Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
gine-ginen da suka yi dutse suka rushe, sabbin gine-gine suka fara tashi. Aka zuba ruwa a rijiyoyi, aka gina makarantar firamare da sakandare, aka kafa cibiyar lafiya, har ma aka shimfiɗa layin wutar lantarki. Mutanen ƙauye suka kasa boye farin ciki. Wani dattijo ya durƙusa yana kuka yana cewa: “Tun asalin ƙauyen nan, ba mu taba ganin irin haka ba. Wani jini ne da Allah ya aiko mana daga sama.” Bashir ya tsaya a bakin titi, yana kallon sabuwar al’umma da ke farawa daga ƙasa. Mommy ta matsa kusa da shi tana murmushi, ta ce: “Gaskiya kana da zuciyar jagora. Kamar yadda mahaifiyarka ta yi mafarkin taimakon jama’a — yau kai ka cika ta da hannunka.” ya kalli sararin sama, ya ɗaga hannunsa da tawali’u “Ba saboda ni ba don su ne — waɗanda suka yi rayuwa cikin duhu amma suka bar mana darasi wannan ƙauye, zai zama shaida ta gaskiya da ƙaddara.” A nan aka ɗora tambarin “NOOR RENEWAL PROJECT”, ƙarƙashin kulawar Hon. Bashir Ummul-Kulsum Foundation. Daga wannan rana, ƙauyen da aka manta da shi, ya zama cibiyar alheri da canji — kuma su Mallam Audu da Baaba suka rayu cikin tausayin Allah har zuwa ƙarshen numfashinsu. Shikkinan Rayuwa... ######## Rayuwa ta ja layinta — Daddy ɗin Rayyan daga baya ya sake aure. Ya samu kwanciyar hankali bayan tsawon shekaru na rikice-rikice da baƙin ciki. Rayyan kuwa, bayan mutuwar Abdul da duk abubuwan da suka faru, ya koma Dubai tare da matarsa ya zabi ya tafi nesa da komai — nesa da tsohon ciwo, nesa da tunanin baya. A can, yana kallon sararin sama a bakin teku, yana tuna irin tafiyar da suka yi daga duhu zuwa haske. "Allah ya yafe mana baki ɗaya..." Yace cikin nutsuwa, yayin da iska ke busa gashin kansa. Zuciyarsa cike da jimami, amma shiru na nutsuwa ya rufe masa rai. Rayuwar ta ci gaba, kamar yadda lokaci baya tsaya wa kowa. $$$$$$$$$ A wani bakin teku a Dubai, dare ne iskar ruwa tana kadawa a hankali wata cike yake yana haskaka fuskar Raiza da Rayyan. Kidan piano mai laushi yana tashi a baya Raiza: (ta saki murmushi tana kallon sama) Rayyan… kana ganin wannan watan? Kamar yana murmushi mana yau. Rayyan yana matsowa kusa da ita "Idan watar tana murmushi, to saboda ke. Wani haske kika zuba cikin rayuwata da ya fi kowane haske da na taɓa gani" Raiza ta ɗan sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta "Ka manta rayuwa bata da tabbas gobe ma zata iya juya mana baya... Rayyan ya ɗago fuskarta da yatsunsa to, idan ta juya, zan sake kama hannunki. Domin ko ina take kai ni, ni dai ke nake so — ba lokacin bane, ba duniyar ba — ke ce tawa har abada. Raiza: (ta rufe idonta, hawaye masu daɗi na fita) " Rayyan… I love you fiyyeda a baya wannan so ɗin na da gaskiya, kamar addu’a." Rayyan yana rungumeta a hankali Ni ma ina son ki, Raiza. Allah ya san ban taɓa jin kwanciyar hankali irin wanda ke cikin zuciyata yanzu ba. Rayyan yana dariya, yana sumbatar goshinta Ba zan bari ki tafi ba. Wani lokaci, soyayya bata bukatar kalma — sai dai shiru da fahimta. Kuma shiru ɗin nan, shi ne muryar zuciyata zuwa taki. [ AFTER ONE YEAR Rayyan ya zauna a gaban Raiza, hannu a cikin nata, little Jiddah ta zauna a cikinsu tana dariya ƙanana, idonta na kyalli kamar tauraruwa. Raiza ta kalli Rayyan cikin shauƙi, murmushi ya