ta, sun yi kisan kai!" Haka ta fita bakin zauren gidan tana tsalalla ihu da wanda suka hallara da masu hallara abin da ya ɗaurewa Inna kai. Ganin yaron ya kuma ciki da kallon tuhuma, ta nufi Baaba da sauri ta antayo idon ta waje: "Na rantse miki Inna, ban yi komai ba. Asali ma na fita don ina tsoron gawa..." Inna ce ta fito daga sunkuye tana hango tillon ɗanta Audu da ya zabga uban tugumi cikin tsoro da fargabar abin da zai iya faruwa a gaba. Da sauri ya matso kusa da Inna: "Ina fatan bata mutu ba..." Cikin murya mai amo da ƙaraji daga bayan sa: Is just a beginning gaisuwa ta musamman ga Sister Ummi Nagode sosai Allah ya saka da alheri Allah ya biya da gidan Aljanna , Allah ya sauke ke lafiya , HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. Ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya...** Itta baiwa daga Allah ce, Ubangiji ke bada itta ga wanda ya so. Duk wanda aka ba wa itta, sai ya sarrafa ta yadda ya ƙi so: wani ta jawo masa arziki, wani kuma ta janyo masa ɗaukaka da masoya masu girma da daraja... PAGE 1 Paid book 300 only , posting daga Monday zuwa Friday in Sha Allah 08101235739 FREE PAGE NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️ https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC?mode=ac_t YouTube channel domin samun littattafai na Hausa don't forget please like and subscribe , Thank you. https://youtu.be/6-Jrkc2kmmE FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI 08101235739 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE 2 “You are under arrest, Audu Dogoro!” Juyowa yayi a tsoraci, jin yaren Turawa ta ki hanjin cikin sa suka murɗa, zubewa yayi a ƙasan. Ɗan sandan yafara bigima da rantse-rantse... Cikin firgici da tashin hankali wasu ƙoƴaƴyun 'yan sanda suka shigo gidan, sun zo bisa kiran gaggawa da maƙwabcin su Mallam Sambo ya yi, wanda tun farko yake leƙen halin da ake ciki daga katagangarsa Ganin halin da Kaltume ke ciki da kuma faɗuwar jikin Mallam Audu a kasa yana birgima cikin ruwa da ƙasa yasa ɗayan 'yan sandan ya ɗaga murya cikin ƙarfi: “Nobody moves! kai, Malam Audu Dogaro, ka tashi mu tafi!” Audu, cikin fargaba da rawar baki, ya fara birgima yana cewa: “Don Allah malam 'dan sanda kuyi hakuri! Wallahi ba ni na kashe ta ba! Allah na sani, wallahi ba da gangan ba! Tukunyar ce kawai ta zube... ni dai ban kashe ta ba!” Cikin ƙarya da ruɗu ya fara zubo rantsuwa, yana yunƙurin kare kansa daga halin da ya jefa kansa ciki. Ya koma yana yi wa kansa kuka, yana nannade hannayensa yana roƙon gafara. Maƙobtan sun cika harabar gidan, wasu suna hawaye, wasu suna siffanta ta da kalmomin alhini. Mallam Sambo kuwa ya kura masa ido yana huci kamar wuta , anan wasu ke furta mugayen abubuwan da yake wa Kaltume “Wannan fa ba da wasa bane,” inji ɗaya daga cikin 'yan sandan cikin takaici. “A jikin mace da ciki kayi haka? Wannan fa laifi ne mai girma, kisan kai da yunkurin kashe jariri!” Baaba kuwa tana gefe, tana ƙoƙarin ɓoye dariyar mugunta a fuska. Amma Inna ta kura mata ido tana tafe da gumi, tana ayyana yanda komai zai ƙare. Sai kawai aka ɗaure Mallam Audu da ankwa, aka ja shi zuwa motar 'yan sanda cikin sarkakiya. Mutane na zagin sa, wasu kuma suna kallon shi da tausayi, amma da yawa daga cikin su sun fi yarda cewa akwai wani abu a ciki – ba rashin sa'a kawai ba ne. Baaba