Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
ɗaya ba zai nuna maka irin ƙarfin da ke cikin zuciyarsa ba Allah ya mallaka masa dukiya da baisan adaddin sa ba. 2. Hajiya Zulaihat – matarsa ta fari, wacce aka aura tun kafin ya samu minister mace mai kishi da son zuciya, tana rayuwa ne a cikin gida da duhu na siyasar mijinta. 3. Hajiya Maijidda – matarsa ta biyu, budurwa ce wacce aka aura bayan samun mulki. Kyakkyawa, mai juna biyu, tana rayuwa cikin jin daɗi da kewar wasu abubuwan da ba a faɗi. 4. Alhassan – ɗan’uwan Minista, wanda ke zama a gidan ba tare da aiki ba, amma yana cin arzikin gidan mai rainin hankali da shagube. 5. Khadija – 'yar gida, bai kai shekaru 20 ba. ba jini ba, amma tana cikin gidan saboda wata alaka da uwar gida. Kyakkyawa ce, amma tana rayuwa ne a cikin inuwa. A yau, suna zaune a babban falo suna karin kumallo. Wajen cike da pancake, toast, coffee, zaƙi, da kusan komai daga Turai, amma kallon da ke tsakanin su yana ɗauke da abubuwan da ba a faɗa. Rayuwa mai kayatarwa ce, amma kowa a ciki na ɗauke da wani sirri, wani fata, ko wani laifi da ba a bayyana ba kuma ko da yake suna zaman lafiya, wata rana... za su gamu da abinda zai girgiza tsarin su.... MUJEEE ZUWA WELCOME TO A NEW JOURNEY OF KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t FREE PAGE ... SHARE FISABILLILAHI 300 only 08101235739 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE FOUR 4 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) PAGE FOUR 4 Asuba ta gabato da sanyi da ƙamshin ganyen lemongrass da aka yayyafa a falo domin dāƙile ƙamshin daddare. Amman cikin zuciyar Hajiya Maijidda — mace mai ciki — sanyi ba ya wanzuwa raɗaɗin cikinta da naƙuda yana tashi yana sauka kamar walƙiya a ɗakin da babu haske. Ministan Lafiya, mijinta, yana can Lagos ya bar gida da jiya don taron kwamitin lafiya na ƙasa ba wanda ya ɗauka zai faru ba shi ba. A lokacin da ya tafi, naƙuda bata da alamar kusa. Amma yau “Wayyo Allah... yallabaiii...!” “Ciki... yana karkarwa... kamar ruwa mai tafasa...” Sai gaban motar gida ya ɗan kaɗa – nurse ɗin da aka kira ya ta iso da ƙyar. Xulaihah, uwargida, ta tsaya a ƙofar falon manya, fuska ɗaure kamar wacce ta gaji da hakuri. “Kada ki shige cikin gidan nan da ambulance. Wannan haihuwa ba zai bar wannan gida ba. In yaro ne ke ciki – sai ya mutu kafin ya sha iska.” Ummi mai duba lafiyar gida, ta tsaya da hargowa. “Hajiya, ai ciki ba a raina masa mutuwa! wannan ba adalci bane. Ko kina tunanin Allah zai zuba ido...?” Zulaihah ta zuba mata harara mai zafi. “Allah da muke kira shi ne na ba ni ɗa — ke kuma kina son a kwace shi daga wurina. Don an ce namiji yana ƙara daraja, da dukiya a gado sai ki ce sai an haife shi...?” Gidansu Minista yana ɗauke da sirri an ce Idan mace ta haifi ɗa namiji a cikin gidan, tana samun cikon gida, gwal , iko da tabbaci a zamanta. Shi yasa Maijidda, da ta haifi mace ta farko kuma ta rasu, take fatan wannan ciki zai dawo mata da ƙima. Amma Zulaihah — bayan sunan uwargida, tana da jinin namiji. Ɗanta, Majeed, yana shekaru goma sha biyar yan gidansu sun fi nuna masa kulawa, Minista ya fi yarda da