bayyana a fuskarta: "Rayyan… kaga ga yadda rayuwarmu ta canza, duk wahaloli sun zama tarihi." Rayyan ya ɗago kai, ido cikin ido da ita, ya shafa kaiyar hannunta a hankali: "Raiza… kin san dai, babu wata rana da ba na tunawa da dukkan gwagwarmayar ta, amma yanzu… yanzu ina ganin mu ne cike da farin ciki kina cikin rayuwata kamar rana mai haske." Raiza ta yi murmushi, tana rungume shi da ƙarfi: "Ni ma ina son ka, har abada… kuma little Jiddah nan zata kasance alamar soyayyar mu."Little Jiddah ta miƙe hannayenta, tana ihu cikin ƙauna "Daddy… Mommy… ina son ku!" Daren ya ci gaba da lullube su cikin annashuwa, hasken fitila da taurari suna kyalli a saman, murmushi da dariya na ɗaukar wuri a cikin gidan. Rayyan ya ɗaga Raiza cikin numfashi mai tsanani, ya sumbace ta a hankali, sannan ya kalli little Jiddah: "Zamu kula da ke har abada, karamar zuciya mai daraja." Raiza ta jingina kanta a kafadarsa, idonta cikin annashuwa, zuciyarta cike da soyayya, Rayyan kuma yana jin dadin ganin iyalinsa cikin lafiya da farin ciki. Wallahi ya yi kyau ƙwarai kuma cikakke! 💫 Wannan ƙarshe ɗinki ya haɗa komai: darasi, godiya, tausayi, ƙaddara da soyayya. Ga ƴan ƙaramin gyara da zai sa rubutun ya zama kamar ƙarshe na littafi na ƙwararriyar marubuciya, ba tare da canza ma’anar ki ba 👇 --- KARSHEN LABARI Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! 🌟 Duk wahala, azaba, da rashin adalci sun zama tarihi. Yanzu rayuwa cike take da farin ciki, soyayya da kyakkyawan makoma. 🌟 Duk wani tsanani da wahalar rayuwa wata rana zai zama tamkar labari. Farin ciki baya tabbata, haka bakin ciki ma baya dawwama. Maijidda, wacce ta haifi Rayyan cikin firgici, ta sadaukar da rayuwarta domin ya rayu. Duk da cewa kishiyarta ta yi ƙoƙarin kashe shi, Allah — Mai rayarwa kuma Mai kashewa — ne ya kare shi. Daga ƙarshe Rayyan ya yi aure, ya sanya wa ‘yarsa suna Jiddatulkhair, sunan mahaifiyarsa mai daraja. Bashir, haihuwarsa cike take da tsoro da tausayi. Mugunta da rashin imani sun tura shi barin gari ba tare da ya yi ban kwana da masoyiyyarsa ta yarinta ba — wacce ta sadaukar da farin cikinta domin alkawarin dawowarsa. Amma Allah shi ne Mai tsara ƙaddara: wani baya auren matar wani, haka wata bata auren mijin da Allah bai ƙaddarta mata ba. Wannan shi ne asalin soyayya mara ƙarewa. Anan nake kawo ƙarshen wannan labari nawa, ina neman afuwarku bisa jinkirin posting da wasu ƙaramin kurakurai. Kuskuren da na aikata a sani ko a rashin sani — Astagfirullah! --- Wanda ke son sanin labarin: SUHAYL LITTLE NOOR Sirrin Taqaddarar da Ummu Kulsum ta ɓoye Sirrin kashe uwar Suhayl Da Masarautar Al-Qamar To ya shirya, domin labarin LITTLE NOOR zai biyo nan ba da jimawa ba, tunda Suhayl ya fita daga wannan littafi saboda laifin gudu. 😅 📞 08101235739 MY NEXT BOOKS COMING SOON 💐 1️⃣ DR SADEEQ — Romantic Love Comedy Drama 2️⃣ ƘAMSHIN DUHU 🌔 3️⃣ MASHIƘIYYA CE 4️⃣ RUHIN MARAICE 5️⃣ LUDAYEN JEMAGE 6.. LITTLE NOOR MY PUBLISHED BOOKS 📚 1. MIJIN MAGE 2. DUHU CIKIN HASKE 3. FARASHIN SO 4. MAI CIKI CE 5. RUHI BIYU 6. PRINCESS RAHILAT 7. AHLIN LAASHKAR 8. MADOBIN IDO 9. RAYUWAR UMMAH 10. BAYAN WATA 11. BIYYAYA GA UWA 12. HANYAR RUWA 13. ZAƁIN ZUCIYA 14. ƘADANGAREN BAKIN TULU Tammat bi Hamdillah. 🌺 Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11