ta tsaya cak! Idanunta sun kafeshi ana ja da shi cikin ankwa, zuciyarta na huci kamar wuta da aka watsawa fetur. “Wayyo Audu! Audu na! Me kuka masa?! Wannan ba gaskiya bane wallahi! Ba zai iya kashe mace ba! Wayyo duniya ta bani!” Ta kwalla ƙara, ta zube a ƙasa ta dafe kai, numfashinta na hauhawa. Idanunta suka cika da hawaye, amma zuciyarta cike take da rudani da wata irin firgici da ba ta taɓa ji ba. Cikin wannan rikicin, sai kawai Inna ta rikice. Ta lumshe ido, jikin ta ya yi sanyi kamar daskararre. “Subhanallah!” Ta faɗi a ƙasa tamkar sanda aka sare itace. Kamar ba rai a jikinta. Hankalin kowa ya tashi! Maƙobtan suka nufo da gudu. “Ku kawo ruwa! Ku ɗaga kafafunta!” “Ina mai zare mata mayafi? Tana numfashi?” Wani dattijo ya sa hannu a ƙirjinta yana duba bugun zuciyarta. “Alhamdulillah tana numfashi... amma zuciyarta na bugawa kamar ana kara mata wuta.” Wasu suka ce a kaita asibiti, wasu kuma suka tsaya suna ambato. Maƙobtan sun firgita, gidansu Audu ya koma gidan tashin hankali. Yara suna kuka, mata suna salati, maza kuma sun rude. Wani dattijo daga cikin su ya tsaya yana kallon su yana girgiza kai: “Wannan fa ba ƙaramin al’amari bane. Gidan nan ya haukace. Wannan ba ƙaramin sharrin aure bane , ina gawar Kaltume a Kaita asibitin ƙauye ko za'a samu damar ceton yaron cikin ta cewar wani ɗam cooper ” Kamar hadari su Inna da Baaba suka runtuma da ƙafa suna bin Malam Sambo da wanan cooper min , sai maƙobta su ka biyo su da hawaye da addu’a. Har wasu daga cikin matan ƙauyen suka ɗauki jariran su, suna kuka da sambatu. Asibitin ƙauyen—wani tsohon gini ne da GOVNATI ta manta da shi. Bangon sa ya faɗi gefe, ɗakin haihuwa kuwa yana da bargo na tantanin sauro a maimakon labule. Kujerun dakin jiran gwaji duk sun karya, sai murɗaƙƙen jini a kafet da iska mai wari. Duk da haka, shi ne asibitin da suke da shi. A nan Malam Sambo ya shigo da babur ɗinsa, yana ihu: “Ku taimaka! Ku ceci ta! zai mutu! Jariri yana fitowa!” Wata nurse – mai dogon hanci da rashin jinkai – ta fito da leda a hannu, ta dubi Kaltume daga gefe: “Kai... ashe wannan ce?! Waye ya ce a haifi a gida? Ta yi rajista kuwa?” Malam Sambo na haki kamar wanda zai faɗi: “Bani da rajista! Ku karɓe ta da gaggawa... wallahi ta mutu Amman yaron na motsi !” Sai wani dattijo malamin lafiya ya fito daga wani daki, yana watsa idanu da kausasa murya: “Mun gaji da wannan halin! Duk da gwamnati bata ba mu albashi ba, har yanzu ku zo da matan ku cikin jini, babu kati, babu kudi, babu rajista. Ku na so mu yi aiki da soyayya ne?!” Inna ta faɗi a ƙasa tana kuka: “Don Allah... mu talakawa ne. Katin ba mu da shi, amma ku taimaka. Ku ceci 'yata da jaririnta. Ta riga ta shure... amma ba a gama ba...” Nurse ɗin ta girgiza kai tana faɗa: “Wani likita ba zai taɓa tabawa ba idan ba katin haihuwa. Ko a ƙarƙashin bishiya ne aka haife ta. Wannan ba matsalar mu bace.” Yayin da su ke ta masifa, wata karamar ma’aikaciyar asibiti – mai sauƙin hali – ta leƙo, ta ga halin da Kaltume ke ciki. Sai ta fasa tsawa: “Koma menene, wannan jariri yana cikin rai! Idan kuka bari ya mutu, kun kashe shi da gangan! Bari in kira Likita Bashir. Wallahi, na shiga tsakani.” Ta nufi ɗaki da gudu. Yanzu dakin asibitin cike da mutane ne. Muryoyi sun rikice. Wasu na kuka, wasu na masifa. Malam Sambo yana zamewa daga jini, ya