shi. Yanzu kuma... ana zargin cikin Maijidda zai iya zama ɗa namiji. Zulaihah ta kira wasu daga cikin maidens nata, suka ɗauko wata ƙaramar sanda da ruwan zafi, suka ce: “Muna iya ɗaukar ciki da taimakon zafi da matsa cikin hanji. Hakan ba saba wa doka bane — ba asibiti, ba 'yan jarida...” Umme ta zazzaro ido. “Hajiya! Wannan kisan kai ne fa!” Sai Zulaihah ta ce cikin siririyar murya: “To ki zabi — a haife da sunan ni ce uwargida kuma in koma gefe? Ko in kare gadona kafin su janye min kujera?” Wata mai aiki, mai suna Latifah, ta durƙusa a ƙasan gado, tana share zufar Maijidda da kyakyawar kyalle. “Wallahi idan wannan jariri na mace ne, zamu tuba — amma idan ɗa ne... ya kamata ki ɓoye shi. Ko in taya ki... mu gudu da shi.” Maijidda ta ji kalmomin a cikin firgici, numfashinta na tsinke kamar mai jin karar mutuwa. Kiran asuba na ta ƙoƙarin fasa duhun dare da salati, amma a cikin babban gidan Ministan Lafiya, wani irin duhu ya mamaye zuciyoyin da ke cikinsa fiye da na dare. Hajiya Maijidda – mai ciki, tana kwance cikin zafin naƙuda, tana kiran Allah da numfashi mai sarkewa: “Ya Allah... Na shiga tsanani... Ku taimake ni… ya Rabbi...” Sai wata murya mai sanyi da duhu ta dawo da ita daga tunanin ceto:ma “Taimako ba ya nan. Ki haifi jaririnki — idan Allah ya so mace ne, zamu bar ki da rai. Idan namiji ne... toh, kiyi sallama da duniya da ke da yaron da zaki haifo .” Tana ƙoƙarin tashi da kuka tana neman ƙofa, sai tayi ido hudu da Hajiya Zulaihat, uwargidan da ke kallonta da sanyi amma idanu cike da ƙiyayya. A bayanta kuwa, ƴan aikin Xulaihah ce Hannun su na riƙe da ruwan zafi da abin nade kai. A gefe ɗaya kuma, Nurse Umme ta ke tsaye a jijjiga, amma da bindigar gwiwa a kanta! “Ki motsa ki kira ambulance, ki gwada kaita asibiti — wallahi sai kin gane wannan cikin ya fi ki muhimmanci!” Zulaiha ta faɗa cikin zafin kishi, tana wani mika ƙafafu kamar zakanya. Nurse Umee ta fashe da kuka: “Amma Hajiya... zafi take ji… ciwo! wataƙila ciki ne ke kusa fashewa! Wannan zubar da jini ba alama ce mai kyau ba tana da matsalar haihuwa !” Zulaihat ta sake matsar da bindiga, ta ce: “Ki tsaya mu gani duk wanda ya yi motsi sai dai a fitar da shi da gawa cikin nan zai haifu a nan mu gane ko Allah zai bar ni da sarkin gida ko wata ’yar gata ce zata kwace gareni.” Maijidda tana kwance – hannunta yana ƙoƙarin shan numfashi, idonta sun yi jajir, jinin zufa da hawaye na gauraye da jini daga kasanta. “Ku taimake ni... don Allah... ku ce masa bana neman matsayi... bana neman gado... bana neman komai! Sai dai in haifi nawa!” Amma kowacce murya da ta fito daga bakinta sai ta tashi ne a cikin dakin da zuciyoyi sun mutu da rahama. Sai aka ji wata shigowa — yaron ƙarami Abdul-Majeed, ɗan Zulaihat, ya shigo da sanda yana kallon uwar Maijidda cikin jini. Ya ce: “Mommy Me yasa tana kuka haka?” Zulaihat ta kalle shi, ta ɓoye bindigar hannun ta “Domin tana so ta kwace gidanmu ne, ta haifi ɗan da zai sa ku manta da kai. Amma Allah bai yadda ba. Ka tafi ɗakinka babo wanda zai ƙwace maka matsayin ka a gidan muddin ina numfashi , Nurse Ummee ta fashe da kuka, ta jefar da duk wata tsoro. Ta ce: “Ni ba zan ƙare da rayuwa a haka ba wannan jaririn zai fito, in har ina numfashi!” Amma kafin ta ƙarasa zuwa kusa da Maijidda Zulaihat ta sauke yatsa kan bindiga! TATT! An ji ƙaramin harbi — ba kai tsaye ba, amma an harba kusa da ƙafarta. “Wallahi zata sake haihuwa , yanzu ne! Cikin nan yana fitowa da yardar Allah!!”sai wani abu ya faru wanda ya gigita kowanne numfashi a dakin: Jinin haihuwa ya ɓarke! Ya zubo kamar ruwan rijiya, ya ratsa zanin da ke ƙasan Maijidda, ya haɗu da gumi da zufa. “Ku taimake ni... Allah... ku ce masa… ban mutu saboda soyayya ba… na mutu ne don na yarda da ƙaddara!” Nurse Ummee ta fasa kuka sosai, ta zare hijabi ta nade hannunta Sai wata murya mai ƙarfi ta bugo daga ƙasa cikin ƙirjin Maijidda: “Uhhh... uhhh... yaa Allahhhh!” Sai kuma ƙaran kuka — kukan jariri! Na farko, sai na biyu — amma ɗaya daga cikinsu yana cikin jini sosai. Jariri biyu! Namiji... da mace. Zulaihat ta tsaya cak. Hannunta ya ɗauke da bindiga amma zuciyarta ta firgita. “Me? ta haifi... biyu?!” Nurse Ummee ta dube ta da kallo na tausayin banza: “Ke kadai kika haifi ɗa. Amma wannan matar ta haifi kaɗangaren bakin tulu — biyu ne! Kuma duka suna numfashi.” Zulaihat ta zube a kujera a daidai lokacin, an ji ƙarar buɗe ƙofa — motar asibiti ta iso daga ƙofar waje! Amma kafin su isa — Maijidda ta kalli jariranta, ta fashe da ƙara mai sanyi. Sai ta ce da numfashi na ƙarshe: Nurse Ummee ta daure gwiwa, ta jawo jarirai biyu, ta share musu fuska da jinin uwarsu. Sai ta dora su a ƙirjin Maijidda da hannuwanta da ke rawa da sanyi. “Ki riƙe su... sun riga sun fito Maijidda... ki sumbaci rayuwarki a cikin su.” Maijidda ta kama su, ta rungume jariran da sauran ƙarfinta, sai ta fashe da kuka da dariya a lokaci guda. Idonta cike da hawaye, zuciyarta cike da azaba. Ta ɗaga ɗan namijin da hannunta yana rawa, sai ta ce da karamin murya: “Kai ne... kai ne Kaɗangaren Bakin Tulu... Na haife ka a gaban maƙiyanka... sun kashe ni, amma ba za su kashe kai ba! Zan mutu ba tare da jin daɗin uwa ba... amma zan bar musu KAƊANGARE...” Ta kalli Nurse Ummee da murmushi, ta ce: “Ke ce mataimakiyar Kaɗangare... karki bar su cutar da shi... karki bar su ce ba zai rayu ba...” “Ke ce masa... bana son ya zama mara haƙuri da juriya sai dai idan zai warke da haƙuri TABBAS NA HAIFO IDON DUNIYA NA HAIFU KAƊANGAREN BAKIN TULU na haifu ka a gaban maƙiyan ka .” Idanunta sun lumshe... jikinta yayi sanyi. Sai Nurse Ummee ta fashe da kuka: “Maijidda ta mutu... amma ta bar mana jarirai biyu — kaɗangaren bakin tulu. Daya zai yi sanyi kamar uwarsa… ɗaya zai ƙona... kamar yadda gidan nan ke ƙonewa yanzu...” Sai dai kafin Ummee ta amsa, wata ƙara ta bugu! TAW!! Bindiga. Jariran sun karye daga hannunta! Nurse Ummee ta juyo da hanzari — Zulaihah ce, ta harbe iska .. sai ta bindiga taye akan yaran dukkan biyu kuwa ya tsaya chakk jikinsa ya saki. Tayi shiru amma kafin wani ya motsa, an ji karamin murya daga bakin kofar: “Oyooo Daddy! Yaaa Daddy!!” MAJEED ne, ƙaramin yaron gidan — ya shigo da dariya da nishadi. Zulaihah ta rikice! Ta jefa bindigar a bayan labule, sai ta ce cikin dukan zuciya: “Duk