tsaya a gefe yana zubar da zufa. Rayuka biyu ne ke rataye da ƙaramin zaren kulawa da imani. haka wanan cooper ya shiga cikin office nin ya bashi dubu biyar da ban haƙuri domin a ceto wanan abinda yake cikin matar nan... Is just a beginning 🦎KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 PAGE 1 Paid book 300 only , posting daga Monday zuwa Friday in Sha Allah 08101235739 FREE PAGE NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️ 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI 08101235739 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE THREE *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Likita Bashir ya fito da hanzari cikin ɗamarwa, yana ta girgiza kai kamar zuciyarsa ta ƙi amincewa da abin da idonsa ke gani. “Ina marar lafiyar take?!” ya faɗa da ƙarfin da ya ɗauki hankalin duka cikin asibitin. Nurse ɗin da ta kira shi ta nuna wata ƙaramar ƙofa, jikinta na rawa da ɗuwatsu a ido. " can ne, Doctor... jini ne ke ta zuba kamar an buɗe rijiya...!”ba tare da wata tattaunawa ba, sai ya ɗaga hannunsa cikin hanzari, ya umarce su da su ɗauke mata da ake fama da ita zuwa ɗaya daga cikin tsofaffin ɗakunan haihuwa ɗakin nan cike yake da wari, gadon da ke cikinsa na daure da wayoyi, ya ruɓe, ruwan rijiya yana cicciko daga gefe, yana gauraye da jinin da bai daina fita ba. An shimfiɗa Kaltume hannayenta duk sun kumbura fuskarta fara ta kumbura kamar wacce aka ƙwace rai. Idanunta a rufe, bakinta bude kadan kamar mai neman taimako daga sama nurse biyu suka kama ƙafafunta da gaggawa suka buɗe su, yayin da Likita Bashir ya zura safar hannu, zuciyarsa cike da damuwa “mu ceci jariri... sai mu ceci wanda ba shi da laifi!” ya faɗa da huci, yana kai hannunsa cikin mahaifar Kaltume. Sai yaron ya fara motsawa, yana kokarin fitowa daga duniyar duhu amma jinin—jinin nan yana zuba kamar an karya madatsar ruwa nurse ɗaya ta tsayar da numfashinta, tana kallo da hawaye a idonta. “Tayi mutuwa,” wata daga cikinsu ta faɗa cikin sanyin murya mai tsanani “tayi mutuwa tun kafin a zo...” A ƙasan gadon, jini ya wuce ƙafa. Ya gauraye da ƙura, ya kumbura kamar ruwan sama da ba’a dafa ba jikinta na laushi, ba numfashi, ba motsi qmma cikin cikinta, ga rayuwa na ƙoƙarin fito da kukan farko. “Dokta, za a iya ceto yaron?” nurse ɗaya ta tambaya, murya na karkarwa. Likita Bashir ya runtse idanu, ya kalli gadon da bai dace da ɗan Adam ba ya kalli Kaltume, wannan marainiyar Allah da aka saki kamar dabba a kasuwa. Sai ya ce da zuciyar da take dukan azabar gaskiya “Zan yi iya bakin ƙoƙarina amma wannan ba haihuwa bace wannan ƙasa azaba ce, wannan haihuwa kuka ce!” Yayi ƙwace, ya jawo jaririn da ƙarfi hannunsa yana rawa, numfashinsa yana tashi da sauri. daga nesa, aka ji kukan wani yaro mai raɗaɗi, mai rauni, mai kukan ban kwana da duniyar da bai iso ba tukuna kukansa ya sare dakin gaba ɗaya dukkansu suka tsaya cak, da hawaye, da kaɗuwa, wannan yaro ba kawai ya zo duniya ba ne... ya zo ne da ihu, da baƙin ciki, da jini mai ɗumi, ya zo ne da alhini mai nauyin dutsen dutse. Inna ta durƙusa a ƙasa ta aza hannu a kai. wannan ba haihuwa bace – wani sabon babi ne a cikin littafin ƙaddara. Sai wani mutum – dogo, siriri, farin fata – ya faɗo cikin ɗakin da sauri. Likita ne, amma bakinsa kamar ya cika da al’ada ya karɓi yaron yana jijjigashi, yana kallo kamar yana karanta labarinsa ta fuska yron ya yi ihu... amma bai tsagaita ba kamar yana faɗin "ni ne wanda aka kore daga jinƙai, na fito daga cikin azaba... ni ne wanda duniya ba ta shirya karɓa ba..." Mutumin nan ya karɓi jaririn daga hannun likitan, hawaye na zubo masa “wannan yaro ba da wasa aka haife shi ba wannan... wannan shi ne Kaɗangaren Bakin Tulu!” “An barka ne, amma ba a barkar da murna ba. an kore ka, an fasa tulun da kake ciki, aka zubar da ruwan da ya kamata ya rike ka an zagaye ka da tsinuwa kafin ka ɗan sha iska. Amma Allah ya bar ka da numfashi!” Ya fito da yaron zuwa harabar jama’a. Ya ɗaga shi sama kamar ya nuna duniya cewa: “Ko ba a so shi ba, ya zo ko ba a shirya masa ba, ya fito wannan yaron... wannan yaro shine jarumin da ba a nemansa ba amma dole duniya ta karɓe shi!” Mallam Sambo – tsoho mai hangen nesa – ya karɓi jaririn da hannayen da suka girgiza. “Yaro namiji ne! ya fito da ihu! ya fito da ƙarfi da baƙin cikin rasa mahaifiyarsa a cikin zafin haihuwa ya zama Kaɗangaren Bakin Tulu! Tabbas... wannan wata aya ce, aya mai cike da darasi!” Yaron yana ta ihu, yana jijjiga hannu kamar yana faɗa da duniya da zarar ya shigo cikinta. jikinsa ƙururuwa ne, hannuwan sa kamar yana murɗa takobi ne cikin iska. Cooper ɗin likita, wanda ke rike da yaron, ya rungume shi da ƙarfi kamar yana ƙoƙarin ba shi ƙarfin rayuwa da ɗumi hawaye na gangarowa daga gefen fuskarsa, yana kallo cikin idon jaririn kamar yana neman amsar wata tambaya da zuciyarsa ta kasa bayarwa shekaru da dama. “An haife ka ne ba don ka zauna ba, Kaɗangare…” ya faɗa da siririyar murya. “An haife ka ne don ka girgiza tarihin waɗanda suka saba wulaƙanta marasa laifi.” Yaron ya yi kukan da ya tsayar da kowa cikinsa. Yana kallon sararin sama da ido da ba ya ganin komai wata tsohuwa mai suna Inna Uwaliya, tsohuwar unguzoma ce ta kauye, ta durƙusa gefen gadon inda gawar Kaltume take kwance. “Wannan haihuwa ce mai sako,” ta furta da bakin da ke rawar murya. “Wannan yaro... yaron da ba’a so ba ne amma baƙin tulu ya fasa kansa, ruwan da ke ciki ya fito da rana. Wannan yaron... zai ƙone da wuta, zai raba gaskiya da ƙarya!” Likita Bashir ya matso ya lulluɓe gawar Kaltume da farar zani ya juya yana hawaye, ya kalli nurse ɗin da ke kusa da shi. YACE ********* ABUJA Abuja — babban birni mai lulluɓe da kyalli, gine-gine masu ƙayatarwa, cike da gurbatacciyar iska mai ɗauke da kamshin arziki da sirri A cikin anguwar Asokoro, daga cikin jerin manyan gidajen gwamnati da jakadun kasashen waje, akwai wani gida wanda kallo ɗaya ka masa zaka san cewa kuɗi bai da daraja a ciki. Wannan gida ba kawai na gida ba ne Gida ne da ke da murmushin wadata, zuciyar iko, da ƙahon sirrika shi ne gidan Ministan Lafiya: Alhaji Abba. Gidan — mai matakai uku, rufinsa marmara ne na Turai, falonsa na ciki na cike da tagogi masu haske da tagulla, sai fitilun chandelier masu ƙyalli kamar rana cikin dar jikin bangon falon, hotuna ne na manyan mutane — shugabanni da ‘yan siyasa, da kuma wasu hotunan da ke ɓoye manyan al’amura da ke tafiya a bayan fage. A cikin wannan gidan kuwa akwai mutane guda biyar da rayuwarsu daban take — kowanne da nasa salo, da burinsa, da nishadinsa: 1. Alhaji Abba – Ministan Lafiya; dattijo mai mulki, mai iya ɓoye dariya da fushi a lokaci guda kallo

Chapter 1 of 11