wacce ta ce magana akan wannan... sai dai ta rasa rai! wallahi zan sa a kasheta kamar itama Maijidda!!” Kafin kowa ya ƙarasa wani motsi — an ji ƙarar siren ambulance. Minista ya shigo da ƙarfi da jami’an tsoro masu mara masa baya don su ji ƙarar abu yaran kuwa ihu sukiye wanda ya karaɗe dukkan gidan . Kallon da yayi wa Zulaihah kamar ya fi kisa: “Ina matata?! Ina Maijidda?!” Ummee ta miƙa jariran biyu da hawaye, ta ce: Ta haihu biyu ita kuma ta mutu cikin azaba Minista ya ɗauki numfashi da ɓacin rai — sannan ya juya. Abu ya canza. Rayuwa zata canza. 🥀 Idan Maijidda ta mutu — to da rayuwarta aka rubuta babin farko. Kadangaren Bakin Tulu ya zo. Amma wa zai tsare shi daga guba, kiyayya da mugunta a gidan da aka haife shi? Is just instructions har yanzu ba'a fara labarin ba mujee zuwa free page is going Godiya mai tarin yawa ga masu mun fatan alheri Allah ya saka da dubbun alkaire daram daram tsakani na daku mujee zuwa KAƊANGAREN BAKIN TULU NA BIYU YA Bayyana a Birnin Abuja.. 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/LJDc3GDF3Kt3wo6Mp1Bl17?mode=ac_t بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE FIVE 5 300 only FREE PAGE 08101235739 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) PAGE FIVE 5 ( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕). TSIBIRI Cikin duhun dare da sanyin iska, wata mata tana gudu cikin dajin yankin Maiduguri. Ƙafafunta cike da ƙura da jini, ciki kuma na ƙaton ciki yana girgiza tamkar zai fito kamar wacce ta ratsa azaba, tana ta rawar jiki tana duban baya lokaci-lokaci. "Allah Ka kare ni da abin cikin nan… Allah ka cece mu daga hannun su…" ya faɗa da karamin murya yayin da hawaye suka haɗu da zufa a kumatunta. A lokacin da ta iso gaban kogin Bula, sai ta tsaya ta shaƙi iska – tana ƙoƙarin cewa da kyar ta iso amma karar bindiga ta sake girgiza gabobinta. sai gashi TSAA!! an harbe ta a tsakiyar bayan ta , jinin ya ƙara zuba daga ƙafarta – amma bata tsaya ba, tana ƙoƙarin kare cikin cikinta. Da wani kishi mai ban mamaki, sai kawai ta faɗa cikin kogin tsunduma, ruwa ya ɗauketa da sauri ya niste ta zuwa cikin duhu da ruwan kogin… Ba da jimawa ba, motar jeep mai baƙin gilashi ta tsaya a gefen dajin sai wasu mutane uku masu sanye da baƙin kaya, suka fito, fuskar su a rufe da baƙin mayafi suka tsaya a bakin kogin, ɗaya daga cikinsu ya kalli cikin kogin sannan ya ɗaga waya: Yallaɓai mun kammala aikin mun kawar da ita da abin cikin ta ko gawar ta baza a tsinta ba." sai suka koma motarsu suka bar wuri cikin gaggawa, yayin da kogin ke ci gaba da kwarara da sirrin da yake ɗauke da shi… ( Amma a cikin ruwan kogin akwai tsarkakken jariri wanda Allah ya tanada masa tsira zai rayu, ko da kuwa ba a san yadda ba tukuna. Wannan shine Kaɗangaren Sarauta – wanda ba ruwa, ba bindiga, ba makircin duniya zai iya hana sa bayyanar da ƙaddararsa. ) Tsssshhhhh... Karar ruwan teku yana bugawa da ƙaƙƙarfan dutse a bakin wani tsibiri da ba a tasamma — babu kowa a kusa, sai tsuntsaye masu fari da baki suna shawagi sama, suna kururuwa tamkar suna shaida wani sirrin da duniya ba ta sani ba. A can cikin kwarin kogin, wata mata mai ciki ta farka daga dogon suma, ta gaji, jiki ƙalau. sai ta buɗe idonta da ƙyar, tana kallon rana mai taɓa gashinta mai danshi jiki na rawa, ta fara motsi, tana jin zafin ciki da naƙuda. A lokacin da numfashinta ke yin nauyi kamar zata shude, sai kawai aka fara hango tsohuwar mata mai farar kaya tana karasowa daga cikin ƙasar tsibirin. Fuskarta cike da natsuwa, kamar ba ta da tarihin duniya, kamar kuwa aljana ce ta bakin ruwa, annuri ya lullube ta. Ta ƙarasa wajen matar da ke buƙatar taimako, ta durƙusa, ta ce da ita "ki zauna... kar ki tsorata. Allah na tare da ke. Lokacin haihuwa ya yi, kuma wannan ɗa ba zubin azzalumai bane — jarumin ƙasa ne da murya mai ƙarfi." Cikin hanzari da tausayi, tsohuwar ta taimaka mata – sai aka ji kuka... kuka mai ƙarfi, wanda ya sa tsuntsaye suka firfito daga duk inda suka buya. Jaririn da aka haifa namiji ne – mai cikakken lafiya da farin fata, kamar haske a cikin duhu sai matar ta ɗaga shi sama – hawayen farin ciki a idonta, jikinta rawa, jini yana ƙara zuba daga kafarta, ta ce: "Na haifu KAƊANGAREN BAKIN TULU! Ko ana so ko ba a so… watarana zaka tsaya cikin alfahari ka hana zalunci da murya ka." "Ina fatan ka zama cikakken ɗan jarida – ka daga muryarka a gaban duniya da masarautar ku, har kogin ya rabe biyu daga ƙarfinka. Ka zama farin cikin masu shiru da mafitar masu rauni." Sai ta lumshe ido, ta miƙa jaririn ga tsohuwar, sannan ta faɗi – numfashinta na ƙarshe. Ruwa ya tsaya kamar yana girmama jarumar da ta kawo ɗan ƙasa duniyarta. Tsohuwar ta ɗaga sa sama cikin kururuwa ta tace na saka maka suna SUHAYL yakai bil adama ta shige da jaririn ciki tsibiri… ba a ƙara ganinta ba 🌊 KAƊANGAREN TSIBIRI / SARAUTA Suna: Suhayl Ma’ana: Tauraro mai haske daga cikin duhu Halinsa: Rayuwarsa cike da asiri da wahala. An haife shi a bakin kogi, mahaifiyarsa ta faɗa ruwa bayan an harbe ta. Zai zama ɗan jarida mai zamewa murya ga marasa murya, kuma zai tunkari masarauta da kalmar gaskiya. Shin ya kuke tunanin rayuwar sa zai kasance tsakanin aljannu da namun daji .. shin burin mahaifiyar sa zai cika? shin waye shi ? me asalin labarin jinin sa ? Ina muku barka da juma'a 08101235739 🦎🦎 KAƊANGAREN BAKIN TULU 🦎 🦎 BY NARNAH ƘANWAR SOJA Follow my Wattsp group 👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/C1fwfKiUPGgJQTONvJGjqN?mode=ac_t بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين والحمد لله رب العالمين ♥️ PAGE SIX 300 only FREE PAGE 08101235739 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) PAGE SIX 6 ( Akwai wacce ta biya kuɗi banyi save number ta ba and I don't know u at all idan kinga post nan DM Please Wattsp na yayi disappeared thank you 💕). Happy birthday 🎉 to my lovely big brother Allah ya ƙara shekaru masu albarka da amfani more more money in ur bank account.. 25 august.. GARGAƊI Ban yarda ba , kuma ban amince a juya min labari ko a sauya ta zuwa audio ba tare da amincewa ta ba , GAISUWA Gaisuwa na musamman ga masoyyiya ta a bar alhafari ba sister Habiba Ubangiji na tare dake a dukkanin motsin ke da shirun ke.. KANO A cikin ƙasar Kano, a gindin duwatsu masu launin toka, a bakin goggin da ke fitar da iska mai sa sanyi ta huci da dare, akwai ƙauye da lokaci ya ci—amma bai jefar da mutanensa ba. Sunansa: Gidan Rini. Ƙauyen da gwamnati ta manta da shi, da bishiyoyi suka maye gurbin gine-gine, da rijiya ce kaɗai ke zama asibiti, da masallaci ya zama gindin bishiya. A nan ne ake haifar rayuka da ake kawar da su kafin su futo duniya gaba ɗaya. Mallam Sambo ya kura musu ido. Bai ce komai ba. Sai kawai ya rungumi jaririn da ƙarfi kamar yana kare masa duniyar da ta riga ta bijiro da masa da zafi. Zan baka suna Bashir domin ka kasance mai bushara a wanan rayuwar muna godiya ga likita Bashir da ya fito dakai wanan duniyar da taimakon Ubangijin Halitta,, nan Baaaba ta juya da bakin ciki da takaice da sasaqesaqeen abinda zuciyar ta ke gayama ta akan wanan yaron da ta so kashewa tun a cikin mahaifiyar sa . Nan Inna ma ta kama hanyar ta kai tsaye sai wani ruɓaɓen Police station nasu wanda bashi da bambanci da kasuwa mai ɗakunan mashaya da ƴan chacha da zuwan ta taga Audu zaune yana cin kurasa da ganin ta ya miƙi " Inna me ya faru a asibitin" hararra ta buga mai da cewa " ita wanchan ta mutu Amman ta bar yaro mai ban mamaki kamar ba kaine uban sa ba jajajjur dashi kamar uwar sa " nan wani mai uniform na ƴan sanda yazo yace Yaya mekekeso goron bakin ta ta zubar a kusa dashi " to Mallam ɗan sanda abinda aka saba shine yanzu ma ka gayyamin nawa zamu baka ka kashe wanan maganar dukkan ta kawai yayi Amman bai kashe ta ba lokacin ta ne yayi " girgiza kan sa yayi yasan hakan zai faru daman nan yaja tumbin sa da ya zaxzzago yana waige waige ya matsu kusa da kunnen ya " ke kawo dubu goma yanzu sai ku tafe gida " zaro ido taye waje Amman kaima ka fara shaye shaye ko to ko sata zanyi ai banga wanan uban kuɗin ba ". tsaki yaja " kedai anyi tsohuwar banza yaron ke yayi kissan kai zamu rufa masa asiri kicce wai bazaki iya ba to zan kira shugaban mu nawan nan qara mar hukuman....................kai malam dan sanda kai meya sa baka iya magana haka ba karufa min asiri duk inda zan shiga zan fita zan nemo maka dubu goma don ka sake min yarona don shi kadai na mallaka malam audu bawa ni bayan shi duk duniyan nan......................." Cikin azama da gaggawa ta fita tana azama ta zazzago akuyar gidan su tayi wojen malam jauro har tintub be takeyi yi tana qwala kira hakan yasa Malam Jauro ya fito da ga bukkar bayan gida daga jin Salaman Inna yasan me ya kawo ta, " kai Jauro muyi ciniki nawa zaka seya haba innar audu ko gaisuwa babu abu ne na gaggawa ya tashi.............sai yace ya maganar gawan kultume an dawo da ita duk cikina na ciwo na dawo gida,? kaga Jauro ba wannan ya kawo ni ba na kawo maka akuyar sayarwa ne kaban dubu goma ko rance ne ka aramin ga akuyar nan " yace to Allah ya kyauta" ..................bai jima da shiga ba yafito da ɗan kuɗaɗen sa bayan ya rataya akuyar cikin tumakin sa ************* A guje ta shigo police station in ko sallama babo takalmin ta a hannu sai dogon hali takiyin cikin azama Mallam ɗan sanda ya fara lashe baki ganin ta dawo da wuri don tabbas yau akwai dabkee a gidan sa .. tana bashi wanan kudin ya ɗirgasu

Chapter 